nihaad 26
Kunna wutan dakin Khalil yayi ya koma gefen gadon ya zauna fuskarsa daure yace "Ohk, dauki torchlight din ki fita" Har sannan gabanta bai daina faduwa ba, a hankali ta dawo edge din gadon tana satan kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Dauki ki fita nace" Ta sauke ƙafafuwanta kasa a hankali tana kallon karamar wayarsa da ta hango gefen pillow, Ya jefa mata wani mugun kallo yace "Ko bayan shi da wani abun da kike so ne?" Ta ɗan turo baki tace "Ga can torchlight din da xan ara" Ya kalli inda take nuna masa, sai kuma yace "Ohk" dauko wayar tasa yayi ya mika mata yana kallonta, a hankali ta kai hannu xata amsa, da karfi ya buge mata hannu da wayar, da sauri ta janye hannunta ta bude baki tana kallonsa tana yarfe hannun, ya mike ya dau shirt dinsa ya saka sannan ya nufi kofa ya bude mata da kyau, fuska daure yace "Zo ki fita" Ta fashe da kuka tace "Shine har sai ka kwala min waya a hannuna? Sai kace kai baka shigo min daki idan ina bacci" Cikin kakkausar murya yace "Zo ki fita nace" ganin babu alamar wasa tattare da shi ta mike ta nufi kofar hawaye cike idonta, tana fita ta juyo ta kallesa tace "Ban yafe buge min hannu da kayi da shegen wayarka ba, don ma ka samu xa a ari torchlight din shegen wayar" Yi yayi kamar xai bi ta, ta ruga ta shige dakinta ta kulle kofar da sauri tana maida numfashi. Washegari da yamma bayan Khalil ya gama shiryawa yanda xai je ya sanar ma Nihad ta shirya xa su yi tafiya ne babban aiki a wajensa, tun safe ya fice gidan don kawai ya daina ganinta, ko awa daya bai yi da dawowa ba kuma bai ji motsinta ba bai kuma duba dakin nata ba, daga karshe kawai yayi dialing number Nihal tana dagawa ta gaishesa ya amsa yace "Ya makaranta?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin dawo ne?" Tace "Aa ya farooq yace min yana hanya" Khalil yace "Toh Allah ya kawo ku lafiya" Tace "Ameen" Shafa kansa yayi yace "Dama so nake ki sanar ma er uwarki ta shirya kayanta kala uku xa mu je can gida, kawai haka xa ki ce mata" A hankali Nihal tace "Baxa ka iya gaya mata ba kai kenan?" A takaice yace "Ehh" Tace "Toh Shkkn, ka bata wayar" yace "Zan kai mata yanzu" Nihal tace "Ohk" mikewa yayi ya tafi dakin Nihad ya bude kofar dakin, tana tsaye jikin window abun duniya ya tarar mata, har ta gaji da kuka, tun da garin Allah ya waye ruwa kawai take ta sha don ta gaji da cin indomie gashi babu kayan miya a gidan, yunwa take ji sosai, jin ya bude mata kofa ta juya a fusace tace "Malam ka daina shigo min daki kanka tsaye kamar wata matarka, idan ma wani abun ne baxa ka kwankwasa ka jira in fito ba?? Balle ma ni bana son kana min magana a gidan nan har abada" Kallonta kawai yake, ta murguda baki ta ci gaba da kallon tsuntsayen da take kallo ta window, khalil ya sa handsfree a wayar hannunsa yana daga inda yake tsaye yace "Gashi ki gaya mata" Nihal tace "Hello Nihad" Nihad ta wani tamke fuska tace "Menene??" Nihal tace "Abba yace ki shirya kayanki xa ku je can gidan" Nihad ta buda ido sosai tace "Don Allah da gaske?" Nihal tace "Ehh" Wani farin ciki ne ya rufeta, cike da murna tace "Ai kayana a hade suke ban ciro su a akwatin ba" Khalil bai bari Nihal tace komai ba ya katse wayar ya juya ya fita, kan kace me Nihad ta gama rurrufe akwatunanta ta ja su ta kai parlor gaba daya, ji take kamar mafarki wai xata koma gida, she sooo happy, da ido Khalil ya dinga bin ta, haka ta ja akwatunan duk da nauyinsu har gun mota sannan ta koma ta dauko handbag dinta, xata fita khalil dake ta bin ta da kallo yace "Duk wa enan kayan ina xa ki kai su?" Tayi masa wani shegen kallo tace "Ohk da so kayi in bar maka wasu ka dauka kaje ka siyar ka samu na xubawa a aljihu? To baxa a bari ba" tana gama fadin haka ta fice ta tafi jikin mota tana jiransa, bayan few minutes sai ga shi ya fito, cike da gadara tace "Bude min booth Malam" Ba musu ya bude mata booth din, ta daddage ta shigar da akwatunanta booth da duk karfin da Allah ya bata, back seat ta bude ta shiga ta zauna farin ciki fal ranta, ta lumshe ido tare da sauke wani ajiyar xuciya, at last.... Ganin ya ki tada motar ta ki ce masa komai, don ita kam baxata biyesa ba tunda dai ta samu xata koma gida, bayan few minutes ya sauka motar yaje ya bude gate, lumshe ido Nihad tayi bayan ya ja motar sun bar compound din, ya sauka ya kulle gidan sannan ya dawo cikin motar, Ta madubi yake ta kallonta kai kana ganinta kasan she is over happy, tun Nihad na tunanin traffic yake kaucewa ganin hanyar da suke ta bi har dai taga sun dau hanyar da baxae ta6a kai ka gidansu ba, ta dake tace "Malam mance hanyar gidan namu kayi ne ko kuma Shaye shaye ka fara? Ba ga can hanyar da xaka bi ba" Banza yayi mata, a mugun fusace tace "Tunda kai ba kurma bane nasan kana ji na, ka gaya min ta ina hanyar nan da muke bi xai kai mu gida??" Nan ma yaki tanka ta, mamaki ne ya cika Nihad ta dinga bin hanyar da kallo, to ina xai kai ta, bata kuma ce masa komai ba tana ta kallon ikon Allah, bayan tafiyar kusan minti arba'in taga sun shigo wani karamin gari da xa a iya kiransa da kauye, she was more than shock, wanda hakan yasa ta kasa ce masa komai, sae kallonsa take baki bude, a wani gida da aka xagaye da katangar kasa yayi parking bayan sun lula can cikin garin, ya kashe motar, sannan ya bude ya sauka, duk motar tayi butu butu da jan kasa, ga yara da ke ta bin motar tun shigowarsu karamin garin, har Khalil yayi parking, yaran duk suka kewaye motar suna murnan ganin mota, Haka Nihad ta dinga kallon inda suke with shock, khalil ya bude side dinta yana mata kallon cikin ido yace "Sauko" Ta fashe da wani matsanancin kuka tace "In sauko in yi me?? Wallahi baxan sauko ba" Duk da dariyar da ta basa haka ya dake ya hade rai yace "Baxa ki sauko ba??" Cikin kuka tace "Ehh, ina ne nan din da ka kawo ni da kake cewa in sauko?" A takaice yace "Garin mu!!! don ki tabbatar mu ma muna da gida, dolenki kuma ki sauko ki gaida iyayena, sannan adadin kayan da kika kwaso adadin kwanakin da xa mu yi a garin nan kenan" Ta fashe da kuka hankali tashe tace "Na shiga uku na lalace...." Ko sauraronta bai kuma yi ba ya xaga bayan booth ya hau sauke akwatunanta, ta gwale ido ganin yayi hanyar shiga cikin gidan da shi, kuka take kamar ranta xai fita tana cewa ta shiga uku ta lalace, tun da aka haifeta ita kam sai dai taga irin wajajen nan a Tv, dama da gaske akwai irin garin nan a reality?? Ba a dau lokaci ba sai gashi ya fito da wata dattijuwa tana washe baki ta taho ba ko takalmi a kafarta tana cewa "Lale lale" Sake baki Nihad tayi tana kallonta a tsorace, matar ta karaso kusa da mota tace "Sannu da xuwa, lale lale" Nihad ta hadiye wani abu da kyar tace "Ina yini?" Khalil dake tsaye gefen matan yace "Sauko" Da kyar tayi karfin halin saukowa daga motar, kana ganinta kasan a tsorace take, matar tace "Bismillah mu shiga ciki, lale" Tana jan kafa ta bi matar xuwa cikin gidan, Khalil ya bi ta da kallo yana wani side smile, sai da Nihad ta duka kafin ta iya shiga cikin gidan, nan taga hut a jere kusan hudu a karamin tsakar gidan, lkci daya tsikar jikinta ya dinga tashi taji ta fara jin sanyi kamar xaxxabi xae rufeta, Matar ta shiga wani hut din tace "Bismillah shigo ciki...." Nan ma sai da Nihad ta duka sosai kafin ta iya shiga hut din, banda karnin nono babu abinda hut din yake, sae da ta kara gwalo ido don ta tabbatar kasa ne kwance a dakin kamar waje, sai gadon kara an shimfida wani yamutsatsen zanin gado a kai, daga can gefe kuma kwarya ne sun kusa goma an jera, Matar ta dinga nuna ma Nihad gefen gadon karan wai ta xauna, cike da karfin hali Nihad ta xauna tana kokarin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, dattijuwar ta fita daga dakin tana cewa "Bari a kawo maki ruwa" Wani hawaye ya xubo idon Nihad a hankali tace "Na shiga uku na lalace" da sauri ta goge idonta ganin wasu mata sanye da kaya irin na fulani sun tsaya bakin kofa suna gaisheta da fara'a, Da kyar tayi karfin halin gyada tana kirkiran murmushi tace "Nagode" Ai kuwa da wannan set din matan sun tafi sai wasu set din sun taho duk ana zuwa yi mata lale, sai ga dattijuwar da kwanon sha dauke da ruwa ta ajiye ma Nihad a kasa, Nihad ta dinga kallon ruwan ganin particles na ta swimming a ruwan, tun da aka haifeta bata ta6a ganin irin kwanon shan da aka xubo mata ruwan ba a ciki gashi duk yayi tsatsa, wata mata ce ta shigo rike da kwarya da nono a ciki, ta ajiye mata da wani karamin kwaryar me dauke da fura, tace "Sai ki dama hurar iya yanda kike so, idan kuma kina son suga sai a amso maki" Nihad dai ba bakin magana sai gyada kai, suka fita suka barta ita kadai da kudaje dake ta zaryarsu a dakin, a hankali ta fashe da kuka tana bin bukkar da kallo, who have she offend to deserve this in her life? Why is all this happening to her?? Khalil ya shigo ciki yana kallonta kasa kasa, cikin kuka tace "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ka maida ni gida, wallahi baxan sake maka duk abinda nake yi ba...." Ko rufe baki bata yi ba sai ga akwatunanta ana shigo mata da su dakin, da sauri ta share idonta tana bin yaran da suka shigo da akwatunan da kallo kamar idanuwanta xa su fito, Khalil ya jira har suka gama shigowa da su yace "Yauwa sannunku" Tana kallonsa ya tafi ya hau jera mata akwatunan step by step, ta rushe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace, me nayi maka kake min haka don Allah???" Ko tanka ta bai yi ba, ya dawo yana kallon fura da nonon yace "Ba lallai kin iya damawa ba, bari a dama maki" wata karamar tabarma da ya gani a dakin ya shimfida kasa sannan ya xauna ya tankwashe fararen kafarsa ya hau dama mata furan hade da nono a kwarya, kallonsa kawai take hawaye na sauka idonta tace "Don girman Allah kayi hakuri ka maida ni gida" Ba tare da ya kalleta ba yace "Sai kin gama sanye duk kayan dake akwatinki... Sannan nan din gidanmu ne, gidan iyayena ne dolenki ki xauna, adadin kayan akwatunanki adadin kwanakin da xa mu yi....." Hade kanta tayi da gadon karan da take zaune kai tana shessheka a hankali. Bayan ya gama dama furar ya dauka yana kallonta ya mika mata yace "Gashi" Dago kanta tayi tana kallonsa cikin rawan murya tace "Wallahi baxan iya xama a nan ba kaji na rantse maka" Yace "Xa ki iya idan kika kwana biyu, har ma xaki saba da kowa na garin" Ta fashe da sabon kuka tace "Na shiga uku wayyo Abbana" mikewa yayi ya ajiye mata furan a gefenta sannan ya fita daga bukkar, Nihad ta ci kukanta ta gode Allah, da ta ji alamar xa a shigo sae tayi maza ta goge idonta tayi feigning smile kamar ba komai, ga mutanen are so hospitable, sun ma rasa inda xa su sa ta, they are trying all they can to make her comfortable, hankalinta bai kara tashi ba sai da taga yamma yayi likis alamar dabb ake da magariba, gashi har sannan bata sake ganin Khalil ya shigo ba, Dattijuwar ta shigo tace "Fito kiyi alwala kin ji" Da kyar ta mike ta fito daga bukkar ta tafi inda aka nuna mata buta kusa da tulunaye uku, tana xuwa wajen Dattijuwar ta bi ta tace "Ko xa ki kama ruwa?" Ta girgixa kai da sauri, haka dai tayi alwala ta dawo bukkar matar ta nuna mata inda xata kalla tayi sallah, Nihad na ta xaune saman abinda tayi sallah, ita kam yau xata ga yanda ake kwana a wannan hut din, Wata budurwa ta shigo ta kunna mata wani fitila wanda da shi gwara babu, yarinyar na fita Nihad ta fara sabon kuka, wata mata ce ta shigo mata da tuwon dawa da wata shegiyar miyar kuka wanda warinsa kadai ma ya isa yasa mutum yayi throw up, Nihad ta jinginar da kanta jikin gadon karan wasu hawayen na taruwa idonta, ita kam yau taga ta kanta, miyar kuka da ake yi me dadi da yaji naman kaza ma ba ci take a gida ba balle wannan me offensive smell, ga wani mugun yunwa da take ji, ko furan bata sha ba balle tuwon dawa, khalil kam babu shi babu alamarsa, har kusan Isha'i bata gansa ba wanda wannan ne ya kara daga mata hankali, ko ba komai ta ma dinga ganinsa kawai kilan hankalinta xai kwanta, hakurinta na rashin ganinsa ya kare, tana ganin giftawar tsohuwar ta mike da sauri ta tsaya bakin bukkar cikin sanyin murya tace "Mama ya fita ne? Naga bai dawo ba" Ko rufe baki Nihad bata yi ba sai gashi ya shigo gidan, dattijuwar tace "Toh gashi ma ya dawo" Khalil yace "Sannu Gwaggwo" Gwaggo tace "Yanxu matarka ke Tambayarka" Ya ɗan kalli cikin dakin, Nihad ta hade rai ta koma ta zauna, ya karasa ya shiga ciki ya fito da karamar wayarsa ya haska tuwon dake gabanta yace "Har kin ci tuwon" Cikin rawan murya tace "Ta yaya xan iya cin wannan abun fisabilillah?" Yace "Ta yanda kike cin abinci a gidanku mana, kawai wanke hannu xa ki yi ki fara kai loma" Ta fashe da kuka tace "Wallahi baxan ta6a iya cin wannan abun ba" yace "Ohk, ashe ba yunwa kike ji ba" Ya haska furan nan ma yaga bata sha ba, gyada kai yayi ya juya xai fita, da sauri tace "Don girman Allah ka daina barina ni kadai" Hankalinta a tashe tayi maganar, yace "Me xan maki in na zauna? Yau kuma nine baki son in bar ki ke kadai?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta, ficewarsa yayi daga dakin ta bi sa da kallo hawaye cike idonta, har kusan karfe goma Nihad na xaune inda take sauro duk ya gama yagalgala ta, wata mata ta shigo bukkar da gidan sauro da wani yakunannen zanin gado tace "Can cikin dare xa ku ji sanyi sosai, sai ki rufa da wannan, bari a daura maki gidan sauro don akwai sauro" a hankali Nihad tace "Toh" can gefe matar ta matsar da tuwo da miya da kwaryan fura dake a kulle, ta gama daura net din a saman gadon karan ta fita, Har Nihad ta fara bacci a zaunen da take ba tare da ta damu da sauro ba Khalil ya shigo bukkar, kulle karamin kofar bukkar da yayi ne ya farkar da ita, ya haska ta da torchlight sannan ya haska saman gadon karan yace "Baxa ki shiga ki kwanta ba malama" Cikin rawan murya tace "Wallahi yunwa nake ji" Ya karasa ya dauko kwaryan fura da nonon da ya dama daxu ya ajiye mata, bata da wani option don mugun yunwa take ji, haka ta dau ludayin tana deban furan a hankali tana kaiwa baki, da kyar take hadiyewa saboda kyankyami, tana yin ludayi uku ta matsar daga gabanta ta rufe tana yamutse fuska, shi dai kallonta kawai yake, yace "Shiga net Hajiya" Ta daga kai ta kallesa ta marairaice tace "Kai a ina xaka kwanta?" Ya hade rai yace "Ina ruwanki?" Bata kuma cewa komai ba ta mike ta shiga net din, abinda bata ta6a shiga ba tunda aka haifeta, ji tayi kamar a saman siminti ta kwanta, ta kai hannu ta tattaba wajen, danne dariyarsa kawai yake, can dai ta hakura ta koma ta kwanta a hankali amma sai taji kamar she is going to suffocate inside the mosquito net, xaunawa yayi saman tabarma yana jin babban wayarsa dake aljihunsa na vibrate amma bai ciro ba, wajajen karfe sha biyu ya mike yana haska fuskarta yaga tayi baccin wahala, ya fi minti biyu tsaye kamar me contemplating, can kawai ya dage net din ya shiga ya kwanta ya juya mata baya sannan ya sake net din. Yana jin ta wajajen karfe daya da rabi tana juye juye, don bai yi bacci ba, can ta mike xaune tana lalubasa, hade rai yayi sae dai bai ce mata komai ba, bayan ta tabbatar shi din ne, ta hau tashinsa tace "Don Allah ni ban san inda xan je in yi fitsari ba" A takaice yace "Sai ki fita ki duba ai" Ya dage net din ya sauka don ya bata waje ta fita, ta sauko kasa tana kallonsa cikin duhun tace "Wayyo wallahi ya matseni" Ya kunna fitilar karamar wayarsa ya mike ya bude kofar bukkar ya fita ta bi bayansa da sauri ta dau butar da tagani tsakar gida, yana nuna mata bandakin dake xagaye da kara ta gwalo ido tana lekan ciki tace "A nan din xan yi fitsari?" Banxa yayi mata ya koma gefe ya tsaya, babu yanda ta iya haka ta shige ciki tana toshe hanci, tana fitowa ya koma bukka ta bi bayansa da sauri, ta xauna kasan tabarman dakin hawaye har ya cika idonta tace "Wallahi yunwa nake ji baxan iya bacci hka ba" ledan da ya shigo da shi daxu ya dauka ya ciro bread ya mika mata, ta dinga kallon bread din sai kuma ta amsa ta bude ta jinginar da kanta jikin gadon karan ta fara cin bread din a hankali, bata wani ci da yawa ba haka ta dau ruwan da take kyankyami ta sha kadan, shi dai yana zaune bai ko kallon direction dinta, a sanyaye ta mike ta shiga cikin net din ta koma can karshe ta kwanta, bayan wasu mintuna da shigarta shi ma ya shiga ya saki net din, nan da nan bacci ya kara dauketa, sae kusan karfe biyu da rabi yayi bacci shi ma, kusa da asuba garin yayi sanyi sosai, kamshin da ya ishesa ya sa ya bude ido a hankali, dab da shi ya ganta ta takure waje daya alamar tana jin sanyi, ya kalli gashinta wanda shi ne ya damesa da kamshi, hade rai yayi a hankali ya juya mata baya, ganin tana matsowa ya ɗan juya ya kalleta, bayan few minutes ya daga net din a hankali fuska daure ya sauka kasa, zanin gadon da mata ta kawo mata ya shimfida saman tabarma ya kwanta, bai sake komawa bacci ba har asuba tayi. Zaro ido Nihad da ta farka da safe tayi ganin gari yayi shar, ta kalli gefenta taga baya nan, da sauri ta sauka ta fita tsakar gida, bayan ta dauro alwala ta shigo bukkar ta dau hijab dinta tayi sallah, bayan ta idar ta mike ta koma gefen gadon karan ta zauna abun duniya duk ya dameta, ta kalli uban kayanta bayan ta tuna abinda ya ce mata wai sai ta gama sa su sannan xa su bar kauyen nan, da daddaya da daddaya aka dinga shigowa gaisheta, mata ta farko da ta fara shigowa gaisheta haka ta bude akwati ta bata atamfa riga da skirt, a haka ta dinga rarrabar da kayan nata, ai ko har da makota a shigowa gaisheta, har kayan kwalliya da shafe shafenta bata bari ba, daga karshe ta ba dattijuwar akwati daya, mata biyun dake gidan su ma duk ta basu kyautar akwatuna daddaya, da atamfa kala daya da Hijab ta tsira sai turare shi ma daya da handbag dinta da takalmi sauran duk ta yi sadakansu, ai ko ta sha godiya sannan albarka ta sha shi kwando kwando, wani kunu me ruwa ruwa aka dire mata as breakfast da dumamen tuwon da bata ci jiya ba, Nihad tayi tagumi tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta ya xubo ba, wajen karfe takwas aka kai mata ruwa tayi wanka bayan ta dawo bukkar ta shirya sai ga khalil ya shigo gidan tun daga bakin kofa Dattijuwar ke basa labarin alkhairin da Nihad tayi masu da makota, har da fito da akwatin da Nihad ta bata ta nuna masa, yana shiga bukkar da Nihad take yaga babu kaya ko daya ya kalleta, ita dai kanta na kasa, can yace "Ina kayanki suke?" A takaice tace "Na rabar, ko kai baka ga kayan da suke sa wa bane" Yace "Ohk, ashe xaki yi ta maimaita kaya kenan...." Ta fashe da matsanancin kuka tace "Toh meye don na masu sadakan kaya, idan haka ne mu koma gida in kwaso wasu kayan sannan mu dawo mana" Yace "Koh?" Tace "Ehh mana" yace "Okay, xamu koma ki debo duk kayan naki sai mu dawo" tana share idonta tace "Na yarda, daga nan ma sai mu taho da ruwan gora da biscuits" Yace "Toh" Daga haka ya fita daga bukkar. Har rana ya fara yi Nihad na ta baza ido bata ga Khalil ba balle su bar garin, da rana aka kawo mata ordinary wake da aka dafa aka xuba masa man gyada ita da bata cin wake, ga shi wani axababben yunwa take ji, haka ta bar masu tsiyarsu, wasa wasa har kusan la'asar ba khalil ba labarinsa, da taga yunwa xai mata illa haka ta daure ta dinga danna fura da nonon da aka dama mata, shiru shiru har magrib, bayan ta idar da sllh ta ci kukanta ta gode Allah, har aka yi isha bata ga Khalil ba har ta daina tambayar dattijuwar dake assuring dinta yanxu xai shigo, bayan tayi sallan isha kawai ta dage net ta shige tana shesshekar kuka ba tare da ta bi ta kan tuwon dawar su ba, can wajajen karfe goma sha daya saura ta dinga jin kamshin turarensa, sai kuma ta ji suna gaisawa da mutanen dake tsakar gida kafin ta shigo, xa a kawo masa abinci yace masu ya koshi, bayan like 10 mins ya dage net ya hau saman gadon ya haskata da karamar wayarsa, duk da tana jin sa bata yarda ta bude idonta ba, kashe fitilan yayi ya kwanta, ta bude ido ta dawo kusa da shi ta fashe da kuka tana shessheka tace "Kai fa kace idan na gama sanye kayan da na kawo za mu tafi gida, toh gashi yanxu ko kayan da xan canza gobe bani da shi" Yace "Sae ki maimaita na yau" kuka take sosai, ya juya mata baya, ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta koma ta kwanta a hankali, bayan kusan awa daya ya kunna torch dinsa ya haska fuskarta ya ga bacci take. Can kusan asuba xafin jikinta ya farkar da shi, kamar jiya tana kusa da shi ta takure waje daya, ya kai hannu jikinta ya ji da xafi....
*Ki biya dari biyar ki karanta hankalinki kwance er uwa*
NIHAAD is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via👇🏻
07087865788....
Leave a Comment