Fulani 13


 *13*


Tun ranar da Fadime ta ji ga mutumen nan mai busa bata sake ganinsa ba, hakan kuma be saka ta fasa zuwa gurin manyan duwatsun ba a kullum tana leka ko zata

ganshi. 

Kuma tun ranar bata sake jin busar ba, bata sake mafarkinsa ba, a lokacin ne ta fara rayawa a ranta cewar aljani ta gani kuma shi take mafarki. 

Kasancewar yau friday da safe ta fito da shanun kiwo, daman duk Friday da safe take kiwon kasancewar jumma'a kurarren lokaci ne. Shanunta na gaba tana biye da su, kanta sanye da malfar saƙa, ta daura zare a wuyanta da gaban goshinta, dan karamin kare na binta hannunta rike da sandar korar shanu bata fasa wakewaken da Inna take hanata ba. 

Sai da suka isa bankin rafi sai ta nufi inda ta saba zama, ta zauna tana hango wasu shannun da wani bafullatani dake can nesa da ita yake kiwo. 

Kanne ido daya tai ta fara kirga masa shanu daga inda take zaune, sannan ta dawo kirga nata. 


“Nawa sauran 37, idan wata ta sake mutuwa yau sauran 36 idan wata ta kara mutuwa sauran 35...”


Bata karasa kirgen ba ta soma jiyo busar sarewar tana karade dajin. Bude baki tai ta zaro ido ta fara dukuduku ta ratsa cikin marar sannan ta mike tsaye tana leken inda ta fi jin busar na fitowa, sai kuma tai dukuduku ta dawo ta haye saman dutsen ta mike tsaye. Hangoshi da tai a saman wani dutsen zaune yasa ta kara gwale idon. 


“Kai...........”


Sai ta ji muryarta ta amsa duka dajin da kiran da tai masa. 


“Laaaaaaa”


Ta yi dariya, wani dadi taji yadda ta ji muryarta ya gwauraye dajin, a yanzu ta gano dajin ne ke da daukar sauti. Saukowa tai saman dutsen da sauri ta fara gudu tana daga kanta sama tana hango dutsen da yake zaune, kamar wacce aka koro haka take yankan dajin tana gudu har ta isa gaban katon dutsen a lokacin ne ta ji sautin busar sarewar sosai a kunnenta, labewa tai jikin dutsen tana dariya marar sauti tana kara zaro ido. 


Gaba daya ta manta da wani zancen aljani ne ko mutum, sai ta dan lekesa ta sake boyewa tana dariya har da su kyakyatawa kadan ta rufe bakinta.  

      Zaune tai a gurin tana ta sauraren fusar sarewar dake shiga kunneta, har da wani lumshe ido take tana budewa. Lokaci daya ta daina jin busar saurara tai na dan lokaci ta ji ko za a cigaba, shirun da ta ji ne yasa ta tashi ta leka sai ta ga babu shi a gurin, hakan yasa ta fito gaba daya tana kallon dutsen. 


“Ina yaje?”


Ta tambayi kanta tana tare hasken ranar dake haskata da hannunta, domin malfar dake kanta ta fado bayanta igiyar malfar ce kawai a wuyanta, kara natsawa tai tana rabon ido, sai ta hangoshi yana saukowa saman dutsen. Saurin komawa tai ta boye tana yarfar da hannunta tana dariya da jindadin ganinsa da tai. Amman da yake saukowa ina zai je? Gurinta ko wani guri? Ta dan zaro ido kamin ta kara shan jinin jikinta jikin dutsen tana saurare ko zata ji takun tafiyarsa ko motsin wani abu, amman sai ta ji shiru hakan yasa ta fara takawa kadan kadan ta leka sai ta ganshi tsaye yana kallon inda take kamar daman can jiran yake ta leko ya ganta, da sauri ta koma sai a lokacin ne tsoro ya fara kamata. 


“Wayyo Bapppa.....”


Ihun da tai ne yasa ya karaso kusa da ita yana kallonta, hannunsa rike da sarewa, sai dan walkin dake daure a kugunsa, fari ne sol kuma kyakkyawa gashin kansa ya kwanta luf kamar bafulatani idonsa ma fari kal kamar madara ga dogon hancin daya kara kawata fuskarsa. Dukewa Fadime tai kasa ta rufe ido tana kuka. 


“Bapppa.....”


Bappan kawai take kira kamar ance mata zai ji ta daga inda take, tasa hannayenta ta rufe fuskarta sai rusar kuka take kukan da ba hawaye. Shi dai kallonta kawai yake cike da burgewa ba yau ya fara ganinta ba, kusan a duk lokacin da ya bar gulbin dake kusa da garinsu ya iso wannan dan yi wwanka ko yin wani abu sai ya ganta ta zo kiwo ko deban ruwa, sai dai ita bata taba kula da shi ba sai a yanzu da yake busar kusa da inda take ji. 

Jin be mata komai ba yasa ta dago ta kalleshi kadan ta runtse ido, gabanta sai dukan tara tara yake. 


“Bapppa”


Ta kira sunan Babanta da kuka, sai kuma ta sake bude ido ta kalleshi yanzu kuma so take ta tantace mutum ne ko aljani. 


“Ban maka komai ba, ni ban maka komai ba, ni mutum ce ni ka yi hakuri ba zan sake ba”


Bayan kallonta babu abun da yake, matsawa tai baya tana yi tana kallon gefensa inda hanya take sai kuma ta kallesa, cikin wayo ta zo da mugun gudu ta taba shi da yatsanta ta daka wani uban tsalle tana son ta ranta a na kare, sai yai hanzare cafko hannun nata ya rike gam. Wani irin shidewa tai ta dawo ta bude ido sosai tana kallon hannunsa da ya rike ta da shi tana bude baki kamar zata kwala ihu kuma ba tai ihun ba, sai ta sulele kasa tana wani jan numfashi, so take ta suma kuma suman be zo mata ba. Dayan hannunsa yasa ya rikota ya jinginar da ita jikin dutsen tana kallonta. 


“Bapppa...”


Ta sake kwala masa kira. Uffan be ce mata ba sai kallonta yake duk ganinta da yake bata taba burge shi ba irin yau, he never thought haka take da wauta sai yau and he like it. 


“Bapppaa Na...... ”


“Wuta na binki ba ki gani ba....?”


Ya fada cikin siriyar muryarsa mai dadin sauraro yana daga mata kai alamar ta duba. Cikin wani irin tsoro marar misaltuwa Fadime ta waiga kasanta.


“Ba wuta dutse ne”


Ta fada numfashinta na rawa domin a yanzu kam da gaske tsoro take ji. Matsowa da ita yai kusa da shi kamar zai rumgume ta dan filin dake tsakanin bayanta da dutsen yai wani abu da hannunsa kamar zai kama abu ya cafke hannunsa ya jimke sai ga wutar tana ci a cikin hannunsa. 

Kadan Fadime ta juya ta ga wutar sai ta kara bude ido ta kwala ihu. Shi kam kallonta kawai yake har tai ta gama sannan ya juya ya fara tafiya. 


“Kai a aljanine?”


Ya girgiza mata kai alamar a'a. 


“Kai ka saka min wutar?”


Nan ma kan ya girgiza. 


“Ya akai ka ga wutar waya saka min wutar?”


Daga inda take tsaye take aiko masa tambayoyin cikin daga murya ta yadda zai ji ta, sai a lokacin ya juyo ya kalleta sai tai saurin rufe fuskarta da hannayenta. 


“Wutar maita ce, mayu suke sakawa mutun ita, idan mutum yana da baiwa sai su kwashe ta su saka masa wuta, komai ya rika ko ya taba ba zai yi albarka ba, ba zai amfane shi ba, idan suka kasa cin kurwarsa sai su daddanketa mutum ya koma wawa ko mahaukaci ko musaki, akwai wanda ke bibiyarki”


Yana fada mata haka ya juya ya cigaba da tafiyarsa yana murmushi, fitowa tai tana kallonsa har ya haye saman dutsen yai tsaye yana kallonta, daga inda take tsaye ta daga masa hannu shi ma ya dago mata sannan ya gangara ya sauka ta arewa da dutsen. 

A lokacin ne ta samu kafafuwan gudu ta dawo gurin kiwon shanunta ta zauna tana ta tunanin abunda ya fada mata. Har ta gama kiwonta nagge ko daya bata mutu ba, cikin jindadi ta kora shannun suka nufi gida, kamin su isa gida duk ta matsu, suna isa bata ko tsaya saka hannun ciki gida ba, ta shige Bukkarta ta dauko littafinta ta fara rubuta abun da ya faru, sai da ta rubuce komai tsaf sannan ta fito waje tana neman Inna ta labarta mata. 


FALMATA POV. 


Tana cikin wanke wanke ta ji Tumba a bayanta tsaye, juyawa tai da sauri ta kalleta, sai Tumba ta risino daidai kunnenta tana fadin


“Wai ke Falmata ba ki da irin samarin nan masu yi ma budurwa anko? Kullum suka zo ba su da abun yi sai kawo miki abu a leda ko su baki yan kudi a hannu, haba Falmata ki rika sakin jiki mana”


Cike da damuwa Falmata ta sanda kanta kasa, ta fahimci inda Tumba da dosa a yanzu. 


“Ke baki ga sauran yan mata yadda suke ba? Ki rika sake musu jiki da fuska kinji kina far'a samari suna son mace mai far'a”


“To”


“Yauwa yau duk wanda ya zo ki ce ya baki dubu uku ko biyar, in dai kina kawo min kudi haka zan rika miki komai”


“To”


Ta sake amsawa a ranta tana mamakin yadda Tumba take son ta zama, ta rasa me ta tare mata a dubiyar da bata son farincikinta, yau kwana uku kullum sai dare ya raba take satar kafa ta fita taje shago ta ci bashin garin kwaki ta saka a cikinta, sakamakon abincin da ba a bata a gidan. 

Yanzu kuma tana nuna mata wani mugun hali wanda ba halinta ba. Tana wanke wanke tana hawaye, sai ta share ba tare da ta bari Tumba ta gani ba, haka tai aikin cikin rashin kuzari sannan ta fara shara, ta bi ko'ina na gidan ta masa tas, ta dawo ta zuba ruwa a bokiti ta shiga bandaki, ta nan ta samu damar kuka iya son ranta tana tuna irin gargadin da Mama ta yi mata kamin rasuwarta. 


“Wannan farin jinin na ki kar ya kai ki ga halaka Fulani, tun kina yar jaririya Allah ya saka miki farin jinin jama'a yanzu kuma kin tasa samari sun fara miki sallama, bana son zuwa firar nan karki sake fita duk wanda ke son ki da gaske ya aiko gurin mahaifinki, kuma kin ga kin fara al'ada ko hannunki kika bari namiji ya rike za ki iya samun ciki, dan zai ja a wuce guri, karki kuskura bari a rike hannunki”


Fashewa tai da kuka ta rufe bakinta dan kar kukan ya fito, farar fita zance da samari da take, bayan mutuwar mahafiyarta ne, wanda Tumba take bata umarni, tun tana jin kunya tana boya tana rasa abun fada har ta waye, ta iya magana da tarbar wanda ya zo gurinta. Yanzu kuma tana nuna mata hanyar da ba mai bullewa ba ce, taya za ta ce a bata kudi mai yawa haka? 

Cikin rashin kuzari ta gama wankan ta fito ta shiga dakinsu ta shirya cikin wani farin yadi ta saka hijabinta ta fito tsakar gida. 


“Na tafi”


“To Allah ya tsare yar albarka”


Tumba ta fada cikin daga muryar tana washe mata hakora, Falmata ta dauke kai ta fara tafiya kamar bata son zuwan ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta. 


“Na rasa yadda zan yi da yarinyar nan, komai nai mata kamar ban yi ba, kowa nai ma ya kama ban da ita, ban san me shegiyar uwar nan ta bata ba, kudi kawai na ke kashi a banza”


Tumba ta fada tana rafka uban tagumi, tana tuna abunda Malam na zaure ya fada mata game da Falmata.


“Idan ba ki yi da gaske ba, yarinyar sai ta gawurta, ina ji miki tsoron abun da zata zama nan gaba”


Wani dogon ajiyar zuciya ta ja ta sauke.


“Na rasa yadda zan yi da yarinyar nan idan nai wannan a banza, wacan a banza”


Ta furta cike da jin zafin irin kudin da ta kashe akan Falmata amman har yanzu shiru, farinjinin da take son ya gushe ba daina ba, abu ma kamar ƙaruwa yake. 

Falmata na tafe tana tunanin maganganun Tumba, wace karya zata mata ta tsira? Idan ma bata kawo mata kudin ba zata iya dukanta ko ta mata wani sharin. Bata hankara ta ji an taka burki da karfi wani abu ya bugeta ta fada can gafe, da sauri ta rike kafarta da bata warke daga daurin da Baba tai mata ba, yau kuma ta sake jin ciwo a kafar, da sauri Sirleem ya fito daga motar ya karaso inda take. 


“Ba ki ji ciwo ba? Ina ta horn ba ki lura ba”


Baki sake take kallonsa idonta kamar za su fito gaba daya ta manta da wani ciwo a kafa, ta masa yardar Sirleem take gani da gaske shi? Ko mai kama da shi. 


“Sannu ba ki ji ciwo ba?”


Yana tambayarta ta kuma ta kasa amsawa sai kallonshi take tana ganin abun kamar a mafarki, daman kuma ba jinsa take ba tun sai an yi da karfi take iya ji. 


“Hey”


Ya kada mata hannunsa a fuska sai a lokacin ne ta dawo hayyacinta, a lokacin ne mutane suka fara taruwa kallonsa da kuma ganin abun da ya faru. Rawa jikinta ya fara yi idonta ya cika da kwalla bata san lokacin da ta riko hannunsa da sauri ba. 


“Dan Allah kai ne Sirleem M2 ko kama ce kawai”


Kallonta yake for few seconds sannan ya ce.


“Ni ne”


Tana kallon yadda bakinsa ke motsi da yadda ya nuna kansa ta san magana yai, amman bata ji komai ba saboda be yi da karfi ba, gashi kuma tana son jin muryarsa. 


“Bana ji sosai sai ka fada da karfi, dan Allah kai da karfi na ji muryarka kanji”


Ta sakin hannunsa tai ta rike kafafunsa ta fashe da kuka. 


“Ni ne”


Ya amsa mata da karfi yadda zata ji, ta ji muryarsa sai dai akwai banbanci a tsakanin muryarsa ta cikin waka da kuma ta zahiri, amman tabbas kamaninsa da wacan Sirleem din ba su da banbanci tun daga kan sajen har farin da tsaye da iya wanka.


“Wallahi ina matukar son ka, ni masoyiyarka ce sosai, ina kaunar wakokinka, ban tunanin Allah zai hada ni da kai cikin sauki haka ba, na gode na gode da ka kade na yafe maka na yafe maka Wallahi ina kaunar sosai”


Jikinta har rawa yake sanadin kallonsa da take, hawaye kuma suna ta aikinsu a fuskarta, har yanzu ta kasa yarda ba mafarki take ba. 


“Ko dai mafarki na ke yi”


Ta tambayi kanta tana taba fuskarta, sai yai murmushi ya cire facing cap din dake kansa ya saka mata akai saman  Hijabinta, yana girgiza mata kai alamar a'a ba mafarkin take ba fuskarsa da murmushi. Hannunta ta kai ta cire hular daya saka mata ta rumgune hular tana kuka, a nan wasu suka fara tsaki suna fadin wai abun ta yayi yawa sai kace wacce ta ga wani sahabi ko Annabi, ita kam ta san me take ji a kan Sirleem kuma ganinsa da tai a yau yasa ta kasa yadda ma a duniya take. Hannu yasa aljihunsa ya ciro wallet dinsa ya ciro kudin da za su kai 5k ya mika mata, sai tai saurin girgiza kai. 


“A a ni bana son kudi, na gode da ka kide ni, na gode na yafe maka”


Kai kawai ya kada mata daman kuma be jin zai iya kara ce mata wani abu tun da sai an yi magana da karfi zata ji, sai ya sara mata ya nufi motarsa ya bude ya shiga masu aikin daukarsa a hoto suna ta yi, da kallo ta bishi har ya tashi motar ya hau titi. Sannan ta mike tsaye ta saka hullar cikin hijabinta tana jin wani irin farinciki a ranta marar misaltuwa. Gaba daya ta manta da wani tunani da bacin rai, sai laleben hular dake kamshin turarensa take tana jan numfashi tana saukewa, yadda zata labartawa yan islamiyarsu da kawarta labarin yadda ta ga Sirleem yau kawai take tunani, har ta isa masarautar murmushi be gushe daga fuskarta ba, ji take kamar yanzu komai ya faru. Zancen wani haduwa da Iya da fargaban da take samunta idan zata shigo gidan duk ta manta sai murmushi kawai take tana jindadi a ranta. Door bell ta danna sannan ta samu guri ta zauna a gurin tana jiran a bude mata kofar, after like ten minutes aka bude kofar. 

 Mikewa tai tsaye sai tai arba da Iya hakan kuma ba karamin fadar mata da gaba yai ba, a take murmushin fuskarta ya gushe, Iya sai kallonta take irin kallon nan da ke nuna mata komai na jikinta har yadda jini yake gudana a jijiyarta, Falmata ta yi kasa da kanta ta saka cewa Iya ina kwana balle tace ta bata hanya ta wuce. Ba kallon bakinciki abun da ya faru kawai take mata ba har da na kurwarka dake ta yawa a saman kanta kamar fara, irin ta ce mai wuyar kamu, kurwar da ke yin kasa mai kamar hawainiya ita tafi saukin kamu sai kuma wacce take yawo a kasan kafafuwan mutum, wanda wani lokacin kasan kafafuwan mayu suke kallo su kama kurwar mutum. Akwai wance take kamar tantabara ita ma tana da wuyar kamu sai dai bata kai mai kamar fara ba wacce ke fira. 


A take jikin Falmata ya fara wani tsamtsamtsam wanda hakan ke bata cewar ba mutumen arziki bace, a take ta fara karanta addu'o'in da ta iya, sai iya ta kauce mata da sauri tana mata alama da ta shigo da hannunta. Ita kuma tai saurin ficewa daga falon, sai da Falmata ta juya ta kalli ficewarta sannan ta juyo ta nufi hanyar dakinsu yan uku, tana ta mamakin yadda Iya ta rikirice saboda Addu'ar da tai. 


‘Idan zan sake zuwa sai na samu furen tumfafiya na hada da goro na zauna’


Ta fada a ranta dan ta taba jin Tumba na fadar indai mutum yai haka yai arba da maye ba zai iya kallonsa ba. Yau ma bata tararda yaran ba, daman haka ya fi mata dan bata son tai wani abu ace ta yi ba daidai ba. For the first time yau tana ta ji tana sha'awar yin shara tana kirar suratul Baqara, surar da idan ka karanta shaidane sai yayi wata daya kamin ya sake shigowa gidanka, idan kuma ka karanta ayoyi goma na farkon surar a kullum, to kana cikin tsaron Allah babu wani abun da zai same ka, maita ko aljani ko wani shari kuma zaka wuni cikin nishadi. 

  Daga alif lam min ta fara karatun cikin muryarsa mai dadi da kwantar da hankali ga saukarda natsuwa kasancewar qur'ane take karatu, a yanayin yadda ta kare a kirar ma sai ka dauka wata balarabiya ce ba fulani ba. Har ta yi aikin ta gama karatunta take sai da ta gyara komai tsaf sannan ta fito ta janyo dakin ta rufe ta fito daga corridor, bata wani tsaya kula wadanda suke falon ba ta sa kai zata fice, sai Ammy ta kira wata mata dake zaune kasa tana kallon tv. 


“Salamatu kira yarinyar can”


Jikin Salamatu na rawa ta kwalawa Falmata kira tana mikewa tsaye ta nufi inda take. 


“Ke...


Falmata ta juyo a tsorace gabanta na faduwa, ita dai tsoron ta kar ace ta yi wani abu.


“Na'am”


Ta taho da sauri ta zube kasa ta gaishe da Ammy kamar yadda ta lura da mutanen gidan na yi, ko daga kai ta kalli Ammy bata yi saboda tsoron irin an talaka a gaban sarki. Sai ta karaso sannan Ammy ta yi murmushi kadan tana kallonta cike da burgewa, yadda ta ji tana karatun ya matukar burgeta ga natsuwa da kuzari aiki da take ganin kamar yarinyar tana da shi, ina ma ace Nanarta ce a haka. 


“Duk abun da na ce ki rada mata a kunne”


“To ran ki ya dade”


Salamatu ta amsa, sai Ammy ta maida dubanta gurin tv kamar ba zata ce komai ba, ba dan komai ba sai dan isa da kasaita irin ta matan sarakuna musamman idan suna cikin talakawa. Falmata kan cikinta sai kadawa yake tana ta tunanin abun da tai ba daidai ba. 


“Ya sunanki?”


Salamatu ta rada mata, sai Falmata tai saurin amsawa muryarta har rawa take kana jinta kasan tana daf da fashewa da kuka. 


“Falmata”


“Shekarunki nawa?”


“Cikin ta sha bakwai”


“Kina zuwa makaranta?”


“Eh islamiya, bana boko”


“Saboda me?”


“Ba a saka mu ba”


Ko wace tambaya sai Ammy ta bada tazara take yinta kamar mai tunanin wace tambaya zata mata ko kuma mai hutawa sannan yai wata tambayar.

 Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, daman can Falmata shi take jira sai ta tashi da sauri ta fice daga katon falon jikinta har rawa yake. 

Sai da ta fice sannan Ammy ta kalli Salamatu. 


“Tashi ki nemo min Gambo”


“To ranki ya dade Allah ya kara miki lafiya da imani”


Da sauri Salamatu ta fice daga falon, ba a dauki lokaci ba sai ga Gambo ta shigo ta zube kasa ta kwashi gaisuwa. 


“Gambo yarinyar nan da kika kawo tana da halin kwarai ko?”


“Wallahi ranki ya dade ba zan dauko sheri na kawo a cikin iyalanki ba, ina wace ni, Wallahi sai da na duba na dubo na zabo sannan na dauko ta, kaf a unguwar nan ba yarinya matashi kamar ita wacce tai kunya da tarbiyar Falmata, Allah ya mata natsuwa da kamala, ga ilmin kamar ruwa, sai dai ace ba tai boko ba amman na muhammadiya kam babu abun da bata sani ba”


Ammy ta yi shiru har na wani lokaci sannan ta ce. 


“Ma-sha-Allah, ina son ki fadawa iyayenta za ta rika wuni nan tana rainon su Labib”


“To ranki ya dade, yadda kika ce haka za ayi, yanzu ma daga nan can zanje na isar musu da sakon Hajiya, Allah ya kara miki imani”


Da hannu Ammy tai mata alama da ta tashi ta tafi, sai ta mike da sauri ta fice.




***  ***   ***


Hajiya ta sauke ajiyar zuciya bayan Jarma ya gama yi mata bayanin salin inda garin yake, da kuma abokinsa da zai musu jaroganci.


“Jarma ina tunanin kai ya kamata ka fara zuwa, domin kai ka fada masa matsalar ta yarka ce, ganina zai iya gano wani abu, sannan ba zai yiyu na shirya tafiya a yanzu ba, kai ma kuma a nemeka a rasa cikin masarautar nan, za a fara zarginmu”


Jarma ya jinjina kai. 


“Na yi wannan tunanin Hajiya, sai dai jin cewar ba a musu sako sai dai mutum yaje da kansa yasa dole ne mu yi tafiyar a tare”


Hajiya ta yi shiru na wani lokaci kamin ta kalleshi ta ce. 


“Zuwana kamar zuwanka ne Jarma, domin bukatar da nake da ita ita ce a kanka, idan ka je ka ga guri sai mu shirya wata tafiyar daga ni sai kai mu tafi ba tare da abokin ka ba”


“Abokina amintaccena ne Hajiya karki samu damuwa da shi”


“Bana saurin yarda da mutane kai ma ka sani, kuma ka san Shattima a can yake aiki, zai iya ganinmu”


“Haba Hajiya ya za ayi mu yi saken da Shattima zai gan mu sai kace wasu yara dai?”


“Baka san gayyadar da Zainabu ta tara ba ne, shi kanshi ba dan sa ido ne lamurran gidan nan”


“Zan fara zuwan kamar yadda kika bukata, daman can na yi tunanin fara zuwa ni kadai”


“Haka yayi, ka karanta musu komai idan ka je, idan zai yiyu ka shirya tafiyar nan a cikin satin nan”


“Assabar din nan zan tafi In-Sha-Allah, Allah dai ya bamu nasara”


“Amin”


Hajiya ta amsa tana kashe ido daya. Hannunta ta kai ta dauko wayarta ta soma neman number Talba, ta san ko yana a gari ba saba shigowa ya gaishe ta ba kamar Sirleem amman rashin ganinsa kwana biyu yasa ta damu. Ring biyu ya daga, sai da suka gaisa sannan ta ce. 


“Talba ina ka shiga kwana biyu?”


“Ina nan”


“Kwana biyu baka saka mahaifiyarka a ido ba, kuma hankalinka kwance”


“Hajiya idan wani abu ya same ki ai dole a sanar da ni, na san lafiyarki kalau ai”


“Kana da labarin dai za a daura auren Teema ko?”


“Yeah na sani”


“To kai nake son ka wakilci mai martaba”


Ya zare ido kamar tana gansa.


“Wane irin ni kuma Hajiya, kin san ban saba shiga irin abubuwan nan ba, kuma dai ga Baba Waziri ga Baba Jarma ga Shattima sai ace sai ni?”


“Yanzu ina son ka fara shiga, duniya ta san da kai, wannan umarni ne ba shawara ba, idan ka shigo zan mu tattauna akai ya kamata ka fara mika hannu ana yin komai da kai”


“Gaskiya Hajiya ba zan iya ba Wallahi ban saba wannan ba”


“Shiyasa na ke son ka saba din ai”


Ta kashe wayar bata ma tsaya jiran abunda zai fada ba. Idan ba tai da karfi ba, ba zata samu abun da take so ba, a komai sai Ammy ta tura danta ko'ina shi ake gani ita ba a san da nata dan ba, tana ganin yanzu ya kamata ta zage dange tai da gaske kar a mata yar gidan jiya.


No comments

Powered by Blogger.