Abokin Aikina Book 1 Page 3

 


LAMBA TA UKU.*


Ajiyar zuciya na sauke, sannan na yunƙura cikin rashin kuzari na sauko daga gadon. Ina layi na fice ɗakin saboda yunwar da ke ƙwaƙular cikina, kitchen na nufa kai-tsaye don jirin da nake ji ya tabbatar mini da ban

samu waraka daga ciwon da ke damuna kwana biyu ba, wanda yake hana ni sukuni a duk lokacin da babu komai a cikina. Turus na yi na ja na tsaya gaban kayan shayinmu. Domin a take na gano Mukhtar ya yi abin da ya saba, saboda kofin da ya yi amfani da shi ma a nan ya bar shi bai ɗauke ba, kamar yadda ya bar gwangwanin madarar a buɗe bai rufe ba, bayan milon da ya barbazar a ƙasan tiles har ya yi danƙo, domin ba na tamtama a kan lokacin da zai zuba ya sha shayin ne ya zubar da shi, saboda halin shi da sani na sakankance komai ba ya yin sa a nutse sai ya yi hargitsi. Sau tari idan zai ci tuwo kafin ya tashi daga cin tuwon nan sai ya zubar da miyar. Idan fura ce kuma da wuya ya gama sha a kofi bai zubar da rabi ba.


 Numfashi na ja tare da sauke ajiyar zuciya cikin ƙunar rai, a gurguje na ɗan gyara wurin sannan na ɗora ruwan zafi na haɗa tea. Saboda a yadda nake ji ba zan iya cin komai ba idan ba shi ba. Fitowa ta daga kitchen kenan ina ƙoƙarin komawa ɗaki, na ji muryar maƙociyata tana sallama, hakan ya tabbatar mini da Mukhtar ba ya cikin unguwar, domin a bin da na sani ne ba ta shigowa gidan sai ta tabbatar da ba ya nan, saboda tana cikin mutanen da yake zargin suna kawo mini tsegumin da yake haɗa mu rikici da shi a wasu lokutan. Na amsa mata sallama da disasshiyar muryata irin ta marasa lafiya. Tare muka nemi wurin zama a kan kujerun falon muka zauna, ina kurɓar shayin muka fara gaisawa babu yabo babu fallasa. Yanayin kallon da naga tana yi mini ya tabbatar min da akwai dalilin da ya kawo ta wurina, wanda ba na raba ɗaya biyu a kan rikicin da ya auku ne jiya. Wanda nake da tabbacin zuwa lokacin ya karaɗe ko'ina cikin unguwar da kewaye. Nan take na ji hawaye ya cika idanuwana, na ajiye ɗan sauran shayin da rage kan tebur, saboda zuciyata ta yi duhun da ba zan iya shanye shi ba. 

"Ban samu wayarki ba, shi ya sa na kasa haƙuri sai da na yi wanann tattakin. Saboda ba na so Mukhtar ya gan ni ya yi mini abin da raina zai ɓaci a banza..." "Me ke tafe da ke?" Ita ce tambayar da na jefo mata tun kafin ta dire zancenta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Ban ji daɗin abin da ya faru ba, kuma ban ji daɗin irin zantukan da ake yi a kanki cikin unguwar nan ba" Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da damuwa, shiru na yi na ɗan lokaci sannan cikin muryar kuka na ce "Ban ga laifin duk wanda ya zage ni ba, domin abin zagin ya ji ko kuma ya gani shi ya sa ya zage ni. Idan akwai mai alhakin laifin hakan to ni ce nan. Domin da ban yi biyayyar da nake yi a yanzu ba, da duk hakan bai faru ba. Na sani babu biyayya wurin saɓa wa mahalicci, amma na zaɓi tauye kaina na ci amanar kaina saboda farincikin mahaifiyata. Na sani kuma Allah ma ya sani babu wani abu na assha tsakanina da MD illa gaisuwar mutuncin da muke yi. Amma ban san miye a cikin zuciyar shi dangane da ni ba, domin da ban ji abin da ya faɗa ba kai-tsaye zan ce da kowa sharri Mukhtar yake ƙoƙarin yi masa, sai dai kuma idan na yi duba da sanin darajar ɗan'adam irin na shi. Zan daki ƙirji na ce sai Allah ya isar masa a kan duk wanda ya zarge shi a kaina. Ban ji daɗin kashin kajin da ya shafa wa kansa ta dalilina, duba da mutumtakar shi ta fi ƙarfin kwatar ɗan sauran mutuncin da ya rage, wanda Mukhtar bai gama watsar mini ba. Ban taɓa ganin aure irin nawa ba a duniya, ina ma ban rayu ba har zuwa wannan lokacin da nake wannan maganar. Na tsani kaina kuma na tsani kowa ma a duniyar nan..."  

Kuka na fashe da shi mai ƙarfi saboda ƙololon baƙincikin da ya tsaya mini a ƙahon zuci. Haƙuri ta fara ba ni, tana goge hawayen da na kula suna fareti saman fuskarta tun lokacin da na fara magana, sannan ta ce, "Idan ɓera da sata daddawa ma da warinta. Me ya kai ki shiga motarsa har ki bari ya kawo ki gida? A gaskiya dole Mukhtar ya ji haushin hakan, don ko ke ce kika gan shi da wata a mota za ki ji babu daɗi, shi ma da Allah ya halassta wa ya yi huɗu. Me ya sa ba ki hana kanki shiga motar ba tun a farkon tayin da ya yi miki? Ina da tabbacin da kin kauce wa wannan alfarma ta shi da kin tsira daga yamaɗiɗin da ake yi da ke. Yanzu wa gari ya waya? Ko fita kika yi za a nuna ki a ce ke ce, shin kin manta abin da ya faru baya kafin wannan? Haka za ki yi ta maimata laifi iri ɗaya wane kallo kike ganin mutane za su yi miki? Idan wancan gaskiyarki ta wanke ki, wannan kuma fa?" 


Shiru na yi kawai ina ci gaba da tsiyayar ruwan hawayen da suka kasa tsaya mini tamkar burgaggen famfo. Na sani ita mai tausayin halin da nake ciki ce, amma wani lokaci ina jin haushin yadda take ganin ban iya zaman aure ba ne, shi ya sa Mukhtar yake shuka mini tsiyar da ya ga dama. Duk da ina jin takaicin kallon da take yi mini, ina yi mata uzuri saboda ba ta haɗu da rabin kwatar matsalar da nake ciki ba ne. Na san da ta shiga makamancin halin da nake ciki, wataƙila za ta fahimci yadda abin yake. 


"A tara mata dubu ba za su iya haƙurin da nake yi gidan Mukhtar ba, a cikin matan dubu kuma har ke kanki Maman Taufiƙ ba za ki iya wata ɗaya da Mukhtar ba, a yadda na san halinki da tsattsauran ra'ayinki. Don haka ki bar kowa ya kalle ni a yadda ya fassara ni, ki bar kowa ya zage ni a yadda yake so. Na yafe wa duk wanda ya zage ni a cikin rashin sanin ba bisa haƙƙina ba, amma Mukhtar ba zan iya yafe masa ba ko da zan janyo wuta tana ƙona jikin shi..." 

     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Sau nawa zan ce ki san abin da kike faɗa Zaituna? Yanzu ribar me za ki ci idan kin yi wa mijinki uban 'ya'yanki Allah ya isa? Ba kya gudun wani abu ya same shi ta sanadin hakan?" Tambayoyin da ta jero mini kenan a ruɗe, saboda firgicin abin da ta ji a bakina, wanda inda da sabo ta saba ji amma ta kasa shanye wa kunnuwanta a duk lokacin da irin haka ta kama. 


"Gaskiya ki gyara furutan da kike furzarwa ga mijinki..." "Duk abin da ta yi mini ke kika janyo. Don ke kika shigo zuga ta kina fakewa da ban haƙuri" zancen Mukhtar kenan a tsakiyar kanmu, zumbur ta miƙe tana faɗin "Allah dai shi ne masani a kan komai. Domin yadda nake fatar na zauna da mijina lafiya  ita ma ina mata fatar hakan..." Idona a kanta ta fice ranta a ɓace, hakan ya sa na fara girgizar ƙafafuwana cikin matsanancin fushi na ce "Ranar da duk haƙƙin matar nan ya kama ka, wallahi ba za ka ji daɗin rayuwarka ba. Ka ji da haƙƙoƙan da ka ɗauka ka daina ƙoƙarin ɗora wa kanka wasu. Domin zargin da ke cin zuciyarka zai yi ta janyo maka musibar da ba ka san ina za ka shiga ba ranar lahira..." "Daman ai ke ba ki mini fatar na gama lafiya balle na shiga aljanna..." "Duk abin da za ka faɗa ka faɗa kanka tsaye, ni dai na sani haƙƙi bala'i ne mitsssss! Aikin kawai" 

   A fusace na miƙe na shige ɗakina tare da rufo ƙofa. Gado na faɗa ina rera kukan da na kasa tantance ainahin na mene ne nake yi. Shin tausayin kaina da ban yi sa'ar miji ba? Ko tausayin 'ya'yana da ban zaɓar musu uba nagari ba? Ko kuma tausayin MD da ya rufta rayuwar shi cikin bahagon auren da bai san lokacin haɗuwar shi da sanadin lalacewar shi ba? Ta ya zan fassara mafarin matsalata? Ta ya zan warware wa kaina baƙin ƙullin da ya hana ni jin daɗin aure? 'Allah kana gani ba ni da kowa sai kai. Ka kawo mini waraka daga matsalolin da ban san ya zan yi na shawo kansu ba'. Abin da na faɗa kenan a zuciyata cikin ƙanƙan da kai ga Ubangijina.


No comments

Powered by Blogger.