Abokin Aikina Book 1 Page 9
*LAMBA TA TARA.*
"Tabbas! Akwai wadda ta linka ki fuskantar baƙƙan cikin aure. Kuma ba wata ba ce face ni nan Zaituna"
Kallon mamaki na ga ta bi ni da shi tana jinjina kai, kafin ta yi tagumi tana kallo na tamkar wata sabuwar halitta a gabanta. A hankali na tako na zo wurinta na dafa kafaɗarta fuskata ɗauke da murmushin ƙarfin hali, wanda na yi amfani da shi ne kawai domin na kore rabin damuwata, kuma na ƙarfafa mata zuciya ta zamo jaruma a fagen shanye takaici, jajirtacciya a wurin kawar da kai da hangen nesa.
"Akwai mata da yawa waɗanda suke fuskantar matsalolin aure a wannan lokacin da muke ciki. Saboda sauyin da zamani ya zo mana da shi, da kuma tsarin yadda ake gina tubalin auren tun tushen shi. Ba tare da an yi duba da nagartar mutum ko asalin shi ba".
Zancen da na yi kenan a lokacin da nake duƙe wurin Amina domin na tunatar da ita mutuwar yawa kaka ce. Sannan na miƙe na nufi kujerata na zauna, idonta a kaina wanda alamu ya nuna mamakina da ke kwance a kan fuskarta.
Daga can inda take zaune ta jefo mini tambaya cikin sanyin murya. "Ina mamakin yadda kika iya shanye waɗannan abubuwan duka a cikin zuciyarki. A rayuwata ban taɓa sanin akwai mai ƙarfin zuciya irinki ba, domin ina da yaƙinin da ni ce ke da tuni na mutu har an manta da ni. Amma ke ga ki sharr da ke ma sha Allah tamkar ba ki san wani abu damuwa ko ɓacin rai ba.."
"Ni ma ɗin ba yin kaina ba ne daga Allah ne. Saboda na yi kuka tamkar zan ƙarar da ruwan hawayena, haka ma na shiga ƙunci da damuwa tamkar ba zan sake shaƙar iskan numfashi ba. Amma duk da hakan Allah ya inganta mini lafiya har yanzu ba a ce ina ɗauke da hawan jinin ba. Don haka ke ma ki mayar da komai ba komai ba, ki kalli komai ki kawar da kai kamar ba ki hango komai ba. Ina tabbatar miki sannu a hankali komai zai zo miki fiye da tsammanin ki. Abin da ya saka ki kuka a yau zai dawo yana ba ki dariya, abin da ya ba ki takaici zai dawo hannunki kina juya shi ta yadda kika ga dama. Amma duk wannan ba zai samu ba har sai kin cusa wa zuciyarki haƙuri, haƙurin ma na gasken gaske".
Shiru ya ratsa tsakani kafin na ji ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyi ta ce, "Ke mutum ce har da rabi Zaituna. Na gode wa Allah da ya kawo ki ma'aikatar nan kuma ya haɗa ni zama da ke. Saboda kina da zuciya mai kyau tare da hangen nesa. Na gode sosai Allah ya ƙara mana haƙuri gabaɗaya".
Murmushi kawai na yi cike da jin daɗin yabon da ta yi mini, duk da wani sashe na zuciyata yana tunatar mini da ɓoyayyen laifina, tare da wannan da nake ƙoƙarin aikatawa a sirrance.
Agogon hannuna na duba cikin sauri na fara haɗa takardu ina sakawa jakata, saboda ganin har ƙarfe biyu ta wuce uku ta doso. Miƙewa na yi na nufi ƙofa da nufin zuwa gida, Amina ma ta tashi daga zaman dirsham ɗin da ta yi a dandamalin siminti tana gyara zaman zaninta. Ina ƙoƙarin ficewa ta yi hanzarin dafa kafaɗata ta ce "Ina sha'awar jin labarin tarihin rayuwarki. Idan babu damuwa ki ba ni lokacin da zan zo har gida, domin na ji wannan badaƙalar da kika fara yi mini tsokaci. Saboda jikina ya ba ni zan ƙaru da wasu abubuwa fiye da na yanzu".
"Idan kuma mijina bai aminta da hakan ba fa?"
"Sai na haƙura".
Ta ƙare maganar cikin kwantar da kai da muryar tausayi. Murmushi a kan fuskata na ce, "Zan sanar da ke amma ba gidana ba. Saboda ba na so na yi sara da mutum sama".
Ita ma fuskarta ta faɗaɗa da murmushin alamun ta hasko abin da nake nufi.
Tare muka fito inda muka tarad da mutane da yawa sun yi gida, saboda a ƙa'ida ƙarfe biyu dam muke tashi. Amma yau ga mu har ƙarfe uku saboda batutuwan da muka tattauna sun janyo lokaci ya tafi ba mu sani ba.
Cike da damuwa muka doshi bakin gate ɗin ma'aikatar, saboda haushin rashin ganin motar MD, wanda alamu ya nuna shi ma ya yi gida. Muna ƙoƙarin fita gate sai ga motar shi ta doso babu shiri muka yi gefe ya shige. Kamar na tsaya na yi masa sai gobe, amma na dake na fice muka ja tunga a bakin titi. Abin hawa muka samu dukanmu, ni na fara shiga tawa na zauna har muna ƙoƙarin barin wurin. Sai ga muryar Baba maigadi yana ƙwala mana kira ni da Amina, da sauri na leƙo kai bayan na dakatar da mai adaidaitan ya tsaya. Baba maigadi ya iso wurinmu da ledodi biyu a hannun shi ya miƙo mini ɗaya ya bai wa Amina ɗaya. Kafin mu tambaye shi ya riga mu da faɗar,
"Ranka ya daɗe ne ya ce na kawo muku".
Baki sake na kai kallona cikin ma'aikatar, sannan na dawo da kallon a kan Baba maigadin na ce, "Kuma mu ya ce a bai wa?"
Kai-tsaye ya amsa mini da "Tabbas! Ko tantama babu Hajiya".
"Ka ce masa mun gode. Allah ya ƙara rufa asiri". Cewar Amina kenan cike da jin daɗin da ya bayyana kan fuskarta.
"Hajiya mu je kawai Allah ne ya tsaga da rabonmu".
Abin da ta sake faɗa mini kenan ta shige adaidaita suka wuce, ganin hakan ya sa ni ma na yi godiyar cikin sanyin jiki muka tafi.
Tafe nake cike da mamakin wannan kyauta da MD ya yi mana ni da Amina. Duk da ba wannan ne karo na farko da yake yi wa mutanen wurinmu alheri ba, amma dai ni kam na ji abin har cikin raina.
Ban san lokacin da muka isa unguwar ba, sai da mai adaidaitan ya tambayi wani layi zai shiga. A nan na dawo natsuwata na yi masa kwatance muka doshi ƙofar gidanmu.
Tun daga nesa na hango Mukhtar zaune a kan dakalin ƙofar gidan, tare da wata mai tallar masara bakin shi har kunne suna hira. Haushi ya turnuƙe ni cikin sauri na miƙa wa mai adaidaita kuɗin shi na ja ledata. Ban kalli inda yake ba balle na tsaya sauraron borin kunyar da yake yi.
"Tashi ki je malama, tun da na biya ki kuɗin masararki zaman me kike yi a nan kuma? Salon ki janyo mini zargi..."
Iya abin da kunnuwana suka ji kenan na shige ciki. Da gudu yarana suka tarye ni suna ihun murnar gani na, da masara a hannunsu suna ci. Ban yi mamakin ganin su da masarar ba don na san Mukhtar ne ya saya musu.
Zama na yi a falon ina faɗin "Wash! Allah!" Iman da Haidar suka fara yi mini sannu da zuwa cikin farinciki. Sai ga Ummu Salma da plate ɗin taliya shaƙe ta dire a kan teburin tsakiyar falon. Sannan ta ɗauko ruwa biyu a firij ta dire mini tana wasar bakin faɗin,
"Sannu da zuwa Mama".
Na amsa cike da jin daɗin kulawar da yarana suke ba ni, ledar da MD ya ba mu na buɗe cikin sauri na fito da robar takeaway ɗin da ke ciki guda biyu. Na buɗe nan take ƙamshin jallof ɗin da ke ciki ya gauraye falon, sannan na buɗe ɗayar robar sai ga peppe chicken a shaƙe ya sha jar suya.
Murmushi na shimfiɗa a kan fuskata, cike da jin daɗin wannan kyauta ta musamman. Tire na sa Ummu Salma ta miƙo na juye jallof ɗin da naman duka, sannan na ɗebo taliyar na zuba. Na ce duk su zauna mu ci tare, murna ɗauke a kan fuskokinsu muka fara cin abincin.
Muna tsaka da ci Mukhtar ya shigo ya yi mana tsaye a kai yana ƙallon mu. Ni dai ƙanzil ban ce da shi ba ina ta cin abincina, saboda ban san ina jin yunwa ba har sai da na fara kai loma. Haidar ne ya kula shi ta hanyar faɗin "Abba ka zo mu ci..."
"Rufa mini asiri kada a fasa mini kai Haidar. Wannan abincin ai na manyan ma'aikata ne ba irinmu ba".
Sarai na fahimci bugun gorar da yake yi mini, amma kallo ma bai ishe ni balle na tanka shi. Yana tsaye na gama ci na miƙe na wanko hannuna, sannan na sha ruwa tare da jan jakata na yi ɗaƙina. A jikina nake jin kallon da ya bi ni da shi, hakan ya tabbatar mini da kallon tuhuma ko zargi yake yi mini.
Har zan shiga toilet na fito domin na tunatar da yaran zuwa islamiya. Karaf na ji maganar Haidar yana faɗin "Abba mai masarar ta tafi ko? Har na so na je ta canza mini tawa na fasa, saboda tsoron ka yi mini faɗa tun da ka ce kada mu sake fitowa sai ta tafi..."
"Kai Haidar! Tashi ka je ku yi shirin makaranta lokaci yana ƙurewa". Ina ƙare faɗar hakan na juya zuciyata cike da ƙuna, domin zancen shi ya hasko mini korar da ya yi musu domin ya ji daɗin hira da mai masarar.
Har na gama sallah ban daina jin zafin abin a raina ba, waton shi bai hangen bayan shi kullum gaba kawai yake kallo. Ba ya gudun abin kunyar da zai janyo wa 'ya'yan shi gori musamman yanzu da suka fara girma.
"Allah wadaran naka ya lalace!"
Abin da na faɗa kenan bayan na sauke ƙatuwar ajiyar zuciya. Ina nan zaune kan sallaya suka shigo suna yi mini sallama za su je makaranta. Na yi musu fatan dawowa lafiya tare da addu'ar tsarin da na saba yi musu idan za su fita. Ficewarsu ya sa na goge ƙwallar da ta zubo mini a gefen ido, sannan na miƙe na yi sallar Asr, saboda an fara kiran sallah a masallatan da ke cikin unguwar.
Wanka na yi sannan na dawo falo na zauna ina aikin takardun da MD ya ba ni, zuciyata a cunkushe da damuwar rashin sanin ciwon kai irin na Mukhtar.
Tunanin yi wa MD godiya ya faɗo mini a rai, na ajiye biron da ke hannuna na ɗauki wayata da ke kusa da ni. Data na buɗe na saƙuna suka gama shigowa, sannan na nemo shi aka yi dace yana online. Na tura masa saƙo kamar haka,
"Baba Maigadi ya ba mu saƙonka, mun gode sosai Allah ya ƙara rufa asiri ya saka da alheri."
Sai da saƙon ya tafi sannan na fara dudduba sauran saƙonnin mutane ina bayar da amsa. Karaf na ji muryar Mukhtar a tsakiyar kaina.
"Na san za ki yi zargin wani abu dangane da abin da kika ji Haidar ya faɗa. To wallahi ni babu komai tsakanina da mai masara. Amma fa idan kin yarda don na san halinki da mugun zargin tsiya, mutum bai isa ya yi abu ba sai kin saka mai ido".
Ban kula shi ba balle na tanka, dannar wayata kawai nake yi ba tare da na ɗago kai ba, saboda hankalina yana kan wayar don na hango MD yana typing. Saƙon ya shigo kenan ina ƙoƙarin buɗewa, babu zato na ji Mukhtar ya fisge wayar daga hannuna.
Zumbur na miƙe cikin zafin nama na yi kan shi a fusace, saboda ƙoƙarin duba wayar da yake yi...
Mu haɗu a next page😛
Leave a Comment