Fulani 11


11*


A hankali ya fara driving din da dayan hannunsa dayan kuma yana shafa fuskarta da ke annuri kamar wani sabon ango. Tun ka ya karasa babban gate din ya hango wata

duke ta rufe kanta wanda hakan ke muna alamar kuka take. Very slowly ya karasa kusa da gate din, ya mika hannunsa ya dauko facing cap dinsa ya saka ya dauki bakin gilashinsa dake cikin motar ya saka, sannan ya sauke gilashin motar yana kallonta, kuka take a hankali wanda in baka saurara sosai ba zaka iya ji ba. 


“Ke...”


Ya kirata da muryarsa mai dadi sauraro, sai dai yanayin da yai mata kiran ba zata iya ji ba, saboda ita din ba ta da lafiyar kunne a yanzu.


“Hey....”


Still bata dago ba dan bata san ma yanayi ba. Be sake na uku ba ya data gilashin motarsa ya cigaba da driving dinsa sanyin ac motar na ratsa ko'ina na jikinsa. Kamin ya karasa babban gate din wayarsa tai ring, cikin very low volume, hannunsa ya sa ya ciro wayar daga aljihunsa yana dubawa yai arba da Mansura. Murmushi yai kamin yai picking call din da Bluetooth din dake kunnesa. 


“Hey Baby”


“Baby kana ina?”


“Gani zan fito daga gida”


“Ina zaka je?”


“I don't know kawai na ji bana son zaman gidan ne”


“Baby i miss you”


“Miss you too, on wednesday zan dawo Kaduna”


“I can't wait ina jin kamar na biyoka yanzu, i miss everything about you, your smell, your hug, your smile and everything, ina jin kamar idan ka auri wata ba ni ba zan iya mutuwa”


Ya karshe maganar da muryar da ke nuna tana daf da fashewa da kuka, sai tausayinta ya kara shiga zuciyarsa. 


“Even if na auri Nana still zan aure ki, Hajiya ta yarda na auri Nana first then na auri duk wacce nake son aure daga baya, and i promise you....”


Sai kuma ya kasa karasawa what if yai mata alkawari kuma ya tsaba? What if Hajiya ta hana shi aurenta gaba daya?


“I know lokaci zai zo da zaka kasa daga kirana ma, but no matter what ina son kasan cewa ina kaunarka Sirleem, Hajiya tana son ka auri Nana ne saboda Nana ta fi ni kyau, ta fini kurciya ta fini asali ta fini komai, na san idan ka aureta za ka manta da ni ne”


“C-omon kin san kyau ba ya rudata, da dan kyau ne da Allah kadai ya san matan da zan so, ke kanki da ba mu kawo yanzu ba, kyau be cikin tsarina hasalima na tsani mace mai kyau sosai that's why nake son black girl very dark, but ever since i found you bana bukatar komai”


Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba. 


“Na rabu da kowa saboda kai Sirleem pls karka juya min baya”


“Ba zai taba faruwa ba kin san ina son ki ai”


“I love you too”


He kiss her on the phone, sannan su kai sallama ya aje wayar a saman cinyarsa, ya cigaba da driving dinsa hankali kwance ba dan ya san inda zai je ba, shi din ba kamar sauran mutane ba ne da zai iya fita any how ko zuwa ko'ina at any time, wani gurin yana zuwa za a fara masa ihu ana cewa za ayi hoto da shi ko a fara masa video ko tambayoyi, shi kuma abun da ya tsana kenan a rayuwarsa, that's why be cika son zama ko'ina ba sai a family house dinsu indai yana cikin garin Yola. 

Wayarsa ce ta sake ring for the second time but this time around Hajiya ce, hannunsa na dama ya kai ya danna Bluetooth din kunnensa. 


“Hello Good morning”


“Kana ina?”


“Na fita”


“Ai na san ka fita ba na aika kiranka ba babu kai a dakin kana ina?”


“Wani abu kike so ne Hajiya?”


“Ban isa na tambayi inda kake ba?”


“Ina son na karya ne a waje”


“Ka dawo yanzu gida zaka karya”


“Amman Hajiya har na iso fa”


“Umarni na baka”


Tana fadar hakan ta kashe wayar, runtse idonsa yai for one second ya bude, ya juya motarsa ya dauki hanyar gida. Inda ya bar yarinyar dazun a nan ya sake tararda ita, sai dai wannan karon ba kuka take ba, zane zane take da yatsanta a interlock din dake gidan. 

  Ya dan sauke gilashin motarsa kadan ya leko kansa.


“Ke me kike nan wai?”


Bata ji me yace ba balle ta dago ta kalleshi, kana bata ji karar mota ba balle hankalinta ya bata an tsaya kusa da ita ne. Yanzu kam he realized bata ji domin ya daga muryarsa fiye da dazun da yai mata magana. Horn din motarsa ya danna sai ta dago da sauri ta kalli motar. Marar mota ce fes mai bakin gilashi, an sauke gilashin motar a amman kadan mutumen ciki na sanye da facing cap da katon bakin gilashin ido wanda ya boye fuskarsa. Directions dinta yake kallo tana gani ta san ko dai magana yake mata ko kuma kallonta yake. Mikewa tai tsaye ta kabe jikinta tana kallonsa hawayen da ya bushe ya bata mata fuskarta. Hannunsa ya leko kadan yai mata alama da ta zo sai ta kanne kafada alamar ba zata zo ba, jikinta be bata cewar mutumen da ya kore ta ba ne, domin wacan ya fi wannan fari, idan ma shi din ya za'ayi ya kira ta? And wannan din da ke kiranta waye? Wat if marinta zai yi? Ita dai jikinta be bata mutumen arziki ba ne domin ya ki sauke gilashin motar gaba daya balle a iya tantance ko waye ne, gashi ya saka gilas da facing cap. 

Sirleem be sake kokarin ce mata komai ba ya ja motarsa zuwa gate din bangarensu, haka ta bi motar da kallo har ya shige sannan ta mike tsaye ta fara tafiya tana dingishi har ta isa gate din farko, sai da ta fara lekawa ta gani idan Iya na nan, ganin babu kowa yasa ta jidadi kuma ta ji kuzarin cira kafarta ta karasa har harabar gidan. Bata kai karamin gate ba school bus ta shigo harabar tsayawa tai kallon daliban da ke ciki ba karamin burge ta su kai ba, a rayuwarta tana sha'awar ace mace tana karatu, abun yana burgeta ace wannan yar makaranta ce, tsabanin ita da bata iya karanta komai a cikin boko. Nana ce ta fito ta kofar gaba tana ta turo baki ta shiga motar sannan driver motar yaja motar suka fita daga gurin. Bin motar tai da kallo tana tuna lokacin da Yayanta Fadil ke zuwa makaranta a lokacin tana karama sosai, yana yawan fada mata abun da ake makarantar, yana yawan ce mata ita ma idan ta kara wayo Baba zai saka ta kamar yadda ya saka shi, amman yanzu komai ya gushe, ta rasa mahaifiyarta Babanta kuma ya tsaneta, yayanta kuma ya tafi ya barsu, kanenta uku kuma suna kauye ita kadai take rayuwa cikin wahala. 


“Ko ina Yaya Fadil yake yanzu?”


Ta tambayi kanta idonta na cika da hawaye, a hankali ta fara taka stairs  din tana jin yadda kafarta take diban tsantsin gurin kamar ta fadi. Cikin wani irin tsoro ta danna door bell din dake gefem kofar lake, sai ta koma gefe ta labe jikin fulawoyin kasko dake gurin tana leken ta ga wanda zai bude kofar. Daya daga cikin tsofin dake aikin a gidan ce ta leko tana tambayar waye, Falmata bata ji abunda tace ba sai dai ganin tana waige waige yasa ta fito daga inda take boye tana kallon matar. 


“Ke kika kwankwasa kofar?”


Falmata ta daga kai alamar Eh ba dan tana jin abun da tace ba sai dan nuna da tai. Matar ta koma ta sanar sannan ta sake dawowa tai ma Falmata alama da ta shigo da hannu kamar ta san idan ta fada ba zata ji ba. Babu kalar addu'ar da Falmata bata karanta ba kamin ta saka kafarta cikin falon, tana shiga sai ta tsaya daga jikin kofar ta rakube ta kasa kallon kowa balle ta tantance waye da waye a ke cikin falo. 


“Me ya hana ki zuwa kwana biyu?”


Bata daga kai balle ta gane tambayar da Ammy take mata, gashi ba ji take ba sosai ba a yanzu. 


“Ke yar talakawa ba magana ake miki ba...”


Wannan kam ta ji sarai, domin tsawa ce Baaba ta katsa mata, a take jikinta ya hau rawa hawaye suka ce sallamu alaikum.


“Ba kuka za ki yi ba bude baki ki yi magana....”


A nan ma ta ji domin ba da wasa Baaba take daka mata tsawar ba. A lokacin da ta dago kanta sai ta rasa kan waye zata sauke su, Shattima ko Zainab ko Ammy ko Wasu bakin fuska da bata sani ba? 


“Idan ba za tai magana ba ta fice ta ba mu guri mana”


Zainab ta fada cike da kufula, da sauri Falmata ta girgiza kai kamar ta san abunda Zainab ta fada. 


“Dan Allah ku yi hakuri, bana iya jin komai idan ba a fada da karfi ba, ko kuma kusa da kunnena”


Gaba daya kallonta suke, ba maganarta kadai ba, hawayen da ke fita daga idonta ma da yadda numfashunta ke shudewa ya isa ya sanar da irin tsoron da take ji. 


“Baaba matsa kusa da ita ki tambayeta abun da take so”


Shattima ya fada a hankali yana kallonta. 


“To Ranka ya dade”


Baaba ta matsa kusa da Falmata wacce tak take jiran a sake ce mata ta juya ta zura a guje, daf da kunneta Baaba ta rada mata. 


“Me kike so?”


A lokacin ne Falmata ta duka kasa ta hade hannayenta tana kallon Shattima hantar cikinta na mugun kadawa. 


“Hakuri na ke son na bashi, Dan Allah yai hakuri ya maida ni aikin, na san na yi kuskuren taba masa ya amman ba da wata manufa nai ba, dan Allah ka yi hakuri ka kyale ni na cigaba da aikina, idan baka hakura ba ban san yadda zan yi ba”


Shattima kallonta kawai yake ba dan ya fahimcin inda ta dosa ba, domin be san ya koreta ba, sai dai idan ita ta kori kanta saboda ta kasa natsuwa da abun da tai. Ta share hawayen idonta tana hade yawu daker. 


“Sanadin korar da ka min yasa Babana ya mare ni kunnuwana suka rufe, har Ban iya ji sosai, idan baka maida ni ba zai iya kashe ni”


Wani irin jan numfashi take tana maidawa, daker ta maganar ga kukan tsoron kar su ki karbarta ga kuma na kallonsu da take a gabanta. Ammy ta kalli Shattima. 


“Ta maka wani abun ne?”


Ya girgiza kai ya dan tabe baki alamar no. 


“Waya kore ki?”


Ammy ta tambaya sai matar ta rada mata a kunne.


“Wannan matar wacce take nan gidan ita ta fada min cewar ka koreni, kar na sake dawowa”


“Wace mata?”


Ammy ta sake tambaya tana son tantance gaskiyarta. Sai Baaba ta rada nata a kunne. 


“Wannan wacce take saka zane da mayafi kala daya, wata Dattijiwa ban san sunanta ba”


“Idan kika ganta za ki gane ta?”


Falmata ta gyada kai bayan Baaba ta rada mata. Duk abunda ake Zainab bata ce komai ba Shattima ma be sake cewa komai ba kallonta kawai yake, ba wai tausayi ta bashi ba, kawai kallon mamakin wanda ya koreta da sunanshi yake, shi dai ya san be koreta ba, waya ce ya koreta? Bayan be yi magana da kowa akan haka ba. 

  

“Me kika aikata ne?”


Ammy ce ta sake tambayar, Baaba tai isar da sakonta a kunnen Falmata, sai Falmata tai kasa da kanta ta kasa cewa komai sai hawaye take tana yarfar da hannunta. Dawowar da za tai sai tai arba da Iya wacce shigowarta kenan a falon ko karasowa inda suke ba tai ba. 


“Gata nan ita ce”


Falmata ta fada da sauri tana nuna ta, gabanta sai ya ninka na dazun bugawa, tsoronta ma ya ninka na dazun kamar wace ta ga wani horo, gashi Iya ta sako mata jajanyen idonta tana kallon komai na jiki da jininta. 

    A lokacin ne kallo ya koma gurin Iya wace ta karaso kusa da su ta yi wani tsayi hannayenta a baya. 


“Ya akai?”


“Yarinyar nan ta ce kin ce Shattima ya koreta daga aiki”


Iya ta juya sake kallon Falmata bayan Ammy ta fada mata haka, sai ta nuna kanta. 


“Ni na fada miki haka?”


A zaton Iya Falmata ba za ta iya cewa komai ba, musamman irin yadda ta ga ta tsaya kallonta kamin Baaba ta rada mata. 


“Eh ke kika ce Wallahi ba karya na ke miki ba”


“Okay Iya ita za tai karya kenan? How are you da kika iya munafurci?”


Zainab ta nufo ta tana fadin haka, Falmata dai sai kallonta take irin na kurma, sai dai tana gani ta san fada take mata. Iya ta yi saurin riketa. 


“A a karki dake ta wata kila dai wata tai mata haka amman ba ni ba”


“Ta rasa wanda za ta lakawa sai ke? Ke kadai ce a gidan nan ne?”


Wannan karon Falmata ta ji abun da Zainab ta fada saboda ta fada ne cikin tsawa tana hararta. Sai Falmata ta girgiza mata kai. 


“Idan bata ce ba ba zan mata karya ba, Wallahi Allah yana shaidata ta fada min haka”


Shattima ya mike tsaye yana fadin. 


“Ko ma dai minene ya wuce je ki yi aikinki”


Shattima ya fada bayan ya mike tsaye, yan'uwan Ammy da suke falon dai ba su ce komai ba na su ido ne kawai. Zainab ta juyo ta kalleshi. 


“Kamar ya ya wuce? How yarinya za tai wa Iya kazafi ba ayi komai ba and you are telling us ya wuce like how? Har umarnin taje ta cigaba da aikinta kake ba ta”


Wani wawan kallo mai kamar harara Shattima ya watsa mata, kamin Iya ta wanke mata fuska da mari, da sauri Zainab ta dafe kunci tana kallon Iya. Falmata kuma da bata gama fahimtar abun da ke faruwa a tsakaninsu ba tai kara shan jinin jikinta tana jin kamar ita aka mara. 


“Har abada karki sake, taya Babban Mutum zai ba da umarni ke ki ce ba haka ba? Har kin isa? Waye ke da za ki fada masa abun da zai yi?”


Zainab ba ta ce komai ba ta bayan hawayen da suka wanke mata fuska wanda ta manta rabon da hawaye ko wani abu damuwa ya rabeta, sai da ta kalli Shattima da ke tsaye yana kallonsu sannan ta kalli Ammy, har lokacin tana rike da kuncinta da ke ta mata zafi, da sauri ta fice daga falon tana jin wani irin fusata marar misaltuwa. Sai da ta fice sannan Ammy ta ce. 


“Iya da ba ki mareta ba ai”


“Sam ba zan lamunci kowa yai ma dan cikinki maganar banza ba, balle har ya musa masa, ban yarda wani yai masa ba ina ga yata? Na sani Zainab kadai ta rage min a duniyar amman Wallahi da zata cigaba da musa miki ko Babban Mutum sai na yafe ta gaba daya a duniyar nan” 


Kowa na cikin falon jinjina kai yake yana ganin ta girmama Ammy da Shattima, ban da Ammy da take ganin kamar da biyu tai haka, ko dai tana jin kunyar abun da Falmata ta fada ne tana son kare kanta ne, ko kuma da wata manufar tai. Shattima be ce komai ba ya fice daga falon. 

  Kallo Falmata kawai Iya tai ta dauke kai ta fice ita ma daga falon. Da kai Ammy ta nunawa Falmata dakin yan uku, sai ta tashi jiki ba kwari ta nufi dakin, yau biyu ne sabanin waca zuwan nata na karshe da ta tararda da daya, sai dai yau ko da wasa ba ta kalli inda yaran suke ba, har tai abunda zata yi ta gama bata kula yaranba, tana daf da gamawa Shattima ya shigo dakin ransa a bace cikin tsawa ya ce. 


“Ya za ki yi shara da yara a cikin daki? Baki da hankali ne?”


Da sauri ta juyo ta kalleshi ta girgiza masa kai. 


“Idan na taba su zan iya yin laifi, dan Allah kai hakuri”


Ta duka har kasa ta hade hannayenta tana bashi hakuri, wani dogon tsaki yaja ya karasa cikin dakin ya kai hannunsa ya dauki dayan ya dora a wuyansa dayan kuma a dauke ta da hannunsa. Kamin ya fice Falmata ta karasa aikinta duk ta tsawwala. Tana gamawa ta fice da sauri kamar wacce aka kora. WASIN POV. 


Yana daga saman icen guava zaune yana kallon yadda mawakan cikin gidan sarautar suke busa suna rawa daga su sai walki a jikinsu, ga wuta kara a tsakiya sai tashi take a tsakiyarsu, mahaifinsa kuma yana zaune a saman wata kujerar ice wacce aka mata kwaliya da fatar damisa, sai kallon masu wasan yake yana murmushi cike da jindadin, kusan rabin garin duk suna tsaye a gurin suna kallon yadda ake wasar, mazajen da suke tsaye kuma jikinsu sai rawa yake suna jin kamar su fada ayi da su. 

 A cikin masu wasan har da Liya wacce ke sanye da rigar fatu, ta sako gashin kanta har baya, sai tai masa kwalliya da gashin tantaba yai mata kyau kamar wani ribbbon, hannunta sanye da wuri kamar yadda duka kafafuwanta suke sanye da su, duk wani motsi nata sai sun motsa, wuyanta sanye da kokon kan mujiya wanda ya bushe aka yi mata tsarka da shi. Wasa take sosai kamar wata yar buri, yadda take wankwasa hannunta da jikinta sai ka dauka wata macijiya ce. Mikewa tsaye Wasin yai ya fara busa sarewarsa sai gurin ya dauki wani kalar sauti mai dadi ga iska na kadawa yana daukar busar tana karade ko'ina na gurin. Wani irin kuzari ne ya kara shigar Liya sai ta ji kamar dominta kadai yake busar, a lokacin ne ta fara kada kafafuwanta da kunkurunta wurin da ke jikinta yana ta kara, sauran yan rawan kuma sai suka rika buga kafarsu a kasa su ma wurin da ke daure a kafarsu ya rika kara. 

  Duk abunda ake ran Sarkin cike yake da farinciki da annushuwa, domin wasan ba karamin kayatarwa tai ba, kuma wasa ce wacce ya samu asali tun kaka da kakanin. Bayan ya gama rawar aka shigo da gassashen naman kuraye, yanka daya ake yankawa kowa ya dauka ya ci, haka ake a duk lokacin da akai wami wasa, ta nan suke iya gane wanda ba jininsu ba kuma ba dan garin ba, idan kai ba dan garin ba ne ka ci naman kurar a take makoshinka zai fara kaikaiyi, domin naman tsafafen nama ne. 


Sai da aka gama komai sannan Wasin ya saka daga kan bishiyar, ya isa gaban mahaifinsa ya kwashi gaisuwa, sannan ya fara tafiya barin garin, daman shi be saba kwana a cikin garinsu ba. Yana tafiya yaji ana binsa a baya, tsayawa yai cak ya duba tafin hannunsa, sai sunan liya ya fito rubuce a cikin manyan baki. Juyawa yai ya kalleta sai ta sakar masa murmushi ta biye hannayenta a baya tana wasa da su. 


“Ya akai?”


Ta girgiza masa kai alamar babu komai, sai kawai ya juya ya cigaba da tafiyarsa, sai ya sake jinta a bayansa, sake juyowa yai ya kalleta nan ma kan ta girgiza masa, sai ya nuna mata bayanta, tana juya bata ga komai ba ko da ta juya har ya bace. Dariya yai ta kwala masa kira da iyakar muryarta. 


“Wasin.......”


Manyan duwatsun da suke gaban garin ta fara kallon duk da kasancewar dare ne, sai dai akwai hasken farin wata da zai iya bata damar ganin duwatsun ban da abun da yake kansu domin sun mata nisa sosai. 

  A saman icen da ya saba kwana ya hau ya kwanta yana ta kallon manyan taurarin da suka haska samaniya su kai mata ado, ga iska mai sanyi sai kadawa yake. 


FADIME POV. 


_A yau ba mafarki nai ba a fili na ji busar, amman ban ga kowa ba_


Bayan ta rubuta wannan ta sake buge wani fegin ta rubuta. 


_Kuma yau ma naggen Bappa ta mutu, kuma kadangaren dake bandaki ya biyo ni_


Bayan ta rubuta ta rufe littafin ta aje a inda ta saba ajeshi tare da biron, haka take duk abunda ya faru a wunin ranar sai ta fada, idan tai mafarkin busar sarewar nan ko mutumen nan da yake bayanta ma rubutawa take, ita ala dole ga yar boko. 

 

“Fulani”


“Inna”


“Warre”


Ta mike tsaye ta fito daga dakin zuwa inda mahaifiyarta take zaune tana kiranta. 


“Gashi nan an gama dauki ki je”


Sai ta gama kirga gidar ko ta nawa ce sannan ta dauka ta dora saman kai, ta koma can kusa da dakinta ta dauki wani karen zana ta fice daga gidan. Dandali ta nufa tana tafe tana rera wakar da ake a dandalin ta Fulatanci, tun kan ta isa ta hango yadda dandali ya cika da mutane masu sana'a sun baza, masu samari kowa ya ja tashi gefe suna fira, masu rawa da wasar dandali na yi. An kunna wutar kara ta kama sosai ta haske ko'ina na gurin. A gurin da ta saba zama ta zauna ta aje gidar dake kanta a gabanta tana bawa idonta abinci. 


Sai kusan sha daya sannan kowa ya watse wadanda sukai ciniki sun yi, masu samari kuma akai sallama kowa ya nufi gidansu. Ita ma kanta a gajiye ta dawo gida tana hamma, ko da ta iso Inna ta gyara mata gurin kwanciyarta sai kawai ta shige dakinta ta kwanta. Misalin karfe biyu suka fara jin tafiyar jakuna a rufin dakin na zana, can kuma ta fara kukan mage, kamin ta koma kiran sunanyen mutanen gidan. A take Fadime ta tashi zaune ta kwala wani uban ihu tana kiran sunan Babanta. 


“Bappa Bappa Bapppa.......”


Kamar jira ake sai ta fara jin kokan magen a bakin bukkatar tana koyonta da sautin kukan magen. 


“Bapkwau Bapkwau”


Sai kuma ta ji tafiyar dakuna a tsakar gidan, har da wani tuma suke suna direwa, sai kuma ta ji kamar kukan kare, a lokacin ne tai ihun na gaske wanda ya farkar da Bappa daga bachin da yake domin shi idan sabo ya saba da irin wannan abun, dan haka baya hana shi bachi ita din dai ce da ta kasa sabawa kuma a duk lokacin da ta ji sai ta yi ihu ta kirashi. Da sauri ya budewa zagen da suka sako wanda shi ne murfin bukkar ya fito, sai yai arba da bakar mage tsaye a kofar bukkar Fadime, cikin kuzari ya nufi inda tabaryar gidanta take ya dauk ya jefeta da ita da sauri tai tsalle ta haye saman bukkar tana masa kuka sannan ta sauka da can baya. 


“Bappa....”


“Kone Fulani addu'a akai idan kajji haka haba, kai kullum in zaka kwanta baka addu'a Fulani”

“Ni addu'ar wuya take ba ni”


Ta fada bayan ta ga mahaifinta a cikin bukkatar yana lalaben inda take ya riko hannunta suka fito, komawa yai da ita dakinsu ya saka ta a ta su bukkar, ya kunna ashana ya lika a kyandir yai mata shimfida a kasa, shi kuma ya hau saman gadon karan ya kwanta, mahaifiyarta na daga gefe kwance sai kwasar bachinta take.

No comments

Powered by Blogger.