Bakar Inuwa 10


 *_Episode 10_*



.............*_WASHE GARI_* shugaban ƙasa yay waya da god father nasu na siyasa dake faɗa aji a ƙasar baki ɗaya, sai dai a siyasance babu mai iya jin sunayensu. Ya sanar musu dukanin tsare-tsarensu. Sosai nasu tsarin yay masa shima harya yaba musu, dan yasan

komai sai dai suna bayan fagene, ya kuma tabbatar musu komai zai tafi dai-dai dan Alhaji Hameed Taura a tafin hannunsu yake.

      Cikin farin cikin yabon da shugaban ƙasa ya samu yace, “Na gode ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma da ɗaukaka. Badan ku ba babu mai ganin koda hotonmu a ƙasar nan. Shiyyasa muke addu'ar tsahon rai a gareku domin muyita cin karenmu babu babbaka”. (Ashe kasan shi mai mutuwane, rayuwarsa mai ƙarewace excellency. Inhar kuwa zai mutu to bai isa amfana maka komaiba face wanda yazo cikin ƙaddarar duk wanda kuka hara. ALLAH ka bamu shugabanni na gari🙏🏻🤦🏻).

     Bayan ya gama masa kirari da yabon dake sake buɗa masa kai ya ɗora da bayanin...

      “Ranka ya daɗe a yanzu haka mun gama yanke shawarar ganawa da shi yaron kawai muji ta bakinsa shima”.

      “Tunani mai ƙyau, sai naji ku”. Daga haka ya yanke wayar. Shugaban ƙasa ya cireta a kunnensa yana jan kakkauran tsaki da ballama wayar harara. Cikin ƙunƙuni yace, “Mugu ƴan hana ruwa gudu, ALLAH dai ya kusa kasheku muma mu babake ko'ina, daga sama har ƙasan ta zama tamu. Dan badan kuba da mune taurarin duniya ta kowanne fanni.”

      

(Kai jama'a kamar bashi bane ya gama masa ƴar murya yanzun🤣, siyasa shegiya😂).


*_TAURA HOUSE_*


        Kamar yanda al'adun ƙasashen da  hausawa yake dama musulinci baki ɗaya, irin wannan lokacin ko nace wannan ranar ranakune masu muhimmanci na shirye-shiryen bikin salla. Tamkar kowanne gida dake shiri haka Taura family house ma keyi ƙwansu da kwarkwata. Danko duk ƴammatan gidan zaka gansu da zanen lalle baƙi ko ja. Wasu sunyi kitso wasu gyaran gashi kawai. Hakama matan Alhaji Basheer Hameed Taura babu koma baya dan duk ɗinsu ƴan gayu ne kuma ƴaƴan manya, dan kowacce tana alfahari da irin gidan data fito ne.

      Misalin ƙarfe tara na dare da yay dai-dai da sanarwar ganin jinjirin watan shawwal daga bakin mai girma sarkin musulmi ƙararrawar dake sanar da taron meeting na iya manyan gidan ta kaɗa. Ba sabon abu bane hakan a duk daren kowacce salla, sai dai a wannan karon taron meeting ɗin yazo da banbanci. Sakamakon manyan gidan kawai ake buƙata banda yara.

     Cikin tunani da taraddadin lafiya duka matan Alhaji Basheer Hameed Taura suka kimtsa kawunansu zuwa sashen surukan nasu domin amsa kira. Sai tsoffi guda biyu da suka kasance ƙanne ga Alhaji Hameed Taura da suma suke zaune a gidan a halin yanzun. Sai ƙanin Alhaji Hameed Taura ɗin autansu da ya iso da iyalansa daga ƙasar Dubai a daren jiya domin halartar bikin salla da sukanzo a kowacce shekara...

            

          Duk wani wanda ake buƙatar gani a katafaren falon na alfarma da an tsarasane kawai domin gudar da meeting na ahalin gidan ya iso. Kowa ka gani zaune yake cikin mutuntawa ga dattijo Alhaji Hameed Taura da matarsa Anne. Dan dukan matan Alhaji Basheer kansu a ƙasa yake kasancewar suna gaban surukai.

    Bayan an buɗe taro da addu'a Alhaji Hameed Taura da ahalin gidan ke kira da suna Bappi yay gyaran murya da tasaka kowa sake nutsuwa a wajen.

      “Da farko dai ina tayamu murnar ganin wannan wata na shawwal da rai da lafiya. Ina roƙon UBANGIJI ya amshi ibadunmu da mukayi, ya yafe mana kura-kuranmu. Yasa muna da rabon ganin na gaba da rai da lafiya.”

     A tare suka amsa da (amina).

    Ya cigaba da faɗin, “Nasan zakuyi mamakin canzawar zaman meeting ɗin yau, dalilin hakan kuwa ya dangantane ga Ramadhan kacokal”.

     Da dauri Gimbiya Su'adah da yaran ke kira da (Maa) ta ɗago jin an ambaci sunan gudan jininta mafi soyuwa. Yayinda firgici da taraddadi ya bayyana cikin ƙyawawan idanunta. Dan batason mi kuma ya samu Ramadhan ɗin ba koya aikata. Tunda yau kusan satinsu biyu rabon da suyi waya sakamakon ta masa maganar ya daure yazo musu salla gida......

        .... ya katse mata tunani da cigaba da faɗin, “Wani babban al'amarine ya tasoma gidan nan, sai dai mun ɗaukesa kacokan mun rataya ga shi Ramadhan saboda wasu dalilai. Na farko yin hakan zaisa ya dawo kusa damu dole. Na biyu zaisa yazo shima yay aure. Na uku ya isar da abubuwan da muka kasa isarwa ga sauran mutane bisa ga abinda ALLAH ya azurtamu da shi.”

     Duk da a dunƙule yay dukan bayanin hakan bai hana farin ciki bayyana a fuskar Maa ba. Ji take tamkar Bappi ya mata albishir ne da wani yanki na farin cikin samun ƙyaƙyƙyawar makoma. Tana matuƙar burin ganin yaronta a kusa da ita. Tsabar jin daɗin hakan harta gama yanke masa matar aure a ranta. Dan wannan karon tanason zaɓama yaron nata matar aure ko hakan zaisa ta sanadin matar ya dawo gareta ba wajen Anne ba....”

       Dogon tunanin da gimbiya Su'adah ta tafi yasa har Bappi ya kammala jawabinsa ma bata ƙarasaji wasu abubuwan ba. Sai murmushi take wanda ya kasa ɓoyuwa bisa fuskarta.



      Ana tashi da ga taron tun kan ta ƙarasa sashenta ta fara kiran wayar gimbiya Asma'u yayarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya (Adda Asmah). Su baƙwai mahaifiyarsu gimbiya Naja'atu da ake kira fulani ta haifa, sai dai sauran duk mazane su biyune kacal mata, kuma sune manya. Hakan yasa musu wata shaƙuwa da son juna na musamman dan sun tashine tamkar tagwaye. Kasancewar kuma irin gidansu gidane na tsantsar ƙabilanci da ƴan ubanci yasa kowa da nasa yake shaƙuwa.

       Dai-dai tana saka ƙafarta a ƙawataccen falonta na alfarma da yaji kayan more rayuwa har zaman musaltashi zai iya zama ƙauyanci gimbiya Asma'u ta ɗaga wayan. Itama tayi aure tuni, anan cikin garin Bingo ma take, rana ɗaya ma akai musu aure. Sai dai ita tayi kusan shekara biyar bayan aurensu kafin ta samu haihuwa. Yaranta biyu kuma kawai. Mace da namiji.

      Batare data dubi su Zuhrah dake zaune a falon kowa na harkar gabansaba ta shige tana mai zolayar yayar tata da faɗin, “Haba ƙasa badai har kin fara barcin naki ba ko?”.

      Amsar da aka bata daga can ta sata sakin ƴar dariya tana tura ƙofar glass na corridor ɗin bedrooms ɗinta ta shiga. Ta kan wani tattausan carpet dake a tsakkiyar corridor ɗin ta taka zuwa ƙofar tsakkiya. Ɗaki ne da musaltashi ɓata lokacine. Dan haka kowa ya musalta da kansa. Ƴar sarki matar Alhaji Basheer Hameed Taura. Ta kai zaune tana sake ƙawata murmushin fuskarta da faɗin, “Amin Adda Asmah. Dama albishir na kiraki nai miki”.

      Tai dariya saboda zumuɗin Adda Asma daga can. “Oh god hajiyar ruɗu kwantar min da hankalinki. Bafa wani abu bane yaronkine kawai zai dawo NAYA, dalilin kiran naki kuwa maganar aure da mulki da ya sakko a ciki ne. Inaga lokaci yayi da zamu cika burinmu na haɗa auren Ramadhan da Aina'u tunda ta kammala karatunta”.

     Dariya ta kuma saki wadda inba Asma ɗin ba babu mai iya ganinta a saman fuskar Gimbiya Su'adah saboda izzarta da girman kai. A take a wajen suka gama yanke hukunci komai game da auren ƴaƴan nasu, batare da gimbiya Su'adah tayi wani dogon tunani ko bincike akan mike a ran Bappi ba.


*_★★HAJIYAR BIRNI HOUSE★★_*


    

            Tun shigowarta ɗakin kwance kawai take tana faman murmushin samun mafitar damuwar data shigo da ita cikin gidan. Dan tabbas da damuwa ta shigo kamar yanda hasashen ƴan uwan nata yake, damuwar da keda nasaba da zuwanta wajen first lady.

      Ita ɗin mace ce ƙyaƙyƙyawa kuma gogaggiya, inda a dalilin harkar barikinta ta haɗu da Alhaji Yaro glass babban ɗan siyasa dake riƙe da babban muƙami a ƙasar ta NAYA. Tun a haɗuwarsu ta farko taji sonsa a ranta, inda akai dace shima ya kamu. Dan haka sukai aure cikin ƙanƙanin lokaci. Sai dai abinda bata saniba Alhaji Yaro glass a ƙarƙashin mulkin mace yake a cikin gidansa. Dukkan faɗa ajinsa iyakarta waje ne. Daya taka gate ɗin gidansa sunansa mijin hajiya Fanta. Tabbas ta fuskanci ƙalubale kala-kala a zamanta da Hajiya Fanta da bazasu musaltu ba, har takai sai da ta tsigeta a gidan hankalinta ya kwanta. Ta kuma kauda hankalin Alhaji Yaro glass da ga gareta baki ɗaya, duk da ƙulafucin son komawa garesa da takeyi musamman saboda ƴarsa ɗaya tilo da suka haifa tare dake wajenta. Tun farkon zuwanta gidan suke ƙawance da Hajiya Bushira hamada, wadda sam bata shiri da Hajiya Fanta duk da kuwa mazajensu abokaine shaƙiƙai. Koda yake ance ada ƙawayene suma na amana, sai dai ƙawancen ya watse ne a dalilin ƴaƴansu. Mafari kenan Hajiya Bushira taita tunzura Alhaji Yaro glass ya ƙara aure, tun baya biye mata har yaji sha'awar yin hakan lokacin daya haɗu da Aunty Hannah. 

     Bayan fitowarta a gidan hajiya Bushira tayi iya ƙoƙarinta na ganin Aunty Hannah ta koma gidan Alhaji Yaro glass amma hakan ya gagara, har suka samu nasarar ɗarewa kujerar mulkin ƙasar ta NAYA. Inda Prof... Usama D. Hamada ya samu nasarar zama shugaban ƙasa bisa ƙoƙarin su Alhaji Hameed Taura. Su kuma su Alhaji Yaro glass suka koma gefe matsayin manya sunacin karensu babu babbaka. Dan ko muƙami ɗaya basu amsaba a bayan fage suke nasu mulkin su.

     Hankalin aunty Hannah ya sake tashi dan tana son Alhaji Yaro glass sosai, amma sai Hajiya Bushira Hamada (First lady) ta kwantar mata da hankali akan karta damu, inhar tana raye sai ta koma aure gidan Yaro glass. Aunty Hannah tana cikin manyan ƙawayen first lady da suke mata ayyuka a ɓoye, amma tana ɓoye kantane saboda Alhaji Yaro glass.

        A yau ma first lady ce ta buƙaci ganin aunty Hannah ɗin tun daren jiya akan wani aikin sirrinsu, a hirarsu ne first lady keɗan tsoguntama aunty Hannah batun wanda su shugaban ƙasa suke son tsaidawa takara, tare da burinsu na salwantar da rayuwarsa daga baya Alhaji Yaro glass ya maye gurbinsa, dan shine sukeso ya zama mataimakinsa. Wannan al'amari ya matuƙar saka Aunty Hannah a farin ciki matuƙa. Har takejin zata iya bada gudunmawarta akan wannan al'amari. Sai dai maganar data biyo bayan hakan ce ta sakata a damuwa, dan kuwa first lady ta sanar mata sun tattauna da shugaban ƙasa akan suna son samawa yaron matar auren da zata dinga musu aiki a kansa batare da sanin kowa ba, amma suna tunanin ta yadda zasu ɓulloma Alhaji Hameed Taura game da hakan. Dan samawarwa Ramadhan matar aure daga ɓangarensu ne kawai mafita da hangen nasararsu a tafiyar. Hakan yasa tacema aunty Hannah taje ta tayata tunani da nazarin mafita dan tana son ita ta fara kawoma shugaban ƙasa mafita koda ƙara samun ɗaukakarta na mata garesa, sannan ita kuma ta zama first lady kodan cusama hajiya fanta baƙin ciki. Dan ba hawan Alhaji yaro glass bisa kujerar matamakin shugaban ƙasa ko zama shugaban ƙasa bane matsalarta ita. Hajiya Fanta ta samu muƙami dai-dai da wanda ta taka shine damuwarta kawai. shiyyasa take so ta shiga ta fita wajen ganin ta nakasa Hajiya Fanta kafin lokacin Aunty Hannah ta koma gidan ta zama tauraruwa a mulkin da Alhaji yaro glass zaiyi. 

         Wannan shine dalilin shigowarta da damuwa gidan. Sai dai kuma abinda ta tarar na boran Raudha ya kawo mata mafita cikin sauƙi da take tunanin first lady zatayi matuƙar farin ciki da ita har itama ta samu cikar burinta na komawa gidan Alhaji Yaro glass matsayin matar vice president.


     Ta saki murmushi mai ƙayatarwa tare da jawo hamshaƙiyar wayarta 1phone ta shiga sarrafata. Kai tsaye number first lady ta laluba. Harta tsinke ba'a ɗaga ba, dan haka ta yanke shawarar sake kira dan tasan saƙon da take shirin kaiwa mai matuƙar muhimmanci ne.

     Cikin sa'a kuwa tana gab da tsinkewa first lady ta ɗauka. “Hannah am sorry ina amsa wani call ne. Ina fatan har an samu mafitar ne da gaggawa haka?”.

       “Sosai ma kuwa your excellency. Zumuɗin hakanne ma yasa na kasa haƙurin bari sai nazo nace bara na kiraki”. Aunty Hannah ta faɗa cikin washe haƙora kamar tana gaban first lady. Itama daga can first lady ta amsa ne cike da zumuɗin son jin yaya akai? Dan haka kai tsaye aunty Hannah ta fara jero mata bayani....

        “Akwai yarinyar ƙanwata dake aure acan jihar Ɗillo. Sai dai a wani ƙaramar hukuma suke mai suna hutawa. Yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce son kowa ƙin wanda bai samu ba. Gata ƙarama sosai sweet 17. Tanada yanayi irin na mutane masu haƙuri da komi zatai baza'a zargeta ba. Sannan inada yaƙinin zata shiga ran Alhaji Hameed Harith Taura cikin ƙanƙanin lokaci. Kai harma da uban gayyar kansa dan da gaske yarinyar ta haɗu your excellency......”

        “Ban katsekiba Hannah, amma mu minene alaƙar shirinmu da ƙyawunta ko sanyin halinta? Mufa wadda zatai mana aiki kawai muke buƙata batare da matsala ba”.

       “Hakane your excellency amma bara na kaiki. Alhaji Hameed Taura mutum ne mai son mu'amula da mutanen kirki, a dalilin hakane mazajenmu suka ɓoye masa ainahin fuskarsu suka aro ta mutuntaka suka yafa ma kansu har takai abotarsu yin tsaho zuwa yanzun. Dan haka bazai yuwu mu samo yarinya mai rawar kai ba akan wannan shirin. Dole ta kasance mai irin suffar Raudha, sannan ƙyaƙyƙyawa. Abu na biyu dole ta kasance ɗiyar masu ƙaramin ƙarfi da basu da wata power ɗin zamtowar yarinyar mai buɗaɗen kai da komai zata iya fahimta idan an sakata tayi, sannan kuma zamu iya juyata ita da iyayenta yanda muke buƙata muma cikin sauƙi dan batasan komai ba sai abinda muka ɗorata a kai”.

         First lady ta ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Kai Hannah shiyyasa nake bala'in sonki wlhy. Dan kuwa kanki na ja matuƙa. Sai dai matsalar ɗaya zuwa biyu ce. Matar shugaban ƙasa ƴar 17years, kuma mai kwalin secondary school kawai. kuma ɗiyar ƴar uwarki bayan kinsan shirinmu shine itama idan ta kammala mana aiki rayuwarta zata iya salwanta”.

          Aunty Hannah tai ɗan murmushi tana sake damƙe filo a jikinta. Dan ita inhar buƙatarta zata biya salwantar rayuwar Raudha ba komai bane ba a gareta. “Your excellency matsala ta farko ba matsala bace ba. Dubi da shima ɗin yaro ne matashi da zai zam na farko bisa kujerar mulkin ƙasar NAYA. Karatu kuwa ko tana gidansa za'a iya sakata ta fara badan zai amfanemu ba sai dan kawai zai bada kariya ga masu ƙorafin matar president iyakarta secondary. Na uku kuwa karki damu, dan mun rasa iyayenmu ma munyi haƙuri balle ƴaƴa. Ko Samha ce zan iya sadaukar da ita domin samun cikar burinmu (ƴarta fa😱, anya kuwa gsky aunty Hannah ke faɗa🤦🏻). Abinda kawai zamu maida hankali yanzun shine koya mata rayuwar manyan mata da abubuwa.”

       “Okay na gamsu da bayaninki, sai dai kuma taya zamu haɗa alaƙar su kuma?”.

      “Wannan shine dalilin kiranki your excellency...........”✍


_(Tofa, su Aunty Hannah kumafa🤔🚶🏻)._


No comments

Powered by Blogger.