Abokin Aikina Book 1 Page 1

 


*@HADIZA D. AUTA*



*LAMBA TA ƊAYA.*


*_True life story_*


Tun da na shiga cikin motar shi, zuciyata ta fara dakan luguden uku-uku. Saboda tsananin tashin hankalin da ya kawo mini ziyara, domin ni kaina na san illar da hakan zai haifar mini. Na yi hanzarin dafe goshina tare da faɗin wash! Saboda mugun saran da na ji a tsakiyar kaina. "Subhanallah! Me ya faru?" Ita ce maganar da ta fito a bakin MD cikin kulawa, tare da damuwar da ta kasa ɓoyuwa a kan fuskar shi. Kafin daga baya ya ci gaba da ce wa "Ki daina saka kanki a damuwar da ke haifar miki da ciwon kan nan naki. Saboda lafiyarki tana da matuƙar amfani a wurina..."  ƙarshen maganar shi ba ƙaramin duka ta yi wa zuciyata ba, babu shiri na yi hanzarin kai kallona a kan fuskar shi.. "I, kina da matsayin da ciwonki ya dace mu shiga damuwa sosai a cikin ma'aikatarmu" ba shiri na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, fargabar da ta tokare mini maƙoshi tana ƙoƙarin toshe numfashina ta faɗa. Sannan ya ɗora sharhi a kan maganar shi da ce wa "Dalilin hakan ya sa muke takaicin sabuwar lalurar nan da ta same ki. Wadda take ƙoƙarin kawo mana tawaya a cikin cigaban da muke samu ta ɓangaren jajircewarki. Ki daure ki sha magungunanki kamar yadda likitan ya umurta.  Sannan ki samu relief na tsawon kwana uku kafin ki koma wa aikinki. Ubangiji ya ƙara lafiya" "Amin" na amsa cikin maƙoshi saboda har lokacin ban daina jin saran gudumar da ake yi mini a tsakiyar kai ba. A sakamakon somewar wuccin-gadin da na yi ina tsaka da aiki a cikin Offishina.


Har ƙofar gidan ya ajiye ni ba tare da ya damu da matsalar da hakan za ta haifar mana ba daga ni har shi. Na fito motar jiki babu kuzari ina ƙoƙarin yi masa godiya ya miƙo mini ledar magungunan, da ya tsayu kai da fata jikin shi da aljihun shi har na farfaɗo na samu kaina.  Na zura hannu da nufin karɓar ledar babu zato muka zabura dukanmu, saboda dukan da muka ji an yi wa gilashin motar shi na gaba. Wanda a lokaci ɗaya ya tarwatse har yana barazanar bugun fuskokinmu. Da sauri na yi baya cike ƙoƙarin janyewa daga jikin motar, shi ma MD ya fito daga motar cikin zafin nama. Ƙirjina ya shiga bugawa a dalilin ido biyun da na yi da curarriyar fuskar Mukhtar. Wanda ke tsaye riƙe da ƙaton ice yana huci tare da aika mini mugun kallon da fitsari ya so suɓuce mini.  Kafin na yi wani yunƙuri ya fara ɗaga gandamin icen ya ci gaba da dukan gilasan motar MD babu-ji-babu- gani. Ɗaga icen yake yi yana sauke shi a kan motar iya ƙarfin shi gabaɗaya ya canza mata kamanni. Cikin tsananin tashin hankali na kai kallona ga MD da ke tsaye rungume da hannuwansa a ƙirji, yana ƙare wa Mukhtar kallon da na rasa gane ainahin abin da yake nufi da hakan. Cikin azama na nufi Mukhtar jiri yana kwasa ta da nufin hana shi aika-aikar da yake yi, sai dai kafin na isa wurin shi na yi azamar duƙewa ƙasa saboda hango icen da na yi dishi-dishi a sama yana ƙoƙarin faɗowa kaina. Shirun da na ji ya sa na ɗago kaina na gani da zummar ko dai idanuwana ne bai hango daidai ba. A kiɗime na miƙe jikina ya hau rawa saboda hango Mukhtar a yashe ɗan nesa da ni, icen kuma a hannun MD yana huci cikin matsanancin ɓacin ran da ya bayyana kan shi a kan fuskar shi. Hannu ya shiga nuna Mukhtar da shi cikin wata kausasshiyar murya ya ce "Zan haƙura da rasa komai amma ban da Zaituna. Ka yi duk abin da kake so zan kawar da kai amma kada ka yi gangancin taɓa martabarta balle lafiyarta. Wawa kawai soko wanda bai san darajar aure ba". 


Kafin na gama tantance abin da ƙwaƙwalwata take son sanar da ni, tafin Mukhtar ya fara sauka a cikin dodon kunnuwana, sosai ya so ƙara zautar  da tunanina ya hautsine mini kuzarin jiki da guntun tunanin da ke cikin kaina. Musamman maganganun da ya fara faɗa waɗanda suka zamo tamkar ɗigar ruwan dalma a jikina. "Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Haka ma rana dubu ta ɓarawo ɗaya tak! Ta mai kaya ce. A yau ka fasa ruɓaɓɓen ƙwan da kuka daɗe kuna ɓoyewa a tsakaninku. Da kanka ka yaye labulen sirrinku, ka fallasa asirinku saboda girman haƙƙin aure da ke bibiyar rayuwarku. To ka sani ka yi kuskure kuma ka yi gangancin shiga gonar da ba taka ba. Kuma ko za ka mutu a kanta wallahi ba zan taɓa sakinta ba balle ka aure ta. Ke kuma sai na nuna miki ba irina ake cin amana a zauna lafiya ba..".


Ƙare maganar shi ta yi daidai da fisgar da ya yi wa hannuna tamkar zai raba shi da gangar jikina, ina tirjiya tare da kai wa hannun shi duka da ɗan ƙarfin da ya rage mini. Amma hakan bai hana shi jefa ni cikin gidan ya wullar tsakiyar ɗakina ba. Ina ji ina gani ya saka mini key ya rufe ni ruf a cikin ɗakin ba tare da ya jira jin komai daga bakina ba. Na fara dukan ƙofar ɗakin ina kuka cikin disasshiyar muryata tare da ƙwala masa kira cikin ƙarfi ina faɗin; ya tsaya ya fahimci yadda abin yake, saɓanin abin da ya zata kuma ya yi tsammani tsakanina da MD. Amma hakan bai sa ya buɗe ni ba balle ya yi lokacin jin ta bakina kamar yadda na sha sanar da shi koyaushe.



ABOKIN AIKINA. Zai zo da zafin shi a cikin wannan shekarar. Free ne ga kowa saboda darussan da ke cikin littafin abin tausayi abin takaici abin koyi ga wasu nagartattun halaye. Abin gudu abin ƙyama daga wasu gurɓatattun halayen da za su zo a cikin littafin ABOKIN AIKINA.


No comments

Powered by Blogger.