Daudar Goran Book 2 page 1

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (001)

.......A matuƙar razane Iffah ta shiga girgiza Tajwar Eshaan jikinta na rawa, gaba ɗaya ta daburce jin jikinsa ya saki ma gaba ɗaya a kanta, hannu ta kai saitin hancinsa, ƙirjinta ya sake girgiza tamkar zuciyarta zata ɓallo daga cikinsa ta faɗi. Cikin fita hayyaci ta cigaba da ɗan girgiza kafaɗunsa dake jikinta da faɗin, “Karka min haka, dan ALLAH ka tashi, ka tashi ka faɗamin, ka faɗamin wanene kai, wanene Ajmaal? Minene alaƙarka da shi? Idan ka mutu nima wlhy mutuwa zanyi... wayyo Ummu wayyo Babiy na shiga ukuna....” kuka ta fashe da shi mai tsuma rai tana mai ɗaura goshinta kan nasa da cigaba da ambaton “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Shike nan ni Fhareedah, shike nan na kasheshi Ummu, Ummu na kashshi na shiga ukunaaaaa!!”.

      A tare Miran Jasim da Miran Arshaan dake shigowa suka ɗauki salati, yayinda Malikat Bushirat da kalaman Iffah sukai matuƙar cakar ƙirjinta tamkar saukar mashi juwa ke neman zubar da ita a ƙasa, cikin sauri Daneen Ammarah dake bayanta ta riƙota itama jikinta na rawar. Jasrah dake bayansu kam tuni tayi kukan kura akan Iffah da ruɗani ya hanata sanin shigowarsu duk da salatin da su Miran Jasim ke faman jerawa har yanzu. A birkice ta janyo Iffah baya ta shaƙeta, faɗi take itama sai ta kasheta, sai ta rabata da numfashinta. Ganin Jasrah na neman yin kisa da gaske Daneen Ammarah tai saurin zaunar da Malikat Bushirat a kujera ta nufesu. Da ƙyar ta iya ɓangare Iffah da taimakon Miran Arshaan da sai da yaga Daneen Ammarah ta zaburo sannan shima ya zabura. Yaraf Iffah ta zube ƙasa tana jan numfashi da ƙyar, yayinda Jasrah ke cigaba da zabura cikin kuka akan ita sai fa ta kashe Iffah. Ƙoƙarin tanƙwarata Miran Arshaan yake yi amma sai ta sake kufce masa. A wannan karon kam da ƙyar Daneen Ammarah ta ɓanɓare Jasrah ta hanyar sauke mata mari itama.

        Ɗifff kowa ya ɗauke wuta a ɗakin sai kakarin wahalar da Iffah keyi, dai-dai nan kuma Sayeed Aashiq Ali ya iso da likitoci, kasanwarsa uba a gare su a tsawace ya basu umarnin duk su fice. A kaikaice Miran Jasim da Miran Arshaan suka dalla masa harara kafin su fice, Daneen Ammarah ta taimakawa Malikat Bushirat da bata tofa ko kanzil ba har yanzu, Miran Arshaan kuma ya kama Jasrah. Iffah kasa tashi tayi dan da gaske ta shaƙu, dole sai da aka taimaka mata itama. Da ƙyar aka iya ɓanɓare hannun dake cikin na Tajwar Eshaan har yanzu tana kuka kamar ranta zai fita. Sashenta aka maidata, tare da sake zagaye sashen Shahan-shan ɗin da tsaro na musamman. Likitansa da wasu ƙwararrun likitoci biyu dake a kansa domin ceto rayuwarsa tuni bincikensu ya gano musu dafin macizai da guba da ya sha. Sun sami nasarar kashe kaifin dafin macizan, sai dai sun tabbatar da gubar ta fara ma jikinsa illa, idan kuma ba'a gaggauta yin wani abu ba zai iya rasa ransa duk da a yanzu ma dai sai abinda ALLAH yayi.

       Hankalin su Malikat Bushirat da gaba ɗaya ta gama fita a hayyacinta ya sake tashi, dan gani suke ma Tajwar Eshaan ya rasu ne likitocin na ɓoyewa ne kawai. Saboda duk wanda ya ga a halin da aka samesa bazai taba sakankancewa zai rayu ba. Malikat Haseena tsohuwa mai ƙarfin hali da jarumta, duk da yanayin da nata jikin yake bata gaza nuna ƙoƙarin ta ba. 


       

     Da taimakon Daneen Ammarah aka maida Iffah dake matsanancin kuka tamkar wadda ta zautu sashenta, suna shiga ta riƙo kafaɗunta cikin tashin hankali tana mai girgiza ta, “Ibnati kice min ba haka bane kar zuciyata ta buga, dan ALLAH ki faɗa mana gaskiya miya samesa, minene ya faru?”. 

   Babu alamar Iffah zata kare kanta, sai ma wani irin karkarwa da jikinta ya farayi hawaye na rige-rigen sakkowa a kumatunta. Sai ma kawai ta tafi luuu ta zube ƙasa....



      ★A firgice Iffah ta farka daga barcin da likita ya sakata na dole. Dan tun bayan shafa mata ruwa ta farfaɗo yanda take kuka da surutai sai tai kamar wadda ta zautu. Daneen Ammarah da ke kallon al'amarin nata matsayin ruɗani ne suka saka doctor danƙara mata allurar barci gudun kar wani abu ya samu brain ɗin ta. Saurin riƙota tai cikin muryarta data sha kuka ta shaƙe take faɗin, “Ibnati kwantar da hankalinki...”

      “Mamy hankalina bazai taɓa kwanciya ba. Dan ALLAH a wane hali yake? Ya rasa ransa ko? Ku kaini na sake ganinsa karki ce a'a dan ALLAH Mamy”. Duk wanda ya ga yanda Iffah ke jero waɗan nan tambayoyi yasan har yanzu a birkice take, dan tuni hawaye sun sake ma fuskarta kaca-kaca. Riƙota Daneen Ammarah tai ta rungume itama tana nata hawayen...

    A tsawace Jasrah data faɗo musu babu zato ta bama jami'an dake a bakin ƙofar izinin shigowa ɗakin. Daneen Ammarah tai saurin dakatar da ita itama a ɗan zafafe.

      “Jasrah!! Ki dawo cikin hankalinki, idan kin manta bara na tuna miki. Ita ɗin Zawjata-almilk ce, ba hadimar daular ruman ba, ba ɗakin barcinta ba koda falonta haramunne shigarsu.....”

        Itama Jasrah cikin rufewar idon ta tari numfashin Daneen Ammarah “Nima idan kin manta bara na tunatar dake Daneen Ammarah. Ada wannan abar ke amsa sunan da kike tunanin zai bata waccan darajar da kariya, a yanzu ko sunanta ƴar ta'adda, mai kisan kai, kisan kan ma na Shahan-shan.....”

    “Kin tabbatar da ita ta aikata?”.

Ta katseta itama a fusace.. “Mikike buƙatar ji bayan wanda kunnuwanmu sukaji? Da wanda idanunmu suka gani?”.

        Rikici ne yake neman ɓarkewa a tsakaninsu, kowanne na ƙoƙarin ganin ya tabbatar da gaskiyarsa akan Iffah. Abune da bai taɓa faruwa ba, dan akwai girmamawa tsakaninsu musamman kasancewar shekarun Daneen Ammarah sama dana Jasrah. A yanda suke a fusace su duka ya sake hargitsa kan Iffah da gaba ɗaya ta daina gane komai, sai ma hajijiya da ke neman son sake zubar da ita a ƙasa tai nasarar jingina da bango.....


    ★....


    A ɓangaren al'ummar ƙasar ruman kam dake faman zanga-zanga jin abinda ke faruwa hankali ya rabu gida biyu, wasu sun yarda harda shiga jimami. Wasu ko na kallon abin ta fiskar yaudara ne kawai Tajwar Eshaan ɗin na son ƙetare ƙasar ne saboda baya son yin murabus. Wasu kuma sun kasance ƴan babu manufa ne kawai. Ƙasa ta ɗauki ka-ce-na-ce tako'ina har wani bayajin zancen wani, haka ma kafofin yaɗa labarai da social media. 

          Duk yanda suka so jin bakin likitocin da suka dubashin hakan bai yiwu ba, sai dai an sami hatsabibin da ya haɗa guntun bidiyon cewar Shahan-shan babu lafiya kai babu ma alamar yana raye. Wannan video shi yay rugugin amsa kuwa cikin ƙankanin lokaci a kowace kafar ƴaɗa labarai na ƙasar. Duk da ɗan jaridan abinda yay kuskure ne sai wannan bidiyo ya zama tamkar alkairi, dan kuwa ya sauya labarin Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed daga azzalumin da bai son yayi murabus zuwa abin tausayi da fara tunanin anya kuwa babu wani abu a ƙasa da mutane ya kamata su sani?. Cikin ƙankanin lokaci bakin ƴan jarida da masu rajin faɗa aji suka fara fashin baƙi akan al'amarin, daga sauran talakawan ƙasa ma kowa nata faɗin al'barkacin bakinsa, wasu ɓangarori na mutane kuma suka fara binsa da addu'ar fatan alkairi da samun lafiya..


★★.....


    Al'amarin fa tamkar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Tabbas a yanda su Miran Jasim sukai shiri na gaske akan Iffah bata da wata mafita ta kowanne mahanga, sun kuma tsaya tsayin daka wajen nuna ƙarfin iko da tabbatar da Miran Jasim matsayin magajin kujerar Tajwar Eshaan har lokacin da ALLAH zai bashi lafiya shine zai cigaba da jan ragamar mulkin sarautar Shahan-shan. Wannan damar dake a hanunsu sukai amfani wajen damawa aka miƙa Iffah zuwa cikin kurkukun masarauta. A gefe kuma masarautar ta ɗauki ɗumi fiye da na sanda ake zanga-zanga kan murabus ɗin Tajwar Eshaan. Kowa faɗin albarkacin bakinsa yake, masu goyon bayan Iffah da ganin ta ƙarasa musu abinda suke burin gani, da masu zaginta da ganin gangancinta, da masu yima su Malikat Haseena ALLAH ya ƙara a cewarsu sun fifita lamarin Iffah fiye da Zawjata-almilk na baya da suka rasa ransu. Surutai dai kala-kala sai wanda kunnenka yaso ji. Dan har zuwa dare babu alamar masarautar zata lafa sai ma fita gari da maganar ta farayi har wasu kafafen yaɗa labarai sun fara tsegunta zancen a kaikaice.....


      ★...........★


  Zuwa safiya daular ruman ta gama cika tako ina da sarakuna na jihohi dan labari ya gama karaɗe ko'ina. Dole amintaccen likitan Tajwar Eshaan da suka kwana kansa ya tattauna da manema labarai dan kwantar da hankalin mutane bisa umarnin Malikat Haseenat. Ya tabbatar da Tajwar Eshaan ɗin na raye, an kuma sami nasarar daƙile dafin macizan da aka shayar da shi a cikin madarar da bincikensu ya tabbatar musu. Sai dai zai cigaba da karɓar magani zuwa wasu ƴan kwanakin da zasu iya ji daga garesa. Hankali ya ɗan kwanta kaɗan, nanfa aka shiga jera masa addu'oin samun lafiya tamkar ba suke zanga-zanga yay murabus ba. 

        Sai dai kuma ga wasu hankalinsu ya sake tashi ne. Dan Wannan sauyi da aka samu saɓanin abinda sukai hasashen faruwa ya matuƙar tada hankalinsu. Saboda tun da Malikat Haseena ta bada umarnin sanar da ƴan ƙasa halin da Tajwar Eshaan ɗin ke ciki Miran Jasim da Miran Arshaan suka kasa zaune suka kasa tsaye. Sunbi wasu hanyoyi ta ƙarƙashin ƙasa domin daƙile fitar zancen ga al'ummar ƙasar ta ruman sai dai hakan ya gagara, dan Malikat Haseenat ta tsaya tsayin daka tare da rufe idonta wajen ƙin ganin komai sai ƙoƙarin wanke Shahan-shan ɗin ga talakawansa...


★★......


      “Dole ne mu gaggauta sake salo muma, dan a wannan gaɓar idan har muka bar shaiɗanin yaron nan ya tsallake to mufa bazamu tsallake ba”.

    Miran Jasim ne mai maganar hankali tashe yana faman kai kawo. Cikin gamsuwa Miran Arshaan ya amsashi da faɗin, “Kafin hakan dole ne mu fara kauda yarinyar nan. Dan barinta itama tamkar kashe maciji ne bamu sare kansa ba. Dan na tabbata zuwa yanzu ta dawo hankalinta kamar yanda Barbushi ya tabbatar mana abinda yay mata bazai jima a jikinta ba. Kaga kuwa a ƙalla yanzu muna da kusan awanni takwas da faruwar komai, na kula kuma tsohuwar can son dawo da martabar jikanta take yi kawai ta amfani da wannan ciwon”.

     “Haka ne, kaima kayi magana mai ƙyau. Amma kasheta a wannan gaɓar bazai yiwu ba, dan in har muka aikata hakan zai ƙara tabbatar ma mutane abinda tsohuwar ke son a duba, kuma zai sake ɗaukaka darajar jikan nata dan na kula hankulansu ya fara dawowa kansa duk da ƙoƙarin da mukai na munana shi a zukatansu. Na rasa mi wannan matsiyacin yaron ya taka haka? Haka shima fa ubansa ya dinga wajiga rayukanmu”.

    Ƙwafa Miran Arshaan yayi mai haɗe da cije lips. Cikin takaici da nuna jin zafi yace, “Lokaci yayi da zamuyi yaƙi na gaske wajen shafe babin duk wanda yay ƙoƙarin cigaba da kasancewa a gaban nasarar mu. Ba Eshaan kawai ba, hatta tsohuwar can da uwarsa lokacin kasancewar su larihi yayi”.

         Wani banzan murmushi Miran Jasim ya saki yana mai kallon Miran Arshaan ɗin, a zuciyarsa kam faɗi yake (Har da kai a cikin wannan lissafin Akhi. Dan bazan taɓa hawa karagar mulki da wani maƙiyi shaƙiƙi ba) a zahiri kam sai ya ɗan bubbuga kafaɗar ɗan uwan nasa murmushi kwance a fuskarsa. “Shiyyasa bazan taɓa daina alfahari da kai ba”.

    Murmushi shima Miran Arshaan ɗin yayi, a tashi zuciyar yana ayyana (Kwanaki kawai zakai na ɗan-ɗanar mulkin da ka kwashe tsahon rayuwarka kanayi, dan bazan taɓa bari ka wuce kwanan wata ɗaya ba. Ni kaɗai na dace da cancantar zama magajin daular ruman) a zahiri kam kaɗa kansa yayi har da ɗan risinar da kai alamar girmamawa yana murmushi.........✍️



Hummmm. barkanmu da sake dawowa filin daga ƴan uwa. Barkanmu da salla kuma. Ya ibada? ALLAH ya sa muna cikin bayin da aka ƴanta, ya yafe mana kurakuranmu. Ya biya mana buƙatunmu na alkairi. UBANGIJI ka sadamu da rahamominka marasa yankewa. Fatan alkairi a gareku baki ɗaya🥰😍😘🙏.



   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.