Abokin Aikina Book 1 Page 6



*LAMBA TA SHIDA.*


Shiru kawai Firdausi ta yi mini bà tare da ta ce da ni komai ba, har sai da muka je unguwarmu aka ajiye ni sannan muka yi sallama. Fatan samun sauƙi ta yi mini sannan mai adaidaitan ya juya da ita suka wuce. Da

tunanin yadda zan mayar wa MD wayar shi a zuciyata na isa bakin ƙofar gidanmu, dole na yi turus ina kallon ƙofar da kwaɗon da ke jiki. Juyawa na yi cike da gajiya na yi gidan Maman Taufiƙ, saboda tabbacin da nake da shi wurinta yara suka kai mini makulli idan na zo na karɓa. 

    Da sallama na shiga gidan, tsaitsaye muka gaisa na karɓi makullin na fice. Saboda ba na son tsawaita zance a lokacin saboda burin da nake da shi a cikin raina, wanda nake buƙatar sirri ba tare da kowa ya ji ko ya gani ba. 

   Ban tsaya falo ba kai-tsaye ɗakina na wuce na zauna kan gado. Ajiye jakar da ke hannuna na yi sannan na fito da ledar wayar da MD ya ba ni, wayata na fara cirowa cikin sauri na kunna. A gaggauce na nemo wayar MD ina ƙoƙarin danna masa kira wani kiran ya shigo wayata. Ganin sunan mai kiran ya sa na yi hanzarin ɗaga wayar, 

     "Ke matar nan ina kika shige kwana biyu babu ke babu wayarki?" Murmushi na yi kamar a gabanta sannan na ce, "Kwana biyu ina ta fama da jiki, sai yau na samu sararin buɗe wayar..." 

    "Allah Sarki! Ɗazu na zo gidanki domin na duba ki ba kya nan" Ta ƙare maganar muryarta ɗauke da damuwa. 

    "Ayya! Na je asibiti ne yanzu na dawo gidan". Na ba ta amsa cike da kulawa saboda tuno wace ce ita da matsayin da ta ɗauke ni. "Na so na tarad da ke, saboda akwai maganar da nake so mu yi. Amma dai yaushe za ki dawo wurin aiki?"  

   

"Ranar Laraba in Sha Allah zan shigo. Amma idan babu damuwa ki faɗa mini yanzu mana". Na ba ta amsa cikin ƙosawa da son jin abin da za ta faɗa mini, duk da jikina ya ba ni tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Domin ni da ita kusan duk kanwar ja ce sai dai matsalarta ta fi tawa sauƙi linkin. 

    "Hmmmmm! Na gaji da matsalar Mama, kuma ba na so na yi abin da zai janyo mini wata rigima..." 

     "Ki yi haƙuri kamar yadda kika saba.Saboda mai haƙuri yana tare da Allah komai daɗewar lokaci, zai kawo miki waraka ta gano gaskiya gaskiya ce da yardar Allah..."

     "Mama ta yi nisan da ba ta jin kira, yanzu haka dawowar da na yi na iske ana damun fura a tsakar gidan nan. Amma har aka sha aka shanye daga ni har Yusuf babu wanda aka bai wa. A ganina ko ba mu da haƙƙi za a ba mu ladar ganin ido, sannan abin da kowa ya sani ne ina son fura amma ba su ji kunyar hana muna ita ba, daga ita Mamar har Sadiyar duka. Sannan ko ya dawo na faɗa masa haƙuri kawai zai ba ni. Ƙarshe ma ya bi ni da dogon sharhin ƙarya domin ya kare Mama kada a ga laifinta..." Cikin muryar kuka take magana, kafin na sauke ajiyar zuciya na ce, 

     "Ki yi haƙuri Amina ki bar su da girman haƙƙin da ke kansu, idan kina buƙatar furar ki saya ki sha ai ba faɗuwa ba ce". 

    Sautin sharar kukan da take yi a cikin wayar ya kashe mini jiki matuƙa, da lallami na kwantar mata da hankali har ta fahimta, kuma ta sauko daga dokin fushin da ta hau. Sannan muka yi sallama na kashe wayar bayan na tabbatar mata da zan fito aiki ranar Laraba.

     

     Shiru na yi na ɗan lokaci sannan na furzar da iska a bakina, na ƙara lalubo wayar MD na danna masa kira. Sai dai har ta tsinke ba a ɗaga ba, ban gaji ba na sake danna wani kiran, ringing ɗaya biyu aka ɗauka.


     "Assalamu alaikum" ita ce sallamar da na yi cikin karyayyar murya.

      "Wace ce ke?" Tambayar da aka jefo mini kenan a fusace cikin ɗaga murya, ƙirjina ya buga babu shiri cikin sauri na katse kiran. Saboda muryar macen da na ji hakan ya tabbatar mini da matar shi ta ɗauki wayar. Jikina ya hau rawa musamman kiran da na ga ya shigo wayata ɗauke da sunan MD. Kamar kada na ɗauka, sai dai na yi jarumtar ɗagawa cikin ɗar-ɗar saboda tsoron abin da za ta faɗa mini. 

     "Me ya haɗa ki da mijina har kike kiran shi a waya?" Shiru na yi saboda ban san me zan ce da ita ba. "Wannan kiran ya zamo na ƙarshe tsakaninki da shi matuƙar kina da sauran son kanki. Domin a kan mijina wallahi babu abin da ba zan yi wa duk 'yar iskar da ta raɓe shi ba. Idan kuma kina ganin faɗa ce kawai nake yi, to ki sake kula shi ki ga yadda zan sa a nemo mini ke a duk inda kike cikin faɗin duniyar nan.."  ƙitt ta datse kiran ta bar ni riƙe da waya a hannu na kasa motsin kirki tamkar wadda aka zare wa laka. 

    Cikin sanyin jiki da na gaɓɓai, na sauke wayar daga kunnena tare da sauke wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya. 'Gaba kura baya siyaƙi' zancen da na faɗa kenan cikin raina. Saran da na ji kaina ya yi ya sa na miƙe da nufin ɓoye wayar na ci abinci. Saboda masifaffiyar yunwar da nake ji, na yunƙura kenan saƙo ya shigo wayata. Da sauri na duba saƙon ƙirjina yana bugawa saboda fargaban kada a ce matar MD ce, sai dai na kasa ɗauke idona daga kan allon wayar saboda saƙon da nake ta maimaicin karatun shi a zuciyata. 

     'Ki yi haƙuri Zaituna. Na shiga wanka ne ban san kin kira ba. Me ke faruwa ne?'


     Ajiye wayar kawai na yi saboda ban san me zan ce da shi ba a lokacin, domin kwanyata babu komai a cikinta kamar an goge mini komai. Fita ɗakin na yi na nufi kitchen, cike da tabbacin ganin abin da zan jefa wa cikina don na san Ummu Salma ta yi mana girki. 

      Shinkafa da wake na gani, cikin sauri na zuba na dawo falo na zauna ina ci ina tunanin  kashedin da matar MD ta yi mini, wanda nake jin sautinta yana amsa-kuwa cikin kunnuwana tamkar a lokacin take magana. Ban san lokacin da na canye abincin ba saboda dogon nazarin da na lula.


    A gurguje na gama sallah, saboda kiran da ake ta yi mini wani bayan wani ga wayata da ƙara. Zabura na yi cikin zafin nama na ɗauki wayar a daidai lokacin da wani kiran ya sake shigowa. Da hanzari na danna kore saboda ganin sunan MD ɓaro-ɓaro a jikin wayar, kuma zuciyata ta tabbatar mini da shi ne ba matar shi ba. 


     "Don Allah ki yi haƙuri, kada ki ga na takura ki. Me ya faru ne na ga kiranki..." 

     "Daman wayar da na gani ce a cikin ledar da ka ba ni. Shi ne na ce ko ka manta ne ka sako ta a ledar..." katse ni ya yi da faɗin,

     "No! Taki ce ba mantuwa na yi ba. Kuma kada ki ɗauki ce wa na ba ki ita ne da wata manufa. Na ba ki ne a matsayin kyauta saboda ci gaban da kika kawo mana a cikin ma'aikatarmu. Muna alfahari da samun zaƙaƙurar ma'aikaciya irinki, fatan za ki karɓa hannu bibbiyu domin ki ji daɗin ƙara jajircewa a kan aikinki".


     Girmansa da mutuncin shi ya sa na ce da shi na gode "Na gode sosai Sir. Allah ya ƙara rufa asiri" Muka yi sallama a mutumce, amma a raina na so ya karɓi wayar shi. Ko ba komai zan yi nesa da rashin mutuncin matar shi, duk da ba na zaton ta san da wayar balle zancenta...

      

   "Da wa kike waya?" Ita ce tambayar da Mukhtar ya jefo mini ba tare da na ji motsin shigowar shi ba. Fuska na haɗe alamun babu sassauci ga duk abin da zan furta cikin bakina a lokacin. 

     "Ina ruwanka da wanda nake waya da shi. Ko kana da ikon duk wani motsin da zan yi sai ka san da zaman shi?" A fusace na yi maganar cikin ɗaga murya. Bai kula ni ba ya nufi wurin  wayar da ke kan gado har lokacin, ya fiddo ta a leda yana jujjuya kwalin yana girgiza kai. Ban hana shi ba har ya gama tsugudidin shi ya ajiye tare da rugume a hannu a ƙirji ya ce,


     "Wai me kike son mayar da kanki ne? A tunaninki Allah ba zai kama ki a kan cin amanar auren da kike yi ba...?"

      "Kafin ya kama ni kai ne mutum na farko da haƙƙi zai rataye maka wuya ka mutu a wulaƙance. Yanzu kai har kana da bakin faɗar ana cin amanar aure? Kai nawa ka yi kafin ni na fara? Ko ka manta bala'in da kake yi na tuna maka yanzun nan? Ka san darajar aure kake shiga hurumin wasu matan auren? To bari ka ji abin da ba ka sani ba, a yau duk abin da na zama wallahi kai ne ka ɗora ni a kan hanyar na miƙe ɗoɗar. Saboda matan auren da ka yi rayuwa da su haƙƙinsu ne ke ƙoƙarin fita a saman kaina..." 

     Jikina yana rawa nake faɗar maganar saboda tsananin ɓacin ran da maganar shi ta saka ni. Kafin shi ma ya katse ni da faɗar, 

     "Babu inda aka ce wai don wani ya yi abu kai ma sai ka yi. Ki bar ni da haƙƙinki da kika ce na ɗauka, ke kuma ki sauke wanda yake kanki ki huta. Amma wayar nan ko ki mayar wa ɗan iskan da ya ba ki ita. Ko kuma na sanar wa Umma tun da ni kin raina ni ba kya jin maganata..." 


A harzuƙe na ce "Duk inda za ka je ka faɗa ka je ka faɗa, amma wallahi ba zan mayar da wayar nan ba. Idan ka isa kai namiji ne ɗan halak, ka haɗa ni da takardar sakina uku yanzun nan ba sai anjima ba..."


     "Allah ya ba ki haƙuri. Tun da ke ba ki da wani zance a rayuwarki sai na saki".

      "Aurenka auren tsiya miye amfanin shi? Wallahi da irin wannan auren naka gara zawarcin mace dubu. Don kai ba mijin aure ba ne kuma ba ka kai namiji ba har yanzu..."

     "Ya isa! Kada ki nemi faɗa mini babu daɗi. Waya dai ce ki je ga ki ga ta nan. Idan wadda ta isa da ke ta zo ai sai ku yi maganar tun da ni kin mayar da wani shashasha". 

   

Daga haka ya fice fuu tamkar ya tashi sama, kallon banza na bi shi da shi sannan na yi tsaki. Wayar na mayar a leda sannan na ɓoye ta, don na san tsaf zai iya dawowa ya ɗauke ta ba tare da na sani ba. Zuciyata cike da alwashin ko Ummata ta ce na mayar da ita ba zan mayar ba balle shi.




Ku ci gaba da bi sannu a hankali za mu je inda warwarar ƙullin da ya wargaza zaman lafiyar auren Zaituna da Mukhtar 😅

No comments

Powered by Blogger.