Abokin Aikina Book 1 Page 2

 


*LAMBA TA BIYU.*Ban san ya rigumar ta ƙare ba, domin shi kan shi tun da ya fita bai dawo gidan ba sai da dare ya ɗauke sawu kamar yadda ya ba. Na ci kuka har idanuwana suka kumbure babu

mai rarrashina. Mutum ɗaya ce nake da tabbacin za ta kwantar mini da hankali, sai dai ba zan so ɓata mata farinciki ba kamar yadda nawa ya gurɓace. Ƙarin takaicin kuma yaran duka ba su dawo gidan ba, wanda alamu ya nuna a can za su kwana wurin Ummata. Amma mamakina ba ta kira ta sanar da ni ba kamar yadda ta saba idan sun yi marmarin kwana gidan. 


    Ajiyar zuciya na sauke a lokacin da na juya kwanciyata, wadda nake jin suka cikin haƙarƙarina tamkar a kan ƙayoyi nake kwance. Sanin kuka ba zai yi mini ranar komai ba domin ba yau na saba yin irin shi ba, kuma har yanzu bai warkar mini da mikin da ke cikin zuciyata ba balle ya kawo mini waraka, daga ƙangin rayuwar da nake ciki. Wanda a kullum na tuna ina jin kaina tamkar wata marainiyar da ta rasa komai da kowa nata a cikin duniya.  Saran da kaina ya yi ya sa na yi hanzarin dafe goshina ina faɗin "Wash! Allah!" Saboda wani zafin da nake ji yana bi cikin jijiyoyin idona, wanda ya haifar mini da zugin da ya hana ni buɗe idanuwan har sai da ciwon ya lafa mini. Shiru na ɗan lokaci ina sauraren azabtuwar da nake fuskanta a cikin kaina har ma da zuciyata da ta karɓi nata kason, tana yi mini wani irin ciwo tamkar za ta tarwatse a cikin ƙirjina.


Daren ranar haka na yi bacci cikin rashin natsuwar zuciya da ciwon da ya ƙi bari na na huta. Da ƙyar na samu ƙarfin halin yin sallah sannan na lallaɓa na koma kan gado na ƙudundune cikin bargo. Daga tunanin da zuciyata ta lula ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba. A cikin baccin na ji muryar Ummata tana faɗa a sama tamkar a mafarki, sai dai buɗe idanuwan da na yi na gan ta tsaye saman kaina fuskarta a haɗe ya tabbatar mini gaske ne ba mafarki ba. Na yi ƙoƙarin tashi zaune cikin disasshiyar muryar da ta gaji da kuka na fara gaishe ta, ba tare da ta amsa ba ta fara feso mini abin da ke cikin bakinta, "Me kike so ki mayar da kanki Zaituna? Har yaushe kika yi girman da za ki fara bin wasu mazan waje bayan da auren wani a kanki. A zatona ko babu igiyar aure kanki za ki tsare mutuncinki ko don ki hana zagin da mutane za su yi mini, a kan riƙon sakainar kashin da ake ganin ni ce na yi silar mayar da ke abin da kika zama yanzu. Shin ba kya ganin rashin zaman lafiyar aurenki zai taɓa mini ɗan guntun mutuncin da ya yi mini saura a idon mutane? Kina buƙatar ki kashe aurenki ki zo mu jeru gida ɗaya ni da ke mu dinga haɗa kafaɗa babu mai aure a cikinmu?. Sau nawa zan ce ki yi haƙuri da halin Mukhtar ko don yaranki? To bari ki ji; Idan ma kin kashe auren gidan wani za ki sake zuwa, kuma bai zama lalle ki samu marar mata ko wanda bai da 'ya'ya ba. Kin ga idan kin ƙi sharar masallaci sai ki je ki yi ta kasuwa, domin kuwa dole ne ki yi wa 'ya'yan wasu bauta bayan kin watsar da naki a wulaƙance..." Kukan da ta fara yi ya ƙara damalmala mini komaina. Ban tsaya rarrashinta ba ni ma na fashe da nawa kukan cikin ƙunar zuciya saboda na kasa furta kalma ɗaya da zan kare kaina, wanda na sani ita kanta shaida ce a kan tsare mutuncin aurena da nake yi duk da bai zama ingantaccen aure kamar sauran aurarraki ba. Daga ni har ita kuka muke yi mun kasa rarrashin juna balle mu samu wanda zai rarrashe mu. 


Ita ce ta fara jarumtar tsayar da ruwan hawayen da take yi ta shiga fyace majinar kukan da ta sha, ta janyo ƙafafuwanta ta zauna a bakin gado cikin sigar rarrashi ta ce "Idan ban da tausayin yaran nan da nake yi, me zai sa mu fuskanci baƙincikin rayuwa irin wannan? Ki yi haƙuri Zaituna na san ina sara miki ko babu gaɓa. Amma ki sani ni na san abin da ya sa ba na fatan ki kashe aurenki. Kuma ina roƙon Allah ya hana ki zama bazawara, domin ni kaɗai na san duhun baƙincikin da ke damfare cikin hakan. Ubangiji ya yi miki albarka, yadda kike yi mini biyayya ke ma Allah ya sa 'ya'yanki su yi miki fiye da hakan". Tana ƙare faɗar maganar ta miƙe tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, na bi bayanta da kallo ina goge hawayen da suka kasa tsayawa cikin kwarmin idona.  Kiciɓis suka yi da Mukhtar wanda yake ƙoƙarin shigowa ɗakin fuskarsa a haɗe tamkar bai taɓa dariya ba. Ganin ta ya sa shi sakin fuskar shi kaɗan ya rusuna har ƙasa yana sosa ƙeya cike da girmama ya ce "Umma daman magana nake so mu yi dangane da aikin nan da take zuwa. Ni dai gaskiya ban lamunta da shi ba, idan akwai yiyuwar ta daina zuwa duka a duba mini. Saboda zuwa aikin ne yanzu duk wata matsala take kunno kai tsakanina da ita, amma idan aka jingine shi kamar an yi maganin rabin matsalolin da ke faruwa daga wannan sai wannan".  Shiru ya ratsa tsakani idona a kanta ina jiran amsar da za ta ba shi kafin na yi magana, domin na fuskanci nazarin maganganun shi da amsar da za ta bayar take yi.  "A gaskiya Mukhtar sai dai ka yi haƙuri da zancen aikin nan, domin ka sani ban da wani iko a kan hana mata zuwa aikin nan. Amma tun da ba ka so kana da ikon da ya fi na kowa a kanta. Ka je ka samu Alhaji Ali domin ka sanar da shi a kai ƙarshen maganar, saboda shigar da kaina cikin maganar yanzu zai sake janyo wata sabuwar rigima tsakanina da shi. Wanda ba na fatar hakan an yi na baya ina fatar kuma ba za a yi maimaici ba". ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi ina aika masa harara da jajayen idanuwana tamkar su fito su manne jikin shi. Saboda tsabar takaicin da yake ba ni ji nake kamar na taso na rufe shi da duka. "Ba sai na je ba, a bar zancen kawai. Umma amma a sanar da ita babu ita babu wannan mayaudarin mutumin. Domin wallahi yanzu haka mutane har sun fara zunɗena a kan na zama mijin ho-ti-ho, saboda ganin yadda na kasa raba ta da mutumin da yake ƙoƙarin keta mata haddin aure..." "Wane aure kake zance? Kai har kana da bakin faɗar kana aurena? Na rantse da Allah darajar Umma kake ci, da tuni na watsa maka fetur na ƙone ka..." 


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!" Ita ce kalmar da Ummata ta furta cikin kiɗimewa da tashin hankalin da ya bayyana kan shi cikin fuskarta. "Gara da ta yi gabanki kika gani Umma, haka take yi mini ko a gaban su Haidar. Ba ta jin kunyar faɗa mini magana domin ta wulaƙanta ni a gabansu. Ban san wace irin tsana ce take yi mini ba da ba ta iya ɓoyewa ko a gaban waye..." "Ban ji daɗin maganar nan ba Zaituna, ki san me za ki faɗa wa mijinki saboda gudun shiga matsala da fushin Ubangiji".  Nasiha ta shiga yi mini ina sharar hawaye, shi ma tana yi masa faɗan so-kanka a fakaice. Saboda har kullum tana jin nauyin shi da kunyar surukuntakar da ke tsakaninta da shi. Wadda ya dace a ce tuni ta watsar da ita ta huta, ko don kalolin cin amanar da yake yi mini.  A gabana suka yi sallama ta fice ya dawo kaina yana ƙare mini kallon wulaƙanci sama da ƙasa, sannan ya yi ƙwafa ya fice tare da buga mini ƙofar ɗakin da ƙarfi kamar zai ɓalla ta. 


No comments

Powered by Blogger.