Buri Daya Complete Hausa Novel

 


Ummuanwar😍: *_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _*ZAFAFA BIYAR*_🔥*_DANDANO DAGA LITTAFIN,_*


*_BURI 'DAYA_*

_NA MAMUHGEE_*_1_*


Bismillahir-rahmanir Raheem.Sauri yake faman zubawa Amma yanda saurin nasa yake tamkar Yana gudune sbd yanda ko gani bayayi sosai ga babbar rigarsa sai cika takeyi da iska tana qarawa,


Da safe kafin yafita jin zuciyarsa yakeyi fes sbd tunanin yau ranar sa'arsace tunda zasuje maula gidan mai arzikin da yafi kowane mai kudin jahar kudi harma dana wasu jahohin saigashi masifar datafi ha'darin mashin bala'i ta afko masa Dan gwara yasan sama mashin yayi dashi ya zubar akan abinda rashin hakurinsa yaja masa ayau din,


Yana shanyo kwanar layin gidansa wani mugun zufa ya yanko masa ya tattaro kuzari da qarfin hali yacigaba da tafiya Yana kallon tarin kalolin 'yan ta'addar dake cike da qofar gidansa sun baje sunashan iskar makeken bishiyar durumin dake qofar gidan  kusan su goma Sha biyar kowanne da kalar mugun makamin dake soke cikin qugunsa ko wani sashe na jikinsa Wanda duk qaddara takaisa shiga huruminsu yanxune zasu yiwa rayuwarsa illa Kuma ba Wanda ya isa ya tanka sbd hukumar ma da ikonta suke aiki sbd zakinsu shine amintaccen yaron DIKKO DILLA.


Wasu daga cikinsu fuskokinsu cike sukeda zanen Sara ko Suka haka jikinsu kusanma Babu Wanda fuskarsa bazata saka mai qaramin qarfin jini zawoba sbd Sam babu alamar wasa atareda fuskokinsu ga wani irin warin daga da wiwi dake tashi tun daga farkon layin unguwar shiyasa yawanci duk Wanda yake Dan asalin gari yasan anguwar ba wurin ganganci bace anguwar sarki ZAKI NEYO ce Sam ba'a mata garaje.


Da gudu gudu sauri sauri yaqarasa shigowa gidan tsohuwar babbar rigarsa kalar ruwan madara data koma kalar brown tana sake dibar iska sbd sauri dayake diba kamar zai tashi sama musamman yanzu daya qara ganin bataliyar 'yan daban dake qofar gidansa kamar qofar gidan wani qaura.


Yana shiga tsakar gidan sbd tsantsar rudewar dayake ciki ya kwashi wani mugun tuntunbe saura qiris ya kife cikin garinda iya talatu ta shanya na kayan mata datake siyarwa duk da duk rabi garin kukane take zubawa sbd yayi mata afkin siyarwa. 


Zaune take tana lissafin jarkar tsimin data Saida wadda duk rabi jollyjus ne ta zuba aciki shima sbd afki.


Kallonsa tayi amatuqar sheqe cikin takaicin yanda ya tashi goga mata asara ta hanyar barar mata da gari a 'dan hasale tace"


Wai meye hakane kaketa muzurai kana rawar jiki kamar 6arawon daya ha'diyi kunama?,

Yanzu wannan garin dakake Shirin bararmin kasan hasarar nawane zaka jazamin Wanda nasan ko shekara zakayi kana sana'ar taka ta mutuwar zuciya bazaka Tara kudin biyana ba inyi magana jarabben sarkin gidannan yace bayason hayaniya kokuma yakamamin dabbobi yasa ayanke masa inaji Ina gani qatti suci banza.


To wlh banshirya hasaraba kusa Dan haka kafita idona inrufe.


Takalmin hannunsa ya fitar daga cikin babbar rigarsa data gama jiqewa da zufa,

zufa na qara tsatsafo masa Yana zare qananun idanuwansa dasukafi kama Dana Chinese din hauren qasa yace"


Qaddara takaini daukar aron takalmin ZAKI NEYO wainda kikaji dahiru yace dubu biyar suke nafita dasu wlh sun katse fata fata duka qafar biyu gurin gudun mahaukatan Karnukan da alhaji dikko dillah yasa aka sakarmasa ga yan maula da mabaratan dasuka tarar masa qofar gidansa duk da tarin yan sandan dake gadin gidan.


Wani irin sabon qululun baqin ciki da takaicine ya quleta tana watsa masa wani mugun kallon takaici baqin ciki yahanata ce masa qala sbd duk iya quluwa da baci ranta yayi sbd sanin masifar da hakan zai jawo

ta miqe ta tahau tattara kan akuyoyinta da kajinta dake walwalarsu filin tsakiyar gidan Dan tasan yau akwai saukar aradu a gidan Dan yau ko butar gidan saita ci uwarta idanba Allah ya tsareba baresu

Akuyoyinta da kajinta kuwa tasan tsaf zai take mata kawunansu su mace abanza,

Tana zaman zamanta rukayya taje Lagos ko wata shegiyar qasar ta hado jini da kafirai kokuma qila wata qabilar anxo anhaife mata masifar daba ita kadai ta addababa har yan gari da anguwa Dan kuwa neyo ba ubanda baya tsoro da shakkarsa ga wani irin kwarjini dayake qarawa mutane tsoronsa.


Wani Dan dakin kaji ta gargadasu gabaki daya ta rufe da kwado ta zare mukullin ta dawo tafara tattara garinta tana kwashewa cikin takaici da baqin cikin dake tafasa zuciyarta ta bude murya tace"


NADIA uwar uban me kikeyi a bakin murhun haryanzu dabazaki taso kitayani tattara duk wani tattalin arzikina dake tsakiyar gidan nanba kinaji mara danganar ubanki ya ballo Mana balain dayafi 1990 masifa.


Aje plate din robar dake hannunta tana fifita wutar murhu dashi tayi ta taso gabanta na matuqar faduwa sbd jikinta dayayi sanyi dajin abinda babansu yayi Dan tanajinsa duk abinda yake fadawa iya talatun koba komai tasan idanba Allah ne ya fiddataba akantane zaifi sauke haushinsa tunda itace mara galihu agidan Dan idan yafara kowa shigewa daki yake ranar bamai fitowa saiyagama fushinsa ya sauka ita kuwa dole take fitowa sbd balain iya talatu shiyasa idan tafito yake sauke Rabin haushinsa akanta ga wani irin mugun tsoronsa da shakkarsa da Allah ya halitta a dukkanin zuciyoyin 'yan gidan harma Dana waje saidai zata iya cewa itakam tsoronta yafi nakowa duk da dai duk balai da msifar iya talatu da duk anguwar ake tsoro itama shakkarsa takeyi.


Jikinta na Dan rawa tafara tattarawa iya talatu kayanta..


Da 'yar waqar sani sabulu wata 'yar budurwa tashigo gidan taci ado cikin Riga da skirt na atampar sheraton 'yar dubu uku da dari biyar fuskarta a kimtse tsaf da kwalliyar dataji hoda da foundation datai mata kyau ba laifi da Jan jambaki 24 hours hannunta riqeda Jakarta da 'yar wayarta vivo mai Dan dama dama sai qamshin bokhour takeyi daga gani cikin nishadi tadawo.


Cak ta tsaya tsakiyar gidan tareda kallonsu cikin mamaki da 'yar fargaba ganin sai tattara kayan tsakiyar gidan sukeyi fuskar iya talatu ba alamar rahama ko kadan ta maida kallonta kan babansu dake tsaye gefe sai zufa yakeyi kamar Wanda yaci wuta takalli iya talatu tace,


Iya lafiya kuke kakkamta kaya rana tsaka?


Harara iya talatu tafara watsawa dattiya dake tsaye har lokacin kafin tace,


Rashin hakurinsa yakaisa ga daukar takalmin ZAKI NEYO yasa yaje yawon maula aka hadosu da miyagun karnuka sukaiwa takalmin fatafata.....


Kallon babansu tayi cikeda takaicin Rashin danganarsa da ako yaushe baya jawo musu alkhairi sbd fargaba da tsoron masifar daya jawo musu basujiba basu ganiba ta turo baki tace,


Nikam baba meyasa bakason ko yaushe a zauna lafiya agidannan gashi yanzu mutum saiya kwana biyu bai wani dogon motsiba sbd tashin hankalin yaya neyo

Yanzu wlh ko mai neman aurena yazo qofar gidannan saiya gwammaci karo da mahaukacin matashin kare akan fushin wannan abin daka yi baba.


Kallon iya talatu tayi cikin takaici tace,


Ni wlh nakoma gidansu anty saratu sai dare ko gobe zandawo Dan wlh bazan yarda a mari wannan kyakkyawar fuskar tawa abanzaba tunda babu Wanda yake siyamun mai.


Juyawa tayi rai abace cikin haushi da takaici ta fice tabar gidan tana guna guni sbd tasan tsaf da marin neyo gwara mashin yayi sama dakai.


Nadia kuwa cikin sanyin jiki duk takai ma iya kayanta daki tadawo ta gaban baban nasu dake tsaye Yana muzuran ido cikin mirsisi yace,


Ke ungo nan yi musu dubara da allura da zare ki dinkesu kikai dakinsa ki ajiye masa Kuma wlh duk rintsi Kar shegen dayace nine nasakasu.


'dagowa tayi da sauri takallesa da manyan fararen idanuwanta cikin tashin hankali.


Harara ya watsa mata yace,


Bazakiyi bane kike kallona kamar nace ki kashe mutum.


Sunkuyar da kanta tayi tareda girgizawa idanuwanta na cikowa da hawaye ta karba da hannu biyu ta wuce.


baza babbar rigarsa yayi tareda kada mata iska ya fada dakin iya talatu Yana sharce zufan daya kasa daina jiqasa.


Nadia kuwa bakin akurkin dakinta ta zauna bayan tadauko allura da zare tahau yiwa takalman kwaskwarima jikinta na matuqar rawa sbd sanin yau kwanan wahala zatayi idan yadawo yaga wannan dinkin a jikin takalmansa bayan antsinka.
'Daga takalmin tayi ta qura masa ido tsawon mintuna hudu kafin ta sake sakin ajiyar zuciya akaro na Babu adadi bayan zamanta na Shirin dinkin takalmin.


Iya talatu dake zaune ha'deda rai zuciyarta na qara cika da takaicinsa ta harari qafafunsa cikin quluwa tace"


Kaga nidai yi daga can gefe karka takani da wannan qafafun naka dasukafi kama da kofato,

Kuma wlh kasani matuqar Zaki yayi mummunan sauke mana balainsa aka gogamin asara wlh saikaji a aljihunka da cikinka Dan wlh sainayi sati banbaka tuwonaba tunda zuciyarka tagama mutuwa Sam ko kunya bakaji kullum Kaine daga ha'darin mashin sai karo da keke kokuma gudun fanfalaqin ceton rai duk gurin yawon maular mutuwar zuciya.


Bai kulataba yahau cire babbar tsohuwar rigarsa dake sharkaf da zufa duk saita qara canxa kala.


Ficewa yayi ya dauki buta ya nufi bayin dake tsakiyar gidan ya fito ya zauna ya wanke qafafunsa da ako yaushe talatu ke shammata sbd shegen yawonsu dashima yasan yanadashi sbd idan ya bazama cikin gari yafara yawo sai Rana ta fadi yake dawowa gida wanda wani lokacin wahalar banzace yakeyi sbd haryagamo gantalinsa yadawo bayasamo ko nera biyar.


Yana cikin wankin qafar yajiyo qarar fito Yana dosowa cikin gidan qafa daya dama ya wanke zaifara ta biyun yaji fiton Yana sake dosowa cikin gidan atake ya aje butar ya miqe sukai ido hudu da Nadia dake zaune tana kallonsa cikeda tausayin kanta na aikin daya data.


Cikeda borin kunya ya dauke Kai daga kallonta ya nufi dakinsa da iya talatu yashige bai tsaya wanke dayar qafarba tunanin qila Zaki ne yadawo duk da yasan Zaki Sam baya fito sbd tsabar mulkin dayake murzawa a dabanci Dan ko wani hakimin bai kaisa baza mulkiba atasa duniyar ta 'yandaba Wanda shiyasa ake kiransa da sarki Zaki.


Itadai iya talatu Bata sake kallonsa ba sbd tana lureda duk hankalinsa duk ba kwance yakeba sbd abinda yayi din Saidai bazatayi masa mgn ba qyalesa zatayi ai zakin shine daidan kowane dan banza na gidan Dana waje.


Cigaba tayida hada garin kayan matanta tana daurawa a leda batareda ta kalli ko inda take zaune Yana qoqarin shafawa qafafuwan nasa Vaseline kamar Wanda zaije wani gurin.


Lalah ne yashigo gidan Yana fito daukeda wata baqar leda ta kayan neyo daya daya karbo masa guga sbd akwaisu da babbar hidima sbd AMBY DIKKO DILLA na gari Kuma zakinsu shine babban yaronsa dayafi yarda dashi da boyayyun ayyukansa.


Dakin zakin dake farkon shigowa ta zauren gidan ya shiga ya ajiye masa kayan kan katifa yafito ya jawo qyauren dakin.


Harzai fice ya dakata tareda juyowa da sauri ya kalli Nadia dake riqeda takalmin Zaki da aka siyo masa daga kaduna....


Baki ya sake cikeda mamaki da tantama ya dawo gabanta ya tsaya Yana kallon hannunta dake riqedasu Yana rawa alamar amatuqar tsorace take.


Cikin tsananin mamaki da muryarsa irinta riqaqqun yan ta'adda yace"


Wannan meyene a hannunki?? Yana nunawa da hannunsa sbd sanin ba magana takeyiba.


Jikinta har wani irin rawa yakeyi sbd tsananin halinda zuciyarta da gangar jikinta suke ciki hannu na rawa ta daga zata nuna qofar dakin babansu saita tuno da gargadinsa tayi saurin sauke hannu tana sake qanqame takalman.


Amasife yace"


Ke ubanwane yace ki shiga dakin sarki harki dauko wannan takalmin Dan......zaro manyan jajayen idanuwansa yayi sbd sai alokacin ya lurada yanda suke ya hadiye wani yawu cikin jinjina mata yace"


Wlh idan ko sunana yafito acikin Wainda suka gani saina qarasa mayarda maraji bayan Rashin magnar dakike fama dashi.


Ficewa yayi Yana jinjina mata Dan kuwa ba qaramin jarumtar tabama takalmin tayiba.


Yana fita qofar gidan atake ya tseguntawa Nanu Yana cewa"


Babahh yaufa akwai saukar aradu a cikin gida da anguwarnan mubi ahankali Dan kuwa yau antabo sarki inda ba'a tabowa.


Cikin gidan kuwa jiki a salube ta tashi ta sidada dakinsa ta ajiye daga ciki bakin qofa tadawo cikin gida taci gaba da aikin tuwon iya talatu na siyarwa da dare jikinta amatuqar sanyaye Dan har wani zazzabi takeji.

##Mamuh..

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee2_*

Iya talatu na gama daurin garinta na mata ta tattara ta zuba cikin jakar datake yawon sana'ar kayan matan ta miqe batace masa qalaba musamman ganin magriba ta gabato tana saneda idan ba Allah ne ya rufa asiriba bazai fita sallar ba Saidai yayi agida.


Daga baqin qofar dakin ta tsaya itama zuciyarta na qara tafarfasa takalli Nadia tace"


Ke Kinga bar tuwon nan Dan kuwa ko anyisa kwantansa zanyi sbd Babu mai gigin zuwa yau gidan nan idan sarki yadawo yafara sakin boma boman balainsa.


Babu 6ata lokaci ta sauke qatuwar tukunyar tuwon miyar kuwa tunda sunyi sai ayi tuwon siyarwar gobe da ita Dan dama iya talatu na hakan acewarta miyarma tafi zaqi sbd magi da kayan miyar sun qara tsuma.


Ana Kiran magriba tagama tsare tsakiyar gidan da bayinsu Wanda wannan Kuma qaidar zaki ce dole ake share gidan da yamma awanke masa bayi sbd wankan maraice duk da bayin Babu siminti haka take kelaya masa ruwa ta wanke.Gama alwalarta keda wuya ta hangi JJ yashiga dakin ya Zaki da wata irin qatuwar sharbebiyar wuqa Mara kyawon gani atake hankalinta yatashi ta miqe sbd dazarar kaga JJ to sarki nanan sbd shine amintaccensa shikuma Babu abinda yakeyi Saida jj sbd JJ yakasance tamkar wani sashe na jikinsa da rayuwarsa,


JJ shine mutum na farko dayake gani tamkar amatsayin 'dan uwansa na jini wanda yasani kowane balai JJ zai iya runguma akansa,

Sunsha fafatawa da manyan 'yan taaddar wani yankin JJ ke kare masa kowace irin Sara da sukane shiyasa jikinsa da fuskarsa kusan koina dinkine na sare sare.A sulale tashige dakinta daya zamto na mamarta tun tana raye ta shimfida tabarmar sallarta ta kabbarta da sauri sbd tasan daga yanzu komai na iya faruwa.


Iya talatu na fitowa alwala ta hango fitowar JJ daga dakinsa ta sake hade Rai takaicin dattiya nadawo mata sabo ta zauna Babu Bata lokaci tayi alwala ta miqe tanaji yaro na sallamar abashi gishiri da daddawa na saba'in tayi kamar batajiba ta fada daki tana mitar"


Yanxu ga ciniki na bibiyar mutum Amma ba hali sbd ni nafi kowa asarar rayuwa ta auren Dan maula,acikin masu maularma Mara dangana.


Shidai dattiya najinta baice qalaba yatayarda sallarsa yafara sbd yasan talatu idan tafara mitarta saita Hana duk wani jindadinsa walwala.Babban durom 'dinta dake gefen randar tsakar gidan cikeda tsiminta data zubawa jollyjus harda qarin tiara  sacet 'daya taji yayi wata irin qara alamar ball akayi dashi atake ta tayarda sallah tana hararar bayan dattiya dayaqi sallame sallah bayan tasan yagama.Wata irin kakkausa,budaddiyar murya dake natse da iko tareda tsatsauran Rashin arziki yace"


Duk ubandake gidan nan yafito kafin wlh yanzu nasa bulldozer tazo tabi takan gidan gaba daya...Wani yawu dattiya ya hadiye Yana fici fici da ido cikin qarfin hali irin na yanuna sallah yakeyi yayi gyaran murya alamun sallah sukeyi.


Sake daga murya yayi yace"


JJ kiramin anny awaje yazo duk ubunda ke cikin gidan nan idan bai fitoba ya sakar musu bingo yaci uwar kowa da kowa yafitomin dasu.


Assalamualaikum assalamualaikum""iya talatu da dattiya Suka sallame sallar atare tana takallesa tace"


Wlh katashi kafita kafada masa gaskia tun kafin asako mana shegen bingo dinnan yazo yayimin banna kana gani wancan karon inaji Ina gani aka sakosa yayimin kaca kaca da katifa tayi kamar injin aka sata aka 6arza.


Kallonta yayi Adan hasale yace"


Wai talatu meyasa bakida Imani ne Sam bakya girmamani amatsayin mijinki kullum sai Rashin da'a.


Wani sheqeqe takallesa tace"


Yanzune kake maganar miji da mata kanaji 'dan ta'addar 'dan qanwarka yanamin fatali da kayan tattalin arzikina.


NADIYA data gama sallah a sadade tafito tanabin bango hannuwanta a fuskarta sbd tasan itace zata fara Shan mari.


Fitowa dattiya yayi Yana zaku'do kafada fuska da alamar tambaya yace"


Kai zaki banason Rashin arziki meya faru kake mana barazana da bulldozer da mangaribar nan iyeee?


Wani kallo zakin yayi masa da manyan idanuwansa masu rikita mutane da kwarjininsu atake yagama laranto yanayin baban Kuma yasan duk duniya Babu ubanda keda jarumtar dazaiyi qalula yadauki abinsa bada izininsaba sai baban kallonsa yagama na mintuna kafin ya juyo gurin Nadiya data rabe a bango kamar munafuka atake 'dinkin zare da allurar dake jikin takalminsa Suka dawo masa yasan ba aikin kowane Dan iska bane sai ita atake ya fizgota ya kifa mata wani lafiyayyan mari tayi saurin zubewa qasa tana girgiza masa Kai alamar yayi hakuri hawaye na cikowa idanuwanta.


Cikin muryar bada umarni yace"


Wlh kika sake shiga huruminda banakiba saina karya wuyanki nabawa bingo namanki dagake har ubandake dake saki.


JJ yayiwa wani kallo yace"


Kasan mezakayi akan hakan.


Juyawa yayi yafice Yana murda zaren layar maganin qarfe dake daureda murdaddiyar qwandar hannunsa kasancewar Babu riga ajikinsa sai baqar singlet sa dogon wando baqi Wanda kusan kullum sune kayansa shiyasa murdadden jikinsa ke sake sakawa mutane shakkarsa.


Kallon baba JJ yayi tareda sake wani lalataccen murmushi kafin ya juya yabi bayan Zaki Yana 'dan kallon gefen Nadiya sbd jin sheshekar kukanta data fara bayan barin Zaki gurin.


Ba kunya baban ya kalleta cikeda qarfin hali yace"


Ke banason shashanci me akayi na kuka?maza maza tashi kibar nan.


Miqewa tayi ta nufi dakinta ta zauna inda tagama sallah tanajiyosa lokacinda ya sauke wani irin numfashi mai qarfi Yana cewa"


Waiiiii fitar kutso.


Baza rigarsa yayi ya wuce waje hankalinsa kwance ya nufi qofar gidan mal idi maqwafcinsa dasuke firar dare tare harma dacin tuwon dare tare hakama sana'arsu guda wato yawon maula.


Wani tsakin takaici iya talatu tasaki data fito taga yanda tsakar gidan yayi jajir da kalar tsiminta dayayi fatali dashi tana tattara robobin durum din daya fashe tace"


Wlh dai ruqayya kin cuci rayuwata nidai ko bayan mutuwarki banhutaba Dan gwara ace kinanan da wannan masifar dakika barwa jama'a,,

Kai wlh Allah yatsinewa yawon duniya.


Itadai Nadiya najinta ta lafe sbd kullum idan aka tabo iya saita tsinewa yawon duniya dayayi sanadin samuwar yah Zaki wani zubin kuwa tata uwar ake zagi.


Dakinsa yakoma zuciyarsa ba wata doguwar damuwa sbd yau babbar ranace agaresu sunyi nasarar qwace mulkin shiga da fice na duk wani baqin mai ta hanyar ruwa Wanda yasa gobe sukeda babbar hidimar bikin murna Wanda alh dikko yasaki wasu mahaukatan kudi aka tsara shiyasa kawai yau baiyi wani daukar matakiba duk dai za'a Dan koyawa baban hnkali badan haka ba wlh da yau kowa saiyaji ajikinsa ko dukiyarsa.


Qarfe goma da arbain baba yataso daga gurin fira yayo gida Yana shigowa Kai tsaye ya nufi butar dake bakin gurin wanke wanke Yana juyowa yayi ido hudu da bingo Yana wani irin shesheka Yana zaro harshensa dake dalalar yawun dake nuna tsantsar ha'darinsa.


Butar saki cikin tsananin tashin hankalin dabai saniba yace"


Ya salamu,,,ya azzizu....Wai menake gani haka..ke talatu...ke talatu..Nadiya.. Nadiya Zaki fito kosainaci gidanku idan nasameki.


Wani irin tsalle bingo yayi 

Bai direba baba yayi wurgi da buta ya nufi dakin Yana isa qofar yajita gam alamar iya talatu ta rufe Dan dama tasan wlh Zaki bazai bar babanba.


Ganin bingo yayo gurinsa aguje ya nufi qofar fita yatararda an qargameta Yana juyowa bingo na yowar tsalle zan afko masa shima tsallen ya daga yayi gefe yakama katanga zai hau Amma kasancewar dattijanci yasa yakasa Amma Kuma bai fasaba Yana kama katangar yanaji hannunsa ya gwafce Amma bai tsayaba ba wata wata ya dire waje sai cikin kwatar gidan mal idi atake ya miqe Yana dingisawa ya fada gidan mal idi Yana rafka gigitacciyar sallama.


Kallonsa mal idi yayi Yana haskasa da fitila yace"


Lfy mal dattiya?


'dingisawa yayi Yana gyara tsayuwarsa sbd qugunsa daya riqe yace"


Haba mal idi yaza'ayi kabar kwata qofar gida haka ba'a ragewa gashi yanxu naje wucewa na fada

Yanxu Dan Allah idan banibane wani yaji ciwofa?""ya qarasa zancen Yana matse ido cikin duhu sbd tsananin zugi da qafarsa da hannunsa suke masa.


Cikin jimami mal idi yace"


Naji zan gyara kwatar kaje kajida kanka dai yanxu.


Cikin masifa yace"


Au hakama zakace??


To mal datti yanxu kakeson nagyara da daddaren kokuwa?nace zan gyara da safe.


Waiwayen qofa yayi Yana hararar idin cikin duhu Dan so yayi yace zai gyara yanxu saiya tayasa har bingo yabar gidan ga qafarsa da hannunsa sai shegen zugi suke masa,,,kaiii Allah ya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin Zaki dandai shikam Zaki yazame masa masifa da balai yanzu dabai guduba yanaji Yana gani bingo zai yayyage masa Kaya da mazaunansa ta yanda saiyafi wata baije yawon maularsaba..

MAMUH.

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee3_*

Jan qafarsa data riqe yayi Yana 'dingisawa a duduqe ya nufi qofar gidan nasa Yana tura qyauren yaji yabude yasaki wata irin qwafa yana cewa"


Nibansan menayiwa ruqayya ba zataimin wannan sakayyar ta ha'do zuri'a da dangin marasa Imani gashinan 'danta zai kasheni kwanana Basu qareba.


Tunda yaji qofar abude yasan sunkama bingo dinsu shiyasa yashigo Kai tsaye 

Itama iya talatu tsabar Rashin 'da'a ga miji sai yanxu daya gama hasarewa zata bude qofar dakinta.


Tsuke fuska yayi ya kwadawa Nadiya Kira tafito tana sunkuyar dakai sbd sanin dazu Bata fitoba daya kirata.


Ciki ciki yayi da qananun idanuwansa yafara zuba mata fadan Rashin arziki kafin yasata ta debo masa ruwa ya wanke jikinsa da duk yabaci da kwata ya dudduqa ya qarasa 'daki Yana sakarwa talatu nata fadan a kaikaice itadai Bata kulasaba sbd gabaki daya ranta har lokacin abace yake.


Haka Suka kwana kowa na hararar Dan uwansa.


Qarfe 6 na safe ta Dora ruwan kunu a babbar tukunya tahau aikin sharar gidan kafin ta bude dakin kaji da akuyoyin iya talatu Suka fito Suka hau walwalarsu a tsakar gidan tana cikin wanke wanke yashigo gidan wuyansa rataye da towel milk da brush tareda Colgate toothpaste.


Kallo daya tayi masa taci gaba da aikinta sbd batada muryar ko gaisuwa shiyasa iyakacinta da kowa ido.


Ruwa yadiba a qaramin plastic bucket yakoma dakinsa ya zura heater ya kunna ya fito qofar gidan inda yake cikeda yaransa wasu na karyawa wasu na wasa makamansu sbd taron yau.


Wata kujerar busashen katakoce dake kafe acikin qasar gurin alamar tariga tashiga qasa bazata taba daukuwaba ga sulbi sbd alamar dadewarta da qarkonta

JJ yayi saurin dauke wuqar daya Dora gurin Zaki ya zauna ya karbar wuqar Yana bin bakin kaifinta da ido yace"


JJ wannan qwamar taka yau cikin takalmina zan sata akwai Wanda dikko keson nayiwa zanen yorbawa agurin taron.


Dariya JJ yayi shida Nanu..


Nanu yace"


Sarki kowaye wannan za'ayiwa na yorbawa tasa taqare tunda sarkine dakansa zai masa aiki.


Wani irin murmushin gayya yayi Wanda ya lotsarda kumatunsa ya 'daga wuqar Yana kallo yace"


Yau uwarsa bacci zatayi tana sauke ajiyar zuciyar kukan dazata yini tanayi.


Dukkaninsu dariya Suka sheqe da ita suna"""Allah ya tarwatsa maqiyanka sarki.


Ruwa Nanu yakawo masa yafara brush dinsa daganan zaune sukuwa nan wasu Suka cigaba da gyara makamansu.


Kallon JJ daya qura masa ido yayi yasaki wani slow murmushi Yana jingina da bayan kujerar yace"


Yaya akayine magajin Zaki.


Cikeda jin dadi jj yashafo tarin sumar kansa da akayiwa kitson cuku bayan anyi dying dinta zuwa baqi da brown yace"


Neyo yau kwarjinin naka bazai Barima ko alh dikko yafika cikawa mutane idoba.


Murmushi yasakeyi Yana shafo gemunsa na tsantsar ta'addancinsa dayake tarawa ya miqe tsaye tareda nufar qofar gida zai shige yace"


Magajin Zaki Kaine kadai kakewa Zaki kwarjini bayan Kai Babu ubanda bazan ketawa rigar mutunci ba ciki kuwa harda tsohon najadun gidan nan.


Shigewa yayi jj yabi bayansa da kallo Yana girmama girman qauna da matsayinda neyo yakedashi arayuwarsa sbd shine yamaidasa mutum yacirosa daga basifa da balain dayafi ta'addanci,

Yazame masa uwa uba tareda cike duk wani gurbi na Dan uwa dayake buqata aduniya shi

yasa zai iya sadaukarwa da neyo rayuwarsa.


Wanka yayo yafito daga bayin tsakar gidan sanyeda threequater wando da qaramin tawul rataye a wuyansa.


Kallo daya Nadiya tayiwa qaqqarfan jikinsa dake bayyanarda qarfinsa,

Wani dogon tabone da sarar Adda yake zane a qirjinsa har zuwa gefen qugunsa Wanda aka ta6a yimasa lokacin daya fara haduwa da JJ sadai Wanda yayi masa sarar yananan yarasa qafafuwansa har abada Dan kuwa Saran rage yaran neyon sukaiwa qafafuwansa Allah yasa yanada kwana agaba.


Wannan tabo shine tabo 'daya dake jikin neyo sbd tsananin tsaron dake taredashi na yaransa Wainda Suka sadaukarda rayukansu akan sarkinsu.


Cikin wani tsinannan army three quarter da baqar riga Mara hannu data bayyanarda qwandarsa dake bawa baba tsoro yafito fuskarnan sanyeda baqin goggles yafito inda qofar gidan take cike dam da duk wani 'dan daba dake qarqashin ikonsa agarin kowane da kalar mugun makaminda ke soke ajikinsa atake guri yadau ihu da kirarin sai sarki.....


Wuqarda JJ ke miqo masa ya karba Yana sokewa cikin takalminsa Yana qarasawa jikin motocinda alh dikko ya Basu Dan hidima 

Yana shiga JJ yashiga nan kowa yasamu Suka shiga atake Suka cike golf guda da bus biyu tareda Hilux 'daya Suka wuce cikin wani matsiyacin gudu dayasa mutane kakkaucewa da gudu suna matsarda kayan sana'arsu.


Baba ma Yana tashi yau din yaji qafarsa taqara tsami radadi take masa sosai ya dingisa ya fito tsakar gidan iya talatu dake zaune suna lissafin kudin kunu da Nadiya ta kallesa a dage tana dakatawa daga lissafin tace"


Wannan Kuma wane irin sabon salone kake mana gurgunta?


Qin tankata yayi yakalli Nadiya data sauke Kai Yana hada 'yan biyar biyar guri 'daya yace"


Ke tashi kaimin ruwa bayi nayi wanka inada gurin zuwa.


Tashi tayi ta nufi bokiti 

Iya talatu tasake kallonsa tace"


Magana fa nayi kanaji kayi uwar shegiya Dani.


Tsuke fuska yayi Yana sake dingisawa yace"


Talatu wlh wata Rana Saidai kijiki cikin takaba tsundum matuqar ba rabuwa mukayi da Zaki ba,

Wannan masifa tayi yawa 

Gabaki daya tsufa neman damqata yakeyi sbd masifar gidan nan,

Ga naki gana 'yayanki gana wannan sarkin dababu rawani sai neman gigita rayuwata yakeyi.


Kallonsa talatun tayi tana girgiza Kai tace"


Ai wlh kwadayinkane da zalamarka ta abin duniya takaimu ga haka,

Qiri qiri katura ruqayya aikatau qasar inyamurai gashinan takawo Mana abinda yaci uwar uban kwadayinmu ta mutu ta barmu da jidalin qaqa nikayi

Gashi kaikuma Allah bai samaka danganar tsayawa inda kakeba shiyasa muke azabtuwa muda tattalin arzikinmu konace tattalin arzikina tunda Kai bayan matacciyar tsohuwar rigar ba abinda ka aje.


Sake tsuke fuska yayi yace"


Wannan tattalin arzikin naki na hainci gwara na mutu da tsohuwar rigar tawa danayi irinta.


Yanxu dai naji wannan Ina kake cewa zakaje da gurguwar qafar?


'dan sake fuska yayi Yana cewa"


Yau wani gagarumin taro za'ayi daya hada kaf dukkanin qusoshin qasa dasukaci Suka tada wuya musamman sbd taron na alh dikko Dilla ne

Dan haka dole naje Dan kuwa yau 'yan maula ma kasuwarsuce 

Bazan zauna acinye duniya badaniba koba komai da 'dingisarnan zan qara lankwashewa nafi kowa samu.Baka daddara ba kenan""tafada tana hararar gefensa.


Yana kama hanyar bayi yace"


Daka mutu gwara kazama biri.


Bayin yashege Bata sake kulasaba Suka cigaba da lissafi sbd kullum ita arayuwarta a lissafi ta qare.


Cikin wani yadin 'dan Madina kalar baqi da siminti yafito da babbar rigarsa ta kullum ya sanyo hularsa datai mugun masa yawa wadda itama gurin maular yasamota.


Wani irin zaku'do kafada yakeyi Yana gyara babbar rigarsa da hularsa qafafunsa da fuskarsa kuwa tsaf sukaji Vaseline sai maiqo sukeyi ya kalli Nadiya dake gefen talatu tana gyaran shinkafa yace Ina takalmin Zaki na jiya daya zuciya ya wurgo?


Kallonsa sukayi atare itada iya talatu Saidai Kuma basuyi mamakiba saboda sanin waye baban.


Miqewa tayi ta nufi inda ta ajiyesu kusada dakinsa ta dauko takawowa baban ya karba Yana cewa"


Wannan dinkin dakikayi bai tsukuba Amma hakan zaiyi maleji.


Sakawa yayi batareda yakalli talatu ba ya baza rigarsa ya wuce sbd ganin baqin ciki talatun ke yimasa.

#MAMUH

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee9_*

Bayan sati biyu da magana ranar jumaa da yamma Bello yazo qofar gidan tareda abokinsa nuhu dukkaninsu sunyi adonsu cikin yadin wagambari na leda sai qyalli yakeyi na gugar dayaji,


Dattiya dake tareda idi a bakin masallacin layin suna magana Yana hangosu ya washe baki cikin jin dadi sbd yanzu yagama adduar Allah yakawo masa hanyar samun ko dubu 'dayace.


Atareda mal idin Suka fito sarari dansu hangosu aikuwa suna hangosu gurinsu Suka nufo har qasa Suka durqusa Suka gaidasu 

Dattiya sai saka musu albarka yakeyi Yana washe baki kafin yayi gaba Yana cewa"


Bismillah ku qaraso ciki aikaima Bello yanzu kazama 'dan gida tunda zaka auri NADIYA.


Wasu ruwa da JJ yasaka abaki Suka mugun dawo masa da qarfi sbd jin maganar qarshe da kawun yafada,


Tari yafara mai qarfi sbd sosai ruwan Suka sarqesa,

Kallon qofar dakin sarki yayi sbd yabarsa Yana bacci yakumasan qila yatashi.


Saurin juyawa yayi yashiga dakin yagansa Yana motsin tashi Kuma ya tabbatarda baijiba.


Juyowa yayi yafito zuciyarsa na jujjuya zancen to kodai shine baiji daidai ba Amma Kuma su bellon yanda suke wani sassauke Kai yatabbarda akwai wani abin.


Kasa zama yayi yakoma dakin yaga yatashi Yana zaune bakin katifa Yana waya cikin basarwa yagane da ale dikko ne yake wayar,


Sake juyawa yayi ya fice duk hankalinsa ba'a kwance ba sbd bayason sarkin ya fito.


Bai gama tunaniba yagansa ya fito fresh skin dinsa mai haske Yana zufa alamar zafine yafito dashi koba komai lokacin wankan maraicensa ne.


Bai kalli qofar gidanba idan su JJ da sauran yaransa suke yayi cikin gida Dan yin wanka da threequater dinsa da armless riga dama sai tawul rataye a wuyansa fuskarnan tamke kamar ko yaushe.


Zainab ce tafara hangosa ta miqe tareda daukar wayarta dake gefenta tareda takalmanta data gama wankewa ta nufi dakinsu tana cewa"


To Bello sai anjima nizan shiga na Dan yi waya.


Cikeda jin dadi bellon yace"


Yauwa zainab to nagode.


Cikin 'daga murya iya talatu tace"


Ke Nadiya bazakiyi sauri kifito bane kinbarsu sun gaji da tsugunawar qafafuwansu harsun fara rawa.


Batareda dattiya yasan da zuwansa ba yace"


Shashanci me kika tsayayi haka za'ayi auren kije kina masa sanyin jiki?


Baice musu qala sai ita daya kalla lokacinda tafito sanyeda sabon hijabi zainab ta sanyo mata Hoda harda janbaki maroon dayayi mata kyau sosai kasancewar Bata taba saka janbaki mai kalaba iyakacinta Vaseline abaki.


Wani mugun kallo ya watsa mata atake ta rikice tana neman juyawa cikin muryarsa mai saka shiga taitayinta yace"


Bani ruwan wanka.


Da sauri nuhu abokin Bello ya miqe Yana cewa"


Sarki Bari na debo maka da kaina ma...


Wani kallo sarkin yayi masa dayashi saurin sakin bokitin...


Gyaran murya dattiya yayi tareda hararar gefen zakin yasaki yaqen Dole yace"


Nuhu Aida kabarshi ta Diba tabashi saiku koma daga soron gidan zaima fi muku nutsuwa can din.


Aikuwa kamar jira suke Suka miqe Suka koma soron gidan Dan dama dukkaninsu a tsarge suke da ganin Zaki na gida sun dauka bayanan.


Aikuwa tana Kai masa ruwan tadawo ta nufi soron gidan tanajin ba dadi cikin ranta sbd ganin wani kallo dayayi mata lokacinda ta aje masa ruwan.


Suna ganinta Bello yahau washe baki sai alokacin Suka saki jiki Suka fara gaisawa itadai tana rakube a gefe.


Nuhu ne ya zaqe yanata jawo musu fira sbd yafi bellon rawar Kai da iyayi shikuwa bellon sai kallonta yake Yana murmushi Dan kuwa shi harya farajin sati biyar dinda Suka rage sun masa nisa.


Qamshin sabulun wankansa na imperial L da ita kadai tasani yasata sake rabewa tareda sunkuyar dakanta 


Bello kuwa harda qara Ware idanuwansa da kyau Yana sake mata kallon qurulla 

Ga nuhu sai kawo musu zancen soyayya da yanda Bello kesonta  yakeyi Yana qarawa.


Tsaf fararen idonsa Suka shiga cikin nata atake jikinta yadau rawa taji hawaye na ciko idanuwanta.


Yana shigowa soron JJ yataso daga qofar gida yashigo 

Kallo daya yayiwa Zaki yaga ba fuskar masa magana harya shige dakinsa shikuma yajuyo gurinsu Bello fuska a hade yace"


Kai ku Ware daga nan bamason hayaniya,


Wuqa ya fitar mai shegen kaifi da qyalli ya Dora saitin wandon Bello da jikinsa yafara mazari yace"


Duk Randa nasake ganinka gidan nan saina maka zanen gobirawa anan""yaqarasa fada Yana zungurin wandon da wuqar.


Nuhu tuni yayi muryar sanyi yace"


Zamu kikyaye oga JJ.


Qofa ya nuna musu tuni Suka wuce da sauri wani na tunkudar wani musamman sauran yaran neyon dake cikeda qofar gida duk sun mimmiqe.


Kamar Bello zai fashe da kuka haka ya isa gida ya tube yasaka riga da wandonsa na aiki ya nufi shago Yana fushi Dan kuwa wlh JJ yacucesa daya korosu Dan kuwa so yayi yau ya dasa soyayyarsa a zuciyar nadiyarsa.JJ kuwa bayan fitarsu mayarda wuqarsa yayi ya juyo gurinta fuskarsa a sake sosai Dan dama dashi kadaine take dadewa Yana Mana fira.


Fira yadinga mata wani lokacin har murmushi takeyi tana rufe fuska sbd rabi duk tsokanarta ne yakeyi da maganar soyayya.


Ahaka har kusan magriba kafin yabarta tashiga gida tana murmushi shikuma yayi waje Dan kuwa yasan sarki baison kusancin kowa ayanxu.


Dattiya dake jiran shigowarta ya qurawa hannunta dake cikin hijabi ido 

Cikin sanyi take qarasowa tana murmushinda itama Bata saniba 


Ahasale dattiya yace"


Wai meyene haka kike tafiya kamar Mara ruwan jiki???bazaki cire hannunki daga hijabin bane saikace matar alaramma.


Fitarda hannuwanta tayi yaga Babu komai a hannun ya tsuke fuska yace"


Ruwan alwala kikazo dibar musu???


Girgiza Kai tayi tareda masa alamar sun wuce.


Cikin yayi da qananun idanuwansa tareda miqewa ya dauki buta baisake cewa kowa qala ba yashige bayi tun acan ma yayo alwalarsa Yana fitowa butar kawai ya aje ya fice.


A masallaci ma koda yaje kusada Zaki da JJ yasamu sahu nan yasake tsuke fuska musamman dayaga JJ namasa wani ladabi yasan cutarsa zasuyi Saidai ganin fuskar JJ a tamke tam Babu Wasa yasa yasake tsuke tasa shima Dan ko gaisuwa baiso.


Ana gama sallah yafito JJ yabiyo bayansa suna fitowa yaja ya tsaya yace"


Lafiya zaka bini?


Murmushi JJ yayi Yana Sosa Kai cikin 'dan ladabi zaiyi magana kawun ya katsesa da cewa"


Wannan ladabun mai amsheka ba sam,

Kafitomin a zallar yanda kake kamun magana idan ma itace kakeda ita.


To kawu dama inson Nadiya ne shine nakeson sanarda Kai Kuma Nima aurenta nakeson yi......


Wani kallon takaici kawun yamasa kafin cikin bacin Rai yace"


'yar tawa zanbawa magajin dake jiran gado a dabanci,ta'addanci,da Sara Suka?

Wato gani dattiyan mahaukata tunda kaga Ina sake muku fus....


Ido hudu yayida Zaki dake bayansu saiya qarasa maganarsa da cewa"


Kaga jabiru kabarni da wannan maganar nariga nabawasu Bello saura sati biyar bikin ma.


Juyawa JJ yayi sbd jin yanda kawun yayi magana cikin lalama sabanin farko daya fara masa Rashin arziki

 saiyaga Zaki yasaki murmushi kenan ganinsa yasa kawun sassauta harshensa.Ahankali yaqaraso yau kyawunsa duk yasake bayyana sbd jallabiyace yasako ash data fito da farin fatarsa ta asalin Igbo.


Kallon kawu yayi yace"


Muje gida kawu.


niba gida zani ba inada abinyi.


Juyawa sukayi Suka barsa 

Sanin akwai abinda ke Shirin faruwa yasa yabiyo bayansu Yana zuba masifarsa suna jinsa sukai banxa dashi.


Har tsakar gida Suka shiga Zaki ya kalli kawun yace"


JJ nason auren waccan yarinyar

Meyasa baza'a bashiba?????


Kallon JJ kawu yayi yace'


Sbd Ni ubanta namata miji.


Kallonsa Zaki yayi yace"


Shikenan????


Eh"kawun yada Kai tsaye sbd shima yau Rashin arzikin yakeji.


Juyawa yayi ya wuce JJ yabi bayansa suka fita.

#MAMUH.

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee6_*

Sanin Babu Wanda ke ragarwa mahaifiyarsa a gidan yasa Babu Wanda yake ganin girmansa acikinsu saima dai idan Yana gida Babu mai iya yanka mata Rashin arziki sbd tsoron Rashin mutuncinsa Dan kuwa Duk da yake bamai shekaru sosaiba yanada matuqar kwarjini dakuma farin jini saidaifa baida sauqi ko kadan idan katabasa.


Sosai dahiru yamayarda hankali kan karatu Amma Zaki Sam yaqi mayarda hankali ga manyanci yafara kama umman tasa yanzu Bata iya cewa kullum saitaje makaranta taga idan yaje,


Yau zuwa gobe Rashin zuwa ahaka dai yagama primary yashiga js 1


A wannan lokacin ne dattiya ya auro amaryarsa daga wani qauye dasukaje maula gurin wani mai kudin qauyen,


Amaryar tasa yarinyace 'yar kimanin shekara goma Sha Tara shiyasa abin yafi baqantawa iya talatu yarasa wadda zai aura sai yarinyar daya kusa haihuwa.


Tun zahra'u najin wuyar rayuwar gidan harta Saba da taimakon ruqayya Dan kuwa tun satin farko dattiya ya daina siyo mata abinci yace tashiga Sanaa Dan kuwa gidan kowa sanaa yakeyi yaciyar dakansa dukda idan yayo samu yakan siyo mata tsire da nono sushige dakinta su cinye yace ta goge bakinta.


Ahaka shekaru Suka ja harta samu ciki 

Lokacin ruqayya ke kulada ita sosai sbd cikin yazo mata da matsaloli gashi na farin tuni ta kumbure tako ina 

Sosai ruqayya kejin tausayinta.


Dattiya ma tuni hankalinsa yatashi sbd har cikin ransa yanason zahra'u sbd biyayyarta da yanda ta iya zama acikinsu ta koyi hakuri da duk halayensu.


Zaki madai duk gidan itace abokiyar shirinsa anty zahra'unsa abinda take fada mata ko ummansa baya fada mata sbd karta masa fada ita kuwa anty zahra'u Saidai tayi masa nasiha.


talatu tahaifi mace da sati biyu

Zahra'u ta haihu Saidai tana haihuwa atake Allah yakarbi ranta yabar 'yar jaririyar data Haifa wadda taci suna *_NADIA_* 'yar talatu kuwa aka saka mata suna ZAINAB.


umman Zaki itace taci gaba da rainon Nadiya wadda ta taso cikin maraicin uwa da uba Dan kuwa dattiya tunda zahra'u ta rasu kamar Wanda aka zarewa notin Kai 'daya ya qara zaburewa Sam baya ragawa uban kowa yanzu ga shegen son kudinsa daya qaru

Danma wani lokacin Zaki na shige masa gaba sbd ta'addancin daya fara qarfafa acikinsa.


Nadiya tunda tafara girma umma ruqayya tagano Bata iya magana suka fara yawon asibiti Saidai koyaushe kudine ake tsago musu Wainda Batasan Ina zata samosuba shiyasa suka dangana,Zaki da Nadiya Sam Babu wata jituwa sbd Sam bayason iskanci da raini bare wata banzar shagwaba wadda umman ke shagwabata duk da haka alqawrine ya dauka da yardar Allah shine zai nemowa nadiyar lafiya kowace irin qasace tunda ummansa naso.


Ahankali shekaru suka shude Nadiya nada shekara goma Sha biyu ummansu ta rasu tabarta cikin maraici Dan kuwa tuni rayuwar gidan tafara mata tsanani duk da ba duka ba zagi Saidai fa rayuwar gidan wata juyayyar rayuwace ta kowa da kalar halinsa da dabiarsa,

Makaranta ma tunda tagama js 3 sai karatun ya tsaya kasancewar Bata mgn gashi batada Wanda ke janta a jiki da kulawa bare tasamu qwarin gwiwar yin karatun.


*_SARKI ZAKI NEYO_* yazama riqaqqen sarkin yan daba da Babu kamarsa a yankin Dan kuwa kowa na tsoronsa da shakkarsa,

Babu ubanda yake tsoro sbd girman mulkin dayake bazawa a dabanci gashi manya sun daure masa gindi ko hukuma Bata tabasa,

Daqyar ya hada diploma wadda itama rabi zuwa rabi Rashin zuwa,


Shahararren mai kudi DIKKO DILLA dake zaune a qasar south Africa da matarsa 'daya da 'yayansa biyu mace da namiji, yadawo qasar Nigeria sbd wani boyayyan burinsa dayakeson cikawa akan wasu takardu dayafi shekaru goma Sha takwas Yana so Saidai bazai samesuba Saida jajirtaccen mara tsoro wato Zaki Wanda ya dade Yana bibiyarsa sbd labarinsa da aka kawo masa akan izzarsa da tarin mulkin dayake bazawa a troway yakuma tabbarda shine kadai zai iya samo masasu shiyasa yajaza ajiki tun dawowarsa Nigeria yazamto shine babban yaronsa Wanda duniya ta shaidar Dan kuwa yafi yarda dashi akan 'dansa dayake kusan sa'anni da zakin kokuma ma ya girmi zakin.


Zaki shine yasan dukkanin wani sirri na dikko na dukkanin gurbatacciyar sana'arsa da dukiyarsa,

Duk wani aiki dikko baya shawara da kowa sai amintaccensa Zaki Dan kuwa ba laifi Yana matuqar qaunar Zaki duk da shima wani lokacin Zaki baya ragar masa Kuma shima ba'a taba Wanda yaji Yana shakka da fargababa kamar Zaki Dan kuwa Zaki shine yaronsa Amma shine yake shakkar Zaki ba zakine yake shakkarsaba.


Hakan yasa *_AMAAN DILLA_* da mahaifiyarsa *_MRS DILLA_* tsananin kishi da tsanar zaki wanda sukaci alwashin nakasta rayuwarsa ta yanda har abada za'a manta da sunan zaki atarihi.


Zaki tun bayan rasuwar ummansa Babu Wanda yake qauna samada Nadiya saidai Bata gabansa har mantawa yakeyi da ita musamman dayaga irin rayuwar kadaici da maraicin datakeyi a cikin gidan idan bai dauke idanuwansa akansu ba zai raba dukkanin yan gidan da wasu sassa na jikinsu ne kawai shiyasa ya tattarasu ya watsar,


JABIR shine mutum na biyu da Zaki yake tsananin qauna aryuwarsa sbd tsintosa dayayi adaidai lokacinda dikko Dilla yasa aka kashe masa iyaye shima aka biyosa akashesa shine ya kubutar dashi duk da shima baisan dikkone yasa aka kashe iayayen jabir ba,


Abin yaso taba qwaqwalwar jabir sosai Dan har tabin hankali yayi tsawon lokaci Zaki na kula dashi agidan 

Kosu baba dattiya da iya talatu sunci wuyar ciwonsa sbd yanda yake hauka tuburan 

Haka Zaki yayita wahala dashi harya warke yazama babban yaronsa shima duk da ba wata tazarar shekarune a tsakaninsu ba,


Zakine ya gabatarwada dukkanin yaransa na kusa Dana nesa jabir amatsayin JJ baban yaronsa wato magajinsa.


JJ ayanzu duniya baida kamar Zaki Wanda yakejinsa tamkar jininsa Dan zai iya bada rayuwarsa akan zaki.,


Lurada abinda Zaki yafiso duk duniya yasa baida abin qauna kamar Nadiya,

koyaushe shine mai tattali da bawa Nadiya kulawa duk da Zaki ko ajikinsa Saidai Yana fada masa bayason kowa nashiga shaanin cikin gidan.


Dattiya da talatu kuwa tuni Zaki yazamar musu uban Dole Dan kuwa cin uban kowa yakeyi a gidan shiyasa ba'a masa ganganci,

Shikuwa dattiya Rashin danganarsa kesa Yana shiga huruminsa

Shikuwa yasa adaidata masa shi.


Zainab Sam Bata jin magana akwaita dason rayuwar qyale qyale Wanda yasa kullum take cikin kwashe kwashen qawaye da samari Wanda koda Gigi basa zuwa qofar gidan fira sbd hurumin zakine Saidai su hadu wani wajen,


Zakine kawai ko sunansa taji take shiga taitayinta sbd tsoronsa sanin baya wasa yanzu ne zai sauya mata kamanni hardai idan yaji tanayin Rashin kunya cikin gida.


Dahiru dai malamin makarantar secondary ta kwana ta maza a wata local government shiyasa Sam baya zama acan yake zaune staff quarters.
**********

Babban gurin taron na stadium yacika maqil da manyan qusoshin qasa shiyasa securities sukai yawa agurin ga yan jaridu da masu tv stations sai dauka sukeyi ana cikin haka shugaban taro dikko Dilla ya iso da babban yaronsa Zaki tareda securities nan aka dinga daukarsu hoto harsuka shigo gurin nan aka fara gabatarda taron.


Ana cikin yi Zaki yafito JJ na gefensa tareda wasu daga cikin manyan yaransa wato su nano.


Kallon mabarata da 'yan maula dake jere cikin uwar Rana yayi zai gumi suke hadawa idanuwansa suka sauka kan kawunsa dattiya da mal idi sai gumi sukeyi suna qyallin Vaseline Sam hankalinsu naga qofa suga wani babba yafito sufara shiyasa Basu lura dashiba.


ya daure fuska tareda kallon qafafuwan kawun dake nade kamar gurgu alamar yau qaryar qurgunta zaiyi.


Kallon JJ yayi masa alama da ido man take JJ yasaki murmushi suka koma ciki.

#MAMUH

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee8_*

'Dagata yayi cak tana buge buge yakwantarda ita qasa tareda danneta Yana neman wuyar rigarta inda zai zura hannunsa.,


Sake lalubar kofin silverta tayi hankalinta a matuqar tashe ganin rabata da mutuncinta zaiyi Dan kuwa tuni ya farka rigarta dataqi Bari hannunsa yahau kan qirjinta da kyau.


Wani irin kuka takeyi mai qarfi Saidai ba sauti,


Hannunta ne ya sauka akan kofinta ta wuwuri kofin ta jefa saitin qofa da qarfi gashi qofar itama langa langa ce.


Sautin qarar sai akan kunnen Zaki sbd hakanan yau yakasa bacci Wanda JJ ma ganin hakan yakasa bacci.


Dattiya ma yaji ya miqe yataso da fitilarsa Yana fitowa tsakiyar gidan gabansa yayi mummunan faduwa jin motsi mai qarfi Yana fitowa dakin nadiyar.


Sbd tashin hankali sakin fitilarsa yayi ya banka dakin da qarfi Yana kiran sunanta hankali tashe.


ba zato yaji mugun bugu a bakinsa a gigice ya dago cikin duhun ya riqo hannun Nadiya Yana qoqarin qwaceta ban qaton ya haushi da bugu.


Tun lokacinda kawun yakira sunan Nadia ya rufe idanuwansa ahankali sbd jin jikinsa nafara rawa.


JJ ne yayi saurin miqewa daga kwance yadauki fitila da wata sharbebiyar kakkaifar Adda yafito ya nufi tsakar gidan.


Bayan fitars JJ sake rintse ido yayi wannan karon numfashinsa yaji Yana shaqewa kamar  mai asthma.JJ na isa yaga abinda ke faruwa nadiyarma kamar ta suma ga kawun yariqeta yaqi sakarwa shegen shikuwa dukan hannun kawun yakeyi Yana janta.


Cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki jj yakaiwa kb din wani mugun naushi a fuska Saida yasaki wani razanannen ihun daya tayarda sauran mutanen gidan duk Suka fito.


Sunan Nadia da kawun yasake Kira da qarfi yasa iya talatu kallon kayanta dasuke yage tafara salati tana tsinewa kb.


Shaqosa JJ yayi a fusace ya daga hannu zai Kai masa mugun duka kb din ya daga hannu zai tare sai ganin hannun sukayi a qasa jini na wani irin tsirtawa wani guntun fitsari iya talatu tasaki zainab kuwa gabaki daya tasaki nata fitsarin sbd Basu taba ganin wannan tashin hankalin ba.


Dukkaninsu juyowa sukayi sukaga Zaki riqeda addar da JJ ya ajiye.  


Atake kb yafadi Yana ihu da qarfi sbd ganin hannunsa a qasa ga Zaki ya sare,


JJ ne kawai baiji tsoron ganin jini da abinda Zaki yayiba tunda sun Saba gani aikinsu ne,


Shaqo kb din yayi Zaki ya hanasa tareda jawo kb ko gani bayayi sbd tsananin halinda yake ciki yau idan bai raba kb da duniyaba bayajin abinda yakeji zai fada masa,


Rintse ido yayi ya hangota kwance some jikin kawu kayanta dake babbarke ne suke neman haukata qwaqwalwarsa.


Wata sharbebiyar wuqa ya fizgo a jikin jj ya yaga wandon kb din da ita ya daga da qarfi zai sare masa gabansa JJ dasu nano dasuka firfito daga dakin qofar gidan Suka riqesa suna Allah ya huci zuciyarka sarki Amma karka masa wannan hukuncin,


Cikin hasala jj yace"


Neyo kabarmu dashi,

Yataba hurumin da ba'a tabawa zamuji dashi.


Wurgi yayi da wuqar Yana yamutsa kansa jin yake kamar ya cinnawa kansa wuta sbd zafin da zuciyarsa keyi,

Jiyake abinda ya tokare masa a qirji kamar zai kashesha,

Da qarfi yace"


Ku sauyamin kamanninsa yanda ko uwar data haifesa koya warke bazata ganesa ba,

Ku karya sauran dayan hannunsa daya taba suturar dake jikinta,

Ku karyamin qafafunsa,

Ku kasheminshi,


Ruwa JJ yayi saurin kawo masa yayi wurgi dasu Yana cewa"


Zuciyata zata saukane idan nagansa kwance cikin mummunan yanayi.


Aikuwa wani irin duka su JJ dasu Nanu sukai masa duk da dare ne atake gurin yacika Dole aka Kira police ganin zasu kashesa.


Koda police sukazo kb kawai Suka dauka sukai asibiti dashi tareda gundulen hannunsa a leda.


Cikin gidan kuwa ruwa zainab ta debo qafafunta da hannuwata na rawa taba baban ya kelayawa Nadia


Atake ta farfado a firgice cikin tsananin tsoro jikinta na rawa 

Zainab tayi saurin rungumeta tana hawaye itama sbd kaf dinsu gidan suna tsananin son junansu Saidai halayensu ne kesa ka dauka basason junansu.


Baban kuwa miqewa yayi yace suje dakin zainab su kwanta tare.


A Daren Kam kowa bai koma bacciba musamman Zaki da dattiya daya qara gama yanke shawarar aurar da ita cikin qanqanin lokaci.


Washe gari duk wasu yaran Zaki Saida sukai baqin cikin wannan Rana sbd sarki dai ranar ko qofar gida bai fitoba ataqaice dai Saida ale dikko ya Aiko masa da babban likitansa ya dubasa sbd ko miqewa tsaye daidai ciwon kirji mai qarfi yaqi Bari yayi.


Kb Kuwa ba'a mutuba Amma anci wuya Dan kuwa gabaki daya a kumbure yake ga jini daya zubar sosai sai qara masa akeyi gashidai yanxu baida hannu daya Kuma hukuma nagani tayi biris yanajin sauki aka sallamesa yayi alwashin saiya Rama abinda sarki yayi masa shida yaransa Dan kuwa shima baya tafiya.Bayan kwana biyu duk tasake zama wata iri da ita sbd sanyi data qarayi sosai gabaki daya rayuwarta mutum biyune rayuwarta,BABANTA da YAYA ZAKI tunda abin nan yafaru Zaki ya daukewa 'yan gidan wuta gabaki daya sai shakkarsa taqara shigarsu sai kaffa kaffa sukeyi musamman ma ita.


Baba kuwa tuni yasamu mal zailani da maganar auren da 'dansa bello yace yanaso na Nadia.


Babu wani dogon qunbiya qunbiya Suka gama maganarsu tunda kowa yasan kowa tare sukai samartakarsu.


Bayan mal zailani yayi magana da bello kan maganar shima yace a shirye yake asa Rana kawai.


Har gida mal zailani yasamu dattiya shida wani yayansa da abokinsa

Shima dattiya yakirawo mal idi

 Suka sake magana akai neman aure Suka bada kudin nema dubu goma.


Washe baki dattiya yayi ganin 'yan dubu dubu Yana cewa aransa""Ankwana biyu baa haduba"


Karba sukayi aka yanke ranar aure wata biyu masu zuwa insha Allah.


Suna tafiya dattiya yasake qirga kudin Yana murmushi yaciro dubu biyu ya miqawa mal idi ya zuba saura aljihu Suka fita.


Lokacinda ya sanarda iya talatu maganar kallonsa tayi cikeda haushi tace"


Kai yanxu Dan Allah shine ka karbi kudin gaisuwar zuqeqiyar yarinya kamar Nadia a dubu goma??


Kunna radio dinsa yayi Yana kamo gidan fm yace"


Eh ko dubu biyar ne dai na bayar

Lokacinda wani shegen zai sake shigowa ya asarani kinacan kina baccin wahala ko dubu 'daya bazatayiba.


Tsuke fuska tayi tana hararar qafafunsa dasukai 'yar banzar qura tace"


To nidai karka doramin wainnan qafafun masu dau'da a tabarmar sallah ta tunda Nima koda nahada kudin gumina nasiyeta kanacan kana yawon ta zubar a gari.


A kufule ya kalleta yace"


To ko natashi ma akai gaba daya?

Talatu kin renani waike bakisan darajar miji bane koyaushe bakimin 'daa sai gasa baqaqen maganganu.


Tabe baki tayi tana cigaba da hada garin matarta data gama zubawa 'yar fulawa.


Miqewa yayi Yana masifa ya zari babbar rigarsa ya fice koba komai yau basuje sana'ar ba gwara ko ita yaje yasamo ko dubu biyu ko 'daya yamaga ana taro acan gaba.


Da harara tabi bayansa tana cewa"


Kadaiji dashi

Lokacinda jarababben mai mulkin gidannan zaiji ka karbi kudin gaisuwar nan ai lokacin ne zanbaka tabarmar jinyar kanka.


Zainab dake fitowa cikin daki tasaki dariya sbd tana jinsu sbd itama tasan daga baban har bellon na ruwa tsundum.


NADIA kuwa yitayi kamar batasan abinda ke faruwa tacigaba da sha'ainin rayuwarta.

#MAMUH.

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee7_*

Ana tashi taron nan maroqa Suka hau aikinsu aka dinga musu barin kudi suna godia 

Kawu Dattiya ji yayi yau ranar datafi kowace Rana sa'a ce Dan kuwa tuni kudinsa Suka Kai dubu takwas ya tura aljihun wandonsa tareda qara gyara zama yayi Yana cewa"


To Ashe musakan nan sunfimu samun kudi aikuwa yau Nima cikinku zan lafe tunda qiris yarage tantirin can bai maidani musakinba.


Sake lanqwashe qafa yayi kamar musakin gaske yayi kalar tausayi.


Saida duk baqi Suka watse kafin ale dikko yafito tareda Zaki sake da Amaan 'dansa.


Kallon tarin mabaratan yayi ransa na baci shi arayuwarsa ya tsani mabaratan nan da son banza yayi musu yawa wato su sai mutum ya Nemo zuso karban banxa.


Yanayin yanda ya dauke Kai daga kallonsu yasa ran Zaki ya baci sbd duk lalacewar kawunsa Babu Wanda ya isa ya wulaqanta masashi,

Shi shikadai ne yakeda ikon masa Abu bawai Kuma Dan Baya sonsaba saidan yanasone yaji wuya ya canxa wata sana'ar.


Kallonsu yayi yakalli security yace"


A sallamesu abar musakai su kadai za'ayiwa sadaka.


Idi najin haka yayi saurin nade qafarsa shima Dan kuwa baza'ai babushiba,


Kallon baqin ciki dattiya yayi masa Yana hadiye yawun fargaba sbd yasan Dole akwai balainda yake Shirin qulla musu shine shikuma tsohon banxan nan idi ya nade baisan balain dake cikeda kallondq zaki ke musuba.


Aikuwa duk aka watse aka barsu su tara musakai nan dikko ya kalli Zaki yace"


Lion yaya hakane?


Batareda yakalli dikkon ba yace"


Ale sadaka zakayi musu ta musamman sbd banaso su manta wannan ranar.


Ba musu ale dikko yafito da maqudan kudi bunch guda na dubu 'daya 'daya 

Atake Suka hau zare idanuwa kamar sunga aljanna idi har wani qaiqayi hannuwansa ke masa.


Kallon JJ Zaki yayi atake ya dauko wani buhu Dan qarami yafara walwalewa.


Zaki na kallonsu ya karbi rafar kudin ya miqawa nano yace"


Ka Raba musu ita Amma bayan munga waye musakin gaske.


JJ kuwa Yana gama warware buhun ya cillo musu abunda ke ciki.,


Wani sharbeben baqin dogon maciji ne aciki yafado tsakiyarsu..,


Wani irin juyin waina dattiya yayi tareda miqewa yayi gabas aguje rigarsa na cika da isa yana dingisa qafarsa datai tsami sbd lanqwasawa,


Idi kuwa duk abinda yasamu yayi watsi dashi yanka a guje hularsa datai masa yawa tana faduwa,


Sauranma atake Suka kwasa aguje suna tsinewa Zaki.


Mutum biyune musakan gaske Wainda aka Bari Basu iya gudu su dinma qoqarin guduwar sukeyi da Jan gindi.


Kallonsu Zaki yayi ya girgiza Kai kafin ya kalli Nanu dake dariya yace raba musu rabonsu ne sukadai.


JJ kuwa mataccen macijin ya dauka Wanda bamai cewa matacce ne sbd bada jimawaba yaransa Suka kashesa agurin taron.


Mota Suka nufa dikko na 'yar dariyar jin dadin abinda Zaki yayi musu.


Bude masa mota drivern sa yayi yashiga Suka wuce Yana jaddadawa Zaki gobe qarfe goma na safe zasuje wani guri.


Bayan tafiyarsa shima shida yaransa Suka shiga motocinsu Suka bar gurin.Dattiya yariga idi isowa gida duk da qafarsa tuni tadau wani irin zogi musamman yanda ta kumbura tu da yashigo gida ya zauna qofar dakinsa kan shimfidar tabarma yakalli talatu dataqi tambayarsa ya akayi yadawo yau ko sauran takalmin Babu a qafarsa.


Numfashin 6acin Rai yasauke cikeda baqin ciki yace"


Wlh yau nayi baqin ciki da Dana sanin Rashin tambayar ruqayya waye uban wannan nan yaron harta rasu tabarmin ajalina.,


Sai alokacin talatu takallesa tana zubawa tsiminta ruwan magananin 'dan kanoma sbd yayi Dan bauri anfi cewa yaji magani tace"


Idan dai qashi nada tauri to kare baida aikin komai,

Bazaka kama kankaba Zaki bazai daina wahalarda rayuwarkaba.


Qwafa yayi yace"


Kinkuwa San yau Wai Ni Zaki zai jefowa baqin kumurcin maciji dabanda qafafu yau dakin shiga taqaba.,

Wlh cikin tsananin rashin Imani yasa JJ ya jefo manashi 

Ni yanxuma idi nakeji idan ba akansa iftila'in yafada ba.


Sallamar idi ce ta katsesa fuskarnan murtuk Babu alamar rahama sbd shi komaima nasa ya zubar acan har 'yan dubunsa bakwai da 'dari hudu duk ya watsar wannan wace irin masifa ce,


Cikin tsananin zafin Rai da baqin ciki yace"


Allah ya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin balai.


Amin dattiya da iya talatu Suka fada atare sbd tsananin matsen dasuke da zakin.


Dattiya dake jin tsananin zugin qafarsa data fara kumburi yace"


Allah yaji qanki ruqayya ya saka Miki da duk Wanda yayi Miki wannan ta'asar Dan kuwa yaci amanar marainiya baiwar Allah ta tafi ta huta da ganin wannan balai.......


Shigowar JJ ce tasa dukkaninsu yin tsit suna matse fuska da bacin rai sbd sunsan Zaki na kusa tunda sukaga JJ.


Nadiya dake zaune gefen talatu tana mata aiki tana dago Kai Yana shigowa 

Kyakkyawar fuskarnan tasa a tamke Saidai wani sirrin kwarjininsa dake Hana ayi masa kallon qwaf yasa tayi qasa da kanta kafin yaqarasa sauke takaicinsu baba akanta.


Dakinsa yashiga daidai shigowar zainab da hijabin data aro gurin anty samira amaryar baba idi sbd sanin Yaya Zaki nanan tunda taga bataliyarsa a qofar gidan.


Tashi baba idin yayi Yana sake daure fuska Yana Harare Harare ya fice Yana cewa"


Allah dai baya bacci tunda gumi akace dai mutum ya hada gurin neman halas Kuma mun hada Amma gashinan.


Kawu Dattiya najinsa yaqiyin magana sbd kar ajisu Dan shidai yagaji da wannan masifar daga yanxu zai ringa iya yinsa gurin raba hanyarsa da Zaki Dan yagama sani yanxu Kam tsaf Zaki zai iya ganin bayansa,

Shi wlh dama yasani yabari neyo ya auri ruqayya dabataje ta samo musu wannan iftila'in ba Dan kuwa gwara ta'addancin neyo so ba adadi akan na Zaki tunda gashinan sbd harta haihu ta rasu Bata daina qaunar neyoba tunda Zaki ma aliyu haidar neyo tasaka masa gashinan sunan neyon yabisa.


Tashi Nadiya tayi sum sum ta dauki bokiti ta Debi ruwa da tsintsiya ta nufi bayi tafara wankewa sanin duk yafita yashawo Rana idan yadawo Yana wanka.


Tana gama wankewa tafito kenan shikuma zai shiga baisan da itaba 

Itama batasan dashiba sukai karo tayi saurin yin baya zata fadi

Da hanu daya yariqo hannunta a tsorace ta dago Saidai takasa kallon fuskarsa kafin tasake dagowa ya jehota waje tareda rufo bayin.


Dattiya da tun dazu ya miqe zuciyarsa na tsalle ganin Zaki zai shiga bayi 'yarsa na ciki Yana ganin anjehota waje yasake ajiyar zuciya sbd Rashin madafa sai kawai yahau Nadia da fadan Rashin dalili,


A zuciyarsa kuwa sauqi yakeji da duk iskancin Zaki baya ko kallon mata bare nemansu da lalata sbd 'yar Nadiarsa yake gudun a lalata tunda ita zainab uwarta ta daure mata gindi tana yawonta bai saniba ko tagama lalacewar,


Ita kuwa Nadia ko maqure masa ita akayi za'ayi lalata da ita batada muryar idon neman ceto,


Kai shidaima gwara yayi mata aure ya huta ta huta itama Dan haka zai bama 'dan gidan mal zailani dayake sana'ar gyaran su fanka dama tunda yace Yana sonta.


NADIA kyakkyawar black beauty ce Saidai ba baqa bace sosai Sam batada wani jiki sosai hakama tsawonta daidai misali Saidai kusan dukkaninta daka ganta kasan mahaifiyarta ta 'dauko Saidai 'dan duhun fatar na mahaifintane ta dauko.


Sanyin haline da ita shiyasa ayukanta Suka zama suma a sanyaye takeyinsu.


Juyi tayi kan shimfidarta tareda bude ido ahankali sbd kamar jin alamar wani acikin dakin....


Faduwa gabanta yayi da qarfi sbd tunanin hakan datayi gashi tsakiyar dare ne komai Bata gani sbd duhu gashi ita ko fitila batada.


Miqewa tayi zaune tafara laleben kofin silver datake kwana dashi kullum sbd amfani dashi dan irin haka.


Tana cikin lalaben taji ta lalabo qafar mutum wata muguwar zabura tayi jikinta na tsananin rawa tayi bayi tanason ihu takasa sai hawaye tafara qoqarin tashi zata gudu taji kowanene ya damqota tareda matseta a bango Yana dariya qasa qasa.


Rawa jikinta keyi sosai tana qoqarin kwace kanta hawaye tuni Suka fara jiqa rigarta musamman ma wani irin tsamin giya dake tashi ajikinsa.

#MAMUH.

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee5_*

Cikinta na wata bakwai Abu yayi tsanani Dan kuwa kumburi ne tayi tako Ina Wanda ya sauya kamanninta tsaf Dan kuwa ko qafafuwanta daqyar take dagawa.


Lokacinda abin yayi tsamari yahada kudi daqyar yakaita asibitin kudi atake Suka Bata gado sbd ganin mummunan halinda take ciki Suka tabbatar masa lallai dole za'ayi mata aiki acire abinda ke cikinta Dan kuwa za'a iya rasasu su biyun sbd sanyi yakama qashi da bargon jikinta sosai ta yanda yazamo ha'dari ga rayuwarta data abindake cikin,


Kudi naira dubu saba'in Suka masa total tareda basa telar biyan kudin.


Kallon telar yasakeyi tareda rintse idanuwansa dasukai mugun jajir suna neman zubo ruwan tausayin ruqayyarsa.


Fitowa yayi asibitin Yana tafiya da qafa kan hanya Yana tunanin shida ko dubu 'daya baida ina zai samo dubu saba'in?.


Zama yayi bakin wani babban shagon siyarda kayan masarufi ya rafka tagumi baiko damu da ranar dake dukansaba.


Yafi awa biyu zaune agurin har wasu na basa sadaka idan sun fito atunaninsu bara yakeyi.


NEYO"""yaji ankira sunansa ya dago ahankali cikeda sanyin jiki.


Yayi saurin miqewa Yana qoqarin tattaro kuzari yake kallon Wanda yakira sunansa Yana cewa"


Dikko Kaine nake gani haka????


Rungume juna sukayi dikko na sakin wata dariyar jin dadi ya janye Yana kallon neyo daga qasa zuwa sama yadan yamutsa fuska Yana cewa"


Neey what's happening?

You look terrible??


Numfashi neyo yasaki tareda gyara zaman rigarsa data gama yimasa yawa yace"


Dikko matata na asibiti aiki za'ayi mata sbd ceto ranta da abinda ke cikinta Kuma ana neman kudi nera dubu saba'in Wanda wlh banidasu banida inda zan samesu.


Jansa dikko yayi sukaje mota yashiga tareda bude masa shima yashigo ya tayarda motar Suka fara tafiya 

Batareda ya juyo daga kallon hanyaba yace"


Neyo kasan ni,

Kasan yanda nake Kuma bazan taba canxawaba,

Bana aikinda nasan banada riba Dan haka bazan iya baka dubu saba'in ba kyauta Saidai zanbaka wani aiki dazakai kasamu dubu 'dari biyar Wanda zaka biya kudin aikin matarka harma kayi lalurar komai na bayan haihuwar.


Kallonsa NEYO yayi batareda mamakiba sbd yasan waye dikko

Yasan akan kudi baida yarda ko ragi ko akan waye,

Duk aikinda zaiwa dikko yabashi dubu dari biyar yasan ba qananan maqudan kudi shi dikkon zaisamuba Saidai yasan aikin dikko Babu Wanda ba gur6atacce neba

Dole wani mugun abun ne zai masa.


Sauke numfashi yayi yakallesa yace"


Wani irin aikine??


Wani sample na maganin chloeziadenes zaka samomin a matatar magunan qasa dake cikin Lagos 

Na dauko 6oyayyun ma'aikatan daga qasar China zasumin irinsa a sirrintaccen kamfanin buga maganin bugina zamu sakarwa mutaneshi duk da Sha kawai zasu riqayi basusan bugineba Babu maganin cutar dazai ringa musu.


Kallonsa NEYO yayi tsawon mintuna hudu Yana jinjina Rashin Imani da mugun son abin duniya na dikko sbd kowace gurbatacciyar sana'a ya iya bayako jin shakku da fargabar yanda mutane ke rasa rayukansu akan abubuwan dayakeyi.


Girgiza Kai yayi kawai sbd shi yanxu bayako sha'awar rayuwa da dikkon,


Kai tsaye yace"


Fadamin inda zanje nakaima idan nasamo,

Kuma ka tabbatarda kudina nanan ajiye hannunka ayau zan kawo maka sample din da yardar Allah.


Dariyar jin dadi dikko yayi sbd shiyasa yake mutuwar son mu'amala da neyo ya iya aiki ba tsoro ba shakka ga sa'a dayakeda ita.


Bakin wani qaton factory dikko ya tsaya da motarsa yacewa neyo"


Idan kadauko kasameni bayan gari gidan mai mai suna Dilla filling station,

Best of luck.


Maimakon yaga neyo ya fita saiyaga ya fada wajen motar Yana mulmulawa kamar baida Rai take kansa dake bubbuguwa da dutse yafara fashewa bai damuba sbd ganin masu tsaron gurin suntaso suna qoqarin taimakosa sbd sunga lokacin aka jefosa daga cikin motar data gudu.


Dikko bai tsaya komaiba ya fige motarsa da mugun speed Yana wani shuumin murmushi sbd yasan aikine neyo yafara.Daqyar Suka taresa suna qoqarin dagosa sbd tuni fuskarsa ta baci da jini kamar Wanda aka Dade ana ganawa azaba,


Sam basuga numfashi atareda shiba nan Suka daukosa sukayo ciki dashi sbd basuda fargaba ko tunanin komai akan factory dinsu tunda sumsan tsaftataccen aiki sukeyi ba gurbatacceba bare suji shakkar shigoda wani.


'yan lokitocin dake cikin factory din Suka dubasa sukai masa dressing shidai yanajinsu yaqi motsawa Saidai numfashinsa dake fita ahankali alamar dawowar numfashin.


Bayan futar dukkaninsu daga 'dan dakinda Suka taimaka masa ya miqe da sauri tareda fara bincike cikin dakin cikin sa'a yasamu uniform din ma'aikatan gurin yadauki daya yasa da sauri tareda Jan hular uniform din yarufe fuskarsa yafito Yana sunkuyar dakai sbd kar aganesa atake ya saje da 'dinbin ma'aikatan dake gurin.


Kai tsaye computer room dinsu ya nema ya sidada yabude qofa ya leqa yaga numbern room dinda samples suke yafito ta nufi room 17 inda yaci babbar sa'ar security din qofar abude yake wani doctor Yana ciki da sauri yafada dakin 

Doctorn na juyowa yakai masa wani mugun duka a hanci atake likitan ya yanke jiki ya some 


Nan yafara dudduba sample dinda dikko yace

Yanayi Yana kallon qofa.


Takun tahowa yaji daidai lokacinda yagansa yayi saurin dauka daga cikin wani box mai kamar fridge yasaka cikin wandonsa yayi saurin ficewa.


Daqyar ya mayarda kansa dakinda aka barsa yayi saurin cire uniform din ya mayarda kayansa yakoma Yana kwantawa aka bude qofar.


Yanaji an buga alarm na danger ya miqe ya fito da satar jiki ya iso gate sukuwa security Suka bude masa ya fice.Gudu yakeyi sosai sbd wajen garine sosai

Kusan kilometers tara ne tsakaninsu da cikin gari.


Daqyar ya kawo titi Yana hango mota tafe yayi sauri daga hannu Saidai bai gama aje hannunba motar tayi sama dashi yafado gefen titi jini na fita jikinsa sosai.


Atake mai motar ya gudu yabarsa nan

Rai hannun Allah.


Jini yake fitarwa sosai gashi ko motsi baya iyayi atake yasan mutuwa zaiyi Saidai yayi baqin cikin mutuwa cikin wannan yanayin gashi ruqayya da cikinta baisan wane hali zasu shigaba..


Dishi dishi yake gani idanuwansa na neman rufewa yaga dikko yazo kansa ya tsaya tareda wasu yaransu biyu.


Cikin Rashin tausayi dikko ya girgiza Kai yace"


I'm really sorry best friend Amma Kona daukeka yanxu lalura zaka zamarmin gskia sbd dai mutuwa zakayi Dan haka bazanyi hasarar kudina gurin kaika asibiti muyita wahalar banxaba koba komai kaga Allah nasona da yawa shiyasa hakan tafara sbd kar kudina dazan baka suzama west...


Kai ku cajesa kuciromin sample Dina.


Yanaji Yana gani Suka ciro sample din daga jikinsa Suka wuce Suka barsa hawaye na gangarowa daga idanuwansa harsuka rufe.
Asibiti sunyi jiran dawowarsa har kwana biyu ba labarinsa tuni Suka sallameta nan hankalinta yayi mummunan tashi tafara nemansa lungu da saqo cikin abeokuta

Ga ciwo ga nauyin ciki Amma haka take yawon nemansa Takoma kamar mahaukaciya tun ana Bata sadaka tana qin karba harta fara karba.


Bayan wata daya wani abokin aikinsa daya gaji da zaryar datakeyi gashi yace Takoma gida taqi ita saitaga neyo

Kawai sai yazo yasanar mata anga gawarsa hanyan Lagos sunje sunmasa sallah sun rufesa

Ban yabata kudin mota yace Takoma gida arewa.


Tanajin haka tayi tawakkali Bata tsaya Bata lokaciba bayan kwana biyar tadawo arewa.


Ranar data isa agalabaice ta isa sbd kwana biyu ahanya suna tafiya kodata iso tafara ficewa hayyacinta.


Talatu na zaune tsakiyar gida da tsohon cikinta tana Shan radio taganta tashigo tana daddafa bango.


Gyara zama tayi tareda kallonta dakyau ta tabbatarda ita dince ruqayya.


Batayi mamakiba ta kalli qofar dakinta tace"


Dattiya saika fito kaga baqin magribar dasuka sauka 

Dama nafada komai Daren dadewa saita dawo 

Gashinan harda 'dan kawu aka samo maka.Fitowa yayi Yana saka hula akai Yana ganin ruqayya ya zaro qananun idanuwansa akan cikinta hankali tashe yace"


Ruqayya mezan gani ajikinki?

Nida nasaki jiki duk Randa Zaki dawo da 'dibbin dukiya Zaki dawomin shine kika kwaso min wannan iskancin Lagos 'din???to wlh ko zama bazakiyiba dashi acikin gidannan maza wuce tun kafin nayiwa shegen jikinki duka...


Wato tunda na hanaki auren tubabbe shine kika 'daukomin abinda yafi auren tubabben kunya da takaici.Wata dariya talatu tasaki tana cewa"


Dan Allah da gaske dattiya kasan kunya dahar kake gudun abin kunya?


Rufe ido yayi yafara zazzaga mata Rashin mutunci sbd shi cikin bai wani damesaba kamar yanda tadawo hannu rabbana kamarma wata mabaraciya...


Cikin tsananin azaba ta durkushe gurin sbd naqudar data dirar mata lokaci 'daya.


Beda yanda zaiyi Dole yaje yakirawo shafa'atu matar idi da innaje sukazo dole akai cikin dakinta tun na budurcinta Suka fara qoqarin karbar haihuwarta.


Cikin ikon Allah ana Kiran magriba ta haifi yaronta Wanda yake fari tas jinin Igbo tamkar mahaifinsa.


Cikin qanqanin lokaci aka shiryata 

Dattiya da fada dakomai yasiyo kala biyu da sabulun jarirai guda daya da man jarirai yakawo aka sawa yaron.


Dattiya kuwa Duk yanda yake fada da kukan baida dole yake yimata wasu abubuwan itada jaririnda da kanta tayiwa yaronta huduba da sunan mahaifinsa wato *_ALEEYU HAYDAR NEYO_*.


Yanaji yana gani ya yanka mata 'dan ragonsa Yana sake jaddada mata aro yabata zata biyasa kudinsa tace taji idan ta warke zata biyasa.Ahaka suka fara Gina wata sabuwar rayuwar mai cikeda qalubale gashi bayan haihuwarta da wata biyu talatu ta haifi namiji itama aka saka masa suna dahiru.


Dole ta mayarda hankali tafara sana'a sbd lalurarta data Zaki Dan kuwa tun Yana yaro take kiransa Zaki tunda sunan babansa yaci,


Babu Wanda yataba tambayarta ya akayi tasamu cikin Zaki sai itama Bata bi takan zancenba tafara sanointa Dan tallafawa rayuwar 'danta daya girma harta sakashi makarantar primary.


Zaki ya taso a cikakken marajin yaro sbd ganin irin rayuwarda akeyi acikin  gidansu ta Rashin taimako da tausayi kowa tasa ta fishesa akeyi a gidan,


Idan kanada kaci idan bakada ka kwana da yunwa,

Ga shegen son kudi da abun duniya tsakanin talatu da dattiya baasan Wanda yafi waniba.

#MAMUH

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee4_*

Yana fita qofar gida yaci karo da mal idi zai kwado sallama shima a shirye cikin tasa babbar rigar shadda kalar blue data wanke takoma kamar sky-blue,


Cikin washe baki yace"


Yawwa mal datti muje Dan Allah Dan nasan yanxu Kam anyi nisa da fara taron.


Cikin 'dingisa Suka kama hanya rigunansu na cika da iska suna qarawa.


Dama ahaka tasu rayuwar take,

Aminaine tun yaranta,

Tare Suka taso,

Kusan atare sukai aure,

Duk wata kalar sana'a tare sukayita har qarshe Suka qare a maula sbd cikinsu baasan wayafi wani son banza da kwadayiba dagasu har matan nasu.Dattiya da ruqayya marayune dasuke uwa daya uba daya suka taso Babu uwa Babu uba sakamakon gudun hijira dasukayo daga wani yankin Cameroon,

Tare Suka kubuto da idi da qaninsa shima Wanda yake kusan tsara da ruqayya,


Alokacin dattiya nada shekara ashirinda uku ruqayya nada shekara goma Sha hudu,

Bayan dogon gararin rayuwa dasuka shiga qarshe Suka miqa ruqayya aikatau gidan wata mai abinci dake kusada Tasha inda sukuma Suka famjama nema,


Da sana'ar Saida rake Suka fara Saidai kullum sune suke shanye fiyeda rabi ahakadai harsuka saketa Suka kama ta shoe shiner itama Babu wani abin garawa daga Suka koma Saida kifi shima dai sune suke karyawa kansu jari

Ahaka Saida sukayi sana'a tafi kala ashirin kafin Suka fara gwada maula aikuwa saigashi sunga harka tafara budewa nan Suka maida himma Dan kuwa maula har wani gari zuwa sukeyi,


Alokacinda Sukai shekaru biyu suka Tara kudin maularsu Suka hada da kudin albashin ruqayya data rigada tazama 'yan mata sbd shekaru zunja yanxu tanada shekaru goma Sha Tara Kuma ba laifi tanajin dadin rayuwarta agidan ladee mai abinci,


Fili Suka siya na dubu dari biyu harda hamsin acikin wata yamutsatiyar anguwa

Ban sabuwar maula ta tashi sbd anfara gini duk da ginin irin nasune na masu qaramin qarfi.


Biyu aka raba filin kowa aka Gina masa gidansa mai tsakar gidan da Babu siminti sai dakuna uku uku da bayi sai daki 'daya a soro.


Dama sunada 'yan matansu atake Suka fara Shirin aure 

Dattiya ya auri talatu 'yar ladee mai abinci wadda ta girmi ruqayya sosai.


Idi ma qawar talatun ya aura shafa'atu.


Bayan aurensu da wata daya ruqayya tadawo gidan Wanda yakasance itama tanada gado dashi tunda da kudin aikinta na shekaru Suka hada akayi aikin gidan shiyasa gidan dattiya yafi na idi dakuna da fadi.


Dawowarta gidan bai hanata cigaba da zuwa aiki gurin gwaggo ladee ba sbd rayuwar gidan kowa tasa ta fishesa ce,


Shidai dattiya tunda aka gama amarci ya daina kawo kayan abinci sai Randa yasamo

Ita talatu dama tasan wa ta aura tahau sana'arta ta Saida mayuka da Hoda da jambakin 24hrs da Rani dasu 'yan kunne.


Itama ruqayya yanxu albashinta a hannunta yake zuwa dashi take ciyarda kanta harda gidanba wani lokaci.Yau kusan sati biyu kenan da zuwan wani inyamurin baqo gurin baban Solomon mai shagon Saida qafaruna dake gefen gidan abincinsu.,


NOAH Wanda ake kirasa NEYO farin inyamurin jahar anambra Wanda yake amatsayin qanin baban Solomon uwa daya uba 'daya,


Farine sosai da Kuma qaqqarfan jikinsa dake nuna Yana motsa jikinsa sosai.,


Kallo daya zakayi masa kasan ko acan garin nasu shi Yana cikin marasa ji sbd dukkanin alamun troway ya bayyana a taredashi,


Tunda yazo yayi aboki 'dan troway irinsa mai suna DIKKO shima asalinsa 'dan haure ne daga qasar Ethiopia acikin jahar Dilla.


Dikko yabaro qasarsane sakamakon kawunsa daya kashe tareda matarsa da 'yayansa ya sato dukiyarsu yayo nesa da qasar shida matarsa dasuka aikata aikin atare.


Tunda yadiro Nigeria yafara sana'ar baqin mai da miyagun qwayoyi tareda safarar gurbataccen magani.


Abota sukeyi sosai da neyo inda Suka hada hannu gadan gadan ga sana'ar Wanda take kawo musu samu sosai,


Banbanci tsakanin neyo da dikko shine,

Neyo baya kashewa Saidai duk inda tantiri yakai yakai harya wuce.,


Dikko kuwa kisa agurinsa ba komai bace matuqar zakai masa shamaki da abinda yakeso to tabbas zai kawardakai Babu gargada,


Dukkaninsu basa shaye shaye basa neman mata sbd tsabar qwarewa da sanin Rashin Imani yasa Sam dikko ko shaawar giya da neman mata bayayi sbd dasune za'a iya Kai mutum qasa.


A boye suke mu'amalarsu Sam Basu so ma asan Wai sunsan juna sbd ha'darin sana'ar tasu shiyasa basa haduwa sai dare.Tunda neyo yaga ruqayya yaji Babu macen dayakeso idan ba itaba,


Yayi bibiyar harya gaji Sam Bata kulasa sbd tsananin kamun kanta da kama mituncinta.


Nacinsa da yanda yafara zama wani Wawa akanta yasa tafara kulasa duk da tasan alaqar bamai dorewa bace tunda addininsu ba 'dayaba.


Ahankali qaunarsa tafara shigarta 

Shikuwa tuni yafadawa bban solo musulunta zaiyi ya auri ruqayya Babu musu bbn Solomon ya amince sbd shima ya matarsa musulmace wanda dama sanadin auren yabaro gida yadawo nan arewa.


Bayan musuluntarsa shida bbn Solomon Suka samu dattiya da maganar ba kunya ya rufe ido yace bazai Bari ruqayya ta auri tubabbe kuma 'dan daba ba.


Da farko kamar wasa saikuwa sukaga da gaske yakeyi Dan tuni ya Hana ruqayyar ko fita.


Daga ruqayya har neyo dayaci sunan aliyu hankalinsu yatashi 


Kullum Yana qofar gidan gurin dattiya Amma kullum da sabon Rashin arzikinda dattiya ke musu.


Ahaka dai Abu yayi tsanani sbd kusan so biyu shedan nasasu kusan aikata 6anna ganin haka yasa neyo yanke shawarar tafiya ya nemi sana'ar halal mai kyau ko dattiya zai canxa yabasa aurenta.


Bayan tafiyarsa ruqayya tashiga mummunan hali na rashinsa gashi ko aikin ta daina zuwa take talauci ya rufto musu abubuwa sukai tsanani ita kanta talatu yanzu sana'ar sai ahankali.


Ana cikin haka mamar shafa'atu matar idi tadawo daga Lagos su dattiya dasukaga irin tarin arzikin data samo nan take dattiya ya yanke shawarar bada ruqayya aje da ita itama tayi aikata tasamo musu abun duniya.


Ruqayya naji tana gani aka tafi da ita Lagos inda ta tararda wani babin rayuwar daya firgitata.


Gidane acike taf da 'yan haya dakuna sunfi guda ashirin kowanne da kalar mutanen dake cikinsa.


Azumi mamar shafa'atu itama daki gudane da ita sai 'yan matanda ake kawo mata Wainda take rarrabawa aikatau gidajen manya.


Kwanansu biyu dazuwa ta miqata wani babban gidan abinci aiki.


Ahankali tafara sabawa da rayuwarsu  tafara 'dan koyon pidgin sbd saidashi kusan kowa ke mgn a garin.


Ranarda tacika wata hudu da zuwa garin ta taso aiki da daddare tana hanyar zuwa gida wasu matsaya Suka biyota 

Tun tana tafiya harta fara sauri daganan Kuma sai gudu sbd kusan su biyar ne.


Gudun fanfalaqi takeyi suna binta gashi anguwar Babu mutane sosai gashi dare yayi.


Tana Shan wata kwana taji an fizgota sun fada wani gida

Arikice ta bude baki zatai ihu ya toshe mata baki ahankali ya furta sunanta Yana cewa"


Keep quiet.


Kallonsa tayi da sauri jin muryarsa tana ganin shi din ne batasan sanda ta rungumesaba tareda sakin kuka sbd harokacin a tsorace take gakuma mamakin ganinsa.


Saida mutanen dasuka biyota Suka wuce kafin ya saketa ya jata zuwa 'dakinsa na mai gadi dake cikin babban gidan daya jawota.


Kallonsa tayi tana cigaba da kuka shima ita yake kallo zuciyarsa na tsananin jin zafi da qunar ganinta amatsayin mai aiki tundaga arewa harnan Lagos inda ya tabbatarda kowane lokaci zata iya lalacewa.


Cikeda damuwa yace"


Ruqayya Dan Allah ki aureni muyi rayuwa cikin amincin Allah kibar maganar dattiya wlh Kai rayuwarki zaiyi yabaro

Yanxu me kike tunani waincan mutanen zasuyi miki dasun kamaki????


Share hawayenta tayi sbd tasan tabbas rayuwar Lagos dinnan idan har bakada mai kulawa dakai to sunan rayuwarka lalatacciya,


Tabbas zata amincewa neyo suyi aure dataje tafada halaka.


Bayan sungama yanke shawara acikin Daren yakaita har qofar gida tashiga kafin yadawo da niyar gobe zasuje adaura musu aure.Haka kuwa akayi washe gari sukaje wani masallacin yorbawa aka daura musu aure bada sanin azumi ba dagacan suka tattara Suka bar Lagos sukai abekuta.


A abekuta yayi amfani da kudinsa Suka kama hayar daki daya da toilet inda yasiyo musu komai na amfani da daidan gwargwadon abinda suke buqata Suka fara shimfida rayuwarsu inda yasamu aiki awani garage dake kusa.


Bayan aurensu da wata biyar ciki da cutar sanyi ta bayyana ajikin ruqayya nan hankalin neyo yatashi gashi yanxu abincima gagararsu yakeyi saiyayi daqyar yake samowa.

#MAMUH

[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee10_*

Tundaga lokacin ba'a sake tayarda maganar ba sai shirin biki sukeyi abinsu musamman iya talatu data fara hidimar bikin gashi dangin mahaifiyarta daga qauyensu sun Aiko kudin nasu gudunmawar har naira dubu arbain da buhun gero da masarasa da dawa kowanne buhu biyu,

Murna gurin dattiya ba'a magana ganin buhuhuwan hatsi jingine yau agidansa abinda bai taba yiba kullum yafison awo idan za'ayi abinci agidansa.


Nadiya kuwa yanxu tasake sakewa da JJ Babu sbd kullum saiya kirata sunyi fira

Tuni taji ita shitake so akan bellon da har yanxu bai sake zuwaba,


Zainab kuwa kullum ita ke sanmata kayanta na kwalliya ta shafa mata.


Tsumi da kayan mata kuwa iya talatu tabatasu marasa sirki Saidai ita kunyar Sha takeyi saida dattiya yajisu ba kunya ya rufe ido yayi mata kaca kaca yace wlh kullum aka Bata taqisha saiya Mata shegen duka.


Sarki gabaki daya ya daukewa duk abinda sukeyi na hidmar biki cikin gidan Kai Sam kota kansu bayabi,


Duk lokacinda tagansa saitaji jikinta yayi sanyi da damuwa sbd jitake idan tayi auren nan sun rabu kenan,


Shine 'dan uwa mafi kusa da rayuwarta da zuciyarta da bazata iyayin nesa dashi ba.


A bangarensu JJ kuwa tuni Suka rarraba manyan katin gayyatar daurin aure daga sarki Zaki NEYO na magajinsa daza'ayi Wanda tuni gari ya dauka wasu suce Zaki wasu suce JJ magajinsa sbd Babu sunan ango ajiki Saidai guri dakuma lokaci.


Ale dikko ma ya gayyaci mutanensa musamman sbd hidimar Lion dinsa ne.


Ansaka Nadiya lalle tuni gida ya cike da mutane dangin mahaifiyarta ma sunxo akori kura guda aka cika gida ga dangin iya talatu nan aka hau hidima sosai dattiya bakin nan har kunne.


Akwati guda cikeda Kaya masu kyau da mutunci JJ yakawowa Nadiya yace tayi hidimar biki.


Sanyi jikinta yayi sai kawai ta fashe masa da kuka mai tsananin tausayi tana kallon qofar dakin Zaki.


Kallon dakin yayi shima saiyaji jikinsa yayi sanyi duk da sunsan sun wargaza aurenta da Bello Amma Babu Wanda yasani Saidai Kuma yasan tana tsananin buqatar Zaki adaidai yanxu tunda shine takewa kallon dakinsu daya tunda ummansu 'daya sbd batasan dadi da soyayyar tata uwarba ummansa ce ta Bata wannan qaunar harta rasu tabarsu.


Jiki sanyaye ya rarrasheta cikin tsananin qaunarta yace"


NADIA ayau zan sanardake sirrin Zaki da koshi kansa baisaniba,


Babu wani Abu ko wata halitta yanxudai a doron qasa da Zaki ke tsananin qauna kamar ke Nadiya...


Kallonsa tayi hawayen cikin idonta na tsananta gudu.


Nadiya kece abinda Zaki yafi qauna fiyeda rayuwarsa sbd akanki Zaki yasoyin kisa abinda yafi tsana fiyeda komai kuma ma'ana kb.


Rufe idanuwanta tayi hawayenta nasake saukowa zuciyarta ke neman yaudararta da wadatuwa da wani irin sanyi da nutsuwa.


Nadia Ni JJ alqawarine na dauka na kulada abinda shine rayuwar Zaki har tsawon numfashina nayi zan kula dake nabaki kariya tareda farin ciki da qarfin jikina,dukiyata tareda rayuwata Dan haka kisa aranki kinada Yaya ko abokinda zai iya Miki komai.


Kasa riqe kukanta tayi tasakesa duk da bayada sauti Amma tayisa sosai sbd JJ ya hargitsa tunaninta gabaki daya da nutsuwarta.


Kodata koma cikin gida dakin mahaifiyarta inda danginta suke can ta nufa ta zauna ahankali kan tabarma gefen qanwar mahaifiyarta dasuke uwa daya uba daya takalleta saita sauke Kai tayi shiru tana gangaro hawaye sbd ayanxu ba abinda take tsananin buqata kamar kulawar uwa Saidai batada bakin magana bare ta roqa daga qanwar mahaifiyartata sai kawai ta soke Kai cikin qafafunta tana sheshekar kuka.


Ahaka ta wuni ta kwana cikin tsananin damuwa washegarin daurin aure da mugun zazzabin da sanyin jiki ta tashi sbd tsananin damuwa musamman yau data ringa mafarkin JJ cikin mummunan yanayi,


Tabbas har cikin ranta JJ takeson aure sbd shikadaine zai iya inganta rayuwarta yabata farin ciki ko Babu soyayya Dan kuwa qauna yake Mata mai tsafta duk da lalurarta bai damuba ya nuna sha'awar aurenta.


Qarfe goma Sha biyu za'a daura auren Dan haka tun yanxu da qarfe Tara aketa share qofar gidan da layin musamman wannan aikin yaran sarki ne duk da gabaki daya yanxu basa gane masa yasake zama wani sarki sbd Sam ko doguwar magana bayayi musu yanxu ga uwar shegu dayakeci babu sauqi yanxu duk Wanda yayi atake yake bada umarnin aci ubansu sai kawai hakan yaqarasawa mutane shakkarsa Dan kuwa yanxu ya qone gabadaya ba tausayi.


Qarfe goma mal zailani da qaninsa malam buba sukazo gurin mal idi da taddiya Suka sanar dasu maganar gaskiya sun fasa sbd dai duk wata barazana da rayuwa anyi musu takai takawo dai Bello harsun masa billen masu nama a kumatu.


Cikeda damuwa da taushin murya mal idi yace"


Don Allah mal zailani kuyi hkr wlh insha Allah Babu abinda zai faru kawai barazanar banza ce da yardar Allah akwai alkhairi acikin abin nan.


Aa mal idi duk inda kake tunanin abin nan ya wuce sbd muma farko cewa mukayi saimunyi tunda anyi niya saikuma mukaga abin Babu 'da'a aciki da azo ayi Dana sani gwaradai ahaquran.


Kasa magana dattiya yayi sbd zuciyarsa data gama gaurayewa da baqin ciki da damuwa,...


Mal buba cikin Rahin dadin Rai shima yace"


Maganar gskia dattiya wannan ba rayuwa bace ace 'yan ta'adda a gidan ikonsu haryakai ace zasu Hana 'yarka aure sannan idan Kuma barinta akayi sune zasu lalata maka 'yaya,

Gskia wannan ba mafitar rayuwa bace Dole kasan abinyi tunda dai gashi yanxu meye amfanin hakan munason abin nan Amma munaji muna gani Dole mufasa.


Aa mal buba tunda duk munaso me rufe ido ayi auren nan Dan Allah kodan mutuncin aminina da 'yarmu NADIYA da batada laifin komai kar abata Mata suna Dan Allah kuduba harkarnan"""mal idi ne yake fadar hakan cikin taushin murya.


Tabbas qaddarace tasashi aika ruqayya Lagos Amma gashinan Yana ganin aikin da son zuciyarsa na aikata yajawo masa,


Zaki wata masiface a rayuwarsa Saidai yanxu Kam bayajin ya ta6osa a inda ake ta6asa ya qyale Dan kuwa bai hada 'yarsa Nadiya da komaiba,


Ya wulaqanta martabarsa data 'yarsa Nadiya shikuwa ayau zai nuna masa shine babba,shine mai iko dasu duka Dan kuwa ko uwarsa ruqayya shine mai iko da ita,


Ayau zai tabbatar masa daya isadashi,

Yanda zaiyi kwanan baqin ciki ayau to tare zasuyishi.


Kallon su mal zailani yayi idanuwansa jajir yasaki fuska murya a shaqe yace"


Tabbas kunyi min karamci tunda harkuna sake nuna qaunar 'yata gareku saidai fin qarfinku da akayi nagode kuje Babu komai Allah yayi Mana mafita da zabi na alkhairi.


Amin sukace dukkaninsu cikeda Rashin jin dadi da tausayin dattiya Dan kuwa kowane uba akayiwa haka Yana cikin tsananin baqin ciki da damuwa.


Bayan fitarsu ya dade kan tabarmar zaune a cikin soron gidan mal idi bai motsaba,


Kallonsa mal idi yayi cikin tausayawa amininsa da takaicin yanda su JJ Suka mayardasu wasu qananan mutane ya sauke ajiyar zuciya yace"


Sai haquri dattiya,aure nufin ubangiji ne Allah beyi matarsa bace shiyasa hakan tafaru wani baya auren matar wani....


Tabbas wani baya auren matar wani shiyasa bazata auri Bello ba hakama JJ dinda yakeson ta aura dinma bazata auresaba shizan aurawa ita Kuma wlh duk Randa ya saketa yagama zaman gidana har abada.


Kallonsa mal idi yayi yace"


Kana ganin hakan shine mafita dattiya???


Duk Wanda zaizo aurenta me kake tunanin zai sake faruwa bayan irin haka??

'dan iska zasu mayardani nazama abin zagi agari gwara na 'yanke komai tun yanxu idan na aura masa ita zance yaqare Babu sauran sani baqin ciki shinema cikinsa tunda shima ba haka yasoba yaronsa yaso abawa.


Shiru sukayi dukkansu ransu a jagule da baqin ciki da damuwa,


Shidai duk abinda yayi gudu shekaru aru aru na baqin cikin hada zuria da 'yan ta'adda daya Hana auren qanwaesa ruqayya da neyo gashinan dai to 'yar cikinsacema zata auri Wanda ya dame neyo ya shanye a ta'addancin,..wannan wace kalar masifa ce.,

Shine yaqi neyo wancan lokacin gashi neyon na girmamasa da masa ladabi musamman ma dayazo ya musulunta Amma yaqisa yanxu gashinan Wanda ko kallon mutunci baya masa zai bawa 'ya,

Wanda Babu kalar qanqancin dabayasa ana masa..Kai shikan Allah yakawo masa dauki.

#MAMUH*_BURI DAYA Yana cikin Zafafa2020 na siyarwane  ba free ba idan baki biyaba ki nemi wainnan numbers din kibiya ki karanta cikin amincin allah._*


07067124863

08030811300*_Mamuhgee11_*

Qarfe goma Sha 'daya su JJ da Suka fito kowane 'dan daba ranar dai manyan Kaya sukaita sawa wani suyi masa kyau wani kamar irin mutanen 9s dinnan sbd tarin sumar kansu gashi ranar Zaki yabada umarnin kowa ya aje makaminsa Babu ta'addanci yau tunda ranar auren magajinsa ce,


JJ kuwa wata farar shadda ce ajikinsa wadda Zaki ya dinka masa ba laifi tanada 'yar tsada Dan kuwa dubu ashirin yasiye ta yadi goma goma  guda biyu shi tasa sky-blue ta jj din fara.


Tuni qofar gidan da layin yafara cika da mutanensu Amma sai 'yan anguwa dasuka fara halartowa 

shidai dattiya kallon kowa yakeyi zuciyarsa ba dadi ga cikin gida ma Nadiya jikinta sai rawa yakeyi sbd tashin hankalin data samu kanta aciki ga zazzabi tanaji ga Rashin sukunin da zuciyarta ke ciki.


Lokacinda yafito cikin sky-blue din shaddarsa 'yar ciki da babbar riga ga hularsa Yana daura agogo yafito daki daidai fitowarta daga daki zataje Kiran iya talatu cak ta tsaya tareda juyowa ahankali daidai ya kallo gefen Suka hada ido.


Wasu irin hawaye ne Suka ciko idanuwanta sanin daga yau idan ta auri Bello bazata sake rayuwa a inda yakeba.


Dauke Kai yayi Yana sake hade fuska ya fito waje.


Wani irin annuri da haiba ke fita a fuskarsa sbd tsananin kyawun da yayi tamkar shine angon musamman izzarsa dake qara masa burgewa da kyau.


Nufosa JJ yayi cikin tsananin farin ciki ya miqa masa hannu sukai musabaha batareda ya saki hannunsa ba yace"


ALEEYU HAIDAR Ina cikin farin cikin ganin kana taredani a yau ranar aurena Rana mafi farin ciki agareni Saidai Ina roqon wani Abu daga gareka.


Wani irin murmushi yayi Yana basarwa yakalli JJ din ganin yanda yayi wani iri sai habarsa ta dakesa atake yaji tsananin qaunar JJ din nasake shigarsa Dan kuwa shikadai yasan irin son dayakewa JJ Wanda yasa yake danne ciwon dayakeji a qirjinsa ganin JJ na farin ciki da auren.


Cikin kulawa yace"


Kafadamin abinda kakeso agurina zan baka kodan tarihin wannan Rana agareni.


Murmushi JJ yayi yace"


_*NADIA*_ nakeson tasamu dukkanin farin ciki da walwala tareda kulawa da qauna data rasa tun rasuwar umma,


Kallonsa yayi tareda dauke Kai Yana zame hannunsa daga nasa fuska a daure yace"


Wannan duk zaka Bata bayan aur.....


Bai qarasaba ya juya zai wuce

JJ yace"


Nayi Mata alqawarin nema Mata lafiyarta matuqar Ina raye da lafiyata,

Saidai bansaniba kozan iya,

Roqona anan shine Ina roqonka da a duk lokacinda na gaza cika wannan alqawarin to cikaminshi koda inanan ko banan.....


Juyowa zakin yayi Saidai kafin yayi magana ya hango kb tafe cikin mutane ya rufe fuskarsa Yana boye wani Abu cikin riga.


Janye JJ yayi da sauri zai tare kb din Saidai jj na juyowa yaga sharbebiyar wuqarda ke hannun kb wadda asalinta bakin lace ne da Ida kamar tafiyar maciji idan aka sokeka da ita yanada wuya ta fito Bata yanko hanjinkaba shiyasa ba'a tsallaketa.


 Kb na daga wuqar JJ ya tare atake ta shige cikinsa gaba dayanta kafin kb ya fizgota da qarfi yanda zatafi yimasa illa.


Wani irin numfashin wahala JJ yasaki tareda zubewa qasa kb na ganin hakan ya gudu musamman da Babu Wanda ya Ankara da abinda ke faruwa


Zaki zabura yayi ya damqo hannun kb JJ yayi saurin riqe nasa a wahalce yace"


Ina buqatar kusa Dan Allah.


Cikin karaji yacewasu nano subi kb su kamosa karsu Bari ya gudu.


Atake guri ya kaure da hayaniya sbd ganin abinda ya faru jini gabaki daya ya Bata farar shaddar jikin JJ har qasa.


Wani irin runguma Zaki yamasa Yana cewa"


JJ Dan Allah karka rufe idonka zamuje asibiti zaka warke yanxu muxo a daura maka aure,

Karka manta Kaine kuzarina da ganina,

Kaine magajina,

Karka rufe idonka Dan Allah JJ......


Cikin tsananin karaji yace akawo masa mota.


Hankali tashe da ganin jininda ke zuba Suka sakashi mota a gigice Zaki ke tuqin hannunsa daya na damqe dana JJ da tuni idanuwansa Suka rufe.


Duk yanda su dattiya ke cikin 6acin Rai hankalinsu yatashi matuqa da abinda yafarun Dan kuwa tabbas kowa yasan JJ shine abunda Zaki yafi so,shine komai na Zaki.


Zancen na shiga kunnen Nadiya ta sulale qasa tana tsiyayo hawaye da idanuwanta dasuka gama kumbura dayin jajir.


Suma sauran mutan gidan sun firgita sosai da jin zancen musamman da aketa cewa JJ yariga ai yarasu.A asibiti kuwa suna zuwa 'yan sandan da ale dikko yaturo musu suna isa nan aka karbesa a gagauce akai cikin theatre dashi.


Kasa zama Zaki yayi tareda yamutsa sumarsa yanajin zuciyarsa kaman tana qonewa sbd tsananin tashin hankali da baqin cikin dayake ciki.


Su nano tuni Suka iso asibitin sbd dai kb ya gudu Amma dai aisunsan bazai guje musu ba idan hankali ya kwanta.


Sosai suke cikin tsananin tashin hankali da fargabar abinda zai faru,


Asibiti kuwa atake kowa yasan yau su sarki na asibitin Dan kuwa tuni kowa ya dauko makansa.


Minti goma Sha hudu da shiga dashiga dashi likitoci biyu Suka fito fuskarsu ba dadi Kai tsaye 'dayan yace"


Sai hakuri Allah yamasa rasuwa..


Akaro na farko arayuwarsa da hawaye Suka sauko idanuwansa yayi baya tareda zubewa a kujera Yana dafe kansa dazai tsage sbd wani irin sarawa da jijiyoyin kan sukeyi.


Su Nanu kuwa tuni duk Suka saki makamansu kowanne na sunkuyar dakai cikeda baqin cikin rasa 'dan uwansu,aminsu mai qaunar dukkaninsu.


Sosai Dr aminu da Dr faruk Suka tausayawa halinda Zaki yashiga musamman dasuka lura kansa yake ruqewa sunsan illar dake cikin hakan sukai saurin sa nurses maza su kamosa ashigo ciki dashi Yana buqatar kwanta suyi masa allurar minti goma.


Miqewa yayi da kansa yashiga kodan yaga gawar JJ 'dinsa Saidai suna shiga yaga gawar JJ din rufe har Kai da qafa 

Atake yaji zuciyarsa na neman tarwatsewa itama ya isa bakin gadon yayi shiru Yana tuno maganganunsu na qarshe.


Ya dade Yana kallon gawar kafin ya juyo baiko tsaya sauraron Kiran da Dr kemasa amasa allura ba yafito atake yaransa Suka Mara masa baya musamman dasukaga fuskarnan ba rahama ko daya.


Cikin motarsu Suka figeta sai qofar gida lokacin Sha biyu saura minti ashirin gashi mutane na nesa basusan da abinda ke faruwaba tuni aka sake cike gurin taf da 'yan zuwa daurin aure.


Dan kuwa tuni akayi shimfidu anata gaishe gaishen barka da zuwa.


Suna sauka Kai tsaye gurin kawun ya nufa shima yana ganinsa yayiwa idi ido nan aka fara shelar za'a daura auren.


Take kowa ya zazzauna aka fara.


Yana isowa ganin mutane da yawa yasa yazo har kusada kawun ya zauna Kai tsaye yace"


Zanyi magana dakai kar a daura sbd JJ ya....


Cikin nutsuwa kawu yace"


Kabari agama daura auren muyi magana yanxudai ka nutsu auren 'yatane bana son matsala.


Miqewa yayi yabar gurin ya hargitse kansa yake.


Cikin nutsuwa dattiya ya fitarda dubu goma a miqawa liman yace"


Ga sadakin 'dana nan.

 

Karba akayi aka miqawa mal idi dashine yayi waliyin Nadiya.


Yakai mota zai shiga subar gurin yaji ana cewa"*_AN DAURA AUREN ALIYU HAIDAR DA NADIYA DATTIYA AKAN SADAKI NAIRA DUBU GOMA LAQADAN BA AJALAN BA ALLAH YASA WANNAN AURE SAI MUTUWA_*


Aminnnnnn jama'a Suka karba anata miqawa dattiya hannu ana tayasa murna nan guri ya kaure da hayaniyar Taya murna.

#MAMUH*_BURI DAYA Yana cikin Zafafa2020 na siyarwane  ba free ba idan baki biyaba ki nemi wainnan numbers din kibiya ki karanta cikin amincin allah._*


07067124863

08030811300*_Mamuhgee12_*

Kasa shiga motar yayi hakama yakasa juyowa

Zuciyarsa nason qin gasgata abinda kunnuwansa Suka jiyo masa musamman yanda numfashi ke sauri gurin fita.


Dukkanin yaransa kuwa wuta Suka dauke Basu nuna farin cikinsuba daya wanxu cikin zukatansu sbd jimami da radadi dasuke ciki na Rashin dayan jigonsu JJ.


Ahankali ya juyo bayan ya rintse idanuwansa ya bude atake Suka qara kadawa Suka rikide.


Kallon kawun yayi daketa miqawa mutane hannu Yana yaqen dole Dan kuwa shima ayau din zuciyarsa dif take da damuwar wannan aure Saidai baida yanda zaiyi Dan kuwa wani bangaren auren Zaki ga nadiyarsa shine mafita Dan kuwa idan tana matsayin matarsa Babu shegen da zaiyi Gigi ko gangancin ko yiwa inda take mugun kallo,

Saidai ta bangaren rayuwar aure yasan Zaki bazai taba kulada Nadia ba musamman ganin yanda yafi hukuntata akan kowa.


Hada ido sukayi sukayiwa juna kallon cikin ido kowanne zuciyarsa cikeda damuwa da tsananin bacin Rai Saidai hakanan ya juya yafada mota sukabar gurin Dan zuwa dauko gawar JJ azo ayi Mata sallah.


Suna barin gurin aka fara watsewa sbd wasu da dama basusan da rasuwar JJ ba.


Acikin gida kuwa lokacinda dahiru yashigo bayan daurin aure shine yafara shigowa ya nufi dakin iya talatu dake 'dan cikeda mutane anata hayaniyar biki ya miqa Mata goro da dabinon daurin auren yana cewa"


Ga goron nan ki ajiye har baban yashigo andaura aure da yardar Allah Saidai abin mamakin baba baya qarewa mu munxo da sanin Bello ne mijin saigashi mukaji baba agurin yacewa liman da Zaki za'a daura auren.


Saurin kamo goron daya kusa zubewa iya talatu tayi tana kallon dahiru tace"


Zaki fa kace????


Eh, Allah yabasu haquri da juna shine fatar kawai tunda andaura.


Numfashi iya talatu tasaki tana sake zare 'yan fici ficin idanuwanta cikeda mamakin dattiya da Rashin sanin abin fada kawai tace"


To Allah ya sanyaya zuciyar Zaki mudai da wannan danyen hukuncin na babanku.


Kallon zainab dake tsaye gefenta tana waya da wasu qawayenta datakewa kwatancen gidan tace"


Auren nan kinji da Zaki aka daura.


Wani zaro ido tayi cikeda mamaki da son qin gasgata zancen tace"


Yaya Zaki yanxu shine mijin Nadiya????


Kwarai kuwa cewar dattiya daya shigo gidan.


Aikuwa nan aka dauki guda ana Allah ya sanya albarka.


Zainab kuwa daki tayi da sauri Dan fesawa Nadiya zancen.


Qare Mata kallo tayi daga bakin qofar tana kwatanta irin dacewarda zasuyi da ace zasuyi zaman aure kamar na kowane maaurata Saidai tasan Yaya Zaki Kam ko kallo Nadia bazata ishesaba duk da wasu lokutan tanayi musu kallon masoya duk da irin tazarar halaye da banbanci dake bayyane a tsakaninsu.


Qarasowa tayi cikin dakin ta zauna kan katifar dake dakin tareda aje wayarta tana daukar Hoda tafara shafawa fuskarta da Bata rabo da kwalliya koyaushe hankali kwance race"


Andaura aure dai yau kukan auren Bello yaqare Saidai na Yaya Zaki....


'dago jajayen idanuwanta tayi takalli zainab din ahankali batareda hawayen cikin idonta sun gangaroba sbd kokawar da zuciyarta keyi gurin auna zancen kafin ta yarda dashi a zuciyarta.


Aje hodar zainab tayi tareda kallonta tace"


Baki yarda bane ko me?kike min kallon qurulla...


Sallamar dattiya tasasu kallon qofar dakin atare,

Zainab ta miqe tareda daukar wayarta da gyalenta ta fice Dan tarbo baqinta.


Cikin sanyin jiki data fara ganin mahaifin nata dashi akaro na farko rayuwarta taga yashigo ya tsaya akanta zuciyarsa ba wani dadi yakalleta tayi qasa da Kai hawayenta na sake saukowa sbd yanayinsa kawai ya tabbatar matada zancen da zainab tafada gskia ne da Yaya Zaki aka daura Mata aure.


Cikin sanyin murya yafara cewa"


Nadiya Allah yayi yau nasauke nauyinki dayake kaina amatsayin mahaifinki Dan kuwa na 'daura Miki aure ayau din da Zaki Wanda shi na zabar Miki amatsayina na mahaifinki Dan haka Babu wani Jan dogon bayani Saidai Ina Miki adduar Allah yasa hakan shine alkhairin rayuwarki duk da nasan Babu abinda Zaki tsinta acikin auren zakin.


Qaramin kuka Mai ban tausayi ta fashe dashi Babu sauti Yana ji yajuya ya fice Yana jin wani qululun baqin ciki da takaicin zakin.


Sosai tayi kuka Wanda sai yanxu take jin gwarama auren bellon tunda shi Yana sonta yanxu wannan auren wace irin rayuwa baban ke tunanin zatayi da mutuminda ko kallon inda take bayayi da daraja bare ma matsayin Mata.


Cikin yan biki kuwa Babu Wanda ya damu da wannan juyi da akayi hidimarsu sukeyi hankali kwance saidaima rasuwar JJ ce dake 'dan rage musu armashin abun duk da dai shiru har yamma tasomayi su zakin Basu dawo da gawar JJ dinba bare ayi jana'iza.


Har guraren magriba Babu labarin dawowarsu bare ayi jana'iza tuni aka gama yinin bikin aka watse ba maganar Kai amarya tunda gida daya suke ataqaice ma Babu gurin kaita.


Ahaka gida ya watse aka barsu sukadai yan gidan Dan ko dangin mahaifiyarta da maraicen Suka tattara Suka tafiyarsu ko Dan ganin angon nata ba irin Wanda zasu tsaya suyiwa nasihar riqe 'yar marainiyar 'yarsu bane Dan kuwa su kansu ranar dasuka fara zuwa sukaga bataliyar makamai da yaransa a qofar gidan a tsorace sukeda gidan har Suka tashi tafiya musamman yanxu dasukaji shugaban bataliyar shine mijin yarsu.
***

Lokacinda Suka koma asibiti Sun Jima suna neman likitanda case din yake hannunsa gashi yashiga theater Dole Suka jira yafito sbd asibitin ta dikko Dilla ce dokace ba'a bayarda gawa sai likitan daya karbeka yazo yasaka hannu kunsaka sai abaku gawar.


Sai kusan yamma Dr jimoh yafito zuwa lokacin ran Zaki yafara baci Amma sbd yanason mutunta gawar JJ bazaiso yin kowane irin Abu na ta'addanci ba akan gawarsa sai angama komai akwai Wainda zaiyi settling scores dasu.


Atare Suka nufi dakinda gawar take bayan ansaka hannu da komi.


Tura qofar dakin sukayi Dr jimoh yayi saurin qarasowa ciki Yana kallon gadon ganin baiga gawar ba.


Kallon nurses dinda ke bayansa yayi suma Suka kallesa da tsoro da mamaki...


Wani irin kallo zaki yayiwa likitan Yana jiran qarin bayanin inda gawar JJ take Dan zuwa lokacin yagama zuciya zai iya tada asibitin kowama ya mutu ahuta.


Zare coat din saman kayansa Dr jimoh yayi Yana taba gadon murya na rawa yace"


Nurse Ahmad go and call all the nurses on duty and Dr ib Idris now.


Jiki na Bari kuwa yafice ko gani dukkaninsu basayi sosai sbd carriers dinsu ce zatayi rawa tunda maganar Rashin ganin gawa akeyi anan.


Cikin qanqanin lokaci hankalin asibitin yatashi sbd dai duk iya bincikensu anyi gawar JJ dai ta Bata Saidai abinda yafi daure musu Kai da mamaki duk security sun tabbatarda Babu gawar da'aka fita da ita Saidai Idan gawar na cikin asibitin a boye kokuwa sai kuwa idan gawar ce tafita da kanta.


Wannan zancen shiya qara hasalta zuciyar Zaki atake yaransa Suka tsare dukkanin qofofin asibitin Babu shiga Babu fita 

Nan hankula Suka tashi Dan kuwa Dole hukuma tashigo ciki sbd ganin irin illar da za'ayiwa Wainda basujiba Basu ganiba. 


Alee dikko dake zaune cikin lafiyayyen palonsa riqeda tumbler yanashan Champaign hannunsa riqeda wayarsa da AM DILLA wato dansa yakirasa yafada masa halinda ake ciki gashi zancen na neman shiga hannun media Wanda zai iya lalata sunan asibiti bama ita kadaiba zai iya taba asibitocinsa da kamfunan maganinsa Wanda bazai iya daukar hakanba Dole something has to be done.


Zeel dilla dake shigowa palon tareda am cikin wata irin Isa da iko tareda wani irin mulki ta qaraso kujerar gefensa ta zauna cikin kwanciyar hankali tadauki remote tana cewa"


Karka Bata ranka tun yanxu sbd ainihin tension din nazuwa matuqar baka kawarda Zaki a duniyarba gabaki daya.


Miqewa yayi tareda zuba hannayensa a aljihu ransa na qara baci sbd da ace wani ne yau yayi wannan abin ko haka baza'a kawoba baibi gawar dayake nemanba,

Amma Zaki na neman caza masa Kai Wanda yake kawarda hakan Dan kawai Yana buqatar zakin Saidai wannan karon Dole zai dauki mataki duk da Yana tunanin abinda zai faru ranarda Zaki zai gano abinda yake Shirin masa

Amma Dole za'ayi hakan Dan kuwa Babu wata Rai dabaya iya kawarwa akan dukiyarsa daya Tara da abubuwa da yawa matuqar yanada damar iyawa.


Juyowa yayi yakalli am dake faman amsa waya Yana bawa security orders na duk yanda za'ayi ayi kar abari media su fitarda abin nan.


Sake kallon am din yayi Kai tsaye yace"


Kaje asibitin da kanka asan yanda za'ayi ayi a nunawa Zaki cewar JJ bai mutuba ya gudu ne......


Cikin wani irin yanayi zeel ta kallesa tana cewa"


Wat???

Kana tunanin Zaki daqiqi ne kamar qaton danka dake gabanka...


Hade fuska am yayi tareda juyowa zai katseta ta 'daga masa hannu tana cigaba da cewa"


Kana tareda shine Amma kamar idanuwanka sunkasa ganin meyene a a tattaredashi,

Wannan zancen idan ma kayisa kana bude qofofin yaqine dashi Dan kuwa kafi kowa sanin waye JJ agurin Zaki.


Cikin fushi da bacin Rai ya katseta da cewa,


Stop giving me lectures akan yaronda na haifa nesa.,idan kinada wani option akan hakan ne just tell us and stop wasting my time bayan kinsan the power of media.


Miqewa tayi tana kallon cikin idonsa tace"


JJ na hannuna Kuma Yana cikin asibitin and he's alive bai mutuba...


Cikeda baqin ciki dayafi mamakinsa yawa yake kallonta duk da yasan wani lokacin zeel tamafisa sanin hanyoyin Rashin Imani Saidai bayason abinda zai taba sunansa koyayane sbd shine kadai yasan irin abubuwan dayayi kafin yayi sunan.

#MAMUH.*_BURI DAYA na kudine idan ba ki biyaba  nemi wainnan numbers din kibiya ki karanta cikin aminci_*


*07067124863*

*08030811300**_Mamuhgee13_*

Rintse idanuwansa yayi ya bude cikin wani irin zafi yace"


Kinfi kowa sanin abinda nake iyayi da Wanda zan iya yiwa kowa akan harkar dukiya,meyasa kikeson batamin ayyuka so da dama?


mezakiyi da JJ dakika sa akace ya rasu???

Wat are you planning this time zeell?


Yafada cikin daga murya da bacin rai,


Wat Eva u're planning karki sake ki batamin aiki sbd Zaki is one of the  precious abunda bana Wasa dashi Dan kuwa Ina hango wa kaina taskokin nasara da ikon mulki dazanyi amfani dashi nasamu so be very very careful with me.


Daukar wayarsa yayi tareda juyowa ya kalli am dake cikin takaicin abinda ke faruwa Rai bace yace"


Nasan kasan inda takai JJ kuyi gaggawar kashesa ku maida gawar inda take tunda anriga ance ya mutu

Bazan dauki ganganci irin nakuba.


Ficewa palon yayi zuwa samansa Yana sake jin haushin abinda zeel din tayi duk da dai yasan tanada dalilin yin hakan Amma Koma meyene dalilin bayason rasa Zaki yanxu batareda yasamu cimma burikansa akansaba.


Acikin daren am yakira wasu yaransa dake boyayyen gurinda Babu Wanda yasani cikin asibitin yace su shaqawa JJ din phamialiasinon shida 'dayan likita dinda yatayasu aikin sace JJ din su mutu su jefarda gawarsu ko Ina suka samu ciki asibitin su gudu.


Hakan kuwa akayi suna shaqa masa Basu tsaya duba koya mutum ba Suka Shaqawa dr shima atake ya mutu Suka fito tareda cinnawa gurin wuta suka tafiyarsu Saidai suna fitowa yaran Zaki sunga fitarsu Suka bisu nan Suka gudu dayake da baqar mota suke atake suka guje musu.


Ahankali wutar tafara yin yawa hartanayi sama nan aka lurada gobara a dayan bangaren asibitin da ba'a zuwa sbd ko gamasa ba'ayiba.


Atake aka fara Kiran fire Bridget sbd ganin wutar naci sosai.


Koda su nano Suka dawo Suka sanarda Zaki take yagane gawar JJ ce agurin nan hankalinsa yatashi Suka fara kashe wutar yanajin kamar yashiga ciki ya fiddo gawar JJ.


Qurmus wutar ta cinye gurin ba'a samu ciro gawar JJ ba sai asuba inda gawar ta cinye ba'a ganesa gabaki daya ya canxa.


Gawa 'daya Suka gani Suka tabbatar JJ ne kawai kenan aciki suka kunna wutar.


Sabon kukan baqin ciki na zuci Zaki yayi zuciyarsa na daukar radadin Rashin JJ,

Kallon qonanniyar gawar JJ yayi ya rintse idanuwansa dasukai jajir yanajin zafin zuciya Dan kuwa ya tabbatarda wannan kisar wulaqanci ce akayiwa JJ Dan kuwa Dole akwai abinda ke boye tunda aka dauko gawar aka kawo nan aka qona.


Ido jajir yadago yakalli su nanu murya can qasan maqoshi yace"


Ku shigoda mota asa gawar muje da safen nan zamuyi jana'izarsa

Asibitin kuwa duk securitynsu da ma'aikatan dake cikinta ku sauya musu kamanni.


Dan kuwa suka Suka rufe ido Suka hau duka da fasa duk wani Abu dake asibitin Wanda yasa jama'a Suka fara guduwa Dan tsira da rayukansu Dan kuwa tuni gurin ya kaure da ihun sare sare da duka.


Shikuwa haka Suka dawo gida da gawar lokacin har gari yayi haske sosai,


Duk Wanda yaga gawar JJ Saida Imani yasake kamasa nan 'yan anguwa Suka dinga hallara cikin jimami da tausayi tareda yimasa kyakkyawar addua Dan kuwa kowa ya kadu da faruwar wannan alamari musamman Zaki daya kasa kuka sai jajir da idanuwansa Sukayi sai jijiyoyin qarfin jikinsa dasuka firfito a damtsen hannuwansa da kansa sbd tsananin nauyi da 'dacinda zuciyarsa ke masa.


Ayau duk wani Mai tashen iskanci yashiga taitayinsa Dan kuwa kada qaddara da tsautsayi takaika kutsawa huruminsa.


Cikin gidanma sosai Suka tausayawa JJ musamman Nadia dake kuka sosai sbd JJ shine mutum mafi kusa da ita mai yaye Mata kewar kadaici da damuwa Dan kuwa shine yafi kowa Bata kulawa,


Shine mai zaunawa yayita yimata fira duk da Bata iya basa amsa Amma sunajin dadin firarsu.,


Shine take yiwa kallon 'dan uwa mafi kusa data bawa mahimmanci arayuwarta bayan babanta da zaki Saidai ayau tayi rashinsa adaidai lokacinda take buqatarsa kodan yanda zata fuskanci wannan aure da aka hada da Wanda batako cikin duniyar gabansa.


Wani 6angaren kuwa Zaki take yiwa kukan sbd tasan yanacikin qunci mai yawa na Rashin JJ tunda tasan waye JJ agurinsa,Bata taba ganin abinda Zaki yafito yanuwa duniya tsananin qauna da son dayake masaba bayan JJ Dan haka tasan yau yayi babban rashinda zai ringa quntata zuciyarsa.Qarfe Tara akayi jana'izar data Tara 'dibbin mutane harda dikko Dilla da 'dansa tareda 'dibbin securities dinsa  aka watse.


Babu wani zaman gaisuwa da zakin yayi duk Wanda yayi gaisuwa wucewa yakeyi sbd zakin ko qofar gidan bai zaunaba Yana cikin dakinsa sbd tsananin ciwon Kai dayake fama dashi ko hayaniya bayaso shiyasa yau ko iya talatu Bata saki dabbobinta ba sbd ma karsu damesa da kukan akuyoyi yanxu ayi Mata waje dasu.


Kawun nema Suka zauna a qofar gidan shida su mal idi suna karbar gaisuwa duk da yawanci ire iren mutanensu ne masu masu wando a sabule da dinkin sare sare fuska sune masu zuwa gaisuwar Kuma duk Wanda yazo yayi saiya miqe sbd Rashin ganin sarki agurin.


Nadia har dare bata hangi fitowarsa daga dakinsa ba saitaqara jin zuciyarta na nauyi musamman tunowa da dah JJ nanan bazai barsa da damuwaba da yanxu yabisa yaji lafiyarsa ko Kai masa abinci.


Tana bakin gurin wanke wanke tsakar gidan tana alwalar ishai taji motsin fitowarsa daga dakin sbd qofar dakin datajiyo qarar anbude

Zuciyarta tafara bugawa da sauri 

Take hannuwanta suka Dan fara rawa takasa motsawa tana jiran jin Ina yayo sbd so take ta tashi tabar gurin tun kafin yaqaraso ya rage zafi akanta.


Cikin gidan yayo jikinsa sanye da three quarter da vest black sai towel a hannunsa da kwandon kayan wankansa da fitila kasancewar Babu nepa.


Tana dainajin takunsa ta hadiye miyan fargaba tareda miqewa tsaye tana qoqarin daidaita numfashinta dake fita da sauri ta juyo kanta aqasa batareda ta kalli fuskarsaba ta nufi bucket dake gefen durum na ruwa tafara zuba masa hannuwanta na rawa sbd tasan abinda yake nufi da tsayuwar dama ta Saba ko ita ko JJ ne masu masa wannan aikin.


Tana gama zubawa ta 'dauka takai har cikin bayin ta ajiye zata fito shikuma zai shiga tayi saurin matsawa gefe daga ciki.


Dattiya ne yashigo gidan da fitilarsa dataji sabbin batir sbd haske ya hango abinda ke faruwa ya zare ido da qarfi  take yaji hankalinsa na neman tashi Sam yama manta da cewar Nadia matar zakin ce yanxu a diririce ya qarawa fitilarsa haske murya a zabure Yana cewa"


Ke Nadia me kikeyi agurin???

maza baro gurin nan zo nan ki wuce daki kafin na karya Miki qafafu.


Yanda yayi maganar yasa Zaki juyowa ya kallesa sbd sosai sautin tsoron haduwar tasu ta fita a muryarsa dakuma rudewa wadda baitaba ganinsa da itaba.


Batareda ta dagoba Sum sum ta fito ta wuce ta gaban baban ta shige daki qafafuwanta na cigaba da rawa.


Baban yabita da harara Yanajin wani irin takaicin ganinsu a keben...

Shidai wlh yaga takansa da Zaki arayuwarsa..


Kota kansu baibi daga ita har uban nata yarufo bayin Yana zare vest dinsa.Washe gari tunda safe tahau ayukan gidan kamar yanda tasaba harta gama tafara wanke wanke tana gab da gamawa taji motsin fitowarsa daga dakinsa take tafara daburcewa tana qoqarin cigaba da aikin Saidai jin muryarsa a bayanta Yana waya da alee dikko yasa ta qarasa rikicewa har batasan lokacinda ta 'dora hannunta da qarfiba kan wuqa ta caketa take jini yafara fita tayi saurin dafe gurin har lokacin hannuwanta rawa sukeyi.


Rintse idanuwansa yayi cikin takaicinta tareda datse wayar cikin tsawa yace"


Tashi kibar nan kafin na taka wuyanki wuwuyar yarinya.


Da sauri ta miqe jikinta na qara daukar rawa ta nufi daki ta shige da sauri tana sakin hawayen datake riqewa na azaba dakuma tsoronsa.Dattiya da tunda yaji muryar zakin yataso da qarfi daga kwancen dayake ya labe Yana kallon abinda ke faruwa Dan gabaki daya yanxu yarasa nutsuwar zuciya idan Zaki na kusada Nadia Sam har cikin ransa bayason su kebe ko yayane Dan kar Zaki yakaisa yabaro.


Zaki na luredashi yaja qaramin tsaki tareda fasa dibar ruwan brush dinda zaiyi ya fice sbd haushi da takaicin dattiyan da Kuma nadiyar

Da JJ nanan da yanxu baishigo yaga wannan abin takaicinba.
***


Kwana bakwai kenan da rasuwar JJ tuni aka fara mantawa dashi aka hau harkoki Saidai Zaki da mutuwar take zaune daram cikin ransa Dan kuwa haryanzu Yana son gano abinda yafaru musamman da alee dikko baice komaiba gameda muguwar barnarda akayiwa asibitinsa saima sake qarfafa masa dayakeyi gameda alamarin.NADIA kuwa tuni duk wani kyalli da lallen amarci ya goge aka cigaba daga inda aka tsaya na rayuwar gidan,


Tananan ayanda take da yin duk wani aikin gidan na iya talatu,

Saidai yanxu da aikin suka dan qarar Mata sbd abubuwa da dama da JJ keyiwa zakin itace keyi yanxu kamar Kai masa ruwan brush har qofar dakinsa kullum da safe sai zuwa fitoda plate ko kular abinci idan a gidan yaci abinci shi dama aikin Kai ruwan wanka tasaba tuntuni tun ummansu nanan.Dattiya kuwa tuni abun duniya ya ishesa sosai yasaka musu ido duk yanda yaga ta nufi dakin Kai wani Abu yake zuwa daga bakin soron ya tsaya Yana wayar qarya da 'yar Tecno dinsa da keys duk sun goge harsai yaga ta fito kokuma ya azalzaleta da Kira,


Idan Kuma zakin ne yashigo haka zai dinga Ware ido akansu harsai yaga yafice

Har wani yamutsewa yayi sbd daga hankalinsa da yayi Wanda kullum saiya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin Zaki Dan kuwa badan balainsu ba da yanxu tana gidan mijinta Bello baida wannan fargabar.


Cikin takaici iya talatu dake zuba 'dan gum din gyaran takalmi a cikin matsin datake hadawa na kayan matanta tace"


Wannan halin daka dauka gwarama ka ajiyesa Dan Banga dalilin wani kasawa da tsarewaba,

Kasan bakason su kebe ka daura musu aure

To nidai kar gurin 'bare 'barenka ka fadamin kan saqe saqen Dana Shanya nayin tsimi.


Katseta yayi da cewa"


So kike insaka ido ya fake da aure tun yanxu ya lalatamin yarinya......


Laaaaaahhhhh haaa ilahh,dattiya daga maula Kuma sai saninka duk ya bace,

Ni talatu yau mezanji daga bakinka?

To kaga tun wuri ka aje wannan maganar Dan kuwa idan Zaki yagama warwarewa daga jimamin Rashin jabeeru yagano wannan abinda kake saqawa aransa game dashi to fa zaku komawa halin ne,


Shi baya ragar maka kaikuma baka riqe tsufanka

Amma Ina maganar an daura aure Kuma wata maganar bakason kebewarsu na fitowa.


Kallon takaici yamata cikin ciwon ran dabaisan yazaiyi dashiba yace"


Wlh nidai ancuceni,

To wlh bazan yarda na xuba ido inaji Ina gani nagama guje gujen gujewa hada iri da 'yan ta'adda ba nazo na qare da jika daga tsotson sarkin Yan ta'addanba,

Idan shi sarkine a dabancin me kike tunanin zaa haifarmin??sai Wanda zai rabani da qafafuwana Kinga ya qarasa aikinda ubansa bai qarasaba.


Kallon uku kwata ta masa tana qarawa 'dan matsinta gum tace"


Saika raba auren tunda bakason samun jika karkaxo ka ishemu da wannan leqe leqen.


Miqewa yayi Yana cewa"


Kibar zancen nan karna Kuma jinsa aure Kam dama ai rabasa zanyi Dana samo Mata mijinda baida tsoro ba kamar wancen lusarinba Bello.


Ficewa yayi daidai lokacinda zakin yafito bayi daga wanka Kuma dukkanin zancensu yaji ya girgiza Kai sbd takaicin zancen Wai shine zai tsaya lalata 'ya.


Qaramin tsaki yaja Yana ficewa daidai tana fitowa zata wanke hannu Babu ko dankwali akanta.


Cikin idanuwansa nata idanun Suka sauka ba zato.

#MAMUH*_BURI DAYA na kudine idan kanaso nemi wannan numbers din kabiya ka karanta cikin aminci_*


07067124863

08030811300


*_Mamuhgee14_*

saurin sauke Kai tayi tana qoqarin komawa fuska a daure yace"


Ke zo nan.


Muguwar faduwa gabanta yayi ta 'dan dago takallesa taga fuskarnan a tamke ba Wasa ya juya ya nufi dakinsa.


Hijabinta ta jawo tasaka jikinta na sanyi ga tsoro da fargaba fal cikin ranta

Ta juya ta kalli gefen da iya talatu ke zaune taga ko dagowa ta kalleta taqiyi ta wuce tabi bayansa qafafunta na 'dan daukar rawa sbd fargaba da tsoro gashi baba baya nan Dan kullum cikin Mata kashedin zuwa dakin zakin yake ko kebewa dashi.


Saidata wuce iya talatu ta dago tabi bayanta da kallo Dan tana kalle dasu tayi kamar batasan meke faruwa ba,


Dire robar hannunta tayi da Dan qarfi tana cewa"


Allah ma yasa yayi Mata ciki ko zamu samu masifarsa ta rage idan yaga Yana Shirin zama uba,idan Kuma rabon wahala ne ke jiranmu kamar yanda dattiya yafada Allah ya nesanta dashi Amma wlh masifa wlh Nima ta isheni duk wani tattalin arzikina kullum a karyewa yake sbd masifar Zaki da badan Allah yayini da farin jinin sana'ar samuba da tuni na kakkarye Babu sauran jarin da kuma tuni nabi bayan dattiya a yawon ta zubar dinsa.


Ita wlh ma ringa cusa masa Nadiya zata riqa Yi daga yau tunda dama ance duk iskancin mutum idan yayi aure Yana raguwa idan Kuma aka haifar masama dainawa yakeyi 

Sudai sunason Zaki ya daina ta'addanci ko zasu samu su shaqi iskan duniya hankali kwance duk da wani lokacin baqaramin dadi takejiba idan tafita duk anguwar dataje indai akwai yayan banza saisun taso sun gaidata ana cewa gwaggon sarki Zaki ce Saidai Kuma wlh tanason itada 'yan dabbobinta su sakata su Wala a gidan duk da dai tasan ba inda zasu a gidan zasu tare Amma dai zai daina Basu gwale gwale komadai yayane.Nadiya kuwa tana isa baqin qofar dakin dake soron gidan ta tsaya tsoronta na qaruwa takasa shiga sai fargabar kar babanta yazo yaganta anan din takeyi gashi ana hango ta waje tunda soro ne,


Kamar daga sama dattiya dake zaune taredasu mal idi dasu mal zailani a bakin masallaci yaga kamar idanuwansa na hango masa hijabi hijabi a soron gidan ya hadiye wani yawu qut da qarfi tareda miqewa Yana gyara zaman hularsa dake kife a kansa kamar ya zura kwano sbd batada wata karyewa ko Dan wani qarfin starch da hula kedashi.


Hankalinsa na soron gidansa yace"


Ina zuwa Bari na dubo wani Abu cikin gidan yanxu....


Ko gama Kai qarshen zancen baiyiba ya wuce Yana Dan sauri Dan kuwa idan har Nadiya ce zata shiga dakin Zaki dantaga bayanan dukan tashi Kisha gishiri zai Mata Dan wlh bazai yarda ya qare a 'yayan troway ba,

Ruqayya ta Haifa masa acema yanxu yarsa ta Haifa masa.


Aikuwa itace'"yafada Yana qaro sauri zai shigo tun daga wajen yake cewa"


Ke Nadiya karki Bari na iso na sameki gurin nan wlh dukan akuya zanmiki idan nasameki agurin wuce ciki maza maza.....


A tsorace ta juyo jin maganar babanta jikinta yasake daukar rawa ta juya da sauri zatayi cikin gida taji anriqe hannunta da wani irin hannu dayasa dukkanin jikinta zazzabi ya sauka Dan kuwa take rawar jikinta ta qaru.


Idanuwa cikeda hawaye ta juyo sukai ido biyu da Zaki daya riqeda hannunta jikinsa ba riga dagashi sai wani sabon three quarter Mai zanen sojoji ajikinsa daga gani baigama shiryawa.


Hawayen idonta ne Suka tsinke suna gangarowa sbd babanta.


Dattiya nashigowa soron afusace zaiyi mgn Zaki ya fizgota cikin dakin dama labulen dakin koyaushe a sake yake.


Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci dattiya baisan lokacinda ya banke labulen dakin ba zai shiga a masife.


Jawota cikin jikinsa Zaki yayi Wanda yasa kusan numfashinsu daukewa atare musamman sbd Babu riga ajikinsa gashi itama hijab din ta robace duk ta kwanta jikinta.


Kasa dagowa tayi sai qoqarin zamewa datakeyi jikinta na rawar tsoron abinda ke faruwa.


Shikuwa Zaki ko ajikinsa ya matseta cikin jikinsa tareda kallon dattiya dayayi mutuwar tsaye cikin Izza yabude baki yace"


Wlh taku 'daya idan ka qaro cikin dakin nan saina Mata abinda bakaso ayau din nan...


Wani irin zafi zuciyar dattiya taqara dauka cikin tsananin baqin ciki da fushi yace"


Naji to saketa tayi cikin gida.


Bai saketaba ya juya da ita jikinsa har bakin katifarsa ya saketa fuskar nan tamke ko kallonta bayayi yace"


Ke kwanta anan.


Juyowa yayi Yana fuskantar dattiya da idanuwansa sukai kamar ruwa sun ciko aciki ya nuna masa qofa da ido Yana Kai hannu kan zib din wandonsa kamar zai cire.....


Da sauri dattiya yafito dakin yayo cikin gida ko gani sosai bayayi yana kaiwa kusada talatu ya zube yayi zaman Yan bori tareda dafe Kai ransa na suya yace"


Wannan wace irin masiface ruqayya tasani aciki ta barni????


Uban waye baban Zaki Dan kuwa tabbas daga tsotson marasa kunya da mutunci yafito,


Wane kalar balaine nake ciki agabana wannan Dan yawon ta zubar din ke tabamin 'ya haryana cewa zaiyi....

sai yakasa fada ya juya zancen cikin fargabar abinda ke can Yana faruwa a dakin zakin yanxu,


Jiyake kamar yaje ya siyo maganin suma yasawa Zaki yayi suman wata biyu bai tashiba.


Itadai iya ko kallonsa batayiba taci gaba da aikinta tana cewa"


Allah yabamu jikoki masu qashin arziki da tagomashinsa tunda dai gashinan 'yayanmu Babu maishi saimu roqa daga jikoki.


Wani mugun kallon takaicinta yasako Mata tareda miqewa a fusace yayi ball da bokitin sauran tsiminta yawuce Yana zuba sabon masifa da kowa agidan.


Shimfida tabarma yayi a qofar dakin zainab ya zauna Yana mita Babu inda zashi saiyaga fitowar Nadiya Dan kuwa yau saiya karyata a gidan nan.Bai juyoba ya dauki rigarsa Mara hannu Mai hula yasaka tareda ficewa bataredama ya nuna tunawa da ita a dakinba,


Ahankali tasamu kuzarin sauke wani wahalallen numfashi bayan fitarsa,


Zamewa tayi qasa ta zauna tareda qanqame jikinta dake rawa har lokacin,

Tsananin kunyar babanta takeji kamar zata kasheta

Batasan ta Yayama zata iya kallonsaba yanxu.


Tunowa tayi da Yaya zakin saitaji kunyarta da tashin hankalinta ya ninku hartana sakin wani irin kukan Rashin sanin abinyi.


Shikuwa Yana fitowa sanin tana ciki yabada umarnin kar Wanda ya shiga dakinsa duk da damacan idan bashine ya aikesu basa shiga dakinsa.


Zama yayi cikinsu Suka hau ayyukansu harsaida alee dikko ya biyo ya daukesa tareda securities dinsa Suka fita shima yaransa Suka Mara musu baya cikin tasu motar.


Har aka fara Kiran magriba Bata fitoba nan hankalin dattiya yasake tashi Dan bai lurada fitar Zaki ba duk tunaninsa suna ciki.


Zuwa lokacin dukkanin jikinsa yagama yin sanyi Dan har wani mutuwa jikinsa yayi Dan kuwa yasan yanzu komai dayake gudu yariga yafaru Saidai Nadiya tayiwa kanta Dan batasan gatan dayake son mataba ta Shirin rabata da wannan auren qaddara dayakeyi.


Miqewa yayi daqyar jiki amace ya dauki buta ya nufi bayi Dan gabatarda alwalar magriba da aka gama Kira.


Yana fitowa bayi itama tana shigowa tsakar gidan a rarrabe da bango kanta a qasa takasa dagowa takalli ko dayansu sai hawaye dake gangaro Mata.


Da sauri talatu ta ajiye aikin daurin datakeyi tana yiwa nadiyar kallon tsaf kamar yanda dattiya yayi Mata kafin ya dauke Kai cikin ransa Yana tsinewa Lagos ma gabaki dayanta da Wainda ke ciki tunda acan uban Zaki yake,

Shi kenan Zaki yakaisa ya barosa.


Iya kuwa wata irin guda ta rangada tareda miqewa da sauri ta nufi nadiyar zata kamota tayo ciki da ita dattiya ya fizgo nadiyar cikin baqin ciki ya turata yace"


Ni mahaifinki naki dokar Rashin zuwa dakin wannan dangin Lagos din kika take maganata kika tafi sbd kin rainani Ni ban isaba ko???

To tunda haka kika zaba wlh kingama zama cikin gidannan ki koma can gurinsa na barmasa tunda ya koya Miki kalar rashin kunyarsa da Rashin mutuncinsa....


Saurin zubewa tayi qasa tana kuka tana girgiza Kai da qarfi.


Wani wawan Marin takaicinta ya sakar Mata yanajin radadin abin aransa Dan kuwa baiso rayuwarta ta wagarce a hakaba yaso taje gidan aurenta tayi rayuwar aure kamar kowa Amma wannan rayuwar da Zaki Babu wani rayuwar aure aciki tunda anan suke zaune agabansu za'a riqa Haifa musu jikoki Sam bai hango ta yanda zasuyi rayuwar aure anan ba.


Wannan abin ke cimasa Rai shiyasa yayita gudun faruwar hakan sbd za'ayita nunasa ana cewa acikin gidansa ake cikin jikokinsa aciki ake haihuwarsu aciki suke girma,ba wannan rayuwar yaso Mata...


Janta yayi da qarfi ransa na qara quna ya jehota soron gidan da qarfi daidai shigowarsa shikuma ba zato ta fado kirjinsa.


Kuka takeyi sosai sbd tsoron ganin fushin baban dabata taba ganiba tayi saurin barin jikinsa tareda durqushewa gefe tana kuka sosai.


Cikin bacin rai kawun ya kallesa ganin yanda yake qoqarin shigewa dakinsa ko kulasu yaqiyi kamar baiga meke faruwaba yace"


Ka Gama daure dauren fuskarka da izzarka ta banxa Wanda Babu ta inda ka gaji sarauta anan Saidai can a qasar dangin oduduwa

Wlh bazan zama wulaqantaccen mutumba dazai taraku agida ku ringa zubamin Rashin kunya ba.,


Gatanan dagayau tadawo dakinka gwara nasan ta tare zaman aure takeyi da in ajeta Ina zagayen banxa Kuna nuna Rashin kunyarku gwara ku qaratacan Kuma wlh kace bazata zauna a dakinkaba to ku tattara kubarmin gidana kuje can kusan nayi.....


Fara neman daburcewa yakeyi sbd fararen idanuwan da zakin ya kafesa dasu,


Fara rawar murya yayi ga fargaba ga bacin Rai yace"


Eh kadaiji abinda nafada bazaku maidani dattiyan banxaba.


Wani malalacin murmushi Zaki yayi tareda Dan kallon gefen nadiyar cikin ko in kula yace"


Ke tashi ki shiga ciki.


Kasa tashi tayi sai kukanta dake qaruwa.


Cikin tsawa yace"


Zan karya Miki qafa fa.


Miqewa tayi da sauri ta nufi cikin gidan dattiya ya daka Mata tsawa yace"


Wuce dakinsa ai daga yau kin tare zaman aure zakiyi tunda kin nuna kinshirya.


Kallonsa takeyi tana tsananta hawaye ta juyo ta nufi dakin zakin ta rakube bakin qofa.


Dogon tsaki yaja tareda nufar qofa Yana cewa"


Wlh andai cuceni Ni dattiya.


Shikuwa shiru yayi agurin tareda rintse idanu ya bude ya juya ya watsar Mata wani mugun kallo Yana cewa"


Zaki min shiru agurin kosaina karya wuyanki agurin.


Tsit tayi tareda qarasa shigewa bayan qofar.


Fasa shiga yayi ya fice shima Dan sallah.


Yana ficewa tayo cikin gidan Dan yin alwala itama tana share hawayenta dasukaqi tsayawa tana kallon iya talatu dataki saka baki a alamarin.

#mamuhh*_BURI DAYA na kudine idan baka biyaba ka nemi wannan numbers din ka biya ka karanta cikin aminci_*


07067124863

08031181300*_Mamuhgee15_*

Butarda baban yabari bayan alwalarsa ta qarasa ahankali ta dauka har lokacin hawaye take zubarwa


Ruwa ta qarasa jikin durum ta Diba tazo tashige bayi har lokacin idon iya talatu na kanta tana Mata kallon qurulla zuciyarta fal farin ciki Dan kuwa ganin take tafi kowa matsuwa da nadiyar tasamu ciki ko zakin zai shiryu su samu yanci itada tattalin arzikinta.


Itadai alwalarta takeyi cikin tsananin damuwa da tsoron yanda zatayi rayuwa a daki daya dashi.


Tana gamawa ta nufi dakinsu itada zainab tashiga tana qoqarin tayarda sallah baban yashigo gidan Yana qwala Kiran sunanta.


Saurin tayarda sallar tayi cikeda tsoron karyazo ya daketa duk da duka   ba dabiarsa bace iyakacinsa cika baki Saidai ganin yanda yau yaketa fada yasa takejin tsoron karya daketan.Ta Jima tana sallar kodata sallame qin fitowa tayi tana qoqarin gyara zama zainab tashigo dakin rataye da jaka ta ajiye tana kallonta tace"


Kije baba nakira yau fada yakeji Dan Nima yanzu yagama zubamin akan zuwa gidan anty nafisa.


Hawayentane ke qoqarin dawowa ta kalli bakin qofar tana sako hawayen kafin ta miqe jiki ba qwari ta fito tana share hawayenta.


Tun kafin ta iso gabansa yace"


Koma ki dauko jakar kayanki kixo ki fice gobe zansa asa muku hanjin gado da katifar Dana siya Miki ta aure.


Qoqarin durqusawa take gabansa alamar roqonsa ya daka Mata tsawa Yana cewa"


Maza wuce tun kafin na karya Miki qafafu Mara kunya,

Kinsan bakyason zama dakin nasa kika biye masa kuka gama nunamin iyakata dazu,


Dama nasan ni shikenan Banda sa'a tunda duniya babu Wanda yagama rainani sai mijin 'yata gashi yanzu kema rainanin zakiyi saura dabancin yarage yakoya Miki saiki hau gyarawa talatu zama kema Kinga zuwa gaba gidan zamu bar muku Dan kungama riqa a harkar ta'addancin,,,


Zaki miqe ki wuce ko saina mangare ki agurin.


Miqewa tayi jiki sanyaye ta juya ta nufi dakinsu,


Zainab da sai yanzu taji abinda ke faruwa tayi saurin jawota cikin dakin tareda 'dan mintsineta a gefen ciki tana 'yar dariya tace"


Iyye Nadiya Ashe yau tarewa za'ayi shine ko kifadamin nabada gudun mawar gyarawa Yaya Zaki amaryarsa.


Gudu hawayenta Suka qara tana qoqarin sunkuyar dakai zainab din tayi saurin tallafota tana cewa"


Ke meyene Kuma abin kuka anan?

Bari kiji wlh damace kika samu kiyi rayuwar dakikeso ta jin dadi 

Yanzufa kowa shakkarki zai riqaji amarya guda a gurin sarki Zaki....


Kallonta nadiyar tayi tareda harara tana 'dan turo baki zata juya ta dauko jakarta.


Sake riqota zainab tayi tana cewa"


Ke tsaya Mana kiji kokuwa duk matsuwar tarewarce bazaki tsaya kiji darasin riqe miji ba tunda iya talatu takasa baki Ni basaina bakiba..


Kinga Dan allah karkije kina masa wannan kwana da hijabin wlh shegen duka zai Miki ya qarasa kunnuwanki dakeji Dan kuwa lokacin JJ yace Sam Babu abinda Zaki ya tsana kamar dunkun dunkun mace..


Kallonta nadiyar tayi da sauri zuciyarta na harbawa..


Dariyar qeta zainab tayi ganin nadiyar tafara yarda da zancenta duk da qarya takeyi sai kawai tasake gyara tsayuwa tacigaba da cewa"


Yes Kuma Yaya Zaki ya tsani taurin Kai wannan ai kema kinsani basai na fada mikiba Dan kuwa kinfi kowa sanin ya sautin Marin Yaya Zaki yake...


Boye dariyarta tayi ganin tsoro qarara na bayyana tattareda nadiyar taci gaba da cewa"


Sai one last thing shine Yaya Zaki ya tsani qazanta duk da dai nasan ba laifi ke ba qazama bace Amma Dole Zaki ninka tsaftarki akan tada tunda kina gani wanka biyu ko uku Yaya Zaki keyi a yini Dan haka kina qazanta kinsan Babu Mai cetonki tunda kowa tsoronsa yakeyi har baba kina gani.,


Dan haka nidai Ina sonki 'yar uwata banason rasaki Dan allah ki kiyaye abinda nafada Miki wlh idan kika mutu rayuwarmu lalacewa zatayi...


Cikin sabon tsoro Nadiya ta fashe da wani sabon kukan tausayin kanta akan abubuwan da zainab tafada Mata wlh itama batason ta mutu yanxu.


A boye zainab tasaki dariyarta ganin ta Dora nadiyar sosai saita daga hannuwanta tana share Mata hawaye tace"


Daina kuka kinji nadiyata idan kin kiyaye Babu abinda zai faru Barima nabaki turare har biyu Wanda Zaki ringa sawa idan kikayi wanka hakan zai qara tabbatarda tsaftarki gurinsa.


Jakarta ta bude ta dauko spray din smart collection na Lacoste tabata da madarar turaren lamsa Mai Dan yawa kadan.


Karba tayi hannuwanta na rawa kafin ta jawo jakar kayanta tasaka 

Zainab din ta daukar Mata jakar Suka fito sum sum kamar munafuka tabi bayan zainab din har qofar dakinsa Suka shiga sbd sanin baya nan.


Wata muguwar harara dattiya yabi bayansu da ita har Suka shige yanajin kamar yace yafasa tadawo tunda ai ba lallaine kebewarsu so daya ace tasamu cikiba.


Ciki mamakinsa da 'dan takaici iya talatu data sallame sallah tace"


Todai karkace tadawo Naga kanata kallon qofar soron kamar kaga kudi agurin 

Kariga kace ta tafi to wlh idan kace tadawo shiyasa Sam bakada qima a idon zakin baida marainin wayo kamarka.


Tsoki yaja cikin quluwa yace"


Wai ke talatu kullum bakya iya zama baki gasamin baqar magana ba,

Yanzu 'dan kanwar tawa kike cewa Banda qima a idonsa saikace wasu 'yan bariki.


Au dama kanada qima a idonsa shiyasa yake sakar maka karensa ko yaransa suna neman zauta rayuwarka.


Eh naji koma meyamin Ina ruwanki inace kece kika qarasa zugani na Hana auren ruqayya da neyo hartaje garin dangin oduduwa tasamo Mana wannan din.


Zatai magana ya miqe ya fice Yana baza babbar rigarsa ransa duk jagule.Sukuwa suna shiga dakin zainab da Bata taba shigowaba tahau kallon dakin tsaf dashi kamar baa cikin gidansuba,


Qatuwar katifa ce Mai tudu sosai adakin sai 'yar wardrobe qarama ta kayan sawarsa Dana JJ sai takalmansa a jere gefe sai wata cupboard dake cike jereda makamai su adda,wuqaqe da gariyo masu matuqar ha'dari da kaifi.


Tsakiyar dakin kuwa dama carpet ce ash shimfide.


Komai na dakin fes yake kamar dai JJ nanan.


Jikin wardrobe zainab ta ajiye jakar kayan nadiyar tana kallon dakin tanajin Ina itace zata dawo nan wlh dataji dadi gashi harda standing rechargable fan a dakin.


Bakin katifar taje ta zauna tana latsawa tace"


Wayyo Nadiya wlh karki Bari kiyi laifinda Yaya sarki zai koreki daga dakin nan.


Dauke Kai Nadiya tayi idanuwanta na sake cikowa da hawaye

Zainab tayi saurin tasowa tana cewa"


Karkima fara wannan hawayen sbd baba yagama Miki gata yarinya.


Yanzu dai muje muci abincin dare saikiyo wanka kidawo ki kwanta cikin wannan qatuwar lafiyayyar katifar wayyo allah inama nice gefe daya ga Yaya Zaki da wannan lafiyayyan jikin nasa daga gani zaiyi laushi......


Saurin matsawa Nadiya tayi daga gefenta tana girgiza Kai cikin tsananin kunya da tsoron zancen na zainab.


Itakuwa dariya tayi Kuma har cikin ranta take wannan zancen tasan wlh Yaya Zaki ba qaramin iya soyayya zaiyiba sbd wannan Jan ajin nasa da kwarjinsa.


Bude jakar sukayi suka cire kayan dau'da sukayi cikin gida dasu da niyar gobe tayi wankinsu.


Indomin da zainab tashigo da ita guda biyu super pack ita zainab din ta dafa sukaci sbd Babu wani abincin dare da akayi ko na ranama ba ayiba sauran biredin da zainab tarage da safe dama taci da ranar.


Bata wani ci indomin ba sbd gabaki daya a tsorace take ga wani irin bugawa da kirjinta keyi na yanda yau din zata kasance Mata duk da tasan ko kallon tsiya bazai bita dashiba bare na arziki.


Suna gamawa ta rafka sabon tagumi batada alamar tashi 

Zainab ta takurata ta hanyar Bata tsoro da zantukan qarya harta sata tayi wanka ta saka doguwar jallabiyarta ta bacci ta saka hijabinta taje har daki tayiwa iya talatu Saida safe a matuqar kunyace.


Wani Abu iya ta miqowa zainba tace"


Ungo Bata wannan kice tashanyefa yanzu agabanki.....


Cikin fushi dattiya daya kawo ya miqa hannu ya karbe tareda watsawa zainab mugun kallo yace"


Bar nan kafin na fasa Miki Kai.


Da sauri ta fito tana dariyarsa sbd ganin yanda fushi bayawa baban nasu kyau ko kadan.


Ita kadai takoma dakin tashiga kamar munafuka tana sunkuyar dakai duk da har lokacin baidawoba.


Qasa ta zauna bayan tayi sallar ishai da akayi tun suna cin indomie,


Shiru tayi tana qanqame jikinta dake tsananin rawa sbd fargaba da tsoron karyazo yamata dukan ganinta a dakinsa.


Ahankali lokaci yaja harta fara gyangyadi daga zaunen saitaji motsin ana rufe qofar gidan.


Wani mugun zufan tsoro da fargaba ne ya karyo mata ta sake qanqame jikinta tareda cusa Kai cikin qafafunta.


Yana waya da wani officer akan wasu yaransa da aka kama a wani gari yashigo da wata irin sallama can qasan maqoshinsa.


Tsakiyar dakin ya tsaya tareda yimata kallo daya ya dauke Kai sbd shaf ya manta ma da zancenta.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee16_*

Maganar yaji kamar tafara isarsa ya datse Kiran tareda sakin qaramin tsaki Yana jefa wayar kan katifarsa sbd jin yafarajin haushin komaima Dan sai yanzu ne ransa ke baci da alamarin danshi bai zata kawun da gaske yakeba ya dauka duk cikin borinsa ne dayakeyi idan yatashi abinsa yanzu Banda raini uban me wannan yarinyar zatayi a dakinsa Banda ganin makwancinsa mitssss.


Gaban wardrobe ya nufa ya tsaya tareda zare shirt din jikinsa take qaqqarfan surarsa qirjinsa ya bayyana wasu irin damtsen hannuwansa dake murde Suka kayar Mata da gaba tasake cusa kanta cikin qafarta tana sakeyi kamar tayi bacci.


Jin bai tareda gajiya ko kadan yasa baiyi tunanin wankaba sbd dare yayi Dan kuwa tunda yafita suna wata ma'aikatar kudi tareda dikko wadda yabude a boye ana buga masa kudin bugi na billions of naira.


Acan suke duk yinin ranar sbd ma 'aikatar can take cikin daji Kuma dama duk sukaje yaransane ke zagaye dajin da mugayen makamai suna gadi harsai sun fito shiyasa dikko ke qara jin Zaki Dan kuwa tsaronda Zaki da yaransa ke basa ko hukuma dayake sakarwa manyan daloli basa basa wannan tsaron gashi Sam basa tsoro duk wani Abu dazai Sha gabansu fitt suke Gama masa aiki.


Kai tsaye katifa ya nufa yahau ya kwanta tareda rufe jikinsa da bargo ya lumshe fararen idanuwansa ahankali Yana sauke numfashi.


Jin shiru bayan Yan mintuna saita dago kanta ahankali ta juyo ta kallesa taga yayi bacci batasan lokacinda ta lumshe manyan idanuwanta ba tareda sakin ajiyar zuciya sbd tsoronta daya 'dan rage.


Zamewa tayi tayi kwanciyarta a qasan tareda sake Jan hijabin jikinta ta rufe qafafunta sbd 'dan sanyi da akeyi.


Ahankali tayi baccinta bayan tayi addua saidai kusan baccin nata rabi da Rabi ne saiyi takeyi tana zabura sbd tsananin tsoro data sawa kanta na kartayi bacci sosai tayi wani laifin Bata saniba.


Asubar farko ya farka kamar ko yaushe ya tashi zaune kan katifa tsawon mintuna yagama jinsa yayi daidai kafin ya zuro qafafunsa zai tashi yaji ya taka mutum.


Cikin wani irin fitinannen tsoro da firgita ta zabura jin mutum ya takata cikin bacci 

Shima cikeda mamaki ya lalaubo wuqa qarqashin pillonsa yakai hannu inda yaji mutum din zai damqo koma waye cikin Rashin sa'a ita Kuma ta zaburo kenan hannunsa ya sauka kan qirjinta gashi Bata kwana Sam da breezier.


Wani irin shock sukaji lokaci daya tayi baya da qarfi cikin tsananin firgici tana neman hanyar guduwa jikin na wani irin mugun rawa sbd tsananin firgicewar datayi Sam kamar kb ne takejin yadawo ta manta a inda take.


Jin tana neman qofa cikin duhu a firgice zata fita yasa yayi saurin fizgota ta dawo jikinsa Dan shima farko Sam ya manta da akwai wata a dakin ya dauka wanine yashigo masa.


Sosai jikinta ke rawa tana fixge fixge tana bude baki yagane ta fice hayyacinta sbd tsananin tsoro da firgita Wanda yawanci indai antaba attempting rape naka to kana iya shiga irin wannan firgicin wasu lokutan,


Riqota yayi da kyau tareda girgizata Amma Sam ta fita hayyacinta da qarfi yasake jijjiga tareda kiran sunanta akaro na farko rayuwarsa tun girmansa sai kawai gani yayi ta sulale ajikinsa some.


What?yafada cikin 'dan takaici da bacin Rai Yana qaramin tsoki kafin yasake jijjigata yaga ta sake sakemasa ajiki.


Saida yakuma sakin qaramin tsaki kafin ya dauketa gaba 'dayanta ya kwantar a katifar kafin ya lalubi wayarsa ya kunnu fitila ya haskata.


Gabaki daya rigarta a cinyoyinta take shi hijab dinta kuwa gurin furgicinta ya cire,


Dauke Kai yayi tareda sake sakin siririn tsakin takaicin wannan kayan takaicin da aka kawo masa.


Juyawarsa yayi ya fice Dan zuwa alawalar zuwa sallar asuba daza'a tayar lokacin.


Cikin gidan yashiga ya dauki buta yacika da ruwa ya nufi bayi.


Yana fitowa aka dallesa da fitila Mai shegen haske.


Kallon daya kawun daya kasa bacci yayi masa ya dauke Kai ganin Babu riga ajikinsa sai kawai yaji kamar yaje masallaci ya zauna yayita rusa kuka ana ja masa ayoyin alqur'ani kozaiji sanyin abinda yakeji aransa.


Shikuwa ko kallon inda kawun yake baiyiba yayi alwalarsa ya wuce Dan yasan Sarai ubanda kawun yafito tsinta da asubar farin sbd ko sallar asuba kawun bai cika fitawoba Amma yanzu saboda tsabar yayi abin yasha masa Kai shine yafito ga dukkanin alama ko bacci baisamu yiba aikuwa wlh inda hakane daga yanzu yaringa sashi fitowar asuba Dole Dan kuwa baisake fitowa da riga da asuba saiya saka masa 'dan qaramin hawan jini.


Dakin yashigo ya saka doguwar jallabiya fara qal ta Sallah ya fice zuwa masallaci batareda yakalli ko gefen katifarba.


A masallaci tunda dattiya yashigo yake hararar gefenda zakin yake Yana babbata Rai har aka fito.


Koda yafito masallaci Saida ya tsaya qoafar gida ya kwankwasa qaton shagonda yaransa ke cike taf suna bacci yace su tashi suyi sallah.


Yana shiga dakin tana bude idanuwanta ahankali.


Kallo daya tayi masa ta tuno abinda yafaru ta miqe da sauri tareda kallon jikinta taga batada hijab gashi yariga yashigo dakin sai kawai tayi qasa da Kai tafara tsiyayo hawaye.


Wata irin tsawa ya daka Mata cikin Isa yace"


Zaki tashi kiyi sallah ne ko saina karya wuyanki a gurin.


Da sauri ta zabura ya sauko katifar jikinta na mugun rawa kanta a qasa  ko hijab Bata tsaya daukaba ta fito alwala gashi lokacin gari yayi haske sosai.


Da babanta tafara cin karo a tsakar gidan ya kasa ya tsare a qofar dakinsa yayi shimfida duk sanyin safiyar bayaji sai radio daya kunna yakai murya qololuwa duk ya Hana mutan gidan bacci da labaran bbc Wanda shima ko zaa kashesa a gurin baisan me suke fadaba and signal din Babu kyau duk hayaniyar zizar radio ne.


Kallo daya yamata yayi saurin dauke Kai Yana qarawa radionsa murya kansa a sama alamar duk ubanda ya tabosa alokacin masifarsa zai sauke masa.


Sum sum ta qaraso ta dauki buta ta Debi ruwa ta shige bayi ko kallon baban takasayi sbd tsoro da kunya.


Tun acikin bayin tayo alwalarta shiyasa ko data fito butar kawai ta aje ta wuce yabi bayanta da muguwar harara.


Da sallama muryarta na rawa ta shiga dakin 

Amatuqar gigice tayi saurin sauke idonta akansa jikinta da zuciyarta na sake daukar rawa har qafafunta Saida Suka fara hardewa ganin dukkanin qaqqarfan jikinsa a bayyane.


Push-up yakeyi na motsa jikin safe daya Saba safiyar kowace Rana

Dagashi sai three quarter na wandon Adidas 

Bayansa dake fari sol sai kyallin 'yan qananun zufa yakeyi.


Rakubewa gefe tayi tana matse jikinta harta qarasa gurinda hijabinta yake ta dauka tasaka ta sake matsawa gefe ta tayarda sallah.


Harta gama sallar bai gamaba saima wasu qarafuna masu nauyi dataga ya dauko Yana dagawa a hannunsa.


Miqewa tayi a hankali ta nufi qofa zata fita kamar daga sama taji muryarsa yace"


Idan kika bude qofar dakin nan saina karya wainnan shegun qafafun naki.


Cak ta tsaya tsoronta na qaruwa ta dawo batareda ta dago ta kalli inda yakeba Takoma inda ta kwanta jiya ta zauna tareda kwantarda kanta kan gwiwoyinta gabanta na tsananta faduwa.Duk wani motsa jikinsa Saida ya gama zuwa lokacin ya hada zufa sosai sai kawai ya dauki towel da brush ya fito.


Kai tsaye cikin gidan yashiga har lokacin Dattiya na zaune sai iya data fito tana Shanya garinta dabai Gama bushewaba jiya.


Wani mugun kallo dattiya yabi jikin zakin dake tsiyayar zufa ga farar fatarsa ta asalin Igbo sai daukar ido takeyi musamman shi zakin da Sam baisan wahalaba.


Ji yayi kamar idonsa zai kawo ruwan baqin ciki saikuma ya dake Yana tsuke fuska aransa Yana cewa"


Wlh wannan basamuden kashemin yarinya zaiyi da sunan aure tunda ba wani qwari daukar lalurarsa tayiba Amma Koma meyene laifin idi ne dabai basa shawarar qin hada wannan aure ba.


Kashe radionsa yayi ya miqe ya fice a fusace


Ko gaisuwarda zakin yamasa ta can qasan maqoshi bai amsaba.


Ruwan brush ya Diba yafito qofar gida inda masarautarsa ke cike da yaransa sunata faman gyara makamansu.


Nan yazo ya zauna nanu ya qaraso Yana gaishesa sbd yanxu shine mafi kusansa.


Sama sama yake 'dan fira da yaransa sbd har cikin ransa yakeson dukkanin yaransa dasuke qarqashin sa suma shiyasa suke matuqar qaunarsa da kiyaye masa Dan duk cikinsu Babu Wanda ba 'dan gani kashenin zakin ba.


Ita kuwa daga zaune tasake bingirewa da wani sabon baccin safenda rabonta dashi harta manta batamasan ya dadin baccin safen yakeba tunda batayi.


Tana bacci yashigo haryayo wanka yazo ya shirya ya fita.


Cikin bacci taji ana buga qofar dakin ta bude ido ahankali ta tashi zaune da sauri taji ansake buga qofar ta miqe tareda gyara hijabinta ta nufi qofar ta bude.


Nanu tagani tsaye tayi saurin sauke Kai cikeda tsananin kunya.


Cikin sakewar fuska da girmamawa yace"


Gashi akace akawo Miki.


Hannunta na rawa ta miqa ta karba har lokacin takasa dagowa.


Juyawa yayi ya fice itakuma takoma ciki ta aje ledar ta dauki brush tayi cikin gida neman Maclean wurin zainab.


Rana ta fito sosai shiyasa kodatashiga da zainab da iya duk suna tsakar gidan zainab na waya iya kuwa tanata ayukan sana'arta tana hadawa da mitar Rashin fitowar nadiyar ta tayata ayyuka.


Aje waya zainab tayi da sauri tayo gurin nadiyar sukai cikin daki tana tsokanarta akaro na farko saita samu kanta dayin murmushi Wanda yasa zainab sakin ihu da qarfi tana tsalle.


Abin saiya sake saka Nadiya murmushi ta qarasa da sauri ta dibi Maclean din ta fito zainab din na sake biyota.


Brush tayi tana gamawa taxo gurin iya talatu tai Mata alamar gaisuwa 


Iya talatu ta bita da ido ganin sai sunkuyar dakai takeyi itama sai abin yabata dariya tace"


Nadiya karma ki kuskura kice wannan soke soken kan zakimin na kunya acikin gidan nan jeki ki karya kixo ga ayyuka nan sunyi yawa.


Tareda zainab Suka koma dakin ta ajiye brush dinta kafin ta juyo zainab ta bude ledarda Nanu yakawo tana zuba wani ihun jin dadi tana cewa"


Wayyo wlh har yunwata ta qaru

Yaya zakine ya siyomiki wannan dadin da safiyar fari.


Take away ne guda biyu 

Na chips da kwai sai na source din hanta dataji cabbage.

#MAMUH*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee17_*

Cikin farin ciki zainab din tadauki daya takai baki tana cewa"


Shikenan wlh Nadiya cikin wata daya Zaki canxa ki baje abunki hankalin baba yasake tashi.


Girgiza Kai kawai nadiyar tayi Dan itama tayi mamakin wannan cimar tsawon rayuwarta Bata taba cin dadi irin wannan ba har gwara kaza iya talatu wani lokacin idan taso cin dadi takan yanka cikin kajinta ta soya su ci.


Cikin gida suka koma da abincin acan sukaci tareda iya talatu dake faman zuba sanyin dadin hantar.


Lemun exotic dinda ke ciki ma dayake babba ne shiya qarasa cika cikinsu.


Suna cikin hakan dattiya yashigo ya waro ido ganin abinda ke gabansu 

Butarda ke gabansa yayi shuri da ita zai wuce

Iya talatu ta kalli zainab tace"


Kinga daukemin buta ta ba ita ta kar zomon ba.


Nadiya kuwa ganin irin kallon dayake watso Mata yasa ta miqe ta wanke hannu tahau aikin gidan.


Dayake tanason gamawa da taje ta gyaro dakinsa shiyasa take aikin da sauri harta gama ta nufi dakin tafara da gyare katifar tsaf ta goge komai tayi shara tareda fesa turaren dakin data gani ajiye takoma cikin gida Dan wanke kayanta.


Sai azahar ta Gama wankin Dan hardana iya talatu dama itake Mata wankin kayanta.


Tana gamawa tayo wanka tasanya doguwar rigar atamta cikin kayan da JJ yayi Mata na biki wancan lokacin ta fesa spray kawai tayi sallah ta kwanta a gurin sbd can cikin gidan tsit yake zainab batanan baba kuwa antafi sana'ar iya talatu ma ta fita dama haka rayuwar gidan take so da dama ita kaidaice ke yini gidan.


Tana kwancen taji buga qofa ta miqe da sauri Dan tasan qila shine yadawo.


Jin an Kuma bugawa yasa ta taso ta bude taga Nanu ne yanxuma.


Wata ledar yakuma miqa Mata tareda babbar ledar ruwan pure water ya wuce Dan sauri yakeyi daga gani.


Karba tayi tadawo cikin dakin ta zauna bayan ta ginginar da ledar ruwan,


Ta Dade zaune kafin ta bude ledar wani take away din ne

Tabude taga shinkaface soyayya da cabbage sai nama daga gefe sai spoon din roba.


Plate din dakin ta dauko ta zuba abincin kadan aciki ta rufe sauran tafaraci sbd Sam batada wani cin abinci sakamakon hanjinta yunwa tagama nade matasu tuntuni Dan bako yaushe ake abinci agidan ba.


Tana gamawa ta fita da plate din ta wanke tadawo dashi taje ta kwaso shanyar kayanta tareda yin alwalar la'asar da akayi tanacin abinci.


Saidatayi sallah tagama kafin tafara nade kayanta ta saka cikin jaka tasake share dakin tayi cikin gida sbd lokacin iya tadawo.


Siyayyar kayan hadin su tsimi da garintane na Mata nan Suka hau aikinsu iya na kallonta tana mamakin Wai a kwana daya da yini daya harta fara ganin kamar nadiyar ta 'dan canza sbd wani nustuwa dataga kamar tasake shigarta ita sai yanzumane take Mata kama da amaren.


Suna cikin aiki maraice sosai saigashi yashigo cikin gidan da alama yadan Jima da dawowa Bata saniba.


Towel da basket din wankansa datagani a hannunsa yasa tasan wanka zaiyi dayake ta Saba da wannan tun da can sai bataji komaiba ta miqe taje ta dauki bokiti ta Debi ruwa taje takai masa har cikin bayin tana fitowa zai shigo ta rabe harya shigo saitayi saurin ficewa.


Dawowa tayi Suka cigaba da aikinsu tana qara sauri sbd magriba da aka kusa Kira.


Sai bayan anma fito sallar magriba Suka gama bayan tasake kakkamta tsakar gidan tawuce tayo wanka tareda alwala tasaka wata doguwar rigar plain yadi Mara nauyi ta fesa spray ta tayarda sallah.


Tana cikin sallar yashigo daukeda qatuwar ledar kayan tea da bread sai wata ledar takeaway din na indomie da soyayyan kwai sai yoghurts.


Ajewa yayi tareda zama bakin katifa Yana waya kamar cikin izza.


Tana gamawa ta lanqwashe qafafunta tareda yin qasa da Kai tana kallon yatsun qafarta tana qoqarin Dan rage rawar da jkinta keyi.


Batareda ya kashe wayarba yace"


Ke zubamin abinci a plate dincan.


Tashi tayi a natse ta dauko plate din da spoon tadawo gabansa hannunta na Dan rawa ta bude takeaway daya ta zuba masa indomin tareda aje masa agabansa.


Saukowa yayi Yana cigaba da wayar yafara cin abincin hankalinsa kwance kamar wani wani sarki.


Sauran wadda Bata zuba masa ba ta zauna tafara ci ahankali itama batareda ta bude wani takeaway dinba sbd kota bude bazata iya cinyewaba.


Harya Gama waya yakeyi akan wata motar dikko da aka kama da yaransa aciki.


Tana gamawa ta dauki plate din da takeaway din ta fice dasu.


Dakin iya talatu ta nufa sbd tana jiyo muryoyinsu acan Dan akwai nepa.


Take away din indomin dabata fasaba ta miqawa zainab ta fito tareda wanke plate din Takoma.


Ajewa tayi tareda sake tattare gurin ta dauke ledar kayan tea din ta ajiye gefenda taga ana jere kayan tea.


Zaman shiru tayi har akayi Kiran ishai ya fice.


Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikeda tausayin kanta da irin rayuwar dazatayi ta kadaici sabo.


Tanayin sallar ishai gayi kwanciyarta a gurin Bata wani jimaba bacci ya dauketa.


Koda yashigo qarfe goma takusa ko inda take bai kallaba ya tube ya kwanta Dan dama shi baya kwanciya da riga damunsa takeyi.


Da asuba daya tashi yana miqewa yaji mutum a gabansa da sauri itama tayi saurin tashi zaune hartana buge qafarsa dayake bai tsaya daidaiba saiya fado kanta gabaki daya.


Wani irin zaburowa tayi hakan yasa qirjinta ya hadu sosai da nasa Wanda yasa numfashinsa tsayawa na wucin gadi yayi jarumtar miqewa da sauri Yana qoqarin tamke fuskarsa cikin duhun ya kunna wutar dakin sbd har asubar akwai nepa.


Haske na gauraye dakin tafara gyara rigarta da sauri tana saka hijabinta.


Fuska a tamke ya fice batareda ko sake kallonta ba.


Yauma Ras ya tararda kawun a tsakar gida riqeda buta yama kasa alwalar.


Ta gabansa yashige bayin sbd qara manna masa hauka tundaga cikin bayin yayo alwala danma kawun ya dauka wanka yayo.


Yana fitowa yawuce baice masa qalaba.


Itama fitowa tayi tayi alwala lokacin kawu yafice masallaci shima.


Kodata idarda sallah kwantawa tayi agurin tana karatun alqur'ani cikin ranta ahaka bacci yasake dauketa.


Shima Yana dawowa komawa yayi ya kwanta sbd Yana buqatar hutu yau.


Sosai sukayi bacci harsaida goma ta gota ita tafara farkawa tayi saurin miqewa sbd buga daki da akayi.


Gyara hijab dinta tayi ta nufi qofar zata bude kamar daga sama cikin muryarsa data qara girma sbd bacci taji yace"


Idan kika bude qofar nan saina karya hannuwanki.


Juyowa tayi da sauri sbd atunaninta bacci yakeyi.


Still idanunwansa a rufe suke tayi baya ahankali tadawo Saidai Bata zaunaba.


Tashi yayi ya sauko ya nufi qofar ya bude.


Nanu ne ya gaidasa cikeda basa girma ya miqa masa Dan madaidaicin flask na ruwan zafi Yana cewa"


Sarki yau Dan Tani zubawa ruwan shayinsa suka kafin a amso ammasa afuwa sbd mantawa yayi shine fa Saida aka Kira ya dafa maka wannan Mara sugan.


Karba yayi tareda bude baki yace"


Ka Debi yara kuje ku tarbi motocin alee dikko dazasu shigo ta dajin bayan gari karku Bari jami'ai su San dashigowar motocin yau Ina hutu kafadawa Wainda za'a Bari banason hayaniya Kuma akwai wani Dan kasuwa dake barraj shago na shida jiya daya sakarwa su kawu kare daga sunje gurinsa kafin ku wuce kuje kuyiwa arzikinsa kariyarda gyaranta sai Allah. 


Kawu daya kawo yaji abinda yafada ko kallonsu baiyiba ya wuce ciki Yana cewa"


Shi wannan duk qarfinsa bai ishesaba sai yahada Dana Rashin Shan suga Dan kawai ya kashemin 'ya nayi mgana yace zaiyi magani na,


Shikuma alhajin kwatano yau zaisan ya tabo dangin Zaki indai zakine hasararda zai goga masa saiya gwammace baizo cirani Nigeria ba Dan dama tun Yana yaro ba'a taba 'yan gidan shikadai yafiso yayita cin uwarsu basuda maceci sai allah.


Koda yashigo aje flask din yayi yafice yayi brush yadawo yadauki kayan wankansa ya fice.


Ita taje takai masa ruwan wanka tadawo tafara gyaran dakin.


Fes tagyara koina ta gyare shimfidarsa tayi shara.


Yana shigowa ta fita taje tahau gyaran tsakar gidan tadawo ta tararda yasha tea harya koma ya kwanta.


Sauran Wanda yabari Tasha ta tattare gurin tafito Dan taya zainab wankin dataga ta fitar tanayi.


Sai azahar Suka gama tayo wanka a dakin zainab ta shirya zainab harda shafa Mata jambaki daqyar ta iya zuwa tadauki kayan sawa tadawo cikin dakin zainab ta shirya Takoma can tayi sallah lokacin yafita sallah azahar masallaci.Da abincin Rana yashigo Mata wannan karon sakwara ce da Miya anan ta zauna taci sbd sanin bayason dogon iyayi shiyasa taketa taka tsantsan kartayi laifi ya kakkaryata kamar yanda yake fada.


Da daddare ma yau indomi sukaci Suka kwanta Amma saidata Dade gurin zainba ta rage dare kafin tashigo ta kwanta.Ahankali lokacin yafara ja yanzu kusan satinta cikin na uku da tarewa dakin tuni harta Saba da rayuwar shirun dasukeyi sai Kuma hakan yasa fargabarta ta ragu sosai Saidai tsoronsa dayake daram cikin ranta.


Cinta da shanta ya canza gabaki daya sbd cimar datake ci yanzu safe Rana dare harya zamto yanzuma itace ke kawo musu abinci cikin gidan Dan kuwa sosai su iya talatu ke Jan gararsu 

Babanma dayaga dai cutar yawa zatai masa idan ankawo wani lokacin shike karbewa ya cinye ya hanasu Yana cewa ai kullum suke ci yaudai rabonsa ne shikadai.


Lurada Bata iyaci Bata bawa babanta ba yasa kawai yayo siyayyar abinci jibgi guda yasiyo da gaton risho yasa su Nanu Suka kawo.


Buhun shinkafa 'daya da katon din macaroni da spaghetti sai galan na mangyada da manja saisu tarkacen magi dasu ashana harma dadu omo da sabulai.


Sosai iya talatu ta bude baki da hanci tana kallon kayan abincin lokacinda ake shiga dasu dakinsa ta sake numfashi Mai shegen qarfi tana kallon dattiya dake shigowa gidan Yana waiwayen soron gidan da ake shigoda kayan saura kadan yafada cikin durum din ruwa Saida talatu ta riqo rigarsa tana cewa"


Yi ahankali karka karye mu cinye kayan kana kwance.


Fixge rigarsa yayi Yana Mata mugun kallo yace"


Ke Kuma shine baqin cikinki kar aci kayan Dani,

To inagadai ai badan niba da bazaki ciba kema tunda dabanyi masa aurenba zaisiyone yakawo harkici din ke me bakin cin.


Au yanxu Kuma alfaharin auren kakeyi sbd ganin buhun 'yar gote.,

To mudai Kam ai dama munsan arziki yanxu zamu fara cinsa duk uwar dukuyarda dikko ke loda masa yanxu Kam ci zamuyi musamman Ni.....


Ke banason zaqewa talatu wlh ki kiyaye ni.


Kallonsu zainab tayi cikin takaici tace"


Dan Allah baba karku fara fada tun yanxu akan arzikinda ko samunsa baayiba tukuna.

#MAMUH*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*_Mamuhgee18_*

Fusgar iska yayi ya sake ficewa Yana hura hanci duk da cikin ransa yaji Dan dama dama na ganin gararda zai fara kwasa a kwanakin musamman ma da idanuwansa Suka qyallo masa kiret din kwai da doya da dankalin turawa jiyayi wata Yar dariya na neman subuce masa ya dauke Kai tareda tamke fuska ya fice Yana cewa"


Wannan Yar baqin cikin batason naci wannan kayan ai wlh Saidai kowa ya rasa muguwar tsohuwa.


Cikin dakin Suka shigarda abincin suka jera inda yace a ajiye Suka fice.


Harta rufo dakin zata shiga cikin gida Nanu yadawo riqeda wata ledar ya miqa Mata yace"


Sarki yace kiyi abinci.


Karba tayi tayo cikin gida zainab tayi saurin karbar ledar tareda budewa ta zaro ido ganin Naman kajine masu qanqara da kayan Miya.


Wata gudar jin dadi iya talatu tasaki tareda miqewa ta sauke tukunyar tuwon gari datayi niyar dafawa tana cewa"


Yau dau allah yayi wahalata taqare zanfaraci daga Zaki Kuma daga 'yaya.


Itadai Nadiya Babu wani dogon farin ciki ko murna atareda ita sbd tsoron karta dafa tayi masa ba daidaiba dukda dai ta iya girki sosai tunda itakeyi na gidan tun batai hakaba.


Jiki sanyaye tafara wanke kayan miyar da Naman

 zainab kuma ta hada rishon tazuba kalanzir da aka kawo dashi cikeda galan.


Iya talatu daki tashiga ta dauko Mata tukunyoyinta guda biyu sabbi data siya Mata na aurenta da Bello dabaayiba ta miqa Mata tareda kula Mai guda uku da plate biyu sai Kofi uku da cokali biyar duka sabbi Saidai bawai masu tsada bane kawai dai Babu laifi.


Zainab ba wata gwanar aiki bace Saidai fira datake taya nadiyar dashi harta gama abincin,


Tuwo tayi na shinkafa da miyar busashen ku6ewa dataji Naman kajin gidan har wani qamshi yakeyi har maqota 

Dattiya daya fesawa idi Suka kasa Suka tsare a majalisarsu ta dattijan anguwa suna jiran dare yayi suje suci banza Dan kuwa shima idi cewa yayi wlh daga yau tareda dattiyan zasu riqa ci tunda ai tare sukeshan wuyarsa idan yatashi Rashin mutuncinsa akansu.


A sabuwar kula zainab ta dibarwa zakin komai aka goge aka Kai masa daki tareda plates din da sabbin cups dinta.


Iya talatu harna dumame ta Diba a qaton kwanonta tashigewarta daki.


Babansu ma cika masa wata tsohuwar kula sukayi kafin Suka zauna sukaci nasu zainab tabar gurin

Itakuma ta dauki rushon tashigar tsohon dakinta tareda galan din keron ta fito ta tattara gurin ta share gidan tas Takoma ta sharo dakinsu tazo tadibi ruwa tashiga wanka.


Tana fitowa tayi alwala ta nufi daki.


Komai Bata shafaba bayan spray dinda ya siyo Mata Wanda shima yakusa qarewa ta saka bra saita maida zaninta iya qugu tafara neman rigarda zata saka sai kawai taji shigowarsa gashi akwai nepa.


A rikice ta miqe tsaye jikinta na rawa sbd tsananin kunya da fargabar yanda take din.


Aka bra dinta data 'dan yi Mata kadan qirjinta sun fito ta gaban idanuwansa Suka sauka atake ya dauke Kai Yana daure fuska musamman dayaji maqoshinsa yawu na neman qin wucewa.


Hijab ta fizga da sauri tasaka tareda durqusawa ta dauki rigar dake Daman kayanta kawai tafara qoqarin zurawa.


Zama yayi bakin katifata tareda kunna wayarsa Yana latsawa sai kawai yaga yama rasa Mai zaiyi ya miqe tareda sakin tsaki yayi wurgi da wayar Yana cewa"


Ke bani abinci.


Aje hijabinta tayi bayan tagama saka doguwar rigar bacci har qasa Mai kauri ta nufi kulolin takawo gabansa tareda plate da spoon.


Koda yaga tuwo ne bai wani damuba Dan dama shi bazai iya tuna yaushe rabanda yaci tuwaba arayuwarsa tun bayan rasuwar mahaifiyarsa.


Sanin baya mugun ci yasa tazuma masa daidai yanda tasaba ta miqa masa.


Ba laifi yaji dadin abincin Saidai Sam bayason yaji ko kadan can qasan maqoshi yace"


Karki Kara saka yaji abinci wuwuyar yarinya kawai.


Ruwa daya ta dauko takawo masa ta tayarda sallar magriba da akayi tun dazu.


Tana Gama sallah ta tattara gurin ta fita da kayan takai tsohon dakinta inda ta ajiye risho.


Kodata dawo Yana kwance ya rufe idanuwansa kamar mai bacci sai kawai ta zauna itama tana shafawa qafafuwanta Mai sbd akwai sanyi sosai.


Su dattiya kuwa koda Suka zauna cin abinci Babu Wanda Wai washe dukkanin haqoran da Allah yayi masaba shida mal idi sbd farin ciki mal idi yace"


Yaushe rabo"""" 


Cinyar kaza dattiya yakai baki Yana cewa"


Eh ai wahalarmu ce zamu rage anan tunda Allah ne kawai yasan iya hasarar daya goga Mana.


Mal idi da kunnuwansa sukai wata rawar da'din miyar da Naman yace"


Wlh mudai wannan Abu gwara da akayi,

Wata gararma sai Abu yayi nisa qilamafa ayi maka sarkin maroqa kaga ni Kuma mataimakinka ko.


Wani murmushin Jin dadi dattiyan yayi Yana cewa"


Hmm ranarda akamin wannan sarautar ai kaima kasan Banda wani mataimaki bayai Kai.


Iya talatu dake jinsu a tsakar gidan tace"


Allah dai ya shirya wainnan masu mutuwar zuciyar.Washe gari tunda wuri ta tashi tahau aikin gidan tadora ruwan zafi ta cika masa flask tadawo tahau aikin yimasa breakfast lokacin Yana ciki Yana motsa jikin daya Saba.


Doya ta soya masa da kwai Wanda zainab ce take qara nuna Mata yanda akeyi harsuka Gama ta adibar masa nasa takai masa lokacin Yana gurin wanka tana cikin gyaran dakin yashigo tana gamawa ta fice Dan zuwa wanke wanke.


Yana gama cin abinci ya fita.


Sai bayan azahar tsamu ayyuka suka rage Mata tayi wanka tayi sallah ko hutawa batayiba iya talatu takirata suka hau wani aikin.


Da daddare kodata kwanta jikinta har wani ciwo yakeyi sbd wahala Dan aiki Kam yayi Mata yawa fiyeda da can.


Duniya sabuwa aka bude a cikin gidan sbd cima Kam yanzu ansamu safe Rana dare Kuma lafiyayyan abinci sukeci wani lokacin saiyanajin takaicin yanda tun farko baya Basu abinci tunda yanada halin hakan wata qilama hakan da tuni yasa kawun ya daina yawon ta zubar dinsa.


Dattiya kuwa yanzu da aka bude Jin dadi sabo duk inda yake lokacin cin abinci nayi to Yana gida Dan kuwa yanxu wani lokacin idan yaci yaji yayi nas har wata kasalar futa yawon maula yakeji saiyayi zamansa Yana Shan iska Yana sakatar haqori cikin wata irin Isa Yana hura hanci.


Zainab ma ba laifi ta 'dan rage yawo sbd ganin kusan abinda takewa yawon yanzu suna samu a gidansu Dan dama yunwa ce kesata yawon batanan batacan.


Nadiya kuwa yanxu Kam tafara zama abin tausayi sbd duk wata wahala tana cikinta Dan kaf gidan aikinsu suci su qoshi ne kawai duk wata wahala ta gidan ita keyi,


Ko cokali Babu Mai iya dagawa sai itace keyi gashi sanyi yashigo sosai sai abin yafara tabata Dan kuwa kumburi tafarayi sbd sanyi dayayi Mata mummunan kamu yatsar qafafuwanta har wani yankewa sukayi sbd aikin ruwa da sanyi.


Gashi bikin Yaya dahiru yazo sosai ake hidimar biki a gidan sai abun ya ninkar Mata ko zama batayi idan gari ya waye sai dare idan ta kwanta tayita juye juye sbd ciwon jiki da qirji.


Yana lureda ita duk baqar wahalarda takesha idan tazo da dare tanata murqususu sai abin ya ringa qular dashi Amma dai ya qyale yaqi Mata magana.


Abinda yabawa kowa mamaki shine kayanda ya dinka Mata a dinkensu masu 'yar tsada har kala biyar Wainda aka dinko daidai jikinta har zainab na tsokanarta da cewa"


Lallai Yaya Zaki har hannuwansa sun haddace girman komai na jikinki..


Rintse ido tayi da sauri tareda barin gurin zainba din tana saka kayan cikin kayanta Suka fito tana cigaba da tsokanarta.


Ranarda akayi biki aranar da daddare kasa bacci tayi tafara juye juye dafe da qirjinta tana hawaye cikin tsananin azaba ga tarinda takeyi mai tsananin zafi a maqoshinta Wanda shiyasa tafara Yi kamar zata fice hayyacinta.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863


_*Mamuhgee 19*_

Jin nishinta da motsin data daina yasashi daukar wayarsa ya kunna fitila ya haskata,


A miqe take jikinta gabaki daya ya saki ta daina motsi sai bakinta dake budewa alamar tanason Jan numfashi Amma takasa.


Aje wayar yayi lokaci guda ya isa gurinta tareda cirota da sauri ya Dora kan katifa Yana Kiran sunanta tareda 'dan jijjiga fuskarta Yana kallonta cikin tashin hankali Saidai Yana qoqarin dannewa.


Sakewa jikinta yaqarasayi numfashinta ya tsaya cak.


Wannan karon da qarfi ya girgizata Amma Sam tariga ta some batasan yanayiba.


Bai tsaya komaiba ya dauketa tareda wayarsa da key din mota da atm ya fito Yana kallon fuskarta yanaji kamar zuciyarsa zata buga.


Qafa yasa yayi kyauren fita gida shuri 'daya take qofar tabude ya fice baiko tsaya nemansu nanuba ya nufi motarsu dake pake gurin masallaci ya bude da hannu daya yasakata.


Yana qoqarin shigane Nanu yafito riqeda fitila da wata sharbebiyar Adda tana kyalli cikin duhun sbd motsinda yajiyo.


Ganin mutum na qoqarin shiga motarsu yasa ya Dalla fitila ga mamakinsa yaga Zaki da sauri ta qaraso Yana cewa"


Sarki matsala ce????


Batareda ya kallesaba yafara qoqarin shiga motar 

Nanu yayi saurin cewa"


Sarki kawo naja kamar zaifi saika kulada ita a bayan.


Miqa masa key yayi sbd bayason doguwar hayaniyarda zata tayarda mutane suka bar gurin suna Hawa titi Nanu yabata wata irin wuta na mugun gudu.


Dattiya dayaji anyiwa qofar gidan mugun bugu cikin bacci yayi mugun zabura tareda lalubar fitilarsa Yana qoqarin kunnawa Amma taqi kunnuwa.


Ahankali ya miqe tsaye tareda nufar qofa Yana tafiya ahankali.


Bude qofar dakin yayi yafito yanabin bango atake qirjinsa yayi mugun bugawa lokacinda ya hango qofar gidan a wangale

Wani mugun zufane ya karyo masa yadawo daki da sauri qafafuwansa na mugun rawa yasawa qofar dakin sakata yafara lalubar inda talatu take.


Da Dan qarfi ya buga qafarta ta zabura tana cewa"


Wayyo Allah innalillahi.


Wani sabon zufane ya gangaro masa ya bude baki qasa qasa yace"


Talatu yau ranar rabuwarmu tazo wlh barayine Suka shigo Kuma tunda kikaji tsit wlh sungama kashesu Zaki Ni wlh bantara komaiba ahaka nazo duniya ahaka zankoma yau mutuwar wulaqanci zamuyi Dan wlh kashemu zasuyi tunda bamuda abun Basu....


Yana kaiwa nan sai kawai muryarsa ta fara rawar kuka yanason dannewa.


Iya talatu kuwa kuka take sosai harda shesheka tana tuna irin rayuwarda sukayi a baya tanajin tausayin zasu mutu yau wace irin rayuwa zasu tarar.


Har akayi Kiran asuba suna zaune suna jiran tsammani zuwa lokacin tuni idanuwan iya talatu sukayi luhu luhu sbd kuka dattiya ma yayi sharben hawaye harya gaji.


Saidaya tabbatarda anfito masallaci har gari yafara Dan washewa kafin ya bude daki ya leqo Yana qwalawa zainab Kira.


Cikin maganin bacci ta fito tana amsawa.


Yana ganin haka saiya qarasa fitowa Yana goge zufa ya daure fuska yace"


Waike Sam bakya tashi sallah kan lokaci ko??kullum Saidai baccin lalaci maza wuce kije kiyi sallah kafin na fasa bakinki a gurin.


Wucewa tayi tana murza ido tana Dan tura baki.


Shima a dubarance yayi alwalar dan karta gane shima baiyiba yakoma daki ya tayarda sallah iya talatu ma said lokacin ta fito tayi alwala Takoma yin sallah.Suna isa asibiti a gaggauce aka karbeta sbd yanda jikinta yayi sanyi sosai kamar zata sandare Dan tuni ta miqe kamar bazata iya lanqwasuwaba.


Likitocin dake on call (NIGHT DUTY) suna ganinta Suka gano abinda ke damunta Dan kuwa data Jima ahaka to shikenan za'a iya rasabata dankuwa zata iya mutuwa abinda yaji likitocin na fada kenan kafin ace yafito.Zama yayi kan waiting kujerar dake bakin gurin tareda Dan rintse idanuwansa ya fitarda numfashi Mai qarshi idanuwansa na kadawa zuwa ja sbd bacin Rai da tension.


Nanu dayaga yanayinsha Saida yasha jinin jikinsa Yana zazzare ido a qofar Yana fatar kar abinda yasamu nadiyar sbd sarkinsu.

 

Saida gari yayi haske sosai har lokaci yaja guraren qarfe takwas wata nurse tafito tazo gaban zakin tace"


Bismillah Dr na son ganinka.


Miqewa yayi yashiga cikin dakin 

Yana shiga saidayaji wani irin zafi ya daki fuskarsa sbd dakin ya dauki dumi sosai anrufe windows ansaki labulayensu sun kunna na'urar dumama daki sunkai kusan qarshe Wanda hakan yasa jikin nadiyar yafara sakewa daga sandarewar dayayi sbd sanyi daya shiga qashinta sosai.


Kallon Dr dake rubutu a file dinda aka bude Mata yayi batareda ya kalli inda take kwance ba Yana sauraran bayanin dazai masa.


Saida Dr yagama rubutu kafin ya miqawa nurse file din yace"


I've written all the drugs + the injection dazaki Mata immediately after her plasiadmin so just write and give him duka abinda zaisiyo.


 juyowo yayi ya fuskanci zakin tareda Dan juyawa ya kalli nadiyan cikin yanayi na damuwar halinda nadiyar ke ciki Dr din yace"


Maganar gskia yarinyarnan wahalace da sanyi suke neman yimata illa sbd sanyi yashiga jikinta sosai harya kama qashin gefe gefen cikinta wanda Kuma tarinsa ke yagar maqoshinta Wanda yake tashe.,


Saikuma qashin bayanta dake neman 'dan lanqwasawa sbd aikin wahala.,


Ataqaice da gskia tana cikin tsananin hali na cutar sanyi dakeson kamata gabaki dayanta,


Sannan bakwa ganin yanda aiki da ruwan zanyi duk ya yayyanke Mata qafafuwa Amma Sam bakuyi tunanin zuwa asibiti da wuriba shiyasa wasu qwayoyin cutar sukaita shigarta ta nan.


To yanxu dai gashinan munyi duk abinda yakamata muyi Dan ceto rayuwarta Kuma alhmdllh gatanan she's stable now Amma zamu riqeta tsawon kwana biyu harsaita qara zama stable nurse zata baka takardar abinda za'a siya, Allah ya sauwaqe.


Rabasa yayi zai wuce cikin shaqewar murya zakin yace"


Shi toshewar moqoshin akwai mafitarsa????


Tsayawa Dr din yayi tareda juyowa yace"


Eh kala kala ne akwai Mai warkewa akwai Wanda baya warkewa nata yanxu bamusan wane iri bane tukuna sai munyi Mata hotuna da awo zamu iya ganewa.


Gyara tsayuwa zakin yayi suna fuskantar juna da Dr yace"


Yaushe yakamata afara wainnan.???


Duk lokacinda ka shirya zamu komai Saidai Banda yanxu saita warke ko zamu fara Mata na wannan fannin so inaga mu Bari zuwa kamar qarshen watan nan Dan zuwa lokacin duka drugs dinta tagama shansu.


Ok thanks""zakin yafada Wanda yasa Dr sake kallonsa sbd izzarsa da cika idonsa ga tsare gida dayayi yasa Bai masa masifa sosaiba akan halinda nadiyar ke ciki Dan ta basa tausayi matuqa yarinyar dama shi mutum ne Mai matuqar tausayi.


Qofarda Dr yarufo bayan fitarsa ya dade Yana kallo kafin ya juyo ahankali ya kurawa gadon datake kwance ido.


Yaune Rana ta farko a rayuwarsa daya yake Mata kallon tsaf tun daga kanta har qafafunta.


Kwance take miqe andaura Mata ruwa sai qafafuwanta da aka dannade gurin yatsin qafarta da bandages,


Doguwar rigar data Saba bacci da itace ta kode ta wande sbd wanki da tsufa.,


Fuskarta fayau Babu komai sai uwar rama da duhun datayi sai kanta dake kwance sbd zainab data saka Mata relaxer Dan Dole sbd bikin Yaya dahiru Saidai tun ranarda akayi Mata taba sake warware shiba tasake gyarawa Dan tanada cika da tsawon gashi ba laifi.


Sarqewa numfashinsa yafarayi ya dauke ido daga kanta yanajin wani irin zafi da tiririn zuciya na cinsa Dan da akwai inda zai sauke abinda yakeji na zafi a ransa da sunga balai da masifarsa Basu taba jiba.


Dama nurse ta bar masa takarda tun suna mgn da Dr tafice.


Daukar takardar yayi ya fito fuskarnan yau tafi tako yaushe Rashin annuri 

Nanu yataso da sauri Yana masa maganar jikin nadiyar.


Takardar ya miqa masa tareda ATM dinsa kawai ya juya ya koma batareda yace komaiba.


Da sauri Nanu ya juya ya nufi pharmacy yafarajin kudin tukuna kafin yaje yaciro Dan akwaima atm jikin pharmacy na asibitin.


Zama yayi kan kujerar dakin dake nesa da gado ya Dora qafa daya Kam daya tareda rintse idanuwansa dasukai ja ya juya maganar Dr a zuciyarsa gameda maqoshinta na Rashin mgnarta.


Har lokacin sallar azahar suna asibiti sai bayan dasukayi sallah yadawo gida yashiga dakinsa ya zauna tareda dafe Kai Yana furzarda numfashi Jin kansa Kai zai buga sbd tunani da ciwo.Cikin gidan kuwa da hankalinsu yatashi Rashin ganin Nadiya da zakin gakuma anyita dubowa basanan sai hankalinsu yatashi musamman da dattiya ya rafka mugun tagumi yace"


Dama nasan barayin jiya da dare bazasu shigo su tafi lami ba

Shikenan sun daukemin 'yaya wlh kashesu zasuyi..

Take idanuwansa Suka cicciko.


Zainab madai tayi kuka har idanuwanta sun kumbura hakama iya talatu sbd duk da halayensu suke a wani irin barkace suna so da qaunar junansu zuri'ar ta dattiya.


Take zance ya bazu sai zuwa jajentawa akeyi.


Ana haka zakin yadawo bayan qarfe biyu harda rabi.


Nan dattiya ya taso haryana neman faduwa ya nufi dakin zakin Saidai a yanayinsa yagansa saiyaji duk baiji dadiba Rashin ganin Nadiya atareda Zaki saiyaji qafafunsa na neman gazawa murya na 'dan sanyi yace"


Ina 'yata???

Ina kabaromin ita????


Baison hayaniya shiyasa Kai tsaye batareda ya dagoba yace"


Tana asibiti batada lafiya.


Wata ajiyar zuciya dattiyan ya sake sbd sai lokacin yaji hankalinsa ya kwanta ya juya cikin gida ya sanarwa iya talatu kafin ya azalzali zainab data shirya suje asibitin ta zauna da nadiyar.


Bai tsaya sauraren tension dinda kawun zai iya qara masaba yace Nanu yakaisu asibitin yadawowarsa.


Aikuwa Yana kaisu yadawo,

Koda sukaje ta har lokacin Bata farfadoba sbd kosu kansu likitoci basaso ta farka yanxu sai bayan 24hrs jikinta yagama samun isashen hutu da dumamawar dasukeson yasamu.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee20_*

Baban dashi aka yini asibiti Dan kuwa sosai zuciyarsa tayi rauni da ganin halinda 'yarsa ke ciki shidai allah yasani duk duniya Babu abinda dai yake so kamar nadiya shiyasama duk wani Abu daya danganceta yake zarewa yayita masifa tuburan akanta.,


Akaro na farko dayaji jikinsa yayi sanyi daga alamarin aurenta da Zaki musamman ma dayaga asibitin daya kawota gashi komai tsada ga kudi dayake kashewa sosai akanta da duk lalurar asibitin,


Tunda ta farfado itama kowa ke lallabata tsakanin zainab da baban hakama iya talatu idan tazo,

Yaya dahiru da amaryarsama kullum saisunzo da daddare dubata,


Taji jiki sosai Saidai alhmdllh cikin kwana biyar sauqi yafara zuwar Mata sosai Saidai qafafuwanta datakejin azabar takawa Dan kullum saisun warware bandage din sunwanke qafar sun canza Mata wani.


Zainab ce take kwana agurinta shiyasa take Dan sakewa Amma idan yazo zainab guduwa gida takeyi ta Dan huta.


Tsakaninsu dai Yanda nan yanda suke banbancin shine yanxu Yana zuba mata fararen idanuwansa dake dawo da zazzabinta musamman da yanzu kayanta daya siyo Mata na jinyar kusan dogayen riguna ne Amma marasa wani nauyi sai lafewa ajiki gashi Sam sallah kawai ke hadata da hijib zainab daukewa takeyi.


Yauma dagashi zai itane a dakin zainab ta gudu.


Gashinta daya tarar zainab na gyara Mata ya kalla yaga yanda yakeda tsawo andaure Mata da band gashi sosai tayi wani irin haske na alamar tana jinya ya sake kallon dogon wuyanta zuwa qirjinta dake sama Yana qasa sbd numfashinta.


Dauke Kai ganin tanata wani mutsu nutsu alamar wani Abu ya gyara tsayuwa tareda zuba hannuwansa a aljihun wandonsa fuska ba sakewa yace"


Kinyi sallah???


Girgiza Kai tayi tana sunkuyar dakai.


Ya Dade shiru cikin takaicin zainab data tafi batareda ta tsaya yin abinda yakamata dinba gashi yanzu baisan uwarda zai musu ba.


Ganinsa kawai tayi a gabanta tayi saurin dagowa idanuwansu suka shiga na juna tayi saurin sunke idanuwanta tana matse hannuwanta.


Hannu ya miqa Mata batareda ya kalletaba Yana sake tamke fuskarsa.


Kallon hannun nasa tayi tareda dagowa da sauri ta kallesa taga ba alamar sauqi daga fuskarsa take taji jikinta na rawa sbd duk lokacinda jikinsu ya hadu jitake jikinta na vibration.


Ahankali ta dago hannunta Yana rawa ta Dora a nasan kusan atare Suka rintse idanuwansu Dan abinda yakeji idan jikinsu ya hadu kusan yafi wanda takejin.


Ahankali ta miqe Suka nufi toilet din dakin Yana riqeda ita tana dingisawa ahankali sbd qafar.


Suna kaiwa bakin qofar toilet din Suka tsaya shi ya sauke Kai Yana sake daure fuska ita Kuma tayi qasa dakai Dan kuwa zainab ce ke taimaka Mata gurin alwalar.


Daddafawa tayi tashiga bayin tareda turo qofa ahankali tana rintse ido.


Daqyar da dubara tayo alwalar Saidai duk ta jiqa bandage din qafar tana juyowa wani mugun santsi ya kwasheta ta bugu da madubin gurin atake ta zube agurin goshinta na fitarda jini.Shiru shiru Bata fitoba tun Yana basarwa harya maida hankali kan qofar yaji yadainajin motsin ruwa daga ciki.


Yana zaunen zainab tashigo kusan tareda nurse da Dr sayyid dasuka Saba sosai dashi.


Atare Suka kallesa Dr na cewa"


Sarki Ina patient Dina ne bangantaba??


Zainab yayiwa wani kallo yace"


Jeki ciki ki dubota.


Toilet din ta nufa ta bude Kai tsaye zata rufo qofar ta hangota some tsakiyar bayin wani razanannen ihu tasaki tareda qarasawa da sauri tana kiran sunanta.


Da gudu Dr sayyid da nurse sukayo bayin cikin tashin hankali suna tambayar meye.


Ganinta kwance zainab nason dagota takasa yasa arikice Dr sayyid ya qaraso Yana cewa su matsa ya Kai hannuwa zai daukota yaji anriqe hannunsa riqewa irin wadda yasan ya riqu.


Da sauri ya dago abinda yagani a idon zakin yasashi matsawa gefe batareda ya furta ko kalma dayaba.


Hannu biyu zakin yasa ya daukota cak ya fito bayin da ita Suka biyosa zainab na Dan fidda sautin kuka ahankali sbd ganin yanayin zakin tasan Idan tayi hauka itace za'a bawa gado a dakin kusa dana nadiyar.


Cikin fada Dr ke dubata Yana cewa meyasa zasu barta tashiga toilet din ita kadai.


Fitowa yasa sukayi kafin yayi Mata dressing goshinta tareda Mata wasu allurorin Yana saka Mata wasu allurai a ruwa ta bude idanuwanta ahankali hawayen azaba suka gangaro Mata.


Sannu"Dr sayyid yace Mata cikeda tausayinta shidai Allah yasani yanajinta cikin zuciyarsa Kuma sosai ya lurada tana fama da maraici arayuwarta sbd Sam yanda Bata iya sakewa da danginta koyaushe cikin sanyi take kanta a sunkuye.


Zama yayi kan kujera bayan yagama Yana rubutu cikin file dinta Yana cewa"


Nadiya please ki ringa kula kina kiyayewa da duk abinda zai tab lafiyarki.


Wasu sabbin hawaye ne Suka gangaro Mata ta juyarda kanta dayan gefen.


Shiru yayi Yana kallonta kafin ya miqe ya fice.


Zaki baisake shigowa dakinba ya wuce gida Dan Yana tsananin buqatar maganin ciwon qirjinsa kafin aga ya buga a gurin.


Zainab ce ta zauna tana Mata sannu cikin sanyin murya tana dafa goshinta dake nade da bandage cikin tausayin 'yar uwarta.


Kwana biyu tashin shima yayi sauqi tasake warwarewa Saidai wasu irin qaidojinda Dr sayyid ya shimfida akan lafiyarta kafin ya sallamesu Suka koma gida cikeda kewarsa sbd sosai yake bawa Nadiya kulawa Kuma sosai hakan yayi tasiri a zuciyar dukkaninsu musamman dattiya dahar wani sabo sukayi Dan duk zai koma gida idan yazo sai Dr yabasa dubu guda yace yahau acaba.


Iya talatu ma girman dayake Bata Wanda Sam Bata samuba daga yayanta daga Nadiya saishi yasa take jinsa matuqa.


Zainab kuwa dama tuni takamu Dan baqaramin burgeta Dr sayyid yagamayiba.


Zainab ce tayi musu gyaran dakinsu tashare ta goge komai tareda fesa turare takaiwa nadiyar ruwa har bayi taje tayo wanka.


Tana cikin shafa Mai yashigo dakin idanuwansa Suka sauka kan daurin qirjinta datake qoqarin saka hijabi da sauri har jikinta na rawa. 


Qarasowa yayi ya nufi bakin wardrobe ya zare rigarsa ya dauki towel dinsa ya fice.


Miqewa tayi ta dauki rigarta ta bacci Mai tsantsi doguwa har qasa tasaka bayan ta fesa spray.

Har safar qafa tasaka sbd sanyi ta sanya baqar wula ta rufe kanta tareda cusa gashinta ciki Dan tunda zainab tasa Mata relaxer gashinta yayi tsayi sosai sbd miqewar dayayi.


Sallar ishai tayi tayi kwanciyarta agurin tareda qudundunewa cikin hijabinta sbd yau sanyi Sosai takeji sbd asibiti kullum dakin datake dumi  Dr sayyid ke saka masa shiyasa yanzu har cikin qashin bayanta takejin sanyin har gabobinta na fara Mata ciwo.


Yana shigowa dakin yaga yanda ta dunqule waje daya saiyaji kamar hankalinsa zai tashi Amma ya basar yayi duk abinda zaiyi yaje ya rufe gida  yashigo ya rufe dakin ya kashe wuta ya nufi katifa saiya kasa Hawa ya tsaya Yana jujjuyo zancen Dr sayyid akan sanyin daya kamata gashi yanda yake Jin fitar numfashinta yanxu yasan ciwon ne yakeson tashi tunda dr yace ko kadan daga yanxu kar abari sanyi na shigarta.


Shiru yayi kansa na daukar zafi haryaji tana fidda wani irin Nishi alamar dai ciwon ya dawo Mata.


Cikin duhun Kai tsaye ya sunkuceta gabaki dayanta ya kwantar kuryar katifar tareda zare Mata hijabinta ya kwanta tareda bude musu jibgegen bargonsa Mai laushi.


Rawa jikinta keyi sosai na sanyin dake ratsa qashin jikinta ganajinsa kusada ita sosai gashi dama baya kwana da riga ajikinsa.


Jin rawar jikin nata yayi yawa da nishinta yasa ya jawota cikin jikinsa ya rungume tareda zagayeta ya rufe a qaqqarfan jikinsa ga dumin bargo


Baa wani jimaba sanyin jikinta yafara raguwa 'dumi na shigarta sosai ahankali tafara dawowa normal Saidai yanayin yanda qirjinta ke manne da nasa yasa takasa motsi sbd kunya da tsoro ahaka bacci ya dauketa Dan dama akwai maganin bacci sosai acikin magunanta Dan harda hutu Dr sayyid yakeson tasamu.


Bai bacci ba shiru yayi da ita cikin jikinsa akaro na farko yakejin kamar rayuwarsa tasamu nutsuwar datake buqata,

Wani irin sanyin Hali yaji na shigarsa sbd yanda dukkanin gabobin jikinsa suke karbar baquntar jikinta a nasa.


Da asuba koda ya farka bacci takeyi sosai wannan karon hannuwanta zagaye suke da qugunsa hularta ta zame ya qurawa fuskarta ido sbd nepa daya farka yaga akwai. 


Zameta yayi ahankali tareda gyara Mata bargon ya sauko ya nufi electronic cattle dinda ke dakin ya zuba pure water hudu ciki ya jona ya fice zuwa alwala.


Kusan tareda kawun Suka fito sallah sbd sallar asubar yanxu tashiga kawun batareda yasaniba ta hanyar saka idonsa akansu.


Harya dawo bacci takeyi ya juye ruwan a flask yasake zuba wasu yazo bakin katifar ya zauna tareda Dan buga pillow ahankali.


Cikin yanayin bacci dake cinta ta bude idanuwanta tareda mayarwa ta rufe 

Saura kadan zuciyarsa ta fado da hakan datayi Dan kuwa har wani tari ya miqe Yanayi sbd sarqewar numfashi daya kamasa.


Kyaleta yayi ya hawo katifar ya kwanta tareda rufe rabin jikinsa kawai Yana 'dan qara gyara muryarsa kadan sbd yawun dasuka sarqesa sbd qafafuwansu dasuka hadu cikin bargon.


Lumshe idanuwansa yayi ya rufe yanajin yanda dumin numfashinta ke sauka a wuyansa yana dumama dukkanin jikinsa har numfashinsa na slow.


Kamar Wasa sai baccin dabai wani yiba cikin Daren ya daukesa ahakan.


Qarfe bakwai maganin yadan saketa ta bude idanuwanta ahankali tana sake gyara kwanciyarta cikin jikinsa.


Da sauri ta qarasa bude idanuwanta baccin na sakinta gabaki daya tayi saurin matsawa baya tana kallon fuskarsa datayi wani irin kyau dayana baccin,


Bakinsa dayayi wani Dan ja kadan ta kalla zuwa dogon hancinsa da gashin girarsa dake kwance kamar na mace,


Tabbas farine sosai dayake sirke da 'dan yellow na asalin mutan Igbon asali Saidai shi Sam baya wani tara sumar Kai saita gemu Wanda yake bana ustazanciba saina tsabar qwarewa a ta'addanci.


Karo na farko data saki murmushi bayan qare masa kallo.


Ahankali ta sauko tana qoqarin daukar hijab taji yace"


Ki juye ruwan cattle din kiyi amfani dasu idan kika taba ruwan sanyi wlh saina karya dogon wuyankin nan.


A matuqar tsorace da kunyace ta juyo ta kallesa taga har lokacin idanuwansa a rufe suke kenan duk Yana saneda abinda takeyi tun tashinta.


Cikin tsananin kunya da rawar jiki ta dauki cattle din ta fice tana rufe jikinta da hijib sbd sanyi.


Da ruwan zafi sosai tayo alwala tadawo sbd cikin gidanma tsit duk Basu fitoba sbd sanyi.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee21_*

Tana komawa dakin ta nufi dardumar sallah saitaga wata sabuwar safa akai ajiye Mai tsananin kauri,


Dagowa tayi ahankali ta saci kallon gefensa taga alamar yatashi kenan shine ya ajiye Mata safar.


Dauka tayi tareda zama tasaka kafin tana miqe ta tayarda sallah.


Tana gamawa saitayi zuru da idanuwa tanason fita aiki Amma ganin yanda ya matuqar hade fuska sai tsoronsa ya taso Mata tafara kame Kamen son fita.


Miqewa tayi ta nufi bakin qofa tana qoqarin ficewa taji anfixgo hannunta tareda daga hannu zai sauke Mata lafiyayyan mari sai kawai ya kasa ya tsaya da hannu a sama ransa amatuqar 6ace.


Saurin rintse idanuwa tayi cikeda tsananin tsoron yanda Marin zai fasa bakinta saitaji tsit Marin bai saukaba.


Ahankali ta bude idanuwanta dasuka fara sauka Kam hannun dayake sama Amma baiyi marinba,


Kan fuskarsa take qoqarin mayarda kallonta ya rintse idanuwansa cikin bacin Rai tareda sakinta Yana fitarsa numfashi Mai zafi da takaicin abinda yasa yake biye Mata wani lokacin,


Cikin muryarda ta jima batajiba tasa ta tsantsan bacin Rai yace"


Daga yau bayan wanka da alwala kika Kuma fita dakin nan saina raba qafafunki biyu.


Sakin hannunta yayi yakoma ya kwanta tareda rufe idanuwansa kamar bashi yatashi yanxuba..Saidai kallo daya zakai masa kasan ransa amatuqar bace yake.


Sanyi jikinta yayi tadawo a sanyaye ta zauna kan daddumar sallah tareda dunqunqunewa cikin hijabinta.


Hakan sai kawai yaqara Bata ransa ya juya Mata baya tareda shigewa bargo ahaka bacci yasake daukarsa.Qarfe goma ya farka yaganta kwance aqasa ta dunqule waje daya bacci ya dauketa.


Fuskarta ya qurawa ido daga idanuwanta har zuwa 'dan madaidaicin bakinta.


Nadiya ba fara bace sosai saidai Kuma ba baqa bace hakama ta 'dan Dara Wainda ake cewa chocolate haske danma yanayi na wahalar rayuwa da Rashin hutu yaqara canxa kalar fatarta,

Tanada dogon hanci sosai da fararen idanuwa masu Dan girma,


Sake kallon bakinta yayi tareda rintse ido ahankali ya dauke Kai tareda miqewa ya sauko.


Ahankali ya durqusa ya zare Mata hijab ya dauketa ta yanda bazata tashiba ya kwantarda ita kan katifa yana kallon fuskarta ta bude idanuwanta Suka qurawa juna ido akaro na farko kowannensu bai dauke ido ba.


Batareda tasaniba ta qanqame hannuwansa dake jikinta tanajin wani Abu Mai girma cikin zuciyarta dabatasan meyeba Saidai hawaye kawai dataji tanason zubarwa kozataji nauyinsa ya ragu,


Idanuwanta na cikin nasa hawaye Suka ringa gangarowa ta gefen idanun tana sake qanqamesa.


Hannunsa daya taji akan fuskarta yasa ta lumshe idanun da batasanma tanayin hakanba.


Bata bude idanuwantaba taji saukar hannun a wuyanta cikin wani irin sanyi 

Batasan lokacin wani Nishi Mai qarfi ya qwace mataba Wanda yasa qirjinta yin sama ya mannu sosai da qirjinsa dake daf da nata gurin fitarsa Wanda hakan yasa qarfin jikinsa saki ya matseta jikinsa Yana sake cusa hannunsa cikin wuyanta zuwa bayanta.


Rufe idanuwanta tayi hawayen cikin nasake gangarowa tana Jin yanda hannuwansa suke zagaye da ita tanaji qarfin gabobin jikinsa na kashe 'dan qarfin nata gabobin dabasuyi ko kwatar nasaba.


Shiru sukayi ahaka ko motsi Babu Wanda yayi sbd duk sun dawo hayyacinsu daga Dan shagaltar dasukai Saidai har lokacin jikinsu a hade yake bai saketaba itakuma Bata motsaba tananan cikin jikinsa.


Dumin jikinsa Dana bargon yaqara sata Jin bacci bacci Saidai Rana tayi batason yi.


Sun Jima ahaka idanuwansa a lumshe bai budeba Saidai tasan ba bacci yakeba.


Harta fara lumshe ido zatai bacci taji ya zame ya sauka tana kallo ya dauki brush da toothpaste ya fice.


Ajiyar zuciya tasake sai alokacin tsananin kunyarsa tafara dawo Mata taji kamar tanason rasa kunya da control na kanta ne idan Yana tareda ita.


Saukowa tayi jiki a mace da kunya itama tadauki brush ta dauki flask ta  fice.


Duk su iya talatu na tsakar gidan tai musu alamar gaisuwa tareda zuba ruwan zafin dake cikin flask ta sirka tayi brush tana gamawa ta nufi dakin zainab dake Shan waqa a wayarta tana gugar kayanta ta zauna gefen katifarta tana Mata alamar taje ta Dora abinda za'a karya dashi ita Yaya Zaki ya hanata daga yau.


Daqyar zainab tagane Mai take nufi sbd tun can dah Nadiya Bata damu da bayani ba shiyasa Sam bazaka gane Bata mgn ba idan Kai baqone sbd koyaushe Bata dogon zance bare tayi maka alama da hannu.


Wani ihu zainab tasaki tana cewa"


Iyye yarinyar nan kice mijinki ya hanaki aiki wahala sbd tsaro..?


Miqewa nadiyar tayi da sauri zata fice zainab ta riqota tana cewa"


Ke Yar bebiyar Yaya Zaki tsaya kiji to tunda yafara ji dake wlh kiyi sauri kisamu ciki kozamu qarasa samun yanci da Jin dadin duniya a gidan nan.


Zaro ido Nadiya tayi saikuma zancen yabata masifar kunya ta qwace tareda nufar qofa zainab takuma Shan gabanta tana riqo hannunta tace"


Ok let's be serious,wlh Nadiya yakamata kifara zagewa kiyi rayuwar auren,Ina nufin kifara aikinki kamar yanda kowace matar aure keyi a gidan mijinta,

Dukkaninmu Muna tsoron Yaya Zaki Amma yakamata ki rage tsoronsa ko kicire tsoron kwata kwata sbd ke matarsace Dole aringa ganin banbanci.


Zuba Mata ido Nadiya tayi cikeda mamaki da ganin wautar maganarta sbd Babu ranar dazata daina tsoronsa arayuwarta.


Riqo hannunta zainab tayi cikin wani irin yanayi tace"


Nadiya nikadaice 'yar uwarki Kuma tamkar qawa agareki 

Ina fada Miki duk abinda yakamatane sbd zai iya yiyuwa wata Rana bananan bakida Mai fada Miki adaidai lokacinda yakamata ace kinada Mai fada mikin Wanda nasan alokacin zakiyi maraicina fiyeda kowa Nadiya,


Sanyi jikin nadiyar yayi ta kalli zainab din saitaga idanuwanta kamar sun ciko sai itama nata idanuwan Suka ciko ta riqo hannun zainab din tanajin kamar tsoron maganar zainab din nashigarta.


Murmushin qarfin Hali zainab tayi tace"

Nadiya Dan Allah kiyi amfani da matsayinki a gurin Yaya Zaki ki kawo sauyi a rayuwarmu gabaki daya muda iyayenmu sbd gyaran zai faro daga kansa ne to abin zaizo da sauqi,


Nadiya kimin alqawarin kulada iyayenmu karki Bari su mutu a kan turbar dasuke ayanxu.??


Rungumeta Nadiya tayi tana girgiza Mata Kai Dan jitake hankalinta na tashi tsoro na shigarta,


Batasan meyasa zainab ke Mata wannan zancenba Saidai tasan batason rabuwa da zainab itama,

Duk Wanda ke sonta takejin sanyi agurinsa tafiya sukeyi suna barinta wane irin baqin jini ne gareta?


Mamarta ta rasu Randa ta haifeta,

Umman Zaki dake tsananin qaunarta ta tafi tabarta,

JJ ma dayake matuqar qaunarta ya tafi,yanxu ga zainab na Mata wainnan zancen marasa dadi.


Sakin zainab din tayi zata miqe 

Zainab ta saki dariya tana cewa"


Ke duk da Wasa nake Miki sbd kisaki jiki kiji da aurenki wlh Nadiya ke local ce kisaki jiki ki dinga haukata Yaya Zaki da shagwaba kiga yanda duk zai kwashe makamansa daga dakin nan yakaisu waje ya zubar.


Ajiyar zuciya Nadiya ta sauki Jin Wasa zainab din takeyi ta miqe tareda hararar zainab din ta fice tana murmushi.


Tana shigowa tagansa zaune Yana waya tasan Kuma breakfast yake jira tunda taga ledar bread a gabansa dashi yashigo kenan.


Flask ta jawo tareda kayan tea ta ajiye gabansa ta zauna ahankali tareda hada masa tea din Mai kaurin gaske sbd Sam arayuwarsa bayashan sugar.


Miqa masa tayi tareda fara qoqarin miqewa yayi Mata wani kallon qasa qasa 

Komawa tayi ta zauna tareda hada nata tea din kadan tafara Sha.


Kusan tare Suka gama ya miqa Mata magani ta karba ta shanye ta tattara kayan ta fitar ta dauki bread ta dibi kayan tea din taje takaiwa zainab Wanda zata hada musu itadasu baba tadawo dakin.


Gyaran dakin tahau Yi sbd yatafi wanka.

Shimfidar tafara gyarawa tsaf ta goge komai tayi shara ta fesa turare tana qoqarin tubewa yashigo da sauri ta mayarda rigarta tana kame kame.


Saidaya shirya ya fice tukuna ta tube taje tayo wanka tadawo ta shirya cikin doguwar riga Mara dogon hannu cikin Wainda ya siya Mata lokacin jinya ta fesa spray.


Abincin daza'a dafa ta Diba taje takaiwa zainab tadawo tana Jin jiri sbd maganin baccin dake cikin magunanta.


Bakin katifa ta zube take bacci yayi gaba da ita.


Bayan azahar sosai ta farka taje tayo alwala tayi sallah tana idarwa Yana shigowa hannunsa daukeda ledojin takeaways.


Ajewa yayi ya zare rigarsa ya fice waje Yana murza daurin qundarsa sbd wasu yara da aka kamo sun sassare yaronsa harya rasa hannunsa daya.


Yana fita qofar gidan gurin yayi mugun tsit bai tsaya komaiba ya dauki babbansu wani mahaukacin Marin dayasa hancinsa 6arewa da jini.


Goran hannun Nanu ya karba ya bugi qafafunsa atake ya zube qasa Yana roqansa da cewa"


Sarki Dan allah kayi hakuri kabarni da Raina wlh bansan yaronka bane da bazamu tabasaba muma ai yaranka ne wlh,

Dan allah sarki,

Dan allah sarki kayi hakuri

Kayi hakuri karka kasheni....


Wani bugu yayiwa bakinsa Saida haqoransa biyu Suka zubo qasa tareda jini da yawu...


Goran yasake dagawa ya bugi hannunsa,

Ihu yakeyi Yana neman afuwa da yafiya Amma dukan dayake masa bayan jini Babu abinda ke fita gashi guri yacika Babu Mai ikon cewa qala.


Dattiya daya dawo yaga guri yayi mugun cika yafara tambayar lafiya Yana ratso mutane Yana kawowa daidai Zaki ya daga Goran zai buga a tsakiyar kan wancan 

Dattiya ya riqe goran


Ganin fushi da bacin ran dayake tareda zakin yasan yau antabosane a mugun wuri

Kai tsaye yace"


Bantaba shiga harkar ikonka ba a kan sarautarka sai ayau 

Ayau dinma nashigane ba amatsayin kawunkaba sai amatsayin mahaifin matarka,

Ka kyalesa haka karkayi kisa sbd baka taba yiba idan kayi yanxu halinda 'yata zata shiga nake dubi.


Kallon kawun yayi cikin ido yaga tabbas yau ba kawunsa yake ganiba mahaifi uba yake gani Wanda keson Kare martabar auren 'yarsa.


Sakin gorar yayi akaro na farko da shima ya saurari maganar kawun shima baa matsayin kawunsaba Saidai amatsayin mahaifin matarsa.


Kallon Nanu yayi da jajayen idanuwansa yace"


Kasan abinda zakayi daganan sa Kai.


Da sauri Nanu yace"


Angama sarki.


Juyawa yayi yashige cikin gidan duk hannuwansa da jikinsa jini ya Dan batasu.


Akaro na farko dayaji bayason tagansa da jinin wani ajiki da hannuwansa ya tsaya bakin qofar dakin yakasa shiga.


Juyawa yayi yai cikin gidan zainab na aikin girki tagansa ya shigo jina jina tayi saurin dibo masa ruwa a bucket takai masa bayi saidata fito gabaki daya yashiga Yana cewa"


Kice takawomin towel da wani threequater.


Yana shiga ya rufo bayin.


Da sauri taje ta fadawa Nadiya saqonsa tana dariya qasa qasa tana cewa"


Wayyo love dadi wlh 

Idan kin shiga bayin ki goge masa jiki kisaka masa wandon......


Da sauri Nadiya ta tureta tana miqewa ta dauki towel da wandon dayace ta fice.


Ahankali ta qwanqwasa qofar bayin.


Budewa yayi kadan ta miqo masa ya zuro hannu zai karba ya hango kawo na qarasowa da sauri ko gabansa baya kallo nadiyar yake kallo masifa nacinsa bakinsa sai motsi yake yazo yasauke mata Dan yasan Zaki ne Sarai a bayin.


Ganin hakan maimakon ya karbi towel din saiya riqo hannunta ba zato yajawota ciki ya rufe qofar.


Dattiya kuwa sai jinsa yayi ya jefa qafa cikin robar ruwan zafinda zainab tagama wanke shinkafa dasu masu shegen zafi.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee22_*

Wani wahalallen ashar ya jefawa zainab tareda yin gefe Yana jefa qafa cikin tsananin azaba Yana sake daga murya gumi na karyo masa.,


Da sauri iya talatu tafito daki jin muryarsa Yana zubo ashar kamar zaiyi kuka,


Tsayawa tayi kallon yanda ruwan daya zubar gurin fidda qafarsa suke hayaqi ga qafarsa riqe ahannunsa sai zuba fada yakeyi zainab na tsaye tana boye dariyarta cikin fada iya talatu take kallon zainab tana cewa"


Zainab yanzu uban naki kika qona da ruwan zafi Kuma kina tsaye kina kallo????


Ruwan sanyi ta debo da sauri takawo masa ya jefa qafarsa ciki da sauri sai alokacin yaji zufansa yadan taqaita ya kalli talatun yace


"nagode talatu kinji da kika bani ruwan sanyin nan na jefa qafata sbd ke kinsan mahimmanci na a cikin gidan nan,


Ita wannna ja'irar Mai kamada amaryar aljanu tana kallo na nufo ruwan zafin nan taqi dauke 

Nafada ciki Kinga ta tsaya tana kallona da idanuwanda bansan na uban waye ta gadoba Dan banidasu kaf zuriata,


Ita Kuma waccan bebiyar Mai kamada bebin roba tana kallona Ina zuwa wancan qaton marasa kunyar yajata zuwa cikin bayi sbd kowa a gidannan ya rainani baa ganin girmana ga dattiyan banza......


Sa alokacin iya talatu ta katsesa tana watsa masa kallon raini da cewa"


To ita wannan anji ta qonaka ita waccan ta bayi meye ruwanka da abinda yake faruwa,

Wlh dattiya idan baka dauke idonka akan alamrin Zaki ba saiya makantaka wata rana Dan shi inda aka haifi kunya ma baisaniba bare cikakken sunanta da ma'anarta,

Idan ka matsa masa da wannan qananun idon naka wlh wata Rana gabanta sai turmushe maka 'yar taka kaga daga ranar zuciyarka ta buga Ni 'dan ciwon bakinda dama kake sani na huta shikenan daganan har tsohon  ciki zakaga nadiyar na yawo dashi cikin gidan kana daga kwance kana jinya abanza.


Cikin zafin data qara masa da maganganunta yace"


Dama talatu tun shekarun bayan haihuwar zainab nasan kindaina so na bakya kaunar ganin Ina yawona Ina walwala kinfison ki ganni a nakashe to Allah dayayini shikeson ganina cikin walwala saiki hadiyi zuciya ki mutu talatu.


Zainab ya watsawa mugun kallo yace"


Bar nan Mai kama da dangin uwarta.


Da sauri ta wuce tana mamakin baban nasu harda masifarsa tasa taji ta matsu Nadiya da zakin su kusanci juna kozai samu salamar wannan masifar dayasa kansa.


Shima miqewa yayi Yana dingisa qafa ya nufi qofar fita Yana masifar gwara yaje gurin amininsa Dan uwansa mal idi ya shafa masa magani danshi kadaine yasan mahimmancinsa yake qaunarsa

Shi wlh Zaki kashesa yakeson yi da sauran kwanansa,

Banda Rashin sa'arsa ace agabansa ake masa abubuwa da 'ya Kai wlh Allah ya tsinewa shedanun Lagos dasuka qullo masa wannan balain ya dauka ba gammo.


Da harara iya talatu tabisa kafin Takoma dakinta tana nata kalar mitar.Acan ciki kuwa tunda ya jawota ta rintse idanuwanta jikinta ba inda baya rawa numfashinta kuwa kamar zai 6allo qirjinta sbd bugawa da sauri.

 

Batareda ya kalleta ba ya zari kayan dake hannunta yasaka tareda karbar towel ya ratayo a wuyansa harzai fito yabarota saiya tuna kawun na tsakar gidan qila saiya daukota cak ya fito bayin da ita.


Sbd tsananin kunya kuka kawai ta fashe dashi harsuka Kai daki Allah ma yasa ba kowa tsakar gidan sai zainab wadda itama kallo daya ta musu tayi saurin komawa daki hartana tuntube sbd mugun kallonda zakin ya Aiko Mata.


A katifa ya ajiyeta ya juya kamar bashiba yahau shirinsa Yana gamawa ya zauna ya jawo takeaways dinda yashigo dasu ya bude yasha fruitssalad ya dauki wayarsa ya fice yabarta har lokacin kuka takeyi.Bayan fitarsa samun kanta tayi dajin haushin abinda yamatan sbd har cikin ranta batason yanda yake wasu abubuwan Dan takalar babanta dukda dai tasan sunsaba tun Yana yaro tun ummansu nada Rai.Da daddare koda yadawo tayi bacci a qasa ya dauketa yafara sata qurya ya kwanta ya lullubesu sukai bacci.


Washe gari qafar babanta tayi jajir alamar dai qonuwa ta tabbata a qafarsa saita samu kanta da nuna masa fushinta sbd ko kallonsa Sam ta daina idan Yana Dakin ficewa takeyi ta nufi cikin gida duk da Bata aikin komai yanzu zainab ce keyi wani lokacin Kuma iya talatu.


Kwana biyu da hakan tana zaune cikin dakin tana cire farce da Reza saigashi yashigo dakin Yana waya faduwarda gabanta yayine yasa rezar yankarta sosai 

Ta saki rezar da sauri tana dafe gurin sbd jinin dake zubowa sosai.


Juyowa yayi yaga jini a hannunta bai kashe wayarba ya ajiye tareda riqo hannun da qarfi cikin fushi yace"


Ke wace irin wawuyan yarinyace?


Idan baki daina wannna shashancinba nakusa karya wuyanki.


Qwace hannun tayi ahankali tana neman zamewa ya fizgota da qarfi tareda matseta a bango zaiyi magana cikin tsananin fushi ta dago idonta yashiga cikin nasa 

Ya rintse ido da cikin wani irin sanyi yace"


Idan kika motsa daganan zan mareki.


Kallonsa tasakeyi har lokacin hannunta na cikin nasa.


Hawayen datake riqewane Suka gangaro Mata ahankali tafara kuka tareda sauke kanta qasa a qirjinsa dayake matse da ita a bango.


Kasa motsawa yayi yanajin kukanta na shigarsa 

Ahankali ya saki hannunta ya tallabota jikinsa gabaki daya ya rungume sai kawai itama ta qarasa fashewa da kuka tana qanqamesa.


Sun Jima ahaka Saida tayi shiru Dan kanta kafin ya saketa tareda riqo hannunta ya dauki flask Suka fito har tsakar gida yakalli zainab data saki baki da hanci tana kallonsu yace"


Ke so sirko ruwan nan.


Karba tayi ta surko a Kofi takawo tana zubawa Yana wankewa nadiyar hannu.


Iya talatu dake aikin kayan matanta a tsakar gidan ita ko kallo Basu ishetaba  aikinta kawai takeyi,


Dattiya dake zaune miqe da qafa Yana fifita qafarsa qara gudun maficinsa yayi Yana Harare Harare dayaga dai bazai iya hakuriba a qule yace"


Ke zainab banafason barnar ruwan nan idan rijiyar gidan ta qafe waye zai Nemo masu yasarta idan baniba.


Babu wanda ya tankasa Suka gama suka bar gurin still hannunsa na riqe da nata Zainab tabi bayansu da murmushin farin cikin tana langabe Kai suna shigewa ta daka wani tsalle tareda cewa"


Yesssssss.


Tana juyowa taga idon babanta akanta Yana Mata wata muguwar harararda tasan da atsaye yake wlh saiya Kai Mata Mari ya sauke haushi a kanta.


Suna komawa daki yasa tissue ya goge Mata hannun ya kalli fuskarta datai wani irin da hawaye saiyaji dukkanin lakkar jikinsa ta mutu.


 Matse hannunta yayi da 'dan qarfi 

Saitaqi dagowa sbd tasan data dago saisun hada ido Dan tanajin idonsa na yawo ajikinta.


Sake matewa yayi Yana kallon fuskarta Jin murmushi na zuwar Mata yasa tayi saurin miqewa zata gudu ya riqota saita kasa juyowa ta rufe ido tana fidda siririn murmushi tanayin qasa da kanta.


Ki yayi kamar andaki qirjinsa murmushinta daya gani.


Jiyayi yanason sake gani ya miqe tsaye tareda dawo da ita har lokacin murmushi takeyi Jin wani irin yanayi atareda ita.


Juyo da ita yayi suna fuskantar juna ya dago fuskarta tayi saurin rintse ido.

Cikin wuyanta ya cusa hannunsa yanason yin magana Amma baisan mezaice ba sai kawai yaji fuskarsa na sakewa alamar shima murmushin zaizo masa da sauri ya saketa ya juya Mata baya Saidai dayake gaban madubin jikin banging dakin suke tsaye sai yazam suna ganin juna ta jikin madubin ta bude idanuwanta ahankali saitaga wani irin annurin murmushinsa da Bata taba ganiba tsawon rayuwarta sai kawai taji idanuwanta na rufewa alamar zata some 

Ganin tayi luuuu yayi saurin riqota tareda girgiza ta tana bude ido taga fuskarsa tasake luuuu da ido yagano abinda yasata kusan suma sai kawai abin yabasa dariya saiga wani sabon murmushin ya sauka a fuskarsa ta zaro ido cikeda mamaki tana qoqarin luu da ido cikin murmushin dayake riqewa yace"


Idan kika kuskura kika Suma anan saina 6alla qafafunki.


Atare Suka saki murmushi wannan karon tafara qoqarin miqewa zatabar jikinsa ya dawo da ita ba zato taji numfashinsa Mai dumi cikin kunnenta yace"


Ki dauka ga ledar maganin quna nan ki kaiwa kawu.


Yana fada ya juya abinsa kamar bashine yayi maganarba yadauki wayarsa ya fice annuri fal fuskarsa.


Su Nanu na ganin yanayin fuskarsa suka ringa mintsilin juna suna son dariya da mamakin yau fuskar sarki asake.


Daukar ledar maganin tayi tareda sakin wani sahirtaccen murmushi ta dauki harda takeaways din tanufi cikin gida takaiwa baban 

Yana fushi yana daure fuska haka ya karba yafara cin friedrice da kazar dake ciki still Yana mita.


Dakin zainab tashiga Dan yanzu tanason abinda zainab din ke fada Mata Dan kuwa tuni taji tanason samun cikakken matsayinta na mata agun zakin.


Abubuwanda zainab ke koya Mata Sam Bata taba Jin zata iyasu Saidai tana saurarentane kawai.

Oiling gashinta zainab ke Mata tana Mata firar harsuka Gama ta daure matashi.Da daddare harta kwanta sai taita tunowa da maganar zainab tashi ta dauko sabuwar doguwar rigar baccinta daya siyo mata tun suna asibiti tasaka tareda shafa turaren Arabian oud da zainab ta Bata.


Kallon jikinta tayi taga ba laifi rigar ta wuce gwaiwarta sosai Kuma tanada hannuwa Saidai santsin rigar da yanayin iskan da ake ciki yasa gabaki daya ta maqale Mata ajiki.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee23_*

Kunyar kanta taji takamata ta rintse idanu tareda girgiza Kai tana ayyanawa aranta bazata biyewa zainab ba takaita tabarota kunya takeji bazata iyaba,


Daga rigar tayi zata cire yashigo dakin da sauri tasaki rigar jikinta na daukar  rawa sbd batai tsammaninsaba kwata kwata alokacin.


Hijabinta tahau nema cikin sauri duk a rude saima rudewar tasa takasa ganin hijabin sai kawai ta duqa gurinda take tana neman zama ta qanqame jikinta.


Ko kallonta baiyiba cikin yanda ya Saba magana a daure yace"


Da kika saka wannan rigar kika zauna tsakiyar daki da wannan uban sanyin idan ciwonki ya dawo kika dameni da Nishi saina fasa bakinki.


Miqewa tayi zuwa lokacin tuni idanuwanta Suka ciko da hawayen tsananin kunyar datake ciki saidai ganin ko kallonta yaqiyi yasa tadan sidada ta nufi katifar tayi saurin shigewa bargo ta kwanta numfashinta na fita da wuri.


Bata wani jimaba tayi bacci tabarsa Yana sallar nafiloli.


Bayan yagama kallonta yayi tsawon mintuna,

Gangarawa idanuwansa Sukayi kan kalar rigar datai Mata kyau wato kalar light purple.


Miqewa yayi ya tube tareda dauko safarta ya yaye bargon ya kamo qafafuwanta ahankali ya sanya Mata ya gyara Mata kwanciya ya kwanta gefenta suna fuskantar juna

'dumin numfashinta na sauka fuskarsa ahankali Yana karya garkuwan jikinsa,


Lumshe ido yayi tareda kunna wayar fitalarsa ya ajiye saitin fuskarta ya qurawa fuskar tata ido jijiyoyin control dinsa ba kuncewa.


Bakinta ya qurawa ido yanajin bugun zuciyarsa na harbawa yayi saurin dauke Kai tareda rintse ido Yana qoqarin control

Ya jawota jikinsa ya qanqameta Yana sakin ajiyar zuciya da sauri.


Cikin bacci tajita nafe cikin jikinsa dake rufeta koina.


Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda bacci ta saukesu a fuskarsa tana sake lumshe idon alamar bacci sosai me cikinsu.


Hakan datayi yasashi hade goshinsu Yana rintse idanuwansa daqyar ya furta sunanta cikin wani irin sauti dayasa baccin sakinta ta bude idanuwanta fes akan fuskarsa dake ha'deda tata fuskar tanajin zafin numfashinsa na shigarta direct batasan lokacinda itama ta lumshe idoba Saidai kafin ta bude taji bakinsa cikin tsakiyar nata ya kamo harshenta.


Ji yayi ta sake ajikinsa alamar some masa zatayi Saidai bai sauraraba Dan shima tuni control dinsa Suka some.


With passion yake kissing dinta cikin sanyi da nutsuwa 

Ahankali hannunsa ya nufi cikin rigarta data 'dan kwashe dama ya shafo shafaffen cikinta Wanda hakan yasata Jan numfashinta sama da qyar tana qanqamesa sbd sanyin harshensa da qamshin U-FRESH BUTTER MINT dake tashi abakinsa.


Gefen cikinta daya shafo yasa ta dauke numfashi tareda damqe gefen cikinsa gurin bayansa Bata saniba Wanda hakan ya qarasa tayarda dukkanin tsigar jikinsa

Ya zame rigarta gabaki daya tareda sakata gaba daya cikin jikinsa sbd zuwa lokacin sosai tsoronta ya bayyana jikinta ko tsayawa bayayi sbd tsananin rawa shiyasa yayi saurin yimata rumfa da fadaddan qirjinsa Saidai hakan ya qarasa kunce masa komai Dan kuwa qirjinta da Babu Kaya dayake gugar qirjinsa take ya fara daukar zafi zafi Yana qarasa Bata tsoro,


Hannunta daya damqa lokacinta laushin fatar qirjinta ya shiga dayan hannun nasa wani nishin azaba tasaki sbd ta dauka hannun ya karye.


Tsananin tsorone dajin yanda dukkanin qarfinsa yakawo jikinsa yasata fara kuka amatuqar tsorace tana neman qwacewa Saidai Sam ko alamar matsar dashi batada qarfi yi sbd qarfinsa.


Ihu takeson yi Saidai batada maqoshi

Shure shurenma takasa musamman dayake batada komai ajikinta.,


Kamar zaiyi hauka haka yakoma Mata sai tsoronta da tashin hankalinta ya ninku tana ihu baya fita musamman dataji kamar qasusuwan jikinta na kakkaryewa wani mahaukacin cizo ta sakar masa adaidai lokacinda komai ya cika aikinsa

Atake ta sake jiki agurin.
Ruwan na kashe kansa ya juye a flask tareda sake fasa wasu pure water din ya zuba a cattle din ya dauki qaton flask din ya fice.


Bahon iya talatu ya dauka yakai bayin ya juye ruwan yadawo ya dauki sauran na cattle din Suma yaje ya juye.


Daukarta yayi sukutum ya nufi bayin ya tsomata aciki sai alokacin ta bude idanuwanta daqyar ta kallesa da idanuwanta dake gani bishi bishi.


Tanaji tana gani yayi Mata komai Suka dawo dakin ya kwantarda ita yakoma yayi wanka sbd har antayarda sallar asuba lokacin.


Yana fitowa daureda towel a qugu abinda bai taba yiba a gidan Saidai ganin asubace yau din Kuma yasan Babu kowa barema yaune Karo na farko a rayuwarsa daya taba wankan asuba sukayi kicibis da kawu yafito.


Kallonda kawun ke masa yasashi dauke Kai akaro na farko rayuwarsa dayaji kunyar kawun sai kawai ya sake tamke fuska ya wuce jikinsa na tsiyayar ruwa.


Kawun ji yayi jikinsa yayi sanyi yakasa cewa komai bare qwaqwaran motsi da bin bango yashiga bayin yayo alwala yafito sallar anriga an sallame Saidai yayita a dakin talatu.


Baidawoba Saida gari yayi sosai sbd karatun qur'ani daya tsayayi.


Koda yashigo bacci takeyi sosai akan daddumar datayi sallah gabaki daya gabobin jikinta ciwo sukeyi tanajin kamar akwai gwafcewar qasusuwa a gabobinta.


Daukarta yayi ya mayar kan katifa ya rufeta da bargo yau shida alee dikko zasuje Lagos Amma ayau din zasu dawo sbd jirgi zasubi.


Wanka yayi ya shirya cikin qananun Kaya duka black sbd dama yawancin kayansa black ne sbd suke qara fitoda haskensa da kyawunsa.


Cikin gidan ya nufa lokacin qarfe takwas Babu kowa ya nufi dakin zainab shima akaro na farko tun bayan rasuwar mahaifiyarsa rabonda yasake ko zuwa qofar dakin.


Cikin muryarsa mai amo yakira sunanta dama idonta biyu tayi saurin wuntsilowa cikeda tsoro da mamakin yau Yaya Zaki da zuwa qofar dakinta harda Kiran sunanta.


Kamar munafuka ta fito dakin tana Dan sosa Kai tace"


Yaya Zaki Ina kwana?


Bai amsaba Kai tsaye yace"


Ki kulada ita batada lfy zanyi tafiya.


Jinjina Kai tayi da sauri sbd tuni kwarjininsa yagama kashe bakinta.


Kudi yaciro daga aljihunsa ya miqa Mata yace"


Kuyi cefanan koma meyene ake abinci dashi.


Karba tayi hannuwanta na rawa idanuwanta na kan hannunsa na dama gurin damtsen da aka nade da bandage alamar ciwone agurin.


Harya fice Bata dawo hayyacinta ba tanajin wlh Yaya Zaki yayi tako Ina inama itace akaiwa wannan auren dashi da wlh tagama mijinda ko 'yar shugaban qasa batadashi.


Tana dawowa hayyacinta tayi dakinsu nadiyar da gudu saidata fara leqo waje ta tabbatarda ya wuce kafin ta fada dakin.


Ganin yanayin kwanciyar nadiyar da yanayin fuskarta da har wani fadawa tayi yasa tasan lallai ciwon na gaske ne.


Bata tashetaba takoma cikin gida tahau 'yan ayyukanda tadan fara sabawa dasu.


Harta gama duka ayyukan nadiyar Bata tashiba koda Takoma dubota ta tararda ita zazzabi sosai ya saukar mata sai kuka takeyi ga jikinta ko motsawa batason yi ciwo koina ke Mata.


Hankalin zainab bai qara tashiba saidataga nadiyar nata kelaya amai ko ruwa takasasha.


Tadawo da ita cikin gida dakinta 

Iya talatu ma hankalinta yatashi da Aman da nadiyar ketayi gashi ko motsi batason yi 

Ita kawai saima tayi tunanin cikine da nadiyar Aiko taje ta fadawa babansa Yana Shan shayin safe sai gani tayi ya sarqe haryana biyo masa ta hanci a masife ya dago yace"


Dama nasan bakya kaunar ganina talatu basaikin sakamin ciwon zuciya na mace abanxa ba,

Ciki Kuma aidama nasan can akayi su Suka sani ba abinda ya shafeni iyakaci dai Babu wani Dan tawayen da za'a Haifa a gabana ya Kuma girma a gabana yace zai rainani ban fasa kan uwarsaba kowama ya huta.


Itadai tafiyarta tayi bayan tafada masa tabarsa Yana zuba masifarsa duk qaunarsa da shayi ji yayi yafita ransa ya miqe Dan zuwa fadawa amininsa Dan uwansa ya jajanta masa wannan alamari.


Gabaki daya yinin rikice musu tayi Saidai harga Allah Sam Basu kawo tunani ko ganin alamar wancan abin ne akayiba sudai sunma rasa gane wane irin ciwon gabobine ke damunta.


Sai yamma sosai taji Dan dama dama Zainab tadora Mata ruwan zafi tayo wanka ta saka doguwar rigar kanti tayi sallolinda bataiba daqyar Tasha tea taci tuwon shinkafarda zainab tayi da Naman kajinda Nanu yakawo da Rana.


Tana cikin cin tuwon akayi magriba tana gamawa takuma wata alwalar tayi sallah.


Shiru tayi kwance Jan dadduma tana tuno irin azabarda Tasha idanuwanta Suka ciko da hawaye musamman idan ta rufe ido tanajin hannuwansa na yawo ajikinta saitayi saurin budewa tana sake tunosa da abinda ya wakana.,

Ita yanzuma wani tsoro da fargabar ganinsa takeyi.


Har bayan ishai bai dawoba har tayi bacci bai dawoba.


Qarfe goma harda arbain yadawo gidan a gajiye yake sosai Amma Saida yayi wanka da ruwan zafi yazo ya kwanta kusada ita tareda shigewa jikinta ya qurawa fuskarta ido ahaka bacci ya daukesa.


Washe gari data farka tagansa dunqule cikin jikinta saitaji duk jikinta yayi sanyi ta lumshe ido tana qarajin saukar numfashinsa a qirjinta.


Ahankali ta zame taje tayo alwala tana sallah ya farka dayake yayi sallarsa tunda asuba saiya kalli gefenta kadan tareda saukowa ya nufi wardrobe Yana cewa"


Ki shirya yanxu nan.


Kasa kallonsa tayi ta miqe tareda kuye ruwan zafin cikin cattle ta fita.


Wanka tayo baya dakin Yana waje gurin yaransa ta shirya cikin riga da skirt da atampa da hijab dinta sabo.


Tana cikin Shan kununda zainab takawo Mata yashigo ya tube yaje yayo wanka ya shirya ya fita tana bin bayansa kamar munafuka.

 

Nanu ne ke jan motar shi Yana gaba ita kadai abaya Suka wuce su dattiya na zaune qofar gidan mal idi Suka bisu da ido baki sake.


Cikin habbaka zance mal idi yace"


Kaiiii wlh dattiya yaran nan sungama rainaka,

Yanxu agabanka wannan yaron ya wuce da 'yarka ko kallon inda muke basuyiba bare a 'dan cemaka zamu wuri kaza.


Cikin takaici dakecin dattiyan yace"


Kabarsu duk maganinsu zanyi kowama ya huta har ita talatun Mai kama musu iskancin,

Ita wannan Mai zubin ruwa ruwan aljanu zanyi maganintane lokacinda wannan Mai qirar samudawan yagama da ita Dan kuwa har sarkin 'yan iskan garin Lagos daidai nake dashi bare ubansa bare shi.Asibitin Dr sayyid Suka nufa dayake dama sunyi magana a waya tun jiya Kai tsaye office dinsa Suka nufa.


Yana ganinsu ko zama ita batayiba yakira nurses ya miqa musu takardun test test dinda yakeson suyo Mata shida kansa zai Mata hoto.


Ahankali yafara korowa Zaki bayanin irin yanda yake sakaran matsalar tata yake Yana sake tabbatar masa da zatai magana Nanda sati biyu idan akai Mata aikin.


Mintunansu talatin Suka dawo tareda nurse din ta miqa masa results din ya karba ya duba Yana jinjina kai.


Kallonta yayi fuskarsa a sake yace"


Nadiya kinaji wata Rana idan kika bude baki kamar Zaki iya magana????


Ahankali ta daga masa Kai batareda ta dagoba 

Shidai Yana zaune fuskarnan a tamke Yana amfani da wayarsa.


Tambayoyi Dr sayyid yayi Mata sosai kafin Suka nufi dakin hoto da ita akasaka Mata wani Abu a maqoshi da bakinta tsawon lokaci kafin likitocin Suka gama rubuce rubucensu Suka dawo office din Dr sayyid din.


Bai masa wani cikakken bayaniba yace sai angama yimata awo da hotuna tsawon kwana hudu kafin a tabbatarda akwai yiyuwar aikin ta warke ko kuwa Babu chance.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_ALLAH UBANGIJI YAJI QAN DADDY YA GAFARTA MASA YASA ALJANNA CE MAKOMARSA🙏_*

*_NANA HAFSAT MISS XOXO ALLAH YAQARA BAMU HAKURIN JURE WANNAN RASHI AMIN_*
*_Mamuhgee24_*

Da daddare da zazzabi sosai ajikinta tayi bacci Saidai kowa a gefensa ya kwanta yau ko magagin matse masa batayiba 

Shima ganin yaninda take ciki na zazzabi sosai dakuma yanda tsoronsa qarara yake tareda ita yasa ya dauke Kai bai wani tsaya ko kulataba.


Washe gari qarfe takwas Suka Kuma zuwa asibiti wannan karon da Zainab sukaje sbd 'dan taimaka Mata da yanayin mutuwar jiki da zazzabinta ke sakar Mata sosai.


Sai azahar Suka dawo gida daga asibitin yauma gwaje gwaje da hotuna akai Mata.


Kwanansu biyar suna yawon asibitin aka gama komai Suka dawo gida Saidai sosai take lureda yanayinsa tunda yafito daga office din Dr sayyid inda Suka gamo maganarsu.


Ganin yanayin nasa yasa tunda Suka dawo takasa walwala jikinta yayi matuqar sanyi Saidai batada baki ko iko bare samun fuskar tambayarsa.


Da daddare ma tana lureda baiyi wani bacciba itama saita kasa baccin ta lafe shiru tareda saddaqarda bazata taba yin maganaba tunda tagansa haka tun kebewarsa da Dr sayyid.


Jitayi idanuwanta sun ciko da hawayen tausayin rayuwarsa da aka maqala masa bebiya irinta.


Rintse idanuwansa yayi tareda budesu sunyi jajir sbd tension da halinda zuciyarsa ke ciki,


Tsawon rayuwarsa bai taba tambayar kowa kudiba 

Alee dikko ma Saidai kawai ya ringa ganin transfer dinsa cikin bankinsa batareda ya tambaya ba sbd izzarsa bazata taba Bari ya roqi kudi ko tambayar kudiba Saidai baisan ta Yaya zai samu kudin aikin daza'ayi mataba Wanda zai biya naira miliyan biyu harda 'yan Kai,

Ya duba cikin account dinsa duka duka dubu dari uku da saba'in ne aciki gashi yariga yasa antura gayyatar likitan dazaizo yayi Mata aikin daga qasar India ranar lahadi zai iso ranar talata ayi Mata aikin Nanda kwana hudu zuwa biyar kenan,

Yayiwa ummansa, JJ dinsa da kansa alqawarin nemar Mata lafiya indai yanada Rai da lafiya gashi damar tazo Amma baisan ta Yaya zaiyiba.


Idonsa biyu har akayi Kiran sallar asuba ya miqe ya fice yashiga bayi yafito yayi alwala yazo yasaka riga yafice.


Tashi zaune tayi bayan fitarsa tareda rafka tagumin cikin tsananin damuwa tana Jin zafin ganinsa a wannan sabon yanayin damuwar.


Jiki ba qwari taje tayo alwala tazo tayi Sallah tana nan zaune yazo yayi wanka ya fice ko karyawa baiyiba.


Baidawo gidanba sai dare Kuma ganinsa kamar a tsananin gajiye yasake Bata tsoro 

Haka ya kwanta baici komaiba washe gari ma tun safe yasake ficewa.


Cikin kwana biyu ya daina zama idan yafita tun safe sai dare Kuma sosai hankalinta yatashi sbd akwai abubuwan rayuwarsa daya saba Yi yanxu duk baida lokacinyi musamman morning exercise da baya taba fashi Amma yanxu Sam baida lokaci tuni stress yasa idanuwansa mugun fadawa sbd baisaba da wahalaba kullum a hutu yake komai yaransa ke masa.


Kawu Dattiya dayake lureda hakan shima sai yaji hankalinsa yakasa kwanciya da hakan Dan kuwa duk tsamarda da zakin bayason abinda zai tabasa a wani gurin.


Tun tana boye damuwarta har zainab tagane take Dan Bata shawara ahankali sbd abune da bakada ikon tambayar lafiya.


Ana washe gari Dr agrewal zai sauka yaji dukkanin notikan kansa sun kunce gashi asibiti sun taso masa sosai akan yayi depositing sauran cikon kudin aikin sbd Dr agrewal bai tasoba Saida yayi depositing duka 350 thousand dinda ke account dinsa yabar dubu ashirin wadda itama saura dubu Tara acikinta,.


Duk wahala da zagayen neman aikinda yayi a kwana hudun Bai samuba sbd yaso yasamu aikin saiyaci loan din banki ya biya.


Yawo yayi yarasa Ina zai saka ransa 

Zuciyarsa da kansa kamar zasu buga sbd tension da tashin hankali Dan baisan ya zaiyi dasu Dr sayyid ba da Dr agrewal da akasashi tasowa daga wata qasar.


Har Rana ta fadi Yana yawo cikin garin neman aiki 

Farar fatarsa tayi jajir sbd baqar wahala,yunwa da azabar yawonda Bai sababa sbd a jiya yasa Nanu aka siyarda motar ya qarawa asibiti dubu dari uku Suka zama shida da hamsin.


Ana Kiran magriba ya tsaya wani masallacin juma'a yayi sallah yana gamawa ya zauna shiru Yana tunani bayan yagama fadawa allah.


Kudin aljihunsa ya tunada saura qalilan Dan kuwa kusan dubu uku harda dari biyar ya kashe a yawon napep din neman mafita.


Yana zaune cikin masallacin shiru yayi nisa a tunani har akayi Kiran sallar ishai ya miqe jiki ba wani qwari yabi sahu akai sallar.


Bayan anga sallar anfara ficewa shima ya miqe ya fito ya nufi titi ya tare abin Hawa Suka fara tafiya.


Me gida Ina zamu? Mai adaidaitar yafada Yana tuqi.


Kai tsaye yace"


DILLA Mansion zaka kaini.


Dayake duk Wanda yake zaune dai acikin garin yasan Dilla mansion Kai tsaye ya nufi can.


Tafiyar mintuna goma Sha takwas takawosu Saidai kasancewar akwai tsaro tundaga farkon layin gidan yasa Mai napep din tsayawa daga farkon anguwar sbd baa Bari adaidaita ko mashin ko taxi na zuwa kusa.


Dari biyu yaciro yabasa ya wuce ya nufi layin.


Sanin ko wanene shi agurin alee dikko Dilla yasa securities da police din gurin Suka bubbude masa checking point din dake tattareda gurin suna gaishesa cikeda mamakin ganinsa a napep yau.


hannu kawai yake iya daga musu sbd ciwonda kansa keyi masa bayason ko bude baki bare wata doguwar  magana.


Main babban gate din shiga mansion din ya iso Suma suna ganinsa sukai saurin bude masa ya shiga Kai tsaye ya nufi babbar glass door dinda ta killace qofar shiga palon baqin alee dikkon na musamman.


Yana Isa qofar aka bude masa yashiga daidai lokacin alee dikko na sallamar wani babban ma'aikacin kudinsa sai Kuma AM dilla dake zaune suna tattaunawa tare sbd 'yar matsalarda aka samu akan takardun buga asalin kudin da alee dikko yadau tsawon shekaru Yana buri,nema tareda alwashin samu Dan bayanan yanda zai buga asalin kudin gaske suna cikin takardun shine aka kama Wanda suka saka aikin satowar Kuma gwamnati tabada umarnin kashesa nan take sbd abune Mai matuqar ha'dari.


juyowa sukayi dukkaninsu tare suna kallon qofa ganin alee dikko yasaki wani murmushin samun nasara ya dauki tobacco dinsa yana kunnawa cikin alfahari yace"


My lion koyaushe kana zuwa a gabarda Dole anemeka sbd kaine sarki,my lion,my champion my hero

Qaraso sbd Kaine kadai kasan mahimmanci aiki kowane irine kayisa batareda ansamu matsalaba ba kamar wainnan bunch of fools dinda natara nake kashewa kudi a banxa ba.


Cikin wani irin izzarsa da kwarjininsa daya gama cika musu palon ya qaraso ya tsaya tareda zuba hannuwansa cikin aljihun wandonsa Yana kallon alee dikko Kai tsaye yace"


Naira miliyan biyu nake buqata a yau nikuma kafadamin inda takardun suke zan dauko ma.


Wani shu'umin murmushi dikko Dilla  yasaki tareda daukar cup din tsadaddiyar whiskey dinda ke gabansa ya kurba tareda aje tobacco din hannunsa cikin glassbw dinda ke kan table din gabansa batareda ya dagoba yace"


Hmm you know I always admires ur courage and confidence

But open your eyes lion this is not an ordinary papers daka sani King.


Zaki daya gama qarewa dikkon kkallo cikin ko 'dar da zancensa 

Cikin Isa da muryarsa mai amo yace"


Are you inn for the deal or not????


Wani murmushin dikko Dilla yasake saki tareda miqewa shima suna fuskantar juna da zakin ya kalli cikin idanuwansa yaga he is hundred percent serious sai kawai ya juya ya kalli Am daya miqe tsaye shima Yana aikawada zakin kallon qasqanci da fatar yaje din sbd sun mugun Dana masa mummunan tarko dama sunata jiran hanyarda zasu turasa samo takardun saigashi yazo da kansa.


Cikin murmushi dikko yace"


Am abani cash sbd wannan shine deal mafi girma arayuwata Wanda Kuma shine deal na farko dazanyi da my king.


Jakar kudi guda am yakawo gaban dad dinsa ya ajiye tareda xuge jakar kudin ya dire ganan Zaki ya dago Suka fuskancesa yace"


5million in cash gasunan 

Idan Rana ta fadi gobe baka kawo waiinan takardunba 5million a bakacin ran matarka da naka.


Idan nikuma nakawo deal ya sauya ko Ina nan kobana nan kasani har abada bazan bariba sainayi settling scores  agabanka zan yanka wuyan dikko na shayarsa bingo jininsa that's a promise ka rubuta ka ajiye and one scratch a jikin matata ko familyna sunan dillas gabaki daya saina shafesa a doron qasa.


Daukar jakar kudin yayi ya juya tareda cewa"


Send me all the informations da details a Daren yau ta wayana.


Bayansa sukabi da kallo harya fice zuciyarsu na 'dan girgiza tareda 'yar fargabar double crossing dinsa dazasuyi Saidai sunsan waye Zaki idan harya tsallake to sungama yawo barin Nigeria zasuyi tunda sumsan Bai Tara kudinda zaibisu wata qasarba yayi farautar rayuwarsu.


Dikko yasaki wani malalacin murmushi tareda daukar cup din gabansa yace"


Lion lion,,,I wish I can tell idan zakaje kafarayin bankwana da familynka sbd bazaka sake ganinsuba har abada Kuma.,,

Am ka tabbatarda gobe kafin kafin fitowar alfijir nagama da maganar lion gabaki daya saikuma familyn bujuwa da gwamnati tasa aka kashesa suma arufe chapter nasu sbd akwai yiyuwar bujuwa ya sanardasu wani Abu akan hakan so I can't take any risks just finish them all.


Wani barin takardu aqeel dake palon harsun manta dashi yayi jikinsa na Dan rawar tashin hankalin yanda ake lissafin Wainda za'a kashen.


Atare Suka kallosa Dan harsun manta dashi dikko ya dagawa am Kai tareda daukar wayarsa ya Danna Kira.


Wata qaramar pistol am ya fitar daga cikin hannun kejerar palon yace"


Sorry Prof aqeel kaji da yawane ba yanda zamuyi sai hakan.


Harbesa yayi tsakiyar zuciyarsa tareda mayarda pistol din ya daga waya yakira securitynda shine kawai yasanda wannan aikin nasu yazo su biyu suna qoqarin fita da gawar zeel tashigo cikin taqama da wani irin Jan girma kallo daya tayiwa jinin dayake kwance gurin ta daure fuska cikin fada tace"


Am so nawa zance ku dainamin irin wannan Wasa da jinin cikin gida I just hate blood wlh.


Juyawa tayi ta fice tana sake masifa sbd Sam ita Babu ruwanta da kashewar,jinin ne batason ana zubarwa acikin gidan gwara suje inda Suka Saba sbd 'yar gaban goshinta datake gari tazo hutun makaranta daga Amsterdam ta tsani ganin jini ko kadan dakuma irin hakan dasukeyi Dan tana gani zata iya juyawa gobe tafasa musu hutun.

Bayan fitowarsa Kai tsaye adaidaita yakuma Hawa tareda dafe kansa idanuwansa na qara nauyi sbd Jan dasukai,

Cusa hannuwansa yayi cikin sumar kansa tareda yiwa Mai napep kwatancen gidan Dr sayyid Suka nufi can.


Har cikin Palo Dr sayyid yamasa iso sbd yawanci haduwarsu duk asibiti suke yinta sbd zuwa lokacin sun Saba Sosai sbd bayan JJ Dr sayyid ne yakejin ya yarda dashi akan alamarin daya shafi familyn shi.,


Jakar kudin ya dire gaban Dr sayyid batareda ya kallesa da idanuwansa dake wani iriba yace"


Miliyan biyar,

Miliyan biyar ne kacire kudin aikin Nadiya sauran kudin zanje wani a goben daza'ayi aikin bananan idan nadawo zan karba idan bandawoba ka bawa Nadiya da mahaifinta su....


Saurin kallonsa Dr sayyid yayi tareda sake kallon kudin yasake karanto tsananin stress da zakin ke ciki saidai Babu fuskar tambayarsa Dan fuskar tamke take kamar ko yaushe.


Cikin nutsuwa dr sayyid yace"


Kasan wannan aikin Dole Kaine yazama ace anyisa kana kusa sbd girma da mahimmancin dakafi kowa dashi akanta Kuma idan kayi tafiya a goben wayene zai tsaya a dukkanin alamarin idan wani Abu yataso.


Dauke Kai yayi Yana qarfafa jarumtarsa yace"


Dr sbd aminta dakai akan family na yasa nakawo maka wannan din Kuma kasani koban dawo yanzuba bazan taba barinka da nauyinsuba zandawo wata rana sbd matata tawace nikadai bazan taba barinta har wani yasametaba koban dawowa kowaba zandawo mata just promise me zaka kulada ita sbd maraicinta karka Bari komai na cutatarwa yazo gareta.


Kallonsa Dr yayi yasan abin ya girmama cikin sanyi jiki ya daga Kai daqyar ya furta insha Allah zan kula da ita kamar yanda nai maka alqawari.


6arin Kaya sukaji a wani daki dake palon Dr yayi saurin kallon qofar hankalinsa na tashi cikin ransa Yana cewa"


Oh allah kasa kada patient din nan yafito ko yayi magana sbd tun safe yau daya farfado bayan tsawon lokacinda ya dauka a kwance yake masa surutan wani sarki shi baima gane maiyake nufiba kawai dai bayason asan yasamoshi sbd yin amfani dashi yayi bincike cikin sirri akan Dilla ya fallasa asirin asibitin dikko Dillan dake kashe bayin Allah basuji Basu ganiba ta hanyar mugayen qwayoyinsu marasa nagartaba batareda ansaniba.


Kallon Zaki yayi yaga ya qurawa qofar ido sbd sanin Dr sayyid shikadaine a gidan tunda baida aure, 

Saurin nufar qofar Dr sayyid yayi Yana cewa"


Sorry Bari naduba menene sbd nabar Mai gyaran ac aciki Yana aiki.


Shiga dakin yayi tareda rufowa harda saka key ya juyo da sauri ya nufi gadonda patient din yafado ya Gama dinkin gefen cikinsa da har yau yaqi warkewa Wanda dafin wuqarda ta sokesace take kawo hakan shiyasama har lokacin baidawo hayyacinsa ba yake akwance.


Daqyar ya mayardashi kan gadon tareda Dan gyarasa Yana gamawa yaga duk kayansa da hannuwansa sun 'dan baci da jini ya zaro ido tareda kallon qofar fita yasan zaki nacan na palon zai zargi wani Abu.


Toilet din dakin yashiga ya wanke hannuwansa da sauri tareda Dan goge jikinsa Saidai kayan jikinsa Sam Basu goguba sbd jinin yabatasune sosai.


Sharce zufan dayake karyo masa su yayi tareda yin shahada ya fito palon Saidai baisan lokacinda yasaki ajiyar zuciya Mai qarfiba tareda zama bakin kujera Yana mayarda numfashi sbd ganin zakin bayanan ya wuce.

#MAMUH*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_ALLAH YA GAFARTAWA DADDY YAJI QANSA DA RAHAMARSA AMIN🙏_*
*_Mamuhgee25_*

Tsaye take tana nade hijabinda tagama sallar ishai da akayi tuntuni Saidai tana gurin zainab kwance hakanan takejin batada qarfi ko kadan sbd yanayi da damuwa da faduwar gabanda take yawan samun kanta aciki saita alaqanta hakan da halinda take ganinsa kwanakin sai jikinta yake qarayin sanyi.


Aje hijabin tayi tana dagowa Yana shigowa dakin cikin sallamarda tajiyo qasan maqoshinsa.


Juyowa tayi ahankali ta kallesa idanuwanta na cikowa da hawayenda batasan na meyene ba Saidai Sam Bata iya hanasu saukowa kan fuskarta.


Dauke Kai yayi Jin garkuwan jikinsa zai karye da ganin hawayen nata ya qaraso ahankali tareda tsayawa gabanta baice komaiba yajawota jikinsa ya rungume batai wata wataba ta qanqamesa tareda sakin sauran kukan dayake son zuwar Mata tun yinin ranar tana riqesa.


Sunjima ahaka baiyi yunqurin  rarrashinta ba hartayi shiru tana ajiyar zuciya ahankali Saida shima yaji nutsuwa ta shigesa ya saketa ahankali tareda nufar wardrobe ya dauki towel ya zare rigarsa ya fice.


Jinta abayansa yasashi Dan dakatawa Bai juyoba 

Ita Kuma Kai tsaye ruwa ta zuba masa a bokiti ta dauko flask ta zuba na zafi ta kashe masa sanyinsu takai masa bayin tafito.


Harya dawo daga wanka ya shirya dagashi sai wandon bacci Mai santsi yazo ya kwanta cikin jikinta ahankali tareda rufe ido dukkansu sukai shiru kamar sunyi bacci Saidai Babu Wanda yayi baccin acikinsu.


Ahankali ya zagayeta da hannuwansa jikinsu ya hadu sosai sbd rigar jikinta data gama lafewa ajikinta kamar Babu Kaya.,

Fuskarsu ya hade guri guda suna shakar numfashin juna wasu sabbin hawaye Suka ciko idonta yajin duminsu a fuskarsa ya hade bakinsu da juna Yana Bata wani irin deep intimate kiss dayasa hawayenta qarasa gangarowa tana sake shigewa jikinsa gabaki daya.


Da asuba tana goge qoqarin zuwa wanka ya riqota tareda zame zanin jikinta tayi saurin rintse ido tareda shigewa jikinsa 

Ya saki wata irin ajiyar zuciyar datasata Dan bude ido ta kallesa taga wani irin kallo yake Mata ko qyaftawa bayayi ta fada jikinsa tareda sake qanqamesa tana Jin jikinta na rawa.


Towel dinsa ya jawo ya daura Mata ya jawo hijabinta ya sanya mata yaja hannunta har bayi tayo wanka ta fito kafin shima ya shiga itama ta tsaya masa Suka dawo dakin tare.


Tunda yatafi masallaci Bai dawoba Saida gari yadan fara haske Yana zuwa ya shirya cikin wani leader trouser black da black shirt da facing cap Yana kallo itama ta shirya cikin doguwar rigar atampa black and blue tareda dogon hijabinta har qasa milk.


Hannunta ya riqo takasa dagowa ta kallesa ahankali ya furta kije kiga idan sun shirya su fito muje.


Cikin gida ta nufa nan ta tararda zainab ta shirya hakama iya talatu dama babansu tuni ya shirya ya kafe qofar gidan jiran sufito atafi Dan suk sunsan da yaune ake zuwa asibiti aikinta.


Shida Nanu Suka hau napep daya zainab da iya talatu tareda Nadiya ma guda daya Suka hau kawu da amininsa da qut suka hau nasu.


Tunda Suka Isa asibiti Dr sayyid yasa aka shige wani daki da ita hankalinta yatashi musamman lokacinda zasu shige tana kallon yanda duk su babanta Suma sukai wani iri hankalinsu a 'dan tashe Saidai kowa daurewa yakeyi.


Bayan qasu gwaje gwajen da rubuce rubucensu aka kaita wani Ward inda babu kowa sai ma'aikatan asibitin kawa Suma sai qwararrin asibitin.


Kaya aka Bata ta canza zuwa na tiyata  ta zauna tsakiyar gadon dakinda take tana qoqarin danne kukanta da rawar da jikinta keyi taji anbude qofa ahankali.


Zaki ne da babanta batasan lokacinda ta fashe da kukan datake riqewaba  tana kallonsu tana Kuma Jin dadin ganinsu ataren.


Ahankali yaqaraso ya zauna kusada ita tareda riqe hannunta daya ya matse cikin nasa Yana kallonta ahankali ya sakar Mata murmushin dake sumar da ita Saidai yau din Bata sumaba ta sauke Kai tana sake sabon kuka.


Dattiya ma sanyi jikinsa yayi ya kalli hannuwansu dake sarqe saiyaji kamar ya saka igiya yasake daure musu hannuwan karsu rabe juyawa yayi ya fice jiki ba qwari.


Dafa kanta yayi ya jinjina Mata Kai tareda ficewa shima.


Dama anriga andibi jininsa daza ayi amfani dashi angama komai saisuka zauna zaman jiran tsammanin man rabbuka shikuwa ficewa yayi bayan yaga komai ya kammala har anwuce da ita gurin aikin.


Zaman jugum jugum Sukayi Babu Mai walwala ko doguwar nutsuwa acikinsu sbd Basu taba zaman jiran tsammaniba arayuwarsu kaf dinsu sai yau musamman dattiya da sai yaune yaqara sanin irin sonda yakewa 'yarsa Dan kuwa yau karatun alqur'aninda ya manta rabonda yayi Saida yaje masallacin asibitin yayi shidai wlh dama yasani bazai yarda da wannan aikinba gwara abar masa 'yar tasa ahaka tunda ba ido da qafa ta rasaba.


Bayan dogon yinin dasukai gurin jira anfito da ita anyi aiki cikin dibbin nasara suna fatar zuwa Nanda kwana biyu zata iya fara magana idan gurin ya warke ya qame.


Murna da hamdala suka ringa yi Saidai har lokacin zakin Bai dawoba gashi har anyi magriba Babu ko duriyarsa.


Zainab ce ta kwana agurinta Bata farfadoba sai washe gari da safe koda babansu yazo yasake tambayar ko Zaki yazo nanma zainab tace har yanzu dai.


Ahankali Abu yayi tsamari sbd har yini yakuma shigewa Babu zakin tun suna dannewa har Abu dai yafara fitowa sbd dai Bai taba irin hakaba yayi tafiya Babu sanarwa ko yaransa.,


Nadiyarma daurewa kawai takeyi tana boye damuwarta Saidai Sam batada walwala musamman dataji maqoshinta yayi sakayau tanajin zata iya magana Saidai batason yi

Sunansa takeson fara Kira agabansa sbd shi takeson yafarajin sautin muryarta ko Yaya take.


Kawu Dattiya duk inda hankalinsu Nanu yake ya daga musu akan suje sunemo inda zakin yake nan Suka bazama Suma gashi wayarsa Sam Bata shiga.


Dr sayyid sosai ya tausayawa Nadiya sbd shida yake dubata Yana auna jininta yasan yayi mugun Hawa sbd tsananin damuwa da tsoronda ke ranta na Rashin Jin inda yake.


Yau kwana biyar da aikin Babu labarinsa kuma yaune aka gwada maganarta akaji ta fito Ras tana iya magana Sosai Dr sayyid yayi farin ciki da wannan nasarar dasuka samu Saidai su murnarsu ragaggiyace sbd halinda suke ciki.


Ranarda aka sallamesu da safe zainab na hada musu kayansu jiki sanyaye ita Kuma nadiyar na zaune gefe tayi zuru idanuwanta sunyi jajir tayi nisa cikin tunani.


Cikin tsananin tashin hankali babansu yashigo yakallesu kafin ya tsaida idanuwansa kan Nadiya datayi nisa cikin tunani duk saiyaji hankalinsa yayi mugun sake tashi saiya kasa fada musu abinda ke faruwa ya fita inda yayi karoda Dr sayyid dake qoqarin shigowa shima hankalinsa tashe.


Riqosa baban yayi tareda girgiza masa Kai yace"


Karka sanarda ita yanzu.


Wani sabon sanyi jikinsa yayi da tausayin nadiyar ta yanda qaramar yarinya kamarta zatayi takabar Rashin mini da shekaru qanana.


Zainab ce ta riqo hannunta Suka fito har cikin motar Dr sayyid Suka nufi gida Babu Mai magana cikin motar sbd kowa baida dadin zuciya.


Suna isa gida nan ta tararda qofar gidan cike da dukkanin wani yaran Zaki dake jahar komai ita Bata wani ganewa sbd nisan datayi a tunani da damuwa.


Daki zainab ta zaunar da ita ta fito inda taga su iya talatu zaune kamar gidan mutu ta qarasa gaban iya tana kallonta kafin ta kalli babansu da Yaya dahiru daya shigo gidan Yana cire hular kansa cikin wani irin yanayi yace"


Wlh duk hanyar dazanbi Dan nasamu ganinsa a can babbar headquarter da aka rufesa an hanani ganinsa gashi gobe zaa shiga kotu dashi kafin a yanke masa hukunci gashi akwai harbi a jikinsa sbd jamian tsaro sun harbi gefen kafadarsa lokacinda Suka kamasa.


Cikeda tashin hankali zainab ta zube qasa tana neman fashewa da kuka sai kawai sukaji faduwar Nadiya daga bayansu.


Hankali tashe sukayo kanta kowannensu na Kiran sunanta.


Tana bude idanuwanta dasukai jajir ta kalli kowannensu tanason yin kuka Amma takasa sai kawai ta miqe ta shige daki ta sulale qasa sai alokacin kuka Mai qarfi yazo Mata zainab tayi saurin zuwa ta rungumeta itama tana hawaye sbd Zaki bashine gatan nadiyar kadaiba dukkaninsu shine gatansu.***

Cikin tsananin zafi da tension na tashin hankali alee dikko ya kalli am

Muryarsa na tashi da zafin da ransa keyi yace"


Kasan me missing target akan Zaki yake nufi kuwa????

Yana nufin ran uban da ran uwarka da Kai kanka,

Ya za'ayi kace Kunyi missing harbinsa bayan agabanka na karbi takardun a hannunsa Kuma kanaji nagama fada masa duk wani sirrina ciki harda mutuwar ubansa da nine nasa mota ta takasa naso ya mutu a lokacin Amma bai mutuba na barsa ya qarasa  mutuwa da kansa.,,,

Hw cud you Am,


Juyowa yayi ya kalli zeel da itama hankalinta ya yashi da jajayen idanuwansa a fusace yace"


Kinajin abinda good for nothing son dinki yayi he always disappoint me a duk lokacinda nasakasa muhimmin Abu sbd yaga Ina sonsa fiyeda komai 

Nan ana magana akan rayuwarmune mu sbd matuqar ya fito wlh duk kuyi ta kanku Babu Wanda bazaiyi mutuwar wulaqanci a gurinsaba.....


Cikin tension zeel tace"


Idan kuwa hakane wlh bazai fito ba bazaikai gobenba bare yasamu damar fita wannan case din acikin Daren nan yakamata adau mataki.


Kallon am tayi tace"


Ka gyara wanan abin dakukayi acikin Daren nan kaje inda aka tsaresa offer them a huge millions of dollars kawai su bari ku qona dakinda yake ya qone ya mutu chapter closed.


Daga Kai am din yayi cikin gamsuwa da zancenta hakama dikkon ya gamsu da wannan ya juya ya wuce Yana cewa"


You better not make any mistake wannan karon.Cikin Daren duk Wanda yace ya rintsa acikin gidansu zakin yayi qarya musamman iya talatu da babansu dasuke dauka ciki ne da ita kamar yanda iya talatu ta fada shiyasa abin yafi damunsu akan nadiyar da abinda ke cikinta.


Itadai tana zaune tsakiyar daki ta Dora kanta kan katifa duk da kasancewarta anmata aiki tana iya magana Saidai hakan baida wani amfani a yanxun sbd ko kalma daya har lokacin takasa furtawa sai idanuwa datake bin mutane dasu.


Tun cikin Daren takejin wani irin nauyin zuciya da rawar jiki na shigarta sbd jin goben zaa yanke masa hukunci dabatasan ya rayuwarta zata daukesaba.


Da asuba daqyar tayi sallah sbd ko tsayuwa Bata iyayi jiri take ganin sbd tsananin tashin hankalinda zuciyarta take ciki.


Qarfe bakwai na safe ko qarasa bugawa batayiba Yaya dahiru yashigo gidan hankalinsa amatuqar tashe yazoda mummunan labarin wutar data tashi cikin dare ta cinye komai qurmus a bangaren cell dake ciki babbar headquarter ta police force kusan mutum hudu suka rasu ciki harda zakin Wanda akace zuje su karbi gawarsa.


Wani duhu dattiya yaga ya rufe idanuwansa na jininsa daya hau nan take ya yanke jiki agurin.


Nan iya talatu da zainab Suka saki ihun kuka suna Kiran sunansa Nadiya dake daki tanajin abinda ya fada ta rufe idanuwanta a hankali tareda Jin wani Abu yataso daga cikin jikinta ya tokare a maqoshinta kukan ma Sam takasa jinsa sai jikinta dake wata irin rawa idanuwanta na ganin duhu duhu.


Tana gurin batasan lokacinda ta dauka Bata hayyacintaba Saida taji zainab na jijjigata tana Kiran sunanta cikin tsananin kuka tace"


Nadiya kiyi hakuri da tawakkali Allah zai saka Mana akan abinda akaiwa Yaya Zaki 

Amma yanzu Yana buqatar adduarmu ga gawarsa can an kawo.


Kallon zainab tayi kamar wata wawuya batareda ta iya magana ba sbd bakinta daya bushe har zuwa maqoshinta haka zainab ta kamota ta fito da ita inda gidan yake cikeda mutane har gaban gawar ta ajiyeta babansu dake gefen gawar Yana kukansa Babu boyo yakai hannunsa dake rawa ya bude qonanniyar gawar tareda sake fashewa da kuka su zainab ma kukan sukeyi sosai.


Miqewa tayi da sauri tareda ja Baya tana girgiza Kai sai alokacin hawaye Suka sauko Mata akaro na farko datai magana tace"


Wannan ba gawarsa bace,

Komai qonewar dazaiyi Ni zangane gawarsa,wannan ba ita bace 

Ko Yaya Zaki ya qone yafi wannan,

Ba gawarsa baceba........


Da sauri iya talatu da zainab Suka riqota ganin Sam ba a hayyacinta take maganarba ta qwace da qarfi tana kuka tace"


Ina cikin hayyacina ban haukaceba wlh wannan ba gawarsa bace ba......


Rirriqeta akayi ganin hauka tuburan na bayyana cikin maganganunta wasu kuwa tuni tafara Basu sabon tausayi sbd ganin zaucewa ce tayi.Ahaka akayi jana'izar gawar aka dawo nan aka cigaba da zaman makoki.


Sati daya da mutuwar ta koma kalar tausayi kowa tausayinta yafi damunsa yanxu Dan kuwa wata irin muguwar rama datayi gashi Sam Bata magana koyaushe tana dakin Zainab kwance kuka ma Sam ya qafe Mata sai hakan ya taba lafiyarta sosai duk da ma Dr sayyid yazo kusan so uku Yana dubata.


Yau akai sati biyu da mutuwar Nanu yazo yakawo Mata wasu takardun zakin da duk abubuwansa dake hannunsu sukai musu sallama kowa zaije yakama gabansa.


Wani irin kallo tai masa idanuwanta na cikowa da hawayen tafiyar tasu sbd sune Wainda Zaki keyiwa kallon danginsa na biyu haka Suma yawancinsu duk marayune zakin shine gatansu.


Tana kallo Suka taru kusan su talatin da hudu sukai Mata sallama Suka tafi kowannensu na baqin cikin rabuwa da inda Zaki yayi musu gatanda yanxu basuda Mai musu shi gashi tun bayan rasuwarsa aketa kama wasunsu ana rufewa ba wani dogon dalili.

****

Cikin wani irin Jin dadin daya Jima shekara da shekaru Yana jira ya daga takardunsa dasuka gama kammaluwa yace"


Finally Dilla will be the richest business tycoon da Babu kamarsa daga yanzu.


Kallon familynsa yayi da dukkaninsu kowa yasamu cikar burinsa musamman am da ya kawarda Zaki Wanda shine matsalarsa da mum dinsa.


Zeel na karanta wasu takardu tace"


Before mubar qasar gobe akwai wani aikin daya kamata mu qarasa Dan rufe matsalarda muka magance gabaki daya saboda karta bullo Mana a gaba.


Atare dad da am din suka kalleta ta aje takardun tareda kallonsu Kai tsaye tace"


Familyn Zaki,,,,matarsa in particular sbd hankalina Bai kwantaba tunda naji kunce yanda Mata I just can't take any risks sbd matarda aka kashewa miji abar gudu ce,

So Dole arufe chaptern Zaki gabaki daya.


Kallon am dad din yayi tareda dauke gira daya yace"


You heard your mum.


Daga Kai am din yayi Yana cewa"


Done.
****

Ahankali yake bude idanuwansa wannan karon tsaf yake ganin komai har idanuwansa Suka gama budewa yaringa qarewa dakin kallo tareda daga hannunsa daqyar ahankali ya dafa gefen cikinsa dake masa ciwo tareda rintse ido yasaki wani irin Nishi yafara qoqarin tashi zaune.


Yana qoqarin miqewa dafeda gefen cikinsa yaji budewar qofa da sauri ya dauki wata blade din asibiti dake cikin kayan dressing din ciwonsa dake gurin yayi Shirin soke Wanda zai shigo.


Da sauri Dr sayyid yayi saurin ja da baya Yana cewa"


Hey easy man saurara ka ajiye blade din 

Ni ba Wanda zai cutatar dakai bane idan zaka tuna nine na daukoka daga asibitin Dilla lokacinda kake neman fita hayyacinka bayan  yaran am Dilla sun kunnawa dakinda kuke wuta.Dafe gefen cikinsa yayi Yana rintse ido sbd zafin ciwo da zuciyarsa dake ci da wutar fushi da wani irin rage dabaisan yanadashiba yace"


Wlh nine ajalin dillas da.....


Kasa qarawa yayi sbd wata irin azaba da gefen cikinsa keyi ya rintse ido yasake bude jajayen idanuwansa da fushinsa ke qanqantasu yace"


BURINA DAYANE yanzu Nine downfall na dillas.


Saurin riqosa Dr sayyid yayi ganin ciwonsa yafara jini yace"


Sanin hakan yasa na cetoka sbd son samun Wanda zai tayamu cika namu burin na ganin dillas a qasa.


Cikin dauriya JJ yazame jikinsa Yana nufar qofa yace"


Ina buqatar magana da Zaki yanxu nan bana iya tsayawa banyi magana dashiba Dole zaisan waya turo kb ya kasheni sbd naji maganar am kafin su kashemu yace idan sunason samun full control na Zaki saisun kawarda Dani Zaki yakamata yasan wannan yanzu.


Da sauri Dr sayyid yasha gabansa tareda cewa"


Idan dai zakinda nasani kake magana to saidai kayi hakuri ya.....


Kasa fada masa yayi sbd jin nauyin zancen Dan baisan alaqarsu da junaba yanajin nauyin yaji rasuwarsa abakinsa.Da wani irin zafi JJ din ya zame ya fice duk da dare ne sosai baiyi la'akari da hakanba yanufi qofa Yana neman hanyar fita.


Duk yanda Dr sayyid yaso hanasa fita sbd yanayinda yake ciki yakasa Dole yajawo mota yasakashi Suka fita ya nufi inda JJ din yace masa duk da yagane gidansu Nadiya ne Saidai baice masa komaiba.


Qarfe biyun darene gidan yayi tsit Saidai gidan Babu Wanda yayi wani dogon bacci sbd Sam yanzu ji suke basuda wani dogon tsaro bayan na Allah tunda yaran Zaki suka watse.


Yau hakanan taje dakinsu tayi kwanciyarta bayan ta shimfida rigarsa a jikinsa ta rufe idanuwanta hawaye nabin gefen fuskarta.


Kamar daga sama sama tafara jiyo motsi cikin gida da kamar kuka ta tashi zaune tareda saukowa gabanta na Dan faduwa ta lalubi makunnin wuta zata kunna saitayi tuntube da wani sabon takarminsa data gama ajewa gabanta tayi kallo dazu sai Bata tsaya kunna wutar ba ta lalubi takarmin ta dauka tana dagowa taji kamar ihun iya talatu sai kawai ta bude qofar dakin ahankali ta fito tana tafiya a hankali ta nufi cikin gidan tasa qafarta ciki taji anjawota baya da qarfi tareda toshe Mata baki Dr sayyid yayi saurin haska Mata fuskarsa Yana Dora hannu a bakinsa alamar tayi shiru karta motsa

Saiya haska Mata fuskar Wanda ke riqeda ita tana ganinsa Bata zaro ido saikuma tafara rufewa alamar zata Suma yayi saurin jijjigata Yana cewa"


No no no ba yanzu ki bude idanuwanki.


Jin motsi sukai saurin lafewa bayan qofar soron cikin duhu.


Am dilla na yashigo tareda yaransa daya dama yaransa hudu tuni Suka shigo gidan suka fitodasu zainab.


Kallon tsana ya watsawa su dattiya dako dago Kai sun kasayi kafin ya kalli zainab dake tsiyayar hawaye yace"


Matarsa dama mukazo kashewa kamar yanda mukai masa kashewar wulaqanci yanaci da wuta har ransa ya fita itama zamu Dan Dana Mata azaba kamar yanda muka dandanawa mijinta.


Cikin tsananin kuka irin na uwa iya talatu ta dago ta kalli zainab ta bude baki zatai magana zainab ta gangaro da hawaye tareda girgiza Mata Kai akan karta fada musu ba ita bace matarsa.


Da ido am din yayiwa yaransa ido Suka ja masa zainab din iyayenta na kuka suna riqeta sukaqi sakinta 

Ba Imani yasa kan bindiga ya bugi kan dattiya take ya yanke jiki agurin bayan kansa na jini.


Iya talatu kuwa kuwa duka sosai sukai Mata itama ta suma agurin suka ja zainab din daki sudai su Nadiya zai qarar bindiga sukaji 


Batasan sanda ta qwace da guduba ta tareda qwalla qara a mugun firgice dukkaninsu su am din suka fito yace"


Akwai wani a gidan ku kamosa wlh akashesa a duk inda aka cimmasa kuyi sauri.


Da gudu su JJ Suka jawo Nadiya ganin zata kawo musu matsala yasa JJ daukarta tsaf Suka gudu ko mota Basu tsaya shigaba sbd zaa iya ganinsu.


Gudu sukeyi sasai Basusan Ina suka saka qafafunsu ba har Suka bulla titin bayan layin sai kawai suka hango wata mota tafe a guje da sauri Dr sayyid ya Kara saura kadan motar tabi ta kansa akai saurin taka burki.


Direban moyarne kawai ya fito tun baiyi maganaba Suka fada motar shima ganin haka yashiga Suka figa da gudu.


Wani airport suka nufa Saidai suna isa jirginda Wanda ke cikin motar zaibi yariga ya tashi ahankali Wanda ke cikin motar daga baya basuma wani luradashiba sbd Dr sayyid agaba yafada JJ ne dake daukeda Nadiya Suka fado baya.

Cikin wata irin kwantacciyar murya ya bude baki yace"


Muje side nabi private jet.


Dukkaninsu atare suka kallo gefen quryar motar daga baya Jin muryarda Basu taba tsammaniba Saidai ganin Mai muryar yasa dukkaninsu sake dauke wuta sbd tsantsan kamanin Zaki da muryarsa dake gabansu Saidai wannan shi dattijo ne Sosai Amma duk da darene Kuma cikin tsananin tashin hankali suke suna iya hango hutundake tattaredashi.


Nadiya da tuni dama ta suma JJ dashima dinkin ciwonsa ke jini sosai yakejin wata irin muguwar azaba ya girgiza da qarfi Yana kiran sunanta daqyar cikin dauriya 

Jin Abu Mai dumi na bin jikinsa da alama Kuma daga jikinta abin ke fitowa.


Shafo na jikinsa yayi ya dago hannunsa yaga jini gabansa yayi mummunan faduwa ya kalli Dr sayyid  dashima yashiga sabon rudu yakasa magana kafin shima yasake bude baki idanuwan JJ din Suka fara rufewa duk jarumtarsa da daurewar dayake abin yaci qarfinsa  haka idanuwansa Suka rufe ya some a gurin.


Dr sayyid ya juyo gabaki daya bayan tareda riqo hannun JJ yaji pulse dinsa cikin sauri yasaki ta lalubo hannun Nadiya ya riqe yanajin pulse dinta ya dago da sauri ya kalli mutumin cikin tashin hankali yace"


Sir she's pregnant Muna buqatar zuwa asibiti cikin gaggawa idan munason tsayarda bleeding din.


Cikin tsananin zafi da bacin rai tareda wani irin radadi dake fita muryarsa da fuskarsa yace"


Kozaka rasa ranka you better save this baby sbd laifinka da sakacinka sunyiwa rayuwata mummunan illa sayyid hw cud you ever hide this from me bayan kasan Mena turoka kayi Amma kabari na rasa the most precious thing a duniyar,,,I will never forgive you for that sayyid...


Kai tsaye yacewa driver muje side din a Daren nan zamubar qasarnan idan munshiga jet you better stop the bleeding.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863**_Mamuhgee26_*

Murya na rawa da Rashin gskia tareda fargabar halinda nadiyar ke ciki Dr sayyid ya bude baki yace"


Sir bazamu iya barin qasa a wannan halinda take cikiba Dole Ina buqatar Bata wasu injections yanzun nan.


Wani kallo ya watsa masa cikin tsananin zafi da tafasarda zuciyarsa keyi masa na Rashin dansa qwaya daya tal a duniya batareda sun haduba ya danne bacin ransa sbd kar ayi biyu ya rasa dansa yazo ya rasa jikansa Kai tsaye yacewa driver suje gidan Dr sayyid din.Cikin qanqanin lokaci suka Isa gidan Saidai sanin yabaro motarsa acan su am zasu iya ganowa su biyosa gidansa sai yafito motar da sauri ya shiga gidan yafara tattaro duk wani abin buqatar Mai mahimmanci tareda passport dinsa da takardunsa tareda magunguna da allurai ya fito da sauri Suka wuce.


Cikin motar jikinsa na rawa da sauri ya hada ruwan injections yayi Mata guda hudu sannan ya hada na JJ shima da sauri yayi masa Saidai shi Yana yimasa ya farfado Yana sakin wani gurnanin nishin azaba Yana qoqarin bude baki yana tambayar ya Nadiya.


Direct airport suka nufa cikin qanqanin lokaci akai cuku cuku sbd girma da kudinsa sukabi flight din tsakiyar Daren zuwa Lagos.


Bayan sallar asuba har gari yayi haske suka sauka Lagos wata qatuwar baqar jeeb tazo ta daukesu ta private exit inda Babu Wanda yagansu suka bar airport.


Wani qatoton mansion daya ninka na Dilla dasuka sani kusan so biyar Suka shiga Saida suka wuce gate uku kafin Suka Isa main harabar gidan Dana tun acan Sukayi ordering nurses guda uku Mata daga Primus private hospital atake cikin gaggawa aka shigada Nadiya sbd har lokacin Bata farko ba Saidai bleeding din ya tsaya gabaki daya.


JJ ma ciki akayi dashi duk da ya farfado Bai iya tsayawa miqe sbd gefen cikin nasa.


Securities ne suka budewa Mai gidan qofar mota sai alokacin yafito fuskarsa Babu annuri ko daya ya wuce Yana amsa gaisuwarsu da Kai yayi ciki.


Direct qaton bedroom din dake palon ya nufa inda aka Kai Nadiya saidai Bai shigaba ya tsaya tsaye tsakiyar palon Yana kaida kawo cikin wani irin tsananin bacin Rai na shekaru dayake zaburo masa,


Tabbas sbd kada dawowarsa ga dansa yazamo ha'dari ga rayuwar gidansu gabaki daya yasa ya boye kansa ya nesanta kansa da dansa dayasan haka zata faru tabbas daya fito sunyi gaba da gaba da dikko.....


Sir""  


Sayyid yakira sunansa cikin sanyin murya kansa a Dan sunkuye cikeda ladabi ya dago ya kallesa murya cikin sanyi yace"


I'm really sorry sir,

Munshawo kan matsalar Nadiya the baby is safe now komai yayi normal insha Allah she just needs to rest Saidai a yanayinda take ciki gskia I can't assure the safety of the baby sbd her BP is very high.


Kallonsa yayi tsawon mintuna kafin ya juya yayi palonsa ya zauna cikin Dan 'dacin rai yace"


Jabeer fa???


Shima insha Allah namasa wani dinkin Nanda 48hrs zaiji sauqin zafin gurin sosai.Sayyid tell me meyasa ka boyemin abinda ke faruwa???


Gyara tsayuwa yayi cikin jimami da takaicin tsananin damuwar dayake hangowa ga mutuminda yazamo tamkar uba agaresa yace"


Sir dama koda nagama bincike Nagano Zaki shine Wanda muke nema nayi maka email na hotunansa da duk bayanai na yanayiwa dikko aiki to alokacin ne yazomin da buqatar nemawa Nadiya lafiya Kuma abinda yasa muka buqaci kudi daga garesa masu yawa sbd munyi tunanin hakan zaisa yaje ya nemi aikiyi da kansa Wanda nasan samun aikin zaisa yadainawa dikko aiki Saidai abinda bansaniba shine yanda yasamo kudin Kuma aranarda akayi aikin aranar koma menene yafaru yafaru lokacinda labari yafito ankamasa da yiwa qasa sata aranar naje Naga IG nabasa 1million akan case din sbd banasonma kaji hankalinka zai tashi Kuma hakan zaisa ka bayyana kanka Wanda lokacin daka tsara hakan baiyiba tunda akwai gabar da kake jira ka bayyana kanka,


To abinda yabani mamaki shine yanda wuta ya tashi a Daren Kuma babban abin mamaki da zargi shine IG yacemin a Daren dama sukai planning sakin zakin Saidai kafin su Isa wutarne takama and unfortunately......shiru yayi yakasa qarasawa ahankali ya furta"


Kayi hakuri Allah yaji qansa....


Miqewa yayi Bai tsaya sauraron sauran bayananba ya haye stairs Dan kuwa wata irin masiface dikko ya takalowa kansa shida familynsa Bai saniba.


Acikin Daren washe gari ta farka da wani irin tsananin ciwon Mara da zabure zabure Wanda ya tsorata nurses din da sauri Suka dauki waya suka Kira Dr sayyid hankali tashe ya qaraso nan suka hau dubata Yana addua da fatar shock dinda tashiga karyayi affecting babynta da lafiyarta sbd shock ne da high BP suka hadu lokaci daya.Har asuba suna Abu daya daqyar yashawo kan matsalar yayi Mata allurai tayi bacci.


Dafe goshinsa yayi cikin tsananin tension yake kallonta kafin ya kalli nurse din yace"


Please after 30min give her antropespines.


Ok Dr ""tafada itama cikin tausayin Nadiyar.


Fita yayi yaje dakin JJ shima Saidai shi yaji sauqi sosai Saidai wani irin fushi da zafi dake cinsa Sam jijiyoyin jikinsa Dana kansa sun firfito Wanda har fushinsa ke bawa Dr sayyid tsoron irin burin fansar dayake hangowa a idanuwan JJ din.Cikin nutsuwa da tsananin kwarjini Mai gidan ya shigo dakin JJ din Dr sayyid na bayansa tareda Mai aiki data shigoda abinci cikeda tray ta aje a bedside drawer ta juya ta fice.


Kallonsa JJ keyi Babu ko qyaftawa sbd ganin zallar kamanni da kwarjini irin na sarkinsu dake tattareda mutumin,


Baya tantama wannan shine mahaifin sarki sbd dama zakin baida tabbacin shin mahaifinsa mutuwa yayi kokuwa da gasken shi Dan fyade ne kamar yanda so dadama yake tsintar zancen gurin kawunsa,


Baitaba tambayar mahaifiyarsa ba waye babansa harta rasu sbd zaizamo tamkar cin fuskane agareta shiyasa yacire maganar aransa Koda shidin Dan halak ne ko sabanin hakan wannan tsakanin mahaifiyarsa ne da mahaliccinta.Irin kallonta JJ ke masa yasa ya matso gabansa tareda miqa masa hannun ahankali ya furta"


*_ALHAJ ALEEYU NEYO NOAH_* Congress man starling city United States of America,Kuma nine mahaifin marigayi aliyu haidar Zaki.


Jajir idanuwan JJ sukai ya rintse ido suna qara yin ja jijjiga Kai Yana son daure kukansa Saidai Sam ya kasa durgushe qasa tareda sakin kukan mutuwar zakin dake hura wuta a jinin dake gudana cikin jikinsa tun Daren jiyan.


Ahankali jikinsu yayi sanyi cikin dauriya Dad din yace"


Fitar duka zakaji sauqi duk da nasan dikko yayi Mana gibi Mai girma a rayuwa da bazamu iya cikewaba tayin ajalin Zaki.Kuka sosai JJ yayi Amma Sam yakasa Jin abinda ya tokare masa ya fada ya dago da qyar yace"

 

Har abada abinda nakeji gameda mutuwar sarki bazai fadaba sai ranarda Naga qarshen zalinci da mummunan qarshen dillas gabaki dayansu.


Juyawa dad din yayi shima cikin danne nasa fushin yace"


Qarshensu na zuwa jabir karka damu,

Zan mayarda rayuwar dikko shafaffiya a tarihirin masu arziki,

Zan mayardashi mabaracinda ko suturar sawa baida ita ajikinsa insha Allah.


Miqewa JJ yayi yace"


Dikko,zeel,am nayi alqawarin ganin na mayarda asusun arzikinku daga zero me yawa zuwa zero daya tal.

Yanda kuka cutatardamu cikin zamba da aminci ta fuskar amintaka ahaka zan cutatar daku ta fuskar zamba da aminci.


Kallonsa dad yayi cikin jinjina Kai tareda qaunar JJ din sbd tabbas yaji dukkanin bayanin irin so da qaunarsa Zaki kewa JJ tamkar jininsu daya.


Ya rasa 'dansa Saidai dukkanin abinda dansa zai masa yasan magajinsa sai masa,

Yayi alqawarin saiya zubarda dikko ta hanya mafi ciwo da zafi Dan haka alqawarinsa na nan,

Shida JJ burunsu dayane.
Lokacinda Nadiya ta farka sosai hankalinsu ya tashi sbd dai a iya bincike da abinda Dr sayyid ya binciko shock din ya taba qwaqwalwarta Dole a mayarda ita asibiti.


Hankalin dad da JJ yayi matuqar tashi nan dad din yasa aka fara cuku cukun nemar musu visa Dan kaita asibiti anan is very risky dikko ya wuce duk inda ake tunaninsa zai iya ganonsu.Cikin sati guda komai ya kammala Suka daga zuwa US a starling city Suka sauka nan akai asibiti da ita gashi abin yafara taba lafiyar cikinta Dole Suka tattara komai suka aje Dan ganin tasamu lafiya gashi dukkaninsu kowa Yana tsananin qaunar cikin basason abinda zai samesa.


Sannu ahankali likitocin qwawqwalwa suke ganinta ana Bata allurai da magani tun abin na hauka sosai saigashi tafara dawowa normal Saidai idan abin yatashi Babu sauqi hauka takeyi sosai tana ihu da Kiran sunan Zaki da zainab wani lokaci hardana babanta.Ahaka dai Suka Mata transfer zuwa wata babbar asibitin psychiatrist dake Amsterdam inda Sukayi admitting nata ganinta sai wata wata.


Ba yanda suka iya su dad haka Suka hakura Suka barota Saidai kulawarta daban take ta musamman ce sbd cikinta da harya fara tsufa Dan lokacin Yana wata shida.Sannu ahankali dad ya warwarewa JJ dukkanin sirrin dukiyarsa da rayuwarsa tareda dorasa akai duk da dai komai NASA yariga ya yanke shawarar sunan Nadiya da abinda ta Haifa zaa saka dukiyarsa kaf yace tasuce tunda sune Abu mafi soyuwa a rayuwar Zaki.


Sosai rayuwar JJ tafara canjawa musamman da dad din yasa aka ware masa wani program na classes dayake zuwa dauka na degree dakuma na aikin kakin soldier na shekaru biyu dazaiyi yagama.


Yawan geaming dinda yakeyi saiya fara bude jikinsa ahankali yafara zama wani qaqqarfan najimi gashi yanzu wani irin hutu da dukiya sun fara ratsashi musamman dayake dad din baiwani jin hausa sosai tunda asalinsa ga yanda yake Kuma yadawo nan din.


Duk wata tare suke zuwa dubo Nadiya  Amsterdam suyi kamar kwana hudu kafin sudawo sbd dr sayyid tuni ya mayarda hankali kan fannin asibitoci da kamfunan magungunan NOAH.


Lokacinda Nadiya tashiga 9month dinta alokacin ne Suka dawo Amsterdam dukkaninsu harda Dr sayyid Wanda bai wani Jima da dawowa daga Nigeria ba sbd dubo alqawarinda yayiwa Zaki tuntuni na kulada familynsa Saidai Bai fadawa kowa yajeba.Two weeks after labour yazo Mata inda hankalin asibitin yayi mummunan tashi sbd tun Daren jiyan take fama da labor gashi sbd mental problem dinta yasa ihun azaba takeyi sosai Bata wani iya daurewa tunda batasan metake yiba.,


Ganin abin yafara fita out of their control yasa sukai transferring dinta to wani babban asibitin su dad Suka kwasa sukai can Babu Mai nutsuwa.


Da isarsu aka shiga labor theatre da ita sbd bazata iya haihuwa da kantaba gashi tayi weak sosai.Lokacinda dad yasa hannu a takardar tiyatar Saida JJ yariqe hannunsa sbd yanda yake rawa cikin sanyi da dauriya yace"


Dad insha Allah lafiya zata fito.


Daga masa Kai dad din yayi Yana murmushin qarfin Hali da jarumta.


Har dare suna zaman jiran sai qarfe bakwai nurse biyu Suka fito cikin farin ciki dayar tace"


Congratulations Congressman.


Dayar ce ta karbe zancen da cewa"


It a baby girl sir.


Hamdala suka sake dukkaninsu tare cikin farin ciki dad yace"


Thank you for this wonderful news ladies.


Fitowar doctors ne yasa dad kallonsu Yana cewa"


Dr hw about the mother????


Kallonsa Dr Allen yayi ya jinjina masa Kai suka nufi office Yana sake karanto masa reports dinta dasuke saka ran tadawo normal daga mental issues dinta.


Lokacinda JJ yadauki babyn wani irin murmushin farin ciki tareda hawaye yakeyi yanajin tsananin qaunar yarinyar ya Dan shafi fuskarta dake yanayi data babanta ahankali Yana murmushi hawayensa na qaruwa.


Dan motsawa yarinyar tayi Hana 'dan turo harshe cikin tsananin farin ciki ya furta"


Zainab baby.


Dad dake bayansa sukaji yace"


Harkawa 'yarku huduba kenan.???


Qarasowa yayi ya karbi babyn shima yayi Mata addua Dr sayyid ma yayi nurse tazo ta karbeta ta mayarda ita gadonta dake kusadana mamanta da Bata farfadoba.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee27_*

Kwana biyu da haihuwarta taji sauqi sosai Saidai har lokacin Bata yiwa kowa magana sai shiru datakeyi hawaye na fita idanuwanta musamman da dad ya gabatar Mata da kansa dakuma matsayinsa na uba ga mijinta Kuma kakan 'yarta baby z.


Ranarda aka sallamosu Suka koma asibitinta na psychiatric Suma Suka gama nasu binciken Suka sallameta Suka dawo starling city anan Suka tararda Nanny's da qarin sabbin masu kulada gidan da ita kanta nadiyar.


Wani tangamemen hoton Zaki ne na zane dake facing duk Wanda yashigo makeken polon Wanda masu zanen Suka samoshi sosai kamar shi din ne aka dauka.


Tsayawa tayi cak tareda qurawa hoton ido tanason riqe kukan daya danne qirjinta tsawon watanni ta sakesa da qarfi tareda durqushewa gurin komai nasake dawo Mata sabo

Kunnuwanta na dauko Mata qarar sautin kuka da magiyar iyayenta tareda qarar bindigar Daren da abin yarafu dakuma qonanniyar gawar mutum mafi soyuwa a rayuwarta dake dawo Mata a ido.


Nanny Nancy ce tayi saurin riqota tana durqusawa gabanta cikeda tausayinta duk da batasan meye damuwarta ba Amma yanayinta ya nuna tsananin quncin da zuciyarta ke ciki.Dad da JJ ma duk jikinsu sanyi yayi sbd ita yanzune data dawo daidai takejin komai yadawo Mata sabo musamman idan takalli maraicinda yarta zata taso dashi na Rashin uba.


Cikin sanyi dad yace nanny Nancy tayi ciki da ita.


Wani tangamemen dakin dayafi kowanne kayan qyale qyale da haduwa aka kaita inda aka zuba komai sabo na baby z Dana nadiyar tundaga situru da abubuwan buqata na gyara.


Bakin gado ta zaunar da ita tareda kwantar da baby z cikin gadonta ta fice.


Kuka takeyi sosai tanajin wani irin zafi da radadi na qona zuciyarta inda takejin wata irin tsana da qiyayyar familyn dikko Dilla musamman am datake gani a idonta lokacinda ya buge babanta yaja zainab cikin daki ya harbeta.


Cukuikuye jikinta tayi sbd tsananin abinda takeji na wutar tsanarsa dake ruruwa a jininta taci gaba da kuka.


Yini guda a dakin tayisa Bata fitoba tun shigarta gashi daga dad din har JJ Babu Wanda yayi yunqurin shiga dakinta Dan karsu takurata.


Su nanny da masu aikine keta hidimar kulada gidan da baby z sukuma su dad suna can sun maida hankali kan business dinsu.


Washe gari ma Bata fitoba a daki ta wuni kwance idanuwanta sunyi zuru zuru sbd Rashin bacci da tunani.


Sannu ahankali lokacin yafara tafiya har baby z tafara girma takai wata hudu cikin na biyar sosai nanny Nancy ke kulada ita musamman ta bangaren Bata madararta sbd nonon Sam baida wani ruwa sai kawai Suka maida himma gurin Bata Madara.


Duk yanda taso yakice abinda ke rura wutar qiyayyarta saitaji takasa sosai takejin batada sukunin zuciya Dana jiki akan irin kisarda akaiwa mijinta da 'yar uwarta tareda iyayenta,


Abu daya tasani shine bazata taba hutawaba saita biwa 'yar uwarta da mijinta haqqin ransu,

Dole za'a bawa matarda aka kashewa miji justice hakama uwar da aka kashewa ya agabanta.,


Babban abinda yafi azalzala wutar zuciyarta shine yanda ta haukace taso a maidata gurin iyayenta Amma dad ya Hana tareda fahimtar da ita matuqar tanason babanta tanason lafiyarsa ta nesanta kanta dasu yanxu sbd bayyanarta hadarine ga iyayenta dakuma 'yarta.Akaro na farko dataji tana tsananin sha'awa da buqatar karatu Mai tsananin zurfi a rayuwarta sbd da shine kawai zata iya fuskantar Wanda yayi ajalin mijinta wato AM DILLA.Sakin jikinta tafarayi ahankali tana koyan turanci sosai gurin nanny Nancy tareda wasu abubuwan.


Dad ma ganin tasaki jiki sosai lokaci guda sai abin yabasa mamaki Amma yaji dadi sosai musamman yanda tafara sakewa dashi Saidai yanayin zafinta yakan bawa JJ tsoro da mamaki sanin ita din Mai tsananin sanyi ce.


Dad da kansa yasa aka dauko Mata wani Dr Marshall Yana koyar da ita karatu da wasu hanyoyin business sbd shi arayuwarsa komai business ne,

Shi kansa babu abinda yakeso kamar nadiyar tazama independnt business woman dazata jagoranci _NOAH EMPIRE_ nan bada dadewaba.


Ahankali baby z tayi wayo zuwa lokacin Nadiya harta sauya sosai sbd yanda nanny Nancy take matuqar kulada cimarta sbd Sam tace Mata batason tayi jiki.


Rashin fitarta yasa fatarta tayi mugun canzawa musamman dayake cikin masu musu aiki akwai Becca wadda Tai aiki wani babban beauty parlor ita ke sake kulada skin din nadiyar ta bangaren abubuwan datake amfani Wainda suka mugun karbar brown skin dinta.


Baby z nada shekara daya admission dinda dad ya nemarwa Nadiya a university of Toronto Canada yafito dayake duk a shirye suke Babu Bata lokaci ta wuce aka bar baby z agurin nanny Nancy da sabuwar nannyn da aka qaro Mata musulma daga qasar Libya sbd kulada bangaren tarbiyan addininta musamman dayake tafi sabawa da nnany nancy da dad said JJ datakewa kallon shine mahaifinta.Babban Abu na farko da Nadiya ta mayarda hankali akansa bayan karatunta shine shiga harkar tsadaddiyar rayuwa sosai sbd tanason ta iya komai,komai ya zauna arayuwarta da jikinta tareda dabiarta sbd ta hakanne zata samu cikar burinsu daya zamo daya itada dad 'dinta da JJ.


Sosai take karatu musamman da rayuwarta ta sauya cikin shekara daya da fara karatun tuni ta sauya komai ta koma tamkar haihuwar turawa rayuwarsu ta shigeta ta bangare daya dad ma ya dage sosai yake sakata a harkar business tun Bata ganewa harya shigeta tana gane business sosai.


JJ ma yagama karatunsa yanzu yafi maida hankalinsa akan harkar training dinsa dakuma business din sosai sbd shine abinda dad yafison yashigesu.
So biyu kawai tazo starling city hutu tunda tadawo Canada din Saidai kusan kullum tana video call dasu nanny da baby z shi dad kusan Yana yawan zuwa kokuma idan yace tasamesa wata qasar Akan harkar business.,

Shikuwa JJ dama kusan duk yasamu time Yana hanyar zuwa Canada din gurinta.


N.D NOAH take amfani dashi a dukkanin takardunta da passports dinta tareda duk wani id card dinta ma'ana Nadiya dattiya Noah.


Yawanci friends dinta turawa sukan kirata da nadey Noah.

 

Ahankali karatunta yayi nisa harta kai shekarar qarshe Saidai zuwa gabaki daya rayuwarta da ita sunyi nisa da hannun riga da rayuwarta ta dah.


Bazaka taba kallon shape da zubin slimmy figure dinta kace ta taba daukan ciki bama bare haihuwa,


Skin dinta yatashi daga brown yakoma tamkar na half-caste ko black Americans sbd tsabar hutu da kyawun tareda tsadar products dinda take amfani dasu,


Sam ta manta when last ta zauna da wani tayi yarenta na hausa sbd dama dad ne shima Bai wani cika hausaba tunda dama ba tarensa bace,

Sai JJ shima turai tashigesa sosai Sam sai can suke hausa a tsakaninsu kokuma baby z dasukewa sbd ta 'dan iya.Duk wani motsi da tarihin Dilla's suna sane dashi a tafin hannunsu yake yanzu zasu fara nasu wasan THE NOAH'S sbd shima JJ JABEER HAYDAR NOAH yake amfani dashi.


Shekara hudu cikin ta biyar cif ta Gama kammala first and second degree dinta a fannin business da harkar modeling fashion.


Ranarda ta sauka us a ranar cikin dare dad dinta ya hada wani gagarumin taron dinner inda ya bayyanarda ita a matsayin owner NOAH'S EMPIRE.


sosai Yan press Suka dinga daukarta hotuna suna Mata tambayoyi inda ta ringa Basu amsa cikin wani irin yanayin daya ringa rikita zuciyar manyan abokanan business din dad dinta da 'yayansu tun anan wasu Suka fara miqa business offer dinsu sbd duk wata suffar daukar hankalin 'da namiji tagama hadasu atare da ita musamman dinner gown dinta black Mai tsegen kyau dake daukar idon mutane sbd stones da Kuma kyawunta dake kashe musu ido.Washe gari da qyar ta bude manyan idanuwanta dasukai laushi sbd bacci ta lalubo alarm dinda ke gefen gadonta Yana kuka ta kashe tana sake komawa cikin bargon.


Qarar wayarta yasata Jan qaramin tsaki tareda lalubo wayar ta dauka batareda ta duba ba tace"


Yes please.


Cikin yanayi na farin ciki JJ yace"


Nadey come downstairs now,you need to see this.


Bude idanuwanta tayi da sauri tana cewa"


Am coming.


Saukowa gadon tayi tareda zura bedroom slippers dinta na gashi masu tsananin laushi ta fito tana Kama gashinta bayan ta saka jacket saman kayan baccinta.


Palon ta qarasa saukowa tana kallon tvn dasuke kallo 

Take zuciyarta tayi wani irin nauyi ta tsaya tana kallon yanda aketa baza labarai da sunanta ana nunota Saidai sunason ganin ainihin dad dinta Wanda bai taba Bari Yan press sunyi fira dashiba ko daukar hotunansa.


Karbar coffee dinda nanny Nancy takawo musu tayi tafara kurba tana kallon tvn yanda zancen ya baza duniya Yana sanyata nishadi sbd irin zallar dukiyarsu da ake fada tasan duk inda dillas suke yanxu ido rufe nemanta zasu fara Dan hada business da ita Wanda shine first target dama.


Murmushi tayi batareda ta dauke idonta daga tv ba tace"


Am Dilla I'm coming for you.


Aje cup din tayi tareda kallon JJ tana miqewa tace"


Bari naje Naga dad inason magana dashi.


Sun Jima sosai suna magana akan proposals dasuka samu da dama tsakanin jiya zuwa safiyar yau din Wanda Dole JJ ne zaiyi handling rabi ita zataji da sauran sbd dad din kwana biyu Yana fama da Dan nauyin jikin manyanci.


Cikin wata black BMW ta iso Noah's cikin wasu maroon pensil suit na Mata dasuka matuqar fiddo shape dinta sai wasu shegun heels black da black mk bag dinta tashigo companin  tana waya da best friend dinta Annah Lauren.


Dukkanin ma'aikatan tasowa sukeyi suna Mata barka da zuwa su pa dinta da wasu ma'aikatan na biyeda ita har bakin office dinta inda aka rubuta CEO PA dinta ta bude Mata tashige.


Aiki tayi sosai tareda meeting harso biyu sbd yawan aikinma yasa sai dare tasamu damar dawowa gida lookacin baby zee tayi bacci Saidai kawai tayi wanka tasha fruits ta kwanta sbd batacin Abu Mai nauyi da daddare.


Washe gari ma a office ta wuni kusan yamma Annah tazo ta dauketa sukaje wani spa dagacan sai dare Suka dawo gida.


Ayyuka sunmata yawa sosai shiyasa gabaki daya she's busy ko lokacin zuwa yawon shaqatawa dasuke da Annah ta rage samu sosai.


Yauma JJ ne yaje ya daukota suka dawo gida.


Babban abinda yafara tunkarosu batareda sun samu proposal daga Dilla empire ba shine bullowar wani kamfani daya dame nasu akan dukiya da suna Wanda a iya bincikenta kamfanin duka duka baifi shekara uku da fitowa ba Amma Yana neman take nasu dayayi shekaru masu yawa.


Tension yayi Mata yawa sosai musamman safiyar yau dataga jaridar wani sati kamfanin zasuyi bikin bude kamfaninsu dake South Africa.


Sake kallon jaridar tayi ta miqawa JJ tareda miqewa tana zuwa bakin glass wall din dake office din Bata tana kallon qasan harabar kamfanin cikin tsananin damuwa tace"


Idan muka rasa wainnan proposals din rugujewa zamuyi sbd dukkanin ribar shekaru muka zuba a wannan karon sbd kawai mukira attention din dillas da yawan proposals namu Amma out of no where wannan kamfanin yazo yasha gabanmu 

who the hell is this *_HAYDAR'S BUILDINGS LMT_* ????


dafe goshinta tayi tana jinjina irin hasarar dazasuyi idan Basu samu open contract proposal ba Mai tsananin tsoka.


Qarasawo bayanta JJ yayi ya tsaya tareda zuba hannuwansa cikin wandon ash suit dinda ke jikinsa cikin taushin muryar lallashi yace"


Heyy don't stress your self akan Dan wannan issue din, we'll find a way bazamu taba Bari wannan company ya rusheba okk??? So please just calm down kinji?


Kallonsa tayi tareda Dan daga masa Kai batareda damuwar tasaketaba.


Kallonsa tayi tareda nufar kujerarta ta zauna tana rufe apple laptop dindake kunne gefen flatscreem APPL desktop din office din tana cewa"


Dole zanbi flight din chicago gobe Ina buqatar ganawa da wannan haydars buildings din Bari ma naje nafadawa dad akwai wani conference meeting dazanyi da wani sabon company dasuma haydars din zasuyi meeting dasu inason mu hade acan ina buqatar magana da CEO na wannan haydars buildings din kota yayane.

#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee28_*


*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee28_*

Zama tayi gaban mirror din bedroom dinta tareda qurawa fuskarta ido ta cikin mudubin Bata ko qyaftawa tsawon lokaci kafin ta lumshe idanuwanta hawayen ciki Suka gangaro Mata ahankali tasaki wani silent kuka tareda rintse ido.


Shekaru sunja da rasuwarsa Saidai har yau takasa raba kanta da kukan rabuwarsu kowane dare idan zata kwanta,


Shine farin cikinta,

Shine burinta,

Shine walwalarta,

Shine kadai zuciyarta ke bugawa kowace daqiqa da sonsa,

Har abada zuciyarta bazata taba son wani bayan Shiba,

Uban 'yarta Wanda shine sirrinta ciki da Bai dinta,


Meyasa Suka rabata dashi adaidai gabarda sonsa yagama shigewa gaban rayuwarta,

Meyasa Suka rabata dashi Suka maidata marainiyar bazawara itada 'yarta,

Sun rabata dashi,sun rabata da zainab  sun rabata da iyayenta tsawon shekaru,

Tanason ganin mahaifinta da mariqiyarta,

Tanason sanin wane halin suke ciki saidai bayyanarta hadarine ga rayuwarsu duk sbd suna 'daya _DILLAS_ .


Share hawayenta tayi ahankali tareda miqewa tsaye tana sake goge fuskarta ta nufi wayarta ta dauka Kai tsaye ta dannawa p.s dinta Kira tana dauka Kai tsaye cikin bada umarni tace"


I need two chicagos flight tickets by tomorrow.


Yes ma'am."""Jasmin din tafada cikeda girmamawa tareda kashe wayar take ta dauki iPad dinta tafara booking tickets din.


Closet din kayanta ta nufa ta bude tareda kallon inda kayan baccinta ke jere Babu kalar da Babu ta jawo wata white sleeping snowgown tasaka Mai tsananin laushi da 'dan tsawo zuwa cinyoyinta ta daure gashinta da band ta nufi mirror ta fesa calmScentsy jaguar miss tareda shafa body oil Mai qamshi ta nufi gadonta tana Shirin Hawa nanny Nancy tashigo Mata da Black coffee ta karba tana murna tace"


I love you nanny.

Zama tayi tana sake tambayar baby zee da Bata samun kulawarta sosai kamar da sbd wannan masifar ta loss datake ganin ta tunkarosu.


Fira sukeyi da nannyn sama sama tana aiki a laptop dinta tana sipping coffee din 

Nanny ganin hankalinta baya gunta yasa tayi Mata Saida safe ta fice.


Hankalinta sosai taji yafara tashi da wainnan haydars buildings din sbd bincike takeyi sosai akansu Amma takasa ganin ainihin waye Mai kampanin sbd Sam Babu hotunansa a yanar gixon,

Abinda yafara daga Mata hankali da Bata tsoro shine money and power dinsu zasu iya rushe Noah's cikin lokaci qanqani.


Sake tsananta bincikenta tayi akansu Amma Bata samu abinda takesoba harzata kashe wani update na news ya sauka tayi saurin budewa ganin sunan Dilla's aciki.


_DILLAS EMPIRE TO PARTNERSHIP WITH THE HAYDARS BUILDINGS_


what"""tafada da Dan qarfi cikin tsananin tashin hankali da damuwa ta lalubo wayarta da sauri tana neman numbern JJ saiga kiransa yashigo tayi saurin dauka cikin nutsuwar lallashinta yarigata magana""


Hey hey baby relax.,

Relax okay????

Nariga Naga news din yanxunan aka sakesa acikin Daren nan,

Karki daga hankalinki please baby.


Cikin son danne damuwarta tace"


I don't know how to handle this situation, things are getting out of hands,

Da zaran wannan haydars buildings din sunyi amince da proposal din Dilla's shikenan bazan samu yanda nakesoba,

Alqawarin danayiwa dad bazai tashi a banzaba dady j we have to come up with another plan.

Plan B kenan.


Aje remote dinda ke hannunsa tayi tareda zama kan couch Yana daukan coffee dinda aka kawo masa harya fara hucewa yace"


Baby bazan taba Bari ki shiga familyn dillas ba karkima kawo wancan mgnar.


I have to,

Idan har munason cimma matsaya Dole zamubi wannan I promise you Babu abinda zai sameni.


Kashe wayarta tayi da sauri tareda kashewa gabaki daya bayan ta karanta saqon email din Jasmin flight dinsu gobe qarfe Tara na safe.


Washe gari tana tashi tafadawa nanny tafiya zatayi nan akahau shirya Mata Kaya cikin luggages dinta ita Kuma tana gurin baby zee yau itace takeyi Mata Shirin school da kanta.


Sama Suka hau gurin dad 

Da gudu baby zee tayi gurinsa ta haye jikinsa tareda masa peck a kumatu tana cewa"


Gud morning grandpapa?


Hannu yabata Yana cewa"


Gud morning Miss zaynab Noah.


Kama hannunsa tayi tana cewa"


I love you grandpapa.


I love you too my sweet sweet miss Noah.


Murmushi nadey tayi tana qarasowa tace"


Sabaa'ul khaiir dad.


Kallonta yayi Yana amsawa yace"


Yau kece kika shirya miss zee kenan.


Yes Dad Nima yau zantafi Chicago zamu hadu da wasu companies din ne zan duba proposal nasu akanmu saikuma Ina son shigarda tamu proposal din a haydars buildings with 62% interest.


Jaridarsa ya dauka Yana karantawa yace"


Idan har dillas nada open proposal akansu zaiyi wuya su karbi tamu Saidai ki gwada kodan sbd High rate interest dinsu.


Breakfast Sukayi a babban dining room dinsu su uku Sukayi sbd JJ na territory acan ya kwana jiyan sbd wani urgent aikin dasukai.


Har mota takai baby zee tayi Mata kiss tana cewa"


I love you take care Mamma's princess.


I love you too mummy.


Bayan fitar motarsu baby zee din dawowa tayi ta nufi bedroom dinta ta tube Kai tsaye ta shige toilet tashiga cikin ruwan dumin data Tara harsun fara hucewa ta kwanta tareda rufe ido.


Saidatayi relaxing tsawon mintuna ashirin kafin tafara wanka da royal Allie shower cream dinta da qamshinsa yacika toilet din tsawon mintuna goma Sha biyar kafin tagama ta fito daureda brown towel sau dan qarami daure a kanta.


Gaban mirror taje ta zame na kanta tafara goge jiki dashi kafin ta zauna tafara shafa Neutrogena pure laylns oil ajikinta dake fidda wani sirrin qamshin fresh Roselle Flower.


Bata cika wani make up ba Sam arayuwarta Saidai lips dinta dasukam akoyaushe 'dam sukeda hot daity brown mclipstick dake daukar hankalin mutane akanta.


Dogon Palazzo trouser tasa black Wanda saita tafiya zaka gane wando ne ba skirt ba sbd budewarsa.,


White brown free Prada top Mai yankakken hannu sai wasu heels a qafarta masu tsawo da wandonta ya rufe tsinin kawai kake gani sai wata scarf Mai stones datayiwa daurin gefe a kanta aka fito da luggages dinta tafito riqeda handbag dinta taje gurin dad Sukayi bankwana da kansa ya rakota har mota inda Jasmin da PA dinta daya suke jiranta tana shiga Suka nufi airport.


*****

Ahankali yashigo gidan Yana gyara babbar rigarsa zuciyarsa cike fal da bacin Rai da damuwa Yana masifa qasa qasa sbd yanxu ko dogon qarfin tashin hankali baidashi musamman qananan Yan iska dasuka cika anguwar yanxu.


Iya talatu dake zubawa aminatu sabuwar 'yar riqonta ruwa a geron datake wankewa ya kalla ya nufi tabarmar dake shimfide tsakar gidan ya zauna yana cewa"


Saidai hakuri talatu wlh shegun yaran nan sunyi qarmanje akan akuyar nan shima shegen Dan sandan da zanzaronsa me kamada talalar raqumi kamar zakaranda aka sawa wando yayi mirsisi yabi bayansu Ina gani Suka masa dubu daya.


Ajiyar zuciya iya talatun tayi tareda kallon matar dahiru dasuka dawo gidan data fito daki tace"


Zara'u Kama Mata wankin geron nan karta zubarda rabi a qasa.


Gurin dattiyan Takoma ta zauna kan kujerar zama tareda sake sauke wata ajiyar zuciyar cikeda damuwa tace"


Yanxu ko dabbobin gidan nan sunsan basuda gata sbd maraicin Rashin Zaki,


Duk tattalin arzikina na kaji da akuyoyina sun qare sbd sace sacen nan da akeyi haka kawai waiinan yayan banxar ke zuwa cikin anguwa suna damqewa mutane dabbobi suna sacewa bakada ikon mgn sbd mutuwar zuciyarda yansanda keda ita wani lokacin,


Kowa kukan rasuwar Zaki yakeyi anguwa da zagayenta sbd takai har 'yayan mutane suke matsewa yanxu ko ikon Aiken yaro da mangariba 

Yanxu gashi shima dahiru kaduba kaga har cikin gidan nan fa aka shigo aka sace masa Dan babur dinsa.


Shidai dattiya shiru yayi Bai iya cewa komaiba sbd dama tuni hakan yafara zama dabiarsa tun rasuwar Zaki da batan Nadiya yakan zauna yayi shiru Yana tunani sbd duniya a rayuwarsa Babu abinda yake qauna kamar ruqayya tazo ta rasu tabarsa shikadai baida wani jininsa dazai kirada Dan uwansa sai 'danta data Bari,


Yana qaunar Zaki fiyeda ruqayyar Saidai halinsu ne baya jituwa da juna shiyasa Babu wani ragi tsakaninsu,


Sai nadiyarsa da allah ya fifita masa soyayyarta fiyeda sauran yayansa saigashi itama yau Babu ta,


Zainab da har yau itama yakasa cire rasuwarta a ransa sbd irin zalincin da akayi musu Kuma sunaji suna gani basuda ikon fadar yanda akayi sbd tsira da rayuwarsu da mutuncinsu,


Banda talatu da mal idi Suka tashi tsaye akansa da tuni ya zauce yafara tsince tsince lokacinda ya bude ido yaga gawar yarsa daya agabansa 'dayar Kuma suntafi da ita duk da Yana sawa ransa itama sun kasheta  Allah dai ya taqaita abin nan.


Sam yanxu Bai cika yawon maularsa ba sbd tafiya yaje Yana tunane tunane musamman idan sukaje aka wulaqanto su saiyaji jikinsa yaqara sanyi sbd Zaki dake wulaqanta duk Wanda ya wulaqantasa.


Hakan yasa sha'awar sana'a ta 'dan shigesa saiya yanke shawara shida mal idi suka fara sana'ar Saida lemu da ayaba shikuma mal idi doya Amma rumfarsu daya a layin Yan kayan marmari dake jikin babban roundabout ta babbar kasuwa.


Ganin yanayinsa yasa iya talatu Jin jikinta yaqara sanyi ahankali tace"


Allah ya mayar Mana da alheri yanxu shikenan Babu dabba ko daya a gidan nan dama wannan akuyar itace ta qarshe data rage duk sun sace.


Ganin har lokacin baisan metake fadaba cikin Dan daga murya takira sunansa.


Ya Dan motsa tareda dawowa hayyacinsa daidai shigowar abdulhakim 'dan dahiru Dan kimanin shekaru biyar Yana garo Taya baima wani iyaba

Ya qura masa ido wani irin rauni na ziyartar zuciyarsa da yanzu 'dan Zaki da nadiyarsa yakai shekarun Abdul inama ace kafin duk su rasu ko 'yaya sunbar masa Yana ganinsu.


Cikin dan daga murya da damuwa tace"


Dan allah nidai wannan tunanin ka ragesa kar wani ciwon ya kamata bansan ya zanyi da wannan rayuwarba idan wani abin ya sameka,

Ka rungumi qaddarar data samemu to meye amfanin tunanin.


Baice komaiba ya jinjina Mata Kai tareda miqewa ya dauki buta sbd Kiran magriba da ake qoqarin farawa.*****

_CHICAGO_

Daga airport Annah ce tazo ta dauketa  itada ps dinta Jasmin.


Tun a hanya Suka fara maganar abinda yakawota Chicagon itada Annah inda Annah ke sake Bata informations akan abinda tasani gameda haydars buildings Saidai cikin wani irin yanayi annah tace"


Girl do you really think you can handle this haydars?


Batareda nadey takalletaba ta fitarda numfashi Mai qarfi tareda bude wayarta tana kallon wani kyakkyawan hoton AM DILLA cikin ranta tana cewa"


I'm not here for you am Dilla.


Suna isa mum din Annah da kanta ta fito Suka rungume juna da tana Mata sannu da zuwa tareda tambayarta Mr A Noah.


Direct dakin Annah aka Kai Mata luggages dinta Jasmin kuwa guest room aka kaita.


Wanka tayi tayi tayi sallah tayi relaxing a sofa tsawon mintuna talatin kafin ta fito sukai lunch a table dukansu.


Qarfe biyar na yamma tasake wanka ta shirya cikin wata Italiano gown Mai shape sosai da budadden wuya blue color sai wadges aelexendra shoes tafito tana tana fidda qamshin Barbie royalle da posses.


Kallonta Annah tayi tareda kallon lips dinta dasukaji daity Brown lipstick Wanda baida wani kala sosai ahankali tace"


You gatta be kidding me baby... I mean like seriously are you going for business or something else?????


Wani shu'umin murmushi nadey tayi tareda daukar handbag dinta tafito tana cewa"


See you.


Dan hugging mum din Annah tayi a Palo kafin suka fice itada Jasmin.


Ahankali ta zuro qafafuwanta daga cikin motar tana qurawa sunan kamfanin dake rubuce baro baro a saman building din Mai kusan Hawa biyar.


Drivern mum na ajesu komawa yayi Suka nufi cikin building din Jasmin na bayanta securities kuwa sai sannu da zuwa suke Mata sbd itama ba laifi kusan ansata a labarai da jaridu da televisions the queen of Noah empire ltd.


A reception ta tsaya gaban baturiyar dake gurin tana Mata barka da zuwa ta shigarda proposal nason ganin Mr haydars.


Cikin sakin fuska da 'yar damuwa tace"


I'm really sorry ma'am I can't give inn ur proposal, sir is going out of the country may be next time ma'am.


Thank you""tafada tareda tareda juyowa zata wuce sukai karo da wata kyakkyawar yarinya data fito daga wani office ranta amatuqar bace.


Baya Sukayi dukkaninsu kowacce na kallon daya daga sama zuwa qasa.


Sake kallonta nadey tayi da kyau akaro na uku ta dauke gira daya sbd sake tabbatarda _FAMMAH DILLA_ ce....


Wani boyayyan murmushi tasaki tana sake qarewa kyakkyawar fammah din kallo wadda dagani zasuyi shekaru daidai da wayewa daidai Saidai dukiya da kowa ke taqama da tasa

Cikin sauqi tasamu hanyar shiga Dilla's.


Dan gyara kanta tayi tareda Dan yamutsa fuska tana gyara rigarta tareda kallon fammah din cikin wata irin yanga zatayi mgn fammah din da nadey tagama burgeta musamman sanin ko ita din wacece sbd tana ganinta a media dakuma irin matsayinda take Kai da qananun shekarunta da Basu wuce shekarunta,


Nd Noah ta burgeta tako Ina dama da irinsu kawai yakamata ta riqa abota duk da ganinta kamfanin yasamata Jin kishinta kadan akan haydar dinta dataga mutuwa a sonsa Wanda zata iya komai akansa Saidai Kuma bataga alamar soyayyace takawo miss Noah dinba saidaima business.


Fuska tasaki sosai tareda miqawa nadiyar hannu cikin yanga itama tace"


Fammah Dilla.


Ba musu nadey ta miqa Mata hannu tareda sakin murmushinda ita kadai tasan ma'anarsa tace"


Nd Noah,CEO Noah empire.


Cikin Jin dadi fammah tace"


Wow nice to meet you miss Noah.


Zatayi magana aka Kira wayar fammah din ta daga wayar tareda kallon nadey cikin sakin fuska tace"


Sorry I gotta go.,

Zaro wani kyakkyawan Kati tayi ta miqawa nadey din tana cewa"


It's my opening party today 9pm I hope to see you there.


Karba nadey tayi tareda kallon Katin cikin murmushi tace,


Yes sure miss Dilla.


Juyawa tayi ta wuce tana kallon Katin sbd yau tasan zata hadu da duka dillas,,,,AM DILLA am coming for you.

#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee29_*

Tana Isa gida Kaya kawai ta sauya zuwa wata half mini gown ta daure gashinta tareda amfani da wiper ta goge fuskarta da cleanser Mai sanyi ta kwanta Dan tayi relaxing jikin sbd fatarta tasake saki.


Kiran dad tayi tana daga kwancen Suka Jima suna waya kafin Suka gama takira nanny Nancy Suka dinga fira da baby zee da nannyn Saida Kiran JJ yashigo wayarta tasaki murmushin Jin dadin ganin number sa tayi sallama dasu nanny ta datse kiransu ta dauki nasa tana cewa"


Karkayi fada daddy j nakiraka kafin natafi but I couldn't reach you I'm sorry.


Ajiyar zuciya yasaki ahankali yanajin duk qorafinsa na narkewa sbd yanayin yanda take maganar da muryarta dake rusa kuzarinsa ko yaushe.


Cikin wata irin murya data sata Dan kallon wayarta da mamaki yace"


Please baby don't do this again kinji yanda kika sani damuwan tafiyanki batareda munyi mgn ba

Nayi booking ticket samune banyiba da ayau din nan Saidai kawai ki ganni Chicago.


Murmushi tayi Mai sauti cikin zuciyarta qaunar JJ din da tausayinsa na sake shigarta sbd taji qaunarsa ne sbd zakinta na tsananin qaunarsa hakama tanajin tausayinsane sbd yayi Rashin Zaki dakuma soyayyarta dake taredashi Wanda yasani har abada Babu filin soyayyar kowa aranta bayan ta zakinta.


Cikin sanyi tace"


Dady j Dan allah ka kwantarda hankalinka komai na tafiya accordingly so please Just take care of the empire and my daddy.


Aje wayar tayi tareda sake rufe idanuwanta tana sake relaxing jikinta.


Qarfe takwas tagama sallar ishai tafara shiryawa itada Annah zasu 

Ita Annah maison kwalliyace sosai so takira makeup artist akai Mata kwalliya tashirya cikin wata mini dinner gown daity blue Mai shegen daukan ido sai wasu black heels na laveeganxier sai pouch dinta tayi kyau sosai.


Tana gama kallon mirror ta juyo ta zubawa nadey ido data fito daga dressing room din dakin baki sake take cewa"


Holy Spirit,babe ure so damn hot I swear....


Gaban mirror nadeeyn ta iso ta tsaya tareda kallon kanta cikin wata fablic Italiano gown da stones dinta na rainbow ke rawa royal blue daidai jikinta wadda Bata kamataba Amma daidai jikintane sbd shape dinta daya fito sosai cikin tsari,


Blue vintage lious heels na a qafarta sai gashinta data daure cikin wata blue scarf qarami Mai adon tsones shima.

As usual brown lipstick ne a bakinta sai liner kadan da mascara da daliano pk powder.


Qamshin alexendral miss royalle ne ka tashi ajikinta saina oud kadan.


Diamond bracelet dinda ke hannunta da earrings dinta sai qyalli sukeyi ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda rintse idanuwanta takira sunayen Allah kafin ta bude tareda sakin murmushi cikin sanyi kafin ta dauki pouch dinta ta juyo takalli Annah dake kallonta tana murmushi tace"


Shall we???


Yes ma""tafada tana dariya suka fito.


Jasmin ma ta shirya tuni tafito su take jira Suka fito cikin wata baqar marceedes Benz 3600baymach2018 Suka fito Annah ce ke driving dinsu.


Hakanan takejin wani irin Rashin Jin dadi na shigarta,

Zuciyarta wani irin daci da qunci takeji

Da mijinta na raye da yanzu tanacan tana rayuwar aurenta hankali kwance kamar kowane ma'aurata,

Duk wannan dukiyar da daular datake ciki yanzu duk wannan murmushin nata da farin cikinta its all fake cikin zuciyarta qunci ne fal na Rashin mijinta da babanta Wanda take kwana dashi take tashi dashi aranta

 tafison rayuwarta ta dah,

Tafison zama cikin rufin asiri inda mijinta da mahaifinta duk kuwa da Rashin jituwarsu.


Dafa hannunta Annah tayi ahankali tareda Kiran sunanta tana cewa"


Hey Nd are you ok?


Murmushi ta qaqalo tareda mayarda hawayenda Suka ciko Mata ido ta juyo ta kalli gurin sun qaraso.


Wani babban mansion ne Sukazo ta bude ta fito ahankali zuciyarta na harbawa ta juyo ta kalli sunan dake rubuce a locks na gidan daga gefe kan wani Dan madaidaicin block board dake jiki anrubuta _welcom to Dilla's_

Qurawa sunan ido tayi radadin rabuwa da mijinta na dawo Mata sabo hakama mutuwar 'yar uwarta qwaya daya tal da itace hasken rayuwarta.


Gyara tsayuwarsa tayi tareda kallonsu Annah tasaki murmushi tareda yin gaba itada Annah Jasmin na bayansu.


Securities Suka miqawa invitation dinsu aka bude musu qofa Suka shige tasake sakin wata ajiyar zuciya lokacinda tashigo cikin mansion din 

Yau gata ga dillas Wainda Babu Wanda yasanta sai yanzune zasu dandani nata dafin dayafi nasu.


Open space party ne so a wani babban filin shaqatawa dake baya gurin swimming pool na gidan ake bikin anyi decorations masu kyau da tsada gurin sai wani haske da qyallin wuta ke tashi duk yawanci turawa ne Amma akwai baqaqen fata Saidai basukai turawan yawaba,


Duk Wanda ke gurin to tabbas babu Mai qaramin qarfi ga securities tako Ina anzubasu.


Cak ta tsaya tsakiyar filin ta qurawa inda suke ido suna nishadi cikin farin ciki sosai suke 

Babu wata damuwa a rayuwarsu kamar Basu dauki rayukan mutane da damaba,

Sun saka mutane da dama kukan maraici Dana azaba,

Sun mayarda yara da yawa marayu,

Sun mayarda mataye da yawa zawarawa,

Sun saka iyaye da dama kuka da ciwon Rashin yayansu....yanxu lokacinsune dasuma zasu dandani wannan radadin da ciwo.


Dikko Dillan ne a tareda wasu turawa Wainda dagani manyane tasanma daya daga cikinsu mayor ne suna magana kowanne da glass din drink a hannunsa dukkaninsu cikin wasu irin tsadaddun designer kaftan suits,

Sai zeel dilla a gefensa itama taci ado white diamonds da wata Canadian tribe gown black tayi kyau sosai sbd kyakkyawa ce shiyasa daga am har fammah sukeda kyau Dan ita suke biyowa.

 Am Dilla ne a gefen dad dinsa shima yayi kyau cikin wasu ash suit data fiddo kyawunsa da hutun dake tattaredashi dukkaninsu dariya sukeyi cikin kwanciyar hankali da nishadi.


Fammah ce dataci wani irin ado itama cikin doguwar English Morocco maroon gown Mara hannu tayi kyau matuqa musamman dayake ita farace sosai,

Hango shigowarsu nadeey tayi tasaki wani murmushin farin cikin ganinta tana kallon nadey din duk saitaji kamar zata Raina tata kwalliyar tabbas tasamu best friend dinda ta Jima tana nema Dan dama ita batada kwashe kwashen qawaye yanxune Kam zatayi qawarda hotunansu zasu ringa yawo a media da press.


Kallon iyayenta da brother dinta tareda ajiye glass din hannunta tana kallon nadeey tace"


Mum dad and am my special guest is here lets welcome her please.


Dukkaninsu atare Suka juyo inda fammah ke nuna musu.


Cikin wata irin tafiya ta daukar hankali dake nuna isarta tana sakin wani fitanannan murmushinda atake yagama tarwatsa zuciyar am da babansa ta nufo gurin tana juya jikinta kamar wata sarauniya.


Dukkaninsu baki ido Suka zuba Mata cikeda mamaki da farin cikin haduwa da ita Dan kuwa duk sun santa a media da harkar business sunkai proposal dinsu harso biyu wa kamfaninta Saidai Bai samu isaba saigashi yau itace agabansu cikin gidansu the queen of Noah empire 

Tabbas ita din babbar special guest ce.,


Zeel kuwa necklace dinta da brcelet dinta na diamond take kallo tana qiyasta kudinsu kafin ta mayarda kallonta kan kyakkyawar fuskar miss Noah din tana qiyasa,kudi,kyau,gayu,burgewa,ilimi tareda wayewar nadey din duk abinda takeson matar am 'dinta ta hada harta zarta tabbas yau tasamu irin matar datakeson am da ita wadda dukiyarta tasa duniya ta sanda ita.


Mr Dilla kuwa gabaki daya miss Noah tagama basa mamakin haduwa da ita sbd ya Jima yanason shiga cikin business din Noah empire sbd tarin dukiyarsu da success dinsu tareda sunansu Saidai baisamu damaba yau ga dama ta samu tabbas bazai taba Bari haduwarsu ta tsaya iya nanba sun hadu kenan saisun shiga cikin dukiyarta sun mayarda duka dukiyarta tasu,duk wani kamfanin Noah saiya dawo Dilla.


Ahankali am ya ajiye glass din hannunsa Yana kasa dauke idanuwansa akanta zuciyarsa na wata irin harbawa,

Baitaba Jin son wani abuba lokaci daya kamar wannan 

Love at first sight.


Tana qarasowa cikin wani irin murmushin Jan aji take kallonsu 

Fammah takalli iyayenta cikin farin ciki tace"


Dad mum meet my friend Nadey.


Cikin Jin dadi da sakin fuska sosai Mr Dilla yace"


Nice meeting you mss Noah.


Murmushi tasaki cikin Jin dadi tace"


No the pleasure is mine Mr Dilla.


Kallon mss zeel tayi tareda miqa Mata hannu fuska a sake sosai tace"


_ND NOAH_.


Maimakon ta Bata hannu cikin tsananin farin ciki da qaunar nadey din ta rungumeta tana cewa"


Welcome.


Tana boye mamakinta da farin cikinta dake bayyane ta rungumeta tana cewa"


Thank you mrs Dilla.


Juyowa tayi kan am da tuni dukkanin jikinsa yasaki kowane motsinta yagama burgesa da tafiya da imaninsa.


Ganin yanayinsa yasa tasake sakar masa wani shegen murmushin tana masa wani kallo dayasashi sakar Mata murmushi Yana gyara tie din wuyansa dayaji Yana shagesa ya kalleta Yana gyara tsayuwa da muryarsa mai dadi yace"


Am dilla and nice to meet you queen Noah.


Dariya tadanyi tareda cewa"


Thanks Mr am.


Gabatar musu da Annah tayi a matsayin friend dinta nan suka gaggaisa kowanne na qoqarin janta da fira sunayi harta Dan business Saida Sukayi kafin nan aka fara gabatarda partyn.


Duk inda tayi idon am na kanta iyayensa da qanwarsa tuni Suka ganosa mum dinsa kamar ta goyasa sbd dadi hakama dikko ji yayi kamarma su tara Yan press su sanar musu auren ND Noah da dansa am Dilla.


Fammah ma baqaramin dadi tajiba sbd hakanan tahi hankalinta na masifar tashi idan ta tuno haydar dinta da nadeeyn data gani a haydars buildings Saidai yanzu am ya taimaki fargabarta.


Duk abinda sukeyi tana luredasu saima sake sakar musu fuska datakeyi Suka qara shiga cikin qaunar alaqar.


Sosai Suka sake Sukayi enjoying partyn tareda juna duk wani abinda suke so akanta da am Babu wani kwana kwana sun fito sun nuna maitarsu.


Sosai Sukayi fira da am ta Dan sake masa Suka danyi magana 

Bakin zeel gabaki daya yaqi rufuwa sbd farin ciki sai nunawa qawayenta takeyi tana wani dagawa danta yayi matar aure.


Da aka watse am din da kansa yadawo da ita gida da niyar gobe zaiso su fita.


Bayan ya ajeta bayan motarsa tabi da kallo tana jinjina irin wasan dazasu buga.


Tana shiga gidan Bata tsaya kula Annah dake tsokanarta ba ta wuce ta tube ta fada toilet tareda rufe idanuwanta hawaye Suka gangaro Mata.Yana komawa gida mum dinsa ta taresa cikin zumudi tana cewa"


My am hope baku rabuba Saida kayi proposing?


Wani murmushin farin ciki yasaki tareda kallon dad dinsa dake kallonsu yana jiran Jin abinda am din zai fada yace"


Mum gobe zamuyi magana da ita.


Fammah data sauko daga stairs sanye da kayan bacci ta qaraso tana cewa"


Zanyi farin cikin nadey tazamo member ta cikin familyn nan gskia.


Kallonta mum tayi tana cewa"


Idan munason hakan yakamata kiyi convincing dinta tadawo nan gidan gurinki kafin ta tashi komawa Kinga by then am yagama sace zuciyarta I really want this to happen as early as possible gskia.


Kallonta fammah tayi zatayi magana am yayi saurin cewa"


Yes please fammah convince her.


Kallonsu tayi tareda miqewa tsaye tana cewa"" zan gwada nagani

saidai Nima inada baqo goben banso fita koinaba my haydars is coming sbd baisamu zuwa jiyaba.


Wani dadi yasake kashe zeel tana cewa"


Oh my God my children zasu kasheni da farin ciki.


Dilla kuwa shima wani shu'umin murmushin yasaki ganin zai Kama wuyan manyan business tycoons alokaci daya,lallai wannan karon dillas yakusa zama number one top billionaire sbd daga Noah empire har haydars buildings saiya tabbatarda komai nasu sundawo na dillas.

#MAMUH*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


_mamuhgee30_

_Not edited_

Washe gari hakanan ta tashi da farin ciki tareda wata irin nutsuwa datake jinta aciki saita alaqanta hakan da burinsu daya dauko hanyar cikane akan abinda suke jira shekaru.


Cikin nutsuwa tayi waya da dad dinta da JJ tafada musu komai shidai dad hankalinsa Bai wani kwantaba sbd sanin mummunar illar dikko da zuriarsa matuqar Koda Wasa Suka gano ita din wacece ba qaramar illa zasu Mata ba Sam bazaizo wani Abu yasametaba,


Cikin kulawa da damuwa jiki sanyaye yace"


Nadey please be very careful ok???

And please take care don't let them know anything daya shafeki tundaga past naki har yanzu dai komaima dangane da personal life dinki karki Bari su sani,

Ths people are very dangerous,they can kill without any hesitation stay alert.


Ok dad don't worry I will be extra careful and I promise you I will set everything right in a short time.


JJ kuwa irin kallon dayake matane yasa jikinta Dan yin sanyi sbd video call ne sukeyi 

Ko magana yakasa Jin zancen am na sonta Kuma yagama ganin alamar kulasa zatayi Saidai Sam shi wannan plan din Bai masaba sbd sanin Dole zasu iya ganota idan batada backup Kuma wlh bazasuji shakkar kashetaba kamar yanda sukeyiwa kowa

Yayi aiki dasu yasan sirrinsu Dole tana buqatarsa ta wannan fannin.


Kallonta yayi cikin wani irin yanayi Kai tsaye yace"


Zuwa jibi zan tattara komai nayiwa director handling komai na Noah I will be coming to you 

You are not safe alone acikin wainann dabbobin.


Zatayi magana ya datse Kiran tareda miqewa ko magana Bai tsayayi da dad ba ya fice zuciyarsa kamar zata qone sbd zafin kishi.Itama dafe goshi tayi cikin damuwa tace"


Dady j Dan allah karka wahalarda rayuwarmu banason ganinka cikin wannan halin sbd bazan iya baka abinda kakeso you deserve someone better.


Fammah ranar tazo gidan anan ta wuni Saida yamma Suka fita sukaje spa dinta da akai partyn budewa sundan Jima acan suna dudduba abubuwa sai dare Suka dawo ta ajiyesu ta wuce gida sbd ranar gabaki daya she's Moody akaro ba adadi haydar yaqi zuwa.


Tun daga ranar kullum suna tareda fammah sbd tuni sukai shaquwa ta saki jiki sosai da fammah din harta Kai kusan ko yaushe suna tare.


Ta gefen am ma sosai tasake masa yasake matuwa a sonta kusan ko wace hour saiya Kira wani lokacin kuwa shike zuwa ya dauketa su fita yawo shiyasa hankalin zeel yasake kwanciya sbd zuwa lokacin ansanda maganar akwai soyayya da maganar aure a tsakanin Noah's da dillas.


JJ yazo Saidai ta boye suke haduwa suna magana akan wasu takardun bugi datasa yayo Mata zatayi wani amfani dasu.


Zeel baqaramin so da kulawa take nunawa nadey ba musamman takanas ta dauketa Suka fita wani magazine meeting Dan kawai ta nuna nadey dince matarda 'danta zai aura.sanye da half sleeping dress dinta black ta fito sitting room ta tarardasu mum suna kallo dasu Annah ta qarasa  cikinsu tana cewa"


Gud morning mum??


Morning sweetie""mum din tafada tana kalllonta.


Tana qoqarin zama suka miqe Suka hau table breakfast.


Suna gamawa ta wuce daki tashiga wanka kusan mintuna ashirin kafin tafito ta zauna tana qoqarin fara Shirin Annah tashigo tana sanarda ita zuwan fammah.


Mamaki tayi tareda kallon agogo qarfe goma Sha daya na safe ta dauke gira daya tareda Dan sakin murmushi ta miqe bayan tagama shiri ta bude closet ta dauko wata Ashape shaking gown Mai dogon hannu tasa ta fesa turare ta dauki wayarta tareda zuri slippers ta fito palon tana murmushi cikin wata irin yanga tana cewa"


Wow wat a pleasant visit fammah.


Tashi fammah tayi suka Dan rungume juna kafin Suka zauna cikin walwala fammah din tace"


Sorry I came without informing.


It's ok.


Fira sukeyi dukkaninsu harda Annah duk akan wani beauty parlor ne da Annah zata bude itama daganan sai fammah ta kalli mum din Annah dake zuwa tace"


Mum tun jiya brother na ya fita hayyacinsa akan 'yarki and please mum my fiance is coming I would like  nadey to be there with me only for the weekend please.


Kallon nadey mum din tayi tace"


Nadey are you.....


It's ok mum I can go""" tayi saurin fada cikin basarwa Dan dama itama tanason zuwa gidan tashiga jikinsu Sosai.


Cikin farin ciki fammah takira am 

Bayan two hours saigashi yazo daukarsu yaci ado cikin wasu designer mark$spencer.


Cikin girmamawa ya gaisa da mum inda Suka Dan fira kafin su nadey Suka fito fammah na janye da 'yar luggage dinta.


Tunda Suka fito yakasa dauke idanuwansa akanta yanajin zuciyarsa na sake narkewa akan sonta,

Jiyake idan Bai sameta amatsayin tasaba zai iya rasa numfashinsa lokaci daya.


Ganin yanda yake kallonta yasa tacigaba da juya jikinta tana tahowa cikin yanga tana fuskarta ba wani a sakeba.


Fitowa Sukayi Suka wuce.


Wata irin tarba mum zeel tayi Mata cikin tsananin farin ciki sbd so take tayi yanda zatayi nadey ta gabatar musu da dad dinta Dan ayi maganar auren ita so take ayi cikin qanqanin lokaci.


Babban bedroom din fammah da ita kadaice a upstairs din sbd shi am part dinsa daban acikin gidan,

Anan Suka yada zango take aka shigarda kayanta closet Batai komaiba ita Saida tayi sallah sbd bataga alamar gidan suna sallah ba qila.Kwananta biyu a gidan tagama karancesu da duk wani lungu da saqo na gidan tareda sawa harkar business dinsu ido sosai sbd bazasu taba iyawa dasuba tukuna sai sun fara rabasu da dukiyarsu.


Yau tana Gama waya da dad ta fito dukkaninsu Suka hadu a dining room Sukayi lunch inda suna gamawa sukazo Suka zauna itada dad din suna firar business ahankali tareda am din dake zaune kusada ita kamar wasu couples dadi sai sake Kama zeel yakeyi.


Suna cikin firar ne wayarta tayi ringing ahankali tace"


Excuse please""tareda daukar wayar tana miqewa ta koma gefe.


Wat????tafada cikin Dan bacin Rai kafin ta sake matsawa nesa dasu tana cewa"


Ya za'ayi suce abasu wannan proposal din akan 70% basuda hankaline?

Look Jasmin kusake meeting dasu idan sunason nayi musu hanya a Basu wannan deal din saisun yarda zasu zuba 80% Ni kamfanina na zuba 90% and cikin wata shida Suka dawo 150%

So idan zazu saka 80% kuyi magana idan babu kuwa tell them I'm backing out.


Ta jikin tangamemen agogon datake tsaye gabansa tagansu tsaye abayanta suna sauraron duk bayaninta tasaki wani murmushi tareda cewa"


Ok I'll talk to you later Amma yanzu zan turo miki information da details na investment company din saiki Basu.


Rubutu tayi ta turawa Jasmin text din ta juyo saita gansu zaune suna firarsu kamar Basu tashiba.


Tana zuwa ta ajiye wayarta gafen am tana cewa"


 Baby I will just use a washroom and com back ok.


Cikin kulawa yace"


Ok.


Tana hayewa sama ta boye tana kallonsu taga am din ya dauki wayarta yayi forwarding din information da details din investment companyn zuwa email din kamfaninsu.


Ya goge ya ajiye wayar.


Kallonsa Dilla yayi tareda miqewa Yana cewa"


Ka tabbatarda ka riga kamfaninta neman wannan kamfanin ka shigar musu da percentage dinmu Mai yawa yanda zasu karbemu mune zamu samu wannan 150% din wannan karon.


Gyada Kai am yayi 

Zeel kuwa cikin nutsuwa tace"


You better be very careful karta gano anmata zagon qasa a harkar business tazo tace tafasa aurenka.Cikin murmushi tasauko tadawo kusadashi ta zauna tana cewa"


Baby nadawo na dauki wayana I'm little bit tired I will go and have some rest.


Tana zuwa daki ta rufe qofa ta nemi wayar JJ.


Yana dauka tace"


Be ready kowane lokaci zasu nemeka kace 70% share na dukiyarsu zasu saka within 3month zaku Basu 150%.


Harzata kashe yace"


Baby please be careful ok.


Ahankali tace"


You too please.


Kwantawa tayi tareda rufe idanuwanta ahankali tana neman relaxing.


Washe gari tunda safe Suka fice da fammah shopping sbd yaudai baqonta yace zaizo.


Daga can gidansu Annah ita ta sauka fammah din tadawo gida.Zaune suke a office room dinsu dake cikin gidan am ya kalli dad din yace"


Dad munyi magana da wannan investment companyn gskia inaga akwai ha'dari fa musaka fiyeda rabin dukiyarmu aciki kar azo asamu matsala why not musaka kadan mugani.Shiru Dilla yayi cikin nazari Saidai Kuma irin ribarda yaji nadey din tafada tasamu da tana waya yasa yaji Yana kwadayin mallakar fiyeda ribar barema tunda su Noah's sunyi sun samu manyan kudi shima zaiyi.


Kallon am yayi yace"


Ka saka fiyeda rabin kawai zamu fita idanma ansamu matsala zanji da kamfanin Susan dawa sukai.


Batareda hankalinsa ya kwanta da abinba yasaka hannu a takardun dad dinma yasaka ya kwashe files din ya fita dasu Dan zuwa suyi meeting da waincan kamfanin.*****

Qarfe biyar na yamma wata baqar BMW E33class2018 ta iso gaban babban gate din Dilla mansion aka wangale masa yashigo sbd sunsan da isowarsa.


Tunda yayi parking a harabar fammah takasa hakuri ta fito cikin wani irin adon dayayi mugun yimata kyau tana tahowa gurinsa cikin daukar hankali tana farin cikin zuwansa data kasa boyewa yaudai iyayenta zasuga haydar datake damunsu akai.


Ahankali ya bude qofar motar ya zuro qafafunsa dake sanye cikin brown amadeo testoni antiqued leather Oxfords shoes kafin yafito gabaki dayansa sanye cikin baqaqen Louis Vuitton.


Kadan ya rage fammah ta suma sbd yanda numfashinta yake neman sarqewa da sonsa.


Iskar harabar gurin ya shaqa ahankali tareda sauke ajiyar zuciya kafin ya kalli fammah cikin wani sahirtaccen murmushi.


Cikin tsananin farin ciki take qoqarin riqo hannunsa ya saka hannuwan cikin aljihun wandonsa Yana kallonta da mayun idanuwansa cikin maryarsa me dukan zuciyarta yace"


Shall we???


Da sauri tace"


Yes sweetie.


Palon gidan Suka nufa inda mum da da dinta ke zaune suna jiran isowarsa Yana shigowa Suka miqe cikeda farin cikin ganinsa akaro na farko,


Kyakkyawa ne Mai qaqqarfan jikin namijinda daga gani Yana motsa jikinsa sosai,


Farine Saidai ba sosaiba Saidai Dan gefen wuyansa dayayi Dan baqi alamar tabone agurin,


Sake kallonsa zeel tayi tana Yana kyawunsa da quruciyarsa dabai wuce shekarun am dinta ba Amma shine yakeda irin wannan tarin dukiyar.


Hannu Dilla ya miqa masa cikin sakewar fuska zaiyi magana haydar din ya rigada da cewa"


_Haydar A D_


kallonsa Dilla yayi cikeda mamakin muryarsa Mai wani irin amo

Murmushi yasaki tareda cewa"


Nice meeting you haydar.


Thank you yace Yana kallon hannunsu dake sarqen Dana juna.


Cikin farin ciki zeel ma ta Dan matso Suka gaisa ya amsa Yana kallonta da murmushi kan fuskarsa.


Kafin suka dunguma zuwa cikin tsakiyar palon Suka zazzauna suna sake gaisawa.


Daga gurin meeting din am ne yabiyo gidansu Annah ya daukota suka nufo gida tana sake masa wani irin salo Dan son Jin komai gameda sauran shares dinda suka rage musu Saidai Bai wani bude Mata zancen sosaiba har Suka iso gidan.


Sanye takeda riga da wando Palazzo sai wasu wadges brown a qafarta da Yar jakarta Suka nufo cikin palon suna fira murmushin tarkonta dasuka fada yakasa barin fuskarta shikuwa duk ya dauka sbd shine takeyi sai sake sake Mata yakeyi.


Am dinne a gaba gurin shigowa kafin tashigo tana murmushin dake qarawa fuskarta kyau.


Ahankali ya miqe tsaye Yana kallonta da idanuwansa dake rudarwa.


Am na qarasowa yasaki fuska cikin farin ciki ya miqawa haydar din hannu yana cewa"


 wow Mr haydar wat a pleasant meeting.


Kallon am din yayi ya fiddo hannunsa daga cikin aljihu sai kawai ya miqawa nadey da kallo daya tayi masa ta dauke Kai sbd jin bugun zuciyarta na qaruwa.


Dukkaninsu da mamaki sukabi hannunsa daya miqawa nadeyn yace"


I'm haydar.


Kallon fuskarsa tayi tsawon seconds saitaji takasa Hana kanta miqa masa hannu ta dago hannu a hankali ta miqa masa murya na rawa tace"


ND Noah.


Murmushi yasakar Mata tareda zare hannunsa data qurawa ido.

#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*_Mamuhgee31_

Da sauri tasake bin hannunsa daya janye daga nata dukkanin fuskarsa na bayyanarda wani boyayyan murmushinda yasake jefa kowa cikin mamakin abinda yafaru.


Fammah ce tasaki murmushi tana cewa"


Everybody just chill nadey and haydars are business partners I think so please let's all sit and talk about me and my haydar.


Dukkaninsu ajiyar zuciya suka sake a boye musamman zeel da dad din data fara shakkar kar 'daya daga cikin 'yayanta su rasa wainnan biyun.


Zama duk Sukayi ta dago qafafuwanta dasukai sanyi ta zauna kusada am tana qaqalo masa murmushin dole dako gama fitowa baiyiba.


Dagowa tayi ahankali lokacinda am ke gabatar masa da ita amatsayin wadda zai aura ta kallesa idanuwansu suka shiga cikin na juna sbd yanda ya xuba matasu ko qwaqwaran motsi kasawa tayi atake ta sarqe tafara tari ahankali.


Da sauri am ya dauki ruwa ya Bata Yana Mata sannu cikin kulawa Saidai tana saka ruwan bakinta ta qarasa sarqewa sbd azabar dayake Bata da idanuwan nasa Dan har lokacin ko qyaftasu daga kanta baiyiba saima wani irin ja dataga sunayi


Take tsoro da fargaba suke neman shigarta ta miqe da sauri tareda cewa"


Excuse me daqyar tana tari ta nufi stairs da sauri ta haye.


Miqewa am yayi zaibi bayanta haydar yayi qyaran murya tareda cewa"


Ya dawo su Gama gaisawa Mana.


Dawowa yayi Suka cigaba da 'yar fira Saidai dukkaninsu hankalinsu na saman musamman haydar da tuni idanuwansa suka sake rinewa ya miqe batareda yaqara wani lokaciba yace zai tafi.


Duk yanda fammah tayi masa magiyar ya tsaya suyi dinner 

Qarshema yanayinsa ya Bata tsoro tayi saurin tsuke baki ta rakasa mota ko qarasowa batayiba ya fice ya barta tsaye.


Hawaye taji sun ciko idanuwanta tana tsaye taji suna neman sauko Mata.,


Meyasa haydar baitaba nuna Mata kulawa ko so ba?

Meyasa tunda ta hadu dashi a airport Zurich take mutuwar sonsa tana bibiyarsa Yana wulaqanta rayuwarta.


Dafata taji anyi tana juyowa taga am tayi saurin fadawa jikinsa tareda sakin kukanta datake dannewa.


Shima jikinsa sanyaye yake sbd yaje yayi knocking qofa kamar me nadey taqi budewa tamayi kamar Bata jisaba.Ita kuwa nadey hakanan taji hankalinta yayi matuqar tashi tarasa Ina zata saka kanta wani irin shakkar idanuwan wannan haydar din takeji ta rasa meke Mata daidai sai kawai ta zauna bakin gado hawayenda batasan Kona meyeba suna sauko mata.


Tabbas idan har tanason gujewa wannan fargabar koma ta meyene to Dole tayi tagama abinda yakawota tabar nan musamman yanxu da JJ yafara damuwa da maganarta dashi sbd kar wani Abu ya gifta musu ita kuwa idan Koda auren am ne ke nufin kawo qarshensu a shirye take da hakan,

Saita tarwatsa rayuwarsu ta yanda bata taba haduwa zata bar gidan.Daqyar ta tashi tayi sallah tayi wani wankan tasaka doguwar Pakistani gown ta sauko lokacin dinner Sukayi dinner Yan gidan nata farin ciki da murnar zuwan haydar din.


Itadai Bata tsaya wani dogon firaba tana gamawa ta haye Suka bita da sannu cikin kulawa.Washe gari tana tashi ta shirya cikin blue skinny jean da white loose lace chiffon half top tayi rolling din gefe da wata qaramar scarf ta dauki handbag da wayarta takalli fammah dake faman Kiran wayar haydar tunda safen Amma baya dauka qarshema ya kashe wayar.


Ficewa tayi tana cewa"


I have a morning private meeting da wasu client Dina so saina dawo.


Tana fita Bata hadu da kowa a Palo ba ta fice.


A harabar gidan ta hadu da am yafito daga sashenda yake geaming jikinsa sanye da kayan geaming din sai sneakers na Adidas.


Qarasowa yayi gurinta lokacinda take fitowa Yana Mata wani kallon so yace"


Gud morning luv.


Murmushi ta mayar masa cikin kulawa da kashe murya tace"


Morning baby.


Are you going somewhere???


Yes baby I have some clients to attend to.


Ok lemme freshen up and.....


Katsesa tayi da cewa"


No I can manage besides I won't be long.


Ok luv you can take my car then.


Keys din motarsa ya dauko Mata ya Bata ta karba tareda kashe masa ido tana cewa"


Thanks baby.


Shiga motar tayi tareda Bata wuta ta wuce sbd sauri takeyi tanajin wayarta na vibrating cikin Jakarta takuma San JJ ne sbd dashine zata hadu.Tana fitowa ta hau titi da speed sosai sbd yau Dole zasu hadu da lawyers dinsu su karbi takardun fiyeda rabin dukiyarsu Dillan dasuka karba a jiyan.


Wani babban restaurant dake cikin wani babbn 5star ta nufa inda acan suke haduwa da JJ.


Tana Shan kwanar restaurant din wata baqar jaquar Tasha gabanta da qarfi ta Danna burki tareda dagowa tana cewa"


Oh my God wayyo Allah banana.


A fusace ta dago zata fito tagansa ya fito motar cikin kayan geaming shima black dasuka fiddo kyau da farin fatarsa ya nufo mitarta cikin wani irin taku Saidai kallo daya zakawa fuskarsa kasan ransa a matuqar bace take.


Mugun faduwa gabanta yayi take jikinta yadauki rawa musamman yanayin qirar jikinsa datake neman fitarda ita hayyacinta hannunta na rawa ta bude motar tana fitowa Yana kawowa dad da motar zai bude qirjinsu ya hadu da qarfi 

Tayi baya zata fadi ya riqo hannunta tareda fizgota ya matse jikin motar.


Rintse idanuwanta tayi da sauri jikinta na rawa sosai komai takasa tunanin yi.


Shima rinte idanuwansa yayi Yana qoqarin controlling kansa Saidai Sam yakasa da qarfi ya daga hannu ya daki jikin motar Saida ya lotsa yayi baya Yana dafe kansa dake qoqarin tarwatsewa jikinsa har wani rawa yakeyi jijiyoyin qarfinsa duk sun firfito.


Tana bude ido taga yanayinsa hankalinta yasake tashi a rude ta fada motar jiki na rawa ta tayar tabar gurin da mugun speed.Tana Isa 5star din ko parking me kyau batayiba ta fito ta shige.


Saida tashiga elevator takuna tafara dawowa hayyacinta tana sauke ajiyar zuciya har lokacin jikinta na rawa.


Tana isa restaurant din tasake daidaita kanta sbd kar JJ yaga yanayinta hankalinsa zai iya tashi yayita tambayarta.


Share Dan zufanta tayi ta nufi table dinsu dake can qurya tana Dan sake fuskarta.


Tana qarasowa ya kafeta da ido Amma sbd suna tareneda lawyers dinsu guda uku saiya basar Yana tambayarta yanda take cikin kulawa.


Amsawa tayi tana sake daidaita kanta ta zauna tana gaisawa dasu Mr Jonas.


Fitarda takardun JJ yayi masu signature din dikko da am

Takardune na bayarda fiyeda rabin dukiyarsu ga wannan investment kamfanin da sunan su samu ribar fiyeda ninki biyun abinda Suka bayar.


Atake Suka gama duk bayananda zasuyi Suka gama akan daganan Courts zasuje ana bugawa takardun stamp shikenan komai nasu dillas yadawo nasu.


Tasowa Sukayi dukkaninsu cikin farin cikin samun abinda sukeso cikin sauqi.


Itace agaba itada JJ Suna fitowa tayi saurin yin baya ta boye tana leqen Dilla data gani tareda wata former Mayor din San Diego cikeda mamaki.


Kallon JJ yayi tace"


Is he having an affair????


Girgiza Kai JJ yayi Yana leqensu har Suka tsaya jiran lift cikin mamaki shima yace"


Dilla baya neman Mata ko kadan a rayuwarsa sbd son kudinsa da hadamarsa yasan mace zata iya rabasa da komai nasa shiyasa baitaba neman Mata ba sbd gudun sukawo masa matsala idan Kinga Dilla da mace to business ne Kuma babba.


Wani tunanine ya shigeta ta kalli JJ tana kallonsu suna Kiran budewar lift  tace"


Dady j ka tattaro Mana press sumtin is about to happen.


Tana Gama fada ta warware scarf dinta ta rufe fuskarta tareda zuwa gefensu ta tsaya daidai lift na budewa Suka shiga itama ta shiga.*_Dan Allah kuyi manage wlh inada wani babban uzurine yau da gobe Ina fatar zaku fahimceni🙏🙏_*

#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee32_*

6th floor suka nufa suna fitowa lift din itama ta fito ta tsaya tana latsa wayarta tana sake rufe fuskarta da scarf din harsai dataga room dinda suka shiga,

Juyawa tayi baya ahankali taga Babu kowa tayi saurin qarasawa taga room number din ta matsa sosai zata Dora kunnenta taji motsin tahowa tayi saurin matsawa tana tafiya tana Dan latsa wayarta Amma hankalinta nakan waitress dinda tafito wani room zata bar floor din.


Saurin bin bayanta tayi tana Kiran JJ suna shiga lift Yana dauka qasa qasa tace"


JJ pls Ina buqatar tque a bar din cikin restaurant dinsu yanxun nan ganinan zuwa.


Restaurant din ta nufa da sauri bayan sunfito lft waitress din na gabanta.


JJ tafara nema cikin gurin tana duddubawa saigashi Yana zuwa gurinta ya miqa Mata a boye da sauri ta karba tasaka Jakarta ta nufi gurin wata waitress tasaki fuska cikin Dan karyar da Kai yace"


Please can you help me call room 409 I want to make sure of wat to order for my husband please.


Sure ma'am"" waitress din tafada tareda daukar wayar restaurant din tayi dialing room 409 din ta miqawa nadey tareda juyawa dauko wani menu Dan bawa nadey din.


Qasa nadey tayi tareda saurin canza murya ana dauka tace"


It's Restaurant sir wat are your orders???


Sam bai cika wani cin abinci ako Ina yajeba sbd gudun a cucesa shi haka Allah yayisa Sam baida yarda Amma ganin zasu Jima suna magana da mayor sai kawai yabada order din ya aje wayar suna cigaba da duba wani private project dasuyi tsakanin dillas empire da ita.


Aje wayar nadey tayi tareda kallon waitress din tana murmushi tace"


Oh thank you so much miss you just save my marriage today because my husband is very short temper.


Bayarda order dinsa tayi aka kawo aka ajiye ta kalla chicken sandwich ne da fish potatoe soup sai Italian sausage.


Ya mutsa fuska tayi tareda sake kallon  soup din ta zura hannu handbag ta fiddo qaramar kwalbar ta bude ta juye ciki tareda mayarda kwalbar Jakarta tareda sarin juyawa daidai nan waitress din ta juyo tareda daukar arder din ta tafi kaiwa room din bayan nadey tafada Mata room number.


Bayanta nadey tabi da kallo tareda dauke gira daya tana qissima abinda takeson yafaru din.


Komawa gurin JJ tayi tareda yin qasa da murya tace"


Ka kirasu kuwa?


Kai ya daga Mata Yana kallon qofa inda sosai ya qurawa qofar ido baya ko qyaftawa sbd abinda idanuwansa suke gani.


Haydar ne ke shigowa gurin sanye cikin Louis Vuitton black 

ash suits fuskarsa sanye da warby shades fuskarsa ba asakeba Sam Saidai Kuma kwarjinsa da burgewarsa suke daukar hankalin mutane akansa.


Batareda nadey ta luradashiba takira JJ Suka bar gurin zuwa reception.


Agogo take kallo tana qiyasta lokacinda ta dibarwa aikin abinda ta zuba musu yacika ta miqe tareda kalon JJ ta daidai shigowar wani shagararran Dan press a gurin Wanda yake tamkar friend din JJ din ne.


Kallonsa nadey tayi tareda gyara tsayuwa tafara koro masa bayani abinda takeso.


Wani murmushin Jin dadi yasaki yace"


Karki damu miss Noah muda muke neman abin yadawa ido rufe musamman ma yau munsamu akan Dilla's empire I promise yau saina nuna masa the power of media sbd yataba zaginmu ya wulaqantamu.


Room number nadey tabashi cikin Jin dadi shida JJ ne Suka fara zuwa dakin bayan sun rufe fuskokinsu da facing caps.


Ahankali Suka tura qofar dakin ta cikin saa ta bude JJ yafara leqawa yaga dukkaninsu sun sunyi marus a inda suke zazzaune.


Nadeey ce tashigo dakin ta dauki takardun gabansu tafara duddubawa taga contact ne suke Shirin hadawa harma sunyi signing.


Kudine yakeson tabasa almost 1mil dollars yayi wata kwangilan wani babban project Saidai baida millions dinda project din ke buqata yanxu sbd sun zuba fiyeda rabin dukiya da kadarorinsu a wancan investment din.


Yaga takardar tayi ta bude Jakarta ta zuba takardun cikin sauri har handbag din na faduwa abubuwan ciki Suka zube tayi saurin tattarawa ta mayar tareda Kama mayor dake marus ta mayarda ita kan gadon dakin.Ficewa Sukayi dukkaninsu nadey ta koma motarta ta zauna JJ Kuma restaurant ya shige ya zauna.


Amed paaris kuwa Yan media yakira yace anbasa information da cewa akwai abin dauka a room 409 dake 5star din take media tacika gurin Wanda hakan shine ya dauki hankalin mutane sosai nan Suka dunguma zuwa room din kafin ma managern gurin yasamu isowa.


Ita kuwa wayarta ta fidda takira zeel cikin yanayin murya kamar zatayi kuka tace"


Mum please come here I can't handle wats happening here alone, it's serious mum please come right away.


Hankali tashe zeel tace"


Ok sweetie send me the location I will be there in a minute.


Suna zuwa Suka bude dakin atake mamaki yacika duk Yan jaridar ganin yau mayor ambryam tareda dilla kenan they're having an affair...


Atake aka ringa daukarsu hotuna da video wasu Kuma live video suke Yi musu.


Gashi dukkaninsu suna motsawa alamar son miqewa Amma abin ya gagaresu sbd sunkai qarshen maqura gurin high drunk.


Cika 5star din yayi sbd yanda abin yafara qarfafa atake manager yakira police kafin yazo shiga security suna qoqarin korar Yan press Amma Ina sai qara cika gurin yakeyi.


Cikin hanzari manager yace akawo lemon mix Mai qarfi abasu sudawo hayyacinsu.


Ana kawowa aka Basu dai dai shigowar zeel da am sai fammah da  nadey datace musu wani client dinta tazo gani agurin ta tararda wannan abin na faruwa shine takirasu.Lokaci daya daga Basu lemon mix Suka dawo hayyacinsu ganin taron media akansu da dibbin mutane yasa dukkaninsu miqewa da sauri kafin yayi wata maga zeel Bata tsaya komaiba ta daukesa da wani mugun Mari ga Yan media na dauka.


Cakumo mayor tayi cikin tsananin baqin ciki da bacin Rai ta hau marinta tana zaginta da sauri nadey da wasu waitress tareda manager din harma da Dilla da qarfinsa bai gama dawowaba Suka hau qoqarin kwatar mayor wadda batada qarfin jiki Sam sbd abin Bai Gama sakesuba.


Cikin tsananin fushi da bacin Rai zeel take cewa"


I swear I will make your life a living hell,I promise I will make you pay for this you old bitch,I will kill you and whole your family.......


Police ne Suka Kori kowa ana hayaniya ana komai aka korosu harabar gurin aka samu aka fitoda mayor aka bar gurin da ita.


Qoqarin calming mum sukeyi itada am tajiyo qamshin royal possession na sandals water rose take taji gabanta ya Fadi taji tana neman rikicewa da zuwansa gurin,.


Batareda ya kalli inda takeba ya kalli police da Manager dasuke masa bayanin abinda tun a gida yagani live 

Manager daya Kira masu bincike ayi binciken dakin tsaf yanason sanin meya faru sbd kowa yaga hakan yasan set-up ne aka hadawa su mayor yanason sanin komai sbd sunan 5star dinsu dasuma yake rawa.


Jin hakan yasa ta Dan dago ta saci kallon qofa tanason fita tayi waya da JJ akan yaje restaurant yayi handling dinsu sbd da an duba abincin dasukaci zaa gano daga restaurant matsalar ta fito Kuma ana zuwa zaa ganota.


Kallon plates din abincin tayi tareda qura musu ido tana neman yanda zatayi ta Hana a bincika abincin coz this is a serious issue suna ganota ansamu matsala sbd yanda sunansu yagama baci to the core wlh ko am dake kirarin sonta saiya kasheta baresu manyan.


Tana sake kallon qofa tana juyowa sukai ido biyu da haydar daya zuba Mata fararen idanuwansa Yana kallon yanayinta da yanda ta qurawa abincin idanuwa.


Fiddo wayarsa yayi yana latsawa Yana neman wata number ya nufi gurin window batareda Yana kallon gabansaba ya ture plates din gabaki daya zuka zube gurin tareda tarwatsewa.


Cikin sauri manager da fammah tareda securitie biyu sukayi gurinsa suna cewa"


Be careful sir..


Ohhhh shit""yafada Yana kallon kayansa cikin nuna takaici.


Kallonsa tayi da sauri tana sake kafesa da ido sbd tabbas tasan da gangan yayi sbd taga lokacinda yasa qafa gurin ya buge table din.


Mamakinsane tareda sabuwar fargabarsa tasake shigarta ta kalli kayan daya zubar din cikeda mamakin yin hakan zata dauke ido idanuwanta suka sauka kan id card dinta a qasa gurin bakin gado.Atake taji idanuwanta sunyi jajir suna neman cikowa sbd tabbas tasan yau komai ya lalace Mata gashi police din ya hango id card din ya nufi gurin Yana cewa"


I think we found something here.


Kallon gurin haydar yayi yaga fuskarta baro baro akai,

Police din zai dauka yarigasa dauka fuskarsa ba wani sakewa yace"


It's mine,I think it felt dwn from my pocket while I was taking my phone out.


Sakawa alhijun suits dinsa yayi tareda nufar qofa Yana sake goge jikinsa da tissue.Bayansa tabi da kallo yau Kam mamakinta da tsoronsa sunfi na jiya da yau a ranta,


Ta tabbarda da gangan ya zubarda abincin saidai Bata San meyasa yayi hakanba,

Id card dinta kuwa tasan nata ne yasan nata ne Kuma yaganta a jiki Kuma hakan ya nuna baro baro tana dakin kafin yanxu kenan Dole akwai saka hannunta Amma ya dauka ya Hana police su dauka,

Meyasa zai kareta ya boyeta ya Hana asirinta tonuwa????


Idan harya kareta ya Hana akamata akan ta cutatarda in-laws dinsa it means kenan shima yanada wani motive akansu....

Zatai bincike akansa Dole saitasan wayeshi, meyene motives dinsa akansu dillas dahar zaiga Wanda yayi musu abinda akai yau ya rufata,


He seems to be more clever and dangerous than her Dole zatai taka tsantsan tasan wayeshi batasan da wa take dealing ba,JJ zai binciko musu komai akansa cikin 3days.Suma su dillas din fitowa sukayi nadeey na riqeda mum din Suma su am duk ransu a bace yake musamman am daya San wannan abin baqaramar mummunan illa zai musuba sbd business deals dinsu kusan yanxu duk ja Baya zaa dasu sbd sunansu ya baci a media.


Qoqarin shiga motoci sukeyi Amma Ina media ta rufesu sai tambayoyi suke musu Amma Babu Wanda zaikarbu sbd Muni da 'dacinsa shiyasa securities ke kakkaresu su samu shiga mota.


Daga can cikin yan press din wani yace"


Mrs Dilla ko Zaki iya sake bamu bayanin abinda kike nufi gameda cewar da kikayi Zaki kashe mayor da familynta???


Dukkaninsu cak Suka tsaya Jin wannan tambayar sbd fitarta media balaice atake am yayiwa wani securityn dad dinsa ido tareda nuna masa Wanda yayi tambayar.


Nadey data lura da hakan takuma San me zasuyi masa sai kawai ta fidda wayarta cikin style ta dauki hotonsa atake ta turawa JJ tareda masa text.


Aikuwa suna barin gurin shima Dan press din yafito ya hau abin Hawa Yana barin gurin sunyi nisa kadan aka taresu aka fiddosa cikin motar wasu masu mask ne Suka hau dukansa suna cewa waya basa izinin yiwa Mrs Dilla wannan tambayar gaban media.


Dukansa sukeyi sosai tareda yayyanka masa wuqa zasu sokesa daidai nan JJ daya Kira police suka qaraso sukuma Suka gudu.


Da sauri JJ yaqaraso gurinsa Yana cikin ransa Yana cewa"


Sorry nabarka sun dakeka sosai kafin mukawoma ceta munada buqatar hakan ne sbd zaimana amfani gaba.


Daukarsa akayi aka nufi asibiti dashi shikuma JJ yatura Mata massage ya rubuta"""done"""Wani irin sahirtaccen murmushi tasaki tareda sake riqe hannun mum din tana fuskar tausayi cikin munafurci tace"


Mum please don't stress your self about this ok??? everything will be ok wen the cops finds out who is behind this.


Wani numfashin takaici tasaki zuciyarta na qara qonuwa ita Sam takasa yardama da wani banxan zancen cewa wani ne yayi musu hakan tun farko uban me sukeyi a hotel tare while they do all the business atare.


Suna isa gida haka ta ringa lallaba mum din tana rarrashinta cikin munafurci sbd tasan ita daga yanxu anyi eliminating dinta cikin game din.


Ranar a gidan ko dinner Babu Wanda yayi komaima kashewa akayi na kallo sbd yanda aketa saka maimacin abin gidan television na labarai abin Babu ko shaawar nunawa,


A rayuwarsu Basu taba shiga irin wannan baqin ciki da kunyar ba sai yau shiyasa yau gidan tsit Babu ko wani dogon motsi.


Harta kwata taji wayarta na ringing ahankali ta bude ido ta lalubo wayar tana dubawa taga JJ da sauri tayi saurin tashi zaune tana kallon fammah dake bacci gefenta duk saitaji tabata tausayi sbd ita Babu ruwanta Amma zata dandana dacin abinda zai faru.


Toilet tashige tareda kunna shower sbd kar fammah ta farka by mistake ta jiyota.


Cikin wani irin yanayi na tashin hankali JJ yace"


Baby gamunan munxo dauke mayor da 'yarta Saidai muna iso wannan Mr haydar din ya daukesu a gabanmu ya tafi dasu mun bisu har airport munga yasasu wani private jet sun gudu and the biggest surprise din shine da kansa yaje gidan tareda wani yaronso they scattered the hole place in blood.


Zaro ido tayi jikinta na mugun daukar rawa da qyar ta iya cewa"


Mubari gobe zamuyi mgn Amma you'll have to be very careful with him,this haydars is something else.


Fitowa bayin tayi tana daga qafa daqyar zuciyarta fal tunanin zaiyi amfani da hakan ne against dillas ko kuwa.


Kwantawa tayi Saidai Sam takasa bacci sbd tunanin abinda ke Shirin faruwa Saidai ga dukkan alamu taga koma meyene plans din haydars akan Dilla's to su zai amfanesu.Washe gari da safe qarfe Tara ta sauko shirye cikin Armani pep lom top milk da royal blue free Palazzo trouser sai scarf dinta blue Mai touch din black zimbwe heels dinta dasuka qarawa adonta kyau.


Qamshi take fitarwa ahankali ta nufo sitting room din inda dukkaninsu ke zaune cikin damuwa da ciwon ran jiyan sbd yau da safen business deals biyu aka turo musu anyi canceling sbd abinda yafaru jiyan.


Gaidasu tayi dukkaninsu cikin fuskar jimami zuciyarta cike fal da farin cikin ganinsu cikin hakan.


Ko zama batayiba suka dunguma zuwa table cin breakfast.


Zama kowa yayi Babu Mai wata doguwar walwala sbd tun cikin Daren babu kudinda am Bai fitarba Dan Hana abin yaduwa Amma Sam Babu dama media tafi qarfinsu.Suna cikin cin breakfast din Mai aikinsu Lauren ta iso cikin tsananin girmamawa tace"


Ma'am police are here to see you.


Dukkaninsu kallonta Sukayi tareda aje spoons din hannuwansu suna kallon kallo kafin suka taso dukkaninsu Suka fito.


Police ne motaci uku Babu rahama a fuskarsu.


Nadey na ganin hakan tayi saurin yiwa JJ text tace yacewa amed paaris Dan press yayi saurin tattaro Yan press suzo Dilla mansion.


Kallon zeel babban cikin police din yayi tareda daga Mata cuffs yace"


Ma'am we are here to arrest you for the suspect murderer of mayor ambryam Marshalls.


What?????


Dukkaninsu Suka fada cikin tsananin tashin hankali da mamaki.


Nadey kuwa itama mamakin ya kamata so this is Mr haydars plan kenan.??


Duk wani son tsayawa bayani police basuyiba sukai arresting din zeel tana kuka tana komai suka tafi da ita am da Dilla kuwa kamar zasu buga sbd tsabar tashin hankali da baqin ciki Basu Gama fita wancan ba yanzu sunshiga wannan wanda yafi wanacan Muni.Ana fitowa da ita Yan press Suka fara kokuwar dauka suna jefo tambayoyinsu akan maganar zeel din  dinda tayi jiya akan zata kashe mayor itace ta aikata.


Tashin hankali Jin hakan yasa zeel fara ihun kuka tana neman qwacewa daga police Amma Suka dannata mota Suka tafi da ita.

#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863**_Mamuhgee33_*

Fammah dake hawayen baqin ciki ta riqo cikin tausayinta da sigar lallashinta tace"


Karki damu fammah Allah na tare dake.


Kallonta fammah tayi hawayenta na sake gudu cikin muryan kuka tace"


Meyake Shirin faruwa damune????tsakanin jiya zuwa yau komai na neman lalacewa,mun aikata wani Abu ne da muke ganin hakan?????


Girgiza Mata Kai nadey tayi tareda katseta da cewa"


Fammah kidaina fadan haka karki sabawa ubangijinki,

Wannan abin shi ake Kira da fitar haqqi.


Batareda ta wani fahimci maganar fammah dinba Suka dungumo cikin gida dama dad dinsu da am tuni suka dauki mota sukabi Police.


Cikin gidan ganin yanayin fammah yasa tadan nuna damuwarta akanta tana ta sake rarrashinta sbd tabbas fammah bazata iya handling abinda zai cigaba da zuwa ba musamman idan suka wayi gari sun koma zero account.Acan police headquarter kuwa duk inda su am ke tunanin abin ya wuce nan sbd yanda yau waisu dillas ake qin saurara sai wani kwana kwana suke musu anmaqi Bari sugan zeel din tuni aka qargameta su saima anan suke ganin hotunan gidan mayor din da aka dauko jini ko Ina anyi kaca kaca da Kaya.


Abu kamar Wasa saigasu har kusan yamma anqi Bari suyi komai a kan case din gashi suna jiyo ihunta cikin tsananin azabar da ake Bata tafadi inda gawar mayor da 'yarta suke.


Jin bazasu iya daurewaba yasa Suka tattaro Suka dawo gida jiki amatuqar mace zuciya na matuqar daci.


Koda Suka dawo gidan fammah na ganinsu tasake fashewa da kuka sbd ganin Basu dawo da mum dinba dakuma yanayinsu dake nuna Babu wani sauqi.


Ranarma a Daren Babu Wanda yayi dinner sai nadey dataje kicin ta zauna akan kitchen island taci pancakes dinta da Apple ta koshi Tasha fresh milk da ruwa kadan Takoma sama daki ta tube tayi wanka da ruwan zafi sosai ta gasa jikinta tafito ta shirya cikin sleeping dress fara Mai Dan kauri ta daure kanta da band tazo ta kwanta gefen fammah da baccin wahala ya dauketa tun dazu.Washe gari tunda safe dukkaninsu suka sake komawa headquarter wannan karon anbarsu su ganta aka kaisu dakinda zasu ganta Suka zazzauna jiran akawota.


Lokacinda aka shigo musu da ita dukkaninsu Saida Suka miqe tsaye cikin tsananin tashin hankali sbd irin mugun dukan dake jikinta gabaki daya ta sauya kamanni idonta daya ko gani bayayi ya rufe gabaki daya sbd kumburin jini hakama gefen bakinta ya kumbura harya juye gefe.


Daqyar take daga qafa tana ganinsu da idonta daya dake gani tafara wani irin kukan tashin hankali tana cewa su ceceta karsu barta cikin wannan halin.


Dukkaninsu jiinsu rawa yakeyi sbd tashin hankali,

Ita kanta nadey din Saida taji wani iri sbd yanayinda zeel din Takoma a kwana daya da yini.


Ko mintuna goma batayiba suka jata tana ihu tana Shure Shure Suka mayar da ita.


Hakan ya sake daga hankalin dillas musamman da anqi bayarda bail dinta kafin shiga court gashi kamar wani hadin baki ko Wainda aka saka azaba suke gana Mata akan ta fada inda gawar su mayor take.Cikin kwana biyar gidan Babu Mai iya ko Shan ruwan kirku sunkoma kamar gidan mutuwa ko yaushe kowa na palonsa gashi mahaukatan kudi suke saki Amma Sam Babu wani alamar sauqi saisuka fara sakaran case din da saka hannun wasu manyan dasuka fisu sbd duk wata hanyar sauqi an toshe musu gashi Court za'a fara shiga washe gari.Da daddare yunwa tasa fammah sulalewa ta fice daga gidan cikin motar fammah ta nufi gida tana waya da JJ akan fa haydar ya tsananta wannan alamarin sbd dillas anwayi gari ko abinci rabonda waninsu yaci anmanta Saidai ruwa.


Tana Isa gidan ta tararda Babu kowa daga mum har Annah basa nan tanada key harzatayi amfani dashi ta bude sai kawai ta fasa ta juya kota shiga bazataji dadin ci ita kadaiba batama da tabbacin ko akwai sunyi.


Wani restaurant ta nufa batareda tashigaba tana cikin mota ta bayarda order dinta ta cikin waya tana jiran su kawo mata.


Wayarta take amfani da ita tana turawa dad dinta saqon wasu files data sa akayo Mata forwarding daga Noah's tanason yasake duba matasu dakyau.


Dan dagowa tayi sai kawai ta hangosa tafe tayi saurin lafewa cikin motar batareda ya lurada itaba ya bude motarsa dake kusada tashi ya fada yabar gurin Bata tsaya komaiba ta buga tata tabisa sbd id card dinta datakeson karba.


Ahankali ya lurada motar na binsa sai yaqara dubawa yaga tabbas motar fammah ce yaja wani siririn tsaki tareda parkawa Yana fitowa itama tana kawowa saura kadan su hadu da juna tayi saurin yin baya daidai wata mota takawo aguje kan titin yayi saurin fizgota ta fado jikinsa ya Mata kyakkyawar runguma akaro na farko jikinsu ya hadu sosai.


Rawa jikinta yafara numfashinta na fita da mugun sauri jin jikinsa anata yasa hankalinta yasake tashi tafara girgiza kanta da qarfi tana cewa"


No no no ba jikinsa bane,

Wannan jikin ba nawa bane yanayin sukeyi,,,,no no I'm only imagining ne....

Qwacewa tayi da qarfi hawaye na ballewa daga idanuwanta sbd zuciyarta dake neman rudata dajin jikinsa kamar na zakinta,

Meyasa takejin kamar jikin zakintane komai da komai.Juyawa tayi da gudu hawayenta na tsananta tafada mota da mugun gudu Wanda ya daga hankalinsa sbd yanayin yanda taja motar komai zai iya faruwa.


Bin bayanta yakeyi da gudun shima Saidai kasancewar ta roughrider ce sbd a college suna zuwa wasan race da motoci Wanda Annah ce keda son hakan sai itama abin yashigeta.


Tana zuwa gidan ta shige da motar da wani speed tayi parking ta wuce ciki da gudu har lokacin kuka takeyi.


Wani irin numfashi Mai zafi yasaki zuciyarsa na wani irin radadin zafi,

Ako wace safiya yatashi da ciwon zuciyar rashinta yake tashi dashi yake rayuwa,


Tsawon shekarun nan baitaba farin ciki Kona seconds neba sbd rashinta ataredashi Saidai dolene ya boyewa kowa kansa sbd samun zamansu safe har yagama Dora kowa a matsayin daya kamata.


Jan motar yayi da gudu shima ya wuce Yana Jin nauyin zuciyarsa yau Yana qaruwa.


Ya gaji Dole yagama komai cikin qanqanin lokaci yana buqatarta akusa dashi.
Ita kuwa kukan Rashin zakinta tayi sosai acikin Daren kafin tayo alwala tazo tayi sallar nafila tafara jero masa addua shida mahaifiyarta da ummansa.


Yau har wata sabuwar kewar babanta ta taso Mata 

Tsananin qaunar ganinsa ta taso Mata takasa hkr ahankali ta lalubo wayarta ta Danna Kiran Dr sayyid.


Yana dauka ta tasaki ajiyar zuciya ahankali tace"


Babana Dr Ina yawan tunaninsa cikin kwanakin nan I hope canjin damuke buqata ansamesa I can't continue hiding Ina son ganinsa wlh.


Ki kwantarda hankalinki nadey babanki ansamu cigaban da akeso sbd yanxu yafara Sanaa Kuma ba laifi Naga ta karbesa sosai kayan fruits yake siyarwa ammafa wani lokacin shike zama yasha kayansa saiya qoshi.Murmushin Dole ne ya subuce Mata Jin halin baban dai yana nan kawai dai qila kwantawa yayi sbd yanayin rayuwa.


Cikin Jin dadin babanta nanan da halinsa na ban dariya da takaici tace"


To Dr inaga tunda yasan amfani Sanaa yanxu zaka iya bashi kudinda kace Yaya Zaki yabaka.


Kinaga lokaci yayi kuwa?


Eh kabasu kawai aisun wahala ba laifi zasu tanada yanxu nasani.


Ok to insha Allah zanje nakai masa.


Harzai kashe murya cikin tsananin sanyi tace"


Dr idan zaka bashi ka dauko min fuskarsa inason ganin farin cikinsa Dan Allah.


Murmushi yayi yace""


Insha Allah.


Tana kashe wayar ta share hawayen tausayin babanta da iya kafin ta miqe ta kwanta a darare sbd gobe sunada zuwa court.Washe gari dukkaninsu da sanyin jiki Suka tashi har itama din Saidai ita nata daban ne.


A mota daya suka isa court din am ne ke tuqi sai dad da fammah a baya ita agaba cikin wata baqar jeeb Mai daukan ido.


Motarsu na tsayawa Yan media Suka zagayesu ko gurin fitowa Babu Saida securities sukazo suna tutture musu su suka samu fitowa ana karesu Suka samu shiga Court din.


Zamansu bada jimawa ba haydar ya iso kotun tareda securities dinsa biyu ya qaraso gurinsu ya miqawa dad din hannu Yana jajanta masa hakama am fammah kuwa narke masa tayi yadan saki fuska kadan Yana cemata karta damu komai zai daidaita kowa zaisamu abinda yayi deserving.


Satar kallonsa tayi Suka hada ido da ya zuba Mata idanuwansa take tafara kame kame tana hadiye yawu daqyar.


Ahankali ya mayarda idanuwansa kan 'dan space dindake tsakaninta da am wanda dashi gwara Babu.


Ya dauke kai Yana murmushin dashi kadai yasan mezaiyi.


Shigowa akayi da zeel data sauya kamanni gabaki daya cikin sati guda nan aka fara shariar Saidai Sam Babu haske ga dillas saima qara zurfafa zancen keyi ana bankado wasu asiransu Wanda yafara Basu tsoro da mamakin ya akai suke fitowa.


Ranar haka aka tashi court din Babu wani sauqi Suka nufo gida.


Kamar Wasa saiga shariar na tsawo ankasa samun wani taqamaimai dogon sanin inda zeel takai gawarsu meyo gashi dukkanin evidence suna nuna itace tayi kisar nan kotu kawai ta yanke hukuncin arufeta gidan yari tsawon shekarunda zata fadi Ina gawarsu take.


Ihu zeel keyi tana kuka tana Kiran dikko da am su taimaketa karsu Bari akaita prison wlh Bata kashesu mayor ba ita batama San gidantaba haka aka tafi da ita tana kuka tana riqe fammah dake kukan itama kamar ranta zai fita.


Am ma da dad din hawayene kawai basuyiba Amma dukkanin hankalinsu ya tashi idanuwansu duk sun Kade zuwa jajir ga uwar dukiyar dasuka zubar a wannan case din.


Nadey ce riqeta fammah harsuka nufo hanyar gida saigashi aka Kira daga office Kiran gaggawa.


Office din suka wuce gabaki dayansu inda suka tararda wani babban tashin hankalin Yan press ne cikeda gurin suna isowa sukayo gurinsu suna musu tambayoyi Wanda tambayar daya daga cikin Yan media din yake cewa"


Ance kun siyarda gabaki daya shares dinku na Dilla empire da kamfanin gabaki daya harda gidan dakuke ciki yanzu ga Wainda suka siya nan sunzo zasu karbe shin mezaku ce gameda hakan??????


Cak dukkaninsu Suka tsaya cikin mamaki da takaicin Jin abinda ake cewar,

A fusace am ya turesa tareda marinsa Yana cewa"


What rubbish.....


Hakan da yayi yasa Yan media harzuqa Suka ringa daukar abin suna qarfafa yadawa har marinda yayiwa Dan press din.


Basu yardaba Saida Suka Kai cikin building din Suka tararda lauyoyi da ma'aikatansu cirko cirko ga hukumar qasar cike suma ana jiran isowarsu.Takarda lauya ya daga ya miqawa Dilla Yana cewa"


Ga takardar dake nuni da client Dina ya siya dukkanin shares dinku ga saka hannunku nan ga nasa ga namu lauyoyinsa na shedu ga Kuma stamp na Court so munxo karban ragamar kamfanin ne da komai.


Ko gama karantawa Dilla baiyiba ya baya zai zube am yayi saurin riqosa tareda fixge takardar ya karanta yayi wurgi da ita Yana cewa"


Qaryane Babu Wanda muka siyarwa komai mundaiyi investing kuma......


Katsesa dayan lawyern yayi da cewa"


Ba haka bane Mr am Dilla inaga tun farko idonka ya rufe baka karanta waincan takardunba dakayu Amma hakan shiyake a rubuce.


Kallon lawyern yayi tareda kallon takardar da sauri ya tuno ranarda ya karbo takardun zasuyi signing zai karanta nadey dinsa tashigo tace saiyazo sun fita da sauri yanda ta matsa masa tadau hankalinsa yasa Bai tsaya karantawaba yayi signing Yana fitowa yabawa dad shima yayi ya fita dasu daga gurin shaqatawarsu yaje yakai takardun kotu aka saka shedar kotu.


Dafe kansa yayi tareda durqushewa qasa Yana neman haukacewa...


Miqewa yayi da sauri tareda cakumar lawyern dayafi zubo maganganun Yana cewa"


Qaryane wannan abin zagon qasa ake mana,

Wakeson ganin bayanmu,

Idan mun siyar Ina kudin suke toh?????

Nace Ina kudin suke??

Waye keson ganin bayanmu?????Daga bayansa yaji ance"


Nine.


Dauke wuta yayi tsawon seconds kafin dukkaninsu Suka juyo baisan lokacinda yayi baya da  sauriba Yana neman faduwa bakinsa dake kumafar yawun tashin hankali da masifa a sake.


Dilla ma dibis yayi faduwan Yan bori suna kallonsa daga qasa zuwa sama.


Sanye yake cikin wasu irin designer suit black na kamfanin rugbay sai wasu amneelaurenzo cover dinsa yayi kyau harya gaji sai agogon diamond Rolex dake hannunsa Yana kallonsu ido cikin ido.


Duk da tsananin canzawarsa ga wani irin building muscles dayayi hakan Bai sauya musu kamanninsaba.


Cikin wani irin tashin hankali da fargaba dad din ya miqe ya cakumo am tareda daukarsa da wani irin mummunan Mari a haukace yace"


Dama baka kashe JJ ba kabarsa bayan nida mum dinka munce ka kashesa

Dama nasan bazaka taba yin abinda yakamataba kullum kaike kawo Mana matsala Sam bakada amfani 

Gwara haihuwar mace da lusari kamarka.....


Kwacewa yayi cikin tashin hankali yace"


Wlh dad na kashesa wannan ba JJ bane wani ne....


Wani kyakkyawan Mari JJ yadaukesa dashi yace"


Yanzu ka yarda da nine ba wani ba Ina fata.

#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863**_Mamuhgee34_*

_Not edited_

Da jajayen idanuwansu suke kallonsa hawaye na cikowa idon am suka gangaro atake yayi kan JJ zai cakumosa police Sukayi saurin riqesa yanata sakin maganganu masu qarfi jikinsa na rawa idanuwansa na hawaye.


Dilla sai ganin akayi ya yanke jiki ya Fadi fammah tayi kansa tana ihun Kiran sunansa ya kasa ko dagowa ya kalleta jikinsa sai rawa yakeyi sbd tsabar tashin hankali,


Daqyar ya sake zabura ya miqe cikeda balai ya cakumo JJ bakinsa na kumfa yace"


Wlh baka isaba karabani da abinda nayi baqar wahala na Tara tun ba'a haifekaba,

Kasan ta Yaya na Tara wanna dukiyar na tattaleta tazama haka?

Kasan irin gwagwarmayarda nayi Dan ganin na Tara wainnan miliyoyin???

Kasan Rai nawa na dauka akan Naga nakawo yanxu???

Kasan mutum nawa nayi betraying duk akan na bunqasa wannan dukiyar zakazo cikin awanni nawa kace ka rabani da komai bazai taba yiyuwaba kasani,wlh akan dukiyata zan iya kawarda kowa.....Cikin kallon wulaqanci JJ yace"


Yes nafika sanin dawa dawa ka kashe kafin ka Gina wannan dukiyar sbd namu iyayen na ciki muma kanmu Muna ciki saini Dana dawo Saidai kasani kaman yanda kafada zaka iya kawarda kowa akan dukiya nikuma bana barin duk Wanda ya kashe masoyana saina tabbatarda ko rigar sawa ta gagareka dikko Dilla.


Yana fadar haka ya juyo gaban Yan press yafara koro musu bayani shida lawyoyinsa securities na bayansu tareda daga musu takardar ya nuna musu take aka ringa dauka suna dauka aka hau sama aka Ciro sunan companyn aka jefo qasa daga can hawan qarshe.


Aka ringa fitarda kayan companin ana gwanjonsu Yan jaridu Bata dauka.


Ganin wulaqancin rayuwa yaga rufesu ko Kai sun kasa dagowa am hawaye yakeyi sosai nadey tayi saurin zuwa gefensa cikin hawayenta itama tana basa hkr da qwarin gwiwa kafin Suka fito fammah dake tsananin kuka kamar ranta zai fita tana riqeda Dilla Wanda hawan jini yasa idanuwansa ke gani bishi bishi qafafuwansu daqyar suke dagasu suna jansu.


Dan juyowa nadey tayi suka hada ido da JJ ta sakar masa wani murmushi tareda Yi masa wani irin juyi da ido daya sashi sakarwa 'yan media wani kayataccen murmushinda Bai shiryaba.


Wannan karon itace ta karbi driving din sbd ko gani sosai Babu meyi acikinsu dilla koda Suka Isa gida jikinsa ya rikice gabaki daya BP dinsa yayi high numfashinsa yafara sarqewa tuni akayi ciki dashi aka shimfide aka kirawo Dr da gaggawa.


Sosai Dr ya dubasa tareda daura masa drip da oxygen sbd numfashinsa daya toshe a qirji ko numfashi Bai iyayi bare motsi tuni yakoma kamar wani sauran gawa Dan baisan waye yake kansaba.Palo Suka dawo suka zauna jigum jigum Babu wani sauran dogon motsi Kuma a gidan.


Da daddare ma kwantawa kawai Sukayi Babu wani sauran bacci bare yunwa balainda suke ciki ya soye baccin idanuwansu tareda toshe hanjin yunwarsu.


Nadey kuwa kicin taje ta zauna acan Tasha brownflakes da warm milk ta qoshi abunta taci apple daya ta boye tayi waya da JJ akan dad shima ya iso Yana gari.


Murmushi tayi cikin Jin dadi tace"


Alhmdllh,,,, finally wannan abin saura Abu biyu mugamasa nasamu damar zuwa gurin babana da iya talatu,

Inason na zauna gabansu nayi kukan mutuwar zainab dinta Wanda nakasayi agaban kowa,


Sujiyo radadin da zuciyata ta cikin kukana na Rashin mijina da 'yar uwata.


Hawayene Suka gangaro Mata takasa sharewa saima sulalewa datayi agurin tana kuka after all this maraicinta na rashinsa zai dawo sabo agareta.


Ta Dade tana kuka agurin kafin ta tashi jiki amace ta fito ta haye sama tana Shiga ta kwanta gefen fammah datai bacci hawaye nafita gefen idonta.

Itama ahankali ta rufe idanuwanta hawaye na fita cikinsu.Washe gari jikin dad din madai sai ahankali ganin hakan yasa am yafara maida hankali ya duqufa sosai gurin ganin ya kwato musu dukiyarsu gefe daya Kuma ya rasa ta Yaya zaiyi hakan sbd a account abinda suke dashi idan yace yayi wannan harkar dasu kudine zaizubar sosai suzo su rasa komai harka ta qarasa kwabe musu.


Dayaji ya rasa shawarar abinyi saiya shirya ya nufi prison gurin mum dinsa.


Lokacinda yagama Mata bayanin abinda ke faruwa haukace masa tayi tuburan tana kuka sbd jin sun rasa duk abinda suke tinqaho dashi Wanda takesa ran dashi zasu fiddota duk da shedarda wannan Dan press din da am yasa akashe ranarda yayi Mata wannan tambayar a 5star yabada shedar cewa shima tasa akashesa daga tambaya Allah yasa JJ yazo ya taimakesa da yanzu ya mutu.


Ganin lokacinda aka Basu yakusa cika cikin tsananin tashin hankali da damuwa yace"


Mum inason gyara komai gashi bakya nan ga dad Kuma a kwance tell me what to do mum.


Hawaye suka gangaro Mata daga idanuwanta dasukai jajir ta kallesa ganin cikin Dan qanqanin lokaci yanda ya hargitse Yana neman zaucewa shima ta tuno fammah dinta da Bata Saba da irin wainnan tashin hankali ba saitaji hawayenta na qara gudu ta tunoda nadey cikin wani irin yanayi ta kallesa tace"


Ina nadey?


Tana tareda fammah a gida tana rarrashinta.


Ok listen to me very careful kanaji ko???wannan lokacin ne zakayi amfani da soyayyarku musamu abinda mukeso daga gareta.


Da sauri cikin Rashin son bata tarensa da nadey yace"


How mum????


Dole zamu nemi Aron maqudan kudi daga gareta tareda tallafi daga companies dinta su Kama hannuwanmu mu farfado.


Mum kinsan yanda business yake ba'a baka shares irin wannan na manyan kudi daga manyan companies saika bayarda jinginar wani kadaranka which is we have nothing here sai a Nigeria kinsan yanzu dukiyarmu abinda ya rage a Nigeria ne kawai daga mansion dinmu na can sai kamfaninmu 'daya acan....


Yes am ka batasu amatsayin jinginar sbd ba 'yar Nigeria bace Bata taba zuwaba hasalima batasan a Nigeria ta Yaya zataje tayi claiming dinsu ba and our plan ba anan zai tsayaba along with the loan ka fito Mata da maganar aure kuyisa cikin sati guda ta yanda bayan aure Babu wani maganar loan dazai tashi idanma munkasa samun karbar namu companyn saimu mallake nata yadawo namu tunda tazama matarka.Shiru yayi Yana jujjuya maganar sbd stayi hundred percent Saidai Yana tsananin son nadeynsa bayason yayi betraying dinta Amma baida zabi Dole zaiyi sbd family always comes first duk wata so bayan na familynsa yake.


Da wannan shawarar yadawo gida cikeda tunanuka kala kala da tunanin ta inda zai fara.


Koda yadawo anayiwa gidan kudi ma'ana auction,

Police business tycoons da media birjik anata dauka.


Gidan daga 1mil dollars yafara nan aka dinga Yi kudin na hawa.


Cikin tsananin tashin hankali ya qarasa ciki baiko tsaya angama ganoda isowarsa ya fada Palo da sauri tareda kallon nadey dake riqeda fammah dake rawan sanyin zazzabi sosai ya haye dakin dad Bai tsaya komaiba ya bude safe dinsu ya jawo takardun dukiyarsu ta wani babban companynsu da qaton mansion dinsu dake Nigeria ya fito ya qaraso gaban nadey yayi zaman Yan bori.


Da sauri ta miqe tana masa kallon mamaki tace"


Baby wat is this??? are you ok??


Miqewa shima yayi tareda miqa Mata takardun ta kallesa gabanta na Dan faduwa ta kalli takardun tasake kallon fuskarsa takai hannu ahankali ta karbi takardun ta bude file din tagama karantawa ta kallesa da sauri tace"


Baby why are you giving me this???


Kallonta yayi kamar wani Wawa yace"


Inason kar wannan gidan yafita a hannunmu ne so please my love just do wat ever you have to do ga takardun dukiyarmu na Nigeria idan nabiyaki wannan loan din saiki mayar Mana.


Kallon papers din tasakeyi dakyau taga they're real originals din ne they're not fake.


Wani dadi ne ya rufeta batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana cewa"


Yes yes sure baby I won't let anyone take this mansion from you,I mean my family coz you're my family now since I'm going to be the daughter in-law of this family.


Sake kallon takardun tayi tareda daukar wayarta Babu Bata lokaci suka fito tareda am din suka zauna wani British na cewa"


2mil dollars kowa yayi shiru aka sake maimatawa kowa yayi shiru Kai tsaye tace"


3mil dollars from Noah empire.


Tsit kowa yayi ana kallonta.


So uku ana maimaitawa Babu Wanda yaqara take akace ansiyar Mata nan aka fara congratulating nata Yan media na dauka dama akwai lawyer's din gwamnati agurin take aka bugawa takardun mallakar gidan sunanta aka buga musu stamp sai dauka akeyi.


Itama agurin tayi signing check din kudin ta miqawa lawyoyin gwamanatin akayi duk wani procedures aka miqawa JJ kudinsa Wanda haryanzu Babu Wanda yasan sunan companynsa Yan media sunyi tambayar harsun gaji yace karsu damu soon zasuga sunan kamfanin.


Duk yanda taso ta kebe da JJ Bata samu damaba sbd am daya kasa ya tsare yanata wani nunawa media ita tasace Wanda qarshe da wani yayi masa tambayar meyasa Noah's Suka taimakesu daga gidansu da suka kusa rasawa Kai tsaye yace"


Because she's part of the family,

She's going to be Dillas soon we are getting married in a 2 weeks time.


Wani irin kallo tayi masa files din hannunta na neman zubewa Saida JJ cikin taron yayi saurin zaresu a hannunta idanuwansa jajir ko kallonta beyiba yabar gurin tareda mutanensa.


Zagayeta Yan media Sukayi suna tambayarta da gaske ne ta rasa ya zatayi tafara qoqarin barin gurin Amma tuni suka zagayeta am din ne yayi saurin kallonta yace"


My love tell them mana.


Kallonsa tayi tareda sakin murmushin yaqe ta juyo ta kalli Yan media din tace"


Yes we are getting married soon.


Tana fadar haka ta juya tabar gurin zuciyarta na tafasa sbd abin yafara zama wani Abu Kuma,


Tabbas tasan akwai dalilinsa nayin hakan a gaban media Dole yakamata tasan nayi tabar gidan tun abubuwa Basu fara juya mataba.


Da daddare tafito kicin cin abinci taji motsi qofar kicin ta baya gabanta yayi mummunan faduwa sbd Jin motsin babbane.


Kasa hakuri tayi zargin ko am ne ke yin wani Abu cikin Daren ta sidado ta dawo Palo ta nufi qofa ta bude ta fito ahankali da tareda Kiran JJ Yana dauka tayi saurin yin qasa da murya tace"


Dady j am yanayin wani Abu cikin Daren nan bansan ko meyeba Amma Koma meyene is serious.


Cikin sauri yace"


Baby karkije idan yaganki zai iya cutatar dake.


No dady j bazai iya cutatar daniba he loves me...


No no pls baby wlh kashesa zanyi idan ya cutatar dake and.....just put me on video call inason ganin abinda ke faruwa.


Da sauri tasashi video call din tareda yin qasa da murya gabaki daya.


Ahankali ta zagayo ta bayan kitchen din tana karyowa taji an fizgota da qarfi tareda toshe bakinta tafara Shure Shure wayarta ta fadi tasa hannu tana qoqarin lalubo fuskar Wanda ke matse da ita din Saidai takasa hood dinda ya rufe fuska da ita kawai tasamu damar zamewa sbd tsananin rawar tashin hankali da tsananin tsoron data shiga da firgici.


Wani Abu ya shaqa Mata atake jikinta ya saki ya dauketa cak yabar gidan da ita.


Bayan motarsa ya kwantarda ita yashigo ya kwantarda ita a jikinsa driver dinsa yaja Suka bar gurin Yana kallon fuskarta zuwa jikinta dake sanyeda wasu sleeping dress riga da wando pink colour Mai duhu masu santsi da Rashin nauyi.


Hannunta ya qurawa ido tareda riqo yatsarta dake sanye da zoben white gold Mai tambarin A Wanda yasan ALEEYU a din ke nufi.


Akaro na farko yakai hannun bakinsa yayi kissing tareda lumshe ido yasaki numfashi Mai qarfi Yana cewa"


This is enough Mrs haydar Neyo.


Wani babban Banglore dinsa dake kusan 4 kilometers away daganan Suka Isa ya daukota ya nufi qofar palon yashige Bai tsaya ko Ina da itaba sai master bedroom dinsa ya shinfideta tareda rufeta da duvet cover ya zauna gefenta tareda yin shiru ya qurawa fuskarta ido zuciyarsa na wani irin narkewa aduk lokacinda yake kallonta amatsayin ita din tasace shikadai.


Yaso barin yaga yasamu dar qaddamar da burinsa akan Dilla's kafin bayyanar Mata da kansa Saidai kishinta kashesa zaiyi bazai barsaba 

Zuciyarsa yau saura kadan ta buga Saida yasha magani da qila bugawa zatayi,

Bazai qara barinta Takoma koinaba tadawo hannunsa kenan daga nan sai Nigeria zasu koma.


Tashi yayi ya fice bedroom din bayan ya kashe lights ya rage Mata aircon.
JJ dayaga duk abinda ya faru sbd har lokacin da wayar ta fadi tana on video call Babu abinda yayi mugun girgixasa irin fuskar daya gani lokacinda hannun nadeyn ya ture hood dinsa,,,,,


Miqewa yayi tsaye tareda buga kansa da qarfi jikinsa na wani irin rawa sbd rudu da gigitar fuskar daya gani,


Sarki yafada""""cikin tsananin fargaba da shakka,


Gefen fuskarsa yagani Wanda yaga kamar fuskarsa,

To abinda yafi basa tsoro shine abinda ke daure a qwandar hannunsa Wanda tunda yasan sarki dashi yasanshi kozai mutu yadawo yasan wannan abin hannun na sarki ne.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee35_*

Kasa zama yayi ya zari key din mota da sauri ya fito waje ya fada mota Ya figeta da sauri sbd yariga yasan am ne yake qoqarin cutatarda nadey tunda ta riga ta taimakesu tabbas Dama yasan saisun biyo takardun dukiyarsu dake hannunta sun karbe kota sauqi kota wuya 

Babu wani sarki daya gani idanuwansane ke masa gixo ganin kamarsa,


Buga sitarin motar yayi Yana girgiza kansa dake neman bugawa zuciyarsa sai wani tuquqin baqin cikin halinda nadey ke ciki yanxu takeyi,


Ikon Allah ne kawai yakaisa gidan ko kashe motar beyiba yafito yayo ciki securities suka taso ya Ware hannu ya naushi dayansu tareda ture dayan da qafa yabarsu kwance ya shige ciki da sauri ya qarasa inda yakesa ran nan ne yahau duba wayarta 

Can cikin glass carpet dinda ke gurin yaganta yayi saurin dauka ya duba yaga wayar still tana aiki a fusace yayi hanyar palonsu Yana qwala kiran am cikin wani irin Amon bacin Rai.


Am din ne da fammah Suka fito tare cikin fargabar meyake faruwa.


Ganin JJ da yanda yanayinsa yake yasashi daure fuska a fusace shima yace"


After all the humiliation and deceit how dare you come hia you goon.????

Get out of here before I lose my control......


Wani mugun naushi JJ yakai masa a baki dayasashi zubewa dafe da bakinsa dake fidda jini ya miqe a matuqar fusace yace"


Hw dare you hit me..you bast......


Bai qarasa ba wani mugun Marin ya sauka fuskarsa shima cikin zafi ya dauke JJ din da Mari Yana cewa"


Don't you dare hit me again....


Shaqosa JJ yayi cikin tsananin fushi yace"


Where is nadey?????


Tell me Ina kakaita idan ba hakaba I swear I will rip your head...kafadamin Ina ka kaita???


Turesa am yayi da qarfi cikeda mamakin maganganunsa a hasale yace"


Meye ruwanka da matata????

Meye hadinka da ita dasai anfada maka inda take.???


Kallon am fammah tayi tana hawaye tareda matsowa sosai ta riqe hannunsa cikin yanayin kuka da tausayin Dan uwanta tace"


Am nadey fa Bata nan tun dazu Nima na dubata har baya Bata nan da gaske tana tareda Kai bayan nabaka shawarar karkayi wannan rayuwar before marriage.....


Kallonta yayi a hasale yace"


Bata taredani Amma nasan duk inda taje zata dawone karki biye zancen haukar wannan 'dan ta'addar da sare sare da shaye shaye kawai Suka iya....


Cikin baqin ciki JJ yashaqosa Yana kallon cikin idanuwansa yace"


Wlh bakasan 'yan ta'addanci sun iya sare sare ba saina Gama tabbarda nadey na hannunka ranar zakasan qarfinda 'dan ta'adda kedashi.


Wurgi yayi dashi ya juya a fusace yabar gidan Saida yayi nisa da gidan ya parka motarsa Jin hawayen cikin idanuwansa na gangarowa,

Wlh bazai iya jurewaba idan ya rasa nadey ko wani abin ya sameta gashi baisan ta yayama zai fadawa dad abinda ke faruwaba da abinda ya gani.


Sai dare sosai ya koma gida ya shige bedroom dinsa ya rufe tareda kifewa kan gado Yana sake zurfafa cikin tunanin inda zaifara nemanta a boye batareda ansaniba musamman media bayason zancen ya fita ga media.


Am kuwa bayan barin JJ gidan juyawa yayi ya kalli qofar shiga Palo cikin wani irin yanayi na zurfafa tunani,


Tabbas yaga wayar nadey a hannun JJ Kuma gashi fammah tace Bata nan to ya akayi JJ yasan nadey haryasan batanan????

To kenan waya tayi masa ko menene????

Something is really wrong here..


Tunda tashigo rayuwarsu komai yafara lalacewa gashi yanxu sun wayi gari basuda wata kadara ko daya sai kudi a banki Suma sun bararda kusan fiyeda rabi gurin shariar mum da qoqarin kwato dukiyarsu,


Idan Bai mantaba itace sanadinsa suka hadu da wancan kamfanin investment dinda Suka bayarda takardun kadararsu,,,


Hakama ranarda dad yake a hotel da mayor itace takira mum gurin,


Was that all really coincidence or was it all planned????


Something is really wrong here.


Cikin gidan Yayi da sauri ya nufi stairs ya haye fammah na bayansa tana binsa tana tambayarsa Amma ko kulata beyiba sbd haukar dayaji na neman kamasa lokaci daya.


Closet dinsu ya nufa yafara jawo kayan nadey din ya fiddo akwatinta ya bude tareda zazzagewa duka kayan ciki Suka zube har wasu takardu da da hoto ya fado.


Hannunsa har wani rawa yakeyi sbd fargabar abinda zai iya gani...


Takardun yafara dauka ya juyo dasu zuciyarsa na harbawa sbd bayason yaga abinda zai Saba tunaninsa akan nadey Yana Mata tsananin sonda bazai iya rabuwa da itaba Koda ita dince take musu cutar a boye..


Yana juyoda takardun yasaki ajiyar zuciyarda ta rage tsoronsa da fargabarsa akanta sbd takardun asibitine na normal checkup dinta.


Harzai aje idanuwansa Suka sauka kan complete name dinta

_NADEEYA DATTIYA NOAH_

Wanda dama shi ake nufi da ND Noah.


Dattiya yasake fadar sunan Yana sake maimatawa sbd kamar yasan yataba sanin sunan.


Hoton dake kife ya dauka Yana birkitowa Saida yayi saurin yin baya sbd fuskar daya gani tayi mugun murda hanjin cikinsa take yafara mazari 

Fammah tayi saurin riqesa tareda daukar hoton ta duba cikeda mamaki tace"


Wannan Zane nefa ba hoto ba meyesa hankalinka ya tashi haka?


Wannan din waye shi??


*SARKI* "ya fada Mata Kai tsaye.


Sake kallon hoton tayi dakyau tasake kallawa har gefen fuskar zanen itama cikeda mamaki ta kallesa tasake kallon hoton tace"


Wannan asalin fuskar haydar Dina ne kawai banbancin shine haydar Dina ya qone a gefen wuyansa zuwa fusakarsa kadan tun Yana yaro yace shiyasa idan zai fito ake masa gyare gyare a fuskar ana sauya masa kamanni sbd baason iska na hawan gurin saiya warke gabaki daya.


Wani irin karaji yasaki Yana dafe kansa kamar zararre kafin ya damqota da qarfi hartana sakin qarar azaba yace"


Ya akayi kakasan wannan???

Tun yaushe kikasan hakan????

Fadaminnnn""ya fasa da mugun qarfi jikinsa na rawa.


Cikin tsananin tsoro da tashin hankalinda Bata taba ganiba murya na rawa hawaye nabin fuskarta tace"


Dama tun ranarda nafara ganinsa muka hadu a airport shine naji bazan iya son kowaba duniya idan bashiba tun a nan na ringa shishige masa hardai yadan kulani nasamu card dinsa shinefa na ringa bibiyarsa Ina kiransa wata rana ya dauka wata Rana yaqi ahaka dai harya fara kulani muna soyayya Saidai haryanzu baitaba zama Dani munyi firar soyayya ba,

Dama Ina yawan zuwa office dinsa shine ranar Ina zuwa shikuma ya fice sainabi bayansa har gidansa Ina zuwa na bawa securities card Dina da matsayina a gurinsa shine Suka barni nashiga har palonsa nan Naga.....


Zaro ido tayi cikeda mamaki da tuno abinda tafara gani a gidansa ranar,

Kallon am tayi tace"


Tabbas qatoton zanen hoton dake palonsa kamar wani qofa guda nadey ce,

Yes insha Allah itace sai yanxu nake tuno kamannin wancan hoton wlh itace....


Daga Palo Ina cikin kalle kalle saigashi ya fito palon daureda towel fitowarsa wanka kenan yafito daukar wayarsa daya Bari nan.


Cikeda mamaki da takaici yake kallona nikuma cikeda mamakin da qaunar tsananin kyawun fuskarsan nake kallonsa sbd Sam ban gane cewar shi bane Saida yayi mgn na ganesa take na rikice masa sbd tsoro da fargabar mutum daya da fuska biyu.


Ganin haka yasa ya zaunar Dani yamin bayanin Wai qonewa yayi Kuma baason iska na hawan gurin saiya warke shiyasa ake rufe gurin to idan aka rufe nan kawai saiyanayin wani iri shine ake sauya fuskar gabaki daya Amma yasa na masa alqawarin bazan taba fadawa kowaba ciki har iyayena nikuma na masa alqawarin bazan taba fadaba sbd Ina sonsa......


Wani wawan Mari am ya dauketa dashi a haukace yace"


Kinsan waye wannan???

Fatalwace ba mutum din gaske ba ya Dade da mutuwa da hannuna na kashesa shekaru sama da biyar dasuka wuce,

Wannan balai ne,shi masifa ne, marainiya zai maidaki gaba da bayanki Dan kuwa daga dad,mum harni wlh kinramu shikenan maraici zakiyi wannan alqawarinsa....


Jijjigasa fammah tayi da qarfi tana kuka sbd ganin ya haukace lokaci daya sai surutai yakeyi jikinsa na mazari tace"


Am pls stop all this Ni bana gane komai all I want is wannan tashin hankalin ya wuce muyi rayuwa kamar kowa cikin kwanciyan hankali,


My haydar bazai taba cutatarda familyna ba,

Shi ba mugu bane bazai muna komaiba,Yana Sona bazai cutatardaniba...


Tureta am yayi ya fice a dakin ko gani bayayi sbd tsananin tashin hankali,


Meye hadin nadeeyarsa da zanen hoton zaki?

Bazai iya rayuwa Babu nadey ba Koda ita din jinin Zaki ce,


Shin wannan da fammah ke fada zakin ne kuwa kokuwa shine yake qoqarin kasa fahimta

Gabaki daya qwaqwalwarsa ta toshe baya gane komai....


Kwalbar alcohol ya daga ya kwankwada kozaiji sauki Amma saijin yayi qwaqwalwarsa tasake hautsinewa ya daga kwalbar ya shanye 

Atake yaji kansa ya kasa daukar nauyin balainta yafara ihu Yana wurgi ta komai.


Fammah dake rakube tasake fashewa da wani kukan kamar zata shide 

Tabbas ko Basu mutuba tasan ita ko yanxu tana cikin tsananin maraici 

Dad na kwance sai antayar,mum na prison ga am kamar ya haukace.


Sunan nadey yake Kira Yana ihu tareda farfasa Kaya duk yajiwa kansa ciwo qarshe nan ya zube cikin fasassun kayan da kwalba yafara wani irin kuka ahankali sbd duk qarfinsa ya qare itama ahankali tadawo kusadashi ta rungemesa tana cigaba da kukanta itama.***

_6:36 am_


Ahankali ta bude idanuwanta dasukai Mata wani irin nauyi ga kanta da shima yayi Mata wani irin nauyi..


Ahankali tafara qoqarin tashi tana qoqarin tuna abinda yafaru jiyan,


Kallon dakin tahau Yi tana dafe kanta tareda saukowa gadon ta miqe tsaye tana sake qarewa dakin kallo sbd yanayin tsarinsa da haduwarsa tasan cewa ba qaramin wurine takeba.


Kan qaramin frame 'din dake aje gefen bedside lamp idanuwanta suka sauka taga zanen hotonta tayi saurin daukar frame din taga tabbas itace take tasan cewa am ne ya daukota

Ta aje cikin tsananin baqin ciki tahau dudduba kanta gabanta na tsananin bugawa tana tsoron idan ba wani abin yamataba.


Ajiyar zuciya tasake data ganta lafiya kalau Amma yanda zuciyarta ta kasa daina bugawa da sauri da qarfi yasa hankalinta tashi ta nufi qofa cikin sanda ta fito ahankali tana lalleqawa cikin faduwar gaba.


Wani dakin dake kallon inda ta fito yajiyo faduwar Abu tayi saurin kallon qofar tareda dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi ta nufi qofar ta daga hannunta dake rawa ta tura ahankali tana Shiga.


Cak ta tsaya bakin qofar dakin tareda waro idanuwa tana dafe qirjinta da numfashinta na sarqewa sbd abinda tagani.


Tsaye yake gaban mirror daureda towel alamar wanka yafito,


Bayansa zuwa qwandar hannunsa dake daureda abinda a duniya tafi kowa sanin na mijintane Dan baitaba ciresa daga hannunsaba,


Ahankali idanuwanta suka sauka kan tabon cizon datasan itace tayi masashi haryazama tambo a hannunsa duk da tasan Idan yaso zaiyi amfani da magani ya goge tabon Amma yaqi qoqewa sbd Yana buqatar ganin tabon...


Girgiza Kai tayi da qarfi tafara ja da baya tana dukan kanta da qarfi tace"


Oh my God I'm loosing it...ciwona na hauka yadawo,,,why am I seeing tinz....


Faduwa tayi tana neman fita hayyacinta...


da sauri ya juyo Jin faduwar mutum da mgn abayansa 

Yana juyowa Suka hada idanu 


Atake ta zaro ido tana kure fuskarsa da kallo saikuma idanuwanta suka fara rufewa ta zube kwance a sume.


Cikin tsananin tashin hankali yayo kanta Bai tsaya komaiba ya dauketa yayi gado da ita ya kwantar Yana Kiran sunanta.


Fuskarsa ya hanga cikin mirror yaga asalin fuskarsace cikin tashin hankali yace"


Darn it..tariga ta ganni.

#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee36_*

Sake dafe kansa yayi cikeda damuwar yanda zata fuskanci zancensa idan ta farka sbd ta riga ta gansa Babu wata kwaskwarima a fuskarsa takuma tabbarda shine ba fatalwa to Yaya zata karbi alamarin??yaso shine yafara bayyana mata kansa batareda itace ta fara ganowa ba.


Ruwa ya dauko a fridge ya dawo bakin gadon ya zauna ya xuba ruwan a hannunsa ya shafa a fuskarta Yana Jin wata irin kasala na saukar masa.


Sake shafa Mata ruwan yayi tafara bude idanuwanta ahankali ta waresu akansa ta qurawa fuskarsa ido hawaye na cikowa cikinsu gabaki daya,

Tsoro,fargaba tareda tashin hankali sun daddaure jikinta sai wani irin rawa da jikinta keyi hawayen idanuwanta na gangarowa,


Batasan mezatayiba sbd sbd dai ba qaramin alamari bane take fuskanta yanxu na ganin Wanda Suka San ya mutu shekaru biyar baya a gabanta ace bazata sake somewa ko gama wannan tunanin batayiba idanuwanta suka sake lumshewa zata sume yayi saurin girgizata Yana cewa"


No no Not again please....


Ware idanuwanta tayi murya na rawa jikinta na daukar sabon mazarin tsoro da tashin hankali daqyar ta bude baki tace"


Ya...ya...yya yaaa...


Daga Mata Kai yayi tareda sake girgizata sbd ganin alamar Bata hayyacinta sbd tsoro Kuma kamar Bata Gama tabbarwa da shi din bane cikin wani irin yanayi yace"


It's me,nine I'm real ba fatalwa bane ban mutuba da Raina,

Ki dawo hayyacinki karki illata kanki nine da gaske ba wani gixo ba Ni din daine a gabanki......


Wani mugun yunquri tayi ta turasa baya tareda yin baya tana masa wani irin kallo idanuwanta jajir da fargaba tace"


Kana cewa baka mutuba Kaine Kaine,

Kana tunanin gwaninta kayi ko dadi zaka sani da fadar hakan??

Qwalqwalwata bazata iya daukaba,

Ciwon haukana dawowa zaiyi I'm only imagining this,,,,ya Allah karka Bari na sake dandanar ciwo da radadinda ke cikin hauka....


Ya Allah ka tayardani daga wannan mafarkin danakeyi....wlh I'm going insane....


Da qarfi ya damqota tareda girgiza ta da qarfi ya Kira sunanta sbd ganin yanda jikinta ke rawa sosai tana surutai da qarfi....


Qwacewa take sakeyi tana neman ihu da fixgewa ya sake riqeta Yana Kiran sunanta hankalinsa na tashi Saidai Sam batamasan yanayiba gabaki daya ta fice hayyacinta..


Jin zuciyarsa na neman karyewa da halinda tashiga yasashi rungumeta da qarfi cikin jikinsa tareda kwantarda kansa cikin wuyanta Yana Kiran sunanta da wata irin muryar sanyin jiki kamar zaiyi kuka sbd gab yakeda zaucewar shima matuqar wani Abu yasake samunta.


Tabbas yasan Dole zata gigita da ganinsa sbd ana maganar mutuwane,

Tasan ya rasu shekaru sama da biyar saikuma tagansa yanzu Kai tsaye Dole hankalinta zai tashi.


Yanda ya matseta a jikinsa Yana Kiran sunanta ahankali tun tana fixge fixge hartayi sanyi jikinta ya saki gabaki daya alamar ta sake somewa.


Lumshe ido yayi tareda girgiza kansa Yana tallafota gaba daya yasake maidata ya kwantar Yana mamakin yanda take somewa ita tunda can.


Wasu ruwan yasake shafa Mata

Tareda tsayawa bakin gadon yayi folding hannuwansa zuciyarsa duk a hargitse.


Ahankali tasake bude idanuwanta ta kafesa dasu wannan karon ko motsi kasawa tayi ta lumshe ido tasake budewa ta sauke masa

Take taji zuciyarta ta karye sbd yanzu Kam tabbas tasan shi din ne Babu maganar fatalwa kokuma hauka..


Wasu hawayen dataso ruqewane Suka gangaro ta gefen idonta sbd tasake tabbatarda da dai shi dinne Yana raye.Kasa cewa komai tayi sbd wani mugun nauyi da dukkanin gabban jikinta suka dauka sbd mutuwar jikin data sameta,

Wani irin sanyi qasusuwan jikinta suke sake dauka akaro na farko a rayuwarta dataji zuciyarta ta toshe da wani irin nauyin gaske Wanda ya Hana bakinta budewa bare magana.


Fuskarsa take sake qarewa kallo,

Haskensa da kyawunsa na nan saima qaruwa dasukayi sbd hutu da Jin dadin daya samu,


Ahankali ta sauke kallonta a gefen wuyansa zuwa kunnensa na dama dasukayi duku tareda alamar qonuwa  Wanda tabonta yakusa bacewa gabaki daya wasu sabbin hawaye suka silalo Mata.


Ahankali ta dafa ta tashi zaune tareda dauke idanuwanta daga kansa ta sauko gadon yanabin jikinta dake wani irin rawa a boye Wanda ya tabbatarda na ganinsane.


Fuskarta ya kalla yaga yanda yanayinta ya sauya sosai Babu wata rahama a fuskar tata saima hawayenta data share tana miqewa tsaye daidai agabansa.


Am in trouble""yafada tareda sake ajiyar zuciya ya matso zai kamo hannunta tayi baya ahankali batareda ta dago ta kallesaba ta juya zata fice ya riqe hannunta tareda dawo da ita baya zaiyi magana ta rigasa da qwace jikinta cikin qoqarin danne halinda take ciki tace"


Please Ina buqatan komawa inda ka daukoni.


Kallonta yayi da fararen idanuwansa tareda dawowa gabanta ya kalli fuskarta dake sunkuye yace"


Ina kike maganar komawa kenan???


Inda ka dauko ni Dilla's.


Sakinta yayi tareda mayarda fuskarsa yanda yasaba wato a tamke shima ba sauqi Kai tsaye yace"


Bazaki koma can ba infact ko Ina bazaki komaba Ni nasan inda zan kaiki.


Dagowa tayi wannan karon takasa riqe tarin baqin cikin dake cin zuciyarta kamar zata mutu tace"


Nace gida zankoma so inaga Banga wani dalili ko iko dakake dashiba na hanani besides karka manta satoni kayi Wanda Ni bansan manufarka akan hakan ba and inada damar dazansa a Kamaka akan hakan.


Idanuwansa ya zuba Mata cikeda yanayi na tsananin mamakinta akaro na farko dayaga zallar fushi Mai qarfi atareda ita.


Kina tunanin banda wani ikon hanaki kokuma kina tunanin Zaki iya sakawa a kamani din sbd kina taqama da me????


Cikin fushi tace"


Koma Dame nake taqama it's none of your business,

Kai me kake taqama dashi dazakazo bayan shekaru ka tsaya gabana bakaji kunyar Allah da tsoronsa ba na barin matarka dakayi da 'yan uwanka tsawon shekaru kana raye baka nemesu ba,baka dawo garesu ba,

Bakasan irin halinda suka shigaba sbd rashinka,

Bakasan ya rayuwa tayi musu tsanani ba sbd Babu kai....rawa muryarta tafara Yi hawaye na ciko idanuwanta tace"


Dama basuda mahimmanci da wani matsayi a rayuwarkane daka zabi barinsu Babu waiwaye kokuwa dama lokacine ka dibar musu a rayuwarka,


Meye laifina Dana mahaifina daya bakani ko kuwa munzama takurane a rayuwarka????


Meye laifin babana Dani kaina???

Idan duk munada laifi damuka zabeka fiyeda kowa meye laifin baby z ita????


Sai alokacin ya matsota sosai Yana kallonta da idanuwansa dasuka rikide ja sosai ya daga hannu zai kamota tasake ja Baya cikin daga murya tace"


Enough..enough Mr haydar,,,ka daina kusantoni da yawa sbd haryanzu ban manta da darajataba ta 'ya mace Kuma musulma....


Ba zato ya jawoto jikinsa ya matse tareda zuba Mata jajayen idanuwansa jikinsa na rawa sbd bacin ran zancenta yace"


Shi wancan da kike tare dashi a gidansu shi musuluncin Bai hau kansa bane????

Wlh bazaki sake zama a gidanba idan Kuma kinason kwada qarfin ikon danake dashi ne akanki da rayuwarki ki gwada zakisha mamakina sbd inanan bawai canzawa nayiba.....Fixgewa tayi itama cikin Hana kukanta zuwa tace"


Bana magana akan rayuwar kowa da canzawar kowa anan Ina magana akan rayuwatane da abinda Naga damar Yi da Wanda Naga damar bari,

Idan kana maganar baka canza ba to Ni na canza ba Nadiya bace wannan ND NOAH ce...and stay the hell out of my life.....


And bana buqatar ganin qarfin iko ko dukiyan dakake dashi sbd dama Abu ne nasa kaina sbd tunanin anrabani da abinda nakeso fiyeda tawa rayuwar Ashe bansaniba shine ya rabu Dani Dan haka Ni kaina daga yau na fita daga fadanda Babu ruwana zanje na fuskanci Wainda suka cancanci qaunata da lokacina.


Tana Gama fadar hakan ta fice da gudu sbd wani irin kuka Mai tsananin nauyi da qarfi dakeson zuwan Mata tana dannesa numfashinta har sarkewa yakeyi jikinta Babu inda baya rawa.


Kasa motsi yayi sbd duk jijiyoyin jikinsa sun daure da mamakinta da fargabar tashin hankalin maganganunta dake bayyanarda tsantsar radadin baqin cikin barinta datake ganin yayi.


Securities Basu wani hanata fitaba tana fita ta tari wata taxi data kawo ta fada kawai sai alokacin tasake wani irin kuka Mai tsananin cin Rai da damuwa tareda ciwon abin datake ji cikin ranta.


Har Sukayi nisa Bata saniba Saida yasake tambayar inda zai kaita ta bude baki daqyar tareda fada masa tana share hawayenta tareda qoqarin barin kukan duk da tasan bazata iya barinba.


Yana Isa qofar mansion din ta fito ahankali tareda ce masa ya jirata tafito.


Ciki tayi tana qoqarin maida kukan dayake sake taso Mata sbd fammah data hango tsaye jikin qofa tana knocking qofar side din am tana kuka sosai kamar zata shide.


Kasa riqe nata itama tayi tasakesa tareda wucewa ciki da gudu tanajin inama duk shekarun nan a gaban babanta ta zauna tayisu da tabbas bazata cutatu yanda takejin ta cutatu yanzu ba.


Sama ta haye tahau hada duk wasu kayanta tafara jawo luggage dinta tana share hawayenta dasuka qi tsayawa a Palo taci Karo da am da fammah tsaye dukkaninsu Babu Wanda baibata tausayiba take zuciyarta tasake karyewa ta silalo hawaye masu radadi ta rintse idanuwanta ta bude saitaji takasa kallon fammah ga am da zuba Mata idanuwansa dasuka shanye sukai jajir a dare guda ya lalace yakoma tamkar asalin Dan giyar dayayi shekaru ashirin Yana sha,

Hawaye ne cike da idanuwansa Saidai Basu saukoba sbd muguwar karayarda zuciyarsa da gangar jikinsa suke ciki,

 

bude baki tayi daqyar ta furta"


I'm leaving......


Ba zato qafafuwansa Suka sare ya zube gabanta tareda riqo qafafuwanta cikin wani irin yanayi na kuka da tausayi yace"


Baby Dan allah karki barni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,

I can't live or survive without you,

Karki tafi kibarni a wannan halin I will die if you leave me.... please baby idan na Miki wani laifi ne forgive me Dan Allah please baby don't leave.....


Kuka tasake sbd akaro na farko daya fara Bata tausayi musamman yanda fammah ke jansa tanason tayar dashi cikin tsananin kuka Yana kwacewa Yana surutai da kuka sosai..


Cikin tsananin kuka itama ta janye qafafuwanta ta ja Baya yayi saurin rarrafowa Yana wata irin magiya gabaki daya baya cikin hayyacinsa.


Cikin tsananin kuka fammah itama ta zube gefen Dan uwanta ta dago ta kalli nadey din tana kuka tace"


Dan Allah Ina roqonki daki rausayawa rayuwata ki tallafi Dan uwana dashine kadai ya ragemin a yanxu,


Bansan wane sirrine yake boye a tattareda saninki da familynaba Amma Dan Allah kiji tausayin maraicina ki tallafi Wanda zai tallafi tawa rayuwar.....


Girgiza Mata Kai nadey tayi hawayenta na sake gudu ahankali ta furta"


I'm really sorry fammah...


Tana fadar haka ta fice da sauri tana sakin siririn kuka tana jiyo ihun fammah na Kiran sunansa Amma Bata tsayaba sbd zuciyarta data fara karyewa alhalin itama tallafin take buqata a tata kuncin Wanda zuwanta gaban mahaifintane kawai zai yaye matashi.Taxi din tashiga sukabar gurin.

Direct gidansu Annah yakaita canma Basu gane kantaba tana Shiga ta tattara sauran kayanta suna tayata hada kayanta data kasa hakuri anan ne tasaki kukanta Mai qarfi datake riqewa mum din Annah da Annah na gefenta Suka Bata damar tayi kukan duk dake cikin ranta kozataji sauqin zuciyarta.


Sosai tayi kukanta saidataji sauqin nauyin datakeji a qirjinta kafin ta shiga toilet tayo wanka tana fitowa takira JJ da wayan annah ta shirya cikin skinny jeans fari da farar loose chiffon top ta Dora black full-length jacket da black scarf ta fito da kayanta  daidai isowar JJ kallo daya yamata yaji nauyin zuciyarsa ya qaru sbd idanuwanta dasuke a kumbure musamman data gansa sai idanuwanta suka sake cikowa da hawaye tun kafin yayi magana ahankali da rawar murya ta furta"


Dady j I can't handle this anymore,,,inason ganin babana Dan haka it's time for me to go home....


Da sauri ya qaraso gabanta cikeda kulawa Yana cewa"


Baby please karki dagamin hankali tell me yafaru?

Meya sameki?

Waye ya daukeki?

Ina ya kaiki?

Meya Miki?


And....and..fuskar Wanda ya daukeki Dana gani was it re.....


Yes dady j shine,Yana nan da ransa Bai mutu ba Muna wahalarda rayuwarmune akan Wanda baisan munayi ba....


Da manyan idanuwansa yake kallonta ko qyaftawa yakasa Yi shima duk jarumtarsa zuciyarsa bugawa takeyi sosai sbd kukuwar yarda da zancen,


Girgiza kansa yakeyi tareda juyawa da qarfi ya daki iska Yana sake girgiza Kai sbd wannan zancen ya girmi tunaninsa Kai tsaye Rana tsaka ace Wai sarki Bai mutu ba,

To meyesa ya boye musu kansa???

Idanma Bai nemi kowaba shi Bai kamata yakasa nemansaba qarin abin tashin hankalin shine suna taredashi Bai sanarmusuba Kai this is so confusing.


Wani murmushin takaici tasaki tace"


Shall we???


Dago jajayen idanuwansa yayi ya kalleta yaga yanda fuskarta tayi jajir ta kumbura take yaji ransa yaqara baci Saidai shikam yau zasuyi face to face da sarki yau zasuyi magana as man to man.


Direct airport yakaita Babu me magana acikinsu harsuka karbi tickets ta juyo ta kallesa zatayi magana shima daqyar yarigata da cewa"


Karki damu yau zuwa gobe zamu Gama claiming komai a gobe zaa buga sunayen Noah's a kamfaninsu da mansion dinsu da angama zandawo jibi insha Allah.


Jinjina masa Kai tayi tareda juyawa ta shige shikuma ya koma.


Bata fi mintuna ashirin ba aka Kira flight dinsu ta tashi ta shige.


Yamma sosai ta Isa starling city dad da kansa yazo daukarta sbd yayi wata da JJ yafada masa komai dake faruwa gameda haydar.


Ji yayi duk duniya farin cikinsa yadawo Sam kasa boye farin cikinsa yakeyi tuni labarin yafara yaduwa a cikin abokanan mu'amalarsu ta business har zancen yafara fita.


Duk murnarsa raguwa tayi dayaga halinda nadey ke ciki yafara qoqarin danne murnarsa da farin cikinsa Yana duba yanayinta itama sbd tabbas wannan abin abun dubawa ne ga miji yabar matarsa tsawon shekaru Babu waiwaye.


Da gudu baby z tazo ta rungumeta itama cikin tsananin kewa da soyayyar 'yarta ta rungumeta tareda rintse ido hawaye na silalo Mata.


Nanny Nancy ma rungumeta tayi cikin kewarta dasukayi suka shige har dakinta har lokacin baby z na maqale a jikinta itama Sam takasa sakin 'yarta.


Wanka tayi tayi sallah tana qoqarin danne komai tasake dasu Suka hau labarai dad ma sakewa tayi taqara masa bayanin halinda ake ciki gameda mansion dinsu Dilla data siye harda na Nigeria and dad Insha Allah I will be going back to Nigeria next week zanji da maganar claiming takardunsu na can da muka karba.


Kallonta yayi cikin farin cikin ganin Bata wani dauki abin da zafi ba yace"


Ok allah yakaimu Saidai idan kinje ku zauna gidan Dr sayyid tunda nasan za'ayi renovating gidan Yaya dattiya ne sbd nasan no matter what Yaya bazai iya barin anguwar nan ba.


Murmushi tasaki ahankali sbd tuno irin burikan babanta musamman na zama sarkin maroqa.Da daddare da 'yarta ta kwana bayan tayi waya da JJ.JJ kuwa daga airport gida ya wuce ya shiryo cikin wasu irin suits yasa aka Kira media akan yaune zaa karbi sunan dazaiyi replacing dillas Wanda yakeson acan ne zai fuskanci sarki 

Sarki ya fuskancesa.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee37_*

Cikin gaggawa fammah tafara ihun Kiran sunayen masu aikin gidan Suka fito amatuqar rikice a gigice take cewa su kirawo Mata Dr kar am ya mutu ya barta.

Aikuwa amatuqar gigicen Suka fara neman wayar Kiran Dr din daqyar Suka samu tashiga Yana dauka Suka sanar dashi yace gashinan zuwa.


Da kanta ta kamashi tareda taimakon su Jenna Suka kaisa bedroom din mum dinsu dake kusadana dad.


Kasa zama tayi takasa tsayuwa tana kaida kawo cikin tsananin tsoro da tashin hankali.


Kafin zuwan Dr hankalinta yakai qololuwa gurin tashi sbd dad dinsu daya farfado adaidai wannan lokacin shima Saidai basusan ya zasuyi masa su rabasa da oxygen dinda ke maqale a fuskarsaba.


Gaban dad din ta zauna tareda riqo hannunsa cikin tsananin farin cikin farfadowarsa tana Kuma hawayen kwantawar Dan uwanta.


Isowar Dr ce tasa tayi saurin miqewa ta basa guri yafara zare oxygen din dad Yana yabawa da yanda ya farfado lokaci daya kafin ya juya gurin am dake buqatar taimako yahau dubasa.


Sosai ya dubasa tareda dubarunsu na likitoci saigashi ya bude idanuwansa dasukai jajir Yana qoqarin tashi fammah da Dr na dafesa cikin kulawa Dr yace masa Yana buqatar hutu a yanxu.


Wani irin wahalallen kuka ya sake tareda qanqame hannun fammah dake kuka tuni yace"


Fammah meye laifina????

Meye laifina danake Mata mugun so irin wannan??

Fammah kinsan radadi da ciwon danake ji a zuciyata sbd ta tafi ta barni??

Ciwo nakeji anan sosai"""yafada Yana dafe qirjinsa dake masa tsananin ciwo musamman sbd alcohol dinda dayasha sbd Sam baya Sha baima taba  shaba.


Ahankali fammah ta rungumesa tareda lumshe ido hawayenta na sake gudu sbd batamasan mezata iya cewa ba.


Bayan tafiyar Dr gurin dad dinsu Suka tafi acan Suka zauna tasa aka kawo Mata abinci Mara nauyi ita tayi feeding dinsu su biyun tabawa kowannensu magani anan Suka koma bacci tare ta miqe ta kashe musu aircon ta fita.


Dakinta taje ta tube tayi wanka daqyar tayo alwala tazo tayi Sallah Wanda zamanta da nadey ne tasan tayi sallah akan lokaci Kuma duk lokaci idan yayi sbd itadai bazata iya tuna lokacinda iyayenta Suka taba cewa tayi sallah ba kokuma idan tayi shiyasa so da dama idan tayi to wani lokacin Kuma idan lokaci ya wuce shikenan saikuma gobe Amma zama da nadey tun tana basarwa harta fara Jin kunyar nadey na sallah itama musulma kamarta Bata cikayiba sai hakan yasa tafara dagewa tanayi cikin lokacin Kuma ko yaushe,

Tun abin na gasane hartazo tasaba ko nadey na gida ko batanan idan lokacin sallah yayi yin sallarta takeyi.


Tana Gama sallar ta duba agogo taga dare yayi sosai saitayi kwanciyarta agurin tana tunanin yanda rayuwa ta juya musu baya lokaci qanqani.Washe gari tunda safe abinda yafara yaduwa a gidajen tv da jaridu shine makeken sunan NOAH'S PUBLICATIONS daya bayyana baro baro a saman makeken kamfanin dillas dakuma qaton mansion dinsu suna ciki basusan ancire sunansuba ansa Noah's.


A tv Suka fara gani da safen Dilla yayi zuru ya qurawa tv ido sbd balain dayake ciki yafi qarfin magana sbd mamakinsa akan kenan nadey Noah duk sune su JJ tazo ta yaudaresu sun karbe musu komai.


Am kuwa wasu irin hawaye ne ke gangarowa daga idanuwansa jikinsa na wani irin rawa ahankali fammah tasake qanqame hannuwansu su duka biyun sbd tana zaune ne a tsakiyansu.


Babban tashin hankalinsu shine inda zasu zauna sbd yau Dole zasu bar gidan gashi kayan jikinka kawai kake fita dashi.


Cikin wani irin yanayi na sanyi da tsananin damuwa Dilla ya kalli fammah zaiyi mgn ta miqe da gudu tabar gurin tana kuka.


Dakinta taje ta hada kayanta cikin akwati guda da duk abinda yakeda amfani da mahimmanci agareta.


Daga nan dakin dad taje shima ta hada masa komai a akwati daya hakama mum tayi Mata akwati daya ta jawosu ta fiddo dasu ta nufi dakin am shima ta ha'do masa nasa takawo palon tana kallon yanda am ke kuka sosai cikin baqin ciki da radadin da zuciyarsa ke ciki.


Dad ma daka kallesa kasan kowane irin lokaci zuciyarsa na gap da bugawa.


Passports dinsu ta fitar ta dauki wayarta ta fita harabar gidan takira tayi musu booking tickets din Daren yau dazai tashi zuwa Nigeria.


Dawowa tayi ta zauna tsakiyarsu tareda sakin murmushi Mai ciwo ahankali tace"


Wannan wata jarabawace daga ubangiji mu karbeta da hannu bibbiyu insha Allah it will pass.Suna nan zaune jigum jigum akazo Basu tunin lokacin fitarsu gidan yayi fammah ta riqo dad da har lokacin baida wani kuzari suka fito am kuwa idanuwansa sunyi jajir ko dagowa ya kalli tarin media dake gurin baiyiba Suka fito mansion din sai daukarsu hoto akeyi.


Black anaconda fc din haydar ce ta Sha gabansu tareda motar police biyu a bayansa.


Cikin wasu black Armani wears yafito motar fuskarsa sanyeda Benz dark shades ya qaraso gabansu ya tsaya daga gefen JJ dashima yake tsaye gabansu cikin Gucci's.


Kallo daya Dilla yamusu numfashinsa ya sarke yafara Jan numfashi daqyar Yana dafe qirjinsa.

ganin Yana kokuwa da numfashinsa yasa fammah saurin riqosa am kuwa motar police dinda aka bude aka fitoda mum dinsu data sauya kamanni gabaki daya gefenta kuwa mayor ambryam ce cikin shigar kayan sanyi.


Da gudu yayi kan mum din ya qanqameta Yana Kiran sunanta 

Itama kukan takeyi sosai....


Jin fammah na Kiran sunan dad din yasa Suka juyo da sauri Suka yo kansa  cin tashin hankali am ke shafa bayansa Yana kirana sunansa tareda nuna masa yaja numfashinsa da qarfi.


Cikin wata irin murya me Kama da rugugin damuna haydar yakoma zakinsa yace"


Ku daina wahalar ceton Wanda tasa tariga tazo qarshe rufe sauran babinsa zamuyi kamar yanda yasan yasaba rufe babikan wasu....


Dikko ka miqe tsaye da kyau ka fuskanceni sbd yaune zanbaka bugun zuciyarka na qarshe.


Ka godewa Allah haryanzu sa'a na tareda Kai sbd JJ and....kasa fadar sunanta yayi ya lumshe ido yacigaba da cewa"


Sun lalata rayuwarka batareda Ni na qaddamar da abinda na shiryowa rayuwarka ba Wanda zaisa ka dauki makami da kanka ka dauke rayuwarka da kankaba,


Kaji dadi sun baka hukunci Mai sauqi sbd Dilla da nine kasamu hukunci daga gareni toda ko kare bazaici namankaba sbd nayi niyar mayarda rayuwarka mafi qanqancin rayuwa wadda dabba saiyafi daraja a idanuwan duniya Amma saigashi kasamu hukunci Mai sauqi daga familyna Wanda ko hakan ya isa ya tabbatar maka da cewa Zaki ko baya raye zuriata sunfi qarfinka..and one last thing shine dukkanin cases na kashe kashenda kayi tun kafin haihuwata na budesu you're not going anywhere dilla..


Files din hannun lawyernsa ya karba tareda budewa ya saki wani mugun murmushi tareda daga masa files din yace"


17 murders cases,

One murderer,

Kafara da kashe uncle dinka da matarsa da yayansu biyu a Dilla Ethiopia ka gudo da dukiyarsu Nigeria inda ka kashe wani dattijo a wani qauyen jalingo ka gade gidansa,

Ka kashe yayan matarka zeel kuka gade tasa dukiyar kuka Kori yayansa,

Ka kashe ma'aikatan dasuke maka aiki da dama kafin kazo ka kashe Amininka ALIYU HAIDAR NOAH... Owner NOAH'S PUBLICATIONS, Noah's empire....


Dukkaninsu atare Suka dago Suka kallesa cikin mummunan firgicinda tunda aka fara wainnan balain Basu shugesaba....


Dagowa Dilla yayi da kyar ya kalli Zaki da idanuwansa dasukai jajir sbd tsananin azabar ciwon dayake ciki zaiyi mgn Amma yakasa bude baki police suka marmatso cikin bindigoginsu da cuffs zasu kamasa ya kalli zeel,am da fammah ya bude baki daqyar zaiyi magana zuciyarsa ta buga ya zaro ido Yana dafe qirjinsa take yafara tari Mai qarfi Wanda sukaga jini na biyo tarin 

Koda su am Suka riqosa cikin tashin hankali tuni jinin yafara biyowa ta hancinsa da bakinsa Koda Suka tarosa jikinsa yasaki suna ihu suna kuka suna kallonsa ya rasu agurin..


Rintse idanuwa JJ yayi sbd irin kukan dasukeyi da ihunsa irinsane yayi alokacinda aka kashe masa nasa iyayen Yana tuno abin har lokacin yanajin radadin abin...


Zaki kuwa juya baya yayi sbd kukan fammah dayake taba zuciyarsa da dukkanin tausayinta akaro na farko..


Ambulance na zuwa aka daukesa har lokacin kuka sukeyi sosai cikin tsananin tashin hankali da baqin cikin dasuke ganin zai samesu idan sun rasa dad.


Ambulance na barin gurin da Dilla wasu karnuka dake gefen Mansion dindake kusadana dillas din suka qaraso suna shinshina jinin suna haushi.


Karnukan am ya kalla ya dago ya kalli Zaki Suka hada ido hawaye suka gangaro masa ya riqo mum dinsa da fammah dasuke kuka suna shidewa ya sakasu a taxi sukabi bayan ambulance din.Watsewa gurin yayi kowa ya wuce har Yan media tuni Suka watse ana yada labarin rasuwar Dilla.


Juyowa yayi zaiyi magana yaga yanda JJ ya tsaresa da manyan idanuwansa 

Ya saki wani sirrin numfashi tareda zare shades dinsa yayi tareda kallon JJ zaiyi magana saikuma yakasa ya rungumesa da qarfi Suka rungume juna kowannensu najin tsaftatacciyar qaunar Dan uwansa wadda sunsan Allah ne yasaka musu qaunar junansu fiyeda komai.


Sunkoma ahaka kafin Suka saki juna JJ yasake kallonsa cikin mutuwar jiki yace"


Nasan reason dinka baifi karka dawo garemu a cutatar damu sbd Kai Amma meyasa bakayi tunanin idan Muna tare zamu iya Kare junanmu tareba musamman bab.....


Kasa karasawa yayi sbd jin nauyin sunan akaro na farko.


Kallonsa haydar yayi yaji wani iri shikansa sai ya basar da cewa"


Let's go.Zama sukai a palon haydar na qurya 

Haydar ya miqa masa glass of raspberries juice ya zauna suna facing juna ahankali yafara cewa"


Dr sayyid yazo headquarter da Kash masu dibbin yawa akan bailing Dina gurin CM Kuma cikin saa ya amince yace zai sakeni anjima da dare Amma ana Sakina nabar qasar,

Akan haka Suka gama magana Dr sayyid na tafiya cm yakirani har office yayi min bayani tareda nunamin kudi da passports da Visa tareda ticket dinda Dr sayyid ya bayar akan abani Ina fitowa cikin Daren naje airport akwai jirginda zanbi zuwa US.


Cikin Daren nan am yazo da kansa tareda yaransa hudu tareda dukiya Mai yawa akan sunason abarsu su kunnawa cell Dina wuta.


Cm baya headquarter acikin Daren Ina kwance inaji Suka kunnawa side dinda muke wuta sosai atake gobara ta tashi.


Shiru ya danyi cikin tuno irin azabar dayasha alokacin kafin yacigaba da cewa"


Daqyar da yardar Allah nasamu na buge window na fada baya bayan kusan gefen jikina yafara kamawa da wuta Amma I couldn't give up sbd my family needs me.


Naso dawowa gida alokacin Saidai hakan zaikawo fitintinu da dama Wainda nasan Dilla zai iya kashe kowa a familyna without anyi hesitation,

Daga nan ne naje office din cm na balle nashiga na dauki visa da ticket dinda akayimin da check din kudin nafice.


Aranar na wuce sbd qonuwata is getting worst.


I suffer,

I suffer JJ,nayi rayuwar kadaici,baqin ciki,azaba,wahala da gwagwarmaya..tun a cikin jirgi bansake sanin inda nakeba sbd qonuwata is very deep and serious.


Daga airport hospital aka wuce Dani and I spend morethan 2month a kwance asibiti.


Bayan na warke sun sake sakoni jirgi Suka dawo Dani Nigeria acikin Daren direct gida nadawo and unfortunately Ina xuwane cikin tsakiyar Daren na tararda abinda yafaru Wanda adaren suka kashe zainab...


Naganku lokacinda kuka fito,

Nabiku tun adaren nake bibiyar rayuwarku har lokacinda tayi zama a asibitin Zurich,


Sbd ita nakoma Zurich I started my business from there,


Every morning kafin fita aiki sainaje gurinta hakama da yamma before going home.


Ahaka Ina taredaku a asibiti ta haihun Saidai bazan iya zuwa na karbi 'yataba nayi Mata addua duk sbd dillas.,


Bayan haihuwarta tadawo lafiya klau nakoma nashiga school a nan Zurich,


I spend 1 year Ina karatu Ina business din shipping cikin 5yrs nayi achieving duk wani Abu danakeso ciki har soyayyan fammah akaina Wanda da itane dama zanshigo dillas...


Bantaba mantawa daku ba sbd koma meyene nayi nayi ne sbd ku...

Nayine sbd safey dinku,

Nayine sbd girman soyayyar....


Kasa qarasawa yayi sbd ja da idanuwansa Sukayi sbd tuno yanayinda suka rabu da ita jiyan Wanda haryanzu abin ke cin ransa.


Rungumesa JJ yayi tareda buga kafadarsa ahankali ya iya furta karka damu zata saukane just give her time.


Acikin Daren jirginsu ya sauka a starling city inda dad da kansa yaje daukarsu airport 


Kallon juna Sukayi shida haydar kafin ya jawosa jikinsa ya rungumesa da qarfi cikin farin ciki Mara iyaka yaugashi ga dansa.


Sunjima ahaka kafin Suka dunguma zuwa gida inda zuciyarsa ke harbawa da qarfi sbd yaune Karo na uku dazai rungumi 'yarsa cikin jikinsa.


Ya rungumeta a Karo na farko a school dinta dayaje ganinta a boye itama Bata sanshiba kawaidai ya daga Mata hannu Kuma taje da gudu.


Sai na biyu Kuma a garden din wasan yara dasukaje da nanny Nancy..


Mamanta ya tuno take yaji gabansa ya buga Amma a fuskarsa Babu Mai iya gane halinda zuciyarsa ke ciki.


Suna Isa gidan dukkaninsu Suka fito zuwa ciki shikuwa duk takunsa daya qara bugawar zuciyarsa yakeyi.Dad ne agaba baby z tazo da gudu ta fada jikinsa tana ganin JJ tasake tayi gurin JJ tana cewa"


Yehhhhh nanny Nancy my daddy is back.


Dagata sama yayi cikeda farin cikin ganinta ya ajiyeta qasa Yana cewa"


I miss you my angel.


I miss you too Daddy.


Dan matsawa yayi tareda nuna Mata haydar dake tsaye Yana kallonta cikin wani irin tsananin so da qaunar 'yarsa tsotsonsa da kawunsa yake gudun a haifar masa namiji 

Take yasaki murmushi tareda ware Mata hannu aikuwa da gudu tayi gurinsa tana cewa"


Uncle you hia??


Daukarta yayi sama shima ya rungumeta tsam tsam yanajin soyayyar mamanta fiyeda kowane lokaci.


Tsakiyar palon Suka dawo dukkaninsu har lokacin tana jikinsa sai farin ciki sukeyi shikuwa idanuwansa nakan stairs akai akai.


A gajiye tadawo office sanye cikin traditional Milano gown lilac.


Kai tsaye tashigo palon riqeda keys da jakarta musamman datake jiyo hayaniyar baby z.


Tana shigowa a cikin idanuwansa nata idanuwan suka fara sauka qafafuwanta suka harde atake saura kadan ta kife taku daya ya riqota Yana zuba Mata idanuwansa dasuka qarasa rikitata tayi saurin kwacewa tareda Dan kallon gefensa ta wuce tana qoqarin sakin fuska tanawa JJ oyoyo.


Bata wani tsayaba ta haye sama ta zauna tana jero ajiyar zuciya jikinta na Dan rawa.


Saidata nutsu kafin ta tashi tafada toilet tayo wanka tazo tayi Sallah tashirya saitakasa fitowa takira nanny aka kawo Mata abincinta a daki.


Haka taqi saukowa har washe gari,


Cikin sauri tayi Shirin office zata fice gidan ta sauko ko gurin dad batajeba ta sulale ta fice.


Ko zama batayi a office ba aka bude qofar aka shigo ta dago zatai magana suka hada ido ta daure fuska zatayi magana ya jawota jikinsa ya matseta tareda zuba Mata idanuwansa masu mugun rikitata batareda yace qalaba.


Muryanta na rawa tabude baki daqyar ta iya cewa"


Let go of me please.


Please"takuma cewa muryanta na rawa.


Wani irin murmushi yasakar Mata take ta zaro ido tana neman some masa take abin yasake sashi murmushi ba zato taji saukar kiss dinsa akan idanuwanta zata qarasa somewa ya cirata sama gabaki daya ya fito office din da ita baidamu da kallon da ake musu ba yakaita mota yasa Saida yadawo yashiga motar ahankali ya furta"


Nigeria zamu je a cikin Daren nan jirginmu zai tashi.


Da sauri ta kallesa gabanta na bugawa da sauri.


Gida Suka Isa ya bude Mata qofa ya wuce yabarta sake da baki tanabin bayansa da kallo.


Bata yarda da Nigeria zasu jeba Saida taga kowa na shiri haka tahau Shirin kayanta Dana baby z.


A gurin cin abincin Rana tunda tazauna a dining din idanuwansa ke kanta Saidai abinda yafi hautsinata shine yanda yakoma zakinsa tsaf kallonsa ma faduwar gaba yake sata.


Ganin takasa cin komai sai mutsu mutsu takeyi yasa ta miqe tabar dining din Takoma Palo.


Suna Gama cin abinci suka fice ko mintuna goma basuyi da fitaba akai knocking tana budewa taga order ce akayi ta honey pancakes da sunanta.


Murmushi ne ya subuce Mata sbd tasan waye yayi wanan order din.


Karba tayi tadawo ta zauna tana kallo tanason ci Amma ta Hana kanta ci ta ajiye a inda zaigani yasan bataciba.Qarfe biyar na yamma dukkaninsu suna airport zuwa lokacin kowa baida wani dogon kuzari sbd sanyi da jikinsu yayi yanda zasu samu su kawun dakuma yanda zaa karbesu su hudu da ake sakaran sun mutu tun shekaru.


Har cikin jirgi Babu me wata magana acikinsu sai tunani har Suka isa gabanin asuba.


Dr sayyid ne yazo yadaukesu da wata baqar jeeb dinsa.


Ahankali Zaki yace"


Gida zaka kaimu.


Kallonsa dad yayi zaiyi mgn nadey ta rigasa da cewa"


Please dad muje can din first Dan Allah.


Daga Kai yayi suka Kama hanyar gidan kawu lokacin duk masallatai sunfito sallar asuba har gari yafara haske.


A qofar gidan Suka tsaya Allah yasa babu wasu mutane suka shige gidan dukkaninsu suna Jin kewar gidan nadawo musu sabuwa.Da babbar malum malum dinsa yafito daga dakin iya talatu Yana hamma sbd yau baisamu sallar asuba ba sbd kwana yayi da lalataccen ciki na wani romon Kai dasukaje Suka Sha shida mal idi a gurin wani bikin daurin aurenda ko gayyatarsu baayiba.


Buta ya dauka zai shiga bandaki yaji sallama ahankali ya juyo yayi ido biyu da wadda ko mutuwa yayi yadawo fuskarta Bata bace masa,,,


Zaro qananun idanuwansa yayi zai saki ihu saiyaga Zaki yashigo shima cikin sallamar 

Take ya saki butar hannunsa jikinsa na daukar mazari saikga JJ yashigo tareda neyo.....


Hannu ya Dora akai tareda zubewa cikin tsananin tsoro da tashin hankali yafara qwala Kiran sunan talatu Yana cewa"


Talatu zoki bani shahada lokacin tafiyar yazo matacci nake gani wlh,

Gashi nidai wlh ban dandadi dadin arkin danake roqoba Koda na awa dayane na roqi Allah yamin arziki Kona wucin gadin ne Amma Banda rabo.....


A rikice iya talatu tafito dakin tana daura dankwali zatayi magana ganin Wainda ke tsaye saita murza ido tasake murzawa...


A hasale cikin muryar kuka dattiyan yace"


Ke banason diban albarka zakiban shahadane kokuwa saina mutu Banda rabonta...

#MAMUH._*Mamuhgee38*_

Hannu iya talatu ta Dora akai Saidai kafin tasamu ikon yin magana jikinta yasaki tafadi a some.


Dattiya na ganin hakan baisan sanda ya fashe da kuka ba jikinsa na makyar kyarar tashin hankali baki yakeson budewa yakira ceto Amma ya kasa gashi dukkaninsu sun jera masa tsaf a gabansa murmushin Zaki daya Saba masa idan zai masa gayya shiyakeyi ko yanxun sbd shiyace karkowa yayi mgn.


Ahankali ya sanya hannu aljihu yayi kamar zai Ciro Abu dattiyan na ganin hakan yasan addar cire ransa ce zaa fitar sai kawai yasaki jiki yayi baya jikinsa na rawa cikin ransa yace gwara nayi sumar qarya koma menene ayi idona rufe.


Da gudu nadey dake hawayen tsananin farin cikin ganin babanta na nan da hallayarsa ta tarosa jikinta tareda fashewa da kuka tana cewa"


Baba karka Suma wlh Babu wasu matacci dakake gani mune gabanka bamu mutuba,

Kabude idanuwanka kagani mudin daine muka dawo gareka.


Dattiya najin hakan jikinsa yasake daukar mazari yasake sake jikinsa yaqi motsawa danyaqara nuna a some yake,

cikin zuciyarsa kuwa kuka yakeyi sosai Yana tsinewa qarfin aljanunsa dasuka hanashi Suma adaidai yanxun sbd hankalinsa ya mummunan sake tashi ganin matacci gabansa su hudu Ras har Wanda rabonda yagansa shekaru fiyeda talatin.


Murmushi Zaki yasaki tareda matsowa gabansa ya tsaya cikin murmushi yacewa JJ ya shafawa iya talatu ruwa.


Gyaran murya yayi Yana kallon kawun ya dago ya kalli nadey dake kuka cikin sakin fuska yace"


Lemme handle this.


Wayarsa ya fitar daga aljihunsa wandonsa ya kunna fitilar wayar ya kashewa kawun ido da ita saiga idanuwan kawun sun fara marmadi alamar idanuwansa biyu.


Cikin sanyin murya Mai taushi Yana kallon nadey yace"


Ayyya sai hakuri fa yariga ya tafi JJ daukesa muje mu rufesa kawai dama yace idan yatafi kar 'dan dabar dayayi zaman gaisuwarsa.....


Jin kawai Sukayi ya fashe da kuka Yana cewa"


Talatu kinci amanar zaman tare dakika Suma kika barni...


Wata irin dariya Suka sake kusan atare Banda nadey da batasan lokacinda takai masa duka a hannuba tana harararsa da hawayenta


Dad ma matsowa yayi yana cewa"


Ku matsa karku bugarwa da Yaya zuciya.


Kamasa yayi ya miqe daidai iya talatu itama ta farfado Suka zaunar dasu a tabarma dad Yana sake kwantar musu da hankalin Babu wata fatalwa dayake gani ko matattu sudin daine.


dattiya da hankalinsa Bai Gama kwanciyaba murya na Yar makyarkyata yace"


Eh nidai kubari nakira Dan uwana mal idi zanfi Jin hankalina ya kwanta.


Zai tashi iya talatu tarigasa tashi sbd tasan bazai dawoba dagacan zasu iya guduwa shida mal idi din tace"


Bari nakira makashi ta katanga.


Wata irin muguwar harara yabita dashi Yana ayyana irin Rashin qaunar dake tsakaninsa da talatu datake masa irin wainnan abubuwan.


Zaki dayafi kowa sanin waye kawun yasaki murmushin dayasa nadey harararsa ahankali

Ya dauke gira daya cikeda mamakinta wato ta manta waye Zaki Dan bazaice Mata haydar ba sbd shi kansa yafi qaunar Zaki akan haydar.Mal idi da qarfinsa yashigo Yana asuwakinsa babbar rigarsa tun ta jiyace a jikinsa da ita ya kwana da ita yatashi..


Yana ganin baqi masu Kama da turawa yasaki asuwakinsa tareda washe dukkanin haqoransa Yana cewa"


Shikenan mafarkin dattiya yazama gskia da kuzarinsa ya iso shimfidar tareda zagayowa gurin amininsa zaiyi mgn idanuwansa suka sauka akan fuskokinsu yafara binsu daya bayan daya da kallo Yana Dora ido akan Zaki sukaga yayi baya Yana neman kakkafewa.


Dattiya ne ya tarosa Yana basa salati Yana cewa"


Daure danne mal idi wannan duk sharrin talatu ne Kuma zataga matakin dazan dauka.


Cikin yanayi na son fashewa da kuka mal idi ya kalli talatu Yana cewa"


Meya shiga tsakanina dake talatu da kikemin wannan bita da qullin.??


Cikin gyaran murya dad yace"


Wlh anan gurin babu fatalwa dukkaninmu Muna Raye Kuma bamu taba mutuwaba,


Haba Yaya Ina katabajin anmutu andawo ko acikin kafirai bare musulmai,


Tabbas akwai tsoro da bugawar Kai da zuciya kasan mutum ya rasu tsawon Koda wata biyu ne kagansa bare shekaru tabbas wlh akwai furgitarwa..


Daqyar dattiya yabude baki yace"


Wlh Ni ko yanxu mutum ya mutu muka rufosa muka dawo nagansa to akwaifa qura bare shekaru...


Mal idi shidai baisamu na tofawa ba zufan dake masa tsiyaya cikin riga ya sharce sbd wannan shi ake Kira baqar safiya,

Gasu dai an rutsasu cikin gida Babu hanyar gudu to wlh Bari agama dattiya yashiga tsakaninsa da talatu Banda manta alheri dabai tsaya Mata agurin dattiyan ba Aida ba ita zai auraba wata hanne ce.


Sallah Suka farayi dukkaninsu a tabarmar tsakar gidan 

Sudai su dattiya na rabe gefe mal idi jira yake yaji abinda bai masa ba yayi ihun kawo ceto.

Dattiya kuwa Banda tagumi daya rafka Yana Kiran Jin idan su dinne yafara zubo nasa zancen.Aikuwa suna gamawa aka sake gaggaisawa nadey na kusada iya talatu da itakam tuni tafara murna musamman la'akari datayi da cewa nadey dama basuda tabbacin ta rasu tunda Bata tayi.


Ahankali dad yafaro bawa dattiya bayani tun daga ranarda yahadu da ruqayya a Lagos har mutuwarsa da dawowarsa inda yake bibiyan nan gidan haryasan Zaki dansa ne,


Shima yayi gwagwarmaya ta sana'ar Mai kusan shekaru shida kafin yadawo yafada ta masu aikin ginar zinari nanma kusan shekaru goma kafin Allah yayi anan arzikinsa yake gurin aiki yasamu dunqulen zinarenda shine silar arzikinsa.


Ahankali ya koro musu duk labarin nadey Dana haduwarsu da Zaki tareda qarshen dillas...


Cikin tsananin farin ciki iya talatu ta janyo baby z dake jikin JJ ta rungumeta tana hawayen farin cikin tasamu wata zainab din.


Mal idi kuwa gyara zama yayi yana sakin dukkanin fara'ar fuskarsa da bakinsa yafara hamdala Yana kallon dattiya dake kallon nadey baya ko qyaftawa sbd tsananin farin ciki Yana sakin hawayensa dasuka kasa boyuwa.


Zaki yakoma kallo Yana washe baki kafin yasake kallon baby z wadda allah yayi ba agansa zatazo duniyaba duk irin qone qone da azabar dayaci akanta.


Jawota yayi jikinsa akaro na farko da tsananin son qananun yara yakamashi baisan lokacinda ya washe baki ba Yana cewa"


Nadiya wannan 'yarki ce???

Oh ni dattiya Allah nagode maka Ashe dai arzikin ta jikoki zaizo.


Dariya yabasu mal idi yace"


Ai wlh alhaji dattiya kuka da baqin cikin Rashin Zaki da Nadiya ya qare Bari ma naje aikin shelar a dare daya Allah yayi bature.


Washe baki dattiya yayi yace"


Eh daganan ka taramin layin almajirai zanyi sadaka yau dai daya.


Kallon iya talatu yayi haqoransa basa rafuwa yace"


Maza doramin wainar dubu 'daya zanbaki gobe.


Miqewa dukkaninsu Sukayi dad yace zaitafi gida tukuna.

Nadey kuwa nokewa tayi tace anan zata zauna tukuna.


Zakima dakinsu yashiga yaga ya lalace Sam ko shiga baa iya yi Dole ya hakuri yabi dad shida JJ sbd su huta suyi wanka su sake gyarawa.


Bayan fitarsu gyara zama dattiya yayi Yana sake magana Sosai da 'yarsa idan ya kalli ko qafafuwanta wani farin ciki yakeji Wai wannan baqar baturiyar yarsace

Wai har qasashen jirgi tayita Hawa.Zabura dattiya yayi da kansa baby z na riqe a hannunsa Suka fito Yana cewa abi layi yau shine zai bayar ba basa zaayi ba.


Ganin wainar zataja lokaci yasa ya fiddo duk tsiminsa na kudi yafara raba nera hamsin hamsin 

Dasuka qare kuwa yace idi yabasa aro da sauri idi yakwaso duka kudinsa yabasa Yana cewa"


Dama alhaji dattiya wlh munada zuciyar bayarwa Allah ne baiyarda mubayar dinba shiyasa muke a haka.


Wani iska yaji Yana kada babbar rigarsa duk idi yakirasa da alhajin nan

Jiyake kamarma yafi dikko kudi yanxu.Nadey wanka tayi tashige dakin iya tayi kwanciyarta sbd Yaya dahiru da matarsa suntashi gidan sun canxa gida sbd masifar iyayen nasu dabasu Saba da itaba.


Wani manya manyan dankalin hausa da ake soyawa da doya da fresh yo mal idi yasiyowa baby z dake kallon mutane a tsorace sbd Bata Saba ganin mutane hakaba.


Fresh yo din kawai ta karba shima batashaba riqewa kawai tayi saita yo cikin gida tana qwala Kiran mummynta.


Nadey najinta tayi shiru harsaida iya talatu ta nuna Mata dakin da hannu tashiga ta fada jikinta tana cewa gurin daddynta zataje.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee39_*

Manya manyan dankalin dake hannun mal idi ya kalla cikin nishadi yace"


Mal idi waccan me Kama da wankakken karas din kasan bazata iyacin wannan shaquri danne dinba maza hadashi gurin sadaka alhaji idi nawa.


Wata irin dariya da baitaba yiba a rayuwarsa ya sake Yana washe dukkanin haqoransa rigarsa na cika da iskan nishadi Jin dattiya yakirasa da alhaji..


Dattiya yakallesa Yana wani gyara babbar rigarsa hango su mal zailani zuwa yace"


Alhaji idi ga baqi nan inaga gurina zasuzo kasan fa ba damar aji kayi kudi shikenan bakada shaqat sai adameka sauqin abin dai Allah beyini me rawa ba Dan har gyara zansa adanyiwa layin.


Mal idi ma su liman din dake dososun ya kalla Yana cewa"


Alhajin Allah kabari kawai ai Allah yasan tanadin dayayi Mana shiyasa muka debo shekaru a yawon maula sbd muyo ilimin ya abin yake,

Tunda gashi yanzu da bamuyo ilimin abinba ba qaramin wayon jama'a zamu fuskantaba.


Su mal zailani da liman na isowa Suka hau gaishe gaishen barka da arziki tareda sake jinjina alamarin na ubangiji mal idi shine yake zayyano musu labari Dalla Dalla wani abin kamar gabansa akayi 

Shikuwa alhaji dattiya gyada Kai kawai yake yana murmushi kamar wani basaraken da fadawansa ke gabansa

Yau Jin kansa yake ko shugaban headquarter Yan sanda da shugaban 'yan drugs zai iya Mari idan yakawo masa shashanci.


Kusan dai shimfidar karbar gaisuwar Taya murna Suka shimfida a gurin har guraren qarfe daya saiga wasu tawagar motocin Yan daba kusan bus bus uku da golf biyu sai mashin mashin tun acikin garin sukayo rally suna ihu take gari ya hautsine da mamaki dakuma murnar dawowar sarkin Yan ta'addan yankin Wanda duk wani Dan daba dake nan da Wainda suka tuba da Wainda Basu tuba ba tuni suka firfito aka hada rally aka garzayo sbd girman sarki da soyayyarsa da Allah ya Dora a zukatansu sbd yawancinsu sarki shine gatansu.


Dattiya na hango tawagar da ihun makamansu da ake gurzawa da titi tuni Suka miqe Yana cewa"


Tofa ai shikenan dattiya kaidai da Yan daba Allah yayi zakayi rayuwa ka Gama wannan mutu ka raba har Ina???""yafada Yana kasa boye murnarsa na ganinsu Dan harga Allah yanzu yasan kowane mutum ko Yaya kagansa Yana rayuwa to da ranarsa Kuma badan sun watseba yasan duk yanda Zaki ke Kare qimarsa da mutuncinsa Suma zasu tsare masa Amma ko yanzu Kam Yana maraba dasu koba komai yanzu shi alhaji ne yanzu Yana buqatarsu sbd tsaro tunda mutane ba dama kayi kudi magauta zasu taso masa tunda gashi nan mal hamisu yaqi zuwa masa barka da arziki Kuma yagansa Yana nan bai fita anguwaba.Kusan yawansu yasa wasu Basu iya zuwa har gabansu kawun Saidai manya manyan ne suke agaba.


Nanu da Lilo dasu sunny sune agaba Suka qaraso gaban kawu cikeda tsananin farin cikin ganinsa da kewarsa dasuka yi Suka duqa har qasa Suka gaishesu.


Cikin tsananin farin ciki dattiya ya washe baki yahau amsawa Yana saka musu albarka tareda musu adduar kariya akan makamansu ya Dora da cewa"


Zaki baya nan Yana can gidan babansa sunje janzowa Amma nasan yanzu Yana hanya ku jirasa ai Zaki yanzu ne zai buga mulkin.


Ihu Suka dauka ana gwara makamai dattiya na ganin haka sukai saurin shigewa gida kar asamu kuskuren Karo a saresa tun baici arzikin da yayan nasa sukayoba talatu ta cinye ita kadai Yana daga kwance.Yana shigowa gida nadey nafitowa daga dakin tagamo sallah zatakai baby z fitsari Wai Bata iya shiga toilet dinsu.


Murmushin farin ciki yasake tareda kamo hannun baby z din dayake tana Jin hausar ba laifi sbd mamanta da dady j harma da dad duk hausa suke Mata sbd ta iya kartazo kamar irin haka sundawo Babu hausa abakinta.

Yana nuna Mata fadin tsakar gidan yace"


A gidan nan kinfi kowa gata agurin me gidan wato ni,

Ki duba duk inda ya Miki y tsakar gidan nan kiyi fitsarinki sai a wanke kinji 'yar baturiyar matata.


Zaro ido nadey tayi cikin sanyi tace"


Baba ko Ina fa kace??


Eh Nina fada sbd gidana ne

Ke jeki kiyi fitsarinki a can qofar tsohon dakin uwarki.


Tanajin haka ta Kama bakinta sbd duk dokinta dayake tasan tsaf bazai boye ko danne halinsa ba.


Yana tsaye kuwa baby z tayi fitsarinta iya talatu ta Mata tsarki suna gurin sukaji sallamar JJ yasamu shigowa shi Zaki kuwa Sam mutane sun dabai bayesa sun rufesa gabaki daya sai ihu da hayaniya akeyi titin layin yacika da mutane ko wuceba baa iyayi da abin Hawa sun kashe layin.


Wani irin farin cikine yacika zuciyarsa sbd shi duk wani Dan daba a Dan uwansa na jini yake kallonsa,

Jinsu yake cikin ransa kamar yanda suke jinsa,

Babu wani Dan daba dazai iya Bari aci zarafinsa sbd Suma qaddarar Allah ce atare dasu,

Da wani zai dubesu ya tallafi rayuwarsu wasunsu da dama dasun shiryu sbd wasu Rashin mafitane take kaisu ga hakan tareda qaddara Dan haka shi shine gatansu Insha Allah.


Cikin Jin dadin ganinsa nadey tace"


Yawwa dady j pls Ina buqatan waya zankira Jasmin akwai email dinda nasan zaishigo yau akan new project din hannun mss ambryam Marshall.


Kallonta yayi Yana daukar baby z yace"


Kiyiwa sarki maganar zai baki...sai kawai ya share maganar dayiwa kawu zancen abinda ke faruwa waje Yana qara basa bayanin irin qaunar da akewa sarki.


Wani dadi kawun yasake ji ya washe baki Yana cewa"


Aikai jabiru kabarni nan Ni nasan komai bayan tafiyarku wlh duk wagarewa Sukayi Dole su qaunaceku uwa uba Ni tunda nine ake zaune gidana.


Dariya JJ yayi Yana cewa kawu will Neva change.


Nadey datajisa tasaki murmushi sbd tafi kowa sanin baban nata qarshene.


Zaki har dare baisamu kansaba sbd mutanensa da tuni Suka kasa Suka tsare wasu duk sun tafi Amma duk sauran Wainda suke da anan din sunanan sunyi zamansu Dan kuwa tuni aka bude shagon qofar gidan dayake amatsayin dakinsu tun ada.


Sai bayan ishai yasamu shigowa cikin gidan lokacin baba bayanan iya talatu na dakinta itakuma fitowarta kenan daga wanka ta Dora sabon hijabin iya talatu a kan daurin qirjinta Sam Bata lura dashiba Saida ta fito tsakar gidan gabaki daya taga mutum tsaye Yana kallonta gashi akwai nepa.


Daure fuska tayi tafasa zuwa dibar ruwan wanke qafafuwanta dazata sake Yi ta juya zata shige dakin iya talatu.


Taku daya yayi ya riqota tareda dawo da ita jikinsa ya matseta ta baya tareda shinshina qamshin shower gel din jaggins dake tashi a ruwan wankan jikinta ya lumshe ido ahankali gajiyar jikinsa na qaruwa ahankali ya iya bude baki yace"


Please.....


Haka kawai yace take taji jikinta ya mutu da muryarsa Mai sanyin taushi batasan lokacinda ta lumshe idanuwanta ba tana sakin ajiyar zuciya sonsa na sake tsiro cikin ranta.


Jin jikinta ya saki yasashi juyo da ita ahankali ya zura hannuwansa cikin hijabinta zai......


Wani mugun Bari sukaji anyi tareda guntun salati sukai saurin sakin juna suna juyowa,

Iya talatu ma da sauri cikin tashin hankali ta fito tana cewa"


Waye yafada rijiya naji fadawar Abu a ruwa inji dai ba......


Kasa karasawa tayi sbd tsananin mamakin ganin qatoton durum dinta na ruwa me cin jarka goma dattiya yafada ciki Zaki na kokuwar fiddosa babbar rigarsa ta dabaibayesa ya matsu ya fito ya Fadi abinda ke ransa.


Cikin haushi iya talatu tace"


To Kuma me kakeyi kaje ka fada durum baka saniba???kaifa ba dama kaga arziki shikenan zakabi ka addabi kanka saikaje ka halaka kanka abanza  acinye kana daga kwance.


Nadey dake rabe jitayi duk hankalinta na neman tashi sbd tsoro da fargabar Allah yasa Basu yaganiba yafada ruwan.


Ganin yakasa tsayawa aciresa yasa Zaki buga durum din da qafarsa ya fashe ruwan ciki suka tsiyaye sai alokacin ya samu damar zare babbar rigarsa data dabaibayesa ya fito Yana zare qananun idanuwansa dasuka Sha ruwa yayiwa talatu kallo daya yace"


To 'yar baqar fata wacca kullum bataimib fatan kwarai wuce mutafi to ba rijiya na fadaba tunda haka kikeso.


Bayansa nadey tabi da kallon tausayinsa harya shige daki Yana tsiyayar ruwa ta juyo gurin Zaki dake kallonta cikin dauke gira daya wani juya ido tayi ta sakar masa wata hararar datasashi matsota tayi saurin juyawa zata gudu ya riqota tareda Kai bakinsa kan kunnenta Saida ya sakar Mata numfashinsa Mai dumi kafin ahankali yace"


Ina Zaki shigar musu daki kawu na ciki fa.


Rintse ido tayi tareda turesa cikin daure fuska tace"


Babana nefa ka daina yimasa haka.


Dan dauke gira daya yayi yace"


Nikuma kawuna ne abokin adawata akan iyalina.....


A masife ta daga hannu zata turesa yayi saurin yin baya tareda ficewa Yana murmushin da Bai cika yiba.


Kamar munafuka haka ta tsaya a tsakar gidan harya canzo Kaya ya fice tashiga ta shirya Allah ma yasa baby z tabi dady j suntafi gurin dad can zata kwana gurinsu Dan tun safiyar yau aka Kai masu aiki gidan su biyu suka Mata.Washe gari da safe bayan sun Gama karyawa da wata farar wainar shinkafa dataji Naman kaji wanda mal idi ya siyo musu danshifa tuni yasaki dukkanin bakin tattalin arzikinsa Yana kashe musu sbd yasan year uban ribarsu zaici.


Dattiya cikin shirinsa na fita zuwa kasuwa ya bada rumfarsa ga wani nasiru daya damesa tun jiya yanaso zasuje shida idi suyo musu bankawana.


Kallo iya talatu tabisu dashi cikeda mamakin yanda suka are Suka yafe tun ba'a ce musu gashi din ba.


Yana cikin gyara babbar rigarsa dasai zashi babbar hidima yake sawa mal idi yashigo shima fes cikin babbar riga da hularsa sai faraa yakeyi.


Cikin girmamawa nadey tace"


Ina kwana baba????


Lafiya kalau Nadiya ya muka tashi?

Ya kwanan baqunci?


Murmushi kawai tayi tana cigaba da cin wainarta datake zaune gefen iya talatu.


Siririyar sallamar zakice ta sakasu juyowa yana sanye cikin wasu armless adidas masu tsadar na geaming daya gamo dukkanin qwandunansa da muscles dinsa masu nuni da qaqqarfan jikinsa a bayyane suke sbd Rashin hannun rigar sai hular rigar daya rufe kansa da ita asalin asalin jininsa na Igbo ya haskakawa a fatarsa.


Da ido ya kafeta Yana gaidasu kawun dasuka tsaya kallonsa baki a sake 

Itadai iya talatu yi tayi kamar bataga me yake kalloba ta amsa gaisuwarsa tana tambayar zainab.


Ahankali ta Dan yamutsa fuska tace"


Good morning.


Bai amsaba ya dauke idanunwansa daga kanta Yana kallon kawu yace"


Kawu zan tambayeta wani abune.....


Ko amsa kawun Baibasa ba ya juya suka wuce sbd yagama gano dai dagashi har zakin Babu Wanda halinsa ya canzu idan ya biyesu wannan karon babbakesa zasuyi a wutar murhu ko yafada rijiya subar talatu da baqin cikin zaman takaba,

Saidai shikuma gskia bazai iya saka ido ace ko yaushe a gaban idonsa ake iya shege da 'yarsa ba.


Suna fita mal idi yace"


Dattiya gskia yaran nan zuwa zamuyi musake daura musu aure karfa azo ayi irin da kananan sake da baki kaji qaruwa ta samu.


Barni dasu idi duk wani Dan iskan America da shegenta daidai nake dasu baresu baqin haurenta inanan a dattiya Dina jira nake nagama sallamar masu damuna dinnan kafin naji dasu.


Daga bayansu sukaji yace"


Kawu kuje ga mukulli nan nabawa Nanu yakaiku duk inda zaku.


'dan so yayi ya washe baki saiya fasa ya nufi motar Nanu ya bude musu suka shiga zakin ya zuro Kai ya miqawa Nanu ATM dinsa yace"


Kabiya ka cire musu kudi kabasu idan zasuyi amfani dashi.


Duk yanda kawun yaso 'daurewa kasawa yayi ya saki wani murmushin jindadi yanajin wani girma na shigarsa musamman yau yasan a kasuwa saiyayita samun Yan fada.


Suna wucewa yadawo cikin gidan ya kalli iya talatu yace"


Ki shirya zaku fita yanzu JJ zaizo zai kaiku.


Kallonsa tayi da alamar tambaya tana wani daure fuska da basarwa.


Qin Bata amsa yayi ya juya ya fice waje gurin yaransa danshi haryanzu yanason zama acikinsu.


Qarfe goma JJ yazo ya daukesu suka fita zuwa gurin passport.


Sukuwa su kawu yawone Suka fitayi gashi kowannensu anabasa dubu hamsin hamsin ya zuba cikin babbar riga sukaje kasuwa rumfarsu suka ringa bankwana suna rabon kudi anata tayasu murnar yayansa dasuka dawo sunyi arziki dagashi har mal idi sun mayarda sunayensu alhaji da alhaji.Daga kasuwa duk inda sukasan sunyi Sanaa Saida sukaje bankwana daganan Zaki yayiwa nanu waya yace yakaisu ayi musu passport daganan su samu su JJ a immigration office.


Aikuwa acan yakaisu inda akai musu passport da komai a Daren aka aikasu nemar musu visa din umra.


Jin hakan yasasu kusan kasa bacci musamman yau da kowannensu ya riqi dubu hamsin hamsin cikin aljihunsa tuni Suka raba dare suna firar.


Duk yanda Zaki yaso kebewa da ita qi tayi sai sake zamewa takeyi tana basar dashi,

Tun Yana hakuri harsaida yafadawa kawun

Kawun yayi shiru sbd ganin duk dai iya Reni sun rainasa Amma zaiyi mganninsu Dan yafi qarfin iskancin duk wani shegen America bare su na Nigeria.


Dad da kansa yazo Sukayi bankwana ranarda zasu wuce aka kaisu airport,

Ita,baby z,iya talatu,babanta,mal idi da matarsa sai Nanu.


Tunda Suka Isa take cikin tsaka Mai wuya sbd tsabar masifar babanta data mal idi sbd su komai saisun sanshi daki daki.


Babban tashin hankalinta shine tunda Suka tafi so biyu su baban na Bata sai ansaka nemansu shi baba idi ma har wata tsohuwar takari yaso maqalewa Wai zai aureta daqyar aka kashe zancen Suka maida hankali gun ibada.


Su kuwa suna nan ansaka gyaran gidan anroshesa gabaki daya ansaki kudi anfara aikin gidan tuquru sbd dattiya ya dage akan bayason tashi anguwar dole Suka sakarwa wasu kudi sosai Suka siye gidajensu aka hada dasu ana sabon gininda akeson kammalawa cikin qanqanin lokaci.Yau da tashin hankali Suka tashi sbd mugun zawon da baba idin yatashi dashi akan kajinda tunda sukazo qasar dagashi har kawun basuda aiki saicin kajinsu da madarar Laban saigashi ta taba mal idin Suka dunguma zuwa asibiti inda qarahedai Saida aka jingina da Basu gado.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee40_*

Tagumi ta rafka tareda sakin numfashi Mai sanyi lokacinda tasake shigowa dakinda aka kwantarda baba idin ta tarardasu babanta yasiyo musu gasashiyar kasar injin sunaci hankali kwance suna magana komawa gida dasuka kusa Yi.


Cikin dumuwa ta kalli Dr din cikin turanci tace Dan Allah ya sallamesu su koma gida sbd tagaji da abin kunyar dasuke saka mutane Dan musamman babanta dakebin duk ma'aikatan asibitin da kallon tausayi Yana cewa shifa gani yake kazarsu ta Nigeria tafi wainnan mutanen qwari.


Mota tasamu Suka dunguma Suka dawo masaukinsu ita lift tashiga su kuwa dama duk ubanda ya taru basa shiga lift tunda Suka shiga so daya Basu Kuma ba stairs sukabi duk tsawon building din sunfi ganewa hakan.


Dakinsu Suka shige itama tuni ta shige nata inda take itada baby z,sai iya talatu da shafa'atu matar idi Suma daki guda.


Da daddare ita tayo musu order na abinci sukaci taje dakinsu baban tayita bugawa Amma shiru qarshe reception takira akace Mata yanxu Basu Jima da fitaba.


Dafe goshinta tayi Tama fasa zuwa dakinsu iya talatun Takoma daki takwanta tareda Kiran JJ cikin damuwa tace"


Dady j wlh su baba haukatani zasuyi a qasar nan yanxu acikin Daren nan fa sun fita Kuma nasan wlh bazasu iya dawo da kansuba sai anje nemansu inaga gida zamu dawo direct bazamu biya Dubai dinba gskia.


Dariya yayi zaiyi mgn Zaki dake gefensa Yana aiki a laptop ya miqa masa hannu batareda ya juyoba ko cewa qala ba.


Miqa masa wayar yayi tareda miqewa Yana cewa,


Bari nayi magana da dad.


Jin shiru sosai ya ratso wayar yasa zuciyarba harbawa kadan tareda lumshe ido tana sakarwa pillow nauyinta sbd tasan waye ya karbi wayar.


Ahankali yace"


Nine nakira dazu kika qi daukar wayana sbd Kinga damata da yawa right????


Zuuuu tayi da idanuwanta dake neman rufewa sbd yanda muryarsa ke tayar Mata da wata sabuwar kewarsa da tsananin sonsa.


Ahankali itama ta bude baki tace"


Banganibane.


Aje laptop din gabansa yayi tareda kallon wayar yasake tsuke fuska ransa na Dan baci baisan renin yakai hakaba Amma zai dawo da ita hayyacinta idanma hauka tafara zatasan Zaki nanan yanda yake.


'Daure murya yayi kai tsaye yace"


Bani 'yata.


Murmushi tayi Mara sauti tareda kallon baby z da bacci keson daukarta ta miqa Mata wayar tareda cewa"


Your uncle na magana.


Karba tayi cikin murna tana cewa Ina dadynta da granddaddy dinta.


Tanaji yayi fira da 'yarsa Yana gamawa ya kashe wayar baisake nemantaba.


Shiru tayi cikeda tunanin yanda zasuyi rayuwa idan Suka dawo sbd yanxukam Allah yagani tana buqatar mijinta atareda ita musamman yanxu dataga 'yan Mata masu kyau da burgewa na nuna zalamarsu a fili kansa,


Gefe daya Kuma tunanin fammah ne ke neman damunta sbd tanason sanin Yaya take tunda tasan suna cikin tsananin Rashi da buqata.


Wayarta ta dauka takira Annah Suka hau fira daga baya take fada Mata tanason sanin halinda dillas ke ciki.Washe gari dasukaje masallaci acan Suka wuni bandasu baba dasukai wani aminin Wanda shima Dan juma ne da Dan jummai suka bazama yawon Shan shayi da maiqo har dare Basu dawoba 

Sai washe gari tagansu shi dinma tana Jin motsinsu tayi saurin fitowa tun kafin tayi mgn iya talatu da itama take qule dasu ta fito ta watsa musu wani kallo cikin takaici tace"


Allah dai yasa kusan kun tsufa kudaina wannan yawon ta zubar din,

Harda qasardaba qasarku ba bazaku iya riqe qafafuwanku ba ku zauna guri daya wannan abin kunya har ina.


Cikin daure fuska dattiya yace"


Ke talatu ki fita idona banason Rashin mutunci da Rashin iya mgn,

Meye amfanin zuwan idan mutum Bai zaga yaga koina ba......


Cikin takaici ta katsesa da cewa"


Dan Allah dattiya kudaina wannan yawon kungafa gobe zamu koma Amma kun kasa tsay.....


Cikin kufula idi da dama yake cikeda ita tun wancan lokacin yace"


Talatu waike meyasa Allah bai zuba Miki dangana da iya Kama bakinkiba,

Bansan yaushe qiyayya tashiga tsakaninmu ba ranar har farin ciki kikeyi kika kirani sbd nazo Naga matattu da dagaske ne matattun ne wato nagansu zuciyata ta buga na mace agurin tunda dattiya baida kowa saini yanxu,

To dattiya kashiga tsakanina da talatu hakama ita tashige gaba tasa shafa daga hankalina a qasa Mai tsarki akan auren nan danayi niyya ta gashi nan nafasa auren Amma ba yanxu zankoma gidanba tukarin zamuyi muma.


Zaro ido nadey tayi cikeda faduwar gaba tace"


Baba wane irin tukari ana zaune qalau Dan Allah kuyi hkr yau tsakar dare jirginmu zai tashi.


Washe baki dattiya yayi yace"


Badamu zaku koma ba anan zamuyi takari alhaji garba zamu zauna agurinsa hanyoyin dogaro dakai gasunan birjik su zai koya Mana a qasar shekara daya mundawo gida.


Tagumi talatu ta rafka daga tsayen tanajin inama baazo dasuba wannan abin kunyar dasu dattiya zasu jawo musu.


Duk yanda Nadiya tayi dagewa Sukayi akan raayinsu batasan lokacinda tafashe da kuka ba tana sake roqonsu Amma Suka wucewarsu Suka barta iya talatu nabinsu da hararar baqin ciki da takaici.


Zama Sukayi dukkaninsu Suka rafka tagumi cikin baqin ciki da damuwa

Nadey datasha kuka harta gaji ta dauki waya takira haydar.


Yana kallo wayarsa nata ringin yaqi dauka Kuma yasan itace Amma yayi banxa da ita sbd zai banbanta Mata Aya da tsakuwa.


Qaruwa damuwarta tayi sbd tasan mulkinsane da izzarsa yasa yaqi daukar wayarta sai takira dad.


Cikin tsananin damuwa tafara fada masa abinda ke faruwa abin yabasa mamaki sosai sadai Kuma yasan dadine yasasu cewa bazasu dawonba takari zasuyi.


Cikin lallashi yace"


kwantar da hankalinki nadey nasan ya zan musu zasu dawo kafin kutashi tafiya.


To tace murya a sanyaye.

Ita su iya talatu nema ke Bata tausayi musamman shafa'atu da duk tafiyar ta fice aranta tun lokacinda mijinta ya ha'du da takari.


Dad nagama waya da Nadiya yakira layin wayar dattiya da aka siya musu kafin tafiyarsu wadda bayan Zaki da JJ Babu Wanda ya taba kiransu sai yanxu dayaji tana ringin cikin aljihun babbar rigarsa.


Da sauri yacirota Yana cewa"


Zaki ne ke Kira qila yaji bayanxu zamu dawoba bankwana zamuyi.


Dauka kawai yayi sbd koya tsaya duba sunan ba ganewa zaiyi sosaiba.


Jin muryar neyo yasashi sake washe baki Yana kurbar shayinsa na larabawa Mai shegen zafi yace"


Aliyu ya Nigeria??


Murmushi dad yayi tareda cewa"


Lfy klau alhmdllh yaya,

Yaya ibada da Kuma baqunci?


Lafiya kalau ibada baqunci Kuma ai munxama Yan qasa tuni.


'yan qasa Kuma yaya?

To dama Ni akan maganar gidankane kaida Yaya idi dazu aka kawo takardu Wai gidan mallakin wasu ne ba nakuba.......


Wata qatuwar ashar ya mulmulo Yana qonewa da ruwan shayin ya miqe yace"


Wane Mai rabon wahalar ne yace haka?

Gidan damuka gida da guminmu,

Ganinan tafe Nigeriar Inga wane Dan iskan kudun ne.


Alhaji idi da tuni ya dire kofinsa Yana jiran qarin bayani yace"


Meyasamu halalina???


Ciki ciki dattiya yayi da qananun idanuwansa ransa amatuqar bace yace"


Wani Dan baqin cikin dayakasa ganin munyi gaba ne Wai filin gidansa ne.


Miqewa idi yayi Yana cewa"


Dama yanxu magauta tako ina kunno Kai zasuyi Amma daidai nake dasu Dan Ni Dan iskan takari ma nafi qarfinsa bare na Nigeria muje.


Alhaji garba na musu maganar zamansu tuni sukace sun fasa yanxu Amma zasu dawo.


Yace"

to shagon damuka hada kudi muka Kama fa zamuyi sana'a??


Kai alhaji garba bakaji Wai hawun dake neman hawanmubane kake mgnar shagon Saida shayi da kaji.


Masaukinsu suka dawo lokacin har anyi sallar magriba suna zuwa ba kunya Suka hada kayansu tsaf Babu fuskarda kowa zai samu tambayarsu ya akayi dayake Suma sansan halin sai Basu ce musu qalaba har akai ishai Suka sake kakkamta kayansu mota tazo ta daukesu zuwa jidda suna Isa basuyi ko mintuna arbainba aka Kira jirginsu Suka miqe har lokacin su kawun fuskar nan a tsuke tam.


Suma haka Suka fecesu hardai iya talatu ita dama shafa'atu jira take akoma ta gyara masa zama.


Baby z ce kawai ke walwala a tsakaninsu sbd zuwa lokacin tasaba da kakanta sosai suke dasawa Saidai idan tayi Abu kadan turawa nashan zagi ba sauki.


Qarfe goma na safe jirginsu ya sauka a Lagos sun fito Dan neman taxi zuwa masauki sai Jin tayi baby z ta kwace daga hannun babanta tana cewa"


Yeehhh my uncle.


Faduwa gabanta yayi ta dago da sauri ta kalli inda z din tayi tagansa sanye cikin wasu Armani wears normal size blueback sun masifar fitarda kyawun hasken fatarsa yasaki wani guntun murmushi tareda warewa 'yarsa hannu yadagata sama yana cewa"


My baby is back.


Kiss tai masa a kumatu tana dariya sosai tace"


I miss you so much uncle.


I love you so much my little miss Noah.


Su iya talatu ya qaraso Yana gaidawa fuskarsa a Dan sake kafin ya maida kallonsa kansu kawu da mal idi ya bude baki gabaki daya Yana kallon wata taquwar Mata data wuce da wani wando daya gama kamata kusan komai Bata ana gani sai wata riga Mara hannu da wani kalar gashi kalar Blue data saka akai.


Dattiya kuwa takalminta yake kallo Yana tafiya har yayi tuntube da jakar kayansu saura kadan ya kife talatu ta girgiza Kai tana cewa"


Karkaji ciwo alhaji kalli gabanka.


Fuskewa yayi Yana amsa gaisuwar zakin Yana sake kakkallon mutanen dake harkokinsu a airport din.


Allah yagani shikam bai taba ganin anbawa mahaukata damar kaida kawo hakaba sai anan.


Mota Suka dunguma dukkansu dama wata black BMW bus ce aka kawosa da ita ta daukesu duka suka nufi babban gidansa dake Victoria island.


Sosai ikon Allah yagama kamesu kawun tako Ina tun lokacin Suka dau hanyar zuwa gida Zaki yace"


Kawu kana cikin Lagos ne fa.


Kallo juna Sukayi da idi cikin ransa yace"


Ashe mutanen Lagos din sunfini iya tsula tsiya.


A boys quarter aka sauke su baban inda Suka hau baccin gajiya bayan sunyi sallah sunyi nis.


Bedroom biyune a palon qasa su iya talatu Suka shiga daya ta shige dayan.


Wanka tayi tai sallah ta kwanta sbd tana buqatan hutawa Dan tunda sukai tafiyar nan batada hutu haukacewama tasoyi sbd tsabar tension.


Bata fitoba sai yamma shima sbd yunwane.


Babu kowa a makeken palon sai hayaniyar z datake jiyowa a palon sama ta nufi qofar datake sakaran qila kicin ne tana budewa taga Babu komai ba kowa ta bude fridge shima drinks ne kawai sai apples ta dauki daya tanaci ta fito tana duba best restaurant a Lagos din ta wayarta sbd tayi order.


Wani kitchen crafts dake kusa tayi ordern chips source da white veg pasta sai coconut water mix tadawo palon ta zauna tana qoqarin Kiran dad taji qamshin  possession royaltee man yashigo hancinta tareda sanyin aircon split dake daukeda qamshin airfresh na rosallee.


Lumshe idanuwanta tayi tareda budesu ta dago ta kalli direction din saman Suka hada ido take jikinta yasake mutuwa takasa Koda motsi harya sauko yazo ta gabanta ya wuce ya fice yabarta dabin bayansa da kallo jiki amace.


Koda aka kawo order dinta takarba tabiya kudin tadawo ta nufi dining taci.

Tana gamawa tasake komawa daki.Da daddare semo da miyar kaji tareda gasashen kifin dayaji lemon yasa aka kawo gidan kowa yaci yaqoshi.


Saida yabari su kawu sun qoshi yace"


Kawu muje kuga gari.


Ba musu Suka kwasa Suka bishi tun Abu nabasu mamaki harsuka fara gigicewa da balain dasuke gani tuni dattiya yafara shafawa kansa lafiya da  Yan iskan Lagos musamman wani gurin dayake gaisu sukasan da gayyane saiga su da salati suna ya maidasu gida.


Dattiya daya dawo harda hawayensa Yana cewa"


Lallai Ashe iskanci na Lagos shine yake cewa yafi Yan Lagos iya iskanci.

Allah yarabasa da iskanci irin na Lagos.


Dasuka dawo tuni kowa yayi bacci ya hayewarsa sama ya tube yayi wanka ya kwanta Yana danne abinda zuciyarsa keso.


Washe garima haka yasa aka dinga yawo dasu kawun a Lagos saigashi sun haukace da kallon ikon Allah da wani balain dayafi qarfin tsufansu.


Cikin saa kuwa suna wata anguwa lekki fada yatashi akahau sare sare da qona tayoyi take sukahau rawar jiki ba arziki Suka daga hankalin driver jikinsu Babu Wanda bai hada zufan balai ba harsuka dawo gida jikinsu rawa yakeyi mal idi ma Saida yahada dashiga bayi tun daga ranar harsukai kwana biyar basu sake marmarin fita koinaba.


Ranar dasuka cika sati aranar zasu koma gida har wani murna sukeyi sbd sunyi kewar gida matuqa musamman da duk tsorace suke sudai da Lagos din.


Airport Suka nufa kowa da ticket dinsa a hannunsa Banda Zaki sbd badashi zasu komaba Yana wani aiki ne.


Suna wucewa gaba ya kamo hannunta ya dawo da ita baya tareda matseta jikin mota Yana kallon cikin idonta da wani irin kallo dake kashe Mata jiki.


Hannu yasa ahankali ya shafo fuskarta tareda hura Mata iska ya daga Mata gira qasa qasa yace"


Babu ko bankwana Zaki tafi...???


Dan zamewa tayi yasake matseta tareda Kama hannunta yayi kissing yace"


Ki shirya Dana dawo zamu tafi.


Ahankali ta girgiza masa Kai batareda ta dagoba.


Yasaki wani siririn murmushinda yasake kashe Mata jiki yakai bakinsa kunnenta yace"


Okk nagane agaban kawu kikeson ki jere masa jikokinsa kenan ko????


Turesa tayi da sauri murmushi na kufce Mata tayi gaba tareda waiwayosa kadan Suka hada ido tasake juyawa da sauri ta wuce.


Dattiya da tuni yaketa masifa da baby z akan saita koma gurin uncle dinta ya danneta cikin takaici Yana cewa"


Ke banason taurin Kai irin na jajayen kunnuwan america,

Waincan uwayen naki basuda kunya ko kadan musamman ubanki daya Gama tarwatsamin tarbiyar 'ya tun bakizo duniyaba nake fama da Rashin arzikinsu dasunaji dasun daina Amma Ina..


Qwacewa tayi tana cewa"


Banaso sakeni.


Riqota iya talatu tayi cikin dubara tana cewa"


Kyalesu zainab ai yanzu mamanki zatazo.


Barta karma ta qyale kakkarya shegun qafafuwanta masu Kama Dana bebin roba zanyi kowama ya huta,

Iyayenta sun rainani itama ta rainani bazai yiyuba jaira Mai kama da baquwar aljana babbakewa da asarewa nawane banyiba kafin zuwanta duniya saikuma tazo Ina magana tanaimin turanci tunda ga dattiyan mahaukata,

To wlh ko mahaukatan lagos qarya suke bare na turai.


Isowar nadey ce tasa fadan yakoma kanta harsuka shiga jirgi fadan yakeyi idan yaga wani abin kallon saiya saurara ya kalla kafin yaci gaba.


Candai bayan yagama fira ta barke tsakaninsa da aminin Amana yace"


Kai alhaji idi wato su Lagos duk rabinsu mahaukatane.


Hmmm alhaji dattiya Ni wlh yanzu ko labarin Lagos naji anayi Aina daina shiga na zaqalqale,

Mutane ana kallo suna tafe a tsirara sbd lalurar hauka Amma duk ankasa masu taimako Kuma Amma dayake Naga basa duka ko ihu lafiya kalau suke tafiyarsu shinema saukin abin.


Dariya dattiya yayi yace"


Wato sbd girman lagos kana gani mahaukansu ma a natse suke fes fes abinsu,Amma fa Lagos nada dadi kawai dai balainsu ne yafi qarfin dattiya Dole Zaki ya tsula tsiya Ashe ba abanza ya deboba,

Ruqayya tayi qoqarin zama anan.


Itadai nadey tanajinsu har suka iso jirginsu na sauka jj ne yazo daukarsu mota biyu shida nanu tun a mota yake tambayar maqwaftansa sbd so yake Koda zai Isa duk suna nan suyi masa barka da dawowa.


Suna isowa qofar tangamemen gate din gidansu guda biyu da akayi komai iri daya Suka fito da sauri harsuna rige rigen cewa"


Wato dai da gaske wani shegen saman ya mallake gidansu.Dariya Nanu yayi tareda yin horn me gadi ya wangale gate Suka shige sai alokacin suka lurada su mal zailani dasukazo tarbonsu suna musu barka da isowa tareda murnar sabon gidan take Suka gano saisuka hau washe baki suna karba gaisuwarsu ana sake tambayar yaushe rabo.


Koda Suka shigo gidan sosai farin cikinsu yakasa boyuwa sukahau duba gidan suna aikin sakawasu zakin albarka da adduoi.


Qatoton palone da three bedroom sai wani palon me bedroom daya Wanda nan ne na kawun,

Sai boys quarter me Palo da daki sai toilet Wanda shikuma ba nanu ne sai dakin me gadi.


Sai wani babban part dake gefen nasu Kawun Wanda yake babban palone da bedrooms biyu sai kitchen da dining room shikuma shine na zakin JJ yace zai zauna da dad.Komai iri dayane Dana alhaji idi Kuma anzuba musu furnitures da komai na buqata.

Iya talatu da shafa'atu duk bacin Rai dasuka dawo dashi tini suka aje Suka hau murnar sabuwar duniya baqi da Yan anguwa sai murna suke shigowa yi.Daki daya ta zaba a Palo kusadana iya talatu anan ta baje itada baby z dayan dakin Kuma me aikin da aka daukoce.


Basu samu hutuba sai dare sosai mutane suka tsagaita.


Itakam da wuri tayi bacci iya talatu kuwa anacan anata baza sabon lissafin rayuwar daza'a fara.


Daqyar su alhaji dattiya Suka samu sauqin mutane suka shigo gidajensu amatuqar gajiye sai yanzu suke gane wani lokacin ba wulaqanci masu kudin keyiba kawai gajiyace da takura irinta mutane.


Abinci aka Kai masa Mai raida lafiya yaci yakoshi yashige daki yayi kwanciyarsa yana cewa"


Daban dawoba da yanzu talatu ce zataji wannan dadin ita kadai.


Hararar gefensa tayi tace"


Kaikuma baqin cikinka karnaci wannan arzikin nikadai.


Murmushi yayi tareda gyara kwanciya akan lafiyayyan gadonsa Yana cewa"


Ke yanxudai ki koyi daa ga miji dama can zafin talauci da rashine yasa nake dauka,yanzu hayaniyar mutane ma ta isheni.


Dariya abin yaso Bata saita gintse ta miqe ta kwanta itama.


Washe gari bayan ankai masa Kari yayi ya shirya cikin wata babbar shadda gezner fara qal sai daukan ido takeyi ya fito inda akace yanada baqi harabar gidan aka shimfida masu babban dadduma yafito ya zauna suna gaisawa cikin farin ciki baqinsu ne na kasuwa dasukai sana'ar lemo tare.

Alhaji idi ma cikin bulun shadda Mai qyalli ya qaraso Yana gyara babbar rigarsa ya qaraso ya zauna suna sake gaggaisawa.


Har yamma suna tarbon baqi idan lokacin sallah yayi masallaci suke shiga suyi sbd shima angyarasa sosai.


Abinci kuwa haka ake fitowa da kuloli daga gidajen biyu su mal zailani tuni Suka fara lasa arzikin Suma duk da Zaki kusan duk dattijan anguwan yabisu da jari ba laifi.Yau kwanansu biyar da dawowa yaune Kuma jumaa dad da kansa yazo gidan suka Jima sunata magana.


Dukkaninsu hidima sukeyi sosai tsakanin gidajen biyu dadynta kuwa sai tambayarta metakeso yakeyi sai abin yabata mamaki tace"


Dad meke faruwane???


Aurenki zaa sake daurawa yau after juma'a.


Kallonsa tayi da sauri muryarta na rawa gabanta na faduwa tace"


Aure Kuma dad?

Dawa???


Nine na zabar Miki mijin kinji nadey karki damu.


Murmushi ta qaqalo tareda sunkuyar dakai sbd dad bazai taba magana tace aa ba.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


_*Mamuhgee41*_

Duk yanda taso daurewa kasawa tayi bayan fitar dad gurin iya talatu taje inda take kicin tareda matar dahiru da fadima me aikinta suna yanka fruits ta qaraso tanason tambayar iya din saita kasa tasake ficewa.


Tana fitowa tsakiyar palon wasu baqi su biyu Suka shigo farare tas dasu Saidai kammaninsu da dad yasa tasake kallonsu cikin Dan qaqalo murmushi tace musu welcome.


Dayar me Dan shekaru ce ta taso tareda rungumeta jikinta sosai cikin kulawa da qaunarta tace"


Hey nadey nice aunt din haydar qanwar dadinsa amby Sam Noah and this is our younger sister Sarah Sam Noah.


Murmushi ta qaqalo cikin farin cikin ganinsu ta sake rungume Sarah Suka sake gaisawa tace Bari takira mum dinta.


Kicin Takoma takirawo iya talatu Suka dawo palon Allah yasa sunajin hausa nan Suka gaggaisa dasu aka fara kawo musu drinks da cake dinda aka siyo na Leda nabawa baqi.


Fira sukeyi ahankali Suna tambayarta yanayin aiki da Shirin bikin tana Basu amsa a sake.


Saida aka tafi masallaci sallar juma'a kafin Suka fito sai alokacin Suka saka aka dinga shigo Mata da kayan akwatinanda haydar yasa sukazo dasu Suka wuce gidan dady.


Aikuwa kayane sosai set din wasu kyawawan maroon alnafyeel bags take iya talatu tasaka aka sanarwa gwaggo shafa'atu Suka shigo ganin kayan.


Itadai daki tashigewarta tana waya da  JJ daya kirata cikin sanyin murya da tayata farin ciki yace"


Andaura auren Mrs haydar Zaki Noah.


Wani lumshe ido tayi tareda sakin siririn numfashi tana sake gyara kwanciya kan gadon dakin tace"


Nagode dady j.

Allah yabaka matarda tafini komai na rayuwa da kyawawan halaye nagari.


Amin""yace tareda cewa"


Baby z na gida ko tabi su aunty?


Dama tun dazu tana gurin fadima Amma inaga Bata bisuba tana nan.


Tana Gama wayar ta miqe taje tayo alwala ta tayarda sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.


Shiru shiru Babu Wanda yadawo har yamma sai kawai ta share itama taci gaba da hidimarta dama gwaggo shafa'atu takira wata madam eliqueen  Yar sudance Mai gyara tuni tasamu isowa tafara aikin gyaran jikinta duk da tace gskia tana buqatar sati iya talatu tace satin yayi yawa ayi Mata dai yau da gobe sai jibi sbd jikin nadiyar ma a gyare yake da santsin fata da laushi sbd tsadaddun products dinda take amfani dasu gurin wanka da shafa.


Saida aka fara kirayen magriba Suka kammala eliqueen ta wuce ita Kuma ta fada wanka da ruwan scent dinda tabata na rosallee florish purple sandal scent.


Aikuwa take toilet din ya gauraye da qamshinsa sosai har cikin dakinta 

Ita kanta tana wanka tana lumshe ido sbd sanyin qamshin turaren.


Tana gamawa ta fito ta shirya cikin wata purple nolet gown Mara nauyi ko wani dogon hannu batada ta daure kanta daya Dan jiqe baki bakin tasaka hijab ta tayarda sallah.


Tana idarwa ta cire hijabin ta fito tana qwala Kiran z sbd tazo tayi sallar magrib.


Bata lurada mutum a palon ba Saida ta juyo zata sake qwala Kiran z idanuwansu suka hadu gabanta ya fadi sbd wani irin kwarjinin dayayi mata dakuma tsoronsa daya shigeta.


Sanye yake cikin farar shadda qal sai qyalli takeyi yacire babbar rigar tana riqe a hannunsa da alama tunda rana Bai sauyaba.Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda kallonta da idanuwansa dake cikeda gajiya sbd taron aurensu na yanzun yafi na farkon cika da jama'a sosai harda manyan abokanan huldarsa Dana dad dinsa gasu kawu Suma yanzu jama'a sun qarar musu,

Dattiya a gurin daurin auren dayaga maroqa sunata faman kirari suna roqo saiyaji abin nabasa kunya 

Yaringa Jin kansa suka kalli juna da ido kowanne ransa wani iri kenan abin haka yake suna taqura jama'a suna wulaqanta kansu ba girma ba wani mutunci cikin mutane.


Idan kana roqo Wanda kafi qarfin arzikima wlh yafika girma cikin jama'a.


Da wannan tunanin kawu yacewa maroqan gurin su samesa gida bayan kwana biyu insha Allah zai Basu jari Kona sana'ar lemo ne yafi wannan yawon zubarda mutuncin.


Aikuwa nan Suka hau godia suna sake  sakawa aure albarka da jero masa manya manyan adduoi.Ba zato tajisa gabanta sosai harsaida tayi Dan Baya ya riqota a kasalance ya sake kallonta da idanuwansa dasuka sake rikita nutsuwarta yakai bakinsa kunnenta cikin kasala yace"


Yunwa nakeji sbd farin ciki yau ko ruwa banshaba tun safe please ki dubeni kar yunwa ta kashewa baby z uncle takashewa kawu Dan gaban sirikinsa.


Turesa tayi tareda harararsa tana yamutsa baki yasaki murmushi Mai kyau tareda juyawa bayan ya jefeta da wani kallonda yasan sirrin tasirinsa akanta tun a wancan lokacin dabatasan takamu da sonsaba bare yanzu datagama dulmiya cikin son nasa.


Aikuwa take duka gabobinta suka sake taji wani sanyi na shigarta 

Boyayyan murmushi ya subuce Mata ta juya zuwa kitchen tana sake waiwayon qofar daya fice.Yana zuwa part dinsa tubewa yayi yafada wanka sbd yau din amatuqar gajiye yake sosai.

Yana fitowa ya shirya cikin doguwar jallabiya baqa Mai laushi da tsantsi kasancewarsa fari saitayi Masa kyau matuqa ya tayarda sallar ishai da akayi Yana wanka yayi abarsa.


Yana gamawa ya dawo Palo ya zauna jiran takawo masa abincin bayan yakashe dukkanin wayoyinsa.


Agogo yasake dubawa yaga lokaci yatafi sosai shiru sai kawai ya miqe ya fito Yana 'dan dafe kansa dake ciwo kadan.


Tsayawa yayi daga balcony din part din nasa sbd hangota tafe daukeda tray fuskarta a daure sosai Wai ita karyaga damarta 

Abin saiya basa dariya da mamaki yasaki murmushi kadan Yana juyawa kallon gate da aka bude mota tashigo yakumasan kawune ya dawo.


Kawu datun shigowarsu ya hangeta gabansa ya Dan tsinke Yana fitowa mota yace"


Kai waye agurin nan????


Gintse dariyarsa Zaki yayi tareda saukowa ya qaraso gaban nadiyar data tsaya cak jikinta na rawar kunya 


Ya tsaya gefenta cikin cinnawa kawun tashin hankali yace"


Barka da dawowa kawu?

Nadey ce kawu ninace takowomin abinci naci.

Allah ya tashemu lafiya kawu.


Wucewa yayi gaba kawun yabisa da kallo idanunwansa kamar zaiyi kukan takaicin yanda Zaki Sam baisan kunyaba ya iya cinna masa hauka wato ga dattiyan mahaukata ko?

To wlh inanan a dattiya Dina kudi Basu canzaniba cikin masifa yace"


Wato Zaki nidai duk yanda naso shikenan mutanen Lagos sunci galaba akaina jininsu yafi na ruqayya qarfi akanka idona kake kallo kanacemin Allah yatashemu lafiya da 'yar tawa,


Ke Kuma ido tsakiyar Kai kinfito Lilo Lilo dake kamar gwaiwa Zaki kaiwa miji abinci wato dai ko yanzu bazaku Bari ace ku tareba to wlh Babu shegenda zai kaini yabaro kamar wancan karon so kukayi na Gama asarewa gurin zagayen kariyar mutuncina acikin gidana Ina daga kwance Kuna tsallakeni Kuna zuwa shaaninku...Iya talatu da hayaniyarsa tasata fitowa ta tararda abinda ke faruwa ta qaraso cikin takaicin Halinda baya canzuwa kamar na dattiyan tace"


Haba Dan Allah Kai Wai yaushe zakasan ka girmane??

Karka manta yanzu fa jikokine dakai Kuma 'daya na cikin gidan nan idan taji irin diban albarka dakakewa iyayenta wlh ka zubar musu da mutunci a gurinta...


Ke Ni banason qabli da baadi,

Ni bakiga irin renin dasukai min bane Ina ubansu,

Shi wancan qaton mara kunyar dangin Lagos bakiji cemin yake Allah yatashemu lfy sbd tsabar raini to wlh daidai nake da gyarawa ko wane Mara kunya zama a cikin gidan nan sbd gida nawane baza'a rainani cikin gidanaba.


Dawowa Zaki yayi cikin yanayi na sake haukata kawun yace"


Kawu kayi hakuri zamu kiyaye insha Allah baza'a qaraba,

Baby kibawa kawu hkr.


Cikin tsananin mutuwar jiki ta bude baki murya na rawa zatai mgn kawun dake hararar Zaki baqin ciki yagama cinyesa agabansa Zaki ke Kiran 'yarsa da baby a hasale yace"


Kina bude baki agurin zan karya qafarki Mai kama da hayaqin tsintsinyar qamshi.


Tsit Sukayi dukkaninsu harda iya talatu dake boye tata dariyar tace"


To kaji sunbaka hkr dai yanzu muje daga ciki ke Kuma wuce kikai abincin.


Wucewa yayi Yana gyara babbar rigarsa haryayi gaba ya dawo yace"


Idan kinkai karki dawo rufe qofata zanyi Kuma naji kin kwankwasa Ina budewa kusani yau saikun barmin gidana.


Da sauri ta kallesa ta girgiza Kai cikin rawar murya tace"


Nafasa baba wlh Bari na......


Ba shiru taji zakin ya janyeta tana qwacewa tana masifa ya wuce da ita har part dinsa ya bude qofar palon suka shige ya rufe.


Kawu daya saki baki cikin tsananin mamaki da takaicin yanda surukinsa Kuma 'dansa yagama rainasa.


Qyaci yayi yace"


Zakusha mamakina acikin gidan nan Dan wlh bazaku batamin jika da wannan Rashin kunyar da Rashin mutuncin nakuba.


Yana shiga yasakawa qofar babban palonsu key Yana cewa talatu duk kika bude qofar nan kinfi kowa sanin abinda zanyi Dan wlh hanaki kowace irin Sanaa zanyi.

#MAMUH._ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee42_*

Suna Shiga palonsa ta qwace jikinta tareda ajiye abincin ta juyo a fusace zata fara masa masifa taji bakinsa cikin nata ta zaro ido da qarfi zata qwace yasake matseta jikinsa Yana kashe Mata ido daya Yana shafo gefen cikinta.


Saurin qwacewa tayi da qarfi tana sauke numfashinta dake fita da sauri a boye ta zauna bakin sofa tana kasa dagowa ta kallesa.


Zama yayi hankali kwance kusada ita tareda yin balance yace"


Bani black tea din tukuna saiki bani veg din kadan shima.


Kasa motsi tayi sbd gabaki daya yagama hargitsa nutsuwarta hannuwanta har 'yar rawa sukeyi ta matsa kadan ta zuba masa black tea din ta miqa masa ya karba Yana kallon hannuwanta dake rawa ya hada dasu ya riqe tareda sakin ajiyar zuciya ya kalleta da idanuwansa masu sakata nutsuwa ahankali cikin kulawa yace"


Hey it's me,

Your husband,

Nine dai Yaya zakin dakika sani Babu wani qari ko ragi ok??


And I love you more than anything danake dashi arayuwa bazan taba cutatar dakeba,

Kawu duk wannan abin dakikaga yanayi yanayine sbd dabiarsace bawai haqiqanin abinda yake fadane acikin zuciyarsaba besides idan kawu ya daina wannan halayen nasa to ba lafiyaba sbd ciwone kawai zaisa ya daina Wanda bama fatan hakan,,,

So just chill my beautiful baby bride""yaqarasa fada Yana Mata wani siririn murmushi.


Miqewa tayi da sauri zatabar gurin ya riqo hannunta yadawo da ita kan cinyarsa Yana kallon fuskarta dake fidda annuri Yana Shan tea dinsa.


Harya Gama tanakan cinyarsa tana kallon yanda yakeyin komai nasa cikin izza da burgewa tun dacan haryanzu,

Haryanzu Bai wani iya sake fuska sosaiba Saidai murmushinsa da yanzu ya yawaita musamman agareta.


Murmushi tasaki Bata saniba tana kallon hannunsa inda tabon cizonsa yake a hannun haryanzu Wanda tasan da gangan yabar tabon Yana kallonsa bayan yana iya shafa magani tabon ya Bata.


Inda take kallo ya kalla ahankali take nutsuwar dayake Shiga duk lokacinda ya kalli tabon tashigesa sbd wannan moment din shine best moment a rayuwarsa sbd aranar yasan meye mace Kuma macenma wadda zuciyarsa da gangar jikinsa tafiso fiyeda komai.


Murmushi yasake ahankali tareda kallon nadeyn da kyau yana tuna yanda batai qwarin yanzuba a wancan lokacin taci wahala harda taumashi Amma Kuma yanzu tafi sanin ciwon jikinta musamman da hutu ya batata yanzu Amma zai banbance da kansa.


Matso da ita jikinsa yayi sosai tareda shafo cikinta murya qasa qasa yace"


Kinsan dai kawu yace bazaki Bata masa jikoki da Rashin kunyaba ko????


Murmushi tasaki tareda da kallonsa da idanuwanta dasuka mugun ta6asa Amma ya basar da shafo idanuwan Yana cewa"


Hmmmm kinason rabani da nustsuwatane?? That's not gonna happen.


Dauke gira daya tayi tana kallonsa da mamaki tace"


Really??


Hannunta ya matse cikin nasa Yana sake kallonta yace"


Hmmm.


Wani juyi tayi da ido tareda narkewa ajikin nasa tana lafewa tace"


Ok bacci ni nakeji gashi kasa babana ya koroni a Karo na biyu.


Murmushi yayi tareda safa wuyanta dake buso masa wani sirrin qamshi yace"


Kuma nasan yau bazai iya bacci ba Yana tunanin 'yarsa bazata iya daukar lalurar jarumin sarki kamataba....


Dukan qirjinsa tayi tana qoqarin miqewa yasake riqeta cikin jikinsa Yana Kiran sunanta cikin slow.


Shiru Sukayi dukkaninsu kowanne idanuwansa arufe suna sauke numfashi ahankali cikin nutsuwa.Sun Jima ahaka kafin ya miqe da ita ajikinsa ya nufi hanyar bedroom dinsa Yana kallon fuskarta data rufe idanuwanta.


Kan king-size bed dinsa ya kwantar da ita tareda juyawa ya nufi closet ya fiddo wasu ellecrux sleeping set na couples ya cire na mazan ya ajiye Mata na matan.


Jallabiyarsa ya zare ya nufi toilet yayo alwala Yana fitowa ya tararda tasaka Bata tayi saurin kwanta tareda lallubewa ya dauki nasa yasaka ya fesa Hugo boss spray dinsa ya kashe lights yazo gefen datake ya kwanta tareda shigewa jikinta sosai musamman sbd body contact dasuka samu na yanayin rigarta datafi Kama da Babu duk da taqi Bari yagani Amma yaji sbd Saida yasaka hannuwansa ahankali ya Gama lalabo yanda yanayin rigar yake ajikinta.


Akan cikinta ya ajiye hannuwansa Yana sauke Mata numfashi Mai dumi a wuyanta daya sata qanqamesa tana sake shigewa jikinsa da narkewa cikin jikin nasa.


Jin tagama hautsina duk wani tunaninsa yasa ta janye ahankali tareda sakin murmushin jindadi tana rufe ido cikin sanyin murya kaman zatayi kuka tace"


Bacci nakeji kaina da cikina harma da qafafuwana duk ciwo sukeyi.


Bede ido yayi da sauri cikin duhun ya kalleta saikuma yayi sanyi ya qyaleta tareda gyara musu kwanciya Yana lumshe ido.Qarfe goma na safe ta fito daga part din ta nufi part dinsu baba tana Jin wata irin kunyar hada idanuwa dasu saitafijin kunyarsu ayanxu fiyeda dacan.


Da sallama tashiga palon 

Baby z datun safe ta daga hankalin kawun akan Ina mummynta tanajin sallamarta ta taso da gudu tayi gurin nadeyn tana cewa"


Yehhhhh mummy your daddy said you left me hia and....


Shut up z""tafada tana Dan riqo hannunta.


Kawu dayake cikeda z din tunda ta ishesa da surutun neman uwarta yace"


Jaira me Kama da jikar ifiritu zakisan Dani kikeyi uwayenki bazasu maidani mutumin wofiba kema kizo da jajayen kunnuwanki na inyamurai ki rainani.


Dariya zancensa yabawa nadeyn da iya Amma Suka gimtse tana gaidasu ta wuce daki ta shirya cikin riga da skirt na gold atampa maroon ta fito ta nufi kitchen tahau hada masa breakfast sbd baban ya fita iyace kawai zaune a palon tana kallon African magic hausa.


Veg chips source tayi masa da no shuga black tea sai fresh lemon mix.


Saida takai Masa breakfast din tadawo tayiwa baby z wanka ta shiryata sbd dadynta daya Kira a shiryata zaizo ya dauketa harsu aunt su tafi.


Tana Gama fitowa Sukayi Dan zuwa part dinsa din itada z taji ana hayaniya bakin gate ta juya ahankali tana kallon gate din saitaji kamar hayaniyar na qara yawa ta Dan matsa.


Abinda tagani ne yayi mummunan daga hankalinta ta juya da sauri gabanta na bugawa da sauri 

Yana ganinta ya ture me gadin da sauri yafado gidan ya riqeta tasaki wani irin ihun tashin hankali da tsoro ta turesa tareda daga hannu zata maresa saita fasa ta janye z baya jikinta na rawa tace"


Am bakada hankali ne?

Get out of here tun kana gane hanya da kanka....


Zubewa yayi gabanta cikin tsananin kuka abuge ya riqo qafafuwanta Yana cewa"


Dan Allah baby kidawo gareni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,

Mutuwa zanyi nabi dadyna idan kika barni....


Kukan tsoro baby z tasake tareda qanqame mamanta 

Itama nadeyn jikinta mugun rawa yakeyi tafara qoqarin qwace qafafuwanta daya riqe tana ihu da roqonsa da hadasa da Allah daya saketa....


Ba zato nanu da me gadi suka shaqo wuyansa suka tayar dashi basusan da zuwan kawunba sai saukar Marika uku ajere sukaji ya saukewa am din Yana cewa"


Dan ubanka ubanwa yabaka izinin shigomin gida harka tabamin 'ya sbd ja riqa a ta'addanci ko?

To yau Zan nuna maka Ni haihuwar ta'addancin nayi maza Nanu ku canzamin kamanninsa besan dama nemansa nakeyiba dangin kashe kashe.


Cikin daga murya sukajisa daga bayansu Yana cewa nadey dauki z kibar nan I will deal with you later.


Suna barin gurin JJ na shigowa da motarsa Yana ganin am yafito mota da sauri Yana qarasowa gurin sbd ganin yau ran kawu yayi bacinda Basu taba ganiba shi sarki kuwa baa magana Dan tuni yakira 'yan CTU.

#MAMUH._ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*
*_Mamauhgee43_*

Wani wawan Mari zakin ya sauke masa Saida yakai qasa bakinsa na barewa da jini ya dago a gigice Yana bubbude idanuwansa dake neman rufewa sbd azabar marin,


Cikin hasala kawu yace"


Kai Nanu dauko masa Adda ko wani mugun makami yaci Mana ubansa

Wlh yau ka gode Allah bantaba dabanci ba dakaci ubanka da uwarka.


Hannu zakin yakuma dagawa idanuwansa na qara runewa zai sake Dora Masa wani mahaukacin Marin dayafi na farkon JJ yayi saurin dafasa tareda kallonsa shima ransa amatuqar bace yacewa zakin"


Let me handle this.


Kallon JJ yayi tareda tsayawa din sbd yasan zai iya kashe am din kafin zuwan Yan ctu ma'ana Yan 'drugs.


Am shine ciwon zuciyarsa na cikin zuci Dana sarari,

Duk lokacinda yatuno da nadey tayi soyayya da am Jin yake zuciyarsa na zafi kamar zai cinye kansa,

Am yasamu dama akansa wadda Babu Wanda yataba samun wannan damar ta soyayya da matarsa.,

Shine yanzu sbd ganganci da roqarwa Kai mutuwa yazo har cikin gidansa ya taba qafafuwanta matarsa....kaiiiii this is killing me.


Rintse idanuwansa yayi da qarfi yabudesu akan JJ dayasa gorar me gadi Yana yiwa am din dukan tashi kasha gishiri Nanu da Mai gadi na tayasa sbd me gadin shima ya tabo nasa yawon dabancin kafin ya tuba ya nemi aiki.


Kawu kuwa Jin yake dukan Bai masaba sai gyara babbar rigarsa yakeyi Yana saka qafa daga gefe Yana shurinsa ba tausayin am din ko kadan a zuciyoyinsu.


Alee idi dakejin ihun qaton na tasowa daga harabar gidan dattiya din yafito da sauri Yana cewa me gadin gidansa maza dauko gorarka miqomin daya magauta sunkai farmaki gidan 'dan uwana.


Me gadin najin hakan ya rarumo gora biyu ya miqawa idin suka nufo gidan suka fado Yana cewa"


Uban waye agurin?????


Ganin abinda ke faruwa yasashi saurin qarasawa da gudu ya janye am Yana kallon yanda sukai masa cikin mamaki ya kallesu yace"


Lafiya zaku kashesa ana zaune qalau munsamu zamu zauna lafiya ko gama jiquwa bamuyiba ace ankama wani daga cikin dangi ai bamuda wani kwanciyar hankali,

Dan Allah kubari wlh bazadai muso ace wani Abu yasamu dayanku ba,

Bakwa kisa,

Baku taba ba meyasa zakuyi yanxu?????


Cikin hasala kawu yace"


Bar wannan dangin daukan ran sbd abinda Suka iya kenan wato kashe kashe gwara a dandana masa ko kwatan kwacen qanin mutuwarne yaji tunda ubansa ya mutu baici mugun dukan azaba ba shi saiya karba har nasa harna ubansa shegu dangin Ethiopia.


Cikin son fahimta alee idi yace"


Shi din wanene Wai????


Dan gidan dikko Dilla ne.....


Zaro ido alee idi yayi Yana cewa"


Dikko Dilla????


Aiko yau zaici ubansa"""yafada Yana kwabe babbar rigarsa ransa a matuqar bace ya daga gorar hannunsa duk iya qarfinsa zai shemesa aka riqe gorar daga bayansa Suka juyo dukkaninsu.


Kuka takeyi sosai duk iya qarfinta Saidai sbd Rashin qarfin jiki da azabar yunwa data gama cinyeta yasa kukan baya sauti sai sheshekarta da ake gani.


Sakin sandar tayi tareda durqusawa a gabansu cikin tsananin kuka da dasashiyan murya tace"


Dan Allah karku kashesa wlh shikadai gareni shikadai ya ragemin.


Kallonta Sukayi a sheqe Banda Zaki dayaji nauyinta ya qaru akansa sbd tausayinta dakuma kasancewarta mace budurwa.


Rage hargitsin fuskarsa yayi Saidai Bai saki fuskarba Kai tsaye yace"


Get up.


Tashi tayi ahankali batareda takalli fuskarsaba sbd haydar shine abinda zuciyarta take azabtuwa akai.


Ina mum dinku???


Shiru tayi hawaye na gangaro Mata sbd kunyarma fada takeji cewa mum dinsu tasamu tabin hankali sunyi cuku cuku sunsamu ankarbeta asibitin mahaukata ta can dilla.


Cikin hawaye tace"


Mum na asibitin mahaukata..


Ina kuke zama??


Shiru tasake na Dan lokaci kafin tace"


Gidan wasu yorbawa muke hayan daki 'daya.


Shiru yayi batareda ya kalletaba yadan sake kallon am din daidai qarasowar motar Yan ctu Suka shigo harabar gidan Babu wata wata Sukayo kansa zakin yayi musu alamar daka tawa ya Dan kalli gefen fammah din fuska daure yace"


Shiga ciki ke,shikuma zamu miqasa hannunsu su zasu horasa yadawo daidai zai fito idan Allah yasa ya shiryu.


Kuka tafashe dashi tareda rungume am din da qarfi tana girgiza Kai tace"


Am Ina sonka wlh nidai koyaya kazama Ina qaunarka Dan uwana kadawo normal muje mu rungumi qaddaran data samemu,

Dan Allah am kace kadaina karsu rabamu idan katafi waye zai zama gatana,Ni kadai rayuwata lalacewa zatayi.


Akaro na farko dayaji hawayen tausayin kansa sun sauko masa awahalce sbd yau shine yakamata yazama gatan qanwarsa Amma shima rabasu zaayi baisan wace gararin zatayi ba bayan Wanda Sukayi dawowarsu Nigeria sbd abincin cima wuya take musu.


Kuka yasaki ahankali tareda daga hannu daqyar ya riqota yana kukan tausayin rayuwarsu da iyayensu Basu Basu tarbiyan dazata cecesu ko bayan mutuwarsuba,

Basu tarbiyantar dasu kan hanyarda zata taimakesu ba ko bayan sun rasa iyayen,

Yanxu gashi sun tafi sunbarsu a duniyarda basusan ta Ina zasu fara Gina kyakkyawar rayuwaba.


Kuka takeyi sosai shima kukan yakeyi ayau Yana baqin cikin gata da Jin dadinda iyayensa suka basa Basu tarbiyantar dashiba gashi shima yanxu baisan yazai fuskanci tasa qaddararba bare yimusu addua,

Tanaji tana gani aka tafi dashi tun a nan suke dukansa cikin Rashin Imani kosu Saida jikinsu yadanyi sanyi musamman sbd tausayin fammah sbd sunsan Yaya soyayyar 'yan uwantaka take komai lalacewarka kuwa sbd Suma sun Dan yanda suke qaunar junansu tun suna a barbadensu kuwa.Kasa hakuri nadey dake Palo tayi ta fito da gudu tayo gurin fammah din sbd itama kukan takeyi sosai sbd kunci daya lullube zuciyarta na tarwatsa musu rayuwa duk da tasan Suma sun tarwatsa ta wasu Amma data barsu da Allah to tabbas shiyasan irin sakayyar dazaiyi akansu Amma gashi yanxu taje tadauki zunubin daba nataba sbd itama sai Allah yakamata da zambar datayi musu cikin aminci tayi amfani da yarda da so ta lalata musu rayuwa.


Rungume fammah tayi tana sake sakin sabon kuka sbd tabbas ta tabbata itace keda haqqin duk abinda yasamu fammah arayuwa.


Cikin gida tashigo da ita har cikin bedroom dinta tasa fadima takawo Mata ruwa da abinci Amma Sam fammah takasa ko kallon komai sai kukan tausayin Dan uwanta da irin rayuwar dazaiyi hannun Yan drugs ta azaba da ukubar rayuwa.


Itama nadeyn shiru tayi cikin tausayin am dana fammah sbd tabbas ba laifinsu bane tarbiyar da nasu iyayen Suka dorasu akai kenan.


Har Rana tana fama da fammah daqyar tasamu itada iya talatu sukai Mata nasiha ta daukan qaddara akan ta mayarda hankali tayita yiwa Dan uwanta adduar Allah yasa ya samo canjin kyakkyawar rayuwa acan din tareda yiwa iyayenta adduar rahama da yafiyar ubangiji.


Wanka nadey tasata tayi tabata Kayanta tasaka tasata tayi sallah takawo Mata abinci da kanta ta zauna ta ringa Bata taci abincin sosai tabata maganin ciwon Kai tace ta kwanta tayi bacci.Kitchen takoma ta hada masa simple thai salads da white rice ta hada a wani openwood basket Takoma daki tayi wani wankan ta saka dark grey fitted Arabian gown ta saka half hijab da iyakacinsa wuyanta Wanda ma na baby z ne da kawu ya siyo Mata su doxin guda kala kala Wai jikarsa bazata takura karatu cikin gida ita kadaiba da kansa yasata islamiyar anguwar shike kaita shike daukota suna tafe a hanya riqeda hannunta suna fada 

kullum haka suke zuwa da fada su dawo da fada gashi ya Hana asata ta nesa da gida babba yace aa bazai dauki dukaba gwara nan kusa suna dukanta zaikama hanya yaje yaji cikakken bayani Kuma duk malaman yasansu a gabansa Suka tashi yasan uwayensu tsaf zai tariyo musu asalinsu idan Suka Dakar Masa jika sabanin can idan ankaita dogon turanci ma bazai iyaba bare larabci da yanxu alee idi yace sufara zaman karatun tsakanin magriba zuwa ishai shinefa mal zailani ke musu yanxu Kuma ba laifi suna ganewa Dan kuwa dama suna danda ilimin addininsu dama nemane ya Hana karatun.Batai knocking ba ta bude qofar tashige tareda rufowa ta nufi dining ta ajiye abincin ta shiga kitchen ta dauko ruwa da lemon mix dinsa da baya rabo dasu ta ajiye a dining din tareda plates da cup duk saidata gama jeresu kafin ta nufi bedroom dinsa tana Dan dafe gabanta dake bugawa sbd abinda ya faru yau da safen.


Kai tsaye tashiga bedroom din saitaga da Dan duhu kadan sbd komai a kashe yake.


Gadon ta kalla tagansa kwance Yana bacci dagashi sai dogon wando Babu riga a jikinsa tabi jikin nasa da kallo tanajin 'yar fargabar yanda zata ringa fama da wannan maji qarfin sbd jikinsa a bude yake alamar qarfi gashi haryanzu yakasa daina geaming shiyasa muscle dinsa ke sake budewa.


Cikin sanyi ta zauna bakin gadon tareda dafa kansa ahankali ta tana shafawa tareda Dan sakar masa iskan bakinta me dumi a kunnensa.


Wata irin kasala ta sakar masa da hakan datayi Saidai Kuma zuciyarsa har lokacin radadin alaqarta da am yakeji ya tsuke fuska batareda ya bude idanuwansa ba yace"


Kije banason hayaniya please.


Wat???""""tafada cikin tsananin mamaki da haushi.


Zatai magana ya bude idanuwansa ya Dora akanta take takasa maganar tafara rawar murya tana inda inda 


Ganin yasake zuba matasu gasu da alamar baccin dake cikinsu yaqara sauyasu taji duk duniya Babu abinda tafi son kasancewa dashi yanxu kamarsa

Tanason narke masa yadan lumshesu yasake sauke Mata take ta miqe jiki amace ranta na zafi ta fice tana ayyanawa aranta bazata sake dawowaba saiya nemeta da kansa.

#MAMUH._ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee44_*

Tana komawa Kai tsaye daki tashige ta kwabe hijabin ta zauna bakin gadon tareda dafe kanta tana Jin kamar ta fashe da kuka.


Yau da itama 'yar uwarta nanan data Bata shawarar yazatayi sbd batasan yazata iya handling Zaki ita kadaiba ba shawara.


Dataji takasa sake miqewa tayi ta nufi gaban wardrobe tahau cire rigar tanajin damuwa sosai cikin ranta.


Wata Morocco gown tasaka Mara nauyi ta zo gefen fammah data samu baccin wahala ya dauketa ta kwanta tana mayarda hawayen dake ciko idanuwanta.


Sam batasan meyasa yanxu jituwa na neman qaranci tsakaninta dashiba.

Ahankali ta furta"


Allah yaji qanqi zainab yasa aljannace makomarki.


Tun tana tunane tunane har baccin qarfi da yaji yayi gaba da ita.


Sai yamma ta farka kusan lokaci daya da fammah nan Suka miqe atare nadeyn na 'yar miqa da hamma tace"


Fammah ya jikinki?

Hope you're feeling ok now??


Kallonta fammah tayi tareda qoqarin maida hawayen dasuka ciko idonta ta bude baki ahankali tace"


Alhmdllh I'm fine now.


Sake kallonta nadey tayi cikeda tausayi tana tuno gata da Jin dadin da fammah ke rayuwa aciki.


Matsowa tayi ahankali tareda kamo hannun fammah din cikin kulawa tace"


Fammah insha Allah life will become colourful again idan kika rungumi hukunci na qaddaran da Allah ya doro Miki.


Akaro na farko ta qaqalo murmushin yaqe tana qoqarin sake sakawa kanta da zuciyarta nutsuwa yace"


Allah yabani ikon jurewa nayiwa familyna adduar yafiyan ubangiji.


Amin suka furta kusan atare suna kallon juna cikin qoqarin sakewa da junan kamar da can.


Fammah dince tafara miqewa tana cewa,


Bari nayi alwala lokacin sallah ya wuce Muna bacci.


Da kallon tausayi da Jin nauyi nadey ta bita tanajin zafin yanda fammah din Takoma Kuma itace da babban kaso akan mayarda rayuwarta hakan.


Tana tunani har famman ta fito itama ta miqe jiki ba qwari ta fada toilet din tayo alwala tana fitowa gefen fammah ta tayarda sallar itama.Tare suka fito palon itada fammah tajata har kitchen tana qoqarin ganin tasakata tasake jikinta da gidan sosai sai niyar datayi ta Dora fammah din akan rayuwarda zata koyi komai na bangaren addini Dana zaman rayuwa tareda koyan ayyuka.


Tuwon semolina Suka tararda fadime na kwashewa cikin Leda takalli tuwon tana cewa"


Abincin da uncle din baby z yakeso.

Shine yace adafa masa?


Ta fada tana kallon fadime cikin Rashin Jin dadi.


Aa alhajine keson tuwon masara shine akeyi Masa wannan din.


Jiki a sanyaye tace"

Ok.


Kallonta fammah tayi tana Yaba sa'a irinta nadey.,


Bebiyar datayo rayuwar qunci da Rashi da maraici abaya Amma yanzu itace cikin gata da niimar ubangiji Wanda sukuma dasukayo rayuwar gata,yanci,Jin dadi da mulki yanzu Kuma sune suke neman taimako da dauki daga waccan bebiyar,


Ayau namijinda kowace macen datasansa ke fatar ganin yasota Ko kulatama shine bayaji baya ganin kowa agabansa sai nadey.


Ya Allah ka gyaramin rayuwata koban samu gata da niimar nadey na nasamu wadatar ilimin dazai sadani da rahamarka,iliminda zai Kai rahama kabarin mahaifina da rayuwar mahaifiyata data Dan uwana.


Cikin qoqarin kawarda damuwarsa aranta nadey ta nufi fridge ta dauko fruit mix dinda tayi masa dazu da niyar kaimasa da yamma ta dire gabansu tafara Sha tana cewa"


Fadime Gama kwashe tuwon nizanyi miyar nida fammah.


Fammah datai zuru tana kallonsu kamar Mara lafiya takalli nadeyn ahankali Jin abinda tace sbd ita Sam ko ruwan zafi bata taba dorawaba arayuwarta bare girki.


Murmushi nadey tasakar Mata tana daga Mata tace"


Karki damu I'm here,we can do it right????


Kai ta daga Mata ahankali tana qaqalo sakin fuskar dole.


Mix din ta takurata sukasha abinsu sosai suna cikin Sha Kiran JJ yashigo wayarta ta kalli wayar tareda kallon fammah data mayarda hankali gurin jujjuya mix din tanasha ahankali.


Daukar wayar tayi tareda saka handsfree tace"


Yes dady j?


Nadey Kinga Dan Allah ki taimakeni da kawu wlh ya daga hankalina da Kira Wai adawo da baby Wai islamiyya kar a wuceta,Kuma malamai na duka idan anyi fashin zuwa and abubuwa da yawafa ya bayar Ni yau akainama ya qarasa sauke fadan dazu da safe.


Dariya tayi cikin jinjina fada irin na babanta tace"


Dady kawai kakirasa ku daidaita wlh Ni kasan dama a qule yake damu Ina magana zaice mubar Masa gidansa mukoma gurin dad.


Bari nakirasa gskia Ni Zan canza Mata makaranta sbd wancan da kawun keso tayi sunyi lungu da yawa.


Ba ruwana nidai ka nemesa da kanka and pls kar ko sunana yafito aciki wlh akaina zai sauke haushi da fadan.


Kamar daga sama sukaji fammah cikin tsananin sanyin murya tace"


Please kudawo da ita nan I want to see haydars look alike.


Kallonta nadey tayi sbd hakanan zancen yadan kayar Mata da gaba sbd sanin son haydar din ne yasa takeson ganin yarsa.


JJ kuwa tsit yayi tareda son sake Jin muryan sbd Jin yanayin yanda akayi maganar kamar da shagwaba ciki.


Jin yayi tsit yasa fammah din sake cewa"


Please bring her back.


Jin baice komaiba yasa nadey gyaran murya tana kallon wayar tace"


Fammah ce ke mgn dady j.


Wat???yafada ahankali tareda Dan tsuke fuska duk da basa ganinsa Yana daqile wayar sbd takaicinda haka kawai ya kamasa,

Shifa ko gaisuwa baya fatan tasake hadasa da 'daya daga cikin dillas din nan har abada baida wani sauran abinda ya rage yayi dasu.


Su kuwa duka su biyun da ido sukabi wayar kowanne da mamaki.


Mayarda sauran mix din tayi fridge ta bude freezer ta fito musu da Naman rago dayayi qanqara tana cewa"


Ok fammah let's start our soup sbd mugama da wuri.


Ahankali tafara aikin fammah na zaune ta rafka tagumi tana kallonta ita yanzu komai na nadey a burgewa take kallonsa.


Saida aka fara Kiran magrib Suka gama komai fadime tagyara kitchen din Suka fito Suka dawo daki.


Wanka Sukayi tareda alwala sukai sallah suna idarwa tayi qaramin adonta cikin straight Vandana gown fammah kuwa doguwar riga ta zumbula ta bacci wadda take ta nadey din.


Daqyar fammah ta iya daurewa taci abincin sosai tareda nadey a dining sbd gidan Basu wani Saba cin abinci atareba tun da can shiyasa ko yanxu kowa daban daban yakecin abincinsa.


Suna cikin cin abinci suka jiyo muryansa Mai fadar da gabansu duk su biyun yayi sallama qasan maqoshi yashigo palon Yana sanyeda baqar jallabiya data qara fiddo haskensa sosai Saidai fuskar nan tasa a tamke take kamar ko yaushe ba wani Wasa.


Ko inda suke Bai kallaba ya nufi tsakiyar palon Yana gaisawa da iya talatu dake zaune tana kallo itada fadime yace"


Ina kawu yakirani Yana nemana.


Kafin iya talatu tayi mgn saiga kawun yafito daga palonsa Yana daure fuska shima ya zauna tareda sake tsuke fuska yace"


Nakira jabeeru tun dazu akan yadawo da zainabu akan islamiyarta yaqi kawota sbd ya nunamin shine ubanta ko?

To ku sani matuqar Bata dawoba duk barmin gidana zakuyi Dan Banga amfanin aje gardayeba tunda kun karbe yarku.Cikin sauke murya yace"


Kawu kayi hakuri wlh Ni banmasan ya kukayiba Amma aini to Babu ruwana acikin zancen tunda ka kirasa ainasan zai kawota ko zuwa gobene...


Goben idan yakawota uban waye acikinku zai bita yayiwa malamai mgna kar adaketa.


To kawu ko yanzu yakawota ai Dole sai goben zataje tunda yaudai Kam dare yayi ayi hkr.


Qin sake tankawa kawu yayi ya kalli iya talatu Yana cewa,


Talatu bani abinci kinji.


Hkr zakin yakuma basa kafin ya juya ya fito.


Kiran JJ yayi JJ yaqi dauka sbd yasan ko maganar meye bazai wuce ta maido baby z ba.Bayan fitarsa wani irin haushi ya maqale Mata a wuya yanda yashigo ya fita ko inda take yaqi kallo.


Miqewa tayi ta wuce daki babanta yabita da muguwar harara yanajin kamar yace subar gidan adaren kowama ya huta.


Zama tayi tana duba wani email da Jasmin tayo Mata forwarding ta laptop dinta har akayi Kiran ishai ta aje tayi sallah tana gamawa Bata sake bi takan komaiba tayi kwanciyarta tana Jin kamar tayita rusa kuka.
Tunda yagama komai yake zaune Yana jiran shigowarta Amma shiru yakalli agogo akashi na ba adadi Yana sake daure fuska sbd takaici,


Tun Rana baici komaiba Yana jiran tazo takawo Masa Amma shiru Kuma Dan raini tayi laifi shine take sakeyin wani laifin akan wani.


Kasa hkr yayi ya dauki wayarsa ya Danna kiranta Amma wayar Bata zuwa.


Sake Kira yayi still not reachable.


Aje wayar yayi tareda rintse idanuwansa cikin damuwa da takaici ya miqe yashiga daki kawai ya kwanta Yana sakin siririn tsakin takaicin shiririta da Rashin tunani irin na Mata.Dagashi har ita daqyar sukaga wayewar gari tana Gama breakfast ta shirya tacewa fammah ta shirya suje su siyo kayanta na sawa.


Cikin riga da skirt na red super Sheraton Mai golden kadan ajiki tasakata babbar kimono jallabiya akai tareda yin rolling gyalen jallabiyan kawai ta dauki handbag da key din motar Kai baby z school wata 'yar eclass3033 2019.


Fammah kuwa doguwar ash jallabiya tasaka sai qaramin gyalen jallabiyan Suka fito bayan sunyi bankwana da iya talatu akan saisun dawo.Geaming yagamayi dagashi sai wasu riga da wando na Nike marasa hannu sai hularsu ya hada gumi sosai musamman sbd tsananin bacin Rai da tsananin kewarta daya kwana da ita yasa yakeyi yaqi tsayawa saiga Kiran JJ.


Dauka yayi tareda dakatawa ya miqe Yana cewa"


Saida kagama hadani da kawu kake kirana yanzu.


Dariya JJ yayi tareda cewa"


Gani Nan Nazo ai bawa kawun hkr da kaina.


Fitowa yayi harabar gidan daidai shigowar motar JJ ciki Suma daidai lokacin suka fito kowacce na ganinsu ta daure fuska.


Ita fammah hakanan taji Rashin Jin dadin abinda JJ yayi jiya a waya da akace itace tasan cewa yanajin haushinta da takaicintane sbd ita Dilla ce shiyasa ta dauke Kai tareda Dan kame fuskarta data gansa haydar ma Sam ko ganinsa batason yi yanzu sbd kallon datake masa a mijin nadey Wanda itama tata zuciyar haryanzu tana sonsa.


Nadey kuwa ganin Zaki yasata Dan daure fuskarta duk da tsorone fal aranta Dan taso su fice batareda yasan sun fitarba.


JJ na fitowa motar shima kallo daya tayiwa gefenda suke sbd fammah sai baisake kallonsu ba yace"


Nadey Ina zaku this early morning????


Mota ta nufa tana tsuke fuska zatai magana sukajisa yace"


She's goin no where.


Kallonsa fammah tayi ya kalleta shima fuska a daure take gabanta ya fadi tafara neman rikicewa Kai tsaye yace"


Ina zaku??


Kallon nadey data sake daure fuska cikin takaicinsa na yanda ya tsare fammah da ido gashi duk muscles dinsa a bayyane tace"


Dama she's taking me to....


To where????yafada cikin 'yar tsawa sbd ransa dashima yagama baci sbd kallo daya yayi Mata yaji zuciyarsa na quna da kishi.


Kayan sawa zata siyamin I don't have any clothes....


Wani mugun kallo ya watsawa nadeyn data fara saduda sbd ganin fushin dake kan fuskarsa ta dauke Kai da sauri tana Dan gyara tsayuwarta.


Kallon JJ yayi Kai tsaye yace"


JJ Kai fammah din asiyo Mata kayan wannan Kuma let me put some sense into her"""yafada tareda fizgo hannun nadiyar ya nufi part dinsa da ita.


JJ kuwa kasa motsi yayi Yana takaicin wannan yawon banzan dazai fitayi bayan shi gurin kawu yazo Dan yasan idan baizoba yau Babu abinda zai Hana kawun Isa can gidan.


Batareda ya kalleta ba ya nufi mota ta biyosa abaya jiki sanyaye sbd taga yanda qiri qiri Rashin Jin dadi ya bayyana a fuskarsa.


Jiki ba qwari tashiga motar yaja da speed yabar gidan.


Suna shiga palonsa ya saketa ya juyo da wani irin fushi zaiyi magana cikin tsananin bacin da sauri ta hanasa ta hanyar fadawa jikinsa ta qanqamesa sbd tsoron karya mammareta.

#MAMUH._ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_kaimin halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_


*08030811300*

*07067124863*


*_Mamuhgee45_*

Kasa wani dogon motsi yayi sbd yanda ta cukuikuye acikin jikinsa sbd tsoro da shakkarsa Daya bayyana atareda ita Tana sake cusa kanta cikin  jikinsa hannuwanta na Dan rawa da qafafunta.

Rintse idanu yayi ahankali yanajin dumin hannuwanta na kashe duk wani fushi da bacin ran daya shiga lokaci daya,


Ajiyar zuciya ya sake ahankali tareda kasa cewa qala sbd jikinsa dake neman saki ya saka hannuwansa biyu ya dagota ahankali yana kallon fuskarta cikin yanayi na nuna ikonsa yana basarda yanayinda sonta yagama jefasa ya kalleta da idanuwansa dake sake daga hankalinta cikin basarwa da iko yace"


This should be the last time dazaki sake gwada irin hakan,

Next if you try me again saina karya qafafuwanki da hannuwanki and I mean it kinajina ko???


Dan dagowa tayi da kanta ta kallesa Tana sauya fuska kamar zatayi kuka ta juya cikin haushi zata bar gurin ya fizgota saidata tsorata takallesa da sauri.

Cikin kallon cikin idanuwanta yace"


Ina mgn shine Zaki wuce kina fushi???


Hawayen datake riqewane ta bari Suka gangaro mata ta kallesa tareda sake barewa da hawaye tace"


Naji bazan sake futan ba shikenan Ina?


Yanda tayi yasa jikinsa yin sanyi yaji ransa na dacin yanda take tsiyayo hawaye.


Fuskarta ya quraw Ido yanajin dacin ransa na qaruwa.


Ahankali ya sake jawota jikinsa sosai yana riqo hanuwanta cikin nasa yace"


To this guntun hawaye da akeyi sbd a gasani ya Isa haka its killing me inside so please ya Isa Nima naji bazan sake fada haka sosaiba ok???


Wasu sabbin hawayen ta sake matsowa cikin son sake rikitasa tace"


Yafi shekara shida da kake cewa saika karyani nidai na.....


Hannu ya Dora kan bakinta yana kallon cikin qwayan idanuwanta ya dauke gira Daya yana sakin murmushinda bai Gama kama fuskansaba yakai bakinsa kunnenta ahankali yace"


Zan karyaki Amma ba irin wancan karyawanba wannan is very special karyawa irin na lokacin samun cikin baby z.....


Zaro Ido tayi da qarfi tareda turesa Tana sakin murmushi da gudu zata tsere ya damqota tareda dawo da ita yace"


Heyyy miss Noah aikin Riga kinshigo sashenki kenan keda shiga can Sai idan kinje gaidasu kawu Kuma sbd inason raba fadan kawu da dad akan baby z soon ta hanyar Basu kawo musu wani Sai araba gardama and this time Zan ringa ban ruwa ga shukatane Dan tayi kwari da kyau tasamu Ingantacciyar yalwa....


Cikin ihun kunya Tana qanqamesa tace"


Please stop mana ko nafadawa babana what your plans are na zaka lalata Masa 'ya.


Dariya yayi tareda dagata sama yana cewa"


Basaikin fadaba nida kaina Zan nuna Masa tunda ke kikeson a rikitasa yana zamansa.


Aa Allah kasan Kaine kakeson neman maganarsa idan baka dainaba mijin baby z zai ramawa babana wata Rana.


Cakularta yayi tayi zillo ta fado daidai kan gado Tana dariya Tana shafa gurin tace"


Mena Maka to ai gskia ne nafada daga bawan Allah yaji qan ka yabaka yarsa Sai neman rabasa da zaman lafiyarsa kake nidai daga yanzu bamai sake tabamin uba ya hanasa sukuni.


Rigar jikinsa ya zame yana cewa"


Hmmmn.


Jikinsa ta kalla ta Dan juyar da Kai Tana Jin gabanta na Dan faduwa kamar tsoro zai kamata.


Saukowa gadon tayi Tana zame kimonon saman kayanta tasaka closet Tana Dan Fara gyara dakin duk da baiyi komaiba Amma amatsayinta na matarsa gari ya waye ya tashi Dole ta gyara Masa shimfida.


Wanka ya shiga yana sake gyara daurin towel dinsa.


Yana shiga ta saki ajiyar zuciya ta Dan kalli qofar bayin tareda sake ajiyar zuciya kafin taci gaba da aikin gyara dakin.
Tafiya sukeyi cikin motar Babu Mai cewa komai

ita dai fammah sbd a takuren datake ko wani qwaqwaran motsi batayi saima Jin datayi gabaki Daya fitar ta fita aranta gida kawai takeson komawa gashi batason ko mgn tayi Masa ganin fuskarsa a daure ya mayarda hankali yana tuqinsa.


Wani qaton mall kawai ya kaita batareda yace mata komaiba yayi paking ya kashe motar ya fito ya tsaya yana duba wayarsa fuskarsa a Dan sauyayyan yanayi ba laifi sbd ganin zasu shiga mutane.


Share siraran hawayenta tayi cikin tuno rayuwarta ta baya da irin gatanta Amma sauyin rayuwa yasa yau itace akewa alfarma wulaqantawa.


Fitowa motar tayi tadan saci kallansa tareda bude Baki cikin sanyin murya tace"


Ko zamu barshi mu koma gidane karna takuraka bansaniba ko kanada abinyi.


Juyowa yayi ahankali ya watsa Mata wani irin kallo dama itama din shitake kallo idanuwansu Suka shiga cikin na juna Suka qurawa juna Ido akaro na farko suke yiwa juna kallon tsaf.


Itace kunya tasata dauke idanuwanta tareda sauke Kai Tana kallon wani guri.


Shima juyarda Kai yayi cikin basarwa yayi gaba yana cewa"


Muje.


Ba laifi da kansa ya jidar Mata Kaya sbd ganin takasa sakewa shikuma ya gaji da wannan dolen komawa yakeson Yi shiyasa kawai yafara daukar Mata komai yasamu na buqata.


Dayazo gurin akwatina baiyi tunanin komaiba ya zabi wani simple set masu kyau da tsada masu guda hudu Kuma duk bawani girmane dasuba.


Aiko nan yacigaba da zabar komai dayazo kan undies ne ya fuske tareda tsuke kyakkyawar fuskarsa ya fidda wayarsa yana dubawa bai kalletaba yace"


Kiyi sauri kizaba inada gurin zuwa time yakusa.


Matsawa yayi daga gurin tabi bayansa da kallo Tana jinjinawa kanta da irin  tunaninda zuciyarta ta jeho Mata najin inama tanada aure wainnan abubuwan Suka faru da rayuwarta Bata gantale hakaba,

Da koyayane Tana cikin rufin asiri bazata Zama Yar rabe rabe ba ko talakane dashine rufin asirinta take taji so da shaawar aure sun shigeta Amma waye zai sota ya amince ya aureta Tana Yar Wanda sunansa yagama baci a duniya sbd zalunci da kashe Rai ba bakin komaiba.


Kukane da batasan da zuwansaba ya kubce Mata jikinta na wata irin rawar tashin hankalin shikenan iyayensu sun Bata musu rayuwa suntafi sunbarsu da mummunan tabon rayuwa.


Da sauri ya juyo ya kalleta Jin kukanta yaga yanda jikinta ke rawa sbd sheshekar kukanta take yaji jikinsa yayi sanyi tausayinta ya kamasa sbd tabbas yasan iyayensu sun cutatardasu ta wani fannin.


Matsowa yayi bayan ya rintse idansa ya fitarda numfashi mai sanyi ya Dan kalleta tareda zaro handkerchief dinsa ya miqa Mata yana kallonta qasa qasa yace"


Meyasa zakiyi kuka cikin nutane sbd jawo kallo akankine kikeyi so please stop this right now and wipe this now"" yafada yana kallon hawayenta da cikin idanuwanta data dago ta kallesa tayi saurin janye idanuwanta sbd kasa hada Ido datayi dashi hawayenta na qaruwa.


Ganin takasa daina kukan sbd yariga yazo Mata yasa yabata key yace Takoma mota zai biya yazo.


Tattara kayan akayi guri daya aka Fara aikin hada kudinsu kusan minti arbain kafi aka Gama ya biya aka fiddo da kayan aka zuba bt da sit din baya sbd bt din bai dauke duka kayan.Kasa tayarda motar yayi Saida taji shiru ta dago jajayen idanuwanta ta kallesa ya Dan ya mutsa fuska yace"


Kinsan bazan kaiki gida a wannan yanayinba nadey will feel bad seeing you like this.


Kallonsa tasakeyi da sauri jikinta na sakeyin sanyi,

Nadey taji Dadi tayi Sa'ar rayuwa kowa na sonta yanason farin cikinta.


Share hawayenta tayi ahankali ta furta"

sorry.


Ajiyar zuciya yasauke Jin yanda tace sorry din ya tayarda mota sukabar gidan.Koda suka dawo shiru sukayi dukkansu cikin motar tsawon mintuna kafin ta Dan dago ta kalli gefensa vata kalli fuskarsa tace"


Thank you.


Daga Mata Kai yayi Shima batareda ya kalletaba.


Budewa tayi ta fito Shima fitowar yayi tareda bude boot ta dauki wasu kayan tayi gaba yabi bayanta da kallo yanda take tafiya kamar zata karye sbd sanyin jiki da damuwa

Bata ankaraba tayi tuntube zata Fadi taku biyu yayi ya tareta ta 'dan fado jikinsa.


Akaro na farko dayaji wani Abu a taba jikin mace sbd duk turawan dayake huldar aiki dasu yana shaking hands dasu wasuma har hugging Amma baitaba Jin komaiba Sai yau yaji wani irin shock da kasala lokaci guda.


Itama jitayi tasake loosing balance gabaki Daya jikinta yasake sakewa.


Kawu dake Shirin fita yana sanyo kai harabar gidan yayi sauri zaro idanu tareda sake fitowa Yana quresu da kallo daidai lokacin Suma su nadey sun fito Yana riqeda gefen qugunta suna dariya Yana sake riqota Yana Mata rada Tana kamo wuyansa dayayi Mata tsawo Yana sake dagata.


Juyowa kawu yayi gefensu Suma Yana kallonsu kamar zai rusa ihu 

Yasake maida idanuwansa kansu JJ da kamarma sunfi su nadeyn shagala cikin masifa da daga murya yace"


Kowane shege ya tattara yazo yabarmin gidana.


Da sauri su nadey suka saki juna sbd sai alokacin suka Ankara dashi suka ga halinda jj da fammah din suke.


Nadey tayi saurin Isa ta riqo fammah din sai alokacin suka saki juna nadey ta riqeta zasu shiga ciki kawu yace"


Kudawo Nan kafin na karya qafafuwanku masu kama da takandar rage hardai ke me kama da jikar ifiritu Ashe kin koyawa fatimar rashin arzikinki gashinan su arana tsakiyama Kuma Dan tsabar anrainani ko aure Babu....


Cikin sauri jj yace"


Kawu bafa yanda kake tunani bane kayi hakur.....


Jabiru kadaisan a qule nake dakaiko?

To kayimin shiru agurin ko wlh na fusata na daura muku aure ayau saiku qarata can kaida ita

Kema Ina ganinki ta arziki Ashe kinkoyi rashin munyarsu..


Girgiza Kai fammah din tayi da sauri zatai mgn yace"


Zakimin shiru agurin kosaina fasa bakinki Mai kama da qofar kasuwa.


Zaro idanuwa famman tayi da qarfi tareda cewa"


Kasuwa????


Dariya suka danne sbd sukam sunsan halin kayansu tsaf itace sabuwa a abin.Kayan menene nake gani harda akwatina???


Kallon kayan jj yayi yace"


Kayane aka siyo Mata.


Lefenka ne kenan ka hado Babu sanina sbd anrainani ban isaba kokuwa shi aliyun shine yabaka dama to ai ita fatiman a gidana take Dan haka a ikona take bazan bayarba.


Da sauri Zaki ya matso Yana cewa"


Yi hkr kawu dama Ina zaayi wani Abu bada izininkaba kawai kayan ne yasiyo tukuna.


Wani banxan kallo jj ya jefawa zakin Yana cewa"


Sarki karka sake hadabi da kawu mana,

Wlh kawu dama Babu wani wannan mgnar kayane na sawa batada aka siyo Mata thats it.


Kallonsa fammah tayi akaro na farko taji wani na rejecting dinta Kai tsaye duk da tasan he's right saidai yanda yayi mgnar cikin bayyana rashin sonta a fili.


Cikin wani irin yanayi ta bude Baki tace"


Baba Babu komai a tsakanina dashi ya taimakenine da suturar dazan saka ne kawai koba komai mezaiyi da 'yar da akewa kallo da laifin iyayenta,

Bashibama Babu Wanda zaiso aurena sbd karya auri 'yar mutanenda akewa kallon azzulimai,

Nasani Babu Wanda zai taba shaawar Sona bare aurena Dan haka kuyi hkr dukkaninku Nima ba laifina bane....


Kuka tasaki tareda juyawa ta shige ciki Tana toshe bakinta.


Sanyi dukkaninku jikinsu yayi musamman shi jj ya juya jiki ba qwari zai bar gurin kawu yakira sunansa.


Dawowa yayi ya tsaya yana sauke Kai.


Cikin nutsuwa kawun yace"


Jabiru idan nine zanmaka zabi da aure kamar yanda nayiwasu Zaki to haqiqa na zabar Maka Fatima sbd jahadi zakayi ka tallafi rayuwarta marainiyace zaka samu tarin lada da kwanciyar hankali insha Allah.Baisoba har cikin ransa Amma ayanda kawun yake uba agaresu bazai iya musawaba,

Sarkima yayi Masa zabi ya daura Masa aure bai musaba bareshi.


Ajiyar zuciya ya saki a boye kafin ya dago ahankali yace"


Nagode kawu Allah yaqara girma da nisan kwana.


Dafasa Zaki yayi cikin basa qwarin gwiwa yace"


You won't regret this my magaji I promise,

Bakasan yanda auren dolen kawu yakeda Dadi bane zakazo yiwa kawu godia Ina Nan.Wani kallon takaici kawun ya jefawa zakin zaiyi mgn jj yayi saurin cewa"


Yi hakuri kawu.


Jinjina Kai yayi zaiyi mgn saikuma ya fasa ya wuce Yana cewa"


Bazaa dauki lokaciba tunda baa buqatar wani abin inaga kufara Shirin Nanda wata Daya dai zanfadawa babanku.

#MAMUH.*_Mamuhgee46_*

Kamar wani mugun labari haka ya dauki zancen auren Amma Kuma Daya tuna kawun ne yayi Masa zabin saiyaji zuciyarsa ta kwanta da alamarin saidai baisan ta Ina zaifara rayuwar iyali da fammah din ba.


Tareda Zaki suka fita zuwa ma'akatar dasuka bude gini guda sbd 'yan daba irinsu a da wadda aka budeta sbd su kawai Dan tallafi da yancinsu na bawa kowa jarin irin sanaarda zaka iya idan ka shiryo aka bude tsohon case dinka sune ke tsaya Maka da haka Allah yataimakesu abubuwan dabanci suka Fara ragewa yan ta'adda nata shiryiwa wasu Kuma ana tallafa musu suna komawa makaranta masu shaye shaye kuwa idan yayi tsamari gurin yan drugs suke muqasu da sharadin ba azaba Mai tsanani shekara gudane idan Allah ya taimakeka ka daina kenan har abada wasu ko shekarar basayi sun fito sun daina.Cikin dakinsu kuwa nadey ce tafadawa fammah abinda baban yace ta Dora da cewa"


Kiyi hakuri nasan baba zai fahimta idan har bakyaso,

Zaiyi fada sosai amma daga baya zai hkr sbd bayada riqo ko fushi irin na wasu iyayen,

Baba haka halinsa yake saidai shi haka tasa qaunar take idan baya Miki fada to bayasonki sbd shi abinda yakesone kawai yake sawa gaba da fada komai kayi laifine.


Girgiza Mata Kai fammah tayi cikin yanayi na sanyi tace"


Akaro na farko a rayuwata da want yayi min abinda mahaifine kawai keyi,

Banda Mai tsayamin,

Banda Wanda zankira nawa saiku,

Baba yayimin abinda zaiyiwa 'yarsa konace abinda yayiwa 'yarsa Wanda Nima Ina yiwa kaina shaawar samun Ingantacciya,wadatacciya da kwanciyar hankalin rayuwan aure kamar naki to mezaisa naqi zabinda Wanda yadauki matsayin uba aguna?

Na amince da duk zabi da hukuncin baba akaina kowane irine.Murmushi nadey tayi tareda tausayinta sbd Tana hango maraicin dake cin fammah din atareda ita sbd fammah din mutum ce Mai tsananin so da qaunar familynta.

Tasani kewar am haryanxu Tana cinta saidai tamayarda hankali gurin yimasa addua tareda nemawa iyayenta gafara.Ahankali nadey itada iya talatu da fadime suka bude akwatinan suka zuzzuba kayan aciki komai Kuma ya shige abinda Babu daga baya nadeyn tace zataiwa jj din magana saiya qaro ko yabayarda kudi su siyo.
Ana Kiran magrib ta fito kitchen daukeda basket data jero semo dinda tayi Masa da fresh vegetables soup sai lemon mix da Babu sugar ko kadan aciki sai Zuma kadan itama.


Wanka tayo tareda alwala Tana fitowa sallah tafarayi kafin tafara shiri cikin wata doguwar royal blue straight D&G rubber fab gown.


Wani hot red lipstick tasaka na oriflame akan lips dinta sai powder kadan da eyeliners shima kadan baama ganewa ta sake gyara gashinta ta feshesa da hairspray ta dauresa tsakiyan Kai.


Bold hot red lipstick dinta shine yafi daukan hankali sbd yanda ya zauna.


Shape dinta da rigar tabi ta lafe fammah ta kalla Tana ayyanawa aranta itama saitayi haka zata samu zuciyar mijinta da kyau idan sukai aure sbd har cikin ranta ta karbi auren sbd ta tabbata jj zai inganta rayuwarta tabata kyakkyawar rayuwa so ita kam ta karbesa hannu bibbiyu tunda haydar yagama yimata nisa gwara ta rungumi abinda ya sawwaqa gareta sbd inganta rayuwarta karta tsaya hange rayuwar batada tabbas afterall Zama cikinsu shine rufin asirinta da farin cikinta,


Asalinsu basuda alaqar jini kusan dukkaninku zuriar gidan,

Aminci ne da amintaka tun dagakansu baban da amininsa hakama jj dasu Dr sayyid dasu nanu Amma sun riqi junansu tamkar jini daya,

Sun maida kansu zuria daya suna qaunar junansu fiyeda komai,


Iyayenta sune silar duk wani kuka da qincinsu Amma still sun karbeta acikinsu tazama tasu haka Dan uwanta sun basa damar gyara rayuwarsa.

Batada wasu dangi nata bayansu Wanda sai yanxu take sanin dadin qauna da tattalin juna tareda sakewa da juna Wanda basusamuba koyaushe iyayensu na hidimar neman kudi kota kyau kota sabanin hakan.Murmushi yasauka a fuskanta ahankali ta tashi tazo ta rungume nadey data saka kimono da Vail saman kayan cikin farin ciki ta furta"


Thank you nadey dattiya Noah.


Murmushi nadey tasaki tareda rungumeta tace"


And wat are you thanking me for Mrs j.d Noah???


Murmushi fammah din tasake saki sbd Jin itama she'll soon be fammah D Noah.


Sake cewa tayi"


Thank you for giving me a wonderful life and family to call my own again.


Dariya tayi tareda daukan turare ta fesawa Vail dinta kafin ta juyo ta kalleta Tana dariyar farin ciki tace"


Welcome to the family to but ba amatsayin sirikaba but as new daughter of the dattiya Noah family.


Dariya sukayi dukkansu kafin ta juya ta dauki wayarta dake ringing taga dad dintane ta dauka da sauri Tana cewa"


Dad I'm really missing you Amma baba da Uncle sun hanani fita and this is not fair..


Cikin farin ciki yace"


Kyale haydar zanyi Miki maganinsa Amma Yaya kam saidai hkr duk mu duka.


Dariya sukayi itada fammah tace"


Dad kaima kana shakkar baba bare...


Murmushi Mai sauti yayi ahankali Yana tuno masifa da daru irin na yaya dattiyan su basumaga komaiba ai yayi sanyi ahakan Koda sukazo duniya yasake wani murmushin kafin yace"


Kudai kucigaba da lallabasa sauqinsa ma kuka samu shiyasa kuke Masa wani rashin Jin hardai haydar.


Wlh dad ko yanxu da dama dai Amma baba rigimane ahaka muke sonsa.


Maganar wasu takardu na wani sabon contract suka fada tafara yimasa bayani kafin tace Masa sauran bayanin suna hannun jj Dan contract din na hannunsa sbd new Noah's publications na Zurich a hannunsa yake.


Suna gamawa ana Kiran sallar ishai sai kawai tayi sallarta Tana gamawa tasake gyarawa ta fice da wayarta a hannunta.


Allah ya taimaketa Babu kowa a palon ta wuce dining ta dauki basket dinta ta fice.


Koda taje baidawo daga masallaciba ta cire kimononta ta ajiye cikin closet din dakinta dake kallon nasa ta fito Palo ta fitarda abincin ta jera a dining taje kitchen din dake palon ta dauko ruwa a fridge Tana fitowa taji anrungumota ta baya tareda sake ajiyar zuciya ahankali Yana shinshina wuyanta dake fidda qamshim wani sanyayyan oud mara qarfi ko kadan.


Aje ruwan tayi a dining tareda juyowa Tana kallonsa cikin wani irin yanga da basarwa Tana wani narkewa.


Kallo Daya yayiwa lips dinta yaji Yana neman loosing control sbd they look damn hot and seductive.


Ganin yanda yake kallon lips dinta idanuwansa na neman qanqancewa tadan motsasu kamar zatai mgn

Kasa hkr yayi ya matsota qirjinsa ya duqo da fuskarsa ya Dora nasa lips din akai tareda lumshe idanu Yana zura harshensa cikin bakin nata.


Qamshin butter lemon mint din bakinsa ya shiga hancinta take kwadayin sweet din ya kamata ta kama harshensa ahankali ta tsotsa Wanda yasashi sake matseta jikinsa Yana sake lumshe ido cikin nutsuwar dake shigarsa.


Tudun qirjinta ta sake manna Masa yasaki numfashi da qarfi Yana sake kusawa cikin bakinta itakuma Tana tsotsan harshensa dayake sarqe da nata.


Saida suka Gama shanye mint din ahaka kafin ta zame tareda Dan kallonsa taga yanda ya kafeta da ido,


Ahaka jarumine Mai bawa wasu mazan tsoro Amma ayanxu tasan yakai gabarda komai tasashi yanxu yi zaiyi ba wani dogon musu.


Wani irin murmushi tasaki tareda kama hannuwansa ta Dora a qugunta Tana cewa"


Honey come let's have our dinner abincin zai fita ranka idan bakaci yanxuba..taqarasa fada Tana yawo da hannuwanta dake kan nasa kan qugunta zuwa gefen cikinta.


Wani murmushinda ba shiri ya sabuto Masa ya ranqwafo daidai kunnenta yace"


Kawu baisan waye yake lalata wani acikinmu ba dabaice nine Mai Bata Masa 'yaba sbd wannan 'yar tasa ni Tama Gama da wuce wayona.


Wata irin kunya taji Amma saita basar tareda sake riqo kansa itama takai bakinta kunnensa saidata Fara sakar Masa wani numfashi mai dumi aciki cikin kirsa tace"


Dinner.


Kallonta ya dago yayi cikeda mamaki sbd tagama kwance duka notikan kansa.


Zama yayi tayi serving dinsa da abincin kadan sbd sanin becin abu me nauyi sosai da dare.

Lemon mix dinsa nema tasan zaisha da Dan yawa shima dama sbd kaman powerhorse yake Yana qarawa maza lfy ne.


Janyota yayi kan cinyarsa ya zaunar da ita ta ringa basa abincin da kanta idonsa na kanta tun anan tafarajin tsoro na kamata jikinta yafara sanyi duk saita saurara Tana sake sanyi.


Kallonta yayi tareda sakin murmushi Yana tunanin tasan bazata iyaba ta takalosa.


Abinci yakai bakinta ta kallesa ahankali yace"


Eat mana my beautiful bride.


Sake kallonsa tayi da sauri Tana kallon murmushin dake fita a fuskarsa taji tasake shiga Dan rudu.


Shafa fuskarta yayi har zuwa lips dinta ya shafasu tareda kallon cikin idanuwanta yace"


I love this,

And i think its driven me crazy tun kallon farko..yaqara shafasu hot red din nasake rikitasa yanajin control dinsa ba saki Amma ya daure Yana sake kallonta.


Befi ci huduba tace Masa ta qoshi ta zame ta maidai kayan kitchen tareda juye miyar a wani Plastic bowl me murfi ta rufe tasaka fridge.


Ta fito Tana tafiya cikin wani karya jiki duk da a tsorace take.


Kamo hannunta yayi yacirata sama Yana cewa"


My beautiful bride what's wrong??


Shigewa tayi jikinsa harsuka Isa bedroom dinsa ya sauketa kan gado tareda zare jallabiyarsa ya dauki waya yakira P.A dinsa daya kirasa kusan so biyar.


Waya yakeyi hankalinsa kwance Tana daga kwance Tana kallonsa cikin burgewa da shauqin sonsa.


Yana ganin yanda take kallonsa ya datse wayar tareda kashewa gabaki Daya yayo gurinta bayan ya rage hasken dakin sosai.


Ya kwanta gefenta tareda Dora kansa akan pillon da kanta yake ya jawota jikinsa tareda zura hannu ya zuge zip din rigarta ahankali Yana cusa kansa cikin wuyanta zuwa qirjinta.


Yana kaiwa qarshen zip din ya zura hannuwansa cikin rigar Wanda yasata Jan numfashinta da yayi sama kamar zai dauke sbd 'dumin hannuwansa dasuka sauka a kan cikinta zuwa qirjinta.


Jin ta dauke wuta gabaki Daya yasashi sake shigewa jikinta tareda zare rigarta gabaki Daya har qarshe ya mirginata qasa yayi Mata rumfa da qirjinsa me Fadi dake bayyane Yana Kai fuskarsa qasa ya kama bakinta yana kissing ahankali cikin sake yawo da hannunsa Daya a jikinta.
9:40am

Morning.

Daqyar ta mirgina tasauka daga kan gadon Tana dafa kafadunta dasuke Mata kamar an gwafce gabaki Daya gabobin jikinta sbd ciwon dasuke mata.


Tausayintane ya kamasa sbd yanda ko asuba datai sallah jikinta ciwo yakeyi sosai.


Bakin gadon ya qaraso ya dagota sama tareda hadata da qirjinsa Yana kallon fuskarta datai fresh ya hura Mata iska a fuska ahankali cikin kashe murya yace"


Sorry wife.


Kwantar dakai tayi a qirjinsa tareda sake shige nasa tanajin jikinta na sake amsawa tace"


Yunwa nakeji and I can't go inside the house like this.


Kissing lips dinta yayi tareda kamota suka fito Palo ya zaunar da ita tareda cewa"


Wait here bari nadubo fammah takawo Miki wani Abu you know I can't cook,I dont even know how to.


Kallonsa tayi Tana murmushi sonsa tace"


I love you for that.


I love you for this also""yafada Yana shafo wuyanta Yana Mata wani irin kallo.


Da sauri ta turesa cikin shagwaba tace"


No this is sweetmouth.


Dariya yayi Yana kallonta cikeda mamakin zancenta yace"


La ila saina fadawa kawu ya......


Da gudu ta tashi ta bisa ya fice Yana wani smiling.


Fammah ce takawo Mata breakfast suka zauna dining sukaci su ukun harda fammah din suna qoqarin sakewa da juna sosai musamman yanda zakin ke takalar nadey din Yana Mata wasu abubuwan yasa fammah Jin shaawar auren nasake shigarta abinka da dama tasaba da rayuwar sakewa saita saki jiki kawai dasu.


JJ ne yazo ya daukesa suka fita guraren qarfe biyu tareda nanu Wanda shima dattiya yabasa auren asmau 'yar alee idi qwaya Daya sai qaninta Daya Ahmad sukadai Allah yabawa idin Wanda tareda nasu jj zaa hade ayi lokaci daya.Kwananta biyu Tana fama da ciwon jiki ganin idan taci gaba da haka to duk tasamu kasancewa da mijinta za'a riqa ganewa yasa ta Nemo juriya da qarfin Hali tasawa kanta suka cigaba a hakan.Shirin bikin dake gabatowa suka Fara sbd lokaci kadan ya rage.


Iya talatu ta zage da kanta take aikin tsima amaren da ingantattun Kaya masu kyau da tsafta harsuna tuna irin algus dinsu na da suna firar suna dariya itada nadey sbd itace jekadiyarta a lokacin ai cewar iya talatun.Sanin Babu wani sabo a tsakanin fammah da jj yasa nadey dagewa gurin fada Mata abubuwan da jj din keso da wainda beso da sauran abubuwan dasukafi burgesa.


Suma a bangarensu busy suke sbd acan ayyukansu sunyi nisa na tallafin da Hana ta'addanci da shaye shaye ga kowa ayyukan kamfaninsu yayi Masa yawa,

Shi Zaki haydars buildings dinsa shikuma jj Noah empire dinsu and dad girma yasake zuwar Masa hutu yake buqata nadey Kuma aure Dole zai hanata iya riqe wasu abubuwan.Ta bangaren iyayensu kuwa tuni kawu ya maida hankali gurin dannar alee idi da cewa"


Saika danne zuciya da Ido Dan wainnan da kake gani taron marasa kunyane shima nanun dakake gani da qaton kansa kamar tayar akori kura ba kunyar ne dashiba tsaf zakaga Yana kashewa 'yarka Ido agabanka subarka tsaye kamar hotiho.


Kallonsa alee idin yayi Yana cewa"


To yanxu ya aka iya ni wlh na kunya nakeji yanda akai musu gini anan gabanmu inaji Ina kallo yadawo ya shige cikin gida da yata ciki ya rufo qofa.


Cikin tunowa da takaicin Daya qunsa yace"


Hmmmn naka Mai sauqine ubanda yafisu rashin kunyar Wanda a gurinsa suka koya ni shinayi fama dashi nagaji nakawo Ido nasaka musu ko maganar na daina kana gani kwanakin Nan har wani rashin kunya ya qaro agabana yake shigowa idan Tana ciki gurin talatu Yana kiranta da wasu sunayen banxa na turawa

Ita talatu dayake dama babbar iska ce aiko ajikinta,

Itama nadiyar sokai sokai da hannuwa kamar mariqin tubarau Kullum Ina kallo take rakosa mota idan zai fita ni wlh narasa Ina zansa kaina Kuma daurewa kawai nakeyi masifar na cina to ganin wannan me jajayen kunnuwan kamar sabuwar haihuwar 6era yasa nake dannewa sbd karta fahimci fa'dana tace idan Ina fada gidan aliyu zata koma 'yar banxar bayan duk yawon masifar danake makaranta akanta.


Dariya alee idi yayi tareda gyara Zama Yana cewa"


Agama auren ai duk watsewa zasuyi.
**Yau da yamma akayi walimar aurensu bayan andaura auren da qarfe goma Sha biyu na Rana inda dubban jamaa suka shaida auren.


Sosai amare sukai kyau musamman sbd gyara dasukasha na kusan sati biyu.


Nadey ma da ita akayi gyaran duk da hidimar kaida kawo datayi Mata yawa.


Da am aka daura auren sbd sosai yayita roqonsu suka barsa ya fito sbd ganin ya shiryu sosai sbd dama shaye shaye ba dabiarsa bace Kuma tun Randa aka tafi dashi yayi nadama yake tuba da kukan irin rayuwar batan dasukai.


Sutura Mai kyau suka bashi ya shirya a dakin nanu dake kallon na Mai gadi daga hanyar gate.


Wanka yayi ya shirya ya fito fes zuciyarsa cikeda kunya da farin ciki kwanciyar hankali da rufin asirin da 'yar uwarsa tasamu.


Dai bayan daurin aure Zaki yashigowa fammah dashi har palo Tana ganinsa ta rugo da gudu ta fada jikinsa suka rumgume juna cikin tsananin farin ciki suna hawaye.


Yanda takoma yake kallo Yana godewa Allah.


Da kanta yakirawo iya talatu datake cewa mama suka gaisa harda sauran Yan biki nadey ma tafito sun gaisa ya kalleta ya kalli Zaki da jj yasake yimusu godiya da neman gafara.


Fammah da kanta tayi feeding dinsa abinci Tana hawayen farin ciki duk sai JJ yaji notikan kansa na neman kwancewa ya juya ya fice bayan yayi Mata wani kallon qasa qasa sbd yanda take jijjjiga jikinta Tana riqo Dan uwanta.


Zaki ma kama hannun matarsa yayi suka nufi part dinsu Yana cewa"


Zo Nima nayi feeding naki nasan bakice komai sai dare yayi kifara complaining you're hungry.Da yamma qarfe bakwai aka Kai amare gidanjensu.

Fammah gidan dad aka kaita a part din mijinta da dad yayi musu jeren sabbin furnitures masu kyau da tsada,


Sai asmau data tare a sabon ginindasu zakin sukayi gefen gidansu na part biyu dasune zasu zauna da matansu Amma suka fasa sbd kowa yazabi Zama gidan babansa Wanda Suma dad dinne yayi Musu furnitures.
Bayan sundawo daga Kai amaren daqyar tayi wanka ta kwanta Tana nishin gajiya da ciwon jiki sbd qirjinta dake ciwo ga jirin datake ji tun a jiyan.


Tausayintane yasashi Fara yimata tausa ahankali Yana sake sata jikinsa har bacci ya dauketa.JJ kuwa tunda yashigo part din ya rufe koina ya nufi bedroom dinsa yayi wanka yasaka dogon wando da riga na bacci marasa nauyi.


Harya hau gado ya kwanta saiyaji baikamata bari yaje ya dubota.


Da sallama ya tura qofar dakin daidai fitowarta toilet cikin kayan daaka kawota dasu Riga da skirt na red super exclusive da yalwataccen mayafi sai qamshi da sirrin kyau take fitarwa.


Kallon juna sukayi ta sauke Kai tareda qarasowa tsakiyar dakin Tana gyara lullubinta.


Cikin basarwa yace alwala kikayi?


Kai ta daga Masa ahankali Tana sake gyara lullubinta.


Ba wani dogon bayani yace suyi sallah.


Sallah din sukayi suna gamawa ya miqe zai fice itama ta miqe zata nufi bakin gado gurin tashi mayafinta yasata komawa zata Fadi zaune yayi saurin riqota cikin saa hancinsa ya shaqo Masa wani sirrin qamshi dake fita a wuyanta ya lumshe idanuwansa batareda yasaniba yasake cusa kansa cikin wuyanta Jin haka ta qanqamesa da qarfi sbd faduwar gaba Wanda shikuma hakan ya qarasa kunnosa ya rungumeta jikinsa.


Qirjinsu na haduwa numfashinsa yakusa daukewa take ya dagota Yana kallon fuskarta da idanuwanta dake rufe Tana fidda numfashi da sauri jikinta na 'yar rawa.


Bakinta yafara dora bakinsa suka saki ajiyar zuciya kusan atare kafin ya cirata suka nufi gado ahakan.Washe gari da zazzabi nadey ta tashi Wanda ya daga hankalinsa ba Bata lokaci yakira Dr sayyid yazo har gida ya dubata yasanardasu cikine da ita 4weeks.


Fammah ma Saida Dr sayyid ya dubata sbd zazzabi da ciwon jiki.


Acikin dare guda jj ya susuce Mata abin harya fara Bata kunya ga dad ma Allah yasa ba ruwansa take aka kawo Mata sabbin masu aiki biyu tuni kulada ragamar gidan gabaki Daya yadawo qarqashinta itake abinci suna tayata da ayyukan gidan tuni gidan ya rayu sbd da Babu mace acikinsa.Am duk yazo gurin qanwarsa dadi da farin ciki yakeyi ganin rayuwar data samu,

Shine yanxu a dakin nanu Daya bari nacan gidan Wanda shima Allah ya Dora Masa son baby z shiyasa shida kawu yanxu suke dasawa matuqa Dan shine abokin firarsa.

Ta bangaren aikin rayuwa kuwa Zaki ya damqa kula da harkar tallafin Hana dabanci da shaye shaye a hannunsa bayan kula da qwazonsa da yayi agurin aikin shiyasa shima yafara sauya sosai kyawunsa da kamalarsa suka dawo musamman sbd kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya Daya samu gashi yashige cikinsu kawu mutanensa tare suke zuwa daukar karatu tun daga fatiha suke yanxu sun kusa hizifi daya

Tun baisaba da masifar kawuba harya Saba abinsa.Sati uku da bikin suka dunguma su hudu zuwa starling city US inda nadey ta tararda ayyuka sosai itada jj sukai sati biyu suka daidaita komai suka sake damqawa Jasmin komai suka wuce.


Shima haydar yayi wasu ayyukan Amma ba kamar nasuba sbd shi dama yabar wani Alan CEO chair din.


Amsterdam suka wuce acan sukai honeymoon din wata Daya zuwa lokacin itama fammah tafara nata laulayin.


Jikinsu su duka ba Dadi Dole suka dawo starling city kodan ayyukansu.


A gida Daya suke saidai kowa da part dinsa.


Anan sukai azumi da sallah zuwa lokacin cikin nadey yakai kusan wata bakwai na fammah na biyar.


Hajj suka nufa inda suka hade dasu kawu acan kawu yayita Harare hararensa harya gaji Amma farin ciki fal ransa koba komai yace sun Bata da wancan me kama da jiqar aljanun wato z sbd Kullum saisunyi fada shida ita.


Am ma yayi farin cikin ganin yakusa Zama uncle dukda ga z Nan ammadai zai samu qari.


Dagacan Nigeria suka dawo saidai daga airport asibiti aka wuce da nadey sbd naquda data taso mata haiqan.Babu Wanda yabar asibitin acikinsu sbd damuwa saigashi Bata wani wahalaba ta haihu aka samu namiji sak mahaifinsa da kakansa asalin Fata da hasken Igbo.


Kallo Daya kawu yayi Masa ya riqo hannun baby z Yana cewa"


Ke jajayen kunnuwa Zo mushirya dake zanyi wannan ubansa ya dauko daga gani bakinane zai kamani Dan wannan saiyasani fitowa da hula a juye.


Janyewa tayi Tana cewa"


Aa kace bamu sake shiryawa kaje Nima da kaka(iya talatu) zanyi da sabon bany banayi dakai.


Ni kike cewa haka?

jeki indan wannan me kalar inyamuran ne Ina zaune Zaki nemi chetona.


Dariya dukkaninsu sukayi am yace"


Baba kamanta uwayensama daidai kake dasu bareshi.


JJ ne ya karbesa Yana Masa huduba yace"


Dama ai kawu wannan soldier din kaketa fatan samu tuni..


Yaketa tsoron samu dai"""cewar iya talatu Tana dariya.


Tsuke fuska yayi zaiyi mgn alee idi yace"


Kyaleta laifinane...


Ita talatun ta qarasa Masa da cewa"


Daka bari ya aureni ko???


Dariya dukkaninsu sukayi harshi alee idin da alhaji dattiya.


Shidai sarki Yana zaune kusada matarsa sai murmushi yakeyi cikin farin ciki Yana saurarensu hannunsa ruqedana matarsa.


Koda aka sallamosu gurin haj talatu aka maidota sbd samun kyakkyawar kulawa.


Aikuwa kulawa sosai suke samu har ranar suna ya zagayo jj yayi Masa huduba da sunan kawu wato Muhammad dattiya ana kiransa da sayyed.


Bayan suna qiri qiri yaso tadawo taqi komawa Saida sukayi sati shida harda kwana shida.


Ranardata koma ranar suka Dora inda suka tsaya abinsu cikin kewa da tsananin qaunar juna.

****Cikin tsananin murna ta ajiye wayar tareda rungumesa Tana cewa"


Uncle fammah ta haifi little z.


Cikin murmushi yace"


Saida yafara fadamin to cewa yayi karna fada Miki kice anmiki Yan ubanci.


Fadawa tayi kansa Tana cewa"


Wlh ko yanxu anmin.

Daga asibitin itama fammah gida aka dawo da gurin hajja kamar yanda suke Kiran iya talatu yanzu.


Zakine yayiwa babyn suna da ruqayya shima sbd JJ ne keson asa sunan umman Zaki datasa umman da itama ruqayya ne sunanta.Ranar suna aranar jj yayiwa matarsa kyautar sabuwar mota fil hakama dad.


Ko aranar fammah da am sunyi kukan karamci da rashin qyashi da riqo da Allah baisaka a zuciyar bayin Allanba.


Sunriqesu tamkar dama asalinsu Daya Wanda sai yamzu suke gabbatarda ba lallai sai Wanda ka hada jini dashi bane yake Zama Dan uwanka yarda da juna tareda Amana nasa kazama Dan uwan mutum fuyeda wani jinin.


Bayan biki suna da sati uku suka shirya su uku sukaje Dilla dubo mum dinsu.

Am,jj da ita fammah din sai baby r.


Sosai mum dinsu taganesu duk da har lokacin akwai haukar atareda ita Amma ba laifi abin yayi sauki.


Dazasu dawo kamar karsu rabu suna kuka cikin jirgi jj ya rungume matarsa Yana lallashinta cikin soyayya da qaunar abarsa.Itama Saida tayi sati bakwai takoma gidanta shima sbd gajiya da kawu yayi da irin rashin kunyar da ake zuba Masa a gida ya koresu,

Gata Zaki Daya Gama renasa gata jj din gata itama fammah din qafafu kamar zaren kitso ta iya rashin kunyar rako Miji idan zai tafi Tana wani maqalewa.


Ko wata hudu Basu Gama rufawaba suka tarkata suka komawarsu su duka dama kawun a matse yake Kullum yayita masifa kenan tun yanayi a fili Dole Yakoma a boye yakeyi sbd itama Kuma me jajayen kunnuwa batason duk yayi fada kwana takeyi Tana fushi dashi shiyasa yanaji Yana gani abinda yayansa Basu hanasa jikar Daya Gama hawala akanta ta canzasa sbd beda yanda ya iya tunda yafi qaunarta Alan komai yanzu.


*ALHAMDULILLAH.*


_SHI ALKHAIRI DANQONE KA TAUMAKI WANI BAKASAN WAYE ZAI TAIMAKEKABA GOBE._


_DA JINI DABA JINIBA KA RIQI MUTUM DA AMANA DA DARAJA SBD ZAI IYA ZAMA SHINE NAKA WATA RANA._


_RIQO A GABA KO CUTA BAIDA AMFANI SBD BAZAI DAWO DA BARNA BA KA ZAMA MAI YAFIYA ALLAH ZAI SAUKAKA MAKA RAYUWARKA CIKIN NUTSUWA DA AMANA._


_'DAN TA'ADDA MUTUM NE BA DABBA BA KOWA DA TASA QADDARAR,

KARKA KYARESA TALLAFA MASA IDAN KAGA DA HALIN HAKAN KO KABISA DA ADDUA._


_KAYAN MATA BA ILLA BANE IDAN KA ZAUNA KAYI TUNANIN SHAN ABINDA YAKAMATA A TSARI BA HAUKABA KAMAR YANDA WASU SUKA DAUKI ABIN._


*_INA MIQA DUKKANIN GODIYATA GA MASOYA DASUKA NUNA TSANANIN SO DA QAUNA GA DATTIYA DA IYALANSA._*


_*YA ALLAH YASA MU AMFANA DA ABINDA KE CIKI SABANINSA ALLAH YA YAFE MANA.*_


*_NI MARYAM SANI GUMMY WADDA AKA FI SANI DA MAMUHGEEE NAKE CEWA ALLAH YA HADAMU A WANI SABON LABARIN IDAN ALLAH YACE_**AMIN.*

No comments

Powered by Blogger.