Daudar Gora Book 2 page 84


 ..Salati wajen ya dauka da sallami, kowa na tsinema wa da banou. Cikin girmamawa Kaka ya dubi Shahan-shan da shi gaba daya ma komai ya tsaya masa cak. "ALLAH ya karama adalin shugabanmu lafiya da tsohon rai mai amfani, a ganina barin wadan nan bashi da wani amfani, a samu dutsina a juye musu ruwan maganin nan kawai a musu rajamu anan, dan wadan nan mutane nada karfin tsafin da rufesu ko musu hukuncin zaman kurkuku bazai taba iya magance matsalarsu ba. ALLAH yasa ban shiga hurumin da ba nawa ba".


   Shiru baice komai ba. Kusan minti uku sannan ya dubi Sayeed Fayzul-haq. Da ga haka ya taka a hankali gaban Iffah. "A gusa daga jikinta",. Iya abinda ya fada kenan. A take kuwa tai hamma jikinta ya saki gaba daya. Rikota yay cikin jikinsa ya rungume. A take kowa da kowa na wajen yay saurin yin kasa da kansa cikin hanzari. Shiko ko'a jikinsa ya dagata cak dagakasa kamar ya manta ma da wasu halittu a wajen yay wucewarsa.


🥱Wannan fa shine ga abin fada babu damar magana 😝


   Kamar yanda kaka ya fada kuwa haka akai, tuni hadimai suka cika wajen da duwatsu, kaka ya yayyafesu da ruwan magani, Kamar jira suka shiga diba ana ambaton sunan ALLAH ana jifan su Banou.Ihu suke mai tsananin kururuwar sauti. Amma mutanen nan ko'a kwalar rigarsu. Dama wasu harda fushin Banou tai musu sanadin yaya wasu iyaye, wasu maza, wasu matansu. Dan a cikin wanda ta halakar mafi rinjaye hadimai ne. Babu wanda ya tausaya musu a haka aka jefesu har sai da suka daina numfashi.


Kakane ya ce abar gawawwakin a wajen masu su zasu aiko a debe su, dan sune aiken farko da zasu turama kabilarsu. Haka kuwa akayi, sai dai dan daukar da was samari da yammatan gidan sukayi a wayoyi suka saka a social media cikin kankanin lokaci al'amarin yay amsa kuwa. Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam suka shiga caccakar al'amarin a bayyane ta kafafen ya da labari, kafin wasu awanni labarin ya shiga zagaye duniya, ya zama video mafi rinjaye da ke yawo kuma ake kallo.....**
Sun iso gareta a whale, wahalar da duk wanda ke cikin wanna zuri'a sai da ya girgiza. Hakan yasa su yin cirko-cirko da zaman sauraren abinda sukazo da shi. Ita ko tana zaune a cikin kujerar tsafinta hancinta da Iffah ta gundile ya kara saka fuskar munana matuka. Hakama sauran raunikan da taji sun kumbura fuskar ta kara zama humm.


   Cikin gurfana da garshekar hakin rudani daya da ga cikinsu ya shiga zayyane mata abinda ke bakinsa, "Shugaba wannan aikin yafi karfinmu, ba namu bane ba sai dai ke. Sun halaka Rudde da Zambo da Banou Sun halakasu har lahira uwarmu mai share kukanmu".


    Yanda take huci har Kirjinta na dagawa sama zai baka tabbacin tafa kai kololuwar hasala. Cikin wata irin mummunar tsawa ta nuna su da yatsanta mai dauke da zurkeken farce. "Ni uwa nizan sakaku aiki ku dawo kuce anfi karfinku. Idan kun gujema mutuwarku acan anan ma ita kuka tarar. Ahamanu a daure min su, a aka angulu ta dakkomin gawawwakin su Banou!!"


    "Fadi naki cikawa tawa, uwa magajiyar uwa". Wanda aka kira da Ahamanu ya fada cike da girmamawa a gareta. Cikin abinda bai wuce awa daya ba angulu ta dawo da gawawwakin su Banou, ta jima tana kallon gawarwakin guda uku da ke jina-jina da raunikan jifa,hakama sauran mutanen garin tsaitsaye suke yara da manya maza da mata. Sirkullensu a tsafi ta fara sauran suka dauka da amshi kowa ka gani ransa a jagule da bakin ciki. Bayan sun dauka lokaci sunayi ta bada umarnin daukar gawar Banou zuwa dakin gumaka. kasancewar sauran su aljanu ne dama wani ruwa kawai ta yarfa musu namansu suka shiga zaganyewa, a hankali a hankali suka bace bat.


    "Lokacin da zamu shirya akin gaba-da-gaba yayi, Jajjal ne kawai ya jurema umarninmu har yanzu bai dawo ba. Na sani shi dama mai jajircewa ne da naci akan komai. Kuma duk wani dan da ya cika dan halak a zuri'armu irinsa ya kamata ace ya zama. Kuje maza kuje ku shirya yaki. Sai mun sabauta gaba daya al'ummar kasar ruman. Sai mun sake dawo musu da tarihi irin na baya koma mafiyinsa. Kuje maza kuje!!!!!"


    Wani irin hun fusata suka fasa a tare ikkunansu na jujjiga irin an kada musu gangin nan. A take kowa ya nufi dakinsa na Bamboo suna kwada kiran sunan babban gunkinsu suka shiga shirin yaki. Ba wai wuka ko bindugu suke tanada ba. A tsafinsu suka shiga sake tsimawa. Shiri suke karshen shiri dan gaske. Maza da mata, yara kuwa anata faman tsumasu da abubuwa.…. Babu wanda ya sake fitowa sai cikin dare, inda aka dakko gawar Banou dake tire jikin wani katon mashi aka kafe musu a tsakkiya. An yanke wasu sassan jikinta da ke matsayin hakkin uwa, su kuma suka rufu akan gawar suka dinga yagar namanta sunaci da ihu kamar wasu kiyashi sun samu nama, suna kwala kiran sunayen gumakansu da dodanni Jejin har wani girgiza yake saboda tashin sautin muryiyinsu…..


(😱😱🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️)

Washe gari an tashi masarautar a rincabe da tashin hankali kala-kala matuka. Dan haka kawai aka samu gawawwakin hadimai da Ghazi da jami'an taro sama da hamsin an musu kisan gilla a daren jiya. Ga Iffah tun fitar aljanun nan jiya da ga jikinta barci kawai take, lokacin salla ne kawai idan yayi take tashi da kyar tayita. Tana idarwa kuma zata sake komawa ta kwanta kamar wadda tasha wani abu ko batun abinci ma ba'ayi. Tashin duniya Tajwar Eshaan yayi amma taki tashi in har ba lokacin salla ne yayi ba. Ga a jiya da dare yaje ya duba Malikat Bushirat dake ta faman zabura da ihu sam batai barci ba itama jikin ya sake rikicewa. Hakama duk wanda ke zagaye da ita bai barci ba. Safiyar yau kuma kawai ta tashi da wasu irin manya-manyan kuraje masu radadin azabar zafi dana kaikayi. Kuka kawai take tana rokon a cire mata. Ga sunayen Zawjata-almilk da suka rasu sai lissafowa take daki-daki wai sunzo zasu kasheta, sun zo daukar fansa.


   Gaba daya kowa ya kasa fahimtar komai da ga zantukanta, sai dai duk mai imani ya ganta sai ya ji tsoron ALLAH ya sake kamashi. Kusan a tare babban yayansu da Kaka da akaima kiran gaggawa cikin masarautar suka iso. An fara taruwa an ma gawawwakin wadanda aka rasa salla harda Tajwar Eshaan, bayan an kammala biznesu ne kuma aka rufu kan Malikat Bushirat da zuwa yanzu kurajen duk sun rure da ruwa. Duk wanda yay mata kaikayi ta sosa kuma azabace mai zaman kanta. Shiru kawai kaka yay yana kallonta, yayinda duk wanda ke cikin dakin dan yan uwanta duk sunzo kuka suke sosai. Babban yayansu da shima ke kallonta ya juyo yana duban kaka. Cike da girmamawar kasancewar ya fisa shekaru ya ce, "Baba wannan aikin jinnu ne kam tabbas. Amma miya hada Jinnu da Bushirat duk da dal an sanar min da dambarwar da ake fama da ita a gidan.


   Ajiyar zuciya kawai kaka yayi kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da fadin, "Wannan al'amari ne kam da ya kamata muji a bakinta, dan babu rami babu abinda zai kawo rami kam. Ambaton sunayen wadanda suka mutu da fadin karsu kasheta da take babbar ayar tambayece a gareta Abni".


   Babu wanda bai gamsu da zancen kaka ba a wajen, sai dai kuma hankalinsu ya tashi da jin abinda ya fada din. Dai-dai yana fiddo wani magani Tajwar Eshaan ya shigo dakin rike da hanun Iffah da farkawar ta kenan ta zabura. Riketa yay amma ta rokesa ya barta sashen Ammie zataje. Shima bai jima da baro sashen ba, dan tafiyarsa babu jimawa su kaka suka shiga. Zaunar da ita yayi sannan shima ya kai zaune, take aka shiga mata sannu sai dai babu wanda ta amsawa. Kaka da babban wan su Malikat Bushirat din suka sake mika gaisuwa ga Shahan-shan dan sun gaisa tun shigowarsu masarautar. Da ga haka Kaka ya bada maganin da ya fiddo yace amata hayaki da shi. Cikin sauri suka amsa aka zuba a burner da aketa bulama turaren wuta saboda kurajen Malikat Bushirat din duk wanda ya fashe wari yake yi kamar an tono rubabben nama a cikin kasa. Wani irin fisge-fisge ta dingayi da hun da ya saka Tajwar Eshaan lumshe idanu kawai idanunsa sun kada jazur abin tausayi, shi Iffah ta tsurama ido, ji take da'ace tanada damar sashi ya bar masarautar nan a yau data sakashi, dan sam bata son ai wannan tone-tonen a gabansa. Amma yaya ta iya, bazai yuwu ace a wannan dambarwar babu shugaban wanna kasar gaba daya a cikinta ba. Malikat Bushirat ta jima tana fisge-fisge gashi babu damar taba ta saboda kurajen jikinta itama in ta taba radadi take ji, dan kanta ta lafa bayan ta gama jigata. Yanda ta nutsu yasa kowa tunanin ma Kota mutu ne. A razane Jasrah ta shiga kiran sunanta tana kuka, sai da Kaka yace ta kwantar da hankalinta tanada ranta, turaren zai rage mata radadin kurajenne matuka. llai kuwa sai gashi ta bude ido. Gaba dayansu tabi da kallo daki-daki, yayinda wasu keta tofa mata addu'oi kamar yanda yayanta ya basu umarni tun dazun. Wasu. hawayene masu radadi suka shiga zaryar zubo mata lokacin da idanunta ke sauka akan Tajwar Eshaan da Iffah. Ta jima tana kallon su, sai kuma ta sake fashewa da kuka.


   Yayanta ne ya katseta da fadin, "Sai hakuri Bushirat, kuka baya daya da ga cikin mafita, ki daure ki sanar mana abinda ke faruwa domin musan makamar rikewa wajen yimiki magani. Shin garin aya wadan nan abubuwan masu alaka da aljanu ke zagaye da ke? Minene kuka sani ke da Zawjata-almilk da mu bamu sani ba? Mi kuke boye mana da Jasrah har taji kuna sa'insa a shekaran jiya?".


   Idanu Tajwar Eshaan ya bude da sauri ya zubama Iffah idanunsa da suka kada jazur, amma ita sam taki kallonsa ga fuskarta kicin-kicin kamar yanda tashin take, Malikat Bushirat kam kuka ta sake fashewa da shi. Kafin a hankali ta motsa lips dinta wajen fadin, "Ni na jama kaina Akhi. Ni na siyama kaina komai. Komai kuma ya farane a dalilin HAIHUWA. a dalilin neman haihuwa da tsananin bukatar samuwarta. Buri da kwadayin gani da son haihuwar magaji shine silar labarin zamana a wanna masarautar da ma duk abinda na aikata a tsahon shekaru arba'in da a yau nake girbar abinda na shuka tun daga nan duniya........


No comments

Powered by Blogger.