Nihaad 50

 


Nihad ta dinga kallon Nadeeyah dake tahowa tare da Mimi ko kiftawa babu har suka karaso parking space din, Nadeeyah na kallonta murmushi dauke fuskarta cikin sanyayyen muryarta tace "Sannu da zuwa" Babu yabo babu fallasa Nihad tace "Yauwa" daga haka kuma ta dauke kai, Khalil ya kulle motar yana kallonsu ya ɗan yi murmushi yace "Hi Nadeey..." Nadeeyah taki yarda ta kallesa tace "Welcome" Mimi ta nuna ma mai aikinsu Nadeeyah da ta taho trolly dinsu dake cikin mota, yarinyar ta saukar da su daga booth din ta dauka ta wuce ciki, Nadeeyah ta dau wani karamin jaka ta bi bayan mai aikin, Mimi na kallon Khalil tace "Yayanmu xaka shigo ne?" Khalil yace "Yeahh, ki tafi ina zuwa xan yi waya tukun..." Mimi ta kalli Nihad tace "Let go in Neehad" Nihad ta ki ce mata komai, Mimi ta kalli Khalil da ya fiddo wayarsa yana danne danne kamar zai yi sending call, Ta sake kallon Nihad sai kuma kawai Mimi ta juya ta bi bayan Nadeeyah, bayan sun yi nisa Khalil ya mayar da wayarsa aljihu yana kallon Nihad ya dawo kusa da ita yace "Why are you not going in?" A takaice Nihad tace "I am not staying in this house" Ya dinga kallonta, sai kuma yace "Why??" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ban ga zan iya ba" Shiru yayi yana kallonta, ta jingina da motar ta rungume hannunta ta hade rai alamar she isn't moving an inch, Ya jingina gefenta yayi kasa da murya yace "Ohk, How about we spending the night at the hotel together" Ta kallesa da sauri, ya dage mata gira, ta dauke kai tana jin gabanta na faduwa, ya kamo hannunta a hankali yace "Kinsan Mami ce tace ku zo nan yau, so it won't make sense in maida ke gida ince kince baxa ki zauna ba for now reason, so kawai mu tafi hotel" yana gama fadin haka ya bude mata back seat yana kallonta yace "Ur usual spot" Nihad dai ta kasa cewa komai kuma ta ki shiga motar, wayarsa ne ya fara ring ya duba yaga Mimi ce, dagawa yayi tace "Yayanmu Kai Mumy ke jira fa bata wuce sama ba, or ain't you coming in again" Da sauri yace "Ohk, ohk I'm coming" Daga haka ya katse wayar, yana kallon Nihad yace "Bari in je mu gaisa da mutanen gidan, idan na fito sai mu tafi hotel din" yana fadin haka ya nufi cikin gidan, Nihad ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta, why will they bring her to this house, gidansu wannan er iskar yarinyar, tasan baxata bi sa hotel ba but she will surely not stay in this house... Khalil na shiga ya tadda Mum din Nadeeyah xaune a parlor, ya gaisheta da ladabi ta amsa da fara'a tace "Ina bakuwar?" Yace "Yayanta ne ya kira take magana da shi a waje" Nadeeyah dai sai kallonsa take, Mumy tace "Allah sarki" Khalil ya kalli Nadeeyah dake zaune saman kujera suna hada ido ta dauke kai, tunawa yayi bai yi sallah ba ya mike da sauri yace "Mumy xan yi sallah in dawo yanzu" Mum din Nadeeyah Tace "Toh je kayi... Ga abinci xa a zuba maka kafin ka dawo...." Kofa ya nufa ya fita yana kallon parking space, bai ga Nihad a wajen da ya bar ta ba, yayi still yana bin compound din da kallo amma babu alamarta, cikin few seconds ya karasa gun mai gadi dake bakin gate yana kallonsa da sauri yace "Wata ta fita gidan nan yanxu ne Malam?" Mai gadin yace "Ehh bata dade ma da fita ba" Khalil ya zaro ido with shock yana kallon mai gadin ya kasa ce masa komai, sai kuma ya fice da sauri daga gate din, at first ya ma rasa ina zai bi don hanyoyi ne daban daban a area din, kawai ya dau hanyar titi, cikin minti kadan ya iso main road din duk da nisan shi, amma bai ga alamar Nihad ba, ya dinga bin ko ina da kallo zuciyarsa na bugawa, lokaci daya yaji wani xufa na keto masa at the same time ƙafafuwansa suka masa nauyi.... Sai da Nihad ta tabbatar tayi nesa da anguwan sosai sannan ta tsaya, ta cikin layuka tayi ta tafiya har ta ganta a wani babban titi, wanda hakan yasa ta gane she is very far away from the area she just left, tana ta tsaye bakin titi tana bin lafiyayyun motocin dake wucewa da kallo ta rasa next step din da xata dauka, she stood there for more than 15min a bakin hanyar kafin wani mota yayi parking kusa da inda take tsaye, ta koma baya tana kallon motar, wani mutumi da baxai wuce shekara 55 ba ya sauke glass yana kallonta yace "Yan mata ina zuwa? Ki shigo in rage maki hanya mana kina ta tsayuwa a nan" Nihad dake ta kallonsa taki cewa komai, yace "Haba yan mata ya kika yi shiru, naga tun daxu kike ta tsaye a nan, har na shiga wancan supermarket din na yi siyayya na fito" Sai a sannan Nihad tace "Bani da kudin mota ne, na yar da jakata" Yace "Subhanallahi, to shigo in ajiye ki inda za ki ko, Allah ya tsare gaba" Nihad tace "Sai dai ka bani kudin motar" Dariya yayi yace "Toh nawa ne kudin motar" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Ko nawa ne ka bani" Yace "Toh amma me yasa baxa ki shigo in ajiye ki ba, ba fa ɗan yankan kai bane ko ɗan Kidnapper, Kinga dare yayi bai kamata mace kamarki na tsaye bakin hanya a wannan lokacin ba" Tayi shiru ta ki cewa komai, yace "Toh bari a baki kudin motar tunda baki yarda da ni ba, amma wani anguwa kike?" Tace "Can gaba ne" Ya ciro kudi ya mika mata hade da wayarsa yace "To sa min number wayarki yan mata" Ta amshi kudin ta ajiye masa wayarsa kan kujera me zaman banza tace "Nagode, amma bani da waya wallahi" Tana gama fadin haka ta ci gaba da tafiyarta da sauri, ya bi ta da kallo baki bude. Tafiya kawai Nihad take amma bata ga alamar adaidaita sahu ko daya unguwar ba, gashi ta gaji sosai abun ka da bata saɓa da tafiyar kafa ba, har lokacin kuma bata duba nawa mutumin ya bata ba, daga karshe ta ganta a gaban wani babban supermarket, a nan taga wani me adaidaita ta nufesa da sauri tace "Tasha zan je" yace "Wani tasha?" Tace "Inda ake hawa motar kano" yace "Toh mu je" tace "Nawa ne?" Mutumin yace "Dubu biyu" Nihad ta kalli kudin hannunta ta fara kirgawa taga dubu biyar ne, ta shiga adaidaitan, ya tada suka bar wajen, Nihad na isa tashan bayan ta ba mai adaidaita sahu kudin ta shiga ciki, ai ko ta samu mota da xai kama hanyar kano a lokacin, nan ta tambayi nawa ne kudin mota aka ce mata dubu takwas, tayi kuri da ido ta kasa ce masu komai don dubu uku kadai ne a hannunta, can ta koma gefe ta tsaya kamar munafuka, dreban motar yace "Hajiya nawa xaki bada?" Tayi shiru sai kuma tace "Ni bani da kudi amma idan na baka wannan xaka karba?" Tana magana tana kokarin ciro dankunnen kunnenta, duk da akwai haske a wajen sai da mutumin ya kunna fitilar wayarsa yana haska ɗan kunnen da kyau, can ya kira wani abokin aikinsa shi ma ya duba, Mutumin na kallonta yace "Ai kawai ki fadi nawa zaki siyar ba cuta ba cutarwa sai a baki kudinki ki cire kudin mota" Nihad tace "Ai ban san nawa zaka siya ba" Yace "Kin siyar dubu talatin?" Nihad dai tayi shiru sai kuma tace "Toh" Mutumin yace "Toh ina zuwa" Can sai gashi da cash din dubu talatin ya mika mata, Nihad ta amsa ta kirga dubu takwas ta basa, sannan ta shiga motar wanda duk maza ne a ciki, suka bar mata jikin window ta zauna.... Mami ce tsaye parlor tare da Mum din Nadeeyah suna kallon Khalil dake zaune saman kujera ya ki ce masu komai, kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, Mimi sai hawaye take, Noor dai na zaune saman kujera don tare da Mami suka zo gidan, Nadeeyah kuma na tsaye can kusa da dinning area, Mami tace "Magana fa nake maka ka min shiru Khalil, ina kake tunanin yarinyar mutane zata tafi da daddaren nan? Lokaci fa na wucewa" Mikewa yayi without looking at them yace "Nima ban sani ba" Daga haka ya nufi kofa, Nadeeyah ta bi sa da kallo har ya fice daga parlon, Mumy ta saki salati tace "Wallahi duka duka ko minti goma fa basu yi da shigowa gidan ba, har nake tambayarsa tana ina da naga ita bata shigo parlon ba yace tana waje tana waya da yayanta, ina yar mutane ta shiga ni Safeenah" Mami dai ta kasa cewa komai don hankalinta ya tashi ita ma, where are they going to start from, kasa ci gaba da tsayuwa tayi ta nemi kujera ta zauna tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta.... Ko barin Abuja Nihad basu yi ba bacci ya dauketa a motar, Khalil bai jin ya taɓa shiga tashin hankalin da ya shiga a wannan lokacin, ko abinda Abbansa yayi masa bai daga masa hankali irin wannan ba, ganin abun yake kamar a mafarki fa, ya ma rasa wani tunanin zai yi, sai da yaga karfe goma yayi tashin hankalinsa ya fara fitowa sarari, tun takwas su Mami suka koma gida don barinsu ma yayi a gidan yayi wucewarsa, amma saboda yanda hankalin Mum din Nadeeyah ya tashi haka ta sake bin su gidan tare da Nadeeyah, Duk suna zaune parlorn Mami wajen karfe goma da yan mintuna khalil ya shigo parlon ta dalilin kiran da Mami tayi masa, Mami tayi karfin halin cewa "Nace ka kira gidansu ka ki, nace ka kira yayanta ka ki, to wai ya zan yi da kai, in ma baxa ka kira ba ni ka bani numbersu mana, wannan wani irin tashin hankali ne" Khalil that was trying all possible means to be calm yace "In kirasu ince masu me Mami? I should call and tell them I can't find their daughter cikin daren nan? In kirasu ince masu an kasa rike yar su a gidanmu saboda kanwar Abbana tace baxata zauna ba kuma Mamina bata da abinda xata iya yi game da hakan? Mami ni na zata akan yarinyar nan sai inda karfinki ya kare, i thought zaki yi repaying good deeds din da iyayenta suka min ta hanyar riketa just like su Mimi, ina ce you will always be there for her, if not for her family i would have been depressed by now, right in front of u Abbana sent me away from his house and u couldn't do anything about it, kina gani na bar gidan nan baki iya yin komai a kai ba, naje inda suka rikeni ba tare da sun san ni ba har suka damka min amanar dukiyarsu amma ta haka za muyi repaying dinsu mu kasa rike masu tasu er?" Mami dai kallonsa kawai take ta rasa abinda xata ce amma duk jikinta yayi sanyi, juyawa yayi ya fice daga parlon Nadeeyah ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, Hajiya Safeenah ta nemi kujera ta zauna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Wajen karfe biyu da rabi na dare Nihad suka shigo garin Kano, tayi bacci har ta gode Allah a hanya, mamaki ya cikata ganin adaidaita har sannan a tasha, tana kallon wanda ke tambayarta inda xata tayi shiru, tana tunanin ko dai kawai taje hotel ta kwana tunda tana da kudi kuma tasan prices din hotels na Kano, nan ta gaya masa hotel dai dai kudinta ya tafi da ita kuwa, tana sauka ta basa kudinsa ta shiga ciki, ta biya kudin daki aka bata makulli ta wuce zuwa dakin, wanka ta fara yi a bandaki sannan ta dauro alwala tayi magrib da isha ta kwanta, amma ta kasa bacci sai juye juye kawai take, babu wanda ke ranta kuma a lokacin sai Nadeeyah, she just hate her with passion, bata son ganinta kwata kwata, da tasan gidansu zasu je da tun daga gidansu Khalil ta gudu don ko haduwa da ita bata so har cikin ranta.... Karfe takwas saura na safe Nihad ta tashi daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, ta fita waje zuwa supermarket dake kusa da hotel din ta siyo brush da maclean ta koma ciki, kafin karfe tara har ta gama shiryawa ta fito ta tare adaidaita yana tambayarta inda xata tayi shiru, don sai a sannan gabanta ya fara faduwa don bata san me xata je ta tarar a gida ba, kilan ma Abba ya koreta idan taje, amma a haka ta dake ta gaya masa inda xata sannan ta shiga adaidaitan a sanyaye, ya kama hanyar gidansu, tunda suka dau hanya gabanta bai daina faduwa ba, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso gidan, at first kasa sauka tayi daga cikin adaidaitan ganin ya juya yana kallonta, tayi karfin halin sauka ta basa kudinsa ta nufi gate tana tafiya a hankali, she is so afraid, daurewa kawai take, bude gate din tayi taga Aminu zaune bakin gate da er radio a hannunsa, yana ganinta ya zare ido ya mike da sauri yace "Hajiya" Ta ɗan yi murmushi tace "Aminu" Bakin Aminu har kunne ya dinga mata sannu da zuwa, sai kuma ya nufi waje da gudu duk zatonsa tare take da Khalil, Nihad dai ta ci gaba da tafiya gabanta na faduwa ganin motar Abbanta a parking space, taga motar ya Usman ma alamar yana gidan, har ta isa balcony dinsu ta kasa daga kafarta da kyau, tsoro ne fal zuciyarta, ta kusa minti daya a tsaye kafin ta murda kofar a hankali ta shiga ciki tana kallon parlon, Umma ta fito kitchen kenan rike da breakfast din da ta hada ma Nihal tayi sororo bakin kofa tana zaro ido tace "Wa zan gani kamar 'ya ta Nihad?" tun da Nihad ta mata kallo daya ta dauke kai ta nufi bangaren Mumy tana tafiya a hankali, Umma ta buda baki with shock ganin abinda tayi mata ta bi ta da kallon mamaki, tuni Nihad ta bude kofar Parlon Mumy a hankali ta shiga, Mumy ta fito dakinta kenan tayi ido hudu da Nihad, still tayi bakin kofar dakin tana kallonta with surprise, Nihad ta tafi da gudu ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mumy dai ta kasa motsi, can tayi karfin halin dago kanta tace "Daga ina?" Nihad na Murmushi tace "Gida Mumy" Mumy tace "Ke da wa??" Nihad tace "Ajiyeni yayi yaje ya dawo" Bude kofar Parlon aka yi duk suka daga kai, Umma ta shigo, Nihad na ganinta ta shige dakin Mumy ta kulle kofar, Umma tayi kasake a inda take tsaye, Can tayi karfin halin cewa "Ko ba Nihad bace?" Mumy ta kirkiri murmushi tace "Ehh wallahi, yanzun nan ta shigo na ganta nima" Umma tace "Allah sarki, to sannunta da zuwa, ina jin ta gaji ne" Daga haka ta juya ta fita daga parlon, Mumy ta juya ta koma dakinta da sauri tana kallon Nihad tace "Me yasa kika yi mata haka ta zo ganinki Nihad? Why did u leave the parlor" Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mumy tace "Why didn't u greet her?" A hankali Nihad tace "I need rest, and beside ke na zo gani" Mumy dai ta kasa cewa komai ta dinga kallonta, Nihad tace "Mumy ina jin yunwa" A hankali Mumy ta juya ta fita daga dakin don kawo mata breakfast, Mumy na fita ko minti uku ba ayi ba Nihal ta shigo dakin....

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788

No comments

Powered by Blogger.