Fulani 15


 *15 -Last Free Page*


Fadime ta kara lakkamo Ma'u tana dariya


“Wallahi kuwa”


Ma'u da rufe baki tana zaro ido. 


“Kuma Wallahi da gaske koko na sa da safen nan, Fulani da gaske kin iya”


Wani kalar dadi ya kara rufe Fadime jin ta canki abun da Ma'u ta karya da shi yau, bayan ta gama fada mata ita tana da aljannu kuma suna sa ta gane komai na mutum. 


“Yanzu kenan za ki iya fadawa mutum abun da zai same shi”


“Eh amman sai na yi bachi, amman dan Allah Ma'u karki fadawa ko sai wanda kika yarda da shi, idan Bappa ya ji zai min fada ko ya doke ni ma”


“Ba zan fada ba”


Fadime ta yi dariya. 


“Inna tace masu irin wannan abun kudi ake ba su, idan kina ga wani na son a masa ya bada kudi ki kawo shi zan masa amman a boye”


“Aiko zan ta kawo miki mutane Wallahi, sai ki sammin wani abu ni ma”


Sai da hantsi ya bude sosai sannan Fadime ta bar kofar gidansu Ma'u ta dawo gida. Kai tsaye ta nufi bukkatarta ta dauko biro da littafinta ta fara rubuta hau Amo tace zata kawo mata miji, kuma ta fadawa kawarta Ma'u cewar tana dubi.


Gaba daya wunin ranar wuni tai cikin farinciki da jindadi kana ganinta kasan dadi take ji tana murna wai Amo ta mata miji kuma a bunni. 

Amo dai sai kallonta take a ranta tana fadin 


‘Zaka si ubanka idan ka aureshi mutuwa za kai, idan ka gagaran ci ai ba ka gagari wani ba’


Ta fada tana dan murmushi sai da Fadime ta mike tsaye tana kora shanu zuwa daji Amo ta lura yau wutar nan bata biye da ita, a razane ta mike tsaye tana bin bayanta da kallo. 

Inna ma ta mike tsaye daga can cikin bukkar da take zaune tana kallon Amo, wacce razanar ta bayyana, Inna daman can ta dade tana zargin Amo da maita ba tun yau ba, tun daga lokacin da ta bata labarin cewar suna da maitar gado wacce ake bawa yara tun suna kanana amman ita Allah ya tsareta ba a bata ba, ga yayan wabin da Inna tai ta yi a duk inda take neman magani sai ace manya ce take cinye mata yaya, wani cikin ma tun kan ya zo duniya zata yi barinsa, Fadime ce kawai ta rayu ita ma daker dan babu kalar ciwon da ba tai ba, Allah ne dai ya rata ta da kuma addu'oin da take yawan yi mata, Bappa ma yana mata sosai har rubutu yake mata ya bata ta sha, tun a wacan lokacin idan Inna ta fada masa tana zargin Amo sai ya karyarta yace baya son tashin hankalin, har yake ganin kamar kamar Inna tana haka ne saboda Amo kishi, bayan kuma ita ta zo ta tararda Amo.


  Sunsunsun Amo ta shige bukkarta da mugun mamaki, ta sani wani sa'in ana samun akasin abun da tai mata, sai dai ba ko yaushe ba, domin Fadime babu ruwanta da addu'a sai dai idan yi mata akai, kuma wannan wutar ta dade da saka mata ita tun Fadime na karama, taya yau rana daya za a wayi gari babu ta? Ko dai Inna ta karbo mata wani maganin ne? Idan ba haka ba gaya wutar ta bar binta? Adakin ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya.


A kullum idan Fadime zata je kiwo sai ta saka shanun gaba tana binsu a baya, ban da kwana biyun nan da take son sake ganin Wasim, kullum baya take baro shanun sai idan sun kawo kansu. Tana isa ta haye saman dutsen ta fara kiransa. 


“Mai busa”


Haka take kiransa a duk lokacin da ta iso gaban dutsen, duk kiran da zata masa kuma ba zata ganshi ba, ba zata ji busar ba, bata kuma fasa kiran ba. Sai dai shi yana saukowa kasa ne ya boya jikin dutsen yana kallonta har tai abunda za tai ta gama. 

  Sai da ta sauko saman dutsin sannan ta ganshi kasa tsaye ta inda zata ganshi yana kallonta fuskarsa da murmushi, dan tsoro ta ji.


“Kenan shi aljanin dutse ne?”


Ta raya a ranta, a fili kuma sai ya kara hayewa saman dutson alamar ba zata sauko ba. Ganin hakan yasa ya fara haurowa saman dutsen still yana mata murmushi. 


“Ka yi hakuri ni ba dan wani abu na kira ka ba”


Ta fada tana kokarin sauka ta dayan bangaren, ganin hakan yasa shi ma ya juya ya sauka. Sai suka koma kallo kallo ita da shi, ta kira shi ne kawai ba dan tana da abun cewa ba, kuma bata san zai ji ta ba, tun da ta saba kiransa kwana biyu bata ji shi ba. Da hannu yai mata alama da ta zo sai ta kanne kafada alamar ba zata zo ba, ta girgiza masa kai. Zaunawa yai a gurin ta dauke kai daga barin kallonta. Hakan yasa zuciyarta ta raya mata cewar ko aljani ne shi ba zai cutar da ita ba tun da har mafarkinsa take. A da idan Inna tace mata tai addu'a sai tace mata wuya take ji, amman a yau da take son zuwa kusa da shi sai da ta tsaya ta karanta addu'oin data iya sannan ta tunkareshi tana takawa kadankadan kamar mai tsoron ya ji takunta, kansa na kasa har ta kawo kusa da shi ta risina ta leki fuskarsa, sai ya sakar mata murmushi ita kuma tai masa dariya irin dariyar nan ta dole kuma ta tsoro wacce mutum ke yi a rikice. 


“Kai aljani ne?”


“Aa”


Ya amsa mata yana dagowa ya kalleta da kyau. 


“To miyasa na ke mafarkinka?”


Kallonta kawai yake irin kallon nan na son tantace gaskiyarta. Kamar tasan irin kallon da yake mata sai tace. 


“Wallahi ba karya na ke ba, ina mafarkin, da wani mutum kuma da wani kana rike da wannan abun busar kana busa amman kullum baya kake bani, shiyasa lokacin da na ji busarka na zo har nan dan gani idan da gaske ne, kuma busar iri daya ce”


“Ni ba aljani ne bane”


Ya fada cike da mamakin mafarkinsa da tace tana yi. 


“Kuma tun lokacin nan nagge bata sake mutuwa ba, miyasa kake saka wannan abun”


Ta nuna warkin dake kugunsa, sai yai murmushi. 


“Haka muke, kayan garin mu”


“Ina ne garin ku?”


“Garuk”


Ta gwala ido tana matsowa kusa da shi, sai a lokacin ta tuna da taba jin labarin garin ance mutanen ciki basa saka tufafi kuma matsafa ne.

Ta zauna a kasa tana kara kallonsa.


“Kai kake min tsafi nake mafarkinka kenan?”


“Aa”


“Ya za'ayi na tabbatar da kai mutum ne?”


“Idan kika taba jikina za ki ji shi kamar na ki, idan na aljanine za ki jishi da sanyi ko taushi ko gashi ko kiji kamar ba hannun mutum ba”


Dan matsawa tai kusa da shi, sai ya miko mata hannunsa ta taba sannan ta taba nata, sai ta ji shi normal kamar ita. Amman hakan be sa ta gansu ba. 


“Ka yanke kanka na ga jini sai na yarda”


Wannan karon dariya yake, a ransa yana mamakin wauta irin nata taya zata ce ya yanka jikinsa. 


“Samo min kare ko dutse mai tsine”


Ba musu ta tashi taje ta samo masa, ta kawo ta zauna kusa da dan tabbatarwa idan da gaske yankawan zai yi ko a'a. 


“Miye sunanki?”


“Fadime”


Ta amsa mashi tana kallonsa da manyan idonta masu haske da daukar hankali. Murmushi yai ya mike hannun na dama ya saka hannunsa na hadu ya karkari hannunsa na dama kadan jini ya dan fito. Da sauri ta rufe ido tsigar jikinta na tashi. 


“Innalillahi, da gaske ka yanka ni wasa nake maka fa”


“Ba hakan zai sa ki yarda da ni ba”


Ya fada yana kallon gashin kanta. 


“Na yarda”


Ta fada bayan ta bude idon. 


“Miye sunanka?”


“Wasim”


Haka ta fara masa tambayoyi kala kala yana bata amsa, duk abun da ta tambaya sai ya bata amsa, tun tana da sauran tsoron har ta sake jiki da shi. 

Har da karbar sarewarsa ta busa, sai nata busar bata fita saboda bata iya ba. Har sai da ya karba da kansa ya fara busar tana ta kallonsa cike da burgewa. 


“Waya koya maka?”


“Wani tsoho”


“A ina yake?”


“Garinmu”


Ya amsa yana kallonta, mugun burgeshi take, ko wane motsi nata the way da take tambayarsa yadda take sake jiki da shi far'arta kyauta and everything. Ta gyada kai tana murmushi, da yamma lis ta koro shannun ta sako su a gaba ta jeru ita ta shi suna tafiya, sai ya rakota har kusa da hanyar gidansu sannan ya tsaya ita kuma ta daga masa hannu, shi ma ya dago mata sai ta juya ta cigaba da tafiya sai kwasar dariya take. 

 Daman tun dazun take jin dariyar take son ta yi ta kasa, wai basa saka rika kuma basa son shiga cikin mutanen da na nasu ba, gaba daya kallon mahaukata take musu. 


Sai ta kai shannun gida ta shigarda da su gurin da aka saba ajesu, sannan ta sunsuda ta fita, sai da ta kama hanya sannan ta hango Bappa tafe tare da wani makocinsu, da sauri ta boya bayan wata bishiyar dogon yaro. Kasancewar bishiyar katuwa yasa Bappa da mutunen ba su lura da ita ba, domin gaba daya hankalinsu baya gurin yana kan abunda suke tattaunawa ne. 


“Gaskiya ina baka shawarar ka kara aure kawai”


Shine kawai abun da ta ji, duk da bata san abunda ake tattaunawa akai ba, amman tabbas ta ji Bappa na ce masa ya kara aure, a gurin tai ta tsayi har sai da suka karyar kwana sannan ta fito yana girgiza kai tana dariya. 

  Juyawa tai ta canja hanya zuwa gidansu Ma'u, ko da ta shiga ta samu Ma'u na alwala sallah magariba, sai ta risino kusa da ita.


“Ma'u nan da kwana biyu mijin Ande Hanne zai fara maganar aure ce ni na fada miki”


Ma'u ta kalleta da sauri. 


“Aljanin ne ya fada miki?”


“Eh, yau da naje kiwo ma a fili ya ganshi yace zan rika ba da magani zan rika fadawa mutane komai”


Ma'u ta kara zaro ido gaba daya ma sai ta ji tsoron Fadime ya fara kamata.


“Da gaske?”


“Allah amman karki fadawa kowa”


“Ba zan fada ba”


Gaba daya tsoro ya gama kama Ma'u, Fadime ma ta lura da hakan kuma ta jidadi, ita gaba daya tun da Inna ta fada mata masu magani kudi ake ba su su fadawa mutum matsalarsa ta ji tana sha'awar abun. Haka ta kwana da tunani kala kala na irin karyar da za ta yi ma Inna ta yarda ta fara bada maganin.


Sai da Fadime ta gama karyawa da fura mai tsami sannan ta zauna saman tabarmar da Inna ke zaune tana gyaran gida. 


“Inna na sake mafarkin aljanun nan sun ce zan bada magani fa”


Inna ta daka mata tsawa. 


“Fulani kar na sakd jin maganar nan a bakin ki, da kin sake maganar nan sai na fadawa Malam”


Da sauri tace. 


“Na bari”


“Gashi kije ki debo ruwa”


Ta tashi da sauri ta nufi inda tulun daukar ruwan yake ta dauka ta fice da sauri ta nufi gurin deban ruwa, tasan Bappa sarai be son irin abubuwan nan. Tana tafe tana wakewaken har ta isa, sai da ta duka ta fara cikon ruwa sai ta ji a na kirata.


“Fadime”


Da sauri ta juyo suna hada ido ta sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake mata murmushi. Tsaye yake nesa da ita.


“Ashe kana zuwa nan da safe”


Ya gyada mata kai yana karasowa kusa da ita, har yanzu bata daina jin tsoro ba sai dai ba kamar na da ba. 


“Ruwa kike deba?”


“Eh”


Ta fada tana dariya sannan ta duka ta cigaba da cikon, sai kuma ta juyo ta kalleshi. 


“Dan Allah ka taimaka min ka min wani abu”


“Minene”


“So na ke idan na cika tulun nan, ka masa tsafi tun da ku matsafa ne ai zaka iya ko?”


“Saboda me?”


“Saboda Inna ta yarda cewar ina mafarkin aljanun, so na ke ka masa tsafi sai na je gida na aje tulun sai ruwan su zama maciji”


“Ba ki jin tsoro?”


“Ai ba anan ba sai na je gida, amman ka min alkawarin ba za ka cutar da ni ba”


“Ko wani ba zan bari ya cutar da ke ba”


“To ka min ka ji”


Ya daga mata kai. Sai da ta cika tulun dam sannan ta matsa tace yai mata ita dai burinta kar Inna ta karyartata, burinta Inna ta bata hadin kai ba sai Bappa yaji ba. Matsawa yai kusa da tulun ya saka hannunta yana ta kallonta be wani dade ba ya cire sai ta zaro ido. 


“Yanzu shikenan da naje gida zan ga ruwan ya zama maciji?”


Ya daga mata kai alamar Eh yana ta kallonta, sannan ya tallaba tulun ya dora mata saman kai, tsakanin dora mata tulun da fara jin motsin abu mai rai a cikin tulun be yi minti 1 ba. 

Yana kallonta sai ta fashe da kuka.


“Ba yanzu na ce ba, Wayyo Bappa wayyo Bappa wayyo Bapppa”


Sai fitsari, ta fara kukan da gaske gasken hawaye kamar ruwa.


“Idan kika sauke tulun macijin ciki zai cijeki, karki sauke sai kin isa gida”


Ya fada yana dariya. Gaba daya jikin Fadime rawa yake kafafuwanta sai lankwashewa suke kamar zata fadi, numfashinta ya fara sama sama, faduwa tai kasa ta fara rarrafe dan bata ma iya tafiya, haka nan ta isa gari duk da bata zanenta da zawo sai kuka take tana kiran Bapppaa, ga tulun saman kanta. Duk wanda ya kalleta sai ya ganta da tulu saman kai ga kan maciji ya leko, mutane sai gudu suke, kamin ta isa gida har ta canja kammani. 


“Bappppa wayyo Inna na bani na taro aljalina”


Ta kasa tashi tsaye gani ba take idan ta mike macijin zai iya saukowa, mutane aka fara taruwa ana kallonta tai zaure a kasa sai rusar kuka take fuska duk da bace da majina da hawaye zuciya kuma kamar ta fashe dan tsoro, ita gaba daya bata dauka ma da gaske yana iya yin tsafi ba sai yanzu.


“Mike tsaye ki zafar da tulun”


Kowa abun da yake fada kenan, ita kuma babu kuzarin mikewar tsaye gashi yace mata idan bata isa gida bata sauke zai cijeta. 


“Yace sai na kai shi gida, ku dauke ni ku kai ni gida, wayyo Bapppaa na wayyo Bapppaa”


Ta fada tana ta yarfe hannu, idonta har ya kumbura saboda kuka. 


FALMATA POV. 


Da tunani kala biyu Falmata ta isa gida, tunanin saukin kai da jindadin kadeta da M2 yai ga kuma kiranta da Ammy tai ta mata tambayoyi, ko miyasa tai mata haka oho. Sosai ta so ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta labarta mata yadda ta ga M2 sai ta tuna da Baba ya mata iyaka da gidan. Hakan yasa tai hanzarin cira kafa ta isa gida, da zimmar ta gama aikinta dan ta samu isa Islamiya da wuri ta labarta musu. Ko da ta isa gida har Gambo ta sanar da sakon Ammy ta bar gidan dan ita abun hawa ta hau ba kamar Falmata ba da take tafiya a kafa. 

  Falmata na isa ta manta da wani kunci da tsoron fada ko wani abu, ta hau bawa Naja labarin yadda ta ga M2. 


“Dan Allah matsa can mahaukaciya, hala M2 ne banza da zaki ganshi a bagas, sannu kakar farin jini, dan kin ji ana cewa kina da farinjini shine kike wani karya kin ga M2 mahaukaciya”


Ko kadan bata ji abun da Naja ta fada ba, amman a yanayin yadda take harararta take jan tsaki tasan karyarta tayi, hakan yasa Falmata ta kara boye hular da ya bata a cikin jikinta ta mike tsaye cikin rashin jindadi ta nufi dakinsu. Tumba dake zaune bakin kofar dakinta ta bushe da dariya. 


“Wallahi yarinyar can ta fara haukacewa, mugun son M2 da take ne yasa ta fara ganin mutane na zame mata haka”


Naja ta ja tsaki. 


“Ko mai wankewa M2 takalmi ta isa ta gani balle M2, ita fa yadda ake fadar tana da farin jinin nan wani jin kanta take”


“Kira min ita”


Tumba ta fada tana dariya, daga inda Naja take zaune ta kwala mata kira. 


“Ke kurma zo ana kiranki”


Falmata har cikin ranta ta ji sunan, wani abu na rashin jindadi ya ratsa zuciyarta, ta saka hular M2 can ciki bakkon kayanta sannan ta fito ta tsaya bakin kofa jiki ba gwari tun da babu wani abincin kirki a ciki. 


“Ke yar kurma, dazun Gambo ta zo tace zaki rika wuni can kina rainon yara”


Tumba ta fada mata tana mata alama irin na kurame. Naja ta saka dariya. 


“Ban cin kurmanta har da hauka na son kamaki, kin fara ganin mutane kina ce musu M2 ko?”


A nan ma Tumba ta saka mata dariya, a gurin Falmata ta duka ta fashe da kuka, ba karyatata da suke take ji ma ciwo ba, kiran da kurma da suke a yanzu. 


“Ji munafuka salon a shigo ace wani abu Umma tai miki kike kuka mu kuke dariya ko? Da shegen baki kamar zunubi”


Naja ta fada cikin tsawa, sai Falmata ta mike tsaye ta shige dakinsu ta cigaba da kuka tana rufe bakinta dan kar sautin kukanta ya fito. 

 Sai da tai mai isarta sannan ta fito ta zuba surfe ta fara, sai da ta surfe tiya da rabi sannan ta shiga tai wanka ta saka uniform dinta na Islamiya ta dauko qur'ane ta da littafai ta fice. 

  Kusan kullum cikin rashin jindadi taje zuwa makaranta, saboda rashin jin da take a yanzu, idan akai karatu sai Khadija ko wata ta rada mata abun da Malam ya fada a kunne sannan ta ji, sai kuma idan Malamin yayi da karfi, Falmata ba yarinya ce mai yawan surutu ba, amman hakan be hanata fadawa yan ajin su cewar ta hadu da M2 ba, most of them sun karyatata wasu na fadin dan dai tana son shi sosai ne yasa ta ga mai kama da shi. 

 Haka dai ta bar Islamiya cikin rashin jindadin yadda suka karyarta daman ta san ba za su yarda ba, ita ma dai a lokacin ta fara kwankwanto da gaske M2 ta gani ko mai kama da shi? 

 Ko da ta iso gida sai ta tararda wani tashin hankali, yaron da aka aiko yana tsaye yana jiran dawowarta Tumba kuma ta yi wani shegen zama tana rawa da kafa. Ta shigo da sallama Tumba ta hau ta da matsifa. 


“Ashe Falmata zuwa kike kina cin bashin garin kwaki a shago da sunana?”


Dakan shida-shida gabana yai, ta sani yau asirinta ya tonu, tabbas tana zuwa karba kuma idan ta je Tumba take cewa saboda tana jin kunyar tace ita zai bawa bashin gari. 


“Saboda asan ba a baki abinci ko kuma dan ki bata min suna ni da ubanki? To ya aiko yace a bashi kudinshi bari ubanki ya dawo sai kin fadi dalilinki na bata min suna”


Kamar an tureta haka ta fadi gaban Tumba kamar mai neman gafara hawaye sai sallama suke a fuskarta.


“Dan Allah dan darajar Annabi karki fadawa Baba Umma, ki rufa min asiri, zan samu kudinsa yanzu na bashi, ki yi hakuri Umma ba zan, idan na sake ki kashe ni, Umma wallahi yunwa take damuna shiyasa na ci bashin amman daga yanzu ko zan mutu ba zan sake ba, na rantse da Allah Umma, dan manzon Rahama ki rufa min asiri Umma ba zan sake ba har abada”


Tumba ta fisge kafarta tana kallon. 


“Tafi idan Babanta ya dawo za a fada masa”


Yaron ya juya ya fice, sai Falmata ta mike tsaye da sauri.


“Na bani na lalace na shiga uku wayyo ni Allah na Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Ta furta ta karfi kuka na subuce mata, sai ta saka hannunta da sauri ta rufe bakinta, da gudu ta shiga dakinsu ta fada kan shimfidar da take kwana. 


“Wayyo ni Allah na yau asiri na ya bonu, wayyo Mama Mama ina ma ni na mutu ba ke ba, Allah ka karbi raina kamin Baba ya dawo Allah na shiga uku”


Ta fada tana yarfe hannunta hawaye sai zubo mata suke kamar ba gobe. ZAINAB POV. 


Ta dan yi shiru sannan tace. 


“Na ce mishi ya bari har na dawo daga tafiyar da zan yi”


Ammy ta kalleta. 


“Ni fa ina tsoron lafiyar nan Zainab, kin san kasar ba wani tsoro kuma ki ce za ki je garin cikin mutanen da ake fadar basa saka tufafi? Kina ganin ma za su aminta ki dauke su hoto ne?”


“No ba wai kai tsaye zanje can ba, zan sauka garin dake kusa da su ne, nai magana da mutanen tukuna sai na isa garin, kuma ko ban samu zuwa can ba ai ance akwai manyan duwatsu a kusa da su da ruwa, kuma ance akwai Fulani irin masu yin bukka da gidan zana su zauna a kusa da su, ko da ban samu isa can ba na san ba zan sara abun dauka ba”


“To Allah dai ya tsare”


“Amin, Ammy dan Allah ki mata magana, ban zan abun da mutunen nan yai mata ba, ta ki ta saurare ni, ni kuma ina son shi, shi yanzu yace yana son ya turo kuma ya sanar a gidansu amman sai ya samu tabbaci daga gareni”


Ammy ta yi murmushi. 


“Karki samu damuwa, zan yi magana da ita, idan ta aminta sai a sanarwa yan'uwan mahaifinki”


“Na gode Ammy”


Mikewa tai tsaye tana sanye da riga da wando English wears, kanta sanye da dankwalin nan da ake yayi blue.


“Bari na duba dakinta idan tana nan sai na turo miki ita”


Kai kawai Ammy ta daga mata, ta maida dubanta gurin tv dake dakinta, kallon kawai take amman hankalinta baya can, bata da damuwar da ta wuce ta Mai Martaba a yanzu, a iya tunaninta ta rasa gane abun da yake damunsa, gashi idan an gwada yi masa na hausa sai abu ya karu a maimakon raguwa. Kiran wayarta nd ya katse mata tunanin da take, sai ta mika hannu ta dauka.


“Assalamu Alaikum”


Ra'ees ya amsa daga dayan bangaren. 


“Wa'alaiki-Assalam, Ammy barka da yamma”


“Yauwa Ra'ees ya gida”


Ta fada cike da kasaitar da ta zame mata jiki. 


“Al-hamdulillah Ammy an samu wata, amman dai ba mu je, sai dai marikiyar yarinyar tace zata iya aura masa ita”


“Ka fada mata matsalar sa ne?”


“Eh ta ji komai, firar ma ta ji muna yi shine tace tana da ƴa zata ba shi, amman dai ba mu je ba tukuna”


“To yayi kyau, amman fa ba sai kun bayyana dan wane ba, kuma ka yi duk abun da ya dace, karka bari Shattima ya ji komai, sai an kammala yadda ba zai iya ce mana aa ba”


“In-Sha-Allah Ammy”


“Na gode Allah ya maka albarka”


“Ameen”


Tana kokarin aje wayar aka kwankwaso kofar dakin kamin a turo a shigo. Hajiya Balki ce Nana na biye da ita a baya, a baki kofa ta tsaya tana kallon Ammy sai cika take tana batsewa. 


“Yanzu an kyauta kenan? Sai a dauke yarinya akaita gurin Waziri bayan kin san ita da Waziri ba jituwa suke ba?”


Ammy ta kalleta da mamaki kamar ba zata ce komai ba.


“An kaita gidan Waziri kamar wacce aka kai gidan yari? Kanen ubanta ne fa”


“Na san kanen ubanta ne ai, amman tun da bata son zuwa ai sai a kyaleta”


Ammy ta dauke kai bata sake ce mata komai ba. Ganin hakan yasa ta juya ta fita Nana kuma ta zauna saman kujera tana matsar yatsun hannunta tana kallon Ammy. Ko da wasa Ammy bata kalle inda take ba har ta gaji dan kanta tace. 


“I'm sorry”


Ammy ta watsa mata wani mugun harara. 


“Dakinki dai kike so ko? To gashi can idan kin mutu a haka rame a saka ki a ciki, tashi ki fata”


“Ammy ki yi hakuri....”


Bata karasa ba Ammy ta daka mata tsawa.


“Get out”


Ba shiri ta mike tsaye jikinta na rawa ta fice daga dakin tana fashewa da kuka. 

_________________


Al-hamdulillah, a nan na kawo karshen free pages, duk mai son cigaban wannan labarin ya biya 300. Pages din da za su biyo bayan wannan na kudi ne ba kyauta ba, ko kun ganshi a waje na sata ne. 

Patronize me if ku masoyana ne na gaskiya, show me that love.


Son so Fisabilillah.

No comments

Powered by Blogger.