Abokin Aikina Book 1 Page 14

 


LAMBA SHA HUƊU.*


          Tafe nake ina sharɓen kuka tare da jan jakata har na fita unguwarmu. Babu motsin komai da kowa, garin ya tsit illa karnukan da nake jin kukansu nesa da ni jefi-jefi. 

      Sai da na yi tafiya mai nisa sannan na fara jin wani ƙugi da gurnani a bayana, cikin sauri na juya tare da dakan luguden da zuciyata ke yi. Ido na zare ina ƙoƙarin  tafiya da baya-baya saboda wani Mahaukacin karen da na yi  tozali da shi yana zaro harshe. Jefar da jakar kayana na yi cikin matsanancin tsoro na zunduma da gudu. Shi ma ƙaton baƙin karen ya biyo ni aguje yana ta haushi "Wu! Wu!" Tamkar an ba shi kwangilar cinye ni da raina.

        Gudu nake yi iya ƙarfina yana bi na da ihu tamkar yana ƙoƙarin kama ɓarauniyar da ta yi gagarumar sata. Cikin sa'a na afka wani gida da na hango ƙofar shi a buɗe. Saboda duka gidajen da ke unguwar a rufe suke ruf, kuma ban yi Hausar samun wata kwana ko lungun da zan ɓoye masa ba.

        Sakata na danna wa ƙofar gidan jikina yana rawa, ga numfashina da ke ta hawa da sauka cikin sauri saboda tsabar tashin hankalin da na shiga. Haushin da karen yake yi a bakin gidan yana yagar ƙofar ya sa na ƙara ɗimaucewa. Na bazama da gudu na yi ƙofar da na hango ta miƙe, na zarce cikin gidan a miliyan ina ihun a kawo mini agaji.

       Mutanen da na gani suna fitowa daga ɗakunan gidan babu suturar kirki a jikinsu, hakan ya sa na fara rabon ido ina neman wurin wanda zan nufa da sigar taimako. Domin kuwa a kallo ɗaya na gano ba gidan mutanen kirki ba ne, duba da yadda dukansu suke tamkar tsirara kuma ba su ji nauyin fitowa a yadda suken ba.

       Kuka na fashe da shi ina ja da baya saboda mugun kallon da na ga suna bi na da shi, a ruɗe na fara faɗin, 

        "Don Allah ku yi haƙuri Wallahi kare ne ya biyo ni zai cije ni, ga shi can ma yana ƙoƙarin haurowa ta katanga domin ya illata ni."


     Kallon juna na ga suna yi kafin su fashe da dariya, wani ɗan gajeren cikinsu ya nufo ni yana wasar baki. Na fara ja da baya ina faɗin,

           "Don Allah ku yi haƙuri Wallahi ban san lokacin da na shigo gidan nan ba".


      Daga mazan har matan dariya suka fashe da ita, sannan dukansu suka zagaye ni duk da ƙoƙarin guduwar da nake yi sai da suka yi nasarar hana ni. Wata tsamurmurar yarinya ta nufo ni daga ita sai towel a jikinta, ganin yanayinta ya sa na ƙura mata kallo har ta iso gabana ta tsaya. Hijabin da ke jikina ta fara ɗagawa na yi hanzarin buge mata hannu, ta yi mini wata munafukar dariya tana faɗin, 

        "Fuskarki ta nuna za mu ci abinci da ke. Don haka ki bari mu gama tantance ki kafin mu yarda da ke, don ba na raba ɗaya biyu a kan cewa rashin gaskiya kika fito yi a cikin daren nan, da aka zo kama ki shi ne kika gudo kika zo gidan nan domin mu cece..."


      "Ba rashin gaskiya ta fito da ni daga gida ba, asali ma baƙincikin da nake ciki ne ya sa na kasa haƙuri na fito zan koma gidanmu."

        Ban yi aune ba na ji ta kai hannunta ta taɓo ƙirjina, da azama na sake buge mata hannun. Cike da jarumta na fara nuna ta da hannu cikin ƙololuwar ɓacin rai na ce, "Ban zo gidan nan don ku wulaƙanta mutuncina ba, taimako na zo ku yi mini saboda tsoron karen da ya biyo ni. Don haka ku yi haƙuri yanzu zan tafi ba sai kun nemi tozarta martabata ba."

      Ina ƙare faɗar hakan na juya da nufin raɓa waɗanda ke bayana na wuce. Caraf na ji an janyo hijabina ta baya babu shiri na juya cike da tsoron da ya cika mini zuciya, kallon mamaki da rashin mutumci na hango kwance a kan fuskokinsu, ya san natsure.  Nan take hantar cikina ta kaɗa na fara rawar murya ina faɗin, 

           "Don Allah ku yi haƙuri Wallahi mijina ne ya koro ni cikin daren nan."

       "Mu dama irinki muke nema, waɗanda ake cewa je-ki-kya-gani. Domin da kin fito mu ne za ki taras. Ummita tuɓe mana ita yanzun nan mu albarkaci daren nan da kalacinta."

        Abin da na ji ya faɗa ya sa fitsari kufce mini, jikina ya hau rawa tamkar mazari hakan ya bai wa fitsarin damar tsiyaya daga jikina yana sauka ƙasa. Ja da baya na fara yi saboda ganin wadda aka kira Ummitar tana nufo ni, waɗanda ke bayana kuma suka rirriƙe ni ta fara kiciniyar cire mini hijabi ina ƙoƙarin hana ta.  

       Mahaukacin mari na ji ya sauka kan fuskata har sai da na hango taurari, kafin na dawo cikin hayyacina na ji an fisge hijabin nawa. Abin bai tsaya iya nan ba suka fara ɗaga doguwar rigar dake jikina aka yi sama da ita za a cire mini. Hannuna na fara ƙoƙarin ƙwata da nufin na hana su tuɓe ni.

       Wani saukar wani marin na ji a gefen fuskata har saman idona. Azabar da ta ziyarce ni ta sa na fasa ƙara tare da kukan kura da niyyar ƙwatar kaina. Muka fara kokawa ni da su har suka yi nasarar raba ni da doguwar rigata, suka bar ni daga wata guntuwar vest mai kama da bra, sai dogon wandon legis da ke sanye a jikina.

         Idona a rufe na zille daga riƙon da aka yi mini na duƙe, hakan ya ba su damar rufe ni da duka. A duƙen da nake na yi sa'ar damƙo ƙasa, da hannuna biyu na kwaso na watsa musu a idanuwa. Ban yi jinkirin komai ba na nufi hanyar fita gidan da gudu suka biyo ni, cikin sa'a na zare sakatar na fice ina ta gudu. Biyo ni suka yi suna mini ihun ɓarawo har muka hau babban titi, a daidai lokacin d wata mota ta haske ni da ƙwan fitilarta mai mugun haske, wanda ya sa na ja na tsaya saboda na kasa gaba balle baya. 


    "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"   Ita ce kalmar da na ji an ambata cikin kunnuwana.  Muryar da na ji ta sa na hau rarraba ido ina neman ta ina zan hango shi, domin ko a cikin mafarki na jiyo sautin ina shaidar muryar MD balle a farke. 

      Abu na ji an ɗora mini a jiki ana ƙoƙarin yi mini lulluɓi, saboda har lokacin hasken yana kan fuskata ina ƙoƙarin karewa da hannuna.  Ja na na ji an fara yi ina tirjiya tare da faɗin don Allah ku yi haƙuri, saboda ban da tabbacin masu bi na ne ko kuma MD da na ji muryar shi da ƙamshin turaren shi. 

       Lallausan hannun da na ji an riƙa ni da shi ya sa na yi ammana da shi ne kai-tsaye na bi shi. Sai da ya saka ni cikin motar ya rufe sannan ya shiga ya tayar aguje ya bar wurin. Tafiya mai nisa ya yi kafin na ji ya sauke ajiyar zuciya mai sauti, a lokacin ganina ya dawo daidai ina sharɓen hawaye tare da shesshekar kuka cikin sauti. 


    "Ina zan kai ki?"


Ita ce tambayar da ya jefo mini wadda ta zamo magana ta farko da ta shiga tsakanina da shi. Ban ce da shi komai ba ina ci gaba shesshekar kukana har sai da ya sake tambayar, sannan na yi ƙarfin halin faɗin,


      "Tasha"


      "Ba zan je tasha a yanzu ba, domin ko na je ba lalle ne a samu abin hawa ba."

         Maganar da ya yi kenan cikin matsanancin fushin da ya kausasa muryar shi. 

     "Ba ni da kowa a garin nan.. Birnin Keb...bi zan..je." Na ƙare maganar da ƙyar saboda kukan da ya ci ƙarfina. Daga haka bai sake cewa da ni komai ba har muka je wata unguwa, a lokacin da ya isa bakin wani ƙofar gida ya fara horn Maigadi ya wangale masa babbar ƙofa.

        Nan take ƙirjina ya buga, cikina ya katsa saboda tunanin da ya ɗarsu raina. A kan zancen da zuciyata take sanar da ni gidan shi ne ya kawo ni, hakan ya saka ni faɗuwar gaba tare da wani sabon tashin hankali. Saboda tuno masifar matar shi da irin kashedin da ta yi mini a kan shi.

      

    "Fito mu je!"


    Zancen da ya yi kenan sannan ya yi gaba, ni kam motsin kirki kasa yi na yi balle na samu kuzarin fita daga motar, na bi shi kamar yadda ya umurta. Tsawon minti biyar ina cikin motar ban motsa ba, cikin tashin hankalin da ya saukar mini da gumin da ya jiƙa mini fuska nan take.


    "Ki fito na ce!" 


    Maganar shi kenan da na sake ji a cikin kunnuwana cikin tsawa tare da saukar abu a jikina, hannu na saka na  ɗauki abin da ya jefo mini a jiki na shiga warware shi. Fahimtar hijabi ne ya jefo mini na saka, ya sa na yi hanzarin sakawa kafin na  fito daga motar. 

      Bayan shi na bi tamkar raƙumi da akala har muka shiga cikin gidan muka haye sama, mun wuce wasu ɗakuna sannan muka isa wani ɗakin ƙarshe ya tura ƙofar muka shiga. 

      Ƙamshin da ya daki hancina da raɓar da ɗakin ya kwasa nan take jikina ya yi sanyi ƙalau. Kujera ya nuna mini na zauna sannan ya fice mintuna goma tsakani ya dawo ɗauke da plate ɗin abinci. 

       Gabana ya ajiye sannan ya nufi firij ya ɗauko gorar ruwa da Hollandia ya sake ajiyewa a gabana. Zama ya yi nesa da ni yana haɗe fuska ya ce, 

"Ki ci abincin."

 Kai na fara girgizawa domin ba zan iya magana ba.


"Ki ci na ce!"


     Tsawar da ya katsa mini ce ta sa na yi hanzarin jawo plate ɗin na buɗe, Indomie  shaƙe a cikin plate ɗin sai dafaffen ƙwai guda biyu har an ɓare.

      Cokali mai yatsun da na gani a ciki na shiga ɗebo abincin ina kai wa bakina hawaye yana zarya a kan fuskata. Sai da na kusa cinyewa sannan na ajiye cokalin na sha ruwa, bai matsa mini a kan na sha madarar Hollandia ba. Illa kafe ni da idon da ya yi fuskarsa a haɗe wanda idon shi yake nuna mini tamkar ya rufe ni da duka.


     "Me ya fito da ke a cikin tsohon daren nan?"

       Tambayar shi kenan zuwa gare ni, ina zuƙar majinar kuka na ce, "Tafiya zan yi." 

"Zuwa ina?" 

"Kebbi."

        Shiru ya ratsa tsakani bayan na sanar da shi inda zan je, duk da ba haka ne gaskiyar abin da ke raina ba. Domin babban burina a lokacin na yi nesa da duk inda aka san ni, balle na je inda za a dawo da ni gidan Mukhtar domin na ci gaba da zaman 'ya'yan da nake yi. 


      "Me ya haɗa ki da mutanen da na ga sun biyo ki?"

         Ya sake jefo mini wata tambayar, kai-tsaye na sanar da shi duk abin da ya faru. Sai dai ban sanar da shi Ummita ta taɓa ƙirjina ba, saboda na tsani duk abin da zai zubar mini da ƙima a rayuwata.


      "Me ya sa ba ki bari da safe ki yi tafiyar ba? Yanzu da ace wani abu ya same ki a hannun waɗannan azzaluman wa gari ya waya? Ga shi kin zubar da jakunkunanki, wataƙila ma akwai abubuwa masu muhimmanci a ciki."

      Maganganun da ya faɗa kenan cikin faɗa tare da ɗaga murya, cikin tsoro na dinga kallon ƙofar ɗakin saboda tunanin yadda zan kare kaina idan matar shi ta iske ni tare da shi a ɗakin.


      "Daidai ina kika jefar da jakunkunan?" 


          Sai da na haɗiye yawun tsoro sannan na yi masa bayani, tare da tsoron kada ya ce zai koma ɗauko su wani abu ya same shi saboda ni. Bayan haka kuma ba na so ya bar ni gidan matar shi ta nemi salwantar mini da rayuwa, don na san muddin ta yi ido biyu da ni sai buzuna. 


     "Me da me ne a cikin jakar?"  

       "Credentials ɗina ne da wasu 'yan kayana, sai wayata da ATM tare da sauran wasu tarkace."

       Na ba shi amsa jikina yana rawa, kai-tsaye ya nufi hanyar fita ɗakin tare da faɗin,

 "Jira ni yanzu zan dawo."

      Zumbur na miƙe tare da rawar jiki da ta murya ina haɗiyar yawun tsoro masu wucewa muƙut a wahalce. Kuka na dawo yi masa ina faɗin, "Don Allah ka bar kayan nan kada ka koma ba sai an ɗauko ba, idan ma za ka je mu je tare dukanmu daga can ka ajiye ni wani wuri na jira asuba." 

            "Babu inda zan je da ke! Ki jira ni a nan yanzu zan dawo." 

         Yana ƙare faɗar hakan ya fice tare da rufe ni ta baya, dole na durƙushe jikin ƙofar ina wani irin kuka mai kama da na mutuwa. Saboda abubuwa sun cakuɗe mini a kwanya na rasa me zan kama na ji sanyi. 

        

       Na daɗe a cikin halin kafin na fara jiyo sautin kukan yaro wanda ya sa hantata kaɗawa, domin hakan ya tabbatar mini da dole ne matar shi ta farka duk nauyin baccin da take yi. Kuma faruwar hakan tamkar fallasa asirin rufin ɗakin da aka yi da ni ne, wanda alamu ya nuna mini kafin ya dawo ta yi watanda da naman a cikin gidan. 


     Safa da marwa na fara yi da a tsakiyar falon, hannuna a ka ina tsiyayar ruwan hawaye mara sauti. Kukan yaron na ji ya yi yawa, da muryar shi gwanin tausayi. Na nufi ƙofar ɗakin na kara kaina jikin ƙofar domin na ji ko akwai wani motsi bayan na shi. 

      Amma har ya ci kukan ya bari don kan shi  ban ji muryar kowa ba balle wani motsi. Ƙarfe biyu da rabi na dare da mininti shidda, na ji alamun takun tafiya yana kusanto ɗakin da nake, gabana ya ƙire ya faɗi dum-dum! A lokacin da na ji ana murɗa ƙofar ɗakin da nake ciki.


No comments

Powered by Blogger.