Auren Wata Tara Complete Hausa Novel


🅿️.........*1 & 2*

*FUNTUA*
_Unguwar Jabiri_

Tafiya suke cikin unifoam d'in Islamiya su biyu suna tafe suna hira kadan_kadan.

 Asmy ce ta daddabo Zarah ta ce "Zarah gafa mutumin yau ma ya na kofar gidan Ku kuma wlh nasan ke ya ke jira " 

Tsaki wacce aka kira da Zarah taja cikin sanyi murya da daman Chan tun asali haka muryarta take komai takeyi zatayishi cikin nutsuwa da sanyi ta ce ."Aiko bazan shiga gidan yanzu ba Allah har sai ya tafi " sai sannan na K'are mata kallo doguwa Ce mai matsakaicin jiki 


Choculate colour Ce bazaka kirata fara Chan ba haka kuma tafi karfin ka kirata da b'aka 

tana da round face da dogon hancinta sai d'an k'aramun bakinta da ya d'an tsuke ya bada shape d'in heart Dimple d'inta guda biyu dukkaninsu sun lotsa 

wanda tun asali haka suke ko batayi magana ba a lotse wanda suke k'ara fito mata da ainahin baiwar kyaun da Allah yayi mata Fuskarnan tata fresh ba komai sai kwalli da ta kurtawa idanunta Kad'an

Zarah tana da Bala'in shape Wanda ake kira da shape d'in Coca-Cola diri da Zati da Allah yayi mata shine Babban abunda ke Jan hankalin maza gareta Dan Zarah badai diri ba Dan koya tayi tafiya haka zakaga hips d'inta na Juyawa Wanda saika d'auka da gangan ta ke yin hakan alhalin itama Ba so take ba danma koda yaushe cikin hijab take amma dukda manyan hijaban da take sanyawa baya hana bayyanar da surar da Allah yayi mata.


 "Kama hannunta Asmy tayi cikin Sauri suka shiga gidansu Wanda madaidaicin gida ne Suna shiga Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce " Allah yasa mayen bai ganmu ba dafa saiya biyo mu ko"


Aiko da ya biyoki wlh da yaga yanda ake Rashin mutunci Dan ni ba ke bace danfa ya ganki haka salo salo ba umm ba umm umm shiyasa ya rainaki wlh Zarah ki rage sanyin nan Lafiyarki tayi yawa haba ayi mutum kullum cikin sanyi dukda wannan halin naki ya sanya har Rabi take maki irin abunda take maki Dan taga bata gamu da y'ar zamani ba haba ke Ko a makaranta Saidai na shige maki fad'a to tun wuri ma wlh ki koyi kare kanki haba hakurinki yayi yawa wlh "


"Asmy ta k'arasa fad'a tana huci "Mamanta ce Da ta fito daga kitchen ta na sauraransu ta ce " Zarah karki biyeta kici gaba da yanda kike Allah yanason masu hakuri kowani d'an adam yana da nashi kalar jarabawar kinji ke kalar taki kenan kiyi kokari wajen ganin kin cinyeta Allah ya kawo maki sassauci cikin al'amuranki ga abinci nan kuzo Kuci kunji"


k'asa da kanta Zarah tayi tana Goge hawayen da suka zubo mata na tausayin kanta ta ce "Insha Allahu Mama " Kallon Asma'u mamanta tayi ta ce "Karfafa mata gwuiwa ya kamata ki dingayi kullum ba Wai Zuga ta ba kinji" gyad'a mata kai asmy ta yi ta ce "Insha Allah Mama " Tuwon Shinkafar da yaji Miyar taushe mai dadi da Mama ta zubo musu suka zauna Suka fara ci 


Bayan sun gama Ci nan suka fiddo Littafansu na Islamiya suka dinga duddubawa Dan yanzu gaba d'aya hankalinsu ya na Ga saukar da ke tinkarosu Bayan sun gama dibawa jin ana kiran Sallar magriba ya sanyasu tashi Bayan sun gabatar da Sallar magriba Hijab d'inta Zarah ta sanya ta ce Bari na wuce gida sai da safe "Bankwana tayiwa maman asmy tare suka fito su biyu Kasancewar gida Ukku ne tsakaninsu sai nasu Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ganin Nura baya nan A daidai bakin k'ofar gidan Asmy ta tsaya ta ce " Sai Gobe Zarah Zan wuce "Kallonta tayi ta  ce " bazakizo mu shiga tare ba "Girgiza kai Tayi ta ce " Saidai kawai mun hadu gobe"to Sai Allah ya kaimu kawata ta fad'a ta na kutsa kanta cikin gidan cikin siririyar muryarta tayi sallama a hankali 


k'aramun gida ne d'aki hud'u d'aya na Mama Rabi d'aya na Baba sai na ukkun nata na hudun kuma na.kannanta " a tsakar gida ta tarar da Mama Rabi tana ganinta ta watso mata wani banzan kallo cikin Masifa ta fara magana da cewa "an fake da Islamiya ana yawon karuwanci Dan matacciyar uwarki Da kikaje kika zauna uban wani zai d'aura miki girkin ne Eh ko kin Aje wani ne a gidan?girgiza kai ta fara tuni harta fara hawaye dan a rayuwarta kome Mama Rabi zatayi mata batajin ciwon shi kamar irin yanda take zagar mata Mahaifiya da ke k'asa Goge hawayenta tayi cikin muryar tsoro ta ce " Kiyi Hakuri Mama "Tsaki Rabi taja tare da mik'ewa ta ce " Kafin nan da minti Talatin na baki ki gama yimun tuwo da miya Dan uwarki"to "ta fad'a gabanta na fad'uwa tare da shiga kitchen din.


murhu biyu ta hura dukda iccen jik'e ya ke kasancewar yanayin damuna Haka tayi ta hura wutar cikin k'ank'anin lokaci ta na Sauri ta gama Duka ayyukan tukwana ta fito ta yi wanke wanke Su Habiba na Nan zaune suna latsa waya ba Wanda ko tsinke ya kama mata Harta gama komai tukwana ta wuce d'akinta Dan hutawa Cire kayan jikinta Tayi Tare da daura zani Dan zafi takeji kodan yanayin garin kamar akwai hadari a kasa ya sanya zafin fitowa tayi a lokacin Mama Rabi suna cin tuwo ita da yaranta Tab'e baki tayi tare Jan tsaki ta ce "Sai anje an gama yawon ta bugas din azo ana wankan iskanci a gida " Idan da sabo ta saba hakan yasa ko a jikinta harta fito daga bandaki Bayan tayi alwalar isha i d'akinta ta wuce tare da shimfida tsohuwar dardumarta ta sanya hijab d'inta ta Islamiya ta kabbara salla Bayan ta gama isha i tare da shafa'i da wuriri zaune tayi a wajen ta jima tana nemawa mahaifiyarta gafara a wajen ubangiji ta na hawaye ta ce "Allah ya jikanki Mahaifiyata har kullum ina kukan rashinki a kusa dani amma kuma nakanji farinciki idan na tuna da irin mutuwar da kikayi bansankiba ban tab'a ganinki ba Amma ki sani ina tsananin kaunarki kullum da tunaninki a raina nake kwana nake tashi na tabbatar da kina raye da bazan tsinci kaina cikin wannan k'uncinna rayuwa ba amma babu yanda na iya da Lamarin ubangiji haka Allah yaso ya ganni kuma nagode masa Allah yasa kin huta" 


ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka mai cin rai Hade kai da gwuiwa tayi ta na ta kukan halin maraicin da ta tsinci kanta da tasowarta cikin marassa imani"Malam Yusuf Da ya shigo Yanajin y'artashi na yiwa mahaifiyarta addua Saida ya Goge hawayen tausayin y'ar tashi Shi kanshi idan yana tunowa da Mahaifiyarta kuma  masoyiyarsa Zarah mace mai biyayya da hakuri Sai da ya  Goge hawaye karasowa yayi Tare da zaunawa gefenta ya ce "Zahra'u Kiyi Hakuri kinji yaci ace kin saba da irin wannan rayuwar kisani komai yayi farko yana da karshe kinji y'ata Allah yayi maki albarka ya jikan mahaifiyarki ya k'ara miki hakuri da juriyar zama da rabi sannan ya nuna mun ranar aurenki ni kaina badan naso ba nake ganinki cikin wannan halin"  


jin muryar mahaifin nata ya sanyata saurin Goge hawayenta Dan a duniya babu abunda ta tsana sama da tashin hankalin mahaifin ta tare da kirkirar murmushi ta ce "Baba ina yini " Murmushin ya mayar mata ya ce "Lafiya qalau Zarah ta ya makarantar munyi magana da malaminku yau ya ce Akwai kudin sauka da za a kai me yasa baki fad'amun ba tun da wuri Zarah " kasa tayi da kanta ta ce


 "Baba naga baka da kudi kuma naga ba dole bane sai anyi walimar saukar da ni tunda Dai na hardace a kaina ai shikenan " girgiza kai Baba yayi yanajin k'aunar y'ar tashi ta daban sosai hankali da hangen nesa irin na Zarah har mamaki yake bashi akwaita da hakuri irin na mahaifiyarta cewa yayi "Allah yayi miki albarka y'ata amma ko zamu rasa abunda zamuci saina biya miki kudin ba dubu goma bane Allah ya horemun kafin lokacin" ameeen Baba nagode "Kinci abinci dai ko?eh Baba ta fad'a ta na gyada masa kai " yawwa to shikenan Sannan ya mik'o mata d'ari biyu ya ce "Gashi ki boye ki d'an dinga kashewa kinji" Murmushi tayi tare da amsa hannu biyu ta ce "Nagode Baba Allah saka da alkhairi " Ameen y'ar kirki ya fad'a tare da yi mata saida safe "


Bayan fitar Baba girgiza kai tayi tana jin k'auna da soyayyar mahaifin nata ta musamman tasan Shima ba ason ranshi take fuskantar kalubalen wannan ba Boye kudin da ya bata tayi a akwatin kayanta tare da dauko Alquran mai girma ta fara karantawa cikin zazzak'ar muryarta tana rerowa cikin k'iri'a mai dad'in sauraro a haka har bacci barawo ya kwasheta 


kamar yanda ta saba koda yaushe tun asuba da ta tashi tayi sallah bata koma ba nan taci gaba da aikace aikacen gidan Har Safiya tayi wajen 8 da rabi taga su Habiba sun fito Suna hamma tare da d'aukar buta Zasuyi Alwala girgiza kai tayi wai ace Sai yanzu zasuyi sallah Kodan yau sunma tashi da wuri su da har 9 kaiwa suke batace komai saboda bata manta ba ranar da ta tab'a musu magana akan Sallar Safe da suke irin tijarar da suka mata hakan ya sanyata cigaba da Harkokinta Tana cikin d'ora d'umame Khairat ta lek'o Yarinya ce da bazata wuce shekaru goma sha daya ba kallonta tayi tare da cewa " Ina kwana Aunty "Murmushi Zarah ta sakarma kanwartata dan duk cikin gidan itace Ta fita zakka ta ce " 


Lafiya qalau khairat Kintashi lfy "Alhmdllh ta fad'a ta na Amsar tukunyar da Take shirin dorawa ta ce " bari na tayaki Aunty"A a a ki barshi khairat zanyi "Amsa tayi ta ce " Nidai saina tayaki Suna cikinyi Mama Rabi ta lek'o Dan Safiya ta gulmanta mata Khairat na kitchen tana taya Zarah Aiki wata uwar ashar ta kawo ta lafta wadda saida cikin Zarah ya d'uri ruwa tuni ta dabarbarce "Kafin da d'ago Mama Rabi ta kife ta da Mari tare da cewa " Dan Ubanki y'artawa zaki sanya Aiki tayi maki kama da kalar Aiki Sau nawa zan fad'a maki Ke kadai zaki dinga aikin gidan nan Eyye tsabar iskanci ma y'arda na Haifa itace zatayi maki aiki"Khairat ce ta mik'e cike da tausayin y'ar uwar tata ta ce "Kiyi hakuri Mama Ba ita ta sanyaniba ni naga ya kamata na tayata" 


Tsawa ta daka mata Tare da nuna mata hanyar waje ta ce "Fice ki ban waje kafin na waiwayo kanki" Cikin Sauri ta fita ta bar kitchen d'in ta na gunguni"Zarah ko hawaye ne suka zubo mata Inda Mama Rabi ta shiga balbaleta da masifa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba amma bata Ce mata uffan ba harta gama fadanta ta fita girgiza kai tayi tare da mik'ewa taci gaba da abunda ta ke ta na yi ta na hawaye "Bayan ta gama aikin D'akinta ta shiga ta share tare da daura towel ta dauki sosonta da sabulu ta fito Ta shiga wanka Bayan ta fito Nan ta iske Mama Rabi da d'iyan ta suna cin d'umamen Tuwon da ta dafa" bata bi ta kansu ba ta shige d'akinta Tare da Shiryawa cikin Wata Atamfarta da ta d'ansha jiki jin kukan yunwar da cikinta keyi ne ya sanyata mik'ewa tare da fitowa nesa da su ta tsaya tare da K'asa da kanta "Tayi shiru " 


Cikin masifa Rabi ta ce "kikazo kikayi mana tsaitsaye Mayya me za a baki" Dagowa tayi idanunta na zubar da k'walla tayi maza ta Goge ta ce "Daman abinci nazo d'auka " Dogon tsaki taja tare da Banka mata harara ta ce "Mun cinye mu Kanmu bai ishemu ba " Khairat ce dukda yarintarta ta ce "Mama ni bari na bata nawa na k'oshi" Harara ta banka mata tare da dankwashinta aka ta ce "inke kin koshi ni ban koshi ba " girgiza kai kawai Zarah tayi ga abinci nan tana gani Bayan ita ta sha wahalar girkawa amma a hanata ga tsabar yunwa da takeji Juyawa tayi ta koma d'akinta tare da dauko d'ari biyun da Baba ya bata ta boye a jikinta hijab ta sanyo tare da Fitowa Tsawa Mama Rabi ta daka mata ta ce "Gidan ubanwa kuma zaki" 


“Fita zanjena nemi abinda zanci "ta fad'a cikin rawar murya" koma ciki babu Inda zaki Dan Ubanki so ne kike ki k'ara jamun Zagi a wajen mutane duk abunda nake ba gani ake ba To ba Inda zaki"Amma Mama Ke fa kika hanani Abinci kuma zanje na saya ki hanani fita"ta fad'a cikin dauriya"eh bazaki ba ko fad'a zanyi ki mayar mun?


Girgiza kai kawai tayi tana Jinjina Rashin imani irin na Mama Rabi daki ta Koma tare da zaunawa ta rafka ubann Tagumi Hawayen tausayin kanta na zubo mata yaci a ce Inda sabo ta saba da halin da take ciki......✍🏿

No comments

Powered by Blogger.