Fulani 19


 19

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*


Hannun rigarsa ya fara budewa sannan ya bude ya fara bude maballan rigarsa yana ta kallon kansa a jikin madubin dake gabansa. Dan murmushi yai kamar wanda ya tuna abu sannan ya juyo ya cire rigar gaba daya ya dora saman gadon ya dauko vest ya saka ya sauko kasa. 

Kai tsaye kitchen ya wuce ya dauki cup ya aje sannan ya bude fridge ya dauko lemun tsami ya matsa a cup din ya bude durowar kitchen din ya dauko wata farar roba ya bude ta debi kanwa kadan ya zuba a cup din ya saka karamin spoon ya garwaye sai da lemun ya hade da kanwa sannan ya daga cup din ya shanye yana bata fuska tsamin na kai masa har cikin kai. Ra'ees ne ya shigo kitchen din sai zuba kamshin turare yake. 


“Shattima ni zan wuce”


Ra'ees ya fada daga tsayin da yaje bakin kofar kitchen din. Juyowa Shattima yai ya kalleshi, irin kallon nan na ina zaka je? Indai Shattima ne zai bude baki ya tambaye shi ba sai dai kar ya sani, ba dan komai ba sai dan magana taba masa wahala, yana da nauyin baki furta wata kalar tafi komai yi masa nauyi a baki da jiki, abu ne mai wahala ka ganshi a cikin mutane ko da kuwa Ammy ce ko Zainab yana fira, sai dai yai shiru yai ta saurarensu idan sun gama ya tashi wani lokacin kuma sai yi murmushi idan an fadi abun dariya idan kuma tambayarce zai iya ce maka eh ko aa ko ya girgiza kai. Magana ta fi komai yi masa wahala a rayuwa, gashi kuma likita haka nan dai yake ta fama kamar dole.


“Zan je kauyen kaita, akwai wani aiki da nake son yi a can”


Ra'ees ya amsa masa ba tare da ya jira ya tambaye shi ba, daman kuma ya san halin abokin nasa indai sai ya tanbaye shi ne sai a mutu a tsaye. 

Shattima na son ya tambayeshi me zai je yi a can kuma yaji ba ya bukatar wahalar da kansa, sai kawai ya tabe baki ya daga masa hannu. 


“Safe trip”


“Thanks”


Ya juya ya fice daga kitchen din, kamin ya isa gurin motarsa Yayarsa ta masa kira ya kai uku domin mijinta ya shirya shi kawai ake jira. Da motarsa ya isa gidanta sai ya aje motarshi ya shiga motar mijin suka kama hanyar Kaita daga Katsina. 

Suna tafe suna firar kasa da rashin tsoron da ake fama da ahi da yunwa, har suka isa, a cikin garin kaita suka yi sallah sannan suka yi tambaya aka fada musu hanyar da za su bi ta kaisu garin Bandalo. Alhaji Tukur ne yake jan motar Ra'ees yana front seat, yana karewa garin kallon, garin Bandalo gari ne mai cike da burgewa, tun farkon shigowa garin zaka fara arba da manyan gonaki, domin garin ya kasu kashi biyu ne, fulani makiyaya sai kuma hausawa da kusan sune rabin garin, daman fulanin irin masu yada zango nan ne a gari, yamma da garin ne bangaren fulani kana daukar hanyar da tai can zaka fara arba da bukoki da shanu da masu kiwon shanun gwanin burgewa. 


“Rabun da na ga bukka da idona ni har na manta”


Ra'ees ya fada yana kara bawa idonsa abinci, sai da su kai nisa sosai sannan Alhaji Tukur ya tsaya kusa da wasu fulani suka zaune gaban wani massalaci na kasa yana tambayarsu Malam Jauro. 


“Dan Allah muja cijiyar wani Malam Jauro Sama'ila”


“Kun zo gida, daga ina kuke?”


“Daga birni mun zo, gurin Matarsa ne Amo”


Wani bafullatanin mai tsaga a fuska ya mike tsaye. 


“Muje na karasa da ku daman gidan Modibbo zan je”


A kafa yake tafiya su kuma tana binsa a kasa har suka isa kofar gidansu Fadime, gidansa ne mai girma da aka zagaye da zana an share gaban idan tas ga kasar gurin ta kwanta kamar yashi. Malam Bala da kansa ya sallama cikin gidan sai Hajjo ta amsa masa ta fito ta gaishe shi tana karewa mutanen kallo da yaren Fulatanci yake tambayarta ina Malam Jauro, sai ta fada masa baya nan ya tafi gona.


“To ga baki nan ki fadawa Amo, ni bari naje na kira shi”


Ya fada mata da yaren fulatanci, sannan ya kallesu yace. 


“Zanje na kira shi yanzu nan, yana gobarsa”


“To sannu da kokari mun gode sosai”


Duk suka fada Ra'ees har yana dan risinawa domin ya yaba sosai da yadda mutumen yake ta musu karamci. 

Yana tafiya Amo ta fito baki har kunne tana dariya ta nufo su da hijabinta mai multi colors tabarma rike hannunta Hajjo kuma na rike da kwanon ruwa dake cike da kindirmo. Icen dake kusa da kofar gidansu ta nufa ta shinfida kusu tabarmar a can, sannan ta karbi kwanon dake hannun Hajjo ta a gurin. 


“Hannunku da zuwa Hannu da zuwa, kun sha hanya”


Ta hangame musu bakin nan nata mai cike da goro tana musu Sannu ga wata uwar dariya da take musu ta murna da ganinsu domin bata dauka za su zo din da gaske ba. Ra'ees ne ya fara zaunawa yana amsa gaisuwarta kamin mijin yayarsa ya zauna shi ma. 

Da sauri Amo ta koma ciki gida da murnarta, ta nufi dakin Inna wacce ke zaune dakin tare da Fadime tun safe, saboda kukan da Fadime take ta yi, tun tana dan jin tsoron abun da ya faru jiya har ta fara dauriya tana lallashin yarta, duk kukan da Fadime take na hawaye ne kawai bata yarda ta bude bakinta, gudun kar ta sake tsorota wani domin ita ma tsoron muryar take, gashi Bappa da Inna sun hata ta fita balle taje ko zata ganshi ta roki ya gyara mata nuryarta ta koma daidai. 


Hankali Inna da Fadime be kara tashi ba, sai da Amo ta leko bukkar tace ga masu neman auren Fadime nan sun taho, Fadime kamar an mata allurar kuka haka ta ji, Inna kam sai tausayin Fadime ya kamata dan ta san yadda take daukin zuwa wannan ranar. 


“To su gaisa da Malam tukuna mana”


“Eh na aika Hajjo ta kirashi yanzu”


Amo ta juya ta fita tana jin wani irin dadi marar misaltuwa, tasan a komai yanzu ita za a saka a gaba. Cikin hawayen Fadime ta mike tsaye tana nuna ma Inna tufafin jikinta da alama so take ta canja ta, tana son tai magana tana jin tsoro muryar. 


“To wai Fulani hakan zaki tafi musu kanar kurma? Komai sai dai ki da hannu?”


Fadime. Ta dan turo baki ta fice daga bukkar ta nufi bukkarta ta dauko atamfar dake can masa ghana must go, ta tube rufafin jikinta ta debi ruwa ta shiga bandaki. Sai da ta kori kadangaran da ke gurin dan kar su sako mata ido suna kallon tsiraici sannan ta cire zanenta, sama sama tai wanka ta fito tana ta ayyana yadda mutumen yake a idonta, bata ma tsawa shafa mai ba ta saka atamfar ta daura dankwali ta dauko mayafi ta dora a saman kai, ta dauki karamin madubin ta kalli kanta. Dan murmushi tai kamar ba ita ce take kukan tun safe ba har rana. Can zuciyarta ta bata cewar ta shafa hota ai yan birni ne, da sauri ta kwance kullin hodar ta kasa dake cikin farar leda ta dagali kadan ta shafa ta shafa janbaki, abun ka da farar mace sai tai kyau sosai pink janbakin ya haskata ita kanta sai da tai murmushi. Ta dauko talkaminta na sallah ta saka ta fito tsakar gidan ta zauna, Inna na kallonta ta saki murmushi ganin yadda yarta ta fito Ma-sha-Allah, daman can Fadime akwai iya kwaliya ba kamar ta sauran yan matan kauyen ba. 


“To kwalli fa”


Inna ta fada tana kallonsa. Sai Fadime tai murmushi kamar ta bude baki tace ai su yan birni basa saka kwalli kuma ba dama tun da muryarta ta zama abun tsoro, duk da bata da tabbacin muryar tana nan har yanzu ko kuma ta dawo normal a yadda take, abun haushi ma muryar shanun bata fita kadan kamar an saka loudspeaker haka take shiga kunne mutane.

Gaba daya Fadime kasa natsuwa tai taje jikin zanar tana lekensu sai dai bata ga fuskar ko daya daga cikinsu ba kasancewar sun bata baya ne suna magana da Bappa da wani abokinsa. Wani irin tsalle ta buga tana jin kamar ranar za a kaita dakin mijin. Amo de na zaune bakin tata bukkar tana murmushi a ranta tana ayyana ko kwana nawa Fadime za tai kamin ta mutu, ta dayan bangaren kuma tana ta mamakin yadda jiya ma wani abun ya same ta na sauyawar muryar kamar yadda Inna ta fada mata, dan ita dai bata nan komai ya faru. 

Yanzu kam ta fara gasgata cewar Fadime ta hadu da aljanu domin su kadai zasu iya cire nata wutar sai kuma maye irinta ko mai tsafi, wata kila shiyasa ita ta kanta ta nemo mata miji, ko da yake mijin ma daga gani maye ne kamar ita ko zai iya cin kurwa Fadime ko kuma zata gagareshi ne kamar yadda ita ma ta gagareta? 


‘Bari na gani yanzu za a sake cirewa’


Ta fada a ranta sannan ta mike tsaye ta shiga cikin bukkarta, ta mika hannu a karkashin gadon ta na kara ta dauko wata yar karamar tukunyar kasa wacce ke rufe da jan kyalle ta bude kyalle ta kai bakinta ta fara kiran sunan wani aljani tana masa kirari kamin ta fadi bukatarta sannan ta kai kunnenta tana saurare. Can ta sake kai bakinta. 


“Bakin bunsuru zan yanka maka”


Sannan ta aje tukunyar wacce aljaninta na maita yake ciki ta maida ta karkashin gado, ta sake janyo wata tsohuwar roba mai murfi ta bude ta dauki wata yar karamar soyayyar kurwa ta kai baki, har wani lumshe ido take tana shude yatsan hannunta. 


“Saratu kam akwai dadi”


Ta fada tana kokarin maida robar a inda take, sai davta gyara komai tsaf sannan ta mike tsaye ta fito, a tsakar gida ta samu Bappa tsaye yana nunawa Inna kudin da suka ba shi.


“To gashi nan since ase goro”


A take ta ji ranta ya bace akan me zai fara nunawa Inna bayan itace uwargida, sannan ita ta kawo ma Fadime mijin nan, sai dai bata yarda ta nuna musu komai ba ta washe baki tana murna kamar gaske. 


“To Fulani tashi kije ku gaisa”


Bappa ya fada. Abun ka da mai nema sai tai zumunt ta mike tsaye, jikinta sai rawa yake zuciyarta na bugawa da karfi, tana son ta tambayi Inna idan taje me zata fara cewa kuma tana gudun tai magana aji muryarta bata sani ba ko har yanzu muryar tana nan.


“Karki musu magana Fulani, duk abun da suka ce miki sai dai ki daga musu kai ko ki yi dariya, idan suka tambaye ki ki nuna musu wuyanki wuyanki ke ciwo”


Inna ta fada, sai Fadime ta gyada kai ta sinne kai kasa tana dan jin kunyar Bappa, har tafiya sai da Fadime ta sauya ta fara irin na yan zamani a hankali take takawa har ta isa inda suke, tana kokarin zaunawa a saman shimfidar ta tuna cewar bata saka turare ba, gashi dai yan birni suna son kamshi tun da su ma taji sai kamshin suke, sau daya ta kalli Ra'ees ta dauke kai dan ta fi sa ran shi ne mijin nata ganin ya fi kurciya. Da hannu ta gaishe su irin yadda kurame suke yi sai suka kalli juna shi da Alhaji Tukur, domin ba a fada musu cewar ita din kurma ce ba, ga kyau iya kyau amman ba magana. Duk abun da suka tambaye sai dai tai musu na kurame, Ra'ees sai wani irin kallonta yake shi kam gaba daya ta tafi ta imaninsa duk da kasancewar ta kuma. Rashin maganar ba karamin cutar Fadime yai ba domin ta so tai musu turanci su ji cewar ta iya ingilishi kamar yar birni, tsoro tsoro take wai kar su dauka ita kurma ce su fasa aurenta, sai a lokacin ne ta tuna cewar Inna tace ta fada musu wuyanta ke ciwo. Sai ta kai hannunta ta dafa wuyan tana nuna musu.


“Wuya? Ciwo yake?”


Alhaji Tukur ya tambaya a nan kam Allah ya bata ikon magana. 


“Eh tun jiya”


Ba shiri ta zaro ido ta rufe bakinta da sauri, Alhaji Tukur ya kwanta a gurin ya danne kansa sosai yana fadin. 


“Salamun kaulin min rabbirrahim”


Ra'ees kam tsakanin mikewa tsaye da fallawa da gudu ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba, a maimakon yai daji sai ya gaishe gidan makotansu, matan gidan na daka suka saki tabare kowace ta shiga dakinta da gudu suna ihun kwarto. Aka bar Ra'ees tsakar gida sai rawar sanyi yake ga wani uban fitsari daya cika masa mara, tun da yake a rayuwarsa be taba ji murya irin da Fadime ba, zanar gidan ya fara bi da kallo zuciyarsa na raya masa garin aljanu suka zo. Cikin tashin hankali Bappa ya kawo kofar gidan makocin nasa yana fadin 


“Subhanallahi”


“Kado fito gidan matan aure ne”


Matan auren da Bappa yace sai Ra'ees yaji kamar Bappa yace masa gidan matan aljanune saboda sune a ransa, a maimakon ya fita sai ya shige bukkar dake kusa da shi gumi har karyo masa yake, aiko ba shiri matar ta saka ihu ta fito daga dakin da sauri. 


“Wayyo Jama'a ga kwarto”


Sai da Bappa ya shigo yaja hannun Ra'ees suka fita daga gidan, idon Ra'ees na kasa yana ta kallon kafafuwansu so yake ya ga kofatai, dan shi gaba daya ya gasgasta aljanun ne, domin har yanzu yana jin muryar Fadime cikin kunnensa. 


“Dan Allah dan Annabi karku mana komai”


Ra'ees ya fada yana ta kallon kafafuwansu, kana ganinsa kasan baya cikin hayyacinsa natsuwa ta bar jikinsa, Alhaji Tukur tuni ya shige cikin mota ya rufe ta budewa Ra'ees dayan side din yana masa alama da ya zo da rugo su gudu. 


“Inna duk ke kika kore min miji kin ce na taba wuyana na fada masa ciwo yake gashi nan ya gudu”


Fadime ta shiga gida tana kuka tana fadin haka cikin muryarta mai bantsoro, Inna da Amo suka shige bukka daya da gudu jikinsu na rawa, a tsakar gidan Fadime ta fadi ta bude muryarta mai ban tsoro tana kuka, da sauri Bappa da mutanensan dake gurinn Ra'ees suka sake shi suka nufo gida da gudu, a nan Ra'ess ya samu sa'ar aunawa da gudu ya shige motar da Alhaji Tukur ya tayar, Alhaji Tukur ya fisgi motar kamar sun sato mutum. 

Suna barin kofar gidan muryar Fadime  ta koma daidai, kukan da take rirewa ya dawo normal muryarta ta ainahi, aiko da sauri ta tashin ta kabe jikinta ta nufi waje, ganin babu su babu labarinsu yasa ta zube a kasa ta fashe da sabon kuka gaban abokanin Bappa da yan gari da suka fito kallon ikon Allah. 



FALMATA POV.


Kamar ance daga kanki ki kalli sama, sai ta hango wani tsaya a backyard din yana kallonta, baki ne wulik kamar ita sai dai ita din ta fishi kyau, waya rike a hannunsa sai dai ba wayar yake kallo ba ita yake kallo, sauke kai tai kasa tana wasa da yan yatsunta ta dayan bangare kuma tana ta tunanin irin hukuncin da zata fuskanta idan suka isa gida, wata kila Baba ya sake korarta ko kuma ya doketa ko ma ya tsine mata kamar yadda Tumba take fata. Bata raba dayan biyu ba Momy ta fito sanye da wani farin lace da mayafi red da jakarta ma red, tun kan ta karaso ta danna key motar ta cireta daga lock.


“Bude ki shiga”


Momy ta fada tana mata alamar da zata gane. Ba musu Falmata ta bude motar ta shiga gidan gaba Momy ta zauna a mazaunin direba tai warming din motar, mai gadin na gani haka ya bude mata mata gate. 


“Ina ne unguwarku?”


Momy ta tambaya da muryar da Falmata zata iya jinta. Falmata ta fada mata cikin sanyayyiyar murya, kallonta kawai Momy tai taja motarta suka kama hanya. a bakin hanya Momy ta faka motarta domin unguwar irin unguwar nan ce da Mota bata shiga sai babur ko kuma mutum ya taka a kafa. Falmata na gaba Momy na binta a baya har suka isa gidan, ba karamin Hijadi tai ba na saka kafarta cikin gidan duk kuwa da irin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata fasa kirjinta ta fito. Da sallama ta shiga Momy ma ta dora da nata sallamar tana karewa gidan kallo. 

Tumba ce ta amsa musu tana kallon Falmata da mamaki da kuma dake bayanta rike da jakarta, tun kan Momy tace komai Tumba ta shiga dakinta da sauri ya dauko tabarma ta shimfida mata. 


“Sannu da zuwa sannu da zuwa”


Tumba ta fada tana kallon Momy, kana ganinta kasan ba karamar mace ba ce,ba a shekaru ba a aji da zubi da kuma tufafin dake jikinta sun isa su sanarwa Tumba cewa wannan matar Hajiya ce, can ta kalli Falmata sai ta fashe da kuka. 


“Fulani ina kika shiga? Tun da shekaranjiya babu ke babu labarinki hankalinmu duk a tashe ko ruwa na kasa sha, Malam ma jiya cikin dare tashi yai ya zauna saboda baya iya bachi, yanzu kam ban gama da fadawa Allah bukatata ba na bayyana mana ke cikin aminci, ashe kina tafe”


Kamar da gaske ta damu da Falmata haka hawaye ke bin fuskarta, Momy na kallonta cike da tausayawa duk da bata da da tasan yadda batan mutum yake tayardar hankali balle kuma danka. Falmata dai ta kasa cewa komai duk kuwa da kasancewar taji abunda Tumba take fada, dan ba da karamar murya take maganar ba. 

Sanin cewar Falmata bata ji sosai kamar yadda Sirleem ya fada mata yasa, Momy ta daga murya gurin yi ma Tumba bayani. 


“Tana tafe ne a hanya, ina ta horn bata ji ba, har kadeta, sai ta suma da taimakon mutane muka kaita asibiti, bata farka ba sai yau, shine na tambaye ta ina iyayenta tace nan ne gidansu, shine na zo na rakota, daman na san sai hankalinku ya tashi”


“Allah sarki, ai dole hankalinmu ya tashi kam tun da maraya babu shi a kusa da kai dole hankali ya tashi”


Tumba ta fada tana kallon Falmata da taji wani sanyi a ranta, sanadiyar karyar da Momy tai, ta san ta wanke ta gurin Tumba har ma da Baba kuma ga kudin Tumba Sirleem ya bata. Abun da Tumba ta fada yasa Momy ta kare mata kallo, tun nan ta fahimci wacece Tumba, idan tai hada labarin da Sirleem ya bada da kuma yanayin Falmata sai ta fahimci cewa Tumba tana yi ne kawai saboda ta ganta, domin ita na tasan yadda matan uba suke. 

Momy ta saka hannunta a jaka ta dauko 5k ta mikawa Falmata.


“Ga wani Allah ya baki lafiya, kin ga mun manto maganin gida”


Falmata ta saka hannu biyu ta karba, saboda a gaban Tumba ne bata isa tace a a ba. 


“Haba dai har da wahala haka? Ai da kin barshi mun gode sosai Wallahi”


“Ba komai ai yiwa kai ne, ni zan tafi sai anjimanku”


Momy ta fada tana mikewa tsaye, har bakin inda ta aje motarta Tumba ta rakota tana mata godiya sannan ta juyo ta dawo gida. Tana shigowa Falmata ta mike tsaye ta mika mata kudin duka. 


“Ai kara ma data kade ki gashi mun samu 10k”


Tumba ta fada tana kirga kudin. 


“Dubu biyar kudin adashenki ne, a lokacin da naje ban same ta ba sai na wuce da kudin gurin aiki kamin nakai ne abun ya faru”


“Ba komai ai dai kari yafi kara, ni da na dauka ko guduwa kika yi da kudina Wallahi, ashe kadeki akai”


Falmata dai ba ta ce komai ba, ta mike tsaye zata shiga dakinsu zuciyarta fal da farincikin abun da Sirleem yai mata.


‘Yana da saukin kai be da girman kai ba da wata matsala a rayuwarsa, yana son mutane kuma yana taimako’


Ta fada a ranta sannan ta bude jakar kayanta ta dauko hular daya taba bata tana tabawa fuskarta da murmushi. 


“Ka taimake ni ka tsiratar da ni yau”


Wannan karon a fili tai maganar ta rumgume hularsa tana jin wata sabuwar kaunarna na shiga ranta, ko a da can da bata san halinsa ba tana son sa balle kuma yanzu da daya taimaketa. 


“To sai ki fito ki tafi wajen aikin tun jiya ba kije ba kar su ce ba zasu baki albashi ba ko su koreki”


Cewar tumba daga wajen da take zaune ranta cike da farinciki. Da sauri Falmata ta mayarda hular ta fito ta saka takalminta.


“Zan wuce mata da kudin adashen ne ko kuwa?”


“Aa ni zan kai mata da kaina, Wallahi da ban ganki kin dawo ba kuma na aika tace ba ki kawo mata kudin ba, har wani zazzabi na ji ya ta so min, sai yanzu kaina ya zauna ciwo”


Ajiyar zuciya Falmata ta sauke ta kalleta sau daya ta dauke kai ta nufi hnayar fita. Ina aka ganki yaushe kika dawo shine abunda kowa yake tambaya domin Tumba ta yada cewar wai dan Baba ya daketa shine ta ji haushi ta gudu, sai a lokacin ne wasu suke fahimtar Falmata bata ji sosai domin sai sun yi da karfi take jin abunda suke fada, shakku ya fara shiga zukatan mutane game da irin rikon da Tumba take mata, duk kuwa da kasancewar Falmata bata taba fadawa kowa matsalarta ba bayan kawarta Khadija, sai dai labarin da Tumba ta yada da kuma ganin Falmata ta dawo har ta fadi cewar kadeta akai ya ba mutane mamaki. 

Babu wani abun kirki a cikinta kasancewar bata karya batun suka taso a gidan Momy kuma cornflakes kawai ta sha har yanzu bata jin jikinta da karfi, sai dai karfin zuciya da Sirleem ya sama mata a yanzu, ita kanta ta san dawowarta yafi tafiyarta a yanzu duk kuwa da irin wahalar da take sha. 

  A yau kam kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin farinciki da annushuwa, abun da ya dade be rabe ya ba. Ta shiga cikin gidan tana tsara yadda zata shimfida musu karyar da Sirleem ya koya mata. Kamar kullum yau ma gidan na cike da mutane kowa sai shanin gabansa yake, ita ma ta nitsa kai tana tafiya har ta isa gate din Ammy. Tana shiga ta ci karo da Iya tsaye ita da Zainab da alama wata maganar suke, wani irin faduwa gaban Falmata yai sakamakon ido hudu da suka yi da Iya har sai da kanta ya sara, addu'o'i ta fara karantawa tana kallon Iya wacce tai saurin dauke kai ta juya gurin flowers kamar ta rude ta fara taba su, Zainab ma ta lura da hakan sai ita a tunaninta Iya tana tsoron Falmata ne. 


“Barka da yamma”


Falmata ta fada tana risinawa Zainab. Wani uban tsaki taja ta dauke kai ta nufi gurin mahaifiyarta. 


“Wai tsoronta kike ji ne Iya?”


Iya bata yarda ta juyo ba sai da Falmata ta shige falon farko. 


“Ba tsoronta nake ji ba, makircinta nake tsoro, domin zata iya zuwa tace na harareta, kuma tun da har ba ni da gata a gidan nan Ammy zata iya yarda wata kila ma ta koreni ta daga masarautar nan”


Zainab ta juya tana kallon falon da Falmata shiga kamin ta juyo ta kalli mahaifiyarta.


“Haba dai Iya, a yadda kike a cikin gidan nan har wata ta isa ta zo a kwana biyu tace zata saka ki tsoronta?”


Iya ta dafa ta. 


“To ai ta fini gata ne Zainab”


“Kamar ya?”


“Kina tunanin ina da gadon sarautar gidan nan ne?”


Zainab ta girgiza kai alamar a'a. 


“Kina tunani ni ko ke akwai wanda za a bawa gadon Mai Martaba idan ya mutu?”


Nan ma kan ta girgiza. 


“Na isa na samu Ammy da wata magana da dauka? Tsawon shekarun da nai ina bauta musu?”


Zainab ta dan yi shiru.


“Eh ai wani lokacin ma Ammy tana neman shawararki a wasu abubuwan”


Iya ta yi murmushi tana girgiza kai. 


“Karki yaudari kanki, tana daukar shawarata ne idan ta yi daidai da abun da take so, ban isa nace ga yadda za'ayi ba ayi sai dai yadda aka yi ni na bi, shiyasa kullum nake nuna miki hanya kin kasa gani, ina son na samu matsayin da zan iya cewa eh babu mai musa min, idan kuma na ce aa babu mai daga ido ya kalle ni balle yace dan me? Shekarun da nai ina bauta a gidan nan kar su tashi a banza”


Har Zainab ta bude baki tai magana sai wayarta tai kara, kiran Auwal ya shigo mota, murmushi ne ya kayata fuskarta ta amsa kiran da sauri daman abun da take jira kenan. 


“Hello Baby”


“Na'am yakike?”


“Gani a waje”


“Okay ina zuwa”


Ta sauke wayar sannan ta kalli Iya cikin jindadi. 


“Gashi nan ya zo, Iya ki je dakinki zai shigo ku gaisa”


‘Kin kuwa ja masa mutuwa’


Iya ta fada a ranta a fili kuma sai ta sakar mata murmushi ta gyada mata kai, sannan ta nuna ta da yatsa da fuskar dake nuna ba da wasa nake ba tace


“Tau na ji, amman zancen tafiyar nan a bar shi karki waiwayi garin nan”


Zainab wacce har ta juya ta juyo ta kalli Iya da mamaki a fuskarta.


“Ban gane kar na waiwayi garin ba, daman na taba zuwa ne?”


Iya ta daga mata hannu. 


“Je ki tarbi bakonki zamu yi magana”


Zainab ta juya ta nufi hanyar fita tana sanye da doguwar rigar atamfa sai dan karamin mayafin dake kanta.

No comments

Powered by Blogger.