Daudar Gora Book 2 page 10


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (10)



........Daneen Ammarah da dama sanin fushin malikat Bushirat ɗin kan al'amarin ya sata tada hankalinta ganin an kusanto da Iffah ga Tajwar Eshaan tai ɗan murmushi, tasan kalamanta sunyi tasiri, sai dai ba tasirin da zai iya ruguje abinda take son ganin ta ruguje ɗin ba (Wato ƙiyayyar Iffah a zuciyar Malikat Bushirat a yanzun). Kanta ta ɗan rausayar tare da kallon Tajwar Eshaan da yay kamar babu shi a ɗakin, dan idanunsa ma a lumshe suke kamar wanda barci ya ɗaukesa. Juyawa tai ta fice a binta itama zuciyarta cike da ƙudirin tsayuwar daka domin tabbatar da gaskiya da kuɓutar da yarinyar da takejinta har cikin ƙasan zuciyarta. 
      Idanun ya buɗe kaɗan ya bita da kallo tamkar yanda itama Malikat Bushirat ɗin data gagara iya cewa komai ta bita da kallon..      
   
        *_“Hummm!! Bazan iya hakuri ba sai na tofa”_*
  “Idan nace Humm fa ina nufin Humm da gasken gaske. Idan har Iffah ta rayu yaya kuke tunanin a yanzu salon zamanta zai kasance da uwar mijin nata mai tsananin ƙarfin iko? haka koda an tabbatar da jagororin abinda ya faru ta dalilin nata. Masu karatu akwaifa cakwakiya, dan yanzu salon zai fara a ƙarƙashin abu uku ne, da zaku iya canko min su dana baku babbar ƙyauta😉😁🥱”.

            ★.... TA-ƘURYA ★.....

     “Na daɗe da faɗa miki wannan yarinyar hatsabibiya ce kar ki sakaci da rauninta na kasancewa mai ƙarancin shekaru ko ƙanƙanta sama da ƙarfin ikon ki ta-ƙurya?. A duniyar cikar buri raina abokin karo kuskure ne kuma ganganci ne da kan iya rusa duk wani ginin da aka faro komai tsahon shekarunsa.....”
    Ta-ƙurya da ke gurfane gaban Uwa cikin jin raɗaɗi a zuciya ta ɗago idanunta da launinsu ya koma jazur, cikin rufewar idon irin na mai ɓacin rai da manta wake a gabansa ta ce, “Mina gaza Uwa?! Minene ban bi ba a dukkanin sharuɗan ki a shekarun nan? Miyasa matsala bata kasance abokiyar gogayya ta ba sai a lokacin da zan girbi shukar dana ɓata tsahon shekaru wajen yimata barruwa? Miyasa? Miyasa?. Na ce miyasa hakan ne?!. Miyasa sai da na yarda na rasa komai domin samun abinda nake kallo komai a gareni sannan zaki hana mini? Ke ce kika ce karna taɓa kokwanto bazaki taɓa barin zubar waɗan nan hawayen da a yanzu suke kwaranya akan fuskanta ba da ga gareni. (Wa'iyazubillah 😭🙏).  Miyasa? Miyasa a yanzu sabanin hakan nake gani? Yarinya ƙarama da bata wuce na murjeta da tsinin takalmina ba ta shigo rayuwata da barazanar yin kutse akan nasarata. Idan tafi ƙarfinki ne ki faɗa min danni batafi ƙarfi na ba, babu wata uwa data haifi ƴa ko ɗan dazai zama barazana akan cikar burina, in ko uwar ta haifosa har kuma ya kwatanta zan shafe babin zuri'arsa kaf da babu wani abinda za'a kalla a tuna su kuma. A yanzu kam zanyi yaƙin da hannayena dan bana buƙatar k......”
     “K!! Ta-ƙurya ki dawo cikin hankalinki, kalleni da ƙyau ki san a gaban wa kike? Uwar mugu nake bata sakarai ba. Banyi lalacewar da ke zaki ci tuwo a kaina ba koda kuwa tuwun na ƙasa ne mai sauƙin wawaso. Idan kuma zaki gwada ga fili ga mai doki”..
      Cikin nuna halin ko gezau ta-ƙurya taja tsaki mai tsananin sauti dai-dai lokacin da Uwa ke ɓacewa daga idanunta rai a ɓace. Ta rakata da harara tana mai miƙewa da ga durƙuson da tai. Waya ta fusga cikin tsananin fusata ta hau danne-danne tana kai kawo a katafaren ɗakin...

      🙆Tofa al'amarin babba ne tsakanin ta-ƙurya da uwa ta ta😱. Mu dai ƴan kallo ne😜.

      ★★..... ★.....
   
    Alhamdullah a daren yau likitoci suka sami nasarar dawowar Iffah dake cika kwanaki huɗu hayyacinta, zuwa safiya kam sai dai ace Alhamdullah duk da bawai tana a cikin ƙarfin jikinta bane ko warkewa sarai kamar yanda take a baya. Daneen Ammarah har da kukanta na farin ciki, bata ɓata lokaci ba wajen sanar ma Malikat Haseenat. (Alhamdullah) ta dinga jerawa itama tare da jin nutsuwa na saukar mata, dan tunda yarinyar nan ta tsinta kanta a halin nan hankalinta ya gagara kwanciya. 
     Malikat Bushirat duk da labarin farkawar Iffah ya zo har kunenta ta hanyar doctor Afif batace komai ba hakama bata leƙa dubata ba, sai ma yazam a safiyar ranar har zuwa yamma bata leƙa sashen Tajwar Eshaan ɗin ba gaba ɗaya, ta dai kira waya domin jin cigaban lafiyar jikinsa. Shi ɗin ma dai bai shiga duba Iffahn ba sai yamma duk da kuwa jiyan ma a gaban idonsa ta farfaɗo, Sannan har yanzu jikinsa babu ƙarfi shima, dan da gaske gubar da suka haɗa da dafin macizan ta so masa illa ƙwarai da gaske tunda gashi ma har sai da akai masa aiki dalilin taɓa wani sashe na jikinsa data so tayi saboda ƙarfinta. 
    
     Duk da ɗakunan jiyyar tasu na maƙwaftaka da juna a yau bamai iya ganin wani sakamako labulolin da aka zuge suka toshe gilashin da ya raba sun, koda babu labulen gilashin mai ƙarfine da babu mai jin maganar wani koda za'ayi da ƙarfi ne, sai dai zaka iya hango mutum fes. Har zuwa yanzu dai kayan jiyya ne a jikinsa sai dai a kullum yakan canja da wasu sabbi sau fiye da biyu, ya ɗan rame saboda yanda ciwon ya bugesa. Sai hakan ya sake fiddo hasken fatarsa mai launin tar-tar a cikin idanun mai kallo. Cikin jarumtarsa da ƙarfin hali yake tafe doctor Afif biye da shi a baya tare da Sayeed Fayzul-haq dake tsaye da ga bakin ƙofa dan zuwansa kenan. Cikin sauri Sayeed ya danna maɓallin ƙofar gilashin ta zuge kanta a hankali. Baya ya ɗan ja yana mai rissinar da kansa ga shugaban nasa mai matsayin gaske a garesa da bazaya iya musaltuwa ba. Izzarsa da ƙasaita na tattare da shi, dan tamkar itace jinin dake zagayawa a maimakon jininsa, ya ɗan ja iska ya fesar na wasu sakkani kafin ya cigaba da takawa a sannu ya shiga bakinsa ɗauke da sallama can ƙasan maƙoshi. ..
      Daneen Ammarah da ke zaune a gefenta tana ƙoƙarin bata shayi mai zafin gaske da Doctor ya bada umarnin bata ce ta ɗan waigo najin motsi, numfashi ta ɗan ja ƙaɗan tana mai sauke idanunta a kansa. Sai kuma ta miƙe dai-dai Iffah tana damƙe kofin shayin cikin hannunta duk da zafinsa da takeji sakamakon jin Daneen Ammarah ta ambaci “Abni”. Sosai zuciyarta ke harbawa da ƙarfin gaske, kusan tare da ɗaga sawunsa da saukewa cike da izzar da raunin ciwo bai rageta a gareshi ba sam. A tsumen da fuskarsa take ya tabbatar ma Daneen Ammarah a Shahan-shan ɗin sa ya shigo ba ɗanta ba, dan haka ta ɗan ja gefe a yanayin girmama darajar da ALLAH ya basa. Cikin sauri  Sayeed Fayzul-haq ya gyara masa kujera yana mai ja baya kusa da Doctor ya rissinar da kansa. Duk abin nan dake faruwa yana tsaye kaifafan idanunsa masu matuƙar tasiri da tabbatar da girman da ALLAH ya bashi na mulki badan yafi saura ba na a kanta, kallo yake mata irin na ƙasan ido mai hana wanda akema sukuni koda bai san wanda ke masa ba. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya kai zaune sannu a hankali ga kujerar da aka gyara masan...
     Iffah ta kasa sake iya motsi duk da azabar zafin shayin da raɗaɗin da ke ratsa mata hannu, sauƙinta ma ta ɗora shi ne bisa lallausan duvet ɗin da ƙafafunta ke ciki har zuwa cinyarta. So take kawai taji ta ɓata, ɓata irin wanda ta daɗe tana jin labarin masu layar zana nayi, ta kasa tantance ainahin abinda ke razanar da kasancewar sa gareta, shin tsoro ne ko matsananciyar kunyar kai ne?. Inama inama, inama daga halin data tsinci kanta bata sake farkawa ba balle su haɗu, inama an cigaba da barinta ta dawwama a kurkukun da bazata sake ganinsa ya ganta ba har abada. Tabbas har yanzu tana jin zafi, zafi mai haɗe da raɗaɗin rasa ƴan uwanta guda biyu, sai dai saɓanin yanda ta ɗauka abun a da akwai banbanci da yanda take kallonsa a yanzu... 
      Sake maida idanun nasa da ya ɗan kauda daga kanta yayi, sai dai yanzu a kan kofin shayin da take faman damƙa ya sauke su, ya ɗanyi sama da su zuwa ƙirjinta da girman rigar asibitin ta sakaya, sake sama yay zuwa kan fuskarta da ke nuna ainahin yanayinta. Lumshesu yay da sake buɗewa cikin salon shanyesu matuƙa mai son nuna kasala a bayyane, sai dai tsaf ya shanye komai daga kan fuskarsa ya haɗiyema ransa yana mai furzar da iska kaɗan tare da  gyaran muryar da ta sakata zabura alamar hakan yazo mata a bazata. Dubansa ya maida ga Daneen Ammarah da itama gyaran muryar tasa ya sakata ɗagawa kamar su doctor, sai dai maimakon shi bakinsa ya ce wani abu sai Sayeed Fayzul-haq ne yay saurin faɗin, “Ranki ya daɗe, adalin shugaba mai musanya sharri da alkairi na miƙo gaisuwar yaya jiki ga Zawjata-almilk. ALLAH ya ƙara mata lafiya da rayuwa mai albarka.”
     Daneen Ammarah ta ɗan nisa kaɗan da jinjina kanta tana mai gyara tsaiwa. “Zawjata-almilk na godiya da wannan karamci, tana mai fatan alkairi da addu'ar samun lafiya ga Shahan-shan shima”.
        Iffah da ke saurarensu cikin tsinkewar zuciya ta ɗan ɗago ido kaɗan da niyyar duban sa dan rashin gamsuwa da zancen Sayeed Fayzul-haq a maimakonsa, tasan bazai barta ba, dolene ta samu hukunci dai-dai da laifinta. Sake tsinkewa zuciyarta tai sakamakon shigar idanunta cikin nasa da ke mata kallon ƙasa-ƙasa da ta gagara iya bashi fassara, sai kawai taji jikinta ya fara ƙyarma. Bata san ta ya ba, bata san ya akai ba taji an riƙe kofin shayin hanunta da ke faman tangal-tangal zai kife a jikinta. A raunane, a kuma birkice ta sake ɗago manyan idanunta da ciwo ya sakasu raunana haɗe da kumburowa. Damar sarƙesu ya sake samu cikin shanyayyun nasa masu kaifi, sai kawai ta saki kuka, kuka irin wanda ta jima da son tayi, kuka irin wanda take buƙatar mai lallashi, kuka irin mai nuna tsananin bukatuwar ɗumin mahaifa ko shaƙiƙan ƴan uwa da zasu rungumeka su lallasheka. Cigaba yay da kallonta kawai shima zafin shayin na ratsa masa hannun da har ya fara gumi ga raɗaɗi na shigarsa. Baya son ji dan yana matuƙar sukarsa, sai dai bazai hanata ba dan yafi son tayisa har iya iyawar jin ta gamsu a karan kanta. Takoyi ɗin fiye ma da yanda yake buƙata, dan sai da ta kai har ya fara cije lips ɗinsa a tsakkiyar haƙora. Sai dai ƙasaita, izza da tsananin miskilanci mai samun jagorancin gudanar jinin mulki da ke tare da shi ya hanashi cewa da ita komai, koman da koda kuwa abinda ya shafi laifinta ne harta fara jan numfashi a suƙe mai alamar ƙoƙarin haɗiyewa........✍️
      


   
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar  1250CFA
Books hudu  1050CFA
Books uku  850CFA
Books biyu  650CFA
Bookk daya  450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.