Zafin Kai 19

 


19

Ganinta neman gagararta dawowa yayi sbd bata taba samun kanta a mafi tashin hankali irin na wannan daqiqun ba datake cikinsu a yanzu,

Cikin haihuwa fa ake magana sumayyah take dauke dashi,

Ta haifa 'da ko 'ya masu rai fa,Innalillahi wainna ilayhi rajiun,

Qalu innalillahi wainna ilayhi rajiun,

Ya ilahi meye haka kunnuwanta yau sukaji,

Babbar kadaddariyar jarabawarsu ce yau ranarta ta tsaya,

Tsikar jikinta ne gabaki daya suka tashi sbd tinaninta daya dade da tsayawa babu abinda take gani sai gawar kansu su uku ita da Annensu da sumayyar harma da cikin.


Bilal kaante kuwa wutar data dauke jikinsa babu abinda yake zuwa kansa sai tausayin Sumayyah da abinda yake cikin wanda baisan me zai fada akansu ba yanzu,

Kalmar cikin ta girgiza sa ne sbd abune da bai taba zuwa tinaninsa ba a wannan lokacin.

Shi kansa a nasa bangaren wannan wani babban qalubalen ne da tashin hankali sbd tsakaninsa da iyayensa da danginsa wani abune da ko zasu rasa komai bazasu yarda da wannan zancenba sbd karma ya fita,dan gwara ya jewa dd babba da dad kaante da labarin sunyi asarar miliyoyin kudi masu yawan da hankali bazai dauka ba akan yaje musu da wannan labarin.


Daga shi har Benazir babu wanda yakeda nutsuwa ko tinanin kallan junansu kowannesu da nisan da yayi cikin nasa tashin hankalin da baa saka masa rana ba.


Kaman masu jiran sakon mutuwa haka suke babu me motsi,har lokacin Benazir na zube qasa zaune batada qarfin tasowa shima har lokacin yana tsaye,


Benazir tashin hankalinta yasa tini ta manta da yanayi sumayya tinaninta akan cikin yake har lokacin dan kuwa zancen ya kasa zaunuwa a ranta tayaya sumayyarsu zata samu ciki?

Ina ta samesa?

Da wa?

Yaushe?

Sam kanta ya kasa daukan zancen bare tasan yanda zuciyarta zata aje zancen.


Acikin zaman jiran da baifi na awa daya ba Idanuwanta sukai wani fadawa tareda yin jajir 

Daqyar take iya hadiye busashen yawu a makoshinta daga bakinta daya bushe qayau,


Bilal kaante kansa bakin nasa a bushen yake saidai yanayinsa yasa baa iya gane zallar damuwa da tashin hankalin dayake ciki.


Sumayyah batasan halinda take ciki da wanda suke ciki sai bayan awa hudu data share tana bacci sbd ruwan bacci dayake cikin ruwan da aka daura mata,


Tana farkawa Abinci mai lafiya da rashin nauyi Bilal yasa aka kawo mata,

Benazir har lokacin bata dawo cikakken hayyacinta ba gabaki daya bata gane komai sosai dan haka tana gefe rakube tayi zugum batasan me take tinaniba ita kanta tadai san tana cikin mafi girman tashin hankalin rayuwarsu.


Shine da kansa ya bawa sumayyar abinci cikin kulawa da so mai tsanani yanajin inama da aure ne tsakaninsu wannan qaddarar qaruwar ta same su da sai ya nuna mata soyayyar da zata manta da quntatacciyar rayuwarsu ta baya,

Yanzu gashi qaddara ta riga fata,waye zai fara tara da wannan maganar mai girma?


Sumayyah data dan samu kanta sai alokacin ta maida kallanta da hankalinta kan Benazir da zama abin tausayi cikin awanninsu a asibitin,


Magana takeson yi mata amma ganin gabaki daya Benazir na wani yanayi yasa ta kasa mata maganar ta dan dawo da kallanta kan Bilal da shima tin dazun ita yake kalla cikin tsananin tausayi da kulawa dan bayajin zai iya gangancin yimata abortion sbd tsoron abinda zai iya samunta kuma cikin ba laifinsa ne ba qaddara ce ta samar dashi wadda suma suke cikin nadama da neman yafiyar ubangiji tun ranar ra tsautsayin ya afka musu har yanzu kuma bazasu dena neman yafiyar Allah ba har qarshen rayuwarsu sbd shedan da kaddarar wannan samun ya afka musu.


Sabon zaman makokin da bana mutuwa ba suka dasa babu mai iya magana acikinsu kowa da tashin hankalin dayake tada zaman lafiyar zuciyarsa.


Benazir data rasa tinanin kamawa miqewa tayi jiri na neman dibanta tace gida zasu tafi kawai.


Kallanta Bilal yayi yana dago wayarsa da kira ya shigo yaga sunan dd babba ne kuma baa qin daga wayarsa idan ba babban dalili ba dan haka ya daga cikin tattaro nutsuwarsa datake kokarin barin jikinsa sbd komawan sumayyah gida da wannan cikin a yanxu babban hadari ne ga rayuwarta sbd komai ma zai iya faruwa idan Ababa ya sani.


dd babba dake babban lafiyayyan office dinsa na gida yanajin Bilal ya daga wayar kai tsaye yace yazo yanzu yanzu yana nemansa.


Rintse idanuwansa yayi cikin damuwarsa dake bayyana yana kallan su Benazir data miqar da sumayyah har sun kusa kofa yana jin kansa na sarawa da ya biyo bayansu ya bude musu mota yana kallan Benazir da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da sanyin jiki tareda kunyar kansa yace mata gobe da safe zasuyi magana idan ya taho daukansu amma ta kula da Sumayyan kafin goben.


Kai kawai ta iya gyada masa sbd bazata iya magana ba kuma bazata iya dagowa ta kallesaba.


A motar ma babu mai iya magana hankalinsa yayi mummunan tashi zuwansu gida da abinda zai iya biyowa kafin safiyar gashi dd babba na masa neman gaggawa wanda bai taba jin hankalinsa ya rabu biyu akan zuwan kiran dd babba ba sai yau din.


Yana ji yana gani dukkaninsu sukai shahadar rabuwa ya ajesu ya wuce yana sake jin fargaba na shigarsa na barinsu ya nufi gida.


Suna shiga gida suma kai tsaye dakinsu suka nufa sbd ba kowa tsakar gidan Annensu na bangaren dabbobinsa tana shara batasan dawowarsu ba,hande kuma tana daki tana baccin rana.


Kwantar da sumayyah tayi har lokacin bata ce mata komaiba sbd batasan me zata fada din ba sbd zuciyarta data kasa dawowa da bugawa daidai.


Zubewa tayi gefen sumayyar tareda rafka wani mummunan tagumi nauyin idanuwanta na qaruwa,


Sumayyah datake kallanta cikin nauyin idanuwan itama tashi tayi zaune tana kallan Benazir din da damuwa ta bude baki cikin taushin murya mara karfi tace


"Bena meya faru?

Meyasa kike cikin yanayin nan?

Wani abin ya faru ne?


Juyowa Benazir tayi da jajayen idanuwanta ta zubawa Sumayyahn sai alokacin taji hawaye na ciko idanuwanta.


Cikin mutuwar jiki da damuwa mai tsanani sumayyah ta dafa hannun Benazir din dake rawa muryarta na shiga tashin hankalin ganin hawayen dake ciko idanuwan Benazir tace


"Meya faru Bena?

Dan Allah fadamun meya faru,

Meya sameki?


Wani irin kuka mai ciwo da radadi ne ya kufcewa Benazir din mai qarfi da rshin sauti ta sunkuyar da kanta tana kasa magana.


Kukanta ya saka jikin Sumayyah daukan rawa sosai cikin tsoro da fargaba mai girma sbd duk abinda ya saka Benazir hawaye babba ne bare kuka mai qarfi irin haka.


Annensu data shigo dakin tayo alwalar sallar laasar zatayi tana ganinsu ta qaraso tana kallan Benazir datake kuka mai ciwo da radadin rai.


A tare cikin rudewa suka sake jefa mata tambayar abinda ya faru.


Annensu ta dago ta kalla tausayinta ya kamata saidai babu abinda zasu tare daga qaddarar da ubangiji ya doro musu saidai tasan wannan qaddarar mai nauyi ce garesu musamman Annensu da bazata iya daukan wata azabar ba da ciwon lamarin a matsayinta na uwa kuma mahaifiyar sumayyah.


"Menene Benazir ki fada mana,meya faru?"


Takardar da aka basu a asibitin ta cikin Sumayyah ta ciro daga cikik rigarta ta miqawa sumayyah sbd Anne bazata iya karantawaba, taja wani numfashi mai zafi da mutuwar jiki Muryarta a sanyaye ta bude baki tace


"Anne ciki ne kaman yanda kikai tinani......


Kasa qarasa bude takardar Sumayyah tayi ta tsaya cak tareda dagowa tana kallan Benazir datake hana kukanta dawowa tana kallan Annensu data dauke wuta.


"Anne, Anne, Anne" tafada hankali tashe tana taro Annen jikinta sbd yankewan da jikinta ne neman yi.


Tashi tayi hankali tashe koina jikinta na rawa ta taro Annen tana sake kiran sunanta cikin sabon tashin Hankali murya qasa qasa sbd ba daman daga muryar kada a jisu.


Sumayyah da itama tayi mutuwar zaune ta juyo ta kalla cikin tashin hankali tace kawo ruwa Anne zata siqe.

Sumayyahn bata san me Benazir take fada ba sbd suman datayi a zaunen itama.


Tashi Benazir tayi da sauri ko gabanta bata gani tana kimfewa ta sake tashi da sauri ta fice ta debo ruwa tana zuwa ta zubawa Annensu kofin ruwan gabaki daya kafin ta sake fita qafafunta na hardewa ta debo wasu ta zubawa sumayyah ta wurgar da kofin tayi kan Annensu dake jan numfashi daqyar tana dafe kirjinta dake toshewa.


Cikin tashin hankali da tsoro mai tsanani Benazir take shafa mata bayanta tana karanto mata adduoi tana kiran sunanta a hankali.


Sumayyah data dawo hayyacinta kuwa wasu hawayen tashin hankalin da baa saka masa rana bane suka tsinke mata tana jin tsoron da bata taba jinsa ba a rayuwarta yana shigarta sbd tabbas lokacinta yayi.


A hankali Anne ta dawo daidai ta dago ta kalli Benazir da idanuwanta sukai jajir ta maida kallanta kan sumayyah take suka fashe da wani irin kuka mai tsananin ciwo da tashin hankali duka su ukun a lokaci daya.


Kuka sikeyi sosai mara sauti kowannensu na rasa abin fada tsawon lokaci mai tsayi kafin Benazir ta dago tana share fuskarta sbd jin motsin fitowar Hande tsakar gidan tana kwada kiran Annensu dan batasan suma sun dawo ba.


Kowannensu taqaita kukansa yayi suka share fuskokinsu babu wanda yace komai suka fito daya bayan daya fuskokinsu a qasa sbd yanda idanuwan kowannensu yayi jajir ya kumbura.


Kallansu Hande batayiba bare taga halinda sike ciki kai tsaye ruwan datasa a debo mata a bokiti Benazir ta debo mata takai mata bandaki ta fito sukai alwala sai alokacin suka samu damar yin sallolin dake kansu itama Annen me alwalar laasar saida ta sake wata.


Koda suka gama sallah jigum jigum sukayi har lokacin babu me magana sbd bude bakinsu ma a yanzu tsoro sukeji dan basusan ta inda zasu faro wannan maganar ba a cikin gidan da fitar maganar daidai take da tsayuwar alqiyamarsu.


Har akai sallar magriba aka fito babu wanda ya fita acikinsu da alwalar sukai sallar suka sake komawa zaune kowa yayi shiru yayi nisa a tinaninda babu komai acikinsa sai tashin hankali da tsoro tareda tinanin makomarsu a gurin Ababa.


Abincin dare da aka basu a ranar haka ya kwana bar safe babu wanda ya sake kallan inda yake sbd masifar da suke ciki.


Suna gama sallar asuba Anne ta kalli sumayyah da a daren guda ta zabge sbd tashin hankali.


Dukkaninsu babu wanda idanuwansa basu fada ba sukai jajir sbd duk kasancewar bacci barawo a ranar ya kasa sace su ynda suka ga rana haka suka dare.


"Waye yayi miki haka Sumayyah?

Wane qaddara ce wannan sumayyah?

Tsautsayin menene wannan?

Meyasa sumayyah?

Waye ne??


Tsit dakin ya dauka bayan numfashin dake fita a sarqe da damuwa mai tsanani babu abinda akeji a dakin.


Sunkuyar da kai Sumayyah tayi wasu hawayen na gudu kan fuskarta quncinta na tsananta tareda kunyar kanta dana mahaifiyarta da 'yar uwarta sbd wannan qaddarar masifarta ba iya kanta zata tsaya ba dukansu ukun ta tabbatarda sai sun mafi munin halin quncin rayuwa a gurin Ababa.


"Alh Bilal"  tafada muryarta na yankewa sbd kuka mai qarfin dayazo mata.

#MAMUH#

#DD KAANTE#

#LOVE#AMNAH KAANTE#BENAZIR#crazyinlove#


ZAFAFA BIYAR🔥


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR 'KASHI

Safiyya Huguma


-FURAR DANKO

Billyn Abdul


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at

1487616276

Access Bank 

Bilkisa Ibrahim


Send your Shedan biya Anan👇

09032345899


MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇

09033181070


Zafafa🫶🔥🔥

No comments

Powered by Blogger.