Babban Goro 5


 BABI NA BIYAR___5

Direct Asokoro villa ya nufa, yana yin parking ya nufi part ɗin Dad, 

Tsaye yayi lokacin daya isa bakin kofar ɗakin ya shiga kwankwasawa da sallama cike da adabi, 

“Waye ne?” 

Daga can ciki aka amsa mishi, 

   Jin muryar Momi yasa ya tura kofar ya shiga a hankali

“Nine Momi” 

Fuskar mamaki Momi tayi “Lafiya kayi mana sammako haka?” 

Kusa da ita ya zauna ,

“Lafiya kalau wata alfarma nazo nema gareku” 

Dad dake shan tea ya kalle shi 

“Alfarma kuma wace irin Alfarma kake nema?” 

Sai da ya nisa sannan yace

 “Dad So nake ka bada umarni tsayarda duk wani jirgi da zai tashi daga yanzu zuwa nan da karfe goma sha biyu” 

Daga Momi har Dad kasa fahimtar shi sukayi 

Momi tace

 “Miya faru Matsalar tsaron ne ko me?” 

“Babu ko ɗaya Momi yanzu Dr. Salamatu ta kirani tana kuka tace na taimaka mata karta rasa rayuwar yarta tana son guduwa ne tabar kasar. 

Shine nake son ka hana tashi da jiraje idan na kwace passport ɗinta sai komai ya cigaba” 

Kai Dad ya girgiza

 “Bazan maka haka ba Saboda ya ɗaya tilo a hana dubun mutane yin abinda suke so” 

Rokon shi Saif ya shigayi,

 “Dan Allah Dad ka taimaka min ba dan kowa zakayi ba sai dan ni, Dad zata iya shiga ko wane irin hali idan ba'a hanata tafiyar ba, yanzu Dad idan Safiya ce ya zaka ji?” 

Dafashi Momi tayi 

“Saifullah Safiya ba zata yi abinda wannan yarinyar tayi ba wannan ina tunanin bata da hankali ko kuma tana share share-” 

Tarar numfashinta yayi 

“No Momi ba haka bane akwai abunda mahaifiyar ta tayi mata ne”

 Juyowa yayi gurin Dad yana mishi magiya

“Dad Please do this favor for me na riga na faɗi haka zansa ayi dan Allah karkasa naji kunya ka bada umarnin”

Dad yace 

“Kai ke da ikon kasar ne da zaka ce haka za'ayi?”

Tasowa Momi tayi ta dawo kusa da Dad ta zauna cikin lafazi mai alamar tausa ta soma lalla6ashi,

   “Ka taimaka mishi karya ji kunya tunda har ya faɗa, yana nufin yana da matsayi a gurinka” 

Shiru Dad yayi na tsawon lokaci, kamin ya janyo waya ya bada umurni yin hakan, 

  Godiya sosai Saif yayi mishi sannan ya tashi ya fice suka bishi da kallo, 


  Gudu ya rik'ayi kamar zai tashi sama cikin yan mintuna ya isa Airport ɗin, 

Kai tsaye gurin da ake tantance fasinjoji ya nufa, tun kamin ya k'arasa ya rik'ajin sanarwa an hana tashi da jirage na wani ɗan lokaci, 

 Yana isa gurin duk suka tashi tsaye suka sha jinin jikinsu, hannu suka bashi bayan sun gaisa ya kalli babban su,

“List ɗin passenger da zasu tashi nake so” 

“Ok Sir” 

Nan ya kalli na gefensa

 “A kawo mishi list” 

Da sauri mutumin ya juya ya nufi wani ďan tebur dake kusa da su 

 Cikin yan mintuna ya kawo mishi files kusan guda goma sha biyu, 

  Wayarsa ya ciro cikin aljihu ya danna kira ana daukar yace

 “Minene full name ɗin da take anfani dashi”

 Can naji yace ok ya kashe wayar, 

Wadda ke rike da files ɗin ya kallah 

“Duba min Amina Alhassan Minal” 

Jiki na rawa yace,

“Ok Sir bari musa a computer yafi sauki” 

Kai kawai ya ɗaga mishi yaja kujera ya zauna, 

   Ana saka sunan nan take computer ta nuna har da ɗan karamin pic ɗinta, 

Juyowa yayi ya kalli Saif

 “Sir gata amman tana cikin fasinjoji da suka tashi” 

da dauri ya yashi tsaye

Da karfi Saif ya furta

“What bayan an faɗa muku karku bar jirgi ko ɗaya ya tashi.? Mi kuka aikata kenan a baku umarni ku tsaɓa me kuka dauki kanku sai kunyi nadamar abunda kuka aikata” 

B'ari jikinsu ya shigayi ko wanne cikinshi ya ɗori ruwa, ɗaya daga cikinsu ne yayi kokarin yin magana 

“Yan laɓai ayi hak'uri koda aka bada umarnin hana tashi da jirgi jirginsu yayi minti talatin a sama kuma kasan idan jirgi ya riga ya tashi babu yadda za'ayi a tsayar da shi” 

Shiru yayi ya jingina da gurin, can ya kalleshi 

“Ina jirgin ya nufa?”

Cikin sauri ya bashi amsa

“New York” 

“Akwai jirgin da zaije can yanzu?”

 Saif ya Tambaya

“Babu shi yanzu Sir sai dai anjima da maraice karfe hudu abinda yayi kasa” 

Kai ya ɗaga musu ya tashi ya fice. 


    Driving yake yana danna calling ana yin parking yace “Dr. Salamatu jirgin su Minal ya riga ya tashi nasa an tsayarda tashin jiraje amman already nasu ya tashi”

 Shiru ya ɗanyi sannan yace

 “New York ta nufa eh i will try my best nan da 6 hours zan isa can zanyi wani abu akai insha Allah” 

Yana kashe kiran ya sake danna wani kiran

 “Hello Hashin ina son kujera ɗaya daga cikin kujerun da zasu je New York anjima, no yanzu akwai inda zanje karka yarda nayi missed flight” 

Yana kaiwa nan ya danna red bottom ya karama motarshi jiya.   3:11PM...... 

Ya shigo gida da gudu Huda ta tareshi,

“Dear tun safe sai yanzu?” 

Kiss ya manna mata a gefen kumatu 

“Am so sorry dear wani ɗan aikin ne ya rik'e ni” 

“Dear wai wane irin aikine yau fa Weekend” 

Zaunarda ita yayi saman kujera

 “Meeting mukayi da wasu Indian yanzu ma new york zanje” 

“Wasa dai kake ko?” 

Tashi yayi yana faɗin 

“Allah da gaske wani aikin ne ya taso” 

Bedroom ɗinshi ya nufa nan itama ta tashi ta rufa mishi baya, 

Koda ta shiga ta tararda shi yana cire rigarshi, ido ta bishi dashi har ya ɗaura tawul ya shiga bathroom, 

Gefen gado ta samu ta zauna ta zubawa bathroom ɗin idon har ya gama wankan ya fito, 

Wardrobe ya nufa, ganin yadda ake kallon shi yasa ya sakar mata murmushi

 “Wai wannan kallon na lafiya ne?” 

Bata ce mishi komai ba har ya goge jikin shi ya shafa mai yana kokarin saka tufafi tace

 “Wai da gaske tafiya zakayi?” 

“Gashi kina gani karfa ki ɗaga hankalinki ba dadewa zanyi ba” 

Ya k'arasa maganar tare da ɗaukar turare yana fesawa a jikinshi.

Juyowa yayi ya kalleta yadda ta wani haɗe rai sai yasa shi yin murmushi ya fesa mata turaren a gefen wuya ya zauna kusa da ita

 “Wai minene na wannan fushin my heart?” 

Kamar ta fasa kuka “Toh dear kaje new york ɗin dani mana ko kuma ka bari har wani sati” 

Dariya yayi 

“Ai ba zai yiyu ba idan ma yawo kike so toh ki bari har na dawo sai muje duk inda kike so” 

A gogon hanninshi ya duba da sauri ya tashi tsaye 

“Kai kinga har 3:40 tayi kuma 4 zamu tashi” 

Bedside drawer ya buɗe ya ɗauki wasu abubuwan da yasan zai bukata ya saka a wata yar karamar jaka

Hannunshi ta riko cikin yanayin damuwa 

“Dear ko dai baka hak'ura bane?” 

Hannun nata ya manna ma kiss 

“Na hak'ura mana ai da bazan barki ki dawo ba Dad ne ya aikeni ai kinga ai bazan ce masa bazani ba ko?” 

Jikar ya ɗauka tare da riko hannunta suka nufo parlor, har bakin mota ta rakashi, nan ya ɗanyi huge ɗinta

 “Ki min addu'a kinji?” 

Kanshi ta shafa

 “Allah ya dawo min da kai lafiya” 

  “Amin thank you ki kula min da kanki” 

Kai kawai ta ɗaga mishi tana kallon shi har ya tada motar ya fice, 

Sai da ya biya Maitama ministers hill ya karɓi pictures ɗin Minal da information sannan ya wuce, 


NEW YORK..... 

14:44GMT jirgin su Minal ya sauka, kai tsaye ta nufi hanyar fita Airport ɗin, sanye da wani blue jean yayi tight ɗinta sosai, sai yar fashion t-shirt pink color, 

Babu komai a hannunta daga ATM sai Passport, haka ta fito tana janye gashin kanta da iska ke kaɗawa, 

Jin am dafata yasa tayi saurin waigowa, 

“Sarah”

 Abinda Minal ta faɗa kenan tana kallon budurwar farar fata, 

Hannayenta Minal  ta kama tana dariya

 “Mil Barka da zuwa birnin mu birni mai yanci da walwala” 

Mamaki ne ya bayyana a fuskar Minal 

“Sarah ya a kayi kika san nazo?” 

Sama Sarah tayi da glasse ɗin idonta

 “Deen ne ya faɗa min tun jiya kuma shi ne ya faɗa min lokacin da jirginku zai taso da kuma lokacin da zai sauka shiyasa na tare ki nayi marmarinki sosai Mil”

Da dariya ta k'arasa maganar tana jan kumatun Minal, 

Da sauri Minal ta rungume ta idonta cike da hawaye

 “Nima nayi marmarinki Sarah  ina sonki sosai” 

“Nima ina sonki Mil” 

Duk da yaren faransanci suke wannan maganar,

     Nan Sarah ta rika hannunta suka nufi gurin da aka tana da dan aje motoci,

  Wata red sport-car suka shiga Sarah ce a driver seat, Minal na zaune a front seat, a hankali ta tashi motor suka hay t-t.

No comments

Powered by Blogger.