Babban Goro 10

 


BABI NA GOMA___10



Cike da nauyin baki Mummy ta soma magana, 

_“Asalina ni yar garin Kwara ce ni ibira ce shine yare na kuma yaren iyayena da yan'uwa na, Alhaji Abubakar shine mahaifina ma aikacin banki ne Mahaifiyata kuma Hajiya Amina malamar makaranta ce nice first born a gurin iyayena Kanne na huɗu uku maza mace ɗaya dukan mu iyayemu suna bamu kyakkyawar kulawa da tarbiya baya wasa da karatun mu musamman na addini._

_Daga garin Neja akayi ma Mahaifina Transfer zuwa Yola, nan muka dawo da zama gaba ɗayan mu, koda muka dawo Yola na gama Secondary school, sai mahaifina yasa nati jam cikin sa'ah naci sai ya nema min admission a university,_

_Kamar wasa na fara karatun sai gashi na kusa kammalawa da yake mace ce ni mai maida hankali ga abunda na sawa gaba hakan yasa ban taɓa faɗuwa a jarrabawa ba hakan kuma yasa na samu masoya saosai sai dai bana kula kowa har na kammala karatu na._

  _Bayan results ɗina ya fito na sami mahaifina da zancen zan koma makaranta nayi mastas shi kuma ya sauya min tunani da zancen Aure_

_Banyi mashi musu ba na amince dan kawai na faranta musu rai,”_



Shiru ta ɗanyi sannan ta cigaba,

_“A haka Abbana ya bani damar zaɓen duk mijin da nake so, ni kuma duk tarin samarin da suke zuwa kawo min harin banga wadda nake so ba hakan yasa na bawa iyayena zabi duk wadda sukaga ya dace dani. Sun ji daɗe sosai yadda nayi musu sukayi farinciki_

_Bayan kwana biyu dayin maganar mahaifina ya kawo min wani saurayi son kowa kin wadda ya rasa wato mahaifinki kyakkyawa ne sosai fari fes yadda kika ganki babu abunda kika rage a kamaninshi, naji daɗin zaɓin da iyayena sukayi min saboda duk a samarina banga irinsa ba a ɓangaren kyau da iya wanka_

_Wata biyar Abbana yasa na Aurena, duk wani abu da ake bukata na Aure Abbana ya rik'a siya yana aje min_. 

 _Soyayyah ce ta shiga tsakanin mu sosai idan yazo fira kamar kar muyi sallama, idan abu ya same shi kamar ni ya sama, Wata rana rashin lafiya ta kama shi har aka kwantar da shi asibiti mukayi ta yawon zuwa ganinshi har Allah ya bashi sauki aka sallameshi, bayan ya dawo sai ya dinga fushi dani wai banje gida na duba shi ba, Duk Wani far'ar shi da nake gani sai ya daina na rasa gane kanshi gashi kullum cemin yake ciyon shi karuwa yake,_

_Hakan yasa na yanke shawarar kai mishi ziyarar, duk da nasan Addinina na ya hana banyi tunanin wani abun ba kuma ni a tunanina kamar ba komai bane mace ta kaiwa namiji ziyara tunda naga a makaranta ma friends ɗina suna kaiwa samarin su ziyara_

_Nayi Mamakin yadda na same shi dan ya banbanta da yadda kullum yake faɗa min sam babu alamun ciyo a jikinshi, da kanshi ya buɗe firij ya ɗauko lemu ya zuba min sannan ya dawo kusa dani ya zauna muna fira muna shan lemun, daga nn ban sake sanin inda nake ba”_

   

   Lumshe ido tayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, bayan kamar minti biyar ta buɗe ta cigaba da maganar,

_“Koda na farka ya aikata alfasha dani! Nayi ta kuka yana bani hak'uri, nayi bakin ciki sosai a hkan na lallaɓo na nufo gida”_

(Daya daga cikin illolin ziyarar ɗakin saurayi ke nan shiyasa duk abunda musulunci ya hanemu dashi toh barinshi shi yafi Allah ya tsare mu da zuri'armu AMIN)

   _“Sam ban bari mahaifana sun gane halin da nake ciki ba har na tsayon sati biyu, tun lokacin da abun ya faru Alhasan ya dinga jigilar zuwa gidan mu yana bani hak'uri, ni kuma na juya masa baya naki kulashi hakan yasa sai shi kuma ya daina zuwa, haka sai yasa na kara tsanar shi sai na ɗinga tunanin ko auren shi nayi wulakanci kawai zai biyo baya kuma wata kila ya rik'a neman matan banza maybe ma halinshi ne akan wannan dalilin yasa nace wa mahaifina bana son shi sai mahaifina ya taramu a parlor yana tambayar ko wani abun ne ya shiga tsakanin mu nan nace mashi babu komai shi kuma yace shi dai idan bana son shi zai iya janyewa dan yaga yaga take take na kuma daman mutanen unguwa sunce bana da mutunci bansan girma ba. Bakin cikin furucinshi yasa na tashi tsaye gaban mahaifina na nuna shi da yatsa nace, Eh bana son ka duk abinda kasan ka kawo ka faɗa a biya ka,_

 _Baki da da kunya baki da tarbiya a fasa ɗin idan an fasa waye a matsala abun ya fito bakinshi kenan yana rawar kai, a nan ni kuma nace mishi ina da tarbiya alhasan kaine dai baka da ita kuma baka haɗa hanya da ita ba wulakantacce dan karin girma_

_Nan take mhaifina ya watsa min mari yana faɗin taya zamu tsaya gaban idon shi muna faɗin waɗannnan kalamai idan bama son junan mu ai sai mu faɗa ba sai an kai ga haka ba, sai da yayi mana tas daga ni har shi sannan yace idan baya sona ya aiko a karɓar mishi kayanshi, haka ko akayi kamar mai jira sai ga iyayen shi ya aiko wai shi ya fasa Auren kuma duk abinda ya kawo ya yafe Allah ya haɗa kowa da rabon shi, nima ban damu ba dn banyi tunani ina ɗauke da cikin ki ba,_

_Da wani Cousin ɗina Abbah ya haɗa mu, ya saka lokacin Auren mu Wata biyar kamar yadda yasa ni da Alhasan, Wata biyu da faruwar hakan rashin lafiya ta sameni mai tsanani har ta kai bana iya tashi nan mahaifina ya sani a mota da mahaifiyata muka je Asibiti, a nan aka tabbatar min da ina ɗauke da cikin ki_

 Nan kuka ya yaci Karfin ta ta kasa k'arasawa, Wani irin sanyi jikin Minal yayi nan itama ta fara zubar da hawaye.

READ COMPLETE HERE

No comments

Powered by Blogger.