nihaad 39

 


Bayan Azahar Aunty Maryam ta sakko downstairs tana kallon mai aikinta dake parlor tace "Kin kai ma bakuwar can abinci kuwa?" Mai aikin ta tashi da sauri tace "Wallahi na manta Hajiya" Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta tace "Amma ai baki mance naki cikin ba" Da sauri mai aikin tayi hanyar kitchen, Aunty Maryam ta nufi guess room, bude kofar dakin tayi taga Nihad zaune saman darduma, Aunty Maryam ta shiga dakin, Nihad ta daga kai tana kallonta, Aunty Maryam tace "Kiyi hakuri ashe wancan gantalalliyar bata kawo maki abinci ba ni ina can sama ban sani ba" Nihad dai tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kika ki zama parlon kiyi kallo?" A hankali Nihad tace "Ba komai" Aunty Maryam bata kuma cewa komai ba, Sai ga Murja ta shigo da abinci dakin ta ajiye ma Nihad, Aunty Maryam na kallonta tace "Ki karo lemun" Da sauri Nihad tace "Aa ya isa Aunty" Aunty Maryam tace "Toh zuba abincin ki ci" Daga haka ta juya ta fita daga dakin, All through Khalil na compound wajen shan iska tare da Nadeeyah, kana ganinsu kasan they really missed each other, abincin ma waje aka kai masu suka ci tare, bayan Nadeeyah ta zuba masa drink din kwalin gabansa yana kallonta yace "Thank you" Tayi murmushi tace "Continue... ina jin ka" Ya ɗan buda ido yace "Me xan ce kuma,?" Tace "Ba labarin stay dinka a kano kake bani ba, ai baka gama ba" Yayi murmushi yana shafa kansa yace "Shikenan, all the household are very nyc, i think that's the most important of all" Tace "To ita wannan yarinyar da na ganku tare, yar gidan ce?" Yayi shiru, sai kuma yace "Nihal!! Of course yarinyar mai gidan ce..." Nadeeyah tace "Allah sarki, wani school take?" Yace "Ahmadu Bello" Nadeeyah tace "Ohk, but kasan har yau yan gidanku basu san inda kake ba all those while, a lot of time Farhana da Sajida suna yawan tambayata about u, irin dai suna son su san ko i know about your whereabout" Yayi murmushi bai ce komai ba, tayi sipping drink din gabanta tace "Kasan everything happens for a reason, may be don kaje ku hadu da yan gidan ku kulla zumunci shi sa Allah ya kaddara zaka je kano har kuma ka je gidansu, kaga ai baxa ka manta halaccinsu ba" Ya gyada kai yace "Haka ne" Tace "And you mean har yanzu basu san kai waye ba har bayan da ka dawo Abuja?" Ya girgiza kai yace "Basu sani ba" Tayi murmushi tace "Za su yi mamaki kuwa idan suka san kai wanene, but menene ya ja ra'ayinka har ka je gidan nasu ka zauna bayan baka ta6a saninsu ba sannan ba rasa wajen da zaka zauna a kano kayi ba, infact ko hayar nawa ne nasan xaka iya affording, u can even decide to stay in the hotel don duk da ba salary kake samu ba sannan babu wani source of income don duk Abba ya toshe hanyar but still nasan u neva ran out of cash all that period, Mami na tura maka, Aunty Maryam, Aunty Hamida even though bata kasar...." Murmushi yayi yana kallonta murya can kasa yace "And even you yourself" Ta hararesa tace "A'a ni ka cireni a lissafi don anything mine is urs" Ta tallabi chin dinta ta ci gaba tace "So how did u even know about them? And me yasa kayi deciding zaman gidan?" Yayi shiru yana kallonta kamar baxai ce komai, can kuma yace "I will tell u some other time Nadeeyah" Tace "Why?" Yace "I don't want to talk about it now" Ta langwabar da kai a hankali tace "Amma ka ta6a saninsu ne?" Ya girgiza kai yace "Nace xan baki labarin some other time" Tace "Ohk, but ya kamata ko Mami ka hada da yan gidan su gaisa a waya, su ma za su san kayi appreciating dinsu" Yace "I will do that dear" a hankali tace "But why did u keep on telling me kana USA?" Yace "Saboda nasan xa ki iya cewa xaki zo kano saboda ni, shi yasa ma ranan da muka hadu nace maki in few hours time flight dina xai tashi, don kar ki saka ran za mu hadu" Murmushi kawai Nadeeyah tayi tana kallonsa... sai kusan la'asar suka shiga cikin gida, Nadeeyah ta haura sama shi kuma ya zauna parlor, ko minti biyar bai yi zaune parlon ba Nihad ta fito rike da warmers na abinci da mai aikin Aunty Maryam ta kai mata, tun da suka hada ido sau daya bata sake kallon direction dinsa ba, sai dai kuma bata san hanyar kitchen ba don tayi zaton zata hadu da mai aikin ne a parlor, juyawa tayi ta koma inda ta fito, sai ga Mami ta sauko downstairs tare da Mum din Nadeeyah da Aunty Maryam, Mami tace "Khalil xaka ajiyesu gida daga can mu tafi gida, xata kira driver nace ba sai ta kirasa ba mu ma yanzu za mu tafi gwara mu tafi gaba daya" Khalil ya mike yace "Ohk" Mami ta nufi Aunty Maryam dake answering call tayi kasa da murya tace "Kai ni mu yi sallama da ita, ina ga ai daga nan zata wuce in ta amshi abinda xata amsa" Aunty Maryam ta nufi bangaren da Nihad take Mami na biye da ita a baya, Aunty Maryam ta bude kofar, kwance suka ganta a kasa, Aunty Maryam ta katse wayar da take tace "Me yasa xaki kwanta a kasa ga gado?" Nihad ta mike zaune bata ce komai ba, Mami tace "Naga bata da sabo ne da wuri" Mami na Murmushi tace "Ya sunanki?" Nihad bata iya ta dago kanta ba a hankali tace "Fatima amma ana kirana Nihad"  Aunty Maryam ta kalli Mami, Mami tace "To maa sha Allah Nihad, yaushe xa a baki admission letter din?" Sai a sannan Nihad ta daga kai tana kallon Mami, Mami tace "Yaushe suka ce?" Cikin sanyin murya tace "Nima ban sani ba" Mami tace "Toh jiya me suka ce maki a makarantar" Ta sauke idonta kasa tace "Shi ne dai suka gaya ma ba ni ba" Mami ta kalli Aunty Maryam, Sai kuma tace "Toh, ya dai ce kafin sati za ki samu, idan na zo nan din kafin ki tafi to, idan kuma ban zo ba xan bada sako a kawo maki kin ji? Sannan ki gaida su mamanki da kyau" Nihad ta gyada mata kai kawai, Mami tace "Toh sai anjima" Cikin sanyin murya Nihad tace "Nagode" Tana fadin haka ta fara cire dankunnen dake kunnenta tace "Ga dankunnen" Mami tace "Aa, na baki ne ki dinga sa wa Nihad" Nihad ta mayar tace "Toh Nagode, Allah ya saka da Alkhairi" Mami na Murmushi tace "Ameen" Daga haka tace "Mun tafi" Ta juya ta fita dakin, Aunty Maryam ta bi bayanta ta kullo kofar dakin. Khalil kadai ke jiransu a parlon, Nadeeyah da Mum dinta kuwa sun fita compound, Mami na kallon Khalil tace "Ina suke?" Yace "They are outside" tace "Toh mu je" Ya kalli Aunty Maryam yace "Na sa wayata caji idan na ajiyesu xan dawo in dauka anjima Aunty" Mami tace "Ji wani wahalar da kai, ka dau wayar mana idan mun je gida ka sa a cajin" Aunty Maryam tayi dariya tace "Baki ga yanda na saki baki ina kallonsa ba" Ya ɗan yi murmushi yana sosa kai yace "Haka ne" Gun wayar ya nufa, Mami ta juya ta fita daga parlon, ya juya ya kalli Aunty Maryam yace "Kawai bari in bar shi Aunty, ai bamu gama hiran ba dama" Aunty Maryam tace "Toh je ka ajiyesu ka dawo, akwai abinda kake so ayi maka kafin ka dawo" Yace "Aa coffee kawai xan sha idan na dawo" Tace "Toh sai ka dawo son" Daga haka ya fita parlon da sauri zuwa parking space. Wajen karfe biyar da wani abu Nihad ta fito parlor, Aunty Maryam dake zaune parlon tana rungume da autanta Mus'ab ya dawo makaranta ta kalli Nihad tace "Kin fito" Nihad na wasa da fingers dinta tace "Eh, akwai aikin da xa ayi Aunty?" Aunty Maryam tayi murmushi tace "Aa Nihad, Murja ta ma kusa gama girkin ina ji yanzu, karaso ki zauna" Nihad ta karaso cikin parlon ta zauna a kasa, Aunty Maryam tace "Hau saman kujera mana" Nihad ta girgiza kai tace "Aa nan ya isa" Mus'ab dake kallonta yace "Ummi is she our visitor?" Aunty Maryam tace "Yes dear, sauka kasa ka gaisheta" Ya sauka daga jikin mamarsa yace "Good evening" Nihad na kallonsa tayi murmushi don mate din Fadil dinsu ne tace "How are you?" Ya koma jikin mamarsa yace "Fine" Har Bayan magrib Nihad na parlon tare da Aunty Maryam, aka bude kofa Khalil ya shigo da sallama, Aunty Maryam ta amsa masa tana kallonsa tace "Sai yanzu?" Ya karaso cikin parlon ya ajiye jakar hannunsa yace "Eh Aunty, good evening" Tace "Evening welcome, wannan jakar fa? Ko na ta ne?" Ya nufi wayarsa yace "Eh nata ne" Ya dauko wayar ya dawo ya zauna, Aunty Maryam na kallon Nihad tace "Dauka ki kai can dakin" Tashi Nihad tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta dau jakar ta wuce ciki, Aunty Maryam tana kallonsa tace "A kawo maka abincin ko coffeen dai" Yace "Na sha a gida Aunty" Tace "Ohk, Mami tace xaka yi tafiya, yaushe ne tafiyar?" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Nan dai da kwana biyu idan na gama shirye shirye" Tace "Toh Allah ya kai mu" Wayarsa yake dubawa ya ga missed calls din Farooq, ko jiya ya kirasa, Khalil yayi dialing numbersa ya kai kunne, Farooq na dagawa suka gaisa, Farooq yace "Har yanzu baka turo ba Khalil" Khalil ya shafa kansa yace "Nace kar ka damu Yallabai, da da bukatar hakan xan tura maka" Farooq yace "Ehh naji, amma kawai ka turo min" Murmushi Khalil yayi yace "Toh shkkn, Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Farooq yace "Fatan dai kuna lafiya?" Khalil yace "Alhmdlh" Farooq yace "Zariyan a wani anguwa ku ke, ina ga in shigo ko jibi weekend" Khalil yace "Ohk zan tambaya" Khalil yace "Ohk, tana kusa?" Khalil yace "Bari in bata" Mikewa yayi yana kallon Aunty Maryam dake ta kallonsa ya mata alamar yana zuwa sannan ya tafi inda Nihad take, saman gado ya sameta kwance, ya karasa ya mika mata wayar, ta mike zaune tana kallon Iphone da yake mika mata, ta kai hannu ta amsa tana kallon screen din taga number ya farooq don a haddace yake a kanta, ta kai kunne cikin sanyin murya tace "Ya farooq" Daga daya bangaren yace "Na'am Lil sis ya kike" Lkci daya har hawaye ya kawo idonta tana goge idonta cikin rawar murya tace "Lafiya lau" Yayi shiru, sai kuma yayi kasa da murya yace "Yanzu kukan me kike? Ko akwai damuwa ne?" Ta kasa ce masa komai, yace "Nihad" Tana goge idonta tace "Na'am" Shi dai khalil na tsaye yana kallonta, Ya Farooq yace "Bana son wannan kukan naki Nihad, shi yasa ko na kirasa bana cewa ya baki, kukan nan yana damuna idan kina yi" A hankali tace "Toh na daina yaya" Yace "Good girl, kiyi hakuri in sha Allah komai xai wuce, komai yayi farko xai yi karshe in sha Allah, don haka ke dai ki zama me biyayya ku zauna lafiya da mijinki, sannan ki rike Ibada sosai, may Allah guide and protect you for us" Cikin sanyin murya Nihad tace "Ameen yaya" Yace "Har yanzu baki da atm card ko?" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Hello" Tace "Ehh bani da shi" Yace "Toh shikenan, in sha Allah on Saturday xan zo, na gaya masa ma" Nihad tace "Ina zaka zo yaya?" Yace "Wajenku idan Allah ya kai mu, be a good girl always, Allah ya maki albarka" Tace "Ameen yaya" yace "Give him the phone" Mika masa wayar tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai kallonta kawai yake, bai kuma amshi wayar ba, ita kuma taki yarda ta kallesa, ganin still ya ki amsar wayar ta ajiye masa nan gefen gado ta koma tayi kwanciyarta ta juya masa baya, ya shafa beard dinsa, sai kuma ya dauki wayar ya juya ya fita ya kulle mata kofa. Wajen karfe tara da rabi Aunty Maryam ta bude kofar dakin da Nihad ke ciki, zaune ta sameta saman darduma ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam tace "Sai yanzu kika yi isha'in? Nihad ta girgiza kai tace "Aa tun daxu nayi" Aunty Maryam tace "Toh baxa ki kara abinci ba ko?" Nihad ta gyada mata kai tace "Ehh Aunty nagode" Aunty Maryam tace "Toh shkkn, tunda ga kayanki ya kawo ki yi wanka sai ki kwanta, ga zani kiyi amfani da shi don towel din bandakin ba a wanke yake ba" Nihad ta nufeta ta amshi zanin da take mika mata tace "Nagode" Aunty Maryam tace "Ni xan tafi daki, Allah ya tashe mu lafiya" Nihad tace "Toh sai da safe" Juyawa Aunty Maryam tayi ta rufo mata kofar ta bar wajen, Nihad ta koma gefen gadon ta ajiye zanin, sannan ta cire Hijab din da tayi sallah ta linke ta ajiye don a dakin ta gani. Ta kalli jakar da ta shigo da shi daxu dakin, can ta nufi gun jakar ta durkusa ta bude zip din a hankali tana kallon ciki, Hijab da aka yi packaging a leda ta ciro har guda hudu, sai kuma Abaya kala biyar da undies masu yawa, sai kayan shafe shafe with perfumes kala biyar, da nighties su ma biyar, kulle jakar tayi ta mike ta bar wajen. Duk da Nihad felt secured a gidan Aunty Maryam amma wannan daren ma ta nemi bacci ta rasa, for almost 4 days now bata bacci da daddare ko tayi a firgice zata farka bayan wasu mintuna, or is she been traumatic, bata taɓa jin tana kewar Mahaifiyarta yanda take ji yanzu ba, maganganunta na karshe ya kasa fita daga ranta da zuciyarta, she could vividly remember every single word shi told her a rananta na karshe a gidansu, and she wish she could hear more of such from her, Magana da tayi da Ya farooq daxu shi ma yayi contributing a rest of mind dinta but she still couldn't sleep, gaba daya idanuwanta sun kekyashe daga jin bacci, daga karshe ta tashi a hankali ta kumna switch din dakin ta ga karfe biyun dare, cike da karfin hali ta nufi bandaki tana jan kafa, har kusan karfe uku da rabi Nihad bata yi bacci ba tayi sallan har taji bata da sauran strength kawai ta jinginar da kanta da gado tana daga zaune kan darduman, sai a sannan taji hawaye na sauka idonta, cikin rawar murya tace "Ya Allah duk wanda yayi min wannan abun ka tona asirinsa cikin gaggawa, come to my aid ya Allah, Allah ka kawo min mafita alfarman ma'aiki" Kuka take sosai tana roƙon Allah, wanda tun faruwan abun yau ne ta kwantar da hankali take kai kukanta wajen Allah cikin nutsuwa, ko jin sanda aka bude kofar dakin bata yi, cause she is really hurt, sae yanxu take ganin she needs to know who is this that betrayed her, she needs to know who did this to her da ya tarwatse farin cikinta ya rabata da Abbanta ya bata mata suna yayi tarnishing image dinta a idon duniya, Aunty Maryam dai sai kallonta take tana tsaye bakin kofa, dama ka'idarta ce duk in Allah ya farkar da ita cikin dare ko dab da asuba ko da baxata yi sallah ba sai ta fito ta dudduba condition din yaranta idan suna gidan, har dakin mai aikinta takan bude ta dubata, in ma da wani bako gidan in dai ba babba bane xata bude dakin ta duba, sai in Allah bai farkar da ita ba wanda hakan ma ya zame mata jiki dole ko yaya sai ta tashi saboda ta maida shi daily routine dinta a gidan.... (Yana da kyau iyaye mata su sa ido su yi kokarin dinga yin hakan ko da ba kullum ba barin idan kana da yara yan mata teenagers, kai har ma da yara mazan, its very very important, i have this aunty that kullum da daddare sai ta leko ku taga halin da ku ke ciki a daki, ya ma riga ya zame mata jiki, da Mumyn Nihad na kokarin yi ma Nihad haka ko da ba a bangarenta take ba da abubuwa da yawa basu faru ba kamar zuwa night parties da take, wasu yan matan sai su kai har karfe daya ana video call da saurayi kasa kasa, ko chatting din banza, wasu kuma a wannan lokacin xa su samu daman shiga internet su yi kallace kallacen banxa, wasu masturbation da dai sauransu, duk kina can kin shanya baki hangangan kina bacci, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya raba mu da mugun ji da mugun gani) Duk abubuwan da Nihad ke fada Aunty Maryam na jin ta don daga karshe ma kulle kofar dakin tayi a hankali, wanda hakan ne yayi distracting Nihad ta juya da sauri, sai da gabanta ya fadi ganinta tsaye bakin kofar, ta hau goge idonta da sauri, Aunty Maryam ta karaso cikin dakin tana kallonta ta zauna gefen gado tayi kasa da murya tace "It's okay dear, tunda ki ka kai kukanki wajen Allah kika hana kanki bacci a wannan lokacin, to in sha Allah addu'arki baxata tashi a banza ba, ta yanda baki yi zato ba Allah xai maki sakayya ya kuma tona asirin koma wanene yayi maki wannan abun" Hawaye ya dinga sauka idon Nihad ta kasa ce ma Aunty Maryam komai, Aunty Maryam da taji tausayinta ainun tace "Kiyi hakuri ki daina wannan kukan, tunda kika ambaci Allah ai an wuce wajen kuma, amma me yasa kika yarda da kawaye har zaki zauna cikinsu half naked?" Nihad ta girgiza kai cikin rawan murya tace "Wallahi Aunty ni ban taɓa zama ko a gidanmu haka ba, sannan ni ba a hostel nake ba kawai zuwa nake, lokacin da xa mu fara exams din first semester level 3 ne na koma hostel kuma ni ko da zani bana zama cikinsu wallahi" Aunty Maryam na kallonta da mamaki tace "Toh a ina aka dau video din?" Nihad ta buda hannu tace "Nima wallahi ban sani ba, yanda kowa ya gansa haka na gansa" Aunty Maryam ta dinga kallonta dumbfounded, can tace "Ban gane baki san a inda aka maki video din ba" Nihad ta fashe da kuka tace "Wallahi da gaske Aunty, ni ban san ta yaya aka yi hakan ba, kuma ban ma san ko wani waje ne ba" Aunty Maryam ta kasa cewa komai don mamaki, can dai tace "Toh kenan ba ke bace a video din" Nihad na goge idonta tace "Ni ce Aunty, amma ban san ta yaya ba, because under wears dina ne a jikina" Sosai wannan lamarin ya rikitar da Aunty Maryam, can dai ta sake cewa "Kuma ba a hostel din bane?" Nihad tace "Ba nan bane wllh" Aunty Maryam tace "Ba kuma gidanku bane?" Nihad ta girgiza kai tace "Ba gidanmu bane" Aunty Maryam tace "Ikon Allah, kin tabbata bayan gida baki zuwa wani wajen ko da kawaye haka?" Shiru Nihad tayi, Aunty Maryam tace "Kin yi shiru" Nihad ta hadiye abu da kyar amma tana tsoron ce ma Aunty Maryam ai sun kan je hotel da guess lodge da friends dinta, Aunty Maryam tace "Kina zuwa kenan?" Cikin sanyin murya tace "Ina bin kawayena duk inda xa su wani lokacin" Aunty Maryam tace "Toh su suka maki, ki gaya min tsakaninki da Allah baki shan komai?" Nihad ta dago da sauri tana kallon Aunty Maryam tace "Aunty kamar me" Aunty Maryam tace "Kayan maye, gaya min tsakaninki da Allah, kar ki min karya don kina min ma zan gwada ki kuma zan gane, don ni Nurse ce" Nihad na girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Wallahi Aunty bana shan komai kin ji har na rantse, idan ina shan wani abu Allah shine shaidata, ki gwada ki ga Aunty" Aunty Maryam tace "Toh kawayen naki fa?" Nan Nihad ta fara lissafo ma Aunty Maryam abubuwan da su Husnah suke sha Innocently, haka Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta cause taga babu alamar karya a tare da ita, iya gaskiyarta kawai take fada, can Aunty Maryam tace "Ikon Allah, to kuma a gida an san kina bin wa ennan kawayen har ma ki bi su duk inda xa su?" Nihad ta girgiza kai tace "Stepmom dita ce kawai ta sani, ta ma san gaba dayansu" Buda baki Aunty Maryam tayi, sai kuma tace "Kuma bata hanaki alaqa da su ba?" Nihad tace "Aa, tace min in rikesu baxan samu kamarsu ba don suna sona sosai, kuma tana kare ni yanda yan sauran yan gidan baxa su gane ba, idan na dawo da daddare ita take bude min kofan parlon mu idan an kulle" Aunty Maryam was really shock jin abinda Nihad tace, taji zufa na keto mata, tace "Mamarki fa?" Nihad ta girgiza kai a hankali tace "Bata sani ba ai, dama a bangaren stepmom dina nake, so akwai distance tsakanin part din stepmom din tawa da na Mum dina...." Aunty Maryam tace "Wa ya ce ki koma part din stepmom din taki?" Nihad tace "Aa wai tun ina karama ta dawo da ni wajenta shi ne har na girma" Aunty Maryam tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to ina jin ki, idan ta bude maki kofar da daddare sai tace maki me??" Nihad tace "Kawai cewa xata yi inyi sauri in wuce kar a gan ni" Aunty Maryam bata san sanda hawaye ya kawo idonta ba, nan ta kara tsorata da lamarin kishiya, bata san sanda ta dafe kanta da yayi mata nauyi ba, can ta dago da kyar tace "Bata da yara ne?" Nihad ta girgiza kai a hankali tace "Tana da yarinya mate dita, her name is Nihal, ita kuma tana side din Mumy na, sannan akwai Amina da Aunty Kamila that is married" Aunty Maryam tace "Kuma duk su ma yaran nata dake gidan suna fita su kai dare ta bude masu kofa?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Aa babu inda suke zuwa su, ba ma su da friends" Aunty Maryam tace "Nihad" Nihad ta daga kai ta kalleta, Aunty Maryam tace "Ku nawa ne wajen mamanki?" Nihad tace "Mu uku ne, ni ce first born" Aunty Maryam was so heartbroken, tace "Ita kuma fa?" Nihad tace "Babban yayanmu ya Farooq sai ya Usman, sai Aunty Kamila, Nihal da Amina" Aunty Maryam na girgiza kai tace "Yanzu a tunaninki duk gidan wa yafi sonki? Yake maki duk abinda kike so?" Nihad ta sunkuyar da kai a hankali tace "Umma" Aunty Maryam tace "Wacece Umma?" Nihad tace "My Stepmom" cike da takaici Aunty Maryam na girgiza kai tace "Ta cuci rayuwarki, ta cuceki, ta cuci mahaifiyarki, ita kuma salon nata kishin kenan?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, da wannan abun da ta maki da gwara ta fuskanci mahaifiyarki su xuba kishin yanda ya kamata, bata maki adalci ba, kuma ko tantama babu da sa hannun wannan matar a video din naki, Nihad wani masoyinka ne xai dinga supporting dinka kana bad things, kana abubuwan da basu dace ba? Wani masoyinka ne xai xuba maka ido ka fita ka kai har dare shi bai maka fada ba kuma ya kareka ta yanda wasu baxa su sani ba balle su maka fada? Wani masoyinka ne xai ce ka rike yan iska masu shaye shaye a matsayin kawaye har yana ikirarin baxa ka samu kamar su ba, sannan ya daure maka kugu ka dinga bin su duk inda xa su? Nihad me yasa ita nata yaran basu da kawaye sannan basa fitan dare?" Shiru Nihad tayi tana kallon Aunty Maryam ko kiftawa babu, Aunty Maryam tace "Ba shiru xa kiyi min ba bude baki ki bani amsa yanzun nan?" Tunda Nihad take bata ta6a zaunawa tayi wannan tunanin ba balle har ta gane komai tayi reasoning a kai, ita dai Aunty Jamila kawai rabata take da Umma ta karfi da yaji amma bata ta6a zaunawa ta zayyano mata abubuwan nan da Aunty Maryam ta zayyano mata ba yanzu, to ai bata ma san abinda take yi da sanin Umman ba balle har ta zayyano mata wannan abubuwan tunda komanta a boye take yi, Umma ce kawai ta sani... Aunty Maryam bata yi interrupting Nihad a duniyar tunanin da ta fada ba, kana kallon fuskarta zaka fahimci she is slowly trying to comprehend duk wani abinda Aunty Maryam ta fada ne, babu kuma abinda ya fado ran Nihad sai karyan da suka yi ma yan gida wai zata bi Aunty Kamila kebbi alhalin hostel xata koma da zama, Umma da Aunty Kamilar ne kadai suka san gaskiyar maganar, kuma har ta gama zamanta hostel din for more than 3 months Umma bata ta6a zuwa inda take ba, har ita Aunty Kamilan, alhalin idan mutum na hostel kuma iyayensa na garin ko bayan sati uku ne su kan kai masa ziyara.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and ur evidence via07087865788...

No comments

Powered by Blogger.