Nihaad 51

 


Nihal ta karasa har inda Nihad take tana kallonta ta zauna gefenta with smile all over her face, a hankali tace "Welcome sis" Nihad ta sauke idonta tace "Thank you Nihal" Nihal tace "Ina Khalil din?" Nihad ta kalleta tace "He is fine" Nihal tace "Ohk ba tare ku ke ba?" Nihad tace "Ajiyeni yayi kawai" Nihal tace "Ohk, kinyi kyau sosai sis" Ta karasa maganar tana murmushi, Nihad dai bata ce mata komai ba, Nihal ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "And i miss you so much" Nihad tace "Same here" Nihal tace "I am happy u are home" Shiru Nihal tayi bata ce komai ba, can Nihal ta mike a hankali tace "Zan je inyi wanka" Nihad tace "Ohk" Daga haka ta nufi kofa Nihad ta bi ta da kallo har ta fita, Tana fita da few minutes Mumy ta shigo dakin rike da tray, Hafsah na biye da ita da flask, cike da murna Hafsah tace "Sannu da zuwa Aunty Nihad" Nihad ta kalleta tana ɗan murmushi tace "Ya kike Hafsah" Hafsat tace "Alhamdulillah Aunty" Nihad tace "Ya aiki?" Hafsah na washe baki tace "Lafiya lau, munyi kewarki sosai Aunty" Nihad dai tayi murmushi kawai, Mumy dai ta zauna sai kallon Nihad take cike da mamaki, yaushe har ta wani san da zaman Hafsah a gidan balle har ta mata fara'a haka har da tambayarta ya aiki, Hafsah ta juya ta fita daga dakin, Nihad ta sauko ta zauna saman Carpet ta dau cup ta debi ruwan zafi, bayan ta gama hada shayin ta daga kai ta kalli Mumy taga kallonta take, Nihad tace "Mumy Nihal tayi rashin lafiya ne?" Mumy tace "Me kika ga?" Nihad tace "Aa kawai naga ta rame" Mumy tace "Tun dai kwanaki a school but she's better now, kawai stress din makaranta ne, you know she is in her final year" Nihad bata ce komai ba, bayan few seconds cikin sanyin murya tace "Su sudais sun tafi school?" Mumy tace "Ehh..." Shiru Nihad tayi tana juya shayin gabanta, Mumy tace "Ya yan uwan mijin naki gaba daya?" Nihad tace "Duk suna nan lafiya, suna gaishe ku" Mumy tace "Toh maa sha Allah, shi xai shigo nan ne a hada masa breakfast?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa sai anjima" Mumy tace "Toh shkkn" Mikewa tayi ta fita ta bata waje don ta karya comfortably don taga kamar duk a ɗari ɗari take. Nihad na gama breakfast din ta dau tray din ta fita main parlor, har ta mance yaushe rabon tayi breakfast cikin dadin rai haka, Zaune ta ga Nihal da Mumy a parlor, Hafsah dake goge goge ta taso da sauri tace "Bari in kai maki kitchen Aunty" Nihad tace "Aa Nagode, ci gaba da aikinki xan kai" Daga haka ta wuce kitchen din Nihal ta bi ta da kallo haka ma Mumy, Dai dai nan Umma ta shigo parlon daga bangarenta kamar warce aka hankado rike da makullin mota, ko lura da Mumy bata yi ba tana kallon Nihal tace "Idan Abbanku ya fito kice masa jikar Hajiya Turai ta fada cikin ruwan zafi yanzu aka kirani na tafi gidan, bana son tashinsa yana bacci, sannan don Allah ki tafi dakina zaki ga kayana saman gado duk na birkito ki jera min, sauri nake shi sa ban maida su ba" Nihal tace "Toh Allah ya sauwake" Mumy dake ta kallonta tace "Subhanallahi, ayi masu sannu don Allah" Tuni Umma ta fice daga parlon cikin hanzari ba tare da ta ma san Mumy na wajen ba. Nihad ta fito kitchen kenan sai ga Abba ma ya fito daga parlonsa jin tashin motar Umma don ba bacci yake ba, hada ido suka yi da Nihad, Sosai gabanta ya fadi ta makale jikin kofar kitchen din ko ina na jikinta ma rawa, Ita kanta Nihal dake zaune sai da gabanta ya fadi, Mumy dai ta sunkuyar da kanta kawai, Abba dai kallon Nihad kawai yake babu ko kiftawa, Nihad ta sauke idonta kasa, lokaci daya taji hawaye ya cika idonta, Abba ya dauke idonsa daga kallonta yana kallon Nihal yace "Ina Baabarki ta tafi?" Nihal tace "Wai jikar Mama Turai ce ta fada cikin ruwan zafi shine ta tafi" Juyawa Abba yayi ya koma parlonsa, Nihad ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa Mumy tayi ta bar parlon ta shiga nata duk jikinta a sanyaye, Nihal ta karasa kusa da Nihad ta kamo hannunta a hankali tace "Mu je ki gaishesa" Nihad dai bata ce komai ba hawaye sai bin fuskarta suke, haka Nihal ta nufi parlon Abba da ita tana rike da hannunta, Zaune suka gansa parlon ya jinginar da kansa jikin kujera, Nihad ta ki barin su hada ido ta durkusa daga nan bakin kofar tayi gathering courage muryarta na rawa tace "Abba ina kwana" Yana kallonta bayan few seconds yace "Me ya kawo ki gidana?" Ta girgiza kai hawaye me zafi na sauka idonta tace "Kayi hakuri Abba" Bai kuma ce mata komai ba sai dauke kansa da yayi daga kallonta, staring at the Ac in his parlor, Nihal ta juya ta fita daga parlon hawaye cike idonta, mikewa Nihad tayi da sauri ta bi bayanta tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Abba ya bi ta da kallo lokaci daya yaji hawaye ya kawo idonsa, mikewa yayi ya shige bedroom dinsa, Nihad ta koma bangaren Mumy ta shiga bedroom dinta ta ga Mumy zaune gefen gado looking so worried, fadawa kan gadon Nihad tayi tana kuka a hankali, Mumy tayi karfin halin cewa "Me yace maki? Yace ki bar masa gidansa ko?" Nihad ta kasa cewa komai sai kuka take sosai, Mumy bata san sanda ita ma ta fashe da kukan ba, taji zuciyarta na mata zafi, Nihad na ganin haka ta mike da sauri ta rungumeta tana kuka sosai tace "I am sorry i never listened to you mum, kiyi hakuri ki yafe min plsss..." kasa ci gaba tayi saboda kuka da ya ci karfinta, Mumy tayi karfin halin cewa "Baki min komai ba Nihad, na yafe maki duniya da lahira, babu abinda kika min, haka Allah ya tsara maki rayuwarki babu kuma wanda ya isa ya canza hakan" Nihad na kuka bitterly tace "Amma Mumy baki taɓa ce min Umma ba so na take ba, u never told me she is misleading me, nobody was there to tell me all this, Umma caused me all what i am passing through now" Mumy ta dakatar da kukan da take tana sauraronta babu ko kiftawa, Cikin kuka sosai Nihad tace "Duk abinda nake yi a baya Umma ce take sa ni inyi, she neva gave me the chance to differentiate what's good or bad, she is always supporting me in every aspect, i don't know she was just ruining my life, ta cuci rayuwata, me yasa baki taɓa gaya min bata sona ba, me yasa baki gaya min ba masoyiyata bace? mumy me nayi mata?" Mumy ta girgiza kai kawai wasu hawayen na sauka idonta ta kasa ce mata komai, A hankali Nihad na girgiza kai sounding bitterly tace "Ita ta karfafa min gwiwa wajen yin kawance da su Husnah, she encourage me to follow them everywhere, ta nuna min duk wani dake aiki a gidanmu bashi da value i should treat them harshly idan ba haka ba za su raina ni...." Mumy tayi shiru sai sauraron Nihad take, Nihad tace "Mumy ba wani gidan Aunty Kamila da naje, duk watanni hudu da nayi bana gidan nan ina hostel tare da su Husnah, i never went to Auntt Kamila's place Umma planned it for me...." Mumy bata san sanda ta mike tana kallon Nihad babu ko kiftawa ba, Nihad na share hawayen da yaki tsaya mata cike da karfin hali tace "Ita tace ma Kamila ta kira Abba tace za mu je kebbi amma babu wani kebbi da muka je, all those while i am staying in the hostel with my frnds, duk wani hotel da party da su Husnah za su Umma tasan ina bin su ita ke encouraging dina in bi su, duk sanda na fita da daddare zuwa party Umma ce ke bude min kofar parlor babu wanda xai sani, tun da na taso muke haka da Umma....." Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka me ban tausayi, she is deeply regretting everything now, tayi da ta sanin abubuwa da yawa da tayi a baya, nobody was there to tell her Umma ba sonta take ba all that while, wasu abubuwan ma baxata iya gaya ma Mumy ba amma Umma ta cuceta ta cuceta iya cuta, sannan ta nuna mata da ma duniya gaba daya babu wanda take so sama da ita, Mumy dai ta kasa cewa komai sae kallonta take babu ko kiftawa, kana ganinta kasan she is shock, don duk bata san da abubuwan nan da Nihad ke fadi yanzu ba, ta dai san komin laifin da Nihad xata yi a gidan Umma bata barin a mata fada sai ta nuna ai yarinya ce babu abinda ta sani, sannan ko me take so wajen Abba Umma ke taimaka mata wajen amsa, ko kai maye ne baxaka ce Umma bata son Nihad da gaske ba, sai ta siya ma Nihad abu sau goma bata siya ma er ta Nihal ba, wannan ne ma ya sa Mumy ta kara jawo Nihal jikinta sosai.... Nihad ta zamo kasa muryarta na rawa tace "Don Allah ki yafe min Mumy, amma ban taso na gan ni a wajenki ba, i never knew u were my mother at first, Mumy me yasa kika bar ma Umma ni? Why did u hand me over to her?" Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, Wani kuka ya taho ma Mumy bayan memory din yanda Umma ta rabata da Nihad ta karfi da yaji tun tana 5 years ya dawo mata vividly.... Mumy tayi duk iya kokarinta na ganin Abba bai dauke Nihad daga wajenta ya damka ma Umma ba har hakan sai da yayi sanadin igiyar aurenta daya a gidan, babu irin bakaken maganganun da Inna bata gaggaya mata ba a wancan lokacin wai bata da kara bata da kunya akan yar ta ta fari, ina ruwanta da er ta na fari da har zata zakalkake a kanta tana nuna tafi kowa iko da ita sae kace ba bafillatana ba, banda zamani ya lalace, su zamaninsu babu macen da ta isa tayi haka, har inna ke kara tunatar mata cewa Umma bata rike ɗan ta na fari da na biyu ba bata ma san ta yanda suka girma ba ta kauda kai a kansu kamar ba ita ta haifesu ba, Ya Farooq da ya Usman basu taso wajenta ba, tun daga yaye inna ta daukesu suka koma wajenta a Bauchi kuma Umma bata taɓa cewa don me ba, yawancin rayuwarsu duk a wajen Inna suka yi a lokacin ma kakansu na da rai, sae ya kasance Kamila ce kawai gaban Umma and she never complained for once, har dai ta zo ta haifi Nihal, washegari kuma Mumy ta haifi Nihad, wanda sai da Mumy tayi shekara goma a gidan kafin ta haihu, duk tana gidan aka haifi Usman da Kamila amma ita Allah bai bata haihuwa ba, dalilin da yasa da ta haifi Nihad Abba ya dau son duniya ya daura mata gashi fara ce kal kamar zaka latsa ta jini ya fito, ga masifar kyau kamar er larabawa, dama shi farin yaro da shegan shiga rai yake, ita kuma Nihal baƙa ce amma suna kama sosai da Nihad, sai ya dau Nihad sau goma bai dau Nihal sau daya ba don Nihal tana da kiwiya sosai shi sa ma bai bin ta kanta, ba ta yarda da kowa sai Umma, hakan yasa yafi shakuwa da Nihad da ko muryarsa taji ta dingi kuka kenan sai ta gansa ya dauketa, shakuwa me tsanani ya shiga tsakaninsu ya dau soyayya mara iyaka ya daura mata, har cikin ransa yake jin Nihad, wanda Mumy na lura da Umma kamar hakan baya mata dadi don bata iya boye hakan a fuska, ga kuma er ta Nihal shegen kiwiya da kuka, Mumy kan ce ma Abba ya daina bambanta su kar a samu matsala, nuna banbancin bashi da amfani don duk daya suke a wajensa, amma sai yace mata ai Nihal kiwiya gareta bata yarda da kowa, haka rayuwa ya ci gaba har aka yayesu, tun Nihad na shekara uku Umma ta fara nuna tafi damuwa da ita akan Nihal kamar yanda taga Abba ke yi, ta sha attempting mayar da Nihad dakinta gaba daya amma Mumy taki bada fuskar hakan, don babu Alkunya take shiga ta dauke er ta ko da kuwa bacci take a dakin Umma komin dare kuwa, ko hularta bata yarda ta bari a dakin Umma, Umma bata hakura ba har sai da ta san yanda ta hada makircin da ta hada tare da goyon bayan Inna Nihad ta dawo wajenta, Wanda har sai da Abba ya saki Mumy akan issue din wai tana son raba masa kan gida, ga inna ta saka ta gaba da gore gore wai ai ba da ita ta zo gidan ba sannan ina ruwanta da er ta ta fari idan ba rashin kunya ba, karfi da yaji dai aka raba Mumy da Nihad, babu yanda Mumy ta iya tana ji tana gani ta cire hannunta akan wasu lamarin Nihad ta bar ma Umma gaba daya, and that was the genesis of the whole problem.... Mumy ta kasa ci gaba da zama dakin ta fita kawai ta koma parlor tana jin xuciyarta na mata zafi, Umma ta cuceta ta cuceta, ita kuwa bata ma er ta irin rikon da tayi ma Nihad ba, Nihal da kanta ta koma bangaren Mumy a lokacin ma tayi shekara goma, tana ji tana gani sae Umma ta hana Nihad shigowa wajenta, babu kusanci kwata kwata tsakaninta da Nihad, to amma ya zata yi, tunda ga abinda mijinta da uwar mijinta suka ce, kawai sae ta rungume Nihal tana ganinta kamar yar cikinta. Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta koma saman gadon Mumy ta kwanta ta rufe idonta a hankali tana jin kanta na ciwo, a haka har bacci ya dauke ta. Wajen karfe goma da wani abu Nihad ta bude ido a hankali ta dalilin tashinta da aka yi, ta mike zaune tana kallon Nihal dake zaune gefenta, Nihal tace "Ana kiranki a parlor" Nihad na murza idonta tace "Waye?" Nihal ta mike tace "Ki fito" Daga haka ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta mike da kyar ta nufi kofa ta fita Parlon Mumy, zaune ta gansa duk ya wani birkice yana kallon kofar dakin eagerly, suna hada ido ta sunkuyar da kai a hankali, Nihal ta juya ta fita ta rufe kofar parlon, sai a sannan ya mike da sauri, Nihad tayi saurin juyawa zata koma dakin yayi hanzarin bin ta har ciki ya fizgota, zaro ido tayi tace "Don Allah ka bari kar wani ya shigo" kin yarda su hada ido tayi taki dago kanta, da taga he is trying to raise her head up kawai ta kwanta saman kirjinsa tayi lamo, she could feel how fast his heart is beating, ta lumshe idonta a hankali, ya rungumeta sosai, Underneath his breathe taji yayi maganan da ita kanta bata ji ba, jin hawayenta a jikinsa ya dago kanta da sauri yana kallonta, kasa barin su hada ido tayi, cikin rawan murya tace "I am... Am sorry, i..." sai kuma ta kasa ci gaba ta fashe da kuka, Lokaci daya ya saketa jin an bude kofar parlor, ta goge idonta da sauri ta fito parlon sai ta ga Nihal ce ta shigo rike da ruwa da lemo, Khalil ya fito parlon shi ma ya zauna, Nihal dai bata yarda ta hada ido da su ba. Tashin hankalin da Mami ta shiga ba a cewa komai da ta shiga dakin Khalil da sassafe taga baya ciki, kuma bata ga alamar ma a dakin ya kwana ba, tun sannan take kiran duk layinsa taji su a kashe, ta ma rasa takamaiman abinda zata yi, tun cikin dare take Allah Allah gari ya waye ta samesa tace masa ko za su je can kano ne gidan iyayenta ko Allah ya sa can ta tafi, sai gashi ta shigo babu shi a dakin, ta dawo bangarenta cike da damuwa, tana zaune tare da Mimi a parlon tace "Kuma ko number yayanta baki da shi ko?" Mimi ta girgiza kai a hankali tace "Bani da shi" Bude kofar parlon aka yi, duk suka daga kai, Mami ta dinga kallonsa da mamaki don in ba dai tana kwance ba lafiya ba baya shigowa bangarenta kai tsaye haka, sannan ko minti ashirun bai yi da dawowa gidan ba, kuma ba ita ce ma da girki ba, Mimi ta mike ita ma tana kallonsa tace "Good morning sir" Bai amsa mata ba ta nufi kofa ta fita, Mami na ganin yanayinsa ta san ba lafiya, to me kuma ya faru, ta dai mike cikin dakewa tace "Lafiya kuwa Yallabai? Is everything alright" Yana huci yace "Stop asking me that, Ina Ibrahim? Provide him now" Mami sai da gabanta ya fadi, tayi karfin halin cewa "Is everything alright" tsawa ya daka mata yace "Ina maki tambaya kina amsa min da tambaya?" Ta koma ta zauna bata sake ce masa komai ba, ya sake jefo mata tambayar ina Ibrahim, a fusace tace "Tunda dai ba goya Ibrahim nake ba ta ina xan san inda yake da sassafen nan? Ba dai ka san hanyar dakinsa ba" Yana muzurai yace "Ohh haka kika ce?" Tace "Ya kake son ince? Naga dai ba nan yake kwana ba da ka zo nemansa a nan, za ka wani zo ka isheni ina Ibrahim" Ya fi second ashirin yana kallonta yana gyada kai, kafin ya juya ya fice daga parlon almost ripping the door off, tagumi tayi tana tunanin to me kuma yaron nan yayi? Wannan wani irin fitina ne ita kam, Noor ce ta shigo parlon tana kallon Mami a sanyaye tace "Mami kin san me Yayanmu yayi?" Mami da taji gabanta na faduwa sosai tace "Me yayi Noor?" Noor ta zauna cikin sanyin murya tace "He broke into Abba's room and collected all what Abba seized from him, lalata makullin dakin ma fa yayi" Buda baki Mami tayi ta kasa cewa komai zuciyarta na bugawa, Noor tace "Ina jin cikin dare kowa na bacci yayi haƙan, he scattered everywhere in the room" Mami ta saki salati ta rafka uban tagumi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai ga Aunty Hassana ta shigo parlon babu ko sallama cike da rashin mutunci tace "Ke kam fatima kin haifar mana fitina a gidan nan, don Khalil fitina ne wallahi...." Mami ta dakatar da ita tace "Ban haifi fitina ba sai in ke kika haifi fitina wallahi"



*Thanks for being patient with Khaleesat*


Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah



Ur evidence via 07087865788

No comments

Powered by Blogger.