Daudar Gora Book 2 page 2



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (002)




........Murmushi ta saki mai sanyi bayan gama sauraren dogon bayanin nasu, ta ɗan muskuta zamanta na ƙasaita cike da ƙarfin hali da sake bayyanar rauninta na tsufa da halin rashin ƙarfin jiki da jiyyar kwana biyu ta haddasa mata. Malikat Haseenat kenan tare da manyan masu faɗa ajin masarauta da suka buƙaci zama da ita akan lamarin Iffah da suke buƙatar shiga kotu domin yanke mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata bisa tunzurawar Miran Arshaan da Miran Jasim. Cikin dattakonta da ƙasaita ta sake jan numfashi a karo na biyu idanunta akan su Miran Jasim, sai kuma ta ɗan kaudasu tana jinjina kai.

      “Bazan hana ko dakatarwa ba akan gurfanar da mai laifi irin Zawjata-almilk. Sai dai a nawa adalcin ina bada ƙwarin gwiwa da shawara ga masu zaman shari'ar bin komai a sannu da yin ƙwaƙwƙwaran bincike. Sashen Shahan-shan dai zagaye yake da ƙyamarori, hakama madarar da aka tabbatar ya sha tana buƙatar musan daga ina ta fito, shi kansa dafin data zuba waya samar mata da shi har ya shigo cikin masarautar nan?. Abu na ƙarshe shine bata tsaro na musamman da saka idanu a dukkan abinda zata ci. Dan in har wani abu ya sami yarinyar nan batare da gaskiya ta fito ba a tabbata hukunci zai koma hannuna, kuma zan iya zartar da shi akan kowa. Idan nace kowa ina nufin kowa ma koda nice a karan kaina”.

        Babu wanda ya iya tari a falon sai jinjina kawuna kawai suke. Yayinda Malikat Haseenat bata sake tofa komai ba sai ma ƙoƙarin barin falon da tai ta hanyar gara wheelchair ɗinta da remote ɗin jikinta (nace kaga ƴan gatan duniya lols😉). Da kallo suma kawai suka bita babu alamar wani zai ce har lokacin. Sai dai zukatan wasu tamkar zasu kama da wuta dan baƙin cikinta, ji suke kamar subi dare wajen mata yankan rago su zubar da jinin banza. Wasu ko gamsuwa sukai da bayanin nata, dan dama sunbi wannan ayarin ne kawai saboda rashin ƙarfin cewarsu, amma da za'a basu zaɓi sunfi buƙatar ayi haƙuri ma har Shahan-shan ya ƙarasa samun lafiyar da kowa ke fata.....


     ★★★.....


       Kusan a tare suka iso falon kowa ransa a dagule. Sai faman huci suke kamar wasu zakuna. Tamkar basuga juna ba suka fara kaikawo kamar masu safa da marwa. Sunyi haka ya kai sau hur-huɗu kafin Miran Arshaan ya dakata cikin ƙunar zuciya ya furta, “A wannan gaɓar maciji muka kashe bamu sare kansa ba. Kauda wannan yaron a bayan rayuwar wannan tsohuwar sunansa BAYA DA ƘURA....”

        “...Idan har barin wadda rayuwa ta zame mata saura ƙiris a zahirance zai amsa suna baya da ƙura to cigaba da numfashin waccan yarinyar sunansa BAYA DA TARNAƘI”. Miran Jasim ya katsesa a zafafe shima. Tsaye sukai sunama juna kallon kallo. Kafin Miran Arshaan ya katse shirun ta hanyar faɗin, “Tsuntsayen biyu jifa iri ɗaya suke buƙata. Inba haka ba a cikin ƙarfin iko za'a tabbatar da ƙarfafa mai rauni”.

      “Na tabbatar da hakan ta hanyar gani da ido, kunnena kuma sun jiye min tabbacin AKWAI WATA A ƘASA bayan tatsuniyar gizo da ƙoƙi”.

    “Miye mafita?!”.

  Cewar Miran Arshaan cikin tarar numfashin Miran Jasim. Miran Jasim ɗin ya kafesa da idanu yana sakin wani murmushi. “A wannan gaɓar jifar tsuntsu huɗu da dutsi ɗaya ne ba biyu ba”.

     Jimmm Miran Arshaan yay yana kallonsa, dan a saninsa da hasashensa tsuntsayen da ya kamata su jefa uku ne kawai ba huɗun ba. Sai dai kafin yace komai Miran Jasim ɗin ya katsesa da sake faɗin, “Tabbas huɗu ne, sai dai zamu fara kauda ukun kafin cikon na huɗun, dan haka dole ne a gobe mu ziyarci Barbushi”.

       Miran Arshaan zai yi magana sai kuma ya haɗiye, batare da ya ƙara tofa komai ba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “Asuba ta gari”.

    Da wani mugun kallo Miran Jasim ya bisa, yayinda shima Miran Arshaan ɗin ya fice yana taunar lips tabbacin da nasa ƙudirin shima. 


     (Nace “Hummm”).


★★.....


    Yau kwanakinta uku cif a cikin ɗakin da aka garkameta mai tsananin duhu da bata iya banbance dare da rana, sai ɗan hasken da kan leko ta window dake can sama karami na hasken rana ko wutar lantarki. Ta matuƙar zama wujiga-wujiga da fita a hayyacinta dalilin ƙin cin abincin da ake kawo mata sau ɗaya a kowane yini, sai madara. Tun a ranar farko ta gama fahimtar akwai babban ƙuli da ya kamata ta fara fahimta kafin zuwan wannan lokacin. Zuwa yanzu ta gama fahimtar su Miran Jasim sunyi amfani da ita ne, sunyi amfani da ita duk da itama da wannan ƙudirin a ranta. Sai dai kuma cika baki ne kawai, ta fahimci a hakanne a randa ƙaddarar dake tafiya da rayuwarta ta yanzu ta tabbata. Dole ta kira hakan da ƙaddara, dan inba ƙaddara ba babu ta yanda zata iya cutar da waninta mai bautar ALLAH da hanunta. Ƙwarai da gaske tanajin zafi, matuƙar zafi na rasa ƴan uwanta guda biyu a dalilin auren Shahan-shan. Hakan kuma shine ya zama sanadin komai na jin kangarewar zuciya da ƙudirin da babu tabbacin iya aiwatar da shi. Komai ya nema canja mata a lokacin da tai tozali da fuskarsa, bata san dalili ba ta dingajin kamar shi bazai iya kasancewa mai cutarwa ba, ta dinga jin dole akwai abinda yake ɓoye da ya kamata ta sani, sai dai a lokacin data gama shirinta tsaf akan hakan ƙaddara ta sake sauyata, komai ya nema rushewa a zuciyarta batare da riƙe wata makama mai ƙwaƙwarar hujja ba ta yanke hukunci ga wanda bata da wata hujja ko shaida akansa, wanda maimakon ya bada umarnin ɗaukar mataki a kanta ya nuna mata hanyar kuɓuta ta hanyar bata umarnin zubar da madarar da bata san yanda akai takaita gareshi ba. Amma kash, da alama ƙoƙarinsa na kubtar da ita bai tabbata ba. Dan gashi maƙiyansu da alamu suka nuna shirinsu bana yau bane sun gama cin nasara, nasara biyu a lokaci ɗaya, kaudashi da kaudata itama batare da ta san mi taci burin son sani ba. Sai ma sake tsunduma a duhuwa tayi. Dole ta kira gaɓar da suna duhuwa, dan tanada tambayoyi masu ɗunbin yawa akan kanta ma. Mafi girma a ciki sune taya Ajmaal ya zama Shahan-shan? Wake halaka matansa idan har ya kasance ba shi bane? Miyasa bai iya cewa komai bayan shine keda hakkin cewar? Da gaske ta rasa iyayensu suma da ɗan uwanta tilo daya rage kokuwa duk cikin shirin su Miran Arshaan ne?.... Shi kansa Sir Fawzan tana da bukatar sanin wani abu a kansa. Sai dai ta yaya? Ta wace hanya? Duk yanzu bata sani ba. Zafafan hawayen da a kwana ukun nan bata taɓa gwada sharewa ba suka sake zubowa masu zafi. Ta lumshe raunanan idanunta murmushi mai ciwo na suɓuce mata. Fuskarsa take kallo a kan allon zuciyarta a lokacin da yake sakar mata murmushin da har abada bazai taɓa zama mai gogewa ba a tarihinta. Siririyar dariya da tafin dake shiga kunnenta a bazata ya saka ɓacewar murmushin kan fuskar tata da buɗe lumsassun idanun nata lokaci guda..

        Kanta ne ya sara da ƙarfi, da sauri ta maida su ta rumtse sakamakon hasken daya ratsasu mai kaifi, yau kwananta uku tana a cikin duhu, dolene karfin idanunta ya samu rauni a lokacin da aka samar da haske cikinsu. Duk yanda taso sake buɗewa ta kasa, dan har cikin kwakwalwarta taji shigar kaifin hasken na bazata. Ta cije lips a hankali tana mai ƙoƙarin ganin ta riƙe hawayenta da son danne tasirin raɗaɗin dariyar izgilancin da bata san daga wanda take fita ba. Sai dai zuciyarta na bata Miran Jasim ko Miran Arshaan ne. Bata da ƙarfin tashi daga kwancen da take, dan haka tai jarumtar sake buɗe idanun nata sannu a hankali a karo na biyu, zuciyarta na ambaton (Hasbinallahu wani'imal wakil). Da ƙyar ta iya tsaidasu akan Miran Jasim dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya bisa kujerar da basai tayi wani tunani ba da ita aka shigo masa. Raɗaɗi idanun ke mata, gasu a kumbure jajur amma haka tai jarumtar cigaba da tsaidasu a kansa harya gaji dan kansa daga dariyar yay shiru..

        _“Zawgatu al-ibn! (Daughter in-law) proud of you. Kin zama ta daban a cikin dubun da bazan so na manta ba. Duk da nima dai nasan ban cancanci ki manta ni ba ta sauƙi, na san na cancanci zama abin alfaharinki a yanzu. Cikin sauƙi na cika miki burinki, gaskiya na cancanci karɓar tukuyci na musamman. Koda yake kwantar da hankalinki bama sai kin bani komai ba, zamanki anan ma babban tukuyci ne. Zan sake faɗa “Ina al'fahari da ke”. Yay wata ƴar dariya mai ƙona zuciya dake shiga har ƙarƙashin zuciyar Iffah, amma kasancewar ta jarumar gaske mai ƙarfin zuciya sai batako motsa ba, raunanan idanunta kuma har lokacin suna a kansa duk da raɗaɗin azabar shigar haske dake ratsasu har yanzu. Dan kansa ya tsagaita da dariyar tare da gyara zamansa yana binta da wani shegen kallon ƙurulla har yana lasar lips ɗinsa kaɗan.

      “Bana son ki kalleni da irin kallon da nake da yaƙinin shine a allon zuciyarki Zawgatu al-ibn!. Ina son ki dai fahimci ni ɗin mutum ne mai son kansa, zan kuma iya kauda koda yatsan hannuna ne in har zai iya zame min cikas domin samun cikar burina”. Yay wata ƴar dariya a zahiri, a can ƙasan ransa kam kallon da Iffahr ke masa ko ƙiftawa babu yay masa tsaye a kan allon zuciya, amma kasancewar sa gwani sai ya shanye babu alamun hakan a kan fuskarsa. Sai ma miƙewa yay cike da kasaita, a gabanta yaje ya tsugunna tare da kai hannunsa fari sol zai shafa fuskarta. Cikin wata irin zabura da ƙarfin da Iffah bata san yay ragowa a jikinta ba taja da baya tana watsa masa wani mummunan kallo har hucinta na bayyana akan hancinta. Murmushin gefen baki yay da lumshe idanu, sai kuma ya janye hannun nasa cikin ɗage kafaɗa da son basarwa. Idanun ya sake lumshewa da buɗewa a kanta yana shu'umin murmushin dake sukar zuciyar Iffah matuƙa. “Hakan ma ya burgeni Zawgatu al-ibn”.

     Harara ta watsa masa kai kace idanun zasu faɗo, cikin kaushin muryar da ke fita da ƙyar ta fara magana a karo na farko cike da gargaɗi. “Kai fagalalle ka rubuta ka ajiye, a duk ranar da koda ɗan yatsan ka yay kuskuran taɓa jikina ni Fhareedah bint Zayyan na maka alƙawarin karyasa, karaya irin wadda har kabar duniya tabonta bazai goge a idanunka da zuciyarka ba. Iffah babban goro ce sai magogin ƙarfe”.

       Tabbas maganarta ta matuƙar sukarsa, ta kuma zauna daram bisa zuciyarsa tamkar rubutu akan dutse, amma a zahiri sai ya murmusa harda lasar lips a karo na biyu. “Immm bazance kinyi ƙarya ba kam, nima shaida ne ke ɗin babban goro ce, kuma tabbas sai ni magogin ƙarfe. Ina miki albishir daga yau ki fara takaba da irga kwanakin zamowarki babban goro ta magogin ƙarfe ni Shahan-shan na ƙasar ruman Tajwar Jasim ibn Abdul-majeed Aliy! Nayi alkawarin sai na maidake karuwar da zata zama a ƙololuwar abin kwatance a duniya duka bama ƙasar ruman kawai ba. Daga yanzu kisa a ranki ƙaddararki ta fara a hannuna hhhh!!!”.

       “hhahhaha!!!”. 

   Itama Iffah ta fara dariyar kamar yanda yake yi, sai dai tata cike da ƙarfin haline kawai. Tsagaitawa yayi da tasa yana kallonta cike da mamakin da yake ƙoƙarin dannewa, sai dai kuma fuskarsa na ƙoƙarin fallasa shi. Ganin bata da alamar tsagaita dariyar tata ya miƙe cikin zafin rai....

      “Alfahari da ƙaddara akan Fareedah rauni ne ai Aam! Dan ƙaddarar itace hasken fitilar nasarar Iffah. Ƙyaƙyƙyawan mafarki Uncle”. Ta ƙare maganar da cigaba da dariyar da tafi ta farko saka ƙuna a zuciya.

     Miran Jasim dake tsaye cak shi bai fitaba shi bai dawo ba yay wani irin cizar lips, sai kuma ya fice cikin zafin nama dan har ƙarƙashin ruhinsa dariyar Iffah ke shigarsa.. Sai da ta daina jin takun sawunsa gaba ɗaya da kulleta da aka sakeyi sannan ta tsagaita itama, a maimakon dariyar sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Ta tabbatar duk abinda Miran Jasim ya faɗa zai aikata mafiyinsa, sai dai ba tana kuka bane akan kanta, tana kuka ne a maimakon talakawan ƙasarta da Tajwar Eshaan bin Haysam Abdul-majeed. Tana kuka ne akan tsananin buƙatar son sanin zahirinsa da baɗininsa da su Miran Jasim suka zaburar da ita. Sai dai tasan guri ya ƙure, ƙurewa irin ta numfashi da ƙarewar rayuwa. Koda ace shi ya rayu ita bazata rayu ba, koda ace wasun sa na buƙatar ta rayu ita bata buƙatar rayuwar a halin yanzu.........✍️



      (ALLAH sarki Iffah 😭🙏).



   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*



_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.