Auren Shehu Complete Hausa Novel

 


FIKRA WRITER'S ASSOCIATION


AUREN SHEHU 

✍🏾 Khadija SidiKwance ya ke a rigingine kan ciyayi irin wannan ciyayin da ake kira "carpet grass" Hannayen sa biyu tallabe da ƙoƙon kansa,  cikin nazari yake  duban taurarin da ke jere reras suna sheƙi bisa sararin samaniya.

Babban lambu ne mai ɗauke da ɓangare biyu, ɓangaren  bishiyoyin 'ya'yan itatuwa, bishiyar mangoro, gwaiba, yazawa (cashew) da dai sauran su, sai kuma ɓangaren da ke ɗauke da kujerun hutawa. In ka ɗauke kukan tsuntsaya babu sautin da ake ji kasancewar dare ya fara tsalawa, kusan ƙarfe biyu ne. 


Sanye yake cikin rigar saƙa irin na fulani, kan sa ɗauke da rawanin da ya zaga har kewayen fuskar sa hakan ya sa fiye da rabin fuskar shi ɓuya. Kasancewar shi na daya daga cikin masu gadin daddare na gidan, kusan kullum ya kan kai biyu a nan cikin lambun, yayi kwanciyar sa ya na mai nazari, hakan ba ƙaramin nishaɗi ya ke saka shi ba.


 Gefan sa ƙatuwar sanda ce wacce ake kira da gora, ta korar shanun sa ce duk da kuwa rabon shi da rugar su wacce ake kira "Rugar Shehu" ya kusa shekara.


Jin dirar mutum tare da haushin karnukan gidan lokaci ɗaya ya sanya shi yin zumbur ya tashi zauna ya na mai duban in da ya ke kyautata zaton mutum ne ya diro cikin gida. Jin shiru babu wani motsi sai na haushin karnuka ya sanya ya tashi tare da jan sandar gorar shi kai tsaye bakin bishiyar da ke kusa da katangar lambun ya nufa, idan ya ke kyautata zaton koma menene ya diro nan ne hanyar shi.


Tun dirowar ta take ƙoƙarin janye niƙabin ta da ya maƙale jikin reshen bishiyar da ya mata tsani. Ƙoƙari ta ke iya ƙarfinta don ta ga ta ciro amma ina, gashi ta san mutukar ba ta samu ta shige ciki ba lalle masu gadi za su kama ta yau, don kuwa haushin karnukan yau ya fi na kullum. Jin ta ku a bayan ta ya sanya ta juyawa da sauri, ganin ya ɗaga sanda ya na shirin runtsuma ma ta aka, ta runtse idanu ta na mai faɗin 


"Wayyo ni Dady!!!!!"


Cak ya tsaya, hannun shi na rawa tsabar firgici na ganin kyawun halittar Allah, tabbas kyau dai babu irin wanda bai gani ba a Rugar su, amma sam bai taɓa ganin wacce ta firgita shi ba kamar wannan halittar da ke gaban sa. 


Fuskar ta ya bi da kallo, wanda rashin niƙab ya ba shi wannan damar, domin kuwa jikin ta rufe ya ke da hijabi tun daga sama har ƙasa. Kamar yanda ya ke nazartar taurari haka ya tsinci kan sa cikin nishaɗi yayin da ya shiga nazari akan fuskar ta.


Baka ce, irin wannan bakin mai shek'i kamar jikin tarwaɗa. Tsayuwar hancin ta da ya zo dab da ƙaramin bakin ta ba ƙaramin ƙarawa doguwar fuskar ta kyau yayi ba......


Jin  shiru ba ta ji saukar gora kan ta ba ya sanya ya ta buɗe manyan idanun ta, hakan ba ƙaramin sake rikita shi ta yi ba ganin fararen idanun ta bisa kan shi har sai da ya ɗan ja da baya ya na mai tasbihi ga ubangijin sa, domin ya tabbatar wannan halittar da ke gaban shi ba mutum ba ce.


Ta na mai duban shi cike da tsoro musammam ganin mutum mai faɗi da tsayin da tun da ta zo duniya ba ta taɓa ganin irin shi ba, daɗin daɗawa gashi yanayin shigar shiri irin na waɗannan mutanen da suka saka Nijeriya a gaba ko kuma Fulani masu garkuwa da mutane, wannan tunanin tare da jin taku da haushin karnukan da ya ƙaru, wanda hakan ya tabbatar ma ta masu gadin sun kusa shigowa lambun ya sa ta sakin niƙab din ta na mai ɗage hijabin ta yanda za ta sami damar sauri, ta yi amfani da damar gushewar tunanin mutumin da yayi kasake ya na duban ta, ta bi hanyar da zai sada ta da kitchen da sauri, hannu na rawa ta ke ƙoƙarin fidda ɗan mukulli da ta ɓoye cikin dan wando da ke sanye jikin ta.


 Har tuntuɓe ta ke garin waige domin tabbatarwa ba ya biye da ita.

Allah ya taimake ta ƙofar ya buɗu, kasancewar ta sababbiya a harkar, cikin sanɗa da lalube ta ke tafiya domin wutan lantarkin kitchen din a kashe ya ke, sai dai hasken farin wata da yake ratsowa ta taga. Ba ta tsorata ba sai da ta jiyo muryar masu gadi daga cikin garden, ta na mai roƙon Allah ya sa ba asirin ta ba ne ke shirin tonuwa ba, ta bi ta falo ta shige ɗakin ta cikin rawar jiki. Dan tun da take fitar dare ba ta taɓa shiga tsaka mai wuya kamar na yau ba.


Hijabin jikin ta ta cire, ta na mai ajiyar zuciya ta zube bisa gadon ta. 

Hasken da ya gauraye ɗakin sanadiyyar wutan lantarkin da aka kunna ya sanya ta yi zumbur ta tashi  zaune a tsoro ce. Ganin wacce ke jingine jikin bango ya sanya ta fiddo ido tare da faɗin


"Wai ke Halitta ba za ki fita harka ta ba? Wannan masifar har ina haka?" 


A hankali Halitta ke ƙare ma ta kallo, tun daga dan ƙaramin matsattsan wandan da ke jikin ta (bumshort) zuwa matsatsiyar jar riga wacce ta tsaya ma ta iya cibiya, ga kan nan ya sha kitson attachment da aka yi da gashin doki mai tsada da ake kira (Brazilian hair). Ta na mai girgiza kai ta furta


"Yakura......." 


"please Halitta, ba yanzu ba, na gaji da yawa!!" 


Ta katse ta tana ɗaga mata hannu. Ganin an murɗa ƙofar ɗakin ya sanya ta saurin janyo bargo domin ɓoye shigar da ke jikin ta. Mahaifiyar su wacce su ke kira Ammy ce ta shigo, ta na hamma tsabagen baccin da ke idanun ta, ta ke duban su cike da damuwa ta ce


" dama na san dole kuma kun tashi, hayaniyar su Audu da haushin karnuku ne ya tada ku ko?" 


"eh wallahi Ammy....." 


Su ka faɗa a tare wanda hakan ya sanya Halitta sakin baki cike da mamaki ta ke kallan yayar ta ta, ita kuwa ko aji kin ta ta ce


"na kasa gane menene matsalar su da za su na sakar mana karnuka su na mana hayaniya, ya kamata a hana su shiga garden ma kawai...." 


"ke da ki ke ɗaki ya aka yi kika san garden su ke?"


Halitta ta na sane ta jefa mata wannan tambayar, domin kuwa duk wani rashin ji da 'yar uwar ta ta ke yi babu wanda ba ta sani ba.


Jin haka ta san in da ta dosa dan haka sai ta yi burus tare da faɗin


"Ammy dan Allah daga ina hayaniyar nan ke tashi?" 


"eh toh ni ma na fi tunanin garden din ne, ai Malam shi ma ya fita ya mu su magana...." 


Ras! gaban ta ya faɗi 


"Allah ka rufa min asiri ba dan hali na ba ba dan aiki na ba" 


Adduar da ta shiga jerowa cikin ran ta kenan. Ita kuwa Halitta dariyar mugunta ta saki, sannan ta furta


"Allah ya sa Dady ya gano dalilin wannan hayaniyar ta su ya mana magani, ni dai sai da safen ku" 


Ta na murmushin mugunta ta dubi yayar ta wacce ke watsa ma ta harara, ta ƙara da


"a juri kai zuga gabas wata rana ya zo da ruwa, ko ya ki ka ce Yakura" 


"uhum" 


Cewar ta dan tsoro ta kasa magana, gani ta ke burin Halitta ta biye ma ta su yi hayaniya dan ta sami damar tona mata asiri. Halitta na fita Ammy ta bi bayan ta na faɗin 


"bari na bi bayan ki Halitta, babu mamaki Falmata na nan ɗakin ta tsoro ya hana ta motsawa" 


Suna fita ta fidda wayar ta da ya dame ta ta da ƙugi, ganin wanda ke kiran ta ta ja tsaki, ɗagawa ta yi tare da karawa bisa kunnan ta, cikin nuna fushi ta ke magana


"Bobo wai menene? Na faɗa ma ka zuwa na club in dai na dawo hutu gidan nan abu ne mai hatsari, ka bari mu koma school ka ce ah ah, ga shi kai ba za ka iya bari mu dawo da asuba ba sobada jarabar bacci irin na ka, ai gashi yau saura kiris Dady ya kama ni!" 


Shiru ta yi na wani ɗan lokaci ta na sauraran shi, kafin daga bisani ta kashe wayar ba tare da ta sake tankawa ba. Nan ta kwanta ta na jiran tsammani, jin shiru babu wanda ya dawo ta san asirin ta bai tonu ba tukunna, dan haka ta tashi, kai tsaye toilet ta nufa ta yi wanka tare da ɗauro alwala domin rama salloli uku da ke kan ta, la'asar, magariba da isha'i. 


***

Allah yayi dare gari ya waye. Babban ɗaki ne irin na  ƴaƴan manya, komai na ɗakin an yi masa ado da kala biyu, wato shuɗi da fari. Ba wani tarkace ba ne a ɗakin, face ƙatan gado na alfarma tare da setin madubi da dirowa. 


Kamar kullum yau ma sai da rana ta take, bayan ladanin masallacin da ke cikin gidan su ya ƙira sallar azahar sannan ta iya motsawa, wayar ta ta jawo, ta shiga Instagram in da ta saka hotan da ta yi daren jiya a club. Nan da nan hotan ya sami karbuwa in da samari da wasu yan mata su ka shiga danna mata "like" tare da "comments" kamar yanda aka saba. Sai da ta gamsu sannan ta aje wayar ta tashi da kyar ta yi wanka tare da ɗauro alwala. 


Maimakon da ta fito ta yi azama wajen rama sallolin da ake bin ta, wato Asuba da Azahar, sai ma tsayawa ta yi gaban madubi ɗaure da tawul da ya tsaya iya gwiwa, cikin jin daɗi da alfaharin baiwar dirin da Allah ya mata, da ke masha Allah ita kan ta ta san Allah ya mata mata dire. Hakan ya s koda yaushe ta na kan social media cikin saka hotunan ta wanda ta yi da matsattsun kaya, dan kuwa ta na cikin ɗaya daga cikin sannanun matan nan da ake kira "Slay Queen" a Instagram. 


Sai da ta ɓata lokaci wajen shafe shafe da kwalliya, ta fito fes cikin ɗinkin atamfa riga da siket, sannan ta ɗauko hijabi wanda ya ke kai mata har ƙasa ta sanya. Murmushi ta ke ganin yanda ta fito saliha sak, ita da kan ta ta shiga yiwa kan ta kirari


"woo ni Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Daddyn ta" 


Nan ta gama juye juye gaban madubi, sannan ta shimfiɗi sallalaya aka shiga jera sallar asuba da azahar. ***Malam Abubakar Birma sananne kuma hamshaƙin Malami ne wanda ya yi suna a Nijeriya, musamman Kano da Maiduguri. Babarbare ne ɗan asalin garin Maiduguri. Matan shi biyu, Hajja Kulu ita ce matar shi ta farko, wacce ta ke ƙabilar Barebari, ta na zaune ne gidan Malam da ke birnin Maiduguri. Yaran ta da shida, maza huɗu da mata biyu. Sai kuma Hajja Aleesha, wacce ta ke ƙabilar Shuwa Arab. Ita ce ke zaune Kano, ƴaƴa uku gare ta, kuma duka mata, sun haɗa da ɗiyar ta ta farko Zainab mai kimanin shekara ishirin da biyu, wacce ake kira Yakura, sai mai bi mata, Halitta mai shekara ishirin, sai auta Falmata, wacce ta ke da shekaru goma sha takwas a duniya. 


Cikin ƴa'yan Malam, Allah ya jarrabe shi da fitinanniyar ɗiya, wacce babu wanda zai ga ɗabi'un ta ya danganta ta da Malam. Ba kowa ba ce fyace ɗiyar Hajja Aleesha ta farko, wato Zainab. Club ne daga na cikin gida Nigeria kudu da Arewa har zuwa ƙasashen ƙetare babu wanda ba ta zaga ba, sai dai wanda ba ta sami dama ba, haka kuwa buɗe ido babu wanda Zainab ba ta yi ba kasancewar ta na yawan harka da gurɓattun yaran masu kuɗi, yawanci ta haɗu da su ne ta cuɗanyar makarantun boko da su ka yi tare. 


DOWNLOAD HERE

No comments

Powered by Blogger.