Abban Sojoji Takun Karshe Complete


Father of soldiers*


*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*


*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃**nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅BismillahKai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata,

   Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa"Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing,"

  Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour,

  Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu,ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace"Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,"

  on the other hand hayam tace"haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu.....'tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar,

  Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace"Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba,'

     cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa"Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,'

  Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faɗi rasss,ƙasa ƙasa da murya tayi tace"Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai?

  "Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!" tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa

  "kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne....'

  Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi,

   "Wani abusufyan din kuke magana akai,"

  Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin,

  Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin,Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet,

  gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa"kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,'

  A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruɗu yasa ta manta hanyar fita daga ɗakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiɗimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa,

   Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miƙi hanyar wannan tsohon store ɗin data ta6a garƙame su hosana aciki,anan corridor ɗin ta tsaya tana sauraran Hayaam,

  "Wlh Aunty laila da gaske ne,Ni shaidace,Naji komai lokacin da Uncle ɗin nasu yake korama junaid bayani,bama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakan,Babban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashe,kuma dukkansu Mata ne kyawawan gaske,kamannin su sak iri ɗaya,Kuma kina kallonsu zaki gane cewa ƴa'ƴanshi ne......'

  Hannu ɗaya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kanta,yayin da dayan hannun ke ruƙe da wayarta data kara a kunnanta,

  "Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki ba,Taya hakan ma zata faru!mutumin da bai ta6a yin aure ba,Shi za'ace yana da ƴa'ƴa har ƴan uku!Cikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same su!Ni ban yarda da kalamanki ba,Hayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmi,Idan wasa kike mun ki daina!!!!!

6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar 

  Fashewa da kuka tayi saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshinta,ga zuciyarta dake ta faman tafarfasa,Gaba daya bata jin daɗin jikinta,

  Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta,

  Tsoki taja tana jinjina kai tace"dama saida raina ya bani cewa ƙarya take yi mun,tayi mun hakan ne saboda ta tsoratar dani don in saukko,Shashasha kawai,

    "Mommy kin farka kenan"

Muryar hafsat ce ta katse mata zancen zucin nata,

  Juyowa tayi tana kallonta,atsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi jikinta na sanye da riga da wando na jeans,ta ɗaure sumar kanta da ribbom,yayin da hannunta ke ruƙe da Cup mai ɗauke da Tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,

  Tunda Aunty babba taga hafsat na murmushi tasan cewa akwai matsala,hakanan dae ba zakaga fuskar hafsat da murmushi ba tunda farar safiya,

  ƙaƙalo murmushin yaƙe Aunty babba tayi tare da cewa"Lafiya naga kina murmushi"?

  "Lafiya lou mommy,kawai wani abun farin ciki ne ya faru,nasan cewa muddin kema kika ji,zaki yi farin ciki sosai,'

  Murya asanyaye aunty babba tace"Faɗamun daughter har na ƙosa naji wannan abun farin cikin?halan an ƙara maku albashi ne?ko matsayi aka ƙara maki wurin aiki"?

  Dariya hafsat tayi tana girgiza kai tace"Mommy baki canka dai dai ba,wannan albishir ɗin da nakeso inyi maki yafi ƙarfin duk waɗannan abubuwan da kika lissafo,kar6i tea ɗin nan ki fara korawa kafin na faɗa maki,"

  Hannunta na kerma ta kar6i kofin da hafsat take miƙa mata,a hankali takai cup din  bakinta ta kur6i Tea ɗin,kusan sau uku tana kur6arsa,kafin ta ɗan jinkirta bayan ta janye kofin daga bakinta tace"daughter dan Allah ki faɗamun wannan wani abun farin ciki ne!wlh duk na ƙosa naji,'

  "Zan faɗa maki mommy amma mu shiga daga cikin palour mu zauna,'

  "Ba inda zanje,idan zaki faɗamun ki faɗamun kawai,Sae ja mun rai kikeyi," tayi maganar tana faman tamke fuska,

  Hafsat tace"bada jimawa ba,Na kira Aunty azeema,don in gaishe da ita,Anan take sanar dani cewa ƴa'ƴan uncle abusufyan Sun bayyana...!

  Tunkan ta ƙarasa maganar a gigice Aunty babba ta saki kofin dake hannunta,Ya tarwatse ƙasa,Ruwan tean dake ciki ya fallatsar masu a ƙafa,

  ja da baya hafsat ta ɗanyi tana kallonta tace"haba mommy,so kike ki ƙonamin ƙafa ta,daga faɗin abun farin ciki?

  Rai amatuƙar 6ace tace"Ki 6ace mun da gani sakarya kawai,Maƙaryatan banza,bazan ta6a yadda da kalamanku ba,duk bakinku ɗaya da Hayaam,'

Ta faɗi hakan tare da kama hanya fuuuuu kamar zata tashi sama,ranta duk a jagule,bin bayanta hafsat tayi da kallo harta haye upstairs,ta6e baki tayi tare da watsa hannayenta tace"I don't care, Ni dae farin ciki nakeyi,Daddy ma nake jira in tambayeshi yaushe zamu je gidan saboda a qagare nake dana ga ƴa'ƴan uncle ɗinmu Abusufyan,tunkan na gansu har naji ina sonsu sosai,in ma na tashi tafiya hada tsaraba zan tafin masu dashi,'

  Cike da farin ciki hafsat take maganar,zuƙunnawa tayi tana tattare kofin da aunty babba ta fasa,


Lokacin da Aunty babba ta ƙarasa bedroom ɗin nasu,har ta ɗaga ƙafarta zata zura acikin ɗakin taji muryar ishaq yana cewa"Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah!Abba nayi farin ciki sosai,Meyasa tun jiya ba'a sanar dani ba,ae da tunda sanyin safiya zanyi maku dirarr mikiya,Amma ina taya uncle murnar ganin ƴa'ƴanshi,kuma ina tayamu murnar samuwar ƴan uku acikin zuri'ar mu,gaskiya bazan ma iya jurewa ba,Zan shirya nazo ne kawai,saboda na qosa naga ƴan ukun mu bayin Allah....   

    Abba yace"wani abun ma sai kayi tozali da yaran,kyawawan ƴan mata dasu,Yadda kasan photo copy ɗin abusufyan haka suke,kamanninsu sak iri ɗaya da nashi,'

  Murmushi Ishaq yayi tamkar yana agabanshi yace"Abba kafin na ƙaraso,dan Allah a isar musu da saƙon gaisuwata,Ace yayansu General ishaq yana gaishe su sosai da sosai,kuma saboda suma zaiyi zuwa na musamman,'

  "Insha Allah zan sanar masu yanzun nan,Allah ya kawoka lfy,"

  "Ameen Abbana,"

Sun jima suna waya kafin sukayi sallama ishaq ya ajiye wayar,

  tashin hankalin da ba'a sama shi date!!!!!!!

  Magana dae ta tabbata da gaske ne zancen da hayaam da hafsat suka faɗa mata,Tabɗijancan,

  Dakyar ta iya shiga cikin ɗakin,lokaci guda ta rasa kuzarin jikinta kamar wadda tayi Zazza6i na sati ɗaya,

  Jin takun tafiyarta yasa ishaq juyawa yana kallonta fuskarshi a washe har ya kammala shiryawa cikin haɗaɗɗiyar shadda,

  Ganin yana ƙoƙarin buɗe baki yayi mata magana yasa tayi saurin katse shi da cewa"Naji abunda ya faru,Hafsat ta sanar dani komai,ina tayaku murna,'ko amsar shi bata tsaya ji ba,ta faɗa cikin toilet,

  Tana juyo muryarshi daga cikin bedroom ɗin yana cewa"Ni yanzu zan wuce Abuja ne,inyaso kun biyo ni daga baya ko zuwa gobe ko jibi haka,duk dae yanda kuka yanke shawara keda hafsat,

  daga cikin toilet tace"Allah ya sauke ka lpy,in anje agaishe mana da mutanen gidan,"

   "zasuji insha Allah," ya amsa mata tare da kama hanyar fita daga ɗakin.

No comments

Powered by Blogger.