Fulani 10

 


*10*


FALMATA POV. 


Haka ta kwana da ragowar yunwa a cikinta, washe gari tun da asubar fari Tumba ta fito ta fara kunna wuta a lokacin Falmata na waje tana alwala sallah asuba, baya ta gama ta

shiga daki ta dauki hijabinta zata saka tai sallah sai ta ji an rikota sakamakon kiran da ta yi ta mata bata ji ba. 


“Karki sallah bari ki yi wanka”


Ta rada mata a kunne, ba ta isa tace mata bari na gama sallah ba, dan haka ta aje Hijabin ta fito bakin kofar dakin ta zauna tana ta kallon wutar da Tumba ke ta aikin fetawa tana tura ledodi, nan da nan ruwan sukai zafi sai ta dauko wani garin magani ta zuba a cikin ruwa ta juya shi sannan ta sauke ta tsirka mata da ruwan sanyi.


“Zo dauki ga shi nan ki yi wanka maganin tsari ne”


Tana maganar tana mata alama da abunda take nufi irin yadda ake ma kurame. Falmata ta tashi daga inda take zaune ta dauki ruwan maganin ta shiga bandaki ta cire kayan jikinta ta watsa ruwan ta fito. Da hannu tai mata a alama da ta zo, sai Falmata ta aje bokitin hannunta ta karasa inda take tsaye, duba ta tai dan ta tabbatar idan ta yi wanka, ga kuma shaida ta gani maganin ko'ina a jikinta. 


“To je ki yi sallah ma”


Nan ma alamar kurame tai mata, sai Falmata ta juya ta shige cikin dakin ta dauki wasu tufafin ta saka ta saka hijabinta ta fara sallah. 

Bayan ta gama tai addu'ointa kamar yadda ta saba sannan ta fito ta gyara ko'ina na gidan tai wanke wanke, ba ta ko tsaya tambayar abincinta ba ta fice da zimmar zuwa gurin aikin karya.

Tana tafe tana nemawa kanta mafita, ta sake komawa gidansu Khadija ko kuma dai ta koma gurin aikin ta sake ba su hakuri? Domin idan wata yayi Tumba zata tambayi kudinta na albashi to me za ta ce mata? To idan ma ta koma za su karbe ta ne? Sai ta rasa wanda za tai, daga karshe dai ta yanke shawarar zuwa gidansu Khadija domin har ga Allah ita yanzu tsoron zuwa gidan can take, abun da bata sani ba Naja na biye da ita a baya tana lekenta kamar yadda Tumba ta saka ta. Sai dai ita bata lura ba har ta shige cikin gidansu Khadija. Yau kan bata samu Khadija a gidan ba dan ta tafi islamiyar safe kasancewar yau Sunday, Maman Khadija bata tsaya komai ba ta zubo mata abinci, Falmata ta zauna ta ci sai da ta koshi sannan ta nemi guri ta kwanta tai ta bachinta. Sai kusan azahar sannan Khadija ta tashe ta, firgigit ta mike tsaye dan lokacin komawarta gida yayi har ma ya dan gota. 

Duk yadda Maman Khadija da ita Khadijar kanta suka so Falmata ta tsaya ta ci abinci sai ta ki gaba daya hankalinta ya tashi kar ta koma late Tumba ta doketa. 


“Ko na zuba miki a leda?”


“Idan ta gani zata iya min fada”


Duk da rada Khadija take mata maganar. Bata jira abunda Khadija zata sake cewa ba ta fice daga gidan hankalinta a tashe, da sallama ta shiga gidan Naja ta amsa mata tana tabe baki. 


“Ashe idan an tura ki aiki gidansu Khadija kike zuwa kina zaunawa ko? Ai na biki dazun na gani”


Naja ta fada cikin daga murya ta yadda Falmata zata iya jinta. Wani irin bugawa gabanta yai da karfi, da zaro ido tana kallon kofar dakin Tumba sai ta nufo gurin Naja ta riketa.


“Dan Allah Naja karki fada, dan Allah ki rufa min asiri”


Tana rufe baki Tumba na fitowa daga dakinta ta tsaya bakin kofa rike da kunkuru tana hararar Falmata, da sauri Falmata ta mike tsaye ta fashe da kuka, a take tsoro ya kamata ta rika ganin kamar Tumba dukanta za tai sai ta fara ja da baya baya tana ganin Tumba ta motsa ta fice daga gidan da sauri. Komawa tai gidansu Khadija ta zauna, a can ta wuni har dare ba ta fada musu abun da yasa ta gudo ba, sai dai suna ganin yadda hankalinta ya tashi sun ssn ba lafiya ba. Sai bayan sallah isha'i Naja ta zo kiranta, cikin rashin kuzari ta tashi suka fita daga gidan tare tun kan su karasa gida ta fara kuka. 

Suna shiga cikin gidan fara rabawa jikin gina tana kallon mahaifinta dake watso mata harara. 


“Gata nan ashe idan an turata aiki gidansu Khadija take shiga, yau aikin komai ba tai ba can ta wuni, ni dai dan Allah ka yi mata tsakani da yarinyar ba ma yarinyar kirki bace Wallahi”


Tumba ta fada tana narke murya kamar gaske. 


“Wato Falmata duk abun da za a fada miki ba kya ji ko? Kullum sai kin tsiro wani bakin hali ko?”


Bata ji abunda Tumba ta fada ba amman ta ji abunda mahaifinta yace shi da yake da tsawa yake mata magana. 


“Zo nan....”


“Baba dan Allah ka yi hakuri sun kore ni kuma ina tsoron komawa gidan da? Allah kai hakuri gobe zan je”


Ta fada cikin kuka. 


“Zo na ce....”


Ta fara tafiya tana kuka tana kallon Tumba tana jin kamar ta taso ta zo ta cece ta, irin yadda mahaifiyarta take mata idan za a doke ta, gabansa taje ta tsaya ta rika hannunta ya murde iya kar karfinsa sai da ta fasa wani irin ihun ta fadi kasa. 


“Wayyo Baba Wayyo Baba dan Allah kayi hakuri, ka yafe min Baba karka kashe ni dan Allah”


Sakin hannun nata yai ya rika hijabinta yaja ta daga inda take kwance har gurin da tumakinsu suke daure, ya kwance igiya daya ya daure mata kafa tamau, zai juya ta riko kafarsa. 


“Dan Allah Baba ka yi hakuri, karka ba ni na kwana a cikin tumaki dan Allah Baba”


Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya har cikin ransa yake jin kukan yarsa idonsa suka cika da hawaye, amman sai ya ji ba zai iya mata komai ba bayan haka, fisge kafarsa yai ya fice daga gurin ya barta tana ta kuka. Tun tana kukan tana kiran sunansa tana bashi hakuri har koma kiran Tumba tana bata hakuri daga kashe sai ta hakura ta kwanta a gurin tana ta hawaye, ba hawayen kwana a gurin kadai ba har da hannunta da take jin kamar ya karye saboda mugun rikon da Baba yai ma hannun nata, ga kafarta da ya daure da karfen rodi ya tsuke mata kafar sosai. 

Ba tai wani bachi kirki ba saboda kuka da ciwon hannu da kafa da kuma warin fitsarin dabbobin dake gurin, sai da rana ta fara fitowa sannan Tumba ta zo ta kwance ta. 


“Na gode”


Falmata ta fada tana kallon Tumba da idanuwanta da suka kankance tsabar kuka da wahala, ba ta yi zaton za ta kwance ta wuri haka ba ya dauka ko sai ta kwana biyu ko fiye ma. 


“Tashi kije ki shirya ki tafi gurin aikin”


“To”


Ta fada jikinta na ta rawa wani irin sanyi take ji yana ratsata kamar zazzabi na son rufe ta. Duk yadda ta so tai wanka kamin ta fara yin sallah sai ta kasa saboda hannunta bata iya komai da shi ga kafarta ma dingishi take, haka nan dai ta wanke jikinta sannan tai alwala ta shiga dakinsu ta saka wasu tufafin tai sallah ta fito tana jin jiri na dibarta ta durkusa a wahale ta gaishe da mahaifinta. 


“Baba ina kwana?”


Be amsa ba daman yana tsaye ne yana sauraren abunda Tumba take fada masa akan Khadija cikin tsawa ya ce. 


“Babu ke babu Khadija daga yau, balle har ki je gidansu, na miki tsakani da ita”


“To Baba”


Ta amsa masa tana jin kamar ba zata iya numfashi ba, ga idonta sai ciwo yake, mikewa tai tsaye bayan ta gaishe da Tumba ta nufi kofar fita kamar wata musaka ta fice daga gidan. Da kallo Baba ya fita har ta fice sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ta yadda Tumba ba zata ji ya juya ya koma cikin dakinta. 

Kai tsaye Masarautar Falmata ta nufa a ranta tana ta addu'ar Allah yasa su karbe ba, domin idan ba su karbe ta ba bata san yadda zata yi ba, kamar yadda ta saba sai ta gaishe da kowa take shiga ciki, sai dai bata tsaya jiran su amsa tun da ko sun amsa idan ba su kwarai ba ba ji za tai ba. Sai da ta kawo gate din da zai sadata da bangren Ammy cikin rashin sa'a ta hango Iya tsaye ita da wasu matan gidan tana magana, a take jikinta yai sanyi, ta san ko kowa zai ji rokonta ya karbi uzurinta ban da Iya, duk da baya san wacece ita ba amman ta lura da bata son ta tun farkon zuwanta gidan, bayan Iya akwai Zainab da Shattima su ma tana tsironsu ba ma kamar Shattima da shi ya kamata da kansa tana taba masa ya. 

  Ji tai ba zata iya karasawa ciki ba ba kuma zata iya komawa gida ba, sai kawai ta koma gurin kofar babban gate na uku ta zauna tana ta kukanta marar sauti.


*****      *****       *****      *****


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Shi ne abun da kowa yake fada, Ammy ta karbe ta daga hannun Baaba tana jirgizawa, amman babu alamar rai a tare da ita


“Hajiya a kira likita”


“Ko kuma a je asibiti kai tsaye ba”


Ammy ta hada hankalinta a tashe, Iya ce ta karaso gurin tana tambayar abun da ya faru. 


“Wallahi Luna ce, ta buga kwallowa, tana ta ihu ko da muka daukota jikin yayi zafi kamar wuta, daga nan bata sake motsi ba”


“Innalillahi”


Iya ta fada tana karbarta daga hannun Ammy. 


“Ayi sauri a tafi asibiti ai ba tsayawa za ayi ba”


Ammy da kanta ta shiga ta dauko mayafinta ita da Baaba da Iya suka nufi asbitin. A lokacin ne labarin ya karade Masarautar kowa ya san abun da ake ciki ban da Nana da hankalinta be kai can ba, domin tana bangaren Hajiya kuma Hajiya ba ta yi magana a gabanta ba ita kadai ce a falon tana ta kallon Tv duk da hankalinta baya wajen. 

Ta kusan minti talatin a falon sannan ta taso ta dawo bangarensu, ta tararda manyan masu hidimar gidan zaune a falon cikin har da wasu kanen mahaifinta mata da suke zaune cikin masarautar, amman Nana bata tsaya ta kula kowa ba balle ma ta tambayi abun da yake faruwa. Kai tsaye ta wuce dakinta ta shige da rufo kofar ta hau saman gado ta kwanta, jikinta na bata ba lafiya ba amman ba zata iya tambaya ba.

Sai da ta ji hayaniyar na so ma yawa har da masu kuka sannan ta fito ta tsaya jikin kofar dakinta tana kallon Hajiya Karama dake kuka sosai ita da sauran matan, Shattima na zaune kan cushion kansa a kasa Iya kuma na zaune kasa tana kusar kuka kamar ba gobe. Sai a lokacin gabanta ya so ma faduwa, kar dai Mai Martaba ya rasu? Da sauri ta karasa fitowa ta nufo gurin da Shattima yake zaune ta zauna tana tambayarsa. 


“Ya miya faru why kowa yake kuka?”


“We lost Luna”


Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba. A take ita ma ta fashe da kuka ta riko shi.


“Ya How?”


Dagowa yai ya kalleta da idonsa da suka rine su kai ja, kana ganin kasan ransa a bace yake. 


“Lokacinta ne yai”


“Ita take?”


“Tana ciki za a mata sutura”


Ya fada bayan ya nuna mata kofar da bakinsa, kallon kofar tai sai ta kwantar da kanta jikin yayanta ta fashe da kuka sosai. Kusan a falon Shattima ne kawai be yi kuka ba, sauran daga masu kuka suna ihu sai masu hawaye domin ko ba ka yi niyar kuka ba ganin yadda Iya da Nana da Zainab suke kuka dole ya baka tausayi ga kuma Shattima da ya kasa kallon kowa ya kasa tashi daga gurin. 


Sai da ana daf da za a fara mata sallah sannan Hajiya Balki ta shigo falon da Hijabinta da carbi a hannun tana kuka. Sai da aka fara shigowa gaisuwa sannan yaranta suka shigo suka zaune a falon Ammy ana amsar gaisuwa da su. 

Da dare Waziri ya tara kowa na gadan ya fada musu kar wanda ya sanarwa Mai Martaba da maganar mutuwar Luna. Kuma wannan zaman gaisuwar shi ne na karshe duk wanda ya zo sai dai yai musu ya tafi. A cikin daren Mama Fulani ta dawo daga kauyen da tafi sakamakon wayar da aka buga mata aka labarta mata abunda ya faru.

Misalin ten Shattima ya shigo falon tare da wasu friends dinsa su kai ma Ammy gaisuwa sannan ya wuce da su bangaren Hajiya Balki su kai mata gaisuwa ita ma. 


  Bayan sun fita Mama Fulani take cewa. 


“Ni wannan abun har mamaki yake bani Wallahi, abu kamar ba banza ba”


Ammy ta kalleta. 


“Wani lokacin ana munana zato, saboda an san akwai makiya kuma babu abunda basa iyawa, haka Waziri yake yawan fada wai yana ganin kamar da sa hannun wani a lamarin gidan nan”


“Ya Waziri yana da gaskiya, ni kaina sai da mu kai maganar da shi, kuma maganarsa abun dubawa ce, tsakani da Allah da can ba haka ake ba, ki duba ki ga yadda suka mai da Mai Martaba ace kana sarki babban sarki amman an maida ke a daki zaune komai sai dai a labarta maka iyalinka ma ba kowa ke shiga ya ganka ba?”


“To wa za ka yi zargi Fulani? Wasu dabam ko kuma a cikin masarautar ko a tsakaninmu, kanensa ko yan'uwa ko kuma matansa? Yanzu abunda ake ta yayatawa a gidan nan wai har da sa hannu a cikin ciwonsa saboda ina son da na ya gaji mulki”


Mama Fulani ta rike baki. 


“Iko sai Allah ke kuma”


“Wallahi hake ake fada ance na mallake masarauta ni na ke da ikon kowa sai yadda na yi, in ban da rashin tunani taya macen da zata auri mutumen tun tsufansa har kawo yanzu da yara suka girma sai kuma na ce wai ina son ya mutu a dora dana? Wallahi ni ban taba yi ma Shattima kwadayin sarautar nan ba, Shattima da be cika son damuwa ba ina ma zai iya da sarauta? Yau ko babu ran Mai Martaba akwai kanensa masu so na nesa da na kusa, kuma sarautar yanzu ai ta sama waka sani waya sanka me ka tara me kake da shi, ni ban taba masa fatan hawan wannan sarautar ba ko can da balle kuma yanzu”


“Wallahi Hajiya karki ce dan muna uwa daya uba daya nake wani zargi, Wallahi har ga Allah ba dan muna uba daya da jarma ba wallahi sai nake ganin kamar har da sa hannunsa a lamarin nan, saboda kwadayenyen mutum ne, kuma ya so a bashi sarautar nan tun tuni”


Ammy ta sauke ajiyar zuciya.


“Wani lokacin sai ka yi zaton da ba haka yake ba, mu dai mun bar wa Allah komai yai mana magani”


“Amman gaskiya a tashi tsaye nema masa na hausa”


“Ai an gwada, idan aka masa na hausar sai ki ga kullum abun na kara gaba har tsoro yake ba mu, kuma kin ga idan an karbo ta nan ita ma Hajiya Balki ta gurinta tana karbowa sai ka rasa wanene na kwarai wanene mugun, shiyasa aka ce adaina ba shi gaba daya a cigaba da masa addua kawai”


“Allah ya kyauta”


“Amin”


Ammy ta amsa, sannan ta kai hannunta ya janyo cooler abincin da ke gefen gadonta sai ga Nana ta shigo sanye da kayan bachi, ta zauna kusa da Ammy kanta a kasa. 


“Ya akai?”


“Ba komai Ammy nan zan kwana”


“To sai ki kwanta tare da Gwaggonki, ni kin san dakin Mai Martaba zan kwana”


“Ni dai da ke nake son na kwana please”


“No ba zai yiyu ba Nana tsoro kike ji?”


Ta gyada kai. 


“To kije dakin Zainab ki kwana ya miki”


Ta gyada kai sai kuma ya kwantar da kanta jikin Ammy. Ammy ta shafa kanta zuwa kafadarta. 


“Kin ci abinci?”


“Aa bana so”


“Gobe dai za ki koma school”


Ta dago kanta da sauri ta kalli Ammy.


“An samu sabon driver ne?”


“No School bus za ta zo ta dauke ki”


Ta bata fuska har ga Allah ita dai bata son zuwa makaranta.


“Ammy no please”


“Ba ni na saka ba Waziri ne, kamin ya bar nan ma sai da ya fada min zaki koma gidansa da zama idan an gama gaisuwa”


Da sauri Nana ta bar jikin Ammy ta koma jikin kanwar mahaifinta wato Mama Fulani.


“Mama Fulani dan Allah ki saka baki bana son zama gidan Baba Waziri Wallahi”


“Ya Waziri ai daman ba shi da dadin zama da yara ba ke kadai ba duk yara ba son zama gurinsa, zan masa magana ya bar ki zauna nan sai ki cigaba da karatunki”


“Eh dan Allah”


Nana ta fada cikin kuka tana daga mata kai. A dakin ta kwanta duk firar da Mama Fulani da Ammy suke tana ji ta labe sosai kamar mai bachi alhalin idonta a bude yake. 

Misalin sha biyu Ammy tai ma Mama Fulani sallama ta sannan ta leka Nana. 


“Nana...”


“Na'am”


“Ba ki bachi ba? Tashi ki je dakin Zainab ki kwanta, ko nan kike so?”


“A a zan je can”


“Goodnight”


Ammy ta fada tana shafa bayanta, har cikin ranta take kaunar yarta, sai dai dabi'un da Nana take yasa basa jituwa da Ammy har Nana take ganin kamar Hajiya ta fi Ammy son ta. Sai da Ammy ta fice sannan Mama Fulani ta fashi ta shiga bandaki, da sauri Nana ta mike tsaye ta bude wardrobe Ammy ta inda ta san tana aje kudi ta fara mata bincike, tana yi tana kallon kofar bathroom bata samu komai ba yasa tai saurin rufewa ta fice daga dakin da sauri. Zainab na zaune gaban system dinta tana duba wani aiki Nana ta kwankwaso kofar dakin. 


“Waye?”


“Hajiya Karama ni ce”


Jin muryar Nana yasa ta tashi taje ta bude mata kofar. 


“Baby”


Ta kirata da sunan da take kiranta da shi. 


“Na'am nan zan kwana”


“Tos shigo”


Ya matsa nata daga jikin kofar, sai da Nana ta shig sannan Zainab ta rufe dakin ta dawo ta zauna a inda take tana hamma. Nana ta cire talkamin kafarta ta kwanata saman gadon tana ta kallon zoben zinarin da Zainab da aje kan bed side drawer. 


          Washe gari aka tashi gidan kowa shiru shiru ba ma kamar Ammy da Zainab, Ammy ta tsorota da mutuwar Luna ne sai take ganin kamar so min tabi ne zata iya rasa mijinta, gashi kwana biyun nan sai mafarke take da bata gane kansu. Zainab kuma ta damu da mutuwar kuma ta damu da halin da Shattima zai shiga duk da ta san ba zai nuna ba amman abun yana nan cikin zuciyarsa. 

Kowa yana falon suna karyawa ban da Ammy dake kitchen tana hadawa Mai Martaba nasa abun karyarwa dabam. Kadan kadan Nana take cin abincin tana sanye da uniform dinta sai satar kallon Shattima take da ya ke ta kurba tea shi a hankali. Sirleem ne ya shigo falon be yi sallama ba sai da ya iso dinning room din, Shattima ne kadai ya amsa masa Zainab kam tai kamar bata gan shi ba. 


“I'm sorry for your lost Allah ya yasa masu ceto ne my condolences please”


Ya mikawa Shattima hannu, Shattima ma ya miko masa nasa suka gaisa. 


“Thanks”


Shattima ya fada yana kallon Ammy wacce ta fito daga kitchen din tana murmushi. 


“Sirleem”


“Na'am Ammy barka da tashi ya hakuri?”


“Al-hamdulillah”


“Allah masu rahama”


“Amin Thank U”


Yana kokarin juyawa Nana ta mike tsaye da sauri ta ce. 


“Ya Sirleem dan Allah zaka sauke ni makaranta?”


“No School bus zata zo ta dauke ki”


Ammy ta amsa mata, Nana ta bata fuska kamar zata fasa kuka. Sirleem be ce komai ba ya juya ya fice daga bangaren gaba daya, daman saboda yai ma Shattima gaisuwa ya shigo, saboda jiya be masa gaisuwar saboda baya son fitowa cikin mutane. 

 Daga bangaren Ammy ya koma bangarensu, sai ya tararsa falon ba kowa tsabanin dazun da ya bar kanensa suna karyawa. Kai tsaye yai nufi bangaren corridor da zai sadashi da dakin Hajiya. A hankali yake takawa  har ya isa kofar dakin, yana kokarin kai hannunsa ya tura sai ya ji shi a rufe. 


“Hmmm ai na jidadi Wallahi an rage mugun iri, sauran su bi baya mu huta, da sannu mugun abun su zai koma musu ai, kin ga idon shi wai? Da wannan makirar sai kuka take kamar yarta”



Shiru yai yana sauraren muryar mahaifiyarsa. Can kuma ya ji ta ce. 


“To shikenan bari na duba yanzu”


Fasa kwankwasa kofar yai ya juyo zuciyarsa cike da tambayoyi kala kala. Da wa Hajiya take? A waya take magana ko da wani? Be shiga dakinsa ba ya sauka downstairs. Ya nufi gurin motarsa tun kan ya karasa ya danna key hannunsa, yana isa ya bude motar ya shiga, be san inda zai je ba at this early morning, but haka nan dai ya tashi jikin nasa ba dadi yau, haka yasa kowa ya karya shi yana gefen falon zaune.

*🐄🐄 FULANI 🐄🐄* 


No comments

Powered by Blogger.