Bakar Inuwa 80


 *_Episode 80 END_*

...........Cikin sauri-sauri take ƙarasa shirin nata. Tayi matuƙar ƙyau cikin ɗanyan shadda da taji wadataccen aiki. Sosai ta zama babbar mace da duk inda ta gitta dole ne a bata girma kodan yanda take cika idon mai kallo. Kwalbar turaren hanunta ta ajiye tana mai juyiwa jin an buɗe ƙofar ɗakin. 

      Batai magana ba, sai dai ta tsurama ƙyaƙyƙyawar yarinyar da bazata wuce 4years ido ganin yanda taketa faman tura baki gaba cike da shagwaɓa. Sanin halin ɗiyar tata ya sakata takowa a hankali gareta, ta amshi bowl ɗin hanunta tana kallon abinda ke ciki. “Zee miya faru?”.

        Sake ɓata fuska yarinyar tai hawaye na ciko mata ido. A shagwaɓe tace, “Mamie ba Daddy bane da Saleeha suka cinye min”.

      Kai Raudha ta dafe, a zuciyarta tana tunanin yaya zatai da Ramadhan a gidan nan itako akan cin nama, ƙoƙari take duk yanda zata hanashi ci kamar yanda likita ya saka masa doka. Shiko yasan duk hanyar da zaibi yacisa. Komai batace ba ta kama hanun Zainab suka fita. Kai tsaye falonsa ta nufa inda take jiyo ƙiriniyar Jiddah da Saraki. Dan su Abdull sun wuce Islamiyya. Zee ɗin ma dan bata da lafiyane bataje ba, itako Saleeha ganin Zee bazataba itama ta maƙale.

        

    Kwance yake a tsakkiyar lallausan carpet ɗin falon, Jiddah da Saraki nata tsalle a kansa. Tun kan ta ƙaraso ƙamshinta ya sanar masa. Saraki ya sauka daga kansa da gudu ya nufeta. Ɗaukarsa tai tare da subatar kumatun autan nata. Shima ya sumbaceta da faɗin “I love you Mamie”.

      “I love you too Darling”. Ta faɗa cikin shafa kansa tana murmushi

   Fuska Jiddah ta ɓata tana hararan saraki, hakan yasa Ramadhan faɗaɗa murmushinsa tare da sumbatar goshinta itama yace “I love you sweetheart ”.

      Dariya Jiddah ta sanya. Ta rungume Daddyn nasu tana faɗin “I love you too Daddyn mu”.

        Raudha dake kaiwa zaune tai murmushi da girgiza kanta. Sai kuma ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Duk mai kishi da autana dai zai rame a gidan nan”.

      Tashi zaune Ramadhan yayi sosai yana murmushi shima idonsa akan matar tasa, dan kwalliyar tata ta tafi dashi sosai. Kai kace wata anguwa zata. Ido ya kashe mata cike da salo yanda yaran bazasu gane ba. Itako ta hararesa tana nuna bowl ɗin hanun Zee daketa ɓata fuska.

      Idanu ya waro sosai tare da miƙewa ya koma saman kujera idonsa akan Zee. “Zee yaushe kika fara gulma a gidan nan? Mi kikaje ki ka ce?”.

        Cikin shagwaɓa Zee tace, “Daddy bakaine ka cimun dambun nama ba da Saleeha, kuma Mamie tace indai kaci na faɗa mata”.

       Sake waro idanun yay akan Raudha, “Ustazah wannan haɗin faɗan fa?”.

      Fuska ta marairaice masa sosai, a hankali tace, “Dan ALLAH ka daure kabi dokan Doctor, yaushe ka gama shan wahala, sugar ɗinka a shekaran nan kullum sama yake ba ƙasaba Please Noorullah”.

      Murmushi yayi yana kauda kansa. “Ko naci ko banci ba zan mutune Partner. Mizaisa naita azabtar da kaina wajen ƙin cin abinda nake so. Komai inabin dokarsa ai amma bazan iya ƙin cin nama ba gaskiya”.

      Ido kawai ta tsura masa kamar zatai kuka. Dan ita kam batasan taya zata masa bayani ya dinga fahimtarta ba. Su Pa nada sugar amma da yake suna bin doka nasu bai tsanani ba. Shiko sam yaƙi daina cin nama, gashi baya masa cin sauƙi, inhar ya samu zai masa cin tuwo ne. Kuma in zaici safe rana dare bazai gaji ba. Ganin yaƙi yarda su haɗa ido ta ɗauke kanta tana duban Zee da tuni ta ajiye bowl ɗin naman ta koma tsalle-tsalle tare da su Saraki.

       “Zee ina Saleeha?”.

Kafin Zee ta bada amsa Jiddah ta amshe da faɗin, “Taje wajen Granny Mamie”.

        Kowa a gidan yasan a gidan Saleeha ƴar ɗakin Maah ce, dan ita da Dawood (Abbati) ma basa kwana ko'ina sai can, hatta kayan sakawarsu kashi biyu bisa uku nacan. Itako ji take da su kamar mi. Abdull kuwa na gaban goshin Anne ne kowa ya sani.

        Cikin ɗan sauke numfashi Raudha tace, “Okay Zee ki ɗauka bowl ɗin can na saman dining kuje har auta a kaima Granny, ai an kaima Anne nata ko?”.

       “Eh Ya Abdull ya kai mata da zasuje islamiyya”. Cewar Jiddah.


  Suna fita Raudha ta mike ta koma kusa da Ramadhan daya maida hankalinsa akan labarai da ake nunawa a tv. “Wai fushi kake dan nace ka daina cin nama?”.

      Hararta yayi ya ɗauke kansa. Da sauri ta taro fuskarsa cikin hanunta ta hura masa iska ganin zai lumshe ido. “Noorullah Please ka fahimceni, rayuwarka nada muhimmanci a gareni da yaranmu dama duk jama'ar gidan nan. Ina fatan yanda su Bappi sukaga yaranmu muma muga yaran su Abdul haka a duniya. Please sweetheart i love you more”.

       Murmushi ya sakar mata mai sanyi, shima ya tallafo muskar tata. Shanyayyun idanunsa ya zuba mata, “My Heartbeat kinyi ƙyau”.

        Ƙaramar harara ta sakar masa ganin zai kautar da wancen zancen. Ta buɗe baki zatai magana ya manne lips nashi. Idanu ta lumshe a hankali kamar yanda shima ya lumshe nashi, ta san kuma ƙarshen maganar kenan dan haka yake mata a duk lokacin data ɗakko masa irinta. Sunyi matuƙar nisa a faranta ran juna sallamar su Abdull ya ziyarci kunnuwansu. 

      A hankali Raudha ta janye jikinta, shima janyewar yay ya kwanta jikin kujera yana mai lumshe idanunsa da shafa kansa. Sai da ta saisaita kanta ta basu izinin shigowa kamar yanda suka horesu. A nutse matasan samarin uku suka shigo cikin fararen kayan Uniform.

         A nutse suka gaishe da iyayen nasu, Abdull ɗan shekaru goma sha ɗaya da hankalinsa ke kan Daddynsu ya kai zaune gefensa cikin damuwa. “Daddy baka da lafiya ne?”.

       Murmushi Ramadhan ya saki, a hankali ya shafa kan Abdull yana ƙoƙarin saisaita kansa. Muryarsa a dasashe kamar wanda mura take son kamawa ya girgiza masa kai. “Lafiya lau nake My son. Kawai dai inajin barci ne?”.

      Abdull yay ɗan murmushi, cikin nutsuwarsa kamar wani babba ya ce, “Oh Daddy babu ƙyau barcin la'asar fa”.

        “Ai bazanyi ba My dear. Kuje ku canja kaya kuyi alwala ku jirani muje Mosque. A kira Auta ma yana sashen Granny”.

       Yay maganar yana shafa kan Abbati da Alhaji ƙarami da suka lafe masa a jiki suma.

     “Okay Daddynmu”.

Abbati ya faɗa cikin ƙiriniyarsa dan kam shi dai babu sauƙine. Yanzun ma shirun nasa nada nasaba da dukansa da Raudha tayi kafin su wuce islamiyya saboda yayi faɗa da Alhaji ƙarami.

      

     Suna fita Ramadhan ya dubi Raudha yana murmushi. “Kinsa Abbana duk yayi laushi kamar bashi ba”.

     Murmushi tai itama tana ƙoƙarin miƙewa. “Daban masa hakaba da yanzu da gudu zai shigo mana kuma faɗan har islamiyya za'aje anayi dan nacinsa. Nikam dai idan ya biyo darun Abba (Mal. Dauda) wahala zaici”.

     Dariya sosai Ramadhan yayi, tare da kamo hanunta ya maidata ya zaunar. Rungumeta yay cikin raɗa da sakar mata kisses a gefen wuya. “Muje daga ciki kiji wani labari”.

     Cikin ɗan waro ido da ture kansa “Kai Ya Ramadhan sallafa kacema yara zaku”.

      “Wayo na musu ai, dan bazan iya sallar nan a hakaba kuma da sauran lokaci ai”.

          “Wai miyasa kakemin hakane? Duk sanda nai kwalliyata saika bata”. Tai maganar murya a narke cikin shagwaɓa.

       “Tukuyci nake badawa ai, tunda dama ni akaimawa ko”.

     Zatai magana ya sake rufe mata baki ya hanata. Babu yanda ta'iya dole ta amshesa hannu biyu. Daga ƙarshe suka shige bedroom.✍


Hummmm bari dai na tsaya daga nan kar bin ƙwaƙwƙwafin yay yawa kuma😜. 


*_ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!! ALHAMDULILLAHI!!!_*


_Godiya ta tabbata ga UBANGIJI daya bani dama da rai da lafiyar rubuta wannan ɗan littafi. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ya bamu ladan baki ɗaya. Wanda nai kuskure ALLAH ka yafemin ni da ku da kuka karanta._


*Kamar ko yaushe ina neman afuwan duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan littafin. A yafemin, a yafemin, a yafemin. Nima duk wanda ya ɓatamin na yafe masa, sai dai banda wanda ya zalinceni akan ganganci ko son zuciyarsa. Shima inhar yazo ya roƙa gafarata ya sanarmin zan iya yafe masa da fatan zai kiyaye gaba. Zata iya yuwuwa wannan shine littafi na karshe da bilyn Abdull zata rubuta a duniyar rubutu😭🙏🏻 babu ruwan mutuwa dauka take a duk sanda taso.


*_Bazamu gaji da godiya a garekuba masoyanmu, kun nuna mana halacci kamar yanda kuka saba. ALLAH ya saka muku da alkairi ya bar zuminci, alkairin ALLAH yakai gareku a duk duniyar da kuke. Zafafa biyar na muku son so irin trillions ɗin nan wlhy. ALLAH ya saka da alkairi musamman wanda ke tare da mu tun farkon zafafa har zuwa yau. Kai harma wanda suka fara binmu yanzu duka mun gode sosai🙏🏻_*


_Kamar yanda na faɗa BAƘAR INUWA ƙirƙirarran labarine. Idan kaci karo da abinda yay kamanceceniya da rayuwarka kayi haƙuri bakai din ake nufi ba. Sannan bazan gaji da sanar da mai karatu cewar littafi nishadi ne, faɗakarwa ce, harma da ban haushi. Idan kaci karo da nishaɗi kayi badan dole saika samesa ba ko ka nema. Idan kaci karo da ilimi ka amfana gwargwadon fahimtarka. Idan abin haushine ka ɗauka adon labari ne. Rayuwar novel bawai babu ita a zahiri bane, sai dai ba lallai kowa ya sameta 100% kamar littafin ba, idan ma ka samu kasa a ranka akwai ƙaddara da jabawar da zata iya banbanta da hikayoyin marubuta_.


*Abinda kaso gani baka gani na rubuta ba amin afuwa ajizancine irin na ɗan adam da mantuwa. Wanda yazo ba'a yanda kaso ba shima kayi haƙuri ba komai ake samu a yanda ake son gani ba. ALLAH ya sadamu da alkairinsa a zafafa karo na 7 da zasu zo muku nan kusa insha ALLAH😘😘😘😘🙏🏻👍🏻*


*Mallakin Bilkisu Ibrahim musa (Bilyn Abdull)*

No comments

Powered by Blogger.