Abokin Aikina Book 1 Page 15


 *LAMBA SHA BIYAR.*


            Ƙoƙarin buɗe ɗakin da na ji ana yi, hakan ya ƙara ƙarfin dakan luguden uku-uku da zuciyata ke yi. A ɗari na bazama da gudu na faɗa wata ƙofar da na gani, babu jinkiri na saka key tare da shan jinin jikina na lafe a jikin bango. Addu'a na dinga yi a zuciyata bayan na toshe bakina da nake gudun ya tona mini asiri.

        Takun tafiya na ji ana nufo bakin ƙofar toilet ɗin da na ɓuya, hankalina bai ƙara tashi ba har sai da na ji an sake taɓa handle ɗin ƙofar an murɗa. Babu shiri na darje daga tsayen da nake, saboda sulɓin tyles ɗin da ya ja ni zuwa ƙasa na yi zaman 'yan bori.

        Ƙuguna na dafe ina yarfa hannu saboda sosai na ji zafin faɗuwar. Shiru ban san sake jin motsin komai ba bayan takun tafiyar da na ji kamar an bar bakin ƙofar. Mintuna a tsakani na fara jin kukan yaron a cikin ɗakin.

     

     "Shiii!" Na ji ana faɗa wa yaron da muryar da nake da tabbacin ta MD ce, amma fargaba da tashin hankalin da nake ciki ya sa na ƙaryata hakan a zuciyata. Saboda ina gudun na fito ya zamana matar shi ce take kama da muryar shi, ko kuma a ce suna tare tsautsayi ya sa ta gan ni na janyo masa rigima daga taimako.

         

       Tsawon minti goma ina zaune inda nake ban motsa ba, har zuwa lokacin da na ji an fara ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin. Sannan na tsinkayo muryar shi yana faɗin,

       "Wannan shirun na lafiya ne kike yi a cikin toilet kuwa?"

         Dafa ƙirjina na yi sannan na sauke ajiyar zuciya tare da haɗiyar yawun da suka tsaya mini a maƙoshi. A daddafe na dafa bangon na miƙe ina jan ƙafafuwana da suka yi mini nauyi. Na buɗe ƙofar cikin sauri na kawar da kaina gefe, saboda kallon da yake aiko mini fuskar shi a haɗe mai kama da tuhuma. 

      Wucewa ya yi na biyo bayan shi caraf idanuwana suka sauka a kan jakar kayana, cikin sauri na nufi jakar ina faɗin, "Yanzu sai da ka je ɗauko..."

       Kuka ya suɓuce mini wanda ya hana ni ƙarasa maganar da na yi niyya. Shiru na minti biyu sannan ya yi gyaran murya ya ce da ni,       

        "Wannan jakar kaɗai na gani, amma ban ga ƙaramar ba. Ko a can gidan da kika shiga kika jefar da ƙaramar jajar ba ki sani ba?"


        "I, a can na zubar da ita, don ko da na shiga gidan tana maƙale a kafaɗata."

       "Za ki iya gane gidan idan mun je unguwar?"


    "Zan gane"

     "Ok! Tom da safe za mu koma ki karɓo jakar."


      "Ba sai mun koma ba na yafe musu." Na yi hanzarin faɗin maganar don ba na son su yi masa rashin mutunci, domin na fahimci tsagerun mutane ne. Kuma 'yan iska ne ajin farko. 

         "Za mu koma! Idan ma sun kawo mana rashin kunya sai na haɗa su da jami'an tsaro."


    Shiru kawai na yi masa don a ɗan zaman da na yi da shi, na gano mutum ne mai magana ɗaya. Kuma duk abin da ya furta ta tabbata babu sauyi ko da bai yi wa mutum daɗi ba. Jikin jakata na rakuɓe tare da yin tagumi har zuwa lokacin da yaron ya sake motsawa yana kuka. 

       Wanda ban lura da shi a kan gado ba har sai da kukan shi ya shiga dodon kunnena. Na yi hanzarin miƙewa na riga MD ɗaukar shi, jijjiga shi na fara yi tare da bubbuga bayan shi har ya sake komawa bacci. 

       MD ya ce na kawo shi ya kai wa mai aikinsu na ce ya bar shi wurina, daga haka ya fice ɗakin bai musa ba. Na lallaɓa na ajiye shi a kan gadon, sannan na zauna ƙasa na ɗora kaina saman katifar gadon. Hannuna riƙe da hannun yaron na shiga nazarin tafiyar da zan yi idan safiya ta waye. A gefe ɗaya kuma zuciyata cike take da fargabar abin da zai faru, idan matar MD ta yi ido biyu da ni a cikin gidanta.

      Ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba, sai bayan na farka idona ya kai kan agogon da ke manne cikin ɗakin. Wanda nake tantama a kan gaske ne abin da na gani ko kuma daman can ba ya aiki. Domin kuwa ƙarfe bakwai saura na gani. Abin da ya ƙara ba ni mamaki kuma; yaron da nake riƙe da hannun shi ba ya kan gadon, wanda alamu ya nuna an ɗauke shi ba tare da na san an shigo ɗakin ba. 

      Zumbur na miƙe na faɗa toilet na yi wanka agurguje saboda fitsarin da ke jikina har lokacin. Na yi arwala na fito na ƙargame ɗakin da makulli, sannan na yi sallah a gaggauce cike da tsoron kada ina sallah na ji saukar duka. 

       Na shirya cikin doguwar rigar shaddar da ke cikin kayana, sannan na saka mayafi mahaɗin shaddar ba tare da na shafa ko da mai ba. Jakata na ɗauka na fito daga ɗakin babu shiri na ja baya na rakuɓe, saboda ganin wata dattijuwar mata ta nufo ni da tire a hannunta, wanda nake da tabbacin abinci ne za ta kawo mini. 

      Kallon mamaki na bi ta da shi har ta shige ɗakin, saboda ganin ta gaishe ni cikin mutunci da sakin fuska tamkar ta san ni. Yaƙe kawai na yi mata a lokacin da ta ce da ni,     

       "Hajiya ki koma ki karya kafin ki tafi. Yar laɓai ya ce idan kin gama ki same shi waje." 

        Bayan ta wuce na ja jakata ba tare da na bi ta kan abincin ba. Sauka na yi ƙasa da sauri har da sassarfa cike da burin na fita gidan ko da hankalina zai kwanta, domin na huta da fargaban da nake ciki. 


       Cikin motar na same shi yana sauraron ƙira'ar sudes daga cikin ayoyin ƙarshe na suratul Rahman. Ban jira ya ba ni umurni ba na buɗe motar na shige ina zarar ido rungume da jakar kayana. Kai-tsaye ya fice gidan ba tare da ya ce da ni komai ba ya cilla motar a kan titi. Sai da muka yi doguwar tafiya muna gaf da shiga unguwar da na baro jakar, sannan ya ce da ni, 

        "Idan mun kai gidan ki sanar da ni."

        Daga haka ya ja bakin shi ya tsuke ni ma ban ce komai ba sai kai da na ɗaga alamu 'To'. Tun daga nesa na nuna masa gidan ya ci birki a  daidai ƙofar gidan, sannan dukanmu muka fito ya ce na jira shi a nan. Cikin gidan ya ɗan tura kai tare da ɗaga murya ya fara rafka musu sallama, sannan na ga ya dawo ya jingina bayan shi jikin motar shi yana dannar waya.  

       "Ku ƙaraso za ku hango motata."


    Maganar da na ji ya faɗa kenan a cikin wayar sannan ya mayar da ita aljihu, a daidai lokacin da wani ya fito daga cikin gidan yana ƙare mana kallon sama da ƙasa. 

       Yana ƙoƙarin yin magana muka jiyo jiniyar motar 'yansanda, a ruɗe na kai kallona ga fuskar MD, cike da mamakin abin da ya sa shi kiran su tun kafin a yi musu zancen jakar. 

       Ko da na dawo da kallona a kan ƙofar gidan wayam na gani babu mutumin da ya fito gidan balle alamun shi. Yansandan suka ƙaraso wurin suka bai wa juna hannu da MD suk gaisa, sannan wani daga cikinsu ya ce da shi, 

      "Ya kuka yi da su?"


        "A fito mana da su duka idan har sun ƙi bayar da jakar da kayan cikinta a yi musu duk abin da ya dace."

      Abin da MD ya faɗa kenan fuskarsa a haɗe tare da rungume hannun shi a ƙirji yana feso iska a bakin shi. Ɗaya ɗan sandan ya fara yi musu sallama kamar yadda MD ya yi a farko. Mintuna a tsakani sai ga maza da mata suna fitowa daga cikin gidan fuskokinsu ɗauke da tsoro.

       Sai da 'yansandan suka ƙare musu kallo sannan ɗaya ya ce da su, "Ina jakar wannan yarinyar da kuka ƙwace a cikin gidanku?" Kallon juna suka fara yi kamar ba su san komai ba. 

          "A gaskiya ranku ya daɗe ba mu san komai dangane da batun jaka ba."

 Zancen wata koɗaɗɗiya kenan wadda fuskarta ta gama ƙonewa da bilicin. Maganar MD na ji a fusace cikin ɗaga murya ya ce, "A cikinsu wace ce ta zare miki hajabi?"  Idona a kan Ummita na nuna ta da hannu tare da ƙarin bayani kamar haka, 

       "Ita ce ta cire mini hijabi, wurin kiciniyar cire mini riga jakar ta faɗi a wurin, lokacin da zan fito kuma na bar ta a can, saboda gudun tsira na manta shaf ban bi ta kan jakar ba."

       "Minti biyar aka ba ki ki fito da jakar nan yanzun nan." 

          Wani daga cikin 'yan sandan ya yi maganar tare da nuna Ummita da bakin bindigar da ke hannun shi.  Ummita ta fara zarar ido tana nuna kanta cikin wayancewa da ƙoƙarin zare kai ta ce, 

        "Ni ban ɗauki jakarta ba, sai dai idan a cikinsu wani ya ɗauka ban sani..." 

       Bahagon marin da wani ɗan sanda ya kwaɗa mata, babu shi ta fasa ihu tare da komawa cikin gidan da gudu tamkar wata zararriya. Tara-tara 'yansandan suka yi da sauran maza da matan gidan suka jefa su motar shiga-ba-biya, sannan wata 'yar sandar da ke cikinsu ta faɗa gidan a sukwane.


      Minti biyar kacal ta fito riƙe da ƙugun Ummita da ke riƙe da jakata tare da wani matashi hannun shi da ya ɗaga hannun shi sama alamun miƙa wuya. Motar aka watsa su duka sannan aka ba ni jakata bayan na buɗe ta gaban kowa, kuma na tabbatar musu da komai yana ciki yadda na saka. 

       Motar 'yansandan ta fara barin ƙofar gidan tare da mutanen gidan da suka kwasa, kafin ta MD ta bar wurin tare da ni da ke baya na hakimce ina hurar hanci. Amma duk da hakan nan take gumi ya jiƙa mini fuska, zuciyata ta hau bugawa da sauri tamkar za ta fasa ƙirjina ta fito waje. 

       Saboda hango Mukhtar dumu-dumu a cikin 'yan kallon da suka zagaye mu suna rabon idon ganin ƙwam. Wanda shi ma nake da tabbacin ya gan ni a lokacin da zan shiga motar MD, na yi mamaki matuƙa da ganin shi wurin, tare da ko-in-kulan da ya yi wa ganina ba tare ya nuna ya san ni ba, balle ya ɗauki mataki a kaina ko a kan MD.


     Ban dawo natsuwata ba har sai da na ga mun shiga gidajen Sama road, mamaki ya so kashe ni saboda ganin da na yi ya doshi hanyar da za ta kai mu Bafarawa Estate. 

      'Ina zai kai ni?'

Ita ce tambayar da na yi wa kaina a zuciya, sai ga amsa tiryan-tiryan ta bayyana kanta. Domin kuwa ƙofar gidan Kawu Sale ya ci birki, gidan da Ummata take rayuwa tun da jajayen sawu har yanzu da girma ya kamata.

      "Fita ki je! Kuma ki yi mini sallama da Umma!"

      Zancen MD kenan a fusace kuma cikin ɗaga murya. Haka na fito tamkar wadda aka kama ta yi wa Sarki ƙarya. Haka na fito jiki a mace na ja jakar kayana da ta hannuna na yi cikin gidan, ba tare da na waigo ba balle na damu da ce masa na gode. 

        Saboda har raina ban ji daɗin taimakon da ya yi mini ba, tun da har  ya kawo ni gidan a maimakon tashar da nake so ya kai ni. 

       'Tukunna ma wa ya sanar da shi unguwar su Umma da gidan duka?' 

        Tsaki na ja sannan na faɗa gidan ko sallama babu na yi ɗakin Inna Kulu ina haɗe fuska. Ummata da Inna Kulun duk suna tsakar gidan amma babu wanda na yi wa magana. Saboda tsabar mugun haushin da MD ya cusa mini a zuciya, ji nake yi tamkar na kama da wuta na ƙone ƙurmus kowa ma ya huta.

      Ina ji lokacin da wani yaro ya  shigo yana sanar da Ummata ana sallama da ita waje. Ban san ya aka yi ba ni dai na ji ta shigo tana balbala faɗa tamkar ta ci babu. 

     Sai ga ta cikin ɗakin tamkar an jefota, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba kawai ta fara kai mini duka da hannu bibbiyu tana kuka. Da ƙyar Inna Kulu ta taɓe ni a hannunta bayan ta gama jibga ta son ranta har da gwabra kaina a bango. 

         Ban haushin abin da ta yi mini ba, domin ba na tantama a kan ta yi hakan ne kawai saboda ta huce haushin da na ba ta a lokacin, wanda ni ko kaɗan ban ji dukan ba, don zafin da zuciyata ke yi ya fi dukan da take yi mini linkin.

            Inna Kulu ta fitar da ita daga ɗakin tana haki, tare da jifa ta da miyagun maganganun da suka tsaya mini a zuciya.  Wanɗanda suka saka ni sabon kuka tare da yi wa Mukhtar Allah ya isa ta fi dubu, saboda shi ne ya shiga tsakanina da ita, kuma sanadin shi ne ta fara kyara ta, tare da jifa ta da miyagun kalamai munana, a duk lokacin da rigima ta haɗa ni da shi. 


      'Ina mafita?'

            Tambayar da na yi wa kaina kenan bayan na gama naɗe maganganun Umma a kwanyata. Domin babu komai a cikinsu sai muguwar fata gare ni, a kan muddin ban koma gidan Mukhtar na ci gaba da zaman 'ya'yana ba.

No comments

Powered by Blogger.