Zafin Kai 20

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*

20

Shiru dukkaninsu sikayi sbd daman sunsan bazai wuce Alh bilal dinba dan haka kowannensu ya sake shiru sbd basusan mafitar wannan qaddarar ba data rigayi fata.

Cikin rudewa da tashin hankali Annen batama san me dame take fada ba ta fara fada ciwonta na neman tashi sbd kanta da yayi nauyi neman juyewa yakeyi 

Benazir ta taso ta dawo gurinta da sauri tana kwantar mata da hankali sbd kar ciwon ya tashi komai ya lalace asan halinda suke ciki.


Har gari yayi haske suna daki suna fama da kansu ba sauki ko kadan dole Benazir ta fito ta hau aikin gidan gabaki daya ba maganar zuwa makaranta sbd tsoron fita takeyi ma tabarsu kada kafin ta dawo Ababa ya sani ta dawo ta tadda babu su ga kuma yanayin Annen daketa surutai cikin tashin hankali da fita hayyaci 

Sumayyah ma idanuwanta sunkai ko budewa basayi sosai sbd kumbura ga yanayinta na rashin lafiya.


Abincinsu na dare da basu ci ba haka suka zauna su ukun suka turasa cikinsu da sanyinsa harma ta sakewar daya fara yi sbd kada su fitar a san basu ci a fahimci suna cikin wani halin a gano.


Babu mai dadin rai ko nutsuwa a cikinsu haka kowa ya ringa diban abincin yana turawa bakinsa bame magana suna gamawa Benazir ta dauki kwanon ta fice taje tafara wanke wanke.


Annensu zaune take a dakin nasu ta kasa fitowa idanuwanta sunyi ciki ciki tsaban kuka da damuwa ta rafka tagumin da basusan yanzu kuma yanda rayuwa zatayi dasu ba.


Sumayyah kuwa ciwo ne yake cinta sosai amma tashin hankali da damuwa ya hanata nunawa itama tagumin ne ta rafka dukkaninsu kaman wainda ke jiran sakamakon mutuwa.


Benazir ma ayyukan gidan takeyi ba'a cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali ba kowannensu tinanin makomarsu yakeyi.


Sai bayan sallar Azahar ta kammala aikin tayi wanka da alwala tazo tayi sallah aka basu abincinsu data gama girkawa ta kawo ta ajiye musu dole sukai sallah suka zauna suka turawa cikinsu babu me jin dandanon komai a bakinsa cikinsu kowa 'dacin bakinsa yakeji musamman Sumayyah da nata ya hada dana ciwo da laulayi.


Tsit Hande taji gidan yayi suna daki babu me iya motsin kirki sbd damuwa da tinani dan haka ta fito tana qwala kiransu tana tambayar lafiya suke zaman daki kaman masu abin kunya.


Tsinkewa cikinsu yayi Anne ta kalli Benazir da itama ita ta kalla suka kalla sumayyah a tare kafin Anne ta bude baki cikin mutuwar jiki tace


"Ki zauna a dakin karki fito"


Gyada kai Sumayyah tayi tana rintse idanuwanta sbd kunyarsu dake cin zuciya da ganganr jikinta gashi ta kasa ko bude baki ta fada musu kaddara ce da shedan daya shigo ciki.


Anne da Benazir ne suka fito sbd kada hande ta tsananta maganar.


Kallansu tayi taga duk sun jeme a dare daya kaman wainda sukai kwanan zaune,

Fuskar Benazir ta kalla taga yanda ta sauya kwata kwata da alamar bata rintsa ba kuma harda alaman kuka bayan rashin baccin.


Kan Anne ta maida kallanta taga itama fuskarta tayi jajir ta kumbura,

Shiru tayi tana nazarinsu sbd da alamar akwai abinda ya samesu dan duk wuya duk tsanani su biyun nan basu cika kuka ba sbd Anne ta dade da samun rashin lafiyar rashin kuka sbd shekarun data debo a rayuwar gidan zuciyarta ta mace bata iya kukan hakama Benazir sbd taurin rai da juriya ba qaramin tashin hankali da masifa ke sakata kuka ba amma yau gashi da alama kukan suka kwana yi..


"Kodai sumayyah ta mutu ne tsakar dare?" Tayi tambayar kai tsaye tana kallan hanyar kofar dakinsu da mamaki.


Anne wani numfashi mai sanyi ta sauke zuciyarta na sosuwa da abinda Handen ta fada tayi qasa da kanta tana kasa cewa komai.

Benazir ma numfashin mara sauti mai dumi ta sauke tana girgizawa handen kai tace


"Tana nan lafiya ce batada tin jiyan"


"Shine kuka kwana kuna kuka ko me? Ta sake jefa musu tambayar tana kallan Benazir da idanuwanta ke sake yin qasa.


Shirunsu yasata rufesu da fadan batasan dabiar koke koke a cikin gidan da ba mutuwa akai musu ba.


Fada ta ringa yi sosai sai data gaji ta dena tace su wuce ga wankin shagon Ababa can an kawo.


Wucewa sukai inda manyan kullin kayan wankin masu yawa suke suka warware suka ringa kwashe kayan zuwa inda suke wankin.


Benazir ce ta fara debo ruwa masu yawa ta tara musu 

Suna fara wankin Anne ta sunkuyar da kanta qasa wani irin kuka mai sauti na subuce mata mai tafe da tsananin ciwo da quncin da zuciyarta take ciki.


Benazir radadin sautin kukan mahaifiyar tata ya sata kasa wanke kayan dake hannunta tayi qasa da kai itama wasu hawaye na tsinke mata,

Me zasuyi?

Meye mafitar halinda suke ciki?

Ya Allah ka dubi maraicinsu" shine abinda zuciyarta kawai ta iya fada sbd sunsani sun tabbatar mawuyacin hali ne suke ciki mai nauyi.


Saida sukai kuka sosai kafin suka hakura suka fara wankin babu mai magana har suka wuni sunayi sai gab da magriba suka gama sbd abincin dare da Benazir ta dora tanayi tana tashi.


Daki suka shige bayan sunyi Alwala abincin dare kawai sukaci sukai ishai da akai suka lafe dakin babu wanda ya sake fitowa saida Ababa ya dawo Benazir ce ta fita taje takai masa abinci da ruwa ta dawo dakin suka cigaba da zaman damuwa.


Washe gari ma hakan ce ta kasance babu wanda ya fita makaranta cikinsu haka suka wuni cikin mummunan yanayi na damuwa.


*****kusan kwanaki hudu sika share a hakan cikin zallan damuwa da qunci tareda tsoro da firgici mai tsanani,

Sumayyah na daki jikin nata sai tsanani yake qarawa amma basa barinta fitowa sai idan zata je bandaki kokuma idan Ababa ya dawo sbd kada ya saka musu idon zargin wani sai ta daure ta fito dan kawai ya gansu yasan suna nan kalau ba matsala,


Hande data ankara da yanayinsu gabaki daya ya sauya a kwanakin sai ta saka musu ido sosai ga Benazir data dena zuwa makaranta sbd tsoron kada ta fita a ganosu tinda daga Anne har sumayyah idan bata nan zasu iya firgicewa suyi abinda zai bayyanarda halinda suke ciki.


Ta bangaren Alh bilal kaante kuwa a cikin kwana biyun da baya ganinsu duk zuwan dayake yi kullum dan daukansu kaman zaiyi hauka a cikin kwanakin sbd gabaki daya shima ya shiga tashin hankali mai girma rashin ganinsu,

Tsoron Ababa da abinda zai iya yi musu yasashi komawa kaman mai tabin hankali shima dayake mutum ne mai nutsuwa da kamun kai take aka gano yana cikin mummunan yanayi na damuwa da tashin hankali,

Dad kaante da dd babba tini suka fahimci yana cikin mawuyacin hali sukaita tambayarsa ko lafiya amma sam zurfin cikinsa baya barinsa fada musu komai dan haka ran dad kaante ya baci ya kira Mahaifiyarsu Bilal din ya bata lokacin dawowarta idan ba haka ba damuwa zata kashe mata 'da a banza tana can gurin wancan da baya buqatan kowa tinda shine ya zabi zama baa cikin family dinsaba.


Dd babba kuwa ganin da gaske lamarin yayi yawa sai kawai ya tura bilal din wani aiki Kenya dole Bilal ya tafi bayan kusan har kwanciyar jinyar kwana biyu yayi sbd rashin sanin halinda su Sumayyah suke ciki,

Yayi yawo anguwar yafi so hamsin a kwanakin amma babu alamarsu gashi yana gudun ya tinkari Ababan kai tsaye kila bai saniba tukuna kada ya janyo musu fitina wanda ya san da DD ne da tini zai tinkari Ababan duk abinda zai faru ya faru kowama ya dade bai saniba.


Ms aysha ce Aminiyarsa da zata iya masa komai ko baya nan dan haka ita ya sanarwa komai tareda rokonta taje ta dubo masa su tareda kular masa dasu.


Ranar daya wuce washe gari cikin saa sai ga Benazir tazo makarantar itama sbd Ababa yafara fahimtar ta dena zuwa hakama suna neman mafitan yanda zasuyi da cikin daga Bilal din tinda basuda kowa basuda gurin zuwa hakama bayyanar cikin dede yake da basusan ma me zasu ce ba.


Zuwan Benazir makarantar ya hana ms aysha zuwa gidansu ta zauna da Benazir din cikin kulawa ta tambayeta lafiyarsu da yanayin Sumayyar.


Shiru Benazir tayi takasa magana sbd kukan dayazo mata a hankali 

Ta sanar da ms aysha mafita suke nema basuda yanda zasuyi da rayuwarsu.


Kukan Benazir ya taba zuciyarta sosai kusan saida idanuwanta suka ciko da hawayen itama dan haka

Cikin tausayi da baqin cikin qaddarar itama ta ringa rarrashinta tareda yanke shawarar zaa  cire cikin kawai kokuma dole Alh Bilal ya fito fili a yi maganar aure tin kafin maganar cikin ta bayyana.


A gaban Benazir Ms aysha ta kira Bilal sukai magana sosai ta nuna masa damuwar dasu Benazir suke ciki.


Kai tsaye kasa amincewa yayi da cire cikin sbd hadarinsa da cutatarwa ga Sumayyah zatayi yawa.


Bai taba jin karfin soyayyar data danne tsananin tsoro da shakkar dd babba da dad kaante ba sai a yanzu dayake jin zai iya daukan hukuncinsu dana familyn kaantes gabaki daya akan sumayyah.


Kaman yanda Benazir da Anne suke neman mafitar lamarin Ms aysha da Alh Bilal din sun musu alqawarin yana dawowa zai nema auren Sumayyah batareda Ababa yasan da maganar cikin ba hakama duk dukiyar dayakeso yayi alqawarin basa dan ya basa auren sumayyah din.


Wannan alqawarin yasa Benazir daurewa ta tsaya makaranta bayan Ms aysha tayi mata alqawarin tsaya musu har qarshen rayuwarta insha Allah.


Ana tashi makaranta ms aysha ce ta dauketa ranar da kanta ta kaita gida kuma cikin saa Ababa bayanan hakama hande tana baccin ranar data saba dan haka har cikin dakinsu dayasa ms ayshan zubda hawaye suka shiga ta duba sumayyah tareda yiwa Anne Alqawarin zata kula dasu Benazir kaman yayan data haifa a cikinta da yardar Allah.


Kudi ta basu amma tashin hankalin dasuka shiga ma na ganin kudin yasata maidawa jaka ba shiri sbd tsoron kudin.

Tanaji tana gani ta tafi batareda bar musu komaiba sbd sunqi karban kudin.


Tana ficewa Hande ta tashi data fito ta ringa mitar qamshin tiraren manya take jin ya cika gidan koina.


Shi kansa Ababa daya dawo saida ya tsinci qamshin musamman dakinsu dan haka aka bincike kayansu tsaf baa ga komai ba dole aka hakura sedai saka idanun da akai akansu sosai sbd sam hande ta kasa yarda dasu a kwanakin.


Benazir dole ta koma makaranta kullum tana zuwa 

Sumayyah dai dole aka hakura saita warke tukuna.


Kullum idan taje sai tayi magana da Alh bilal din a waya yaji ya jikin Sumayyah ta fada masa da sauki ta wuce karatunta.

#MAMUH#

#BENA#DD#ZAFIN KAI#


ZAFAFA BIYAR🔥


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR 'KASHI

Safiyya Huguma


-FURAR DANKO

Billyn Abdul


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at

1487616276

Access Bank 

Bilkisa Ibrahim


Send your Shedan biya Anan👇

09032345899


MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇

09033181070


Yan Nijar kuma ga inda zaku biya👇👇👇


+22799643131


Zafafa🫶🔥🔥

No comments

Powered by Blogger.