Daudar Gora Book 2 page 82

 


Chapter: 82


..A guje Jasrah ta fado toilet din da tunanin ko faduwa tayine tunda taga jikinta babu kwari. Wanwar ta sameta a tsakkiyar bayi sume harta farke hannu da wani dan karfe da

akaima bayin ado da shi. Ai batama san ta fasa razananninayar kara ba tai kanta itama a kidime. Jijjigata ta shigayi amma babu alamar rai tare da ita. Sai kawai ta sake fashewa da kuka, dan a rayuwa tana matukar kaunar yar uwar tata, itace ta zame mata uwa a lokacin da suka rasa mahaifiya. Ta mata gata irin na Va da uwa bata taba banbantata da dan data haifa ba. Zama ta iya cewa ta fishi samun gata dan shi an dauke sa a gabanta.Itako tunda tasan kanta a gabanta take,duk abinda tace tana so shi take yimata.Idan tashin hankali yay tashin hankali baka tuna-mai ma ya dace kayi, kuka kawai take faman rusawa tama manta a bayi suke.


    Diwa da ke tsaye a bakin kofar dauke da kayan lunch da ta kawo ma Malikat Bushirat din ce ALLAH ya jiyar kukan Jasrahn. Dama kuma itace tace ta hado abinci mara nauyi ta biyota da shi. Bata da hurumin shiga dakin sai da izini, ga kuma kukan tashin hankalin da takeji Jasrah nayi. Tray din ta ajiye cikin dan rawar jiki ta fice zuwa sashen Malikat Haseenat. Suna zaune a falo Daneen Ammarah na faman lallaba Ummu ta sake kwana itako ta ce yau sai gida zataje suyi shirin tarbar amarya gobe insha ALLAHU sai ga Diwa ta shigo a firgice. Kallon mamaki gaba daya suka bita dashi, Daneen Waheeda Sarkin masifa ta daka mata tsawa dan abinda Diwar tayi babban tsaurin ido ne. Malikat Haseenat ce ta katseta da fadin, "'a Waheeda wannan ba dai lafiya ba bita a hankali. K! Miya faru ne?". Kuka Diwa ta fashe da shi tana nuna bayanta bayan ta zube a kasa. "Ku gafarceni ranki ya dade, babu lafiya ne gaskiya. Ga Aunty Jasrah can nata kuka a dakin Malikat, da alama akwai matsala ne why, tabbas akwai matsala, dan dama likita nata zaryar dubata tsakanin jiya da yau"


Babu wanda gabansa bai fadiba

a cikinsu, dan dama basu jima dayin maganar rashin ganinta a kotu ba. Daneen Waheeda ce make cewa kila bata da ra'ayin zuwan ne yau tunda sun san halinta. Gudun kar maganar tai tsaho ga Ummu da take bakuwa a tare da su yasa Daneen Ammarah kauda zancen ta dako wani.
Gaba dayansu suka kunduma sashen Malikat Bushirat, Ummu kawai aka bari. A gaban idon Banou da ke tsaye da wata bakuwar fuska a jikin fulawoyi suka wuce.Da wani mummunan kallo suka bisu, sai dai babu wanda yace komai. Su Malikat Haseenat da basu san sunayi ba ko mota suka shiga zuwa sashen Malikat Bushirat din. Sun sami Hadiman sashen Jigum-jigum, dan zuwa yanzu kusan duk sunji irin kukan da Jasrahn keyi. Babu wanda ya saurari gaisuwar hadiman sukai ciki da hanzari, dan suma dai suna shigowa da kukan Jasrahn suka fara cin karo. A bathroom din suka sameta har yanzu, da kyar Daneen Ammarah ta dagata, rungumeta tai cikin jikinta dan ta sami nutsuwa, Malikat Haseenat kuwa inda Malikat Bushirat ke kwance wanwar ta nufa, tattabata ta shigayi. Daneen Waheeda dai na tsaye babu alamar damuwa tattare da ita. Sai ma bin toilet din take da kallo baki a labe. Da kyar Daneen Ammarah ta lallashi Jasrah har ta dan musu bayani a takaice. Dole aka kara kiran Doctor sannan aka saka hadimai shigowa suka kakkamata aka fiddota aka kwantar saman gado.


  Zuwan doctor ya tabbatar musu ba mutuwa tai ba, ta dai suma ne. Ajiyar zuciya suka dinga saukewa, shi kuma ya shiga kokarin ganin ta farfado, yayinda Malikat Haseenat ke faman tofa mata addu'oi. Wani irin numfashi ta kawo tare da zabura mai karfi, wadda har doctor dole ya kai hannu a kanta domin maidata amma ya gagara shi kadai. Dole Jasrah da Daneen Ammarah suka matso domin taimaka masa. Amma fa sun kasa dan wani karfi na masifa ta musu, ga fisge-fisge tanayi na tashin hankali.


 (Tofa al'amarin fa babbane) cewar Daneen Waheeda a cikin zuciya tana dan tabe baki. Suko da basu san tanayi ba sunata kici-kicin son gain ta lafa, Malikat Haseenat kuma na tofa mata addu'a. Da kyar suka iya tankwarata, har sun hada zufa sharban kamar yanda itama tayi.Numfashi suka shiga saukewa na jigata. Doctor kuma ya shiga aikinsa. ya sake maidata barci sai dai fa barcin yaki yiwuwa. Dan da ya dan figeta sai ta zabura sai sun sake dannata ta

koma kwance. Al'amari fa tun anayi da marmari harya fara gundurar kowa aka karo doctors da was alluran masu karfi sosai da sukafi na farko da akai mata..Cikin kankanin lokaci zancen rashin lafiyar ya zagaye masarautar. Masu tausaya mata nayi masu farin ciki nayi. Masu kuma fassara al'amarin da wani abu daban nayi. Dan danan labarin ciwon nata ya zama latest topic à cikin masarautar. Dama ga nã hukuncin su Miran Jasim da bai gama disashewa ba.

***


Duk wanna al'amarin Iffah nacan kwance tana shan barcinta bata san bikin da ake ba. Dan sai la'asar ta tashi. Wanka tai tayi salla. Bayan ta kammala kimtsawa ta fito neman abinci dan yunwa takeji. Hadimanta da ke dan kus-kus din su suma akan al'amurin Malikat Bushirat din sukai saurin mikewa. Kallo daya ta musu ta dauke kanta, dan har yanzu zuciyarta babu dadi. Zama tai tare da bada umarnin a kawo mata abinci anan. Cikin ko kankanin lokaci amintacciyarta ta jere komai. Ta bude zata zuba mata ta dakatar da ita idanunta kur akan abincin. "Waya dafa wannan abincin?"Ta fada tana kallonsu. Cikin rawar jiki amintacciyar tata ta sanar mata itace da mai girki. Ta nuna mai abincin. Shiru Iffah tana duban wadda aka nuna matan sai faman sinkuy da kai take. Ai bama tasan ta daka mata tsawa ba tace ta dago. Ba ita da taima tsawar ba hatta sauran hadiman sun matukar razana. Dan abu ne da bata taba musu ba. Wani irin kallo Iffah take ma matar rai bace. Jikinta har tsuma yake ga idanunta sunyi jazur na tashin hankali. Duk wanda ya dubeta sai ya razana, idan ma irin su Bily ne fitsari zamu saki a zani😝Dan gaba daya ta juye tabbacin ba Iffah bace.


Wani irin shakota Iffahir tayi ta dauke ta da bahagon marin da ya idasa tsurar da sauran hadiman jikunansu suka fara rawar mazari. Marin matar nan Iffah take tamkar ALLAH ya aikota. Gashi ta shaketa da iya karfi. "Ubanwa ya aikoki nan?". Ta fada da wata irin gigitacciyar murya mai matukar razanarwa da amsa kuwwa. Cikin kakarin azaba matar da gaba daya ta gama jiyo kamshin mutuwa da kyar ta ce, "Uwa."


    "Uwa. uwa. Iffah ta fada kamar mai bitar sunan, sai kuma ta kyalkyale da dariya ta kuma hade fuska. Cikin dage gira da zuba jajayen idanunta a tsakiyar na matar da ke a shake har yanzu a hanunta ta ce, "Ohhhyyyyo ita bata gane karatun kurma kenan. Bakuma ta gane gargadin makawo sai ya doka sandarsa. Shin wai dolene sai ta fusatani ne?!!!!!. Nace sai ta ga ainahina sannan zata tabbatar nafi Karfinta?!!". Ta sake fada cikin karaji tana gwara kan matar da centre table. Wata iriyar wahalalliyar kara ta sake illahirin jikinta na rawa dan fa ta bugu matuka duk da katako ne. Tuni hadiman sun fara sakin fitsari a wandunansu. Yayinda Iffah da bata san sunayi ba tana cigaba da maka kan matar nan jikin centre table. Sai da tai mata ligi-ligi har numfashinta na fita da kyar ga jini yay mata faca-faca sannan ta dagata tsaye, cikin daka tsawa ta dubi amintacciyarta tace a kira mata Ghazi guda biyu. Cikin kankanin lokaci suka iso kuwa. Jefa musu matar tayi taki zube yaraf a gabansu. Rai bace ta ce, "Ku dauketa, a dauremin ita a tsakkiyar masarautar nan". Cikin rawar jiki suka amsa mata da "Umarninki shine abin jiranmu ranki ya dade". Kota kansu batabi ba ta nufi dining, wajen wanke hannu ta nufa ta wanke hanunta da jini ya dan bata, har yanzu a birkicenta take. Bedroom dinta ta koma, babu jimawa ta sake fitowa cikin sabuwar shiga. Har yanzu hadimanta na lafe jikin bango a tsorace. "Ku biyoni da wannan abincin". A zabure duk suka mike, Itako tuni ta ma fice abinta. Kamar yanda ta saba tafiya duk inda take so a kafa yanzun ma hakane. Sai dai yau ko sau daya bata kula gaisuwar kowanne hadimi ba. Koma kallo basu isheta ba har ta isa sashen Malikat Haseenat. Anan din ma babu hadimin data kula Sai dai tana binsu da kallo daya bayan daya. Ganin babu wadda take nema cikin wata irin razananninayar murya ta kwala

kiran sunan "Banouuuu!!!"


    Ba Banou din da taima kiran mafarautan ba, hatta Ummu da Iftihal a dari suka fito, hakama duk wani hadimi dake sashen dama wanda basu san da zuwanta ba har tuntube suke wajen fitowa. Banou da jikinta ke wani kakkarwa ta zube a gabanta, wani irin mari ta kai mata itama tare da shakota ta mikar da ita tsaye. Cikin murya mai razanarwa ta furta, "Ina bakuwar takini?!!!!" 


Ba Banou din kawai ba, kowa ma a wajen jikinsa rawa yake yi, hatta Ummu data raineta yau ji tai Iffahn na bata toro. Iftihal kam ai tuni ta jike dogon wandon jeans din jikinta da fitsari, jikinta ko tsabar rawa da yake tuni har wayarta taje kasa bata sani ba 


   Banou dake watsal-watsal din kakarin mutuwa ta nuna matar da suke tare dazun lokacin da su Malikat Haseenat ke fita zuwa sashen Malikat Bushirat. Sakin Banou din tai, sai gata a kasa rikica. Tako kwalla karar azaba. Da hannu taima waccan nuni da tazo. Zatai mata wani noke-noke tai wani irin fisgota ta buga da bango. Gaba daya falon ya sake ridewa, Iftihal ta shige jikin Ummu ta fashe da kuka. Cikin karaji Iffah ta ce, "Ku nawa ne?!!". Jikin matar na rawa ta ce, "Karki kasheni, nayi alkawarin zan fada miki duk abinda kike bukata, na rokeki.


'"'Na ce dan uban ubanka ku nawa ne?!!".

 

"Mummu biyar ne?"

 

"Kai mi aka aikoka yi? Da har ka koma suffar mata?"


"'Z.z zan taimakawa Banou ne mu karasa uwar masu gida, d. d. Dan ta dade anan din tare da ita…✍️


No comments

Powered by Blogger.