Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
_Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo💫_
*Abban Sojoji part 2*
*EPISODE 1*
Meaning Of Name *AMANI* means *wish* arabic name ne na mata🌹ina faɗin ma'anarsu ne saboda masu tambaya, sunaye ne masu kyau mutun zai iya amfani dashi in yana so wa baby girl ɗinsa😍
Ruwan sama ake yi sosai garin, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni'imtacciyar iska wadacciyar da ta gauraye ko'ina, wurin ƙarfe 5 na marece ne amma sai kayi tunanin dare ne sosai saboda Lullumin da garin yayi, a wannan yanayin kowa na ƙumshe a bedroom ɗinsa saman gadonsa, lullu6e da bargo, baka jin hayaniyar komai ko'ina tsit a cikin gidan 😊
zaune suke acikin mota suna tattaunawa su biyu, Hafsat ce tare da wata Hamshaƙiyar mata wadda bansanta ba, jikinta na sanye da tsadadden leshi Ash colour, fara ce kana ganinta kasan taji hutu Over ya zauna mata, ita ce a mazaunin driver yayin da hafsat ɗin ke gefen ta suna tattauna wa,
Hafsat ta natsu tana sauraronta " Naci sa'a da nasamu address ɗinki kuma na same ki cikin sauƙi, kuma ina fata zaki taimaka mun wurin cimma burina,' matar ta faɗi tana kallonta,
Hafsat tace "ina sauraronki me kike so inyi miki ne "?
Murmushi matar tasaki kafin tace "Kafin na faɗa miki abunda nakeso, pls ina so ki fara bani acct number ɗinki,"
Bin ta da kallo hafsat tayi cikin mamakin jin abunda matar tace,
Amma batayi musu ba, ta shiga karanto mata numbar acct ɗin, ita kuma tana kwashe wa a wayarta dake hannunta,
Bata jima da gama karanta mata numbar ba sai ga Alert ya shigo a wayarta ƙirrrr!
Cikin sauri hafsat tasa hannu ta ɗauki ƴar purse ɗinta dake asaman Laps ɗinta ajiye, ta zugeta ta ciro wayar jiki na rawa ta duba, gabanta ne taji ya faɗi rass !! Ganin Alert na 6millions abun kamar a mafarki take ganinsa
Cikin tsananin mamaki ta ɗago ta kalli matar tare da cewa "Wannan fa? Na menene?
dariya matar tayi kafin tace " akwai wasu tagwayen Yara da Marshal Omar ya kawo gidan nan, Sunan su Hosana da Jahad,'
Jin sunan da ta ambata yasa hafsat kallonta cikin mamaki,.
Taci gaba da cewa "Ba wani aiki bane mai wahala, so nake subar gidan nan ! Suyi nesa da Marshal Omar..........'
Cike da mamaki hafsat ke kallonta , babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda akai tasan cewa Marshal Omar ya kawo yara acikin gidan,.
Daker ta iya cewa "Saboda Me za'ae hakan?
"Saboda basu da amfani," matar ta bata amsa a taƙaice,
Shiru hafsat tayi tana kallonta acikin zuciyarta tana Was wasi akanta,
"Wacece ke? Taya akai kikasan sunan Tagwayen tare da kuma sunan Omer?
"Ba buƙatar wannan, Kawai kiyi mun abunda nace in aikina yayi kyau nayi maki alƙwarin zan ninka miki abunda na baki har sau uku,
Hafsat tace "To shikenan ni zan wuce ciki sai kin jini"
Murmushi matar tasaki tare da cewa "sai mun sake haɗuwa,"
fito wa hafsat tayi daga Motar ta rufe mata sannan ta wuce cikin gidan da hanzari saboda ruwan dake sauka ajikinta,
Yayin da ita kuma Matar taja motarta ta fuce daga gidan fuskarta ɗauke da murmushin nasara,
tana shiga cikin babban falon ba kowa kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, cire kayan jikinta tayi shaf shaf ta canza izuwa riga da wando, ta ɗaure gashin kanta a baya, tana tsaye gaban Mirror tana tunanin maganar Matar nan data kawo mata ziyara sai ga Aunty Babba ta faɗo ɗakin tana faɗin "Hafsat wacece waccan matar da tazo wurinki yanzu"?
Juyowa hafsat tayi tana kallonta tace "Nima bansanta ba address ɗina aka mata shine tazo da buƙatarta,"
"Wace irin buƙata kenan"? Aunty babba ta tambaya tana kallonta,
Hafsat tace "Tayi mun magana akan cewa tana so in raba twins ɗincan da Omar ma'ana subar gidan nan gaba ɗaya, Suyi nesa dashi"
tsoki aunty babba taja tare da cewa "Ita kuma wacece ita isasshiya? halan Omar take so ne shiyasa ta biyo ta wurinki?.
"Bana tunanin hakan, Nafi tunanin Tasan Yaran ne shiyasa take son azubar dasu,"
"To ke kuma kin amince da buƙatarta kenan"?
Murmushi hafsar tasaki tare da cewa "eh mommy na amince da hakan, saboda anan take ta bani miliyan shida kuma tace muddin aikinta yaci ka zata ninkamin abunda tabani ynx,"
tuni aunty babba ta haɗe fuska rai a6ace tace "Amma ke shashashar ina ce? Kawai daga zuwan mata sai ki amince mata da buƙatarta? matar nan fa Omar take so shiyasa takeson a salwantar mata dasu,"
"Koma dai menene Mommy ni bazan bari kuɗin nan su wuce ni ba, saboda ina cikin buƙatarsu, daddy baya sakarmun kuɗi yadda ya dace ke kuma tanadin ki na zuwa wurin bokane kema fa bakya bani ko sisi Burinki akan hayaam da Abrah ne," .
Matsawa Aunty babba tayi kusa da ita tana cewa "Hafsat Anya kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kike faɗama haka"?
"Na faɗi wani abune daba dai dai ba? ta tambaya tana kallon mommyn nata, Ido cikin Ido
Sassauta Murya Aunty babba tayi a ƙoƙarinta nata fahimtar da hafsat tace "duk wannan tanadin da nake saboda kanmu ne fa ! Ƙaruwar mu ce, in har naci nasara akan burina Hayaam tasamu RAFAYET ita kuma Abra tasamu MARSHAL OMAR mune zamu ji daɗi, don haka am commanding u ki tattara kuɗin da tabaki ki mayar mata dasu yanzun nan !!!! ta faɗi a tsawace
Dariya hafsat ta kwashe da ita hada tafa hannu bayan ta tsagaita tace "Mommy kenan !! nima fa lashe Money ce kamarki, bazan bari garabasar nan ta wuce ni ba!! Akace da arziƙi a gidan wasu ƙwara agidanku, kai agidan nakuma kwara a ɗakinku, a ɗakinku ɗin ma ya faɗo akan ka, don haka ni baxan mayar mata da kuɗinta ba!!!!!!!!!
Gaba ɗaya hankalin aunty babba ya tashi don alamu sun nuna cewa Hafsat fa kamar bata cikin hayyacin ta, cikin ruɗi tace "Hafsat anya kina cikin Hayyacinki kuwa"?
Shu'umin murmushi hafsat tasaki sannan tace "Kwarai kuwa! nice dae ƴarki Hafsat ɗiyar general ishaq, jika ga Abban sojoji"
Jinjina kai aunty babba tayi tabbas an samu matsala, domin kuwa tasan Hafsat bazata ta6a fasa abunda tayi niya ba,
Huci kawai take yi tana jinjina kanta a ƙarshe ta fuce daga ɗakin,
Duk wannan suratan da Hafsat su kayi da aunty babba a kunnan Hosana wadda ke la6e a ƙopan ɗakin, jin Takon tafiyar Aunty babba yasa ta gudu izuwa cikin store ɗin da suke,
"Ina kika je hosana bakya jin magana ko? salon sai sun ganki? Mun samu yau sun ƙyale mu basuyi mana komai ba,
Jahad ce ke wannan maganar wadda ke atsaye tana kallon hosana,
Murya na rawa hosana tace "Jahad naji abunda su Hafsat ke cewa ita da Momynta,"
"Me suke cewa ne"? Ta tambaya tare da matsawa kusa da Hosanar don taji dakyau,
Hosana ta kora mata bayani tun daga farko har ƙarshe,
Jahad ta jinjina kai tare da cewa "Ashe buri yayi kama da mutun, shiyasa ta tsane mu kenan saboda tana tunanin cewa Omar zai iya son ɗaya daga cikinmu, ran nan tace mun batason mune saboda mun shiga tsakaninta da abun harin ta, Yanzu nagane inda ta dosa, To amma wacece matar da hafsat ta haɗu da ita yau? Wadda ke son A zubar mata damu!?
"Ni inaji araina jahad so suke su rabamu da ƴa'ƴa Omar kawai," hosana ce tayi maganar ido cike tab da kwalla don bata son duk wani abu yanzu dazai rabasu da Omar,
"Insha Allah burinsu bazai ta6a cika ba Hosana, baza su iya raba mu ba da yaya omar ɗinmu," tayi maganar tare da janyo hosana suka rungume junan su
__________________________________________
Tuni sun kammala aikin su na dinner, har sun kammala jerawa a dining Kowa ya bama cikinsa an ware, yanzu gidan ya ragu ba laifi kasancewar tun week ɗin daya wuce aka tura mutun Huɗu Aiki, Irfan jabeer, khaleed da Fawan duk basa nan, yanzu wanda suka ragu Acikin gidan Haroon, twins, junaid, Sai Marshal Omar da Sgr duk da basu cika zama cikin gidan ba suma, always working saboda suna bada gudummuwa sosai shiyasa koda yaushe suna headquater ɗinsu don ana buƙatarsu sosai game da insecurity ɗin qasar tamu, kasancewarsu kwararrune a6angaren aikin soja dama sun kasance international Armies, kowace ƙasa aduniya suna bada gudummuwarsu wurin kame tantirai sune maganin ƴan Iska, shiyasa sunansu ya shahara a faɗin duniya duk inda suka je, ansansu girmamasu ake gani kamar kamar me (Tiger da Lion) Kenan ba wasa 😇😇😇
SEHRISH
Shiga bedroom ɗinta tayi Wurin isha prayer, duk ta rame kamar ba Reeshi ba, alwala ta ɗaure a toilet, ta shimfiɗa sallaya, ta gabatar da salla, bayan ta kammala ta naɗe hijab da sallayar ta tura a wardrobe ɗinta, komai nata a slow take yinshi saboda rashin kwarin jikinta da fargabar da take fama dashi na Haroon,
Haye wa tayi saman gadonta tare da janyo pillow ta rungume tunani kala kala a ranta, hawaye ne suka soma gangarowa daga idonta sbd tuna yadda haroon ke ta6a jikinta, hannu tasa tana share su, daga bisa ni tayi lamo tana tunanin duniya,
Tana cikin wannan halin taji an kwankwasa ƙofa, shiru tayi bata Yi magana ba cike da tsoron waye ke mata knocking, ji tayi an sake buga ƙopar muryar na rawa tace "wanene"?
Muryar junaid taji yana cewa "Sehrish ni ne,"
Ajiyar zuciya tasaki jiki na rawa ta sauko tare da karasawa wurin kopar ta buɗe,
Gabanta ne yayi mugun faɗuwa ganin haroon hankali tashe tace "Kaineeee !!!!" a tsorace tayi maganar jikinta na rawa,.
Fashewe da dariya haroon yayi tare da wuce ta yashi ga ciki yana cewa "ƴar shila ni ne, ae nasan bazaki buɗe ba shiyasa nayi maki muryar junaid don na lura kuna good time dashi,'
juyowa tayi tana bin shi da kallo a razane,.
"Me ya kawo ka"!?
"Abunda yasa ba kawo ni, Yau nazo ne ayi ta taƙare, Haƙƙina nake son ki bani,"
Cikin shessheƙar kuka sehrish tace "Me kake nufi wai !!! Wani haƙƙi ka ke dashi akaina? Dan Allah kabarni nayi rayuwata cikin salama !! Ka rabu dani mana !!
ta6e baki haroon yayi tare da cewa "Na amince zan rabu dake, amma bisa sharaɗi ɗaya"? Ya faɗi yana kallonta fuska a ɗaure, a lokacin tadawo tsaye front of side drawer ɗinta tana facing ɗinshi,
Gabanta na faɗuwa tace "Menene shi"? Cikin sanyin murya tayi maganar
Haroon yace "Your Virgin!! shine abunda nake so,and if u do so i wll be out of ur life"
Fashewa da kuka sehrish tayi cikin tsananin jin ƙunci da raɗaɗi aranta, tuni zufa tagama wanko mata kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwa, tsanar haroon take ji kamar kamar me, tarasa amsar da zata bashi sai faman kerma take,
A tsawace haroon yace "Ke !!! Ki amsa mun kin amince ko baki amince ba"!?
A Firgice tace "Na'amince" ita kanta batasan ta bashi amsar ba saboda tsoratar da tayi da tsawarsa,
Wani irin shu'umin murmushi haroon yasaki, bin shi da kallo tayi ganin yasa hannu yana zare belt ɗin wandonsa, tuni ta runtse ido ganin gashin jikin shi, bakomai ya faɗo mata arai ba fa ce Sgr shine namijin da take so tafara kasancewa dashi arayuwarta bata buƙatar wani namiji in ba shi ba, shi take so ta mallakawa komai nata muddin ta mallake sa,
Jiki na rawa ta zura hannunta ta baya, taci sa'ar damƙar fititalar Kwan dake gefen gadonta, kafin haroon ya ɗago ta daddage da iya ƙarfin ta na ƙarshe ta ɗago da fitilar dake hannunta ta kwaɗa masa a tsakiyar kai !!!!! Ji kake KWASSS !!! A razane haroon ya ɗago jin saukar fitilar kafin yayi wani yunƙuri tuni Sehrish tabi ta gefensa ta watsa da gudu sai cikin toilet ta datse ƙopa sosai, ta sulale daga jikin ƙopan zuƙunne tana kuka don tasan dole haroon ya ɗauki matakin abunda tayi masa,
Ba ƙaramin buguwa haroon yayi ba, don wurin harya fashe Ae kuwa rai a tsananin 6ace yace "Ke don ubanki ni kika fasa ma kai"?
Sehrish dake acikin toilet murya cike da kuka tace "Ba dai ubana ba sai don Uban Mai zagi !! Fasiƙi ɗan iska insha Allah bazaka ta6a cin nasara akaina ba, sai Allah ya nuna maka iyakarka, wulaƙantacce kawai ƙazami mai warin baki,"
Tuni idon haroon sunyi jawur kamar garwashin wuta, ransa yayi mugun 6aci bai ta6a tunanin yarinyar zata iya mayar masa da martani ba, amma sai gashi yau ta zage shi tass,
"Bazan ƙyaleki ba, sai na wulaƙanta rayuwarki ba dai kina acikin gidan nan ba kuma zaki fito ba, zamu haɗu ne wlh," Ya faɗi tare da tunkarar hanyar fita yana mayar da belt ɗin wandonsa daya fara cirewa,.(ba'aci nasara😂)
Sehrish batayi shiru da bakin ta ba taci gaba da cewa " Ta Allah bata ka ba wlh !! Mugu azzalumi mummuna kawai, da wasu idanuwan ka kamar na Mujiya ni ina kokwanton Cewa anya kai Jinin Abban sojoji ne !! Sbd duk ƴa'ƴansa ba Fasiƙi irinka,"
Jinjina kai haroon yayi kawai yana huci, ya tura ƙopar ɗakin ya fuce,
Wani sabon kukan ta sake fashewa dashi, tana faɗin "wayyo Allah na nasan haroon baxai ƙyale ni ba, nashiga uku........'
Jiki na rawa ta miƙe ta nufi wurin bathroom cabinet ɗinta, akwai wasu Chemicals dake ajiye cikin toilet ɗin masu illah ga jikin mutun tamkar poison suke, ta riga ta yankewa kanta shawarar kwara ta kashe kanta ta huta da fitinar haroon,
Hannunta har kerma yake yi, wata ƙaramar roba ta ɗauko mai ɗauke da chemical ɗin, buɗe murfin tayi yayin da idonta ke zubar da hayawe, bakowa ya faɗo mata arai ba face Hosana Jahad, junaid, Aunty azmee uwa uba Burin ranta, yanzu shikenan duk zata rasa su? Zata mutu tabarsu?
Runtse idonta tayi aranta tana faɗin "bani da wata manufa face wannan, kuyi haƙuri ku yafe mun bazan Iya cigaba da rayuwa a wannan duniyar ba mai cike da tashin hankali, ban ta6a cutar da kowa ba, amma gashi wani nason cutar da rayuwata ....................."
Cikin sauri ta shiga zazzaga hodar abakinta
A dai dai lokacin Motocin Sgr da marshal Omar suka shigo cikin gidan atare jiniyarsu ta karaɗe ko'ina har cikin kunnan Sehrish
Zuciyarta ce taji tayi wani irin bugu, nan take kuma zuciyarta tace "Yanzu kin amince ki mutu baki cika burinki ba!? ke fa musulma ce ! Kin kuma son hukuncin wanda ya kashe kansa da gangan!!
Runtse idonta tayi hawaye na zuba, fuskar sgr kawai take tunawa da fuskar su hosana da jahad,
"Ina son sake sashi a idona," ta furta da wani irin sound, nan take tayi wurgi da robar chemical ɗin dake hannunta, cikin hanzari ta shiga amayar da wanda ke bakinta agaban basin, fanfo ta kunna tashiga kuskure bakinta da hanzari ta kora aman, sannan ta wanke face ɗinta ta fito,
tana tafiya zuciyarta na ƙara bata ƙwarin guiwa da cewa "Saboda wani shashasha zaki halaka kan ki, share hawayenki sehrish kina da damar rayuwa, wani banza bai isa ya tarwatsa miki burinki ba,"
Gyara jikinta ta shiga yi saboda tana son zuwa kai mishi dinner ɗinshi shi da Omar don ta son da yunwa suka dawo, duk da tana tsoran kada suci karo da haroon a fitarta,
dama riga da wando ne ajikinta, gashin bakinta kawai ta manna, ta gyara hular kanta da mayafin da take naɗe hular dashi, bayan ta kammala ta buɗe kopan cikin fargabar ta fuce,.
Ko'ina haske fauuu gidan cikin sanɗa ta wuce kitchen taji sanyi aranta ganin babu kowa,
Cikin hanzari ta shirya ma Omar nasa a tray, a palor ɗinsa takai masa babu kowa aciki alamar yana cikin bedroom ɗinsa, ajiye masa kawai tayi ta fuce, izuwa kitchen ta sake shirya wani a tray sannan ta wuce upstairs part ɗin BABBAN YAYA
Haryanzu jikinta kerma yake, kuma bata fasa maganar shan poison ɗin nan ba, burinta ta sanya Sgr a idonta 4 the last time before tabar duniyar, Baiwar Allah
Babu kowa a palor ɗinsa tsit kake ji sai ƙamshin dake tashi, shiga ciki tayi ta ajiye masa a saman table ɗinsa,
Tsayawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya yayin da idonta ke cike taf da hawaye, kamar daga sama taji muryarsa ta cikin bedroom ɗinsa yana faɗin "who's There"?
Runtse idonta tayi saboda jin sanyayyiyar muryarsa, daker ta dai daita natsuwarta tace "Tukur ne mai aiki,"
Voice ɗinsa tasake ji yace "Come In! i wanna see YOU Right now," zaro ido sehrish tayi jin abunda yace wato ta shigo ciki yana som ganinta 😳😳😳😳😳
Dake ta dai dai ta natsuwarta, ta tafi izuwa cikin bedroom ɗinsa kamar yarda ya umarta ta shiga da sallama"Assalamu alaikum"
"Wa'alaikum salam" ya amsa mata,
tsaye yake agaban mirror jikinsa sanye da sleeping dress riga da wando Milk colour masu ɗigon² baƙi ajikinsu ba ƙaramin kyau su kayi mishi ba, turarurruka yake ta fesa ma jikinsa,
Sam tagaza janye idonta akan shi daker ta iya cewa "barka da dare" ya amsa mata da "Yawwa" sannan ta ƙara da cewa "Gani"
Hannu yakai ya ɗauki kalbar turaren SHUMUKH ya feshe shi sannan ya mayar ya ɗauki wani turaren na Jar yana fesawa, mutun ne mai tsananin son ƙamshi shiyasa baya gajiya da bin jikinsa da turare,
Shiru sehrish tayi zuciyarta na ɗar ɗar, kusan 15 minsa sannan Boss Man ɗin yace "Ni zan zo ne"? Ya tambaya yana jiran amsa,
Cikin sauri sehrish ta ƙarasa hankali atashe ta tsaya daga bayansa jikinta na rawa,
Cikin natsuwa yaso ma magana" Wacece ke"?
Waro ido waje sehrish tayi jin abunda yace murya na rawa tace "Ni.....mai.....aiki...ne ...." a wani irin slow sgr ya juyo kai tsaye ya tunkare ta gadan gadan, a tsorace sehrish ke ja da baya tana kallonsa tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf a jikinta,
Sam idonsa basa a kanta ƙasa suke, har sai da suka ƙurewa bangon gaba ɗaya, yarfa hannu sehrish ta shiga yi a tsananin tsorace take karanto addu'o'in da duk suka zo mata abakinta, kuma abayyane take yi saboda tsaban ruɗi tuni ƴan hanjin cikinta sun motsa, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar wadda sanyi yakama,
Hannunsa yasa ya daki wall ɗin data ke manne ajikinsa ya aza hannun anan jikin bangon ya dafe sannan yace "ƙarya ke bana so arayuwata, am gonna ask u some questions idan aka min ƙarya za'a fuskanci matsala,"
Ya faɗi yayin da idonsa ke a lumshe tamkar a datse suke ba don komai ba sai don gudun kada mai aikin ya Sume a ƙaro na biyu saboda launin ƙwayar idonsa dake razanar da shi, .
Kallon shi kawai take yi zuciyarta na bugawa da ƙarfi, daker take haɗiye yawu ga wani fitsari daya matse ta tunda taji ya ambace ta da mace tasan cewa ya gano ta kenan,
"maca ce ko Namiji"? ya tambaya yana jiran amsa,
Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi, muddin tamasa ƙarya wannan ba ƙaramin shaqa zata sha ba,
Wannan shirun da tayi masa shiya fusata shi, buɗe Blue eyes ɗinsa yayi duka akanta , ta firgita sosai amma sam ta sanƙare ta gaza motsi da alama suman tsaye tayi
Hannunsa yasa ya damƙi hular kan sehrish yayi wurgi da ita tare da mayafin duka, nan take sumar kanta tasoma warwarowa tana saukowa saman kafaɗarta, kyakkyawan sumar kanta mai matuƙan kyan gaske ga laushi,
mayar da hannunsa yayi saman gashin bakin da take sawa ya cire shi shima, nan take ainihin kyakkwar fuskar reesh ta bayyana a matsayim mace 😊😉
sam fa bata motsi idonta sun kakkafe sun ƙame, kamar wata saƙago haka tayi,
jinjina kai sgr yayi maganar Adams ta tabbata, yayi mamakin ganin yarinya ƙarama kamar wannan da ƙarfin halin Yin shigar Maza tazo gidan sojoji aiki, ko nawa aka biyata don tayi hakan? Ya tambaya aransa, sam shi baya tunanin ta haura 12years saboda ƙarantarta dayake gani agabansa Ko shouder ɗinsa tsayin sehrish bai kai ba, daga tsaye inda yake yana kallon tsakiyar kanta saboda ba ƙaramin tsayine dashi ba, kowa yazo gabansa kallon ƙarami yake masa,
Janye hannunsa yayi daga jikin wall ɗin da sehrish take sannan yayi tattaki izuwa inda fridge ɗinsa yake, buɗewa yayi ya ɗauko bottle water mai sanyi sannan ya dawo inda take tsaye,
ya buɗe murfin ya yayyafa mata, a wani irin firgice sehrish ta girgiza ta dawo in sense ɗinsa, sai faman zazzare kyawawan idanunta take, bin chest ɗinsa tayi da kallo izuwa face ɗinsa cikin tsoro, hannu tasa ta shafa sumar kanta gabanta ne ya faɗi jin wayam babu yar hularta, hankali tashe ta wurga idonta inda sgr yayi watsi dasu.........nan fa tashiga faɗin "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un dan Allah kayi haƙuri.....nashiga ukuna........' tana kuka tana magana , gaba ɗaya yayi mata rumfa tamkar Zaki haka take ganin sa agabanta 😳😳😳
Idonsa na kumshe yana sauraronta left hands ɗinsa na riƙe da bottle water ɗin, yayin da ɗayan hannun kuma ya mayar dashi jikin bangon ya dafa, sehrish kuma na agabansa suna fuskantar juna,
"haɗiye wannan kukan bana so" cikin hanzari sehrish ta dakatar da kukan tashiga taitayinta, bakomai take kallo ba fa ce damtsen hannunsa, tunani kawai take yarda zai kai mata naushi tabbas tasan sai dai Uwarta ta haifi wata (Hafsat bature ana magana) 😂
Cikin natsuwa yasoma magana__________________________________
Abt payment 300 ne, still muna free pages ne wanda suka shirya 08103884440 sumin magana
👍
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
_Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo💫_
*Abban Sojoji part 2*
*EPISODE 2*
*💞LAFAZI WRITTERS ASSOCIATION*💞
Cikin natsuwa ya soma magana "tambaya biyu kawai Wacece ke? Kuma waya turo ki"?
Cikin rawar murya sehrish tace "Ni ba kowa bace ba, kuma babu wanda ya turon.......'. Interrupting ɗinta yayi da cewa "ki mun magana a hankali don bana fahimta sosai,"
Gyara muryarta tayi sannan taci gaba da cewa "Sunana Sehrish, kuma ni babu wanda ya turo ni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, aiki kawai nake don nasamu kuɗi........' buga wall ɗin da yayi yasata dakatawa a tsorace "Nace wa ya turo ki!!?
Hankali atashe tace "Allah shine shaidata, wlh ni babu wanda ya turoni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, ƴan uwana ne Basu lafiya an kwantar dasu asibiti ana buƙatar kuɗin aiki shine na nemi aiki gidan wata hajiya...............sehrish bata 6oye masa komai ba ta faɗa masa tass dalilin zuwanta da dalilin yin shigarta na maza batayi masa ƙarya ba ko kaɗan, ta ƙarasa masa labarin tana faman zubda hawaye tsoranta wane hukunci zaiyi mata don tasan watan Cin Ubanta ya tsaya, shiru su kayi na wani lokaci, kafin daga bisa ni Babban yayan yaja da baya ya juya
bedroom ɗinsa ya shige kafin daga bisa ni, ya fito hannunsa ɗauke da wayarsa wuri yasamu ya zauna saman sofa ɗin sannan yaba sehrish damar ta matso kusa, sai da tafara tattara hularta da mayafin da yayi watsi dasu, ta ruƙesu a hannunta sannan jiki asanyaye ta matsa inda yake kamar wadda tayiwa sarki ƙarya, jikinta sai faman kerma yake,
yace "su nan su? da sunan state da sunan hospital da aka kwantar dasu? and the date!?
Murya na rawa tace "Hosana Sayyad, da jahad sayyad an kwantar dasu a Fmc katsina........"
duka ta faɗa masa hada date ɗin da aka kwantar dasu duka don bata manta ba,
danna wayar yashiga yi kafin daga bisani ya danna calling, ta soma ringing, nan take aka ɗaga wayar suka soma magana,
Duk sehrish na tsaye tana kallonsa yadda yake speaking anatse,
Bakowa ya kira ba face Babban Likita, dama already sai da yafara tura masa message na sunan yaran da bayanan dayake son sani sannan yakira, kuma anci sa'a On duty yake,'
Tabbas yayi mamakin ganin kiran Surgeon general rafayet, kuma yayi mamakin jin sunan yaran da yakeson aduba mishi files ɗinsu, tabbas yasan yaran, waɗanda Omar ya taimaka daga wurin Police, ranshi ne ya bashi cewa may be Omar yasanar mishi game dasu ne that's why yake neman Information akansu , without wasting time Babban likita ya binciko masa files ɗinsu Hosana Da jahad na rashin lafiyarsu duka bayanan ya masa snaping dinsa ya tura masa ta whatsapp ɗinsa,
bayan sun kammala phone ɗin, Sgr ya shiga whatsapp ɗinsa ya duba, sai ga Files ɗin yaran na rashin lafiyarsu raɗau da sunansu ajiki Hosana Sayyad Da Jahad Sayyad,
Ajiyar zuciya yasaki yanzu ya shaida maganar Yarinyar duba time yayi dare yayi ga wani bacci daya ke ji gashi ko dinner ɗinsa bai cin ba, Ga yarinyar nan dake tsaye duk a tsorace don yana ganin yadda yatsun ƙafarta ke kerma,
gyaran murya yayi sannan yace "You're not guilty of anything, the mistake you made shine shiga na maza after knowing that it is forbidden in Islam for a girl to dress like a male,' yayi maganar yana danna wayar hannunsa...
Murya na rawa Sehrish tace "bazan ƙara ba........'
Jinjina kansa yayi kafin yace"As from now i don't wanna see u wearing this dress again! u can go" ya bata Umarni ta tafi
Wayyo Allah sam sehrish ta gaza rufe bakin ta don mamaki, kama hanyar fita tayi tana waiwayansa da kansa ya shiga saving dinner ɗinsa yana ci,
Tsantsar farin ciki ne ya cika sehrish sam ta rasa inda zata tsoma ranta, ae tana fita daga part ɗinsa ta buga Wani uban tsalle na murna fuskar nan kamar wacce akayiwa Albishir da gidan Aljanna, watsa wa tayi da gudu gudu sauri sauri tana tattaka Stairs ɗin tana saukowa down a babban falon dama ba kowa nan fa tashiga rawar murna tana zagaye sofas ɗin dake a falon kamar wata yar baby,
Duk wannan abun da take yi akan idon Sgr domin kuwa ya biyo bayanta ashe yana daga can Upstairs yana kallonta, don bai cika yarda da mutane ba shiyasa yayi following back ɗinta don yaga reaction ɗin da zata yi bayan da ta fita daga part ɗinsa,
abunda yayi tsammani ba shi ya gani ba, zura hannayansa yayi cikin aljhun wandon baccinsa yana kallon Ikon Allah,
Sam sehrish bata son babban yaya yana kallonta ba, ita kaɗai tasan farin cikin da take ciki, ta jima tana mamakin yarda Sgr ya kasance mai matuƙar sauƙin kai har haka a tunaninta zai bata horo mai tsanani daga nan akore ta kuma daga gidan,
Nace "*Sehrish ba ke kaɗai ba hatta Hafsat bature da sauran makaranta labarin rayuwarki sunyi tsammanin hakan tabbas Surgeon general Rafayet ya bamu mamaki, haƙiƙa shi ɗin na daban ne*"😍
Yanzu abunda ya rage wanda take yi ma fargaba shine sauran matasan gidan shin zasu amince a ranar da ta bayyana kanta a matsayin mace !? Uwa uba Abban su,kuma tuna wannan yasa jikinta yin sanyi, dakatawa tayi daga yin wasan da takeyi na zagaye gujerun babban falon, jiki a mace ta kama hanyar bedroom ɗinta, ranta ne ya bata cewa akwai mai kallonta, Cikin sauri ta juya ta kalli upstairs a time ɗin har sgr yabar wurin ya koma part ɗinsa
Ganin wayam yasa ta sauke ajiyar zuciya,ba ɗakinta ta wuce ba ɗakin aunty azmee ta wuce don sam tagaza daina murna tafison ta sanar mata abunda yafaru yau ɗin nan da zafi zafinsa,
Haryanzu hannunta na ruƙe da hularta da mayafin duka ta ƙanƙame su, tsayawa tayi a ƙopar ɗakin tana bubbugawa ,
Azmee dake zaune saman darduma tasha hijabi ajikinta ga qur'ani agabanta hannunta kuma na riƙe da Cazbaha sai faman gyangyaɗi take yi, jin bugun ƙopa yasata cewa "Wanene"
sehrish dake tsaye a bakon ƙopan tace"Nice aunty azmee"
Murmushi azmee tayi tare da cewa "Ashe bakiyi bacci ba," tayi maganar tare da tashi daga dardumar ta buɗe mata ƙopa,
Shiga ciki sehrish tayi tana faman zabga murmushi,
a ɗan ruɗe azmee ke kallonta bayan ta rufe ƙopan tace"Yau wata rana! Sehrish kece da Murmushi haka a fuskarki? Wane albishir ne akayi maki?Cos I forgot when last naga wannan annurin a face ɗinki" cikin mamaki azmee ke wannan maganar kafin ta mayar da idonta kan Hular sehrish dake ruƙe a hannunta ta kuma cewa "Ikon Allah yau kuma hularce da mayafin duka a hannu?
Dariya kawai sehrish take yi daker ta tsagaita tace "Aunty azmeee abun mamaki! Abun farin ciki !"
Cike da ɗoki azmee tace "menene shi?
Nan sehrish ta shiga zayyana mata abunda ya faru tsakaninta da Babban yaya daga farko zuwa ƙarshe
Baki washe azmee ta ɗaga hannunta sama tana cewa "Alhamdulillah ! Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala naji daɗin wannan lamarin sehrish domin kuwa Babban yaya shine nafi ji dama, gashi kuma cikin sauƙi ya amince wayyo Allah murna bansan inda zan sa kaina ba don daɗi" cike da jin daɗi azmee ke magana fuskarta a washe
Sehrish tace "Amma aunty azmee su fa sauran kina ganin zasu amince in suka sani"? Ni ina tsoran ta yarda zan fara fitowa a matsayin mace cikin gidan nan," tayi maganar murya asanyaye tana kallon azmee
Ƙarasawa azmee tayi ta dafa kafaɗarta sannan tace "Sehrish matsalarki tazo ƙarshe! tun da har babban yayansu ya amince ba ki da sauran damuwa, Abbansu ne kawai zamu jira muji ta bakinsa, yanzu abunda nake so dake kije kawai ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zamu ga yadda badaƙalar zata kaya idan matasan gidan nan suka ga tukur mai aikinsu a matsayin Mace lallai akwai tashin hankali, " azmee tayi maganar da dariya a fuskarta, sehrish kuwa dafe saitin zuciyarta tayi tana zazzare ido tace "Allah sa su amince suma,"
"Insha Allah" azmee tabata amasa afterwards suke yi sallama, sehrish ta koma bedroom ɗinta cike da zullumi haye wa tayi saman gadonta, ta janyo pillow ta rungume tana sakin murmushi tunawa da haɗuwarsu ta yau da babban yaya, Allah kenan a daren nan Haroon ya ƙuntata mata, har tayi addu'ar sai Allah ya nuna masa Iyakarsa akanta, to yanzu ga Iyakar tasa nan muddin sauran suka amince da ita kuwa, taci alwashin sai ta Ci mutuncin Haroon 😡👊
A fili tasoma magana " gajan haƙuri kenan Irin na ɗan adam, yanzu da na kashe kaina da shikenan nayiwa kaina, ashe Allah yana dab da kawomin sauƙi arayuwata," ta faɗi tana faman murmushi wani irin nishaɗi take ji ayau , ta kuma cewa "Anya ma zan iya bacci kuwa? gashi ina fargabar mai zai faru gobe? kwara kawai nayi Bacci na goben tayi saurin yi, AYI TA, Ta ƘARE kawai🙅, In jalasa jalasa 😂 in Zahaba Zahaba shine kawai 😅😂😹😹😹
tana gama faɗan hakan bacci yayi awon gaba da ita, kai kana ganin yadda reesh ke bacci kasan tana cikin kwanciyar hankali,
murmushi Hafsat Bature tayi tana kallonta wadda ke tsaye shigowarta kenan ta window tabiyo da suffar Farar Tantabara kasancewarta Aljanar sehrish, hannu tasa tajanyo bargo ta lullu6e sehrish dashi sannan ta 6ace 6aaat..............😇
______________________________________
Kwance suke acikin store ɗin su biyu abunsu, kamar yadda Jahad ta saba yi musu dabara, na jera masu jarkoki su koma kamar single bed sai su kwanta suna facing ɗin junansu sam bacci yagaza ɗaukarsu zullumin su mai zai biyo ba? Wata alƙibla rayuwarsu zata fuskanta yanzu?
"Jahad idan Aunty hafsat ta zubar damu ina kuma zamu dosa"? Hosana ta tambaya tana kallon jahad wadda ta zuba mata ido,
Cikin sanyin murya tace "Nima kaina bansani ba hosana, ina tsoran hakan," ta faɗi zuciya a karye
Hosana tace "Dama Allah ya ɗauke mu yakai mu duniyar sama ko? ko duniyar taurari inda ba mutane muyi rayuwarmu mu kaɗai tare da yaya Omar tunda kowa baison mu shi kaɗae ke son mu ko?
Wannan maganar ta hosana tasa jahad fashe wa da dariya daga kwancen da suke ta rinƙa 6a66aka dariya kaman kamar me,
Hosana ta ɗan 6ata fuska don ita bada wasa tayi maganar ba,
Daker jahad ta jinkirta da dariyar tace "Sorry hosana dole nayi dariya mana, wa kika ta6a ganin an ɗauke daga nan an kaisa sama ?
Shiru tayi tana zumbura baki, jahad taci gaba da cewa "sannan kince tare da yaya Omar kaɗai zamu tafi saboda yana son mu, Shin kin manta da Sehrish ne"? Ita kuma fa? akwai wanda yayi mana wahala ne kamarta? sehrish tana son mu fiye da kowa na duniyar nan, saboda mu tashiga duk wani hali da take ciki ayanzu duk da bansan yaya rayuwarta take ba...............wani irin kuka ne yaci ƙarfin jahad har takasa ƙarasa maganar da take yi,
Nan take jikin hosana yayi mugun sanyi tunawa da Sehrish ƴar uwarsu mai tsananin son su da ƙaunarsu, tuni itama idonta sun cicciko da hawaye murya na rawa tace "Ya Allah hada sehrish za'a ɗauke mu akai mu duniyar Taurari.....'
dakatawa da magana tayi ganin Jahad dake kuka ta fashe da dariya, wato tayi tazarce daga kukan da take Zuwa dariya ba don komai ba sai don jin abunda Hosana ke cewa, share hawayenta tashiga yi tana faɗin "Hosana wasan ya isa haka, muyi magana ta hankali, yanzu yaya za'ayi yaya Omar yasan halin da muke ciki kafin Hafsat da Momynta su sa azubar damu yakamata muyi tunanin hakan in ba haka ba zamu shiga wani mugun hannun ne ko mu ƙare rayuwarmu adaji..............' jinkirtawa tayi da maganar tana sauraron shawara daga wurin hosana,
"To ya zamuyi mu sanar mishi jahad? Bayan kullum waccen matar mai kama da samudawa mai kumatun alkubus tana tsare mu da ido duk in yazo tana hanamu kwakkwaran motsi,"
Shiru jahad tayi tabbas dole su nemi mafita in ba haka ba, zasu fuskanci tashin hankali
Can tayi wani dogon tunani tace "Hosana mai zai hana, mu samu paper da biro sai mu rubuta mishi, in yazo sai ki lalla6a kisan yarda zakiyi ki tura masa a aljihunsa? Ko da rungumesa ne sai kiyi kamar yarda kikayi a asibitin nan kin tuna"?
Murmushi hosana tasaki anzo inda keyi mata ƙaiƙayi kallon jahad tayi tace "Shawara mai kyau, amma taya zamu rubuta mishi to? Bamu da paper ba biro jahad,"
Shiru jahad tayi kafin tace "Akwai !!! Na tuna acikin wannan ɗakin da Momyn hafsat takaimu acikin wannan ƴar lokar naga Memo da biro,"
Cike da farin ciki hosana tace "dama ƙopa a buɗe take, yau ta manta bata rufe mu ba, jahad ki lalla6a ki ɗauko ki rubuta masa,"
Miƙewa jahad tayi tana faɗin "Zan fita dan Allah hosana karki biyo ni, nasan halin ki, in kika ja asirin mu ya tonu kashin mu ya bushe mu duka,"
Murmushi hosana tasaki tana cewa "sai dai in baki daɗe ba, kinsan ina jin tsoro fa nikaɗae anan,"
"Karki damu yanzu zan dawo,"
"To shikenan," hosana ta bata amsa,
Ficewa Jahad tayi cikin sanɗa take tafiya babu kowa wayam sai hasken daya gauraye ko'ina,
Wuce wa ɗakin tayi a hankali ta tura ƙopa tashige cikin hanzari ta nufi drawer ta zaro gidan farko ajikinta, anan taga memo ɗin da biron data gani,
Fiddo su tayi jiki na rawa ta aza memon asaman drawer ɗin dayake ƙaramace, daga zukunne jahad ta soma bude papers ɗin sannan ta aza biro ta soma rubutu kamar haka
_ya Omar naji ma inaso na faɗa maka halin da muke ciki, wlh bamu jin daɗin zama agidan nan, saboda basu son mu, uban aiki suke samu har bugun mu suke yi, dan Allah ya omar in kaga wannan takardar ka taimaki rayuwarmu kamar yarda kayi niya ka tafi damu inda kake rayuwa_
Kamar daga sama Jahad taji ance "Sannu da Ƙoƙari"!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
Jin wannan maganar a bayanta yasa jahad dakatawa da rubutun da take yi, hankali a matuƙar tashe idonta sun firfirto azare, jikinta ya soma wata irin kerma, Tuni Zufa ta soma gangarowa daga fuskarta da jikinta don bala'e hatta paper ɗin da take rubutun asamanta ta jiƙe sharkaf da gumin da take fitarwa 😳😳😳
*SHIN WACECE WANNAN*‼⁉❓❓❓
Mgnr payment 300 ne amun magana direct *08103884440*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
*Abban Sojoji part 2*
*EPISODE 3-4*
Sam jahad ta gaza yin kwakkwaran motsi saboda ta riga ta gane muryar wacece.......
Idasa shigowa tayi da wannan takun nata, jikinta na sanye da sleeping dress red colour masu zanen flowers ajikinsu, abunka ga fara ta fito 6au acikinsu, kanta ko mayafi babu ba kowa bace wannan face AUNTY BABBA,
Lokacin da ta isa inda jahad take, hannu tasa ta fisge takardar da take rubutawa, ta ɗago da ita tana karanta wa, zaro ido tayi hankali tashe tace "Keeeeee! Don ubanki ni zaki tonawa asiri!? Wato Omar kike rubutawa wasiƙa don ki faɗa mashi abunda muke yi maku ! Wlh kin shiga uku, bazan ƙyale ki ba sai kin yabawa aya zaƙinta!!!!
a masifance take magana ƙarshe tayi Wurgi da takardar ƙasa sannan azafafe da wannan hannun nata ƙirar samudawa ta damƙo mayafin dake lullu6e akan Jahad nan take ya sul6e ƙasa hakan ya bata damar damƙar gashin kanta, wani irin zafi ne ya ziyarci jahad saboda ruƙon da aunty babba tayiwa gashin kanta,
Janyo gashin tayi ta ɗago jahad dashi, jikinta sai kerma yakeyi duk ta rurruƙe hannun aunty babba dake ruƙe da gashin kanta tana faɗin "Aunty dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba....' bata ƙarasa ba aunty babba takai mata naushi a bakinta, nan take jini ya soma zuba daga bakinta le6enta suka faffashe, saboda tsananin azaba da raɗaɗi yasa jahad fashewa da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali,
Wurgi da ita aunty babba tayi jahad ta tafi jiki a mace ta zube ƙasa, tattakawa aunty babbba tayi izuwa inda take don bata gama dukan nata ba,
Tashi zaune jahad tayi tana jan jikinta da baya da baya tana faɗin "dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba.....nasan nayi kuskure....
"Ke ƙaramar ƴar iska ce ! bakisan koni wacece ba ! Har ni zakiyi wa iya shege acikin gidana ! Ni zaki tonawa asiri Wurin Omar? idan na so yanzu saina sa wuƙa na yanka ki, shashasha...
ta ƙarasa maganar tare da sake damƙo gashin jahad tashiga yi mata azaba dashi, ta ja shi da ƙarfi tamkar zata tsige shi daga kanta, tuni idon jahad yayi jawur wasu irin jijiyoyi suka firfito mata a goshin ta, don rashin imani aunty babba sai ta naɗe gashin a wuyan jahad ta shaƙeta dashi gadan gadan zata kashe ta, murya ashaƙe jahad ke fidda sounds tana faɗin "Ahh...ah..ann...bazan..ƙa..ra..ba' sam aunty babba bata da niyar ƙyale ta sai ma ƙara shaƙeta da take yi
Kamar daga sama Hosana ta faɗo ɗakin saboda tajiyo ihun jahad da farko sai tayi tsammanin kunnanta ne Suke mata gixau,amma rashin kwanciyar hankali da jin bugawar zuciya yasa hosana gaza samun natsuwa ta fito don tazo taga wani hali jahad ke ciki ta rubuta wasiƙar,
Shine ta taras da wannan tashin hankali, ihu tasaki a haukace ta watsa da gudu inda aunty babba ta shaƙe jahad ajikin wardrobe,
"Kada ki kuskura ki ƙaraso in ba haka ba zan haɗa dake kema," aunty babba ce tayi ma hosana wannan maganar batare da ta janye hannunta daga wuyan jahad ba, cikin kuka hosana ke faɗin "ki sake ta...! Ki kyale ta....kada ki kashe mun ƴar uwata.....' amma sam aunty babba taƙiya,
Ganin jahad ta soma kakarin sheƙawa barzahu yasa hosana fita hayyacin ta,
aikuwa ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe tasamu damtsen hannun aunty babba ta Gartsa mata lafiyayyen Cizo da hakoranta 30 cufffff
A firgice aunty babba ta saki jahad tana yarfa hannun ta sai ga jini na ɗigowa, cikin hanxari tasa ɗayan hannunta ta zame hannun rigar jikinta don taga inda hosana ta cije ta, wurin yayi jawur ga sahun haƙoran hosana nan rerass a farar fatar hannunta dama gashi dumurmur na ƴan hutu,
Cike da jin raɗaɗi tace "Innalallahi !ni kika ciza har kika fasa mun fatar jiki na !! Ya salammmm !! Kin mutu wlh !! Kin shiga uku !! tayi maganar idonta jawur saboda taji raɗaɗin cizon hosana wurin har wani Zogin azaba yake yi mata,
Ja da baya hosana tashiga yi a tsorace ganin aunty babba na tunkaro ta Kamar Damusa, gashi jahad tunda aunty babba ta sake ta, ta sulale ta sume a ƙasa balle itama ta taimaki hosana,
Hanyar fita ta nufa da gudu zata fice, cikin rashin sa'a aunty babba tasanya ƙafarta ta taɗiyo ƙafar hosana, aikuwa ba ƙaramin buguwa hosana tayi ba, gaba ɗaya ta kife ƙasan tiles ɗin ɗakin, fuskarta ta dake sa, nan take hancinta ya fashe jini ya soma kwaranyowa, haka goshinta ma ya fashe da La66anta duk sun farfashe ihun azaba kawai hosana ke saki tana faɗin "wayyo Allah na ....! Nashiga uku...na mutu na lalace !!
Aunty babba tace "baki mutu ba, don ubanki, yanzu ne zaki mutun.....tayi maganar tare da kai hannunta kan Gashin hosana wanda ya barbaje ƙasa, kwakkwarar damƙa takai masa, ta ruƙo shi dakyau ta janyo hosana dashi har sai da hosana ta miƙe tsaye tana ihu kamar ranta zai fita, daddagewa aunty babba tayi da iya ƙarfinta na ƙarshe ta buga kan Hosana jikin bangon ɗakin wayyo Allah zoka ga yarda jini ya wanke bangon,
Razanan nan Ihu hosana tasaki na azaba tamkar maƙoshinta zai ballo waje nan take ta sulale ƙasa a mace.......
Ihun da hosana tayi na ƙarshe wanda ya karaɗe ko'ina harya sa Hafsat dake kwance ɗakinta saman gadonta farkawa a firgice, ta diro daga saman gadonta jiki na rawa ta fito ta tunkari inda sautin ke fita cikin hanxari ta faɗo ɗakin,
gabanta ne yayi wani irin bugu ganin Momynta a tsaye tana huci kamar wata zakanya, ga kuma twins ɗin da Omar ya kawo a baje ƙasa jina jina musamman hosana an zubda jini
Hankali tashe hafsat tace "Mommy me nake gani haka !! Me kika yi masu ne !! Kashe su Ki kayi da hannun ki !!!
tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa "Eh kashe su nayi,akwai magana ne ! babu ruwanki dani ki koma ɗakinki zai fi miki,"
Cikin rauni hafsat tace "mommy duk rashin imani na bazan iya aikata abunda kika aikata ma yaran nan ba, ashe baki da Imani ko misƙala zarratin ! Kisan kai da hannun ki........'
Bata idasa maganar ba saboda jin saukar wani irin zazzafan mari a kuncinta, tashin hankali da ba'a sama shi rana,
Saboda zafin marin da aunty babba tayi ma hafsat yasata dafe kumatun ta ido jawur take faɗin "Mommy yau ni kika mara da hannun ki"?
"Naje na mara ! duk kece sular da kika 6atamin raina harna aikata abunda na aikata yanzu!!"
shiru hafsat tayi yayin da idonta ke fitar da wasu irin siraran hawaye masu zafin gaske,
Jikin aunty babba ne yayi mugun sanyi ganin hawayen dake fita a idon hafsat ƴarta tilo,
Cikin tashin hankali tace "ba da son raina nayi hakan ba ! Hafsat ke kika 6atamun rai da 6acin ranki na kwanta, cikin daren nan na fito saboda zuciyata batamun daɗi kawai naga yarinyar nan jahad ta nufo ɗakin nan shine na biyota in ga mai zatayi ashe wasiƙa zata rubutama Omar akan abunda muke aikata musu, da nufin inyazo su bashi.......yanzu yaya zanyi hafsat....na kashe su ba'a hayyacina ba...In Omar yazo bansan me zan faɗa masa ba......" tayi maganar tana yarfa hannunta idonta cike tab da hawaye cikin tashin hankali,
Murya na rawa hafsat tace "Mommy kin ja mana masifa da bala'e duka, ni banji xafin marin da kikayi mun ba, domin wannan kaɗanne akan Marin da zamu kar6a ni dake a wurin Yaya Omar wlh bazai ƙyale mu ba !! Yadda kika kashe su ke ma haka zaisa ayi maki hukuncin kisa babu ruwana ......
Cikin shesshekar kuka aunty babba tace "Hafsat yanzu don na kashe waɗan nan tsintattun marasa galihu nima sai Omar yasa akashe ni?
A tsiwace hafsat tace "Eh.!! dama menene alaƙarki da Shi da zai tausaya miki? Kwarama Ni zan tsira ke kuwa Yayansa kawai kike aure !! Wlh mommy kin shiga uku gaki can an garƙame ki a cell ƙarshe a yanke maki hukuncin ɗaurin rai da rai har sau biyu saboda rai biyu kika kashe.......
Hannu aunty babba ta aza akanta tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga Uku Ni LAILA naja ma kaina mutuwa a lokacin da ban shirya ba,
Jiki a mace aunty babba ta zuƙunna inda hosana take kwance a mace tana faɗin "kee!!!kee!!! tashi !! Maza ki tashi don ubanki ! Wlh baxa ku jamin bala'i ba, hafsat ɗauko mun robar ruwa a fridge dan Allah in yayyafa musu ko sun tashi
tayi maganar tana kallon hafsat, fuce wa hafsat tayi da sauri sai gata ta dawo hannun ta ɗauke da bottle water ta miƙa mata, kar6a Aunty babba tayi jiki na rawa ta cizge murfin tashiga yayyafa ma hosana ruwan ajikinta,
Gabansu ne ya faɗi atare ganin hosana ko motsi batayi duk sanyin da ruwan yayi hakan na nufin ta mutu kenann !!!!!!
tuni fuskar aunty babba tayi jawur kamar wadda aka nannausa saboda tashin hankali
A ruɗe tace "Hafsat mun shiga uku !! Mun lalace !! Wlh ta mutu wayyo Allah na ni laila......
Hafsat dake tsaye hankali atashe itama aruɗe tace "wlh Mommy laifinki ne, kece saurin fushin tsiya ga zafin zuciya gashi nan kin kashe su, To ni wlh babu ruwana aciki, dama ban da wata alaƙa dake haihuwata kawai kikayi.......
ɗagowa aunty babba tayi ta kalle ta ido jawur cikin disashewar murya tace "Hafsat ni kike ce ma baki da wata alaƙa dani, saboda ƙaddara da tsautsayi sun rutsa dani.....'
Cikin kuka hafsat tace "Ae gaskiya na faɗa mommy ! ina bacci na kin katse mun shi da wannan tashin hankalin, Allah mommy ba abunda zai hana Omar yasa a garkame ki a cell , har na hango ki cikin kayan gidan yari Allah bazasu yi maki kyau ba yadda kike haka ɗin nan........' tayi maganar tana nuna aunty babba dake zuƙunne agaban hosana kamar buhun masara,
"Yanzu ya zamuyi ? Hafsat kar6i robar ruwan ki yayyafa ma ɗayar muga in ita zata tashi, wataƙil ita In tafarka sai in samu sassauci awurin yanke mun hukuncin......
Cikin sauri hafsat ta kar6i robar ruwan dake hannun aunty babba ta ƙarasa inda jahad take tashiga yayyafa mata shi a fuskarta, Wani irin dogon numfashi jahad taja kafin tace "La'ila ha illallah Muhammad rasulillah....
Ganin jahad tafarka yasa aunty babba tashi tsaye ta tunkare ta tana faɗin " Alhamdulillah saura ɗayar yaya zamuyi hafsat ? Kodai kawai mu binne gawarta a cikin garden ɗin gidan nan ne?
Wani irin kallo hafsat tayi mata tare da cewa "ashe mommy hankalin ɗiyar roba ke gare ki? mu binne gawa acikin gidan nan ? Idan fatalwarta ta tashi fitowa ke zata fara ziyarta Allah,
Hannu aunty babba ta aza akai tana faɗin "Ya salam duk ni naja ma kaina"
daker jahad ta buɗe idonta wanda suka kumbura sukayi jawur, ga le6anta sunyi sutum sutum inda aunty babba takai mata naushi,
Idonta bai sauka akan kowa ba sai kan hosana dake baje ƙasa jini duk ya wanke fuskarta......
Da ƙarfi ta furta "Hosanaaaa !!!!!!!!!,' tamkar bakinta zai tsage yunƙurawa tayi ta tashi a tsananin razane ta ƙarasa inda hosana ke kwance ta zube saman guiwowinta tana faɗin "hosana ki tashi ! mai ya faru dake ne? Wa yayi maki haka !! Innalallahi'wa'inna ilaihirraji'una .....ta ƙarasa maganar tare da kifa kanta jikin hosanar tajima bata ɗago ba sai daga baya ta ɗago da kan nata tana faɗin "Dan Allah ku kaita asibiti kada ta mutu !! Kada narasa ƴar uwata,"
Kallon juna su kayi sai yanzu suka mayi tunanin zuwa asibiti don sam basuyi tunanin hakan ba,
Jiki na rawa hafsat tace "mommy ki ɗauko ta, bari naje room ɗina naɗauko mukullin mota mu tafi,"
Aunty babba tace "Toh,ki tahomun da mayafi dan Allah"
fucewa hafsat tayi tana faɗin "kiyi sauri mommy,"
Cikin hanzari aunty babba ta ƙarasa jiki na rawa, ta cuccu6i hosana ta aza aka faɗarta ta fuce da ita daga ɗakin, itama jahad ta bisu abaya
Fitowa hafsat tayi itama a lokacin har aunty babba ta buɗe back seat na motar ta kwantar da Hosana aciki itama jahad tashiga ciki sannan ta rufe,
Su kuma suka shiga front seat hafsat na a mazaunin driver ita kuma tana a gefenta,
Da gudu hafsat ta tada motar taja ta a tsiyace suka nufi hanyar fita daga gate ɗin gidan
Nan take sojojin dake gadin gidan suka tunkaro su don jin ba'asi
Aikuwa a masifance aunty babbba ta ɗaga murya tana cewa "Nice nan zan fita kar in ga wani shege ya tare mun ƙopa Wlh in bi takansa....'
Jin muryarta yasa su kayi baya baya suka bata hanya ta wuce.......... da gudu suka miƙi titi sai asibiti, kuma duk da haka sai da sojojin nan suka biyo su abaya saboda aikinsu ne basu tsaro musamman acikin daren nan,
Suna isa asibitin gudu gudu sauri sauri Aunty babba ta ɗauki hosana suka shiga ciki,da hanzari reception nurses suka karbe ta aka shiga da ita ciki, anci sa'a an samu likitan dake a bakin aiki, cikin gaggawa suka shiga duba hosana,
Su kuwa su aunty babba da hafsat suna atsaye sai faman zagaye suke kowa cike da zullumin abunda zai biyo baya in yarinyar ta mutu, jahad kuwa tana abakin ɗakin da aka kwantar da hosana ta kwantar da kanta jikin door ɗin idonta na tsiyayar da hawaye masu ɗumi,😭
Gaba ɗayansu babu wanda ya samu bacci adaren nan saboda da tashin hankali,
(Na zubda hawaye saboda halin da su Hosana da jahad suke ciki Ya Allah ka kawo masu ɗauki) 😭
______________________________________
Ana cikin kiran sallar asuba Sehrish tafarka a hargitse tana faman dafe saitin zuciyarta dake yi mata wani irin raɗaɗi, sai faman ambaton sunan Allah take yi, tabbas ranta na bata cewa wani mummunan abu ya faru dasu Jahad, cikin hanzari ta sauko daga saman gadon tana faman zagaye ɗakim kafin daga bisani ta shiga cikin toilet ta ɗauro alwala,
Fitowa tayi ta nufi wardrobe ɗinta, hijab ta ɗauko da darduma ta shimfiɗa, ta shiga jera sallah, bayan ta kammala ta zauna tare da ɗaga hannayenta sama tana addu'o'i akan su hosana da jahad da sauran al'ummar musulmai, ta jima tana addu'ar kafin ta koma saman gadon nata ta kwanta tana fuskantar sama abubuwa iri iri na zuwa mata aranta daga bisani bacci ya kwashe ta, bata sake farkawa ba sai ƙarfe 10 na safe,
Firgit ta farka har time ɗin shiga kitchen ya wuce,
Zumbur ta miƙe shaf shaf ta shirya cikin shigarta ta maza da ta saba, saboda zullumi bazai barta ta fita a matsayin mace ba, a hankali ta tura ƙopa ta fuce izuwa kitchen,
Bin ta da kallo azmee tayi wadda ke gyara kitchen don harta kammala breakfast ɗin already tun ɗazu,
Da mamaki tace"Sehrish ya akai naganki kuma da shigar maza?
Shiga ciki tayi tana cewa "Aunty azmee ni tsoro nake ji Allah,"
"Wani irin tsoro kuma,ba wani tsoro abunda nake so dake bayan mun kammala jera abinci, sai ki koma ɗaki ki cire wannan gashin bakin ki sauko da gashin kanki zan kira ki, sai ki fito a matsayin mace"
Shiru tayi tana kallon yatsun hannun ta kafin tace "shikenan Allah yasa komai ya tafi adai dai,
Murmushi azmee tasaki tare da jinjina kai tace"Insha Allah yanzu bari na fara jera miki warmers ɗin kina kaiwa dining,"
Ta amsa mata da "toh", tana jin ɗar axuciyarta
Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala jerawa, Ayaan da Jahan ne suka fara fitowa sanye cikin kakinsu gwanin kyau, Suka samu wuri suka zauna kusa da Juna, azmee ta soma saving ɗinsu, time ɗin sehrish ta shige bedroom ɗinta don ta kimtsa kamar yadda su kayi da azmee zata fito a matsayin mace,
Bayansu sai kanal yusif ya fito shima sanye da Jallabiya launin ruwan toka, wuri yasamu yazauna yana gaishe da aunty azmee, da fara'a take amsa musu, cikin girmamawa su twins suka gaishe shi shima ya amsa musu daga bisa ni kowa ya mayar da hankali kan breakfast ɗinsa,
Sehrish na cikin ɗaki cike da zullumin yarda za'ae ta fito a matsayin mace, tana a jikin ƙopar ɗakinta tana ruƙe da handle ɗin kopar cike da fargaba,
Gyaran murya azmee tayi ta ɗan ɗaga murya tare da kwaɗawa sehrish kira da sunanta tace "Sehrish ki fito mana,"
Jin sunan da azmee ta ambata yasa su kallonta da mamaki, sake maimaitawa tayi "Sehrish ki fito nace,"
Kallon juna Ayaan da jahan su kayi sannan suka kalle ta atare suka haɗa baki wurin cewa "Wanene Sehrish kuma? Kanal yusif shima cike da mamaki yake kallon azmee jin sai faman kwala kira take yi, zuba ido su kayi don suga wanene wannan sehrish ɗin da Azmee ke faman kira, shin baƙo su kayi ne a gidan nasu ko kuwa?
buɗe ƙopa sehrish tayi gabanta na faɗuwa ta tunkaro hanyar dining area ɗin, jikinta na kerma a tsorace take tafiya,
gaba ɗayansu suka ɗago suna kallon ta tun kafin ta idasa bayyana a area ɗin da suke, bin ƙafafunta su kayi da kallo waɗanda ke sanye da ƴan silifas ɗinta na gado, sai faman kerma yatsun ƙafarta suke yi,
Time ɗin da sehrish ta idasa fitowa a raxane jahan ya miƙe tsaye, ayaan kuwa baisan lokacin da ya saki cokalin dake hannunsa ba ya faɗa cikin plate ɗin dake agabansa, kanal yusif kuwa kallon abun yake kamar a mafarki,
Bin ta suke da kallo cikin mamaki, kamar a mafarki suke kallon lamarin, ƙarasowa tayi ido a zazzare jiki na kerma, riga da wandon nan ne ajikinta , ta cire gashin bakinta, ta kuma zuba da doguwar sumar kanta har gab da waist ɗinta, ta fito asalin macen ta Tsaleliyar budurwa ƴar matashiyya,
A rude jahan yace "Azmee who's she ? daga ina ta faɗo cikin gidan nan? Da iznin wa!?
Ayaan kuwa cewa yayi "Ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba ! Wannan Hurool ainin fa? daga aljanna ta gudo?
Kanal yusif sam yagaza magana bayani kawai yake jira daga wurin azmee, ita kanta azmee ta ɗan razana da reaction ɗin da suka bayar, Sehrish kuwa a gefen azmee ta tsaya tana faman zare ido,
"Azmeee Explain !!!!' jahan ya faɗi azafafe harda dakar table ɗin gabansa da tafin hannunsa,
Murya na rawa azmee tace " Kuyi haƙuri dan Allah...Am wannan da kuke gani ba kowa bane face Tukur mai aikin ku, nasan zakuyi mamakin hakan......
Dakatawa tayi ganin yarda Ayaan da kanal yusif suka miƙe atare, cike da ruɗu Kanal yusif yace "What ! Wai wane tukur ɗin ake magana ! Ba dai wannan yaron mai aikin namu ba, kina nufin dama mace ce ba namiji ba ....? Ya tambaya hankali atashe ,
Daga sehrish har azmee sun tsorata,
Hannu jahan yasa yasake bugun table ɗin abincinsu yace "Impossible bazai ta6a yiyuwa ba ! muddin kuwa hakan ta kasance dole yarinyar nan ta fuskanci hukunci mai tsanani kuma tabar gidan nan ayau ɗin nan,
Fashewa da kuka sehrish tayi saboda tsorata da maganar Jahan gashi idonsa na akanta ya zare su,
"Dan Allah ku kwantar da hankalin ku, laifi ne nasan ta aikata amma kuyi mata afwa, sam bata da niyar cutar da kowa.....' dakatar da ita Ayaan yayi da cewa "Ba wannan zancen ! Saboda ƙarfin hali irin na Yarinyar nan, tayo shigar maxa ta saje acikin mu tana mana aiki, babu sirrin mu da bata sani ba, babu irin firar da bama yi agabanta, har yawo muke yi da towel a ƙugunmu, muyi yawo da gajerun wanduna duk idonta na akai, kaf ta haddace ashe kallon mu kawai take yi,"
bil'haƙki ayaan yake kora bani, gaba ɗayansu ba komai suke ji mawa ba face yadda sehrish ta saje A cikinsu matsayin namiji na tsawon lokaci tana masu aiki, duk a tsammaninsu namiji ne ashe maca ce, tagama sanin sirrinsu saboda babu irin firar da basa yi agaban ta, sannan babu irin shigar da basa yi suna yawo duk a idonta,
Hannu Jahan yasa yana ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa da nufin ya jibgi sehrish saboda yafi kowa fusata, gashi dama su Mace bata agabansu balle suga kyanta ko wani abu haka don su tausaya mata,
A tsorace sehrish ta ƙanƙame kanta ta 6oye abayan aunty azmee tana faɗin "Nashiga uku ! Dan Allah aunty azmee ki basu haƙuri, kada su buge ni...zan tafi nabar musu gidan,
ture kujerar gabansa yayi gadan gadan ya tunkari sehrish zai jibge ta,
Kamar daga sama suka ji Muryar Abban su yace "Kada ka kuskura ka ta6a ta!'
Atare suka ɗago suna kallonsa kowannan su na huci,
Ruƙe yake da hannun junaid cikin nasa, yana sanye da jallabiya junaid kuma na sanye cikin riga fara da wando baki, ya tsorata da ganin halin da sehrish ke ciki gashi kuma yayi mamakin ganin ta ta bayyana kanta a matsayin mace, ga kuma jahan tsaye ruƙe da belt wato zai jibge ta,
Idasa isowa sukayi inda suke tunkan abbansu yace wani abu Ayaan yace "Daddy dama wannan yaron tukur mai aikin gidan mu mace ne ba namiji baa !!
murmushi Abbansu yasaki yana kallon su yadda duk suka zabura,
Mayar da idonsa yayi kan Yarinyar dake 6oye abayan azmee yace "Ke zonan,"
"Sehrish ki fito Abbansu na kira,"
Azmee ce ke tunasar da ita, fitowa sehrish tayi jiki na kerma ta ƙarasa inda Abbansu yake tsayawa tayi at front of him murya na rawa take faɗin "dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun, nasan nayi laifi wlh ni banzo da niyar na cutar da kowa ba.....'
tsawa Jahan ya daka mata da cewa "Rufe ma mutane baki kona zo nan na nakaɗa miki shegen duka,"
Abbansu yace "Ya isa haka Jahan, bana so kowa yasake magana," shiru su kayi gaba ɗayansu suna sauraron mai abban nasu zai ce,
Shin ina haroon duk wannan abun dake faruwa yana a tsaye fitowarsa kenan, gaba ɗaya ransa ya gama jagulewa mamakinsa yarda akai yarinyar ta bayyana kanta A matsayin mace bayan bai idasa cimma burinsa ba, na tsoratar da ita, Amma ganin yadda su Jahan suka fusata yasa shi jin daɗi aransa burinsa karsu amince su tada 6alli sai anyi mata horo sannan a koreta shi kuma zaiyi amfani da wannan damar wurin ƙuntata mata,
tsayawa yayi da murmushin mugunta a fuskarsa don yaga ya ƙarshen bada'ƙalar zata kaya,
Daga shi sai gajeran wando fari ajikinsa tsaye ruƙe da ƙugu, ɗayan hannunsa na ruƙe da Brush da alama ma daga toilet ya fito,
burinsa yaji mai Abban nasu zai ce,
gyaran murya Abbansu yayi sannan ya soma cewa "Na riga da nasan komai game da yarinyar! Domin junaid ya jima da sanarmun komai agame da ita, duk abunda junaid ya nuna yana so aduniyar nan koma menene shi zan amince dashi, Junaid ya nuna cewar yana son Zaman yarinyar nan agidan nan, don Haka Na AMINCE masa,!"
Cikin mamaki suke kallon abban nasu, Haroon kuwa tuni yayi wata irin raxana har Brush ɗin dake hannunsa ya faɗi ƙasa sbd jin abunda Abbansu yace,
Murmushi kawai junaid ke saki, kallonta Abban su yayi tare da cewa "Ya Sunan Ki"? Sehrish dake tsaye agabansa idonta cike tab da kwalla duk ta tsorata murya na rawa tace "SEHRISH"
Jinjina kai Abbansu yayi tare da sa hannun shi ya shafa gefen fuskar sehrish yace "Daga yau Ba sunanki Sehrish ba,"
cikin mamaki suke kallon Abban nasu, itama sehrish ɗin kallonsa take tana jira taji sunan daya canza mata, azmee kuwa Alhamdulillah kawai take faɗi aranta,
"Kinsan menene sunan ki daga Yau"? abban nasu ya faɗi yana kallonta,
Cikin sanyin murya Reesh tace "a'a".
murmushi Abban nasu yayi sannan yace "daga Yau sunanki *SEHRISH SALAHUDDEEN HUSSEIN ABBAN SOJOJI*"
😇😇😇
Sakin baki su kayi suna kallon Abban nasu
Duk wannan Abun dake faruwa akan idon SGR wanda ke saukowa down stairs jikinsa na sanye da t-shirt mai gajen hannu baƙa, sai dogon wando fari, sun bi shape ɗin jikinsa ya fito Handsome stylish ɗinsa, ya ɗaure sumar nan ta baya ba ƙaramin kyau yayi ba, a hankali yake tattaka steps ɗin cikin tafiyar nan tasa ta majiya ƙarfi, duk suka ɗago suna kallon shi................
__________________________________
Ku hanzarta yin Payment don in na tashi dakatawa gaba ɗaya ne wanda suka shirya suyi mun magana direct = 08103884440*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
*💫LAFAZI WRITERS ASSOCIATION 💫*
*Abban Sojoji part 2*
*EPISODE 5-6*
Ida sa iso wa inda suke sgr yayi idonsa yakai kan Jahan daya zare belt ruƙe a hannunsa, tunkan yayi magana jahan yayi hanxarin mayar da belt ɗinsa, mayar da idonsa yayi kan Abban nasu tare da cewa "Gm dad fatan an tashi lafiya," murmushi Abban su yasaki da cewa "Lafiya Lou son ina fata kaima haka,"
Sgr yace "Alhamdulillah," sannan ya samu wuri ya zauna saman ɗaya daga cikin dining chairs ɗin, kowa so ya ke yaji mai Babban yayan nasu zai ce, musamman haroon burinsa Sgr yace bai amince da zamanta ba, don yasan in dai yace hakan to Zaman sehrish ya ƙare a gidan,
Ita kuwa sehrish hankalinta kwance saboda tasan yarda su kayi jiya dashi haka azmee ma, gyaran murya sgr yayi kafin yace "tsayuwar me kuke yi"? Ya tambaya yana kallon su jahan Ayaan da kanal yusif, koma wa su kayi kowa ya xauna junaid ma yasamu wuri ya zauna, sai Abban nasu dake tsaye sehrish na agabansa yaci gaba da cewa "daga yau kin zama ƙanwarsu kema ƴa' ce acikin gidan nan, duk wani abu da uba keyi ma ƴarsa nima zan miki shi, kuma duk wani abu da junaid zaiyi acikin gidan nan kema zaki iya yin shi, kuma duk wanda yayi yunƙurin 6ata miki acikinsu ki sanar mun zaki ga yarda zanyi dashi,"
Zuru su kayi suna sauraron Abban nasu, sehrish kuwa murmushi kawai take saki koba komai yau tasamu Uba wanda zatayi prouding dashi a faɗin duniya,
ɗago idansa yayi ya kalli Babban yayan nasu, wanda azmee taci gaba da saving ɗinshi breakfst ya kira sunan shi "RAFAYET" amsa wa yayi da "Na'am Abba," batare da ya juyo ba ya kalle su,
Abban yace "Ina fata kaji komai ga me da yarinyar nan ? bansan ko kana da abun cewa ba" ya tambaya yana kallonsa,
kowa ya saurara don jin ta bakinsa, haroon Allah Allah yake akan Babban yaya karya amince da zamanta,
Boss man ɗin sai da ya gama sipping Coffee ɗin dake hannunsa a natse sannan yace" Umarninka Shine abun bi" amsar da ya bayar kenan, wani irin farin cikine yaci ka Abban nasu saboda shi da yake tunanin zai ƙiya gashi ya amince da duk jawabinsa kai tsaye ma yace Umarninsa shine abun bi, wato duk abunda yace game da yarinyar ya amince,
"Kufa kuna da Abin cewa"? Abban nasu ya tambaya yana kallom su, cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Abba ae magana taƙare kawai tunda Babban yayan mu ya amince mu su wanene da baza mu amince ba"?
Wannan maganar tasu tasa Azmee yin ƴar dariya ƙasa ƙasa,
Jinjina kai Abban su yayi sannan yace "hakan yayi mun, sannan ko da gigin wasa ban amince wani ya cutar mun da ƴa ta ba,"
"An gama magana Abba" suka bashi amsa atare yace "Yawwa haka nake son ji, sannan ya mayar da idonsa kan Sehrish wadda ke faman sakin murmushi tayi zuru tana cizar akaifar hannunta da takai bakinta, ba kowa take tunani ba face Haroon yadda zata Zazzaga mashi rashin mutunci, dama taci alwashin hakan
Muryar Abban su ce ta katse mata tunanin nata da cewa " daughter ki zauna kiyi breakfast tare da Abban ki da kuma ƴan uwanki," ɗan zaro ido sehrish tayi jin yace zata zauna taci abinci acikinsu cikin mamaki tace "Abba anan," tayi maganar tana nuna dining table ɗinsu,
"Eh nan nake nufi" ya bata amsa sannan ya ruƙo hannunta gavan ta na faɗuwa suka samu wuri suka zauna tana gefen Junaid Abbansu kuma na gefenta sun sa ta tsakiya, Babban yayansu kuma Na a side ɗin Abban nasu, ta hannun dama yayin da suke facing Ayaan Jahaan da kanal yusif su da suke hannun haggunsu,
"Azmee ke ma ki samu wuri ki zauna A cikin mu," abban su ya faɗi yana kallonta ,
da fara'a a fuskarta tace "ngde ssae Abba, amma ni nafison a barni a iya matsayi na, nafi jin daɗin kasancewata haka, dama damuwa ta Sehrish ce gashi kuma ta samu Ƴanci ka ƴanta ta, Allah ne kaɗai zai iya saka maka, haƙiƙa kai na musamman ne ka kasance ɗaya daga cikin mutanen da ake Alfahari dasu aduniya kuma ake alfahari da Ƴa'ƴansu kowa burinsa yayi koyi da kyawawan ɗabi'unka da halayanka Abba ba abunda zamu ce sai dai Allah yaci gaba da tsare mana kai, ya tsare zuri'arka, Ya kare ka daga sharrin mahassada da maƙiyan ka, Allah yaci gaba da ɗaukaka darajarka da ta ƴa'ƴanka a faɗin duniya, kamar yadda kake faranta ma wasu Kaima Allah ya faranta maka aranar gobe ƙiyama yasa Aljanna tazama makomarka................azmee bata tsaya ba haka taci gaba da yiwa Abbansu addu'oi' dasu kansu , gaba ɗaya sunji daɗin addu'o'inta kuma dukkansu suke amsa mata da Ameen ameen,
daga bisa ni kowa ya mayar da hankalinsa ga abincin dake agabansa zanso kuka sehrish duk ta gaza samun natsuwa ba wai don bata jin daɗin kasancewarta atare dasu ba, sai don tsoran su ayaan da jahan da take yi, saboda wani irin kallo da suke mata Sam tagaza gane kallon menene wannan, dama fa su ƴa'ƴan Alexandra wuyar sha'ani ke gare su kamar uwarsu haka suke basu cika yarda da mutane ba ko kuma sake musu, junaid ne kawai mai sauƙin kai saboda kaf halayansa shigen na Abbansu ne,
shin wai ina haroon ? Ae tuni ya koma cikin bedroom ɗinsa cikin tsananin ƙunci ransa yayi mugun 6aci sai faman yawo yake a ɗakinsa cike da jin baƙin ciki aransa sai faman huci yake bakowa yafi bashi haushi ba face Abbansu da Babban yayansu saboda sune suka nuna Amincewarsu da ita, a can ƙasan zuciyarshi kuma bakowa yafi ƙuntata masa ba fa ce*JUNAID* Saboda shine silar komai daya fara sanar da Abbansu akan maganar yarinyar, dama junaid ya jima yana ci masa tuwo a ƙwarya don ya lura Yaron Abbansu yafi Son shi fiye da kowa tunda har bai iya 6oye son da yake mashi agaban kowa, Kuma ya Lura cewa Babban yayansu ya mutu akansa hakan na nufin shima Yafi Son*JUNAID* bama su kaɗai ba kowa na gidan in kana so kaga fusatar shi to ka ta6a junaid nan xaka ga tashin hankali, shiru yayi a lokacin ya koma gaban mirror ɗinsa yana kallon fuskar shi ta cikin madubi, a fili yace "saboda*Junaid* Abba da Babban yaya suka mare Ni, a gaban ƙanne na, mutun Uku da suka kasance maƙiya na acikin gidan nan muddin inaso In ƙuntata musu dole saina Cutar da *JUNAID* 😳
ya faɗi tare da sakin wani irin shu'umin murmushi yace "Haroon kenan Mai Fuska biyu ! Wasu suna mun kallon shashasha ɗan giya yayin da ni kuma nake masu kallon garori wannan Alwashi ne na ɗaukarwa kaina saina Tarwatsa farin cikin gidan nan kuma ba da kowa zanyi amfani ba fa ce *JUNAID* 👌💔
"na'am " ya amsa yana Satar kallom sehrish da ta kira sunan shi ta wutsiyar idon shi, "nifa tsoro nake ji junaid nagaza cin abincin dake gaba ba," murmushi junaid yasa ki tare da cewa "CALM DOWN your mind reesh, ke fa ynx ƴar gida ce, ki saki jikinki ki ci Abincin ki a natse," murmushi tasaki yayin da ta sa hannu cikin plate ɗin dake gabanta mai ɗauke da fried chicken taci gaba da ci, ta6e baki Jahaan yayi yana kallonta aransa yace " ƴar shisshigi da kutsu bansan daga ina aka samo wannan yarinyar ba yanzu haka bata Wuce Zariyya dama gata nan kamar Zararrriya sai faman zare ido take,' ya yi maganar yana Hura hanci kamar wanda akayiwa dole yana Cusa bugger abakinsa, Ayaan kuwa cewa yake yi aransa "ƙarfin hali irin na Ifritanyar nan kalli yadda ta wani shige tsakanin Abban mu da junaid tana cin abinci ita ga isasshiya mai walkin sa, ala dole ga ƙanwar Sojoji zaki gane kurenki ! Jibi kunnuwanta don Allah kamar na Zomo falo falo sai faman ƴan ƙefce ƙefcen ido take kamar wadda aka aza A saman kujerar lantarki......,😂
Har cikim ranta sehrish duk ta tsargu da su Twins kamar tasan abunda suke cewa aransu, Azmee ce keyi mata alamar ta kwantar da hankalinta don itama ta lura da abunda su twins ke mata, wani irin Kallon hadarin Kaji 😾😼
Tuni sgr ya bar dining ɗin dama breakfast ɗinsa shaf shaf yake yinsa gyaran murya Abbansu yayi ya kalli azmee yana cewa "idan mun kammala ku shirya ke da sehrish da Junaid saboda yi wa daughter siyayyar kayan sawa da abubuwan amfani na mata, hada ma Saloon da gyaran jiki duka komai nake so ayi mata,'
Atare Jahan da Ayaan suka ɗago suna kallon Abban nasu, shima kanal yusif abun ya basa mamaki, Sehrish kuwa murmushi kawai take saki haka Junaid daɗi kamar ya rufe sa,
Azmeee tace "To Abba Insha Allah komai za'ayi mata,"
"Ke ma hada ke, azmee siyayyar duk zakuyi," cike da farin ciki azmee tace "Mun gode sosai Abba Allah yasa ka da alkairi,"
mayar da idonsa Abban nasu yayi kansu Ayaan da jahan da kanal yusif yace "Bafa ni zan biya kuɗin siyayyar ƙanwarta ku ba, wannan nauyin ku ne, don haka kowa ya tattaro ya bada gudummuwa,
babu wasa a fuskar shi yayi maganar, shiru su kayi don baza suyi mashi musu ba, Abban nasu yaci gaba da cewa "Yusuf kai zaka biya kuɗin siyayyar kayan sawanta, Jahan kuma shi zai ɗauki nauyin kayan ado na mata da za'a siya mata, sannan Ayaan shi kuma zai ɗauki nauyin na gyaran jiki hada takalma da bags ɗin da za'a siya mata ina fata duk kunji," sam takaici ya hana twins yin magana bawai kuɗin bane damuwarsu ba sam basu da matsalar kuɗi saboda bada albashinsu suka dogara ba, Mahaifiyarsu duk ƙarshen wata tana tura masu makudan kuɗi dollars wannan ba tare da sanin Abbansu ba ko Babban yayansu ba, haushin su yarinyar da aka ƙaƙaba musu wadda basu san daga ina aka tsinto ta ba, gashi kuma har ana ɗaura musu responsibilities ɗinta,
"Naji kunyi shiru"? Abbansu ya tambaya yana kallo su,
Kanal yusif yace "Atm ɗin yana a cikin side drawer ɗina, junaid yaje ya ɗauko in zasu tafi,"
Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa "Haka nake son ji ku fa"?
har suna haɗa baki wurin cewa "akwai kuɗi cash a ɗakin mu junaid yaje ya ɗibi yarda zai ishe su,in kuma Atm suke so shima yana anan saman mirror muka barshi...." suna magana suna yatsina fuska irin an musu dolen nan,
Kanal yusif yace "A'a Abba ba sai sun bada nasu ba, kawai suyi using da Atm ɗina zasu ishe su har ma su rage," acewar kanal yusif,
Abban su yace "a'a ni nafison su sauke nauyin dake akansu na ƙanwarsu yakamata tun yanzu su son yadda zasu ɗauki ɗawainiyar mace kafin Allah yasa lokacin auransu yazo,"
. atare suka haɗa baki wurin cewa"Aure kuma Abba,"
"Eh mana" ya amsa musu,
Kallon Ayaan jahan yayi tare da cewa "tashi mu tafi lokacin aiki yayi " miƙewa Ayaan yayi yana cirar tissue yace "Abba mu mun wuce,"
Murmushi Abbansu ya saki tare da cewa "adawo lafiya, aure dae ba fashi in lokacinsa yayi mutun ko bai so saina ɗaura masa in yaso ya haɗiyi zuciya ya mutu, zan zauna in ta zuba muku ido ne,"
fashewa da dariya junaid yayi bashi kadae bama hada su azmee da sehrish, kanal yusif dae murmushi kawai yayi,
Na wani lokaci kowa yabar dining ɗin cikin zumuɗi sehrish ta wuce don ta shirya zasu tafi Shopping mall ɗoki har ba'ayi, shima junaid bedroom ɗinsa ya wuce don ya kimtsa yau zasu yi fita ta musamman da sehrish don ya tsara har ice cream sai sunje sha, haka itama azmee kimtsawar take yi don su fice,
Haroon sam yagaza fitowa saboda kunyar haɗuwarsa da sehrish baisan martanin da zata yi mashi ba, dama jiya ta yarda masa magana a cikin toilet ina ga yau da tasamu ƴanci Allah kaɗai yasan Zagin da zaisha, ga yunwa yana ji amma sai faman zarya yake aransa yana faɗin "Ke ma bazan ƙyale ki ba Yarinya saina ƙasƙantar dake kuma bazan fasa abunda nayi niyya ba akan Ki,*YANZU WASAN YA FARA* 🙆
Fitowa azmee tayi jikinta na sanye da doguwar riga ta atampha ta kashe ɗaurin kallabi, sai ƙamshi take cikin hanzari ta wuce kitchen saboda tunawa da Marshal Omar wanda bai fito yin breakfast ba kuma ba'a kai masa ba, shaf shaf ta shirya masa a tray ta wuce part ɗinsa ta shiga da Sallama babu kowa a falonsa hakan na nufin koma bacci bai tashi ba, ajiye masa tayi asaman ƙayataccen table ɗinsa sannan ta fuce,
Tana saukowa down stairs taci karo da haroon wanda ke tafiya cikin sanɗa zai shige kitchen wai don karya ci karo da Sehrish
girgiza kai azmee tayi aranta tace "Shi ko haroon ko lafiya yake faman tafiya cikin sanɗa haka kamar mara gaskiya, Ni wlh nama manta dashi ashe yana nan,'
Gyaran murya tayi tare da cewa "barka da fitowa mlm haroon," firgit yayi tare da juyowa ya kalle ta, ajiyar zuciya yasaki ganin azmee ce "Aunty azmee barka dae fatan an tashi lafiya, shine aka manta dani ina ta fama da yunwa yanzu da ban fito ba da shikenan sai dae yunwa ta kashe ni ko? Ya tambaya hada ruƙe qugu dama ransa a 6ace yake.........
Azmee tace "Kayi haƙuri wlh ni sam na manta ban lura da baka fito ba ba,"
ta6e baki yayi tare da cewa "koda yake dama ae ni ba'a sona na lura, bama kallon mutun ake mun ba acikin gidan nan kowa ya raina ni,"
Murmushi azmee tasaki tana kallonsa tace "kadaina cewa haka bana jin daɗi, koda kowa zai guje ka amma kasan ina tare da kai ko? Ka ta6a ganin inda UWA ta Guji ƊANTA?" tayi maganar ne don ta kwantar masa da hankali ganin ya ɗan fusata,
Sakin fuska haroon yayi sannan yace "Shikenan nadaina aunty azmee tunda baki so, yanzu dai a haɗa mun breakfast ɗina wlh yunwa nake ji har wani jiri nake gani,
Wuce sa azmee tayi tana cewa "a ina za'a kaima abincin anan ko a ɗakin ka," cikin sauri yace "Ki haɗamun kawai natafi da abuna ɗakina naci,Zai fiye mun kwanciyar hankali na"
Kitchen ɗin tashiga ta haɗa masa a tray sannan ta miƙa masa jikinsa na rawa ya kar6a ya wuce ɗakinsa,
Gefen gadonsa ya zuna hannunsa har kerma yake yi yana cusa abincin abakinsa, kamar daga sama yaga sehrish ta bayyana agabansa jikinta sanye da Kayan Sadaukai na Yaƙi, hannunta ruƙe da Zungureriyar wuƙa kanta na ɗauke da Kambun Sarauta, hankali atashe haroon ya fesar da donuts ɗin daya cunkusa abakinsa yana kallonta cike da tashin hankali, fashewa da dariya sehrish tayi tare da cewa "Kai Haroon! Ƙaryarka taƙare ! ka jima kana ƙuntatamun gashi yanzu Allah ya ɗaukakani, babu wata sauran barazana daga gare ka ta ƙare, nazo ne don na ɗauki fansa akan ka, yanzun nan zan fille kanka da wannan wuƙar ta hannu na,
Da ƙarfi sehrish ta ɗaga wuƙar zata fille ma haroon kai, aikuwa a firgice ya miƙe tsaye yana dafe saitin zuciyarshi a tsorace
Lokaci guda Sehrish ta 6ace masa 6aaat hakan na nufin ba ita bace idonsa ne ke masa gizau,amma shi tabbas ita yagani kodai yarinyar Aljana ce ? Ya tambayi kansa,.wannan ba kowa bace face Hafsat Bature Aljanar sehrish 👿
Koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da cin breakfast ɗinsa anatse, yayin da ransa ke saƙa mashi abubuwa da dama game da mummunan ƙudirinsa
__________ 💪 ______________
OMAR a hankali ya soma buɗe idanunsa bakinsa na ambaton addu'ar tashi daga bacci, yayin da zuciyarsa ke cike fal da son ganin Tagwayensa, tun da asuba daya sha maganin mura bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi sai yanzu Allah yayi mashi ikon Farkawa daga bacci, a hankali yasa hannun sa ya janye blanket ɗin daya lullu6a dashi jikinsa na sanye da Night dress riga ce dai dai guiwa mara nauyi, fararen idanuwansa yafara kaiwa ya kalli agogon dake manne jikin bango ƙarfe 12 na safe yayi mamakin yadda lokaci ke gudu har haka, ko don yayi overdose na maganin muran daya sha ne yasa shi yin dogon bacci har haka,
Cikin sauri ya yunƙura ya miƙe direct toilet ya wuce , brush yafara yi yana tsaye agaban wash basin amma idonsa Fuskar Jahad da Hosana take hasko masa ta cikin mirro ɗin gabansa, shaf shaf yayo wanka ya fito jikinsa sanye da Bathrobe(rigar wanka) fara, wadda ta tsaya masa adai-dai guiwarsa, Marshal Omar kenan Son kowa ƙin wadda tarasa 😉
kai tsaye wuce wa yayi ya ɗauki wayarsa dake a saman gadonsa, sak irin ta sgr ce, Company ɗaya ce waya ce ta musamman domin Manyan jami'an sojoji irinsu kirar Companyn Iphone Ce, hamshaƙiyar waya haɗaɗɗiyar gaske wadda kuɗinta sun haura 30millions, ba kuɗinta bane abun mamaki ba a'a amfaninta shine abun dubawa, ƴar bala'en wayace bakowa ma zai iya Controlling ɗinta ba sai mamallakinta.
dannata ya soma yi Contact ɗinsa ya shiga kai tsaye numbar aunty BABBA ya laluba, ya buga mata Calling ta shiga ringing, burinsa tayi picking yasanar da ita cewa Zai shigo kaduna don ya duba su Hosana da Jahad, almost 3 times ba'a ɗaga kiran ba, domin kuwa wayar tabar ta agida, canza ra'ayi yayi ya dannawa Wayar Hafsat kira,
Suna a asibitin nan zaune saman waiting seats, bacci duk ya kwashe su daga zaune don daren jiya ba wanda ya runtsa sai da sassafe wurin ƙarfe 10 suka samu baccin wahala shima saboda likita yasanar dasu cewa Yarinyar da ranta bata mutu ba, farkawa ne kawai batayi ba doguwar suma tayi, shine suka ɗan samu natsuwa suka baje suna bacci kamar wasu shanaye ga uwar yunwa na cinsu, kiran Omar ne yashigo da ƙarfin gaske a wayr hafsat dake acikin purse ɗinta data aza saman cinyarta, a firgice suka farka su duka wuri wuri da ido, cikin hanzari hafsat ta zura hannunta cikin purse ɗinta ta duba me kira sunan MARSHAL OMAR ne ya bayyana, dafe ƙirjin tayi hankali atashe tace "MUNSHI GA UKU ! MOMMY YA OMAR NE KE KIRA"😳
Mu haɗu ranar monday Insha Allah🙏
Kar amanta da paymemt wanda suka shirya sumin magana 08103884440, 300 ne VIP kuma 700 ga wanda basa ra'ayi a grp*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
*Abban Sojoji part 2*
*EPISODE 7-8*
*AYAAN* arab name ne for boys means God's Gift (kyautar Allah) ❤️
Waro ido waje aunty babba tayi tana faɗin "Shikenan komai ya ƙare, Hafsat kada ki ɗaga kiran nan, katse shi kwai , a rude take magana, Hafsat tace "Mommy how can i reject his calls ! Idan zuwa zai fa ? ba kwara na ɗaga naji mai zai ce ba, don mu son yadda za'ae mu dakatar dashi ba.....' ta ƙare maganar tare da ɗaga kiran ta ƙara a kunnanta tana Zabga sallama,
Hankali atashe aunty babba ke cewa "Kisa wayar handsfree," cikin hanzari hafsat ta mayar da kiran handsfree don aunty babba tasamu damar jin abunda Marshal Omar ɗin zai ce,
Bayan ya amsa mata sallama yace "Zan Shigo kd yau insha Allah ki sanarwa Mommynki," yana faɗin hakan ya katse kiran since bfr hafsat tace wani abu,
Cikin tashin hankali Hafsat ta janye wayar daga kunnanta,a wani slow tana kallon mommynta wadda itama kallon nata take yi ido azare,
Murya tamkar zatayi kuka tace "Mommy duk ke kika ja mana wannan bala'en da muke ciki, gashi nan daga ni har ke ba wanda ya runtsa daren jiya rabon mu da abinci ma tun jiyan, yanzu kuma gashi Ya Omar zaizo, Ina fata kin tanadi bayanin da zakiyi masa game da Twins ɗinsa da kika Faffasa ma fuska, ki ka canza musu kamanni, nayi imanin kema Ya omar bazai barki ba, sai ya Canza miki kamanni, don Allah naushi ɗaya zai ma kumatun nan naki Mommy sai an neme su an rasa a fuskarki,'
Tuni ido ya raina fata, aunty babba tace "hafsat ki daina mun waɗan nan suratan naki ki barni inji dakaina, yakamata musan abun yi before Omar ya diro garin nan,'
Zama su kayi zugum kowa zuciyarsa na bugawa daram daram, kowa da irin idea dake zuwa masa akai,
Jahad kuwa na a ɗakin da aka kwantar da hosana dama gado biyu ne aciki, itama doctor sai da ya duba ta, baccin wahala kawai take yi saboda allurar da dr yayi mata don tasamu bacci, duk inta farka sai ta ambaci sunan Hosana saboda itace aranta, so take tama fi ƙarfin allurar da dr yayi mata, don ƙoƙori take ta tashi da ƙarfin gaske don taje ma hosana wadda ke kwance magashiyyan rai hannun Allah 😥
______________________________________
Bayan Omar ya kammala wayar fitowa yayi daga bedroom ɗinsa ya zauna a palor saman sofa yana yin breakfast ɗinsa anatse, wayarsa ce ta shiga ringing wadda ya ajiye agefensa, kai idonsa yayi ya duba Gwaggon katsina ce ke kiransa, murmushi yasaki don kusan kullum saita kira layinsa ta tambayesa ina Ƴa'ƴan Abusufyan ɗinta ya basu su gaisa, hannu yakai ya ɗauki wayar ya kara a kunnansa yana faɗin "Gwaggona kenan fatan kin tashi lafiya,"
Daga can 6angaren gwaggon katsina tace "Allah sarki Omar jiya ko isasshen bacci ban samu ba saboda tunanin ƴa'ƴan abusufyan ɗina, Jiya zuciyata tayi ta bugawa inaji kamar wani abu ya same su, dan Allah Omar karka bari a cutar dasu,
Sai faman zuba take masa a waya sam taƙi bari yace wani abu har sai da ta gaji ta dakata da maganar sannan Omar yace "Ki kwantar da Hankalin ki goggo na, Ƴa'ƴan abusufyan ɗinki suna nan cikin ƙoshin lafiya,"
Ajiyar zuciya tasaki kafin tace "Suna tambayata ko? Suna atare da kai Omar? Ka basu dan Allah muyi waya mana,"
omar yace "Goggo kin manta suna a kaduna,ae gidan Yaya ishaq nakai su..."
Kamar tana agabansa ta zabga salati
tana cewa "La'ila ha illallah Mahammadar rasulillah Omar ! dama gidan Ishaq ka kaisu? Gidan wannan matar Shuwa mai ƙirar samudawa sam matar nan bata da Imani, zuciyarta irin ta kafuran farkon ce wlh, shikenan ni Allah kaɗae yasan wane hali ƴa'ƴan abusufyan ɗina suke ciki . ......fashe masa da kuka goggon katsina tayi,
Sam omar ya gaza gane ma goggon tasu, a tunaninsa haukan nata ne ya tashi, in ba haka ba ina matar ishaq keda aibu har haka, gashi kuma ta fashe mashi da kuka, cikin rarrashi yace "Calm down your mind Goggona, ƴa'ƴan abusufyan ɗinki suna cikin ƙoshin lafiya, yau ma nake shirin zuwa in dubo su,'
Cikin shessheƙar kuka tace "To shikenan amma dan Allah Omar nidai nafison su bar gidan matar nan, adawo mun dasu nan in basu kulawa kamar yadda na kula da mahaifinsu tun yana yaro,"
Murmushi Omar yasaki sannan yace "Insha Allah my aunt don't worry ur self abt them, suna Lou and insha Allah in naje zan basu waya ku gaisa kiji muryarsa may be u will be calm,"
"Shikenan Omar kada ka manta sai na jika,"
Ya amsa mata da cewa "Insha Allah"
daga bisa ni su kayi sallama ya ajiye wayar yaci gaba da Cin breakfast ɗinsa,
Acan ciki kuwa tuni Sehrish ta shirya kayan mazan ne ajikinta tunda su ke gare ta, hijab kawai tasanya ajikinta brown colour, azmee kuwa dama atampa ce ajikinta, Mayafi kawai ta lullu6a a jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba, suna a babban falon sai ga junaid shima ya sauko, bin shi da kallo sehrish tayi jikinsa na sanye da suits baƙaƙe kamar ma'aikacin banki, yayi kyau sosai acikinsu abun sai wanda yagani, sai faman murmushi yake saki da white teeth ɗin nan nasa kamar gonar auduga,
"Gsky junaid bazan iya jerawa dakai ba, Irin wannan kyan haka," sehrish ta faɗi tana nuna shi da hannu,
Ƴar dariya junaid yasaki kafin yace "duk kyan da zanyi bazan fi ki ba, ke fa maca ce, ni kishi ma nakeyi don nasan yanzu zaki fara ɗaukar wanka da zarar munyi Siyayyar nan,"
Murmushi sehrish tasaki ita kanta har ta hango ta cikin Gown ta gayu wow, azmee ma murmushin take saki, atare suka jera suka fuce, a cikin Motar Junaid haɗaɗɗiyar gaske, Shi ke driving yayin da sehrish ke a gefensa sai faman fira suke suna zuba, azmee na a back seat tana sauraron su wani lokacin ma tana sa musu baki suna firar atare, suna ta tiƙar dariya abinsu gwanin burgewa, har suka isa katafaren shopping mall ɗin mai matuƙar girman gaske, sehrish taga haɗuwa yau dae karo na farko data fito kuma karo na farkon data fara ziyartar wuri irin wannan, atare suka fito suka shiga wurin, Mutane gasu nan kowa ya ɗau wanka ana ta siyayya ba kowa ya tsone mata ido ba face ƴan mata da samarin dake a wurin, duk sai taji kunya ta kamata ganin yarda Matasan matan dake a wurin siyayyar suka ɗau wanka iya wanka, ita kuwa kallo ɗaya za'ae mata ansan bazata wuce ƴar aiki ba,
6oyewa ta rinƙa yi abayan junaid da Azmeee, dariya kawai junaid keyi don ya gano dalilin dayasa sehrish jin kunya tana la6ewa abayansu,
Sam ruwan ido ya hana sehrish Sa hannu ta ɗauki wani abu, junaid ne kawai da azmee ke faman ɗebar mata kayayyakin sawa iri iri masu kyan gaske na mata, yawanci arab gowns ne, turkish dress, night dress, Pakistan, english wears komai jidar sa kawai suke yi, laces ne atampa ce, materials, shadda, Everything,
Duk tana tsaye tana kallonsu kowanne ya cike shopping basket dake hannunsa, sai dai in sun matsa nan tabisu, in kuma anzo abunda zata gwada tasanya su bata taje dressing room ɗin dake a wurin ta sanya,
lokacin da suka zo wurin jerin panties da bra, hannu junaid yasa ya ɗauko brazier ya ɗago da ita yana cewa "Sehrish Ga wannan gwada mu gani,"
Sam bata lura ba tana ta faman kalle kalle, ganin hakan yasa shi ta6o hannunta yana nuna mata bra ɗin dake hannunsa yana cewa "Ina magana," aikuwa cikin jin kunya ta zaro ido tare da sa hannu ta rufe fuska tana faɗin "junaid dan Allah kadaina menene haka agaban mutane," fashewa da dariya yayi cikin mamaki yace "menene aciki? Kunya kuma ni bansan wannan zancen ba, ni dae ki amsa kawai kije ki gwada in tayi maki, in batayi ba acanza wata shine kawai,"
Hannunta na kerma ta karba tana ɗan kallon shi, har time ɗin dariyarsa yake Don shi mamaki ta bashi wai kunya,
Shiga dressing room ɗin tayi hada datso kopa, faskekan madubi ne aciki ya cike bangon, cikin hanzari ta tu6e hijab ɗinta da rigarta, ta shiga kiciniyar zira bra ɗin daker hada su sakin nishi,
Tsayawa tayi tana kallon kanta acikin mirrow ɗin wow, ta fito ɗas abunta dama tubarkallah masha Allah full ɗinsu suke, bra ɗin ta hau raɗau launin ta maroon colour ce, abunda sehrish take ma mamaki yarda akai junaid ya nemo bra dai-dai size ɗinta,duk jerin braziers ɗin dake a wurin,
Cikin hanzari ta cire ta, ta mayar da rigarta da Hijab ɗinta, sannan ta fito, karaf suka ci karo dashi abakin ƙopan ɗakin,
a ɗan razane tace"junaid yaushe kazo nan," hannu yasa ya ɗan sosa sumar kansa yana cewa "Naji kin jima ne, shine nazo in ga ko kin gaza sawa ne, sai in taimaka miki.....," ganin yarda ta waro ido waje yasa shi dakatawa, muryarta har wani shaƙewa take yi wurin cewa "Junaid kana nufi brazier ɗin zaka taimaka mun nasa !!" ta tambaya a rikice,
Kai tsaye yace "eh mana," Jinjina kai sehrish tayi tare da wuce shi aranta tana mamakin hali irin na junaid shidae ba ruwansa komai normal ne a wurinsa,
tsayawa ta ɗanyi da tafiya ta ɗago ta kallesa Cike da tuhuma tace "Ya akai kasan size ɗina?
Da buɗar bakinsa sai cewa yayi "Ni dana ga Zahiri,"
Cikin sauri yasa hannu ya rufe bakinsa saboda su6ul da bakan da yayi, kamar zatayi kuka take kallonsa tana cewa "Junaid hakan na nufin ka ta6a gani na babu kaya ko"?
Girgiza kai yayi yana faɗin "No ba haka bane reeesh, baki fahimce ni bane, Ina nufin....," sam ya gaza samun amsar da zai bata gashi ta tsare shi da ido tana jiran amsar shi,
Muryar azmee ce ta katse su da cewa "tsayuwar me kuke yi ne? Ku hanzarta mana muyi mu kammala, yaushe har muka wuce wurin Saloon ɗin," cikin sauri junaid yace "Hakane aunty azmee muje kawai yanzu saura me ya rage," Ya tambaya yana kallonta
yayi hakan ne don ya gusarma sehrish da tuhumarsa da take yi, cikin sauri suka wuce tabi bayansu itama,
A ranar yini su kayi siyayya Kamar zasu kwashe kayan Mall ɗin,komai sai da suka siyar mata shoes & bags ne Cosmetics komai wannan ba abunda suka bari,
Daga nan suka wuce wurin haɗaɗɗen Saloon ɗin duk acikin Mall ɗin yake, a lokacin junaid ya koma cikin mota yana jiran su,
Already sun kammala purchasing ɗinsu an jera Manyan akwatinan guda uku biyu sunfi girma a boot aka zuba su, Wasu kayan kuma na acikin Manyan Shopping bags an zuba su har a cikin back seat na motar,
Murmushi kawai junaid ke saki ya langwa6ar da kansa jikin seat ɗin motar, babban burinsa shine yaga yarda sehrish ɗinsa zata fito amatsayin mace a fili ya furta "Can't wait to seee" tabbas yanzu ne yasan yasamu abokiyar rayuwa wadda zasu kasance atare na har iya tsawon rayuwarsu, shigowar sehrish rayuwarsa ta canza mishi wasu abubuwan da dama da yake kewarsu,daga ciki harda kewar Mommynsu da tatafi tabarsa tun yana jinjiri wannan abun ya ta6a mishi zuciya sosai raɗaɗin na'a ransa yana jin cewa duk cikinsu shike bata so, hakan yasa shima baya sonta duk in ta kira waya tana so abashi tayi magana dashi baya kar6a, har ila yau junaid bai ta6a ganin Mommynsu ba ido da ido sai dae a hoto, babu yarda batayi ba akan akawo mata shi Sydney amma abbansu yace muddin tana son ganin shi ta tako tazo da kanta in ba haka ba ita dashi har abada, saboda batayi mashi adalci ba,' wannan kenan
Ya jima yana tunane tunane shi kaɗae abunsa yana ta faman sakin murmushi, adai dai time ɗin Sehrish ta fito tare da Aunty azmee,
Ƙaraso wa su kayi ta bude gaban motar ta shiga aunty azmee kuma ta shige baya sannan junaid ya tayar da motar yana faɗin "Har an kammala saloon ɗin"?
ya tambaya yana ɗan kallonta tace mashi "Eh,'.
"In munje gida za'a nuna min," ya faɗi da ɗan murmushi a fuskar shi, kai tsaye yabar bakin Mall ɗin yaja Motar kai tsaye ya nufi hanyar gida dasu duk da yaso su biya wurin shan ice cream amma shi kanshi a gajiye yake yafi buƙatar gidan don ya huta, Dama jikinsa sam ba irin na ƴan wahala bane,
Motarsu na shiga babban entry ɗin gidan adai-dai time ɗin kuma Motarsu Marshal Omar ta fuce daga gidan, Tasu na shigowa tashi na Fice wa,
🙅
Bayan yayi parking ɗin motar, wani sergeant ya ƙaraso ya kwashe akwatinan da junaid ya fito a boot ɗin motarsa, , Hada jakunku nan siyayyar na cikin back seat ɗin duk ya fiddo su, yayin da sojan ke kwashe su izuwa cikin gidan,
Agajiye azmee da sehrish suka shiga cikin Babban falon bakowa alamar duk sun fita, azmee ta taimaka mata suka shigar da kayan ɗakin suka jibge su da nufin in sun huta an jera su a wardrobe ɗinta,
Cike da zumuɗi sehrish ta cire hijabinta don taga gyaran gyashin da akayi mata, Gaban mirror ta tsaya tana kallon gashinta, haɗaɗɗen gyaran gashi akayi mata mai haɗe da Twist,
Sai ta rinƙa jinta tamkar Queen saboda haɗuwa, ta jima tana kallon kanta a mirror kafin ta wuce toilet don yin wanka da alwala,
Shaf shaf ta fito jikinta ɗaure da toilet, wardrobe ta wuce ta samu riga da wandonta ta zura ajikinta sannan ta ɗauki hijab da dardumar salla ta shimfiɗa, ta kabbara sallah A natse ta Gabatar da sallar,
Bayan ta kammala Jiki na rawa ta cire hijab ɗinta ta ninke tare da abun sallar asaman gado ta ajiye su,
Zama tayi tana bubbude kayayyakin da aka siya mata na cikin jakun kunan, sam bakinta yaƙi rufuwa, wani haɗaɗɗen takalmi ta ɗauko high heels ta ciro shi daga kwalinsa tana gwadawa a ƙafarta ita kanta ta razana daganin yarda ƙafarta ta fito ɗass acikinsa gashi ash colour jikinsa duk kyalli yake ga wasu igiyoyi na ɗaure sa ya haɗu,
Shigowa azmee tayi tana faɗin "Kai!kai! Irin wannan zallar kyau haka gaskiya naji tsoran haɗuwar da zakiyi anan," .
Dariya sehrish tayi tana cewa "dama yanzu nake so in jera kayan acikin wardrobe bansan ma ta inda zan fara ba,"
Azmee tace "kada ki damu ae shiyasa nazo saboda nata Ya ki jera su Muyi mu gama, akwai sauran aiki agabanmu ga gyaran cikin gida ga kuma aikin Kitchen,'
Miƙewa sehrish tayi ta janyo akwati nan biyu da hannunta izuwa wurin wardrobe ɗinta ta jingi ne su,itama azmee ta janyo ɗayan akwatin tana cewa "Ki barmun jeran kawai, kije ki gyara cikin gidan kafin na kammala Canza ma ɗakin nan naki kamanni," .
Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "Toh aunty azmee," Sai da tafara ɗaukar mayafinta a cikin wardrobe ɗin sannan ta fuce tana murmushi,
Babban falon tafara gyarawa duk da babu wani datti a tsaftacensa yake, shaf shaf tagama, cikin hanzari ta wuce upstairs don gyara ɗakin babban yayansu, tana cikin taka steps ɗin taji motsin mutun a down, juyowa tayi don taga kowane ne, Karaf idonta suka sauka akan na HAR0ON, sam yagaza ɗauke idonsa akanta kallon kallo suka shiga yiwa juna, duk a tunaninsa sehrish zata mayar masa da martani amma abun mamaki sai yaga tasakar mashi wani irin ƙayataccen murmurshin kashe zuciya tamkar ta soke shi da kibiya a ƙahon zuciyarshi haka yaji, don har saida yasa hannu ya tarbe saitin zuciyarshi, wani irin sabon kyau yaga yarinyar tayi mishi (nace ba kabari sai ta fara ɗaukar wanka tukunna munyi wannan maganar,"
Juyawa sehrish tayi cikin hanzari ta wuce apartment ɗin SGR, tabbas taso ta mayarwa Haroon martani amma daga baya tagane cewa ba buƙatar yin hakan, yanzu fa ita tamkar Princess take ƴa ɗaya tak ga Shugaban sojoji kuma ƙanwar sojoji, dole ne taja class muƙami iya muƙami, wannan kaɗae ya isa ya kashe haroon saboda ƙululun baƙin ciki,
Zuru haroon yayi sam yagaza motsi daker ya iya ɗaga ƙafarsa ya soma tafiya jiki a mace, Har time ɗin tafin hannunsa na a dafe da saitin zuciyarshi
Bin shi da kallo junaid yayi wanda fitowar shi kenan daga sashen abbansu,
Ƙarasawa yayi cikin sauri ya nufi haroon yana faɗin "Yaya Haroon lafiya meke faruwa ne, naga ka dafe zuciyarka, ince dai ba wani abu ya same ka ba,'
ɗagowa da ido haroon yayi yana kallonsa yace "Jini Junaid,"
Jin wannan yasa junaid tallabo shoulders ɗinsa yana faɗin "Subhanallahi jini kuma a ina yaya haroon,"
da wannan muryar tasa ta ƴan giya yace "Yanzu duk jinin dake kwaranyowa daga zuciyata ba ka gani ba? Kibiyar da aka soka mun fa? Ko shima baka gani ba"? Ya faɗi a susuce yana kallon junaid,
Baki asake junaid ke kallon ikon Allah shidai baiga komai ba a ƙirjin haroon hannunsa ne kawai daya tallabe wurin,
Cikin ruɗi yace"yaya haroon babu komai fa a wurin hannunka ne kawai daka sa ka dafe,
Muryar tamkar zaiyi kuka yace"Manxon Allah yayi gaskiya Junaid, shikenan bakomai jeka kawai Allah yayi maka albarka, ya kare ka daga sharrin Maƙiya,
Ya faɗi tare da janye hannun junaid daga kafaɗarsa ya wuce sa yana cigaba da sambatu
Girgiza kai junaid yayi tare da cewa "Allah ya baka lafiya yaya haroon ya yaye maka wannan shaye-shayen da kake fama dashi,"
Yana gama faɗan hakan ya wuce direct ɗakin sehrish don yagaza runtsawa burinsa kawai yaganta ta zura kayan mata ajikinta, yana shiga ya samu azmee tana faman jejjera mata kayan a cikin wardrobe ɗinta, ko ina da abunda aka zuba aciki, gasu nan komai ajere, gwanin kyau,
Jin sallamar junaid yasa ta juya da fara'a tana amsa mashi,
Yace "Aunty azmee ina Sehrish ne i thought zanzo na same ta anan ne,"
Azmee tace "ae tuni ta fita don gyara cikin gidan kasan munbar aiki dayawa shiyasa bamu samu hutu ba,"
ɗan zumbura baki yayi tare da cewa "Aunty azmee wane aiki kuma? Mu dawo agajiyen sai kuma ta kama wani aikin, gaskiya bai yiyuwa zanje na dakatar da ita,' ya faɗi tare da juya ya fuce
Murmushi azmee tasaki aranta tana fadin "Romea kenan, Allah dae yasa sehrish tazama mallakin ka, duk da nasan abune mai wuya ayi mashi aure at his age, bansani ba shi da ita waye zai raini wani shi shagwa6a ita kuma shiririta, amma kuma raina na bani cewa akwai wanda sehrish ke so ga dukkan alamu...............
ta ƙare maganar zucin nata ayayin da ta koma gaban dressing mirror ɗin sehrish dayake wayaam babu kayan kwalliya kona shafawa illa kwalba ɗaya tak na turaren junaid da tata6a satar mashi wanda har yau bata ta6a amfani dashi ba,
Janyo trolley ɗin dake ɗauke da cosmetic tayi ta shiga jera mata su, da turarurruka da mayukan jiki masu kyau da ƙamshi da sauransu, sai gashi mirror ɗin yafito sosai na ƴar budurwa,
Cikin ƙanƙani lokaci rishi ta kammala gyara masa part ɗinsa, da wata irin yunwa ta fito ga bacci tana ji tana saukowa down suka ci karo da junaid dake tunkaro stairs ɗin,
da murmushi a fuskarta tace "Junaid dama idonka biyu ae nayi tunanin kana can kana sharar bacci,'
yatsina fuska yayi tare da cewa "taya zan iya bacci bayan banga gyaran gashinki ba, zuwa nayi ki nuna min in gani," ya faɗi hada ruƙe ƙugu,
Dama tana kallon fuskarshi tasan rigimar ta motsa ga Idonshi sai faman lumshewa suke yi alamar bacci yake ji over,
Saukowa ta yi tana cewa "Shikenan zan nuna maka ammma kabari nafara samun natsuwa tukunna, yanzu kitchen zanje na gyara kuma yunwa ma nake ji,"
Shiru yayi baice komai Ba dayaso hannu kawai zaisa ya tu6e mayafin data yafa, abunda ya hanasa yin hakan baiso wani yagani cikin Yayyensa balle ya ƙyasa, don kishinta yake ji ayanzu kamar kamar me,
Shiga gaba sehrish tayi ta nufi hanyar kitchen, cikin hanzari yabi ta yana faɗin "Nima yunwar nake ji, zan tayaki mu gyara kitchen in mun kammala cin abincin atare,
"Shikenan bita zaizai," ta bashi amsa tana dariya, shima dariyar yayi jin sunan da tasa mashi,
"Idan baki so zan daina bin ki,' ya faɗi ayayin da suke shiga kitchen ɗin,
Sehrish tace"Nafison hakan ae, saboda kana ɗebe min kewa sosai,"
Jin hakan yasa junaid sakin murmushin murna,
Wuce wa yayi yazauna saman ɗaya daga cikin dining chairs ɗin dake kewaye da dinner table yana cewa "Ki haɗa mana corn flakes kawai mu sha, in akwai snacks ki haɗo mana dashi,
Ta amsa mashi da "Toh,"
A cup biyu ta haɗa musu sannan ta haɗo masu da snacks suka zauna suna sha suna fira, ❤
________________AUNTY BABBA______________________
Suna cikin wannan fargabar wayar hafsat ta sake yin ringing, cikin hanzari tunkan tasa hannunta ta ɗauka aunty babba ta riga ta ɗaukar wayar asaman cinyarta, a tunaninta Omar ne amma tana dubawa taga Sunan My Dad ya bayyana, ɗagowa tayi ta kalli hafsat hankali atashe tace "Abbanki ne ke kira, Allah yasa dae ba dawowa zaiyi ba, ya salammm ni bansan meke faruwa dani yau Ba
Hannu hafsat tasa ta kar6i wayar, ta amsa kiran sannan takara a kunnanta tana zabga Sallama,
Janar ishaq ya amasa mata da cewa "Wa'alaikum salam my daughter, ina mommynki take ne, i ave been trying her phone number tana ringing ba'a ɗagawa why"? Ya tambaya yana jiran amsa,
Murya na rawa hafsat tace "am..dama...umm...tabar wayar a ɗaki ne ina ji, saboda ta shiga kitchen,
tayi maganar tana kallon mommyn nata data ke faman dafe zuciya,tana sauraron mai zai ce saboda wayar na a handsfree,.
Genar ishaq yace "shikenan ki sanar da ita cewa cikin week ɗin nan zan dawo insha Allah,".
"Shikenan daddy Allah ya dawo daku lafiya," sukayi sallama ta ajiye wayar tana faɗin "Tabɗijan Can akwai matsala fa,"
Aunty babba kuwa miƙewa tayi tana faɗin "Nashiga uku ishaq zai dawo ga zuwan Omar yau, bansan me zan fuskanta ba a wurin kowannan su... '.
Muryar hafsat ce ta katse ta da cewa "Amsar fa abayyane take mommy, ke ma kin sani Allah,saki ukun nan sun Wajaba Akan ki muddin Abba yaji abunda kika aikata, saboda wancan karan Ladi mai aikin mu da kika ma bugun mutuwa sai da ya aika ki maiduguri bayan marukan da kika sha awurinsa ina ga waɗan nan bayin Allahn da kika naƙasa har Su biyu, gasky mommy kin shiga Uku, ga kuma ƴa Omar zaizo ni addu'ata Allah yasa Abba kada ya sake ki yabarki kawai da hukuncin Omar na zuwa prison kowa ma ya huta.....
Hankali tashe aunty babba tace"Hafsat prison fa kika ce? So kike akaini can kin gaji dani kenan"?
Rai a6ace hafsat tace "dole nagaji dake mommy, duk ke kika ja mana wannan masifar da muke ciki muna zaman lafiyar mu,' ta faɗi a ƙuke hada buga tsoki kamar bada uwarta take magana ba,
Jinjina kai aunty babba tayi batare da tace komai ba, adai dai time ɗin dr ya fito daga ɗakin da aka kwantar dasu hosana, jiki na rawa tabishi tana faɗin "dr ya jikin nata ta farfaɗo,"?
dr yace "Alhamdulillah tafarka yanzu haka bacci take yi itama saboda allurar da nayi mata,"
ɗaga hannu tayi tana cewa "Alhamdulillah har naji ɗan sauki, amma dr babu yarda za'ae ciwon fuskarsu ya warke nan take? kumburin ya sa6e, ni dr kodai surgery za'ae musu ne acanza fuskar,' tayi maganar in serious matter tana kallon shi,
Wani irin kallo dr ɗin ke yi mata yama rasa amsar da zai bata,
wuce wa gaba yayi ya tunkari Office ɗinsa yana cewa "sam Bazaiyiyu ba gsky,ba muyin irin wannan aikin anan, kuma fuskarsu batayi komai ba da za'a canza musu Ba,da alama madam kema kina buƙatar Aduba ki,' sarai taji abunda dr ɗin yace amma bata ji zafin maganarsa ba, saboda bata cikin natsuwarta a yanzu,
Yini su kayi cikin fargaba ba salla ba salati dama ba ita bace agabansu ba, an saba haɗa salloli ayisu a lokaci guda,Saboda duniya aka sa agaba Ba lahira ba,
gajiya su kayi gaba ɗayansu da zaman asibitin ga uwar yunwa kamar suyi hauka, ga zullimi da fargabar zuwan Omar, ganin har Magrib tayi babu kiran Omar yasa suka fidda tsammani da zuwan shi,
Ƙarshe basu jira dr yayi discharge ɗinsu ba, aunty babba ta ɗauko hosana dake kwance saman gado agalabaice ta sa6o ta a kafaɗarta ta fito da ita, sai cikin mota ta kwantar da ita, Jahad ma tashiga motar baiwar Allah ga zazza6i tana ji, gashi dr yace suna buƙatar jini su duka biyun amma babu yarda zasu yi, rayuwarsu a tagayyare sai yarda akayi dasu,
Shiga motar hafsat tayi mazaunin driver aunty babba na gefenta suka ja motar suka bar asibitin, a time ɗin har dr ya biyo su da sauri sauri don ya dakatar dasu amma ina tuni har sun bar arean asibitin.............
A tsiyace ta shiga da motar cikin gidan tayi parking ɗinta, tana fito wa ta wuce ciki saboda jirin da take ji na yunwa, fitowa itama aunty babba tayi sam bata tsaya taɗauki hosana ba ta shige ciki itama,
Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba ganin sun tafi sunbar hosana kwance sai faman nishi take saki numfashinta na fita daker-daker,
bata son yaya zatayi ba ta ɗauke ta saboda itama babu sauran ƙarfi ajikinta, fitowa tayi daga cikin motar tana faman zubda hawaye, Iya cuta dae an cuci rayuwarsu,
Ganin yarinya tsaye abakin mota yasa wani soja ƙaraso wa yana faɗin "Lafiya dai ƴan mata meke faruwa ne,"
Cikin shessheƙar kuka jahad tace "ƴar uwata ce ciki kwance bata lafiya bansan yarda zan shiga da ita ciki ba,"
Sojan yace "Can I help"? Jahad tace masa "eh" saboda bata da wata mafita da ta wuce hakan,
Buɗe motar yayi ya zura hannunsa ya sungumo hosana dake kwance magashiyyan ya ɗaurata a kafaɗarta ya shige da ita ciki jahad ta bi bayansa,
A saman 3 seater ya kwantar da hosana, jahad tayi masa godiya sannan tasamu wuri daga ƙasa ta zuƙunna fuskarta na dai-dai saitin ta hosana,
Hawayen fuskarta har ɗiɗɗiga suke yi a fuskar hosana, addu'o'i tashiga karantowa tana tofa mata,.
Duk hosana na jinta tana so ta buɗe idonta amma ta kasa saboda kumburar da su kayi, tana so ta buɗe bakinta tayi ma Jahad magana amma tagaza saboda haƙoranta kansu sun raunata sosai don ba'a rasa mai girgiɗi acikinsu, ga la66anta da sukayi suntum sam bata iya motsa su,
Cikin kuka jahad tace"Hosana na sani nasan akwai abunda kike son faɗa mun amma kin kasa, kada ki damu ina jin duk wani raɗaɗi da kike ji azuciyarki, inaji inama ace zan iya ɗauke maki zafin ciwon da kike ji da tuni nayi wlh.......taƙarasa mgnr tare da kifa kanta ajikin hosanna,sun jima a haka wulaƙance babu wanda ya leƙo su, sai daga bisa ni hafsat tafito har tayi wanka da alama ta canza kayan jikinta, doguwar riga ce tasanya har ƙasa, ta ɗaure gashin kanta,
Binsu da kallo tayi gwanin ban tausayi ita kanta duk rashin imaninta yau ta tausaya ma twins ɗin,girgiza kai tayi tare da wuce wa ta nufi kitchen,
Jim kaɗan sai gata ta fito hannunta ɗauke da tray mai girma, Tea set ne ɗauke asaman shi, sai French toast ɗin da ta hado masu dashi da sauran snacks, duk da tasan ma daker zasu iya ci
Bedroom ɗinta ta shigar masu da shi ta ajiye Tray ɗin asaman table ɗin dake a dab da gadonta, Sannan ta fito ta nufe su jin takun tafiyar hafsat yasa jahad ɗagowa daga kwancen da take tana kallonta da rinannun idanuwanta da suka jigata,
Hafsat batayi mata magana ba hannu kawai tasanya ta cicci6i hosana ta ɗaura a kafaɗarta sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinta tana cewa jahad "Ki biyo ni,"
Cikin sauri jahad ta tashi tabi su cikin ɗakin, kwantar da hosana tayi asaman shimfiɗeɗen gadonta, sannan ta juyo ta kalli jahad tace "Ga tea nan da snacks nasan kina jin yunwa ki ɗaure ki sha,'
Girgiza kai jahad tayi tana cewa "Bazan iya cin komai ba,
"Soboda me"? Hafsat ta tambaya tana kallonta,
Jahad tace "Sabodo ƴar uwata, bata ci komai ba,idan naci ita kuma fa"?
Shiru hafsat tayi jikinta yaɗanyi sanyi aranta har tana mamakin dama har yanzu akwai ƴan uwa masu ƙaunar junansu haka aduniya? Jinjina kai tayi kafin tace " kada ki damu, zan ƙara dubata yanzu insha Allah,zata ji sauƙi,"
Shiru kawai jahad tayi,amma fa ba zancen Cin abinci agare ta muddin hosana bata ji sauƙi taci ba itama, sai dae yunwa takashe ta,
"Ave a seat," hafsat ta faɗi tana nuna mata saman gadonta,
Jahad tace "Ina so nayi sallah tukunna," ta6e baki hafsat tayi tana cewa "okey ga toilet nan ki shiga,"
wuce wa Jahad tayi ta shige toilet ɗin tana rufe ƙopa tafashe da kuka mai cin rai tunaninta yanzu shine yarda zasu gudu daga gidan gaba ɗaya, don yanzu ta kwammace Su ƙare rayuwarsu a titi akan su faɗa hannun wani, tunda abun nasu ba sa'a kowa baisan taimakonsu don Allah batare daya cutar dasu ba,mutun huɗu kawai tasan suna da kyakkyawan niyya akansu, tsohuwa wadda Allah yayiwa rasu sai Goggon katsina da aunty saude da Yaya Omar ɗinsu.....
hafsat na jiyo kukan jahad dake acikin toilet, jikinta duk ya ƙara mace wa, karo na farko da ta fara jin tausayin wani aduniyar nan,
gaban mirror ɗinta taje wata roba ta ɗauko ta magani na shafawa a ciwo mai kashe raɗadi,
Dawowa tayi ta zauna saman gadon ta buɗe murfin tasoma lakuto shi tana shafa ma hosana a fuskarta, cikin lokaci ƙankani wurin yayi mata wani irin sanyi tamkar an ɗebe ciwon,
"Sannu ya jikin naki," hafsat ta tambaya tana kallon hosana wadda ke ɗan buɗe ido a hankali, sam ta kasa magana,
pillow hafsat ta janyo ta sanya mata kan gadon,sannan ta taimaka wurin tada hosana zaune ta jingine ta ajikinsa,
jikinta sai faman kerma yake yi, cup hafsat ta ɗauka ta shiga haɗa mata tea,bayan ta kammala ta sheƙa mata dashi da wani kofin donya rage zafi daga bisani taimaka wurin bata abakinta, la66anta har rawa suke yi wurin buɗesu saboda wata irin mahaukaciyar yunwa da take ji, sosai tasha tea ɗin kaf tashanye har dae hafsat ta ƙara haɗa mata wani ta bata,
Jahad ba ƙaramin sanyi taji aranta ba ganin yadda hafsat ke kula da hosana tayi mamakin yarda take bata tea abakinta, tsayawa tayi tana kallon su har sai da hafsat ta juyo ta kalle ta tace "ki buɗe closet ɗina akwai hijab ki ɗauko tare da Sallaya,"
Bude wa jahad tayi ta ɗauko hijab tasanya sannan ta shimfiɗa carpet ɗin tashiga yin sallah Hada isha'e tayi wadda ake cikin kira,
Daker hafsat tasamu hosana taci kaɗan daga cikin snacks ɗin data kawo mata saboda ciwon da bakinta ke yi mata, tea ɗin dae ne tasha sosai,
Gyara mata kwanciya tayi, sannan ta sanya bargo ta lullu6e ta,
tashi tayi ta koma saman doguwar sofa ɗin dake facing gadonta ta haye sama ta kwanta itama,.
Bayan jahad ta kammala sallar ta ninke mata abun sallar da hijab ɗin ta mayar dasu inda ta ɗauko su,
Sannan ta koma saman gadon ta haye, ta soma haɗa tea ɗinta tasha tana ci tare da french toast ɗin da hafsat ta haɗo masu, sosai taci don bata rage komai ba duka ta lamushe,
Bayan ta kammala ta shiga cikin bargon da hosana take ta kwanta itama, janyo ta tayi jikinta ta rungume ta tana kiran sunanta "hosanna ya jikin ki"? Har yanzu akwai raɗaɗi ko"?
daker tace "Eh,"
Jahad tace "kiyi haƙuri kinji, insha Allah bazamu ƙara shan wahala ba,inaji araina komai ya kusa zuwa ƙarshe bansani ba ko mutuwa zamuyi ba shine sauƙin mu Allah kaɗai yasani,
saurarawa tayi don jin mai hosana take cewa, saboda fuskarta na'a kwance achest ɗin jahad,sam sautin bai fita sosai
"Bana jinki hosana, kibar magana kawai kada ciwonki ya ƙara raunana,"
Shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, bakomai take son faɗama jahad ba face sunan YA OMAR da take kira.....................................*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
*EPISODE 9-10*
https://youtu.be/rnmDunstSN4
Abun da ya faru MARSHAL OMAR bai samu zuwa kaduna ba sakamakon Emmergency Call din daya samu daga wurin Abbansu cewa yana bukatar shi A headquater dinsu, a lokacin Motarsu har ta fita daga garin Abuja amma suka juyo da hanzari saboda Omar baya wasa da Omarnin mahaifinsa ko musu baya iyayi mashi, duk da yadda ya matsu akan son ganin su hosana da jahad amma haka ya haƙura😔
Tun bayan da suka kammala shan corn flakes junaid ya wuce bedroom dinsa saboda dama agajiye yake, sehrish kuwa sai da ta tsaya a kitchen din har azmee tazo suka fara aiki, cikin kankanin lokaci suka kammala dinner,
sannan ta wuce bedroom ɗinta ta kwanta tasha bacci har wurin magrib sannan ta tashi donyin sallah, bayan ta kammala jiki na rawa ta bude wardrobe dinta, tsayawa tayi saboda ruwan ido ta ma rasa me zata sanya acikin kayan, hannu tasanya ta janyo wata haɗaɗɗiyar Gown black colour mai kyalkyali masu daukar ido, jinjina kai tayi tare da cewa "Wannan zan sanya," tayi maganar tare da hanging dinta asaman murfin wardrobe din, shaf shaf ta tube riga da wandon dake jikinta ta tura su, cikin laundry basket dinta, sannan ta dauki rigar ta shiga kiciniyar zira ta ajikinta, bayan ta kammala ta koma gaban mirror tana kallon kanta ta cikinsa, fuskarta dauke da murmushi tana tuna yaushe rabon da taji ta acikin kayan mata, kayan ma irin wannan sabbi masu kyau, rigar tabi shape din jikinta,hannunta mai dan tsayi ne wanda ya tsaya dai-dai elbow dinta,Jujjuyawa tayi tana ƙarewa kanta kallo, kafin tasa hannu cikin jerin Perfumes dinta ta dauko kwalbar turaren TOUCH ta feffesa ma jikinta har wani lumshe ido take yi saboda yarda fragrance dinsa ke dakar hancinta, bayan ta mayar da turaren ta koma cikin wardrobe din ta ɗauko mayafi white colour tayi rolling dinsa irin lagen da larabawa suke yi masha Allah 😍
Kama hanyar fita tayi tana bude kopan azmee na sanyo kai dama dakin nata ta nufo itama, ganin yarda azmee tasaki baki yasa sehrish sa hannu ta rufe fuska don tasan kallon na menene,
"Nama rasa mai zance irin wannan kyau haka? Yarinya kamar ƴar larabawa ashe dama haka kike da Kyau ga ki dirarra,'?
Cikin jin kunya sehrish tace "Aunty azmee ko fa makeup banyi ba, i know u are just teasing me,
Azmee tace "Reesh ae ko ba kiyi kwalliya ba kyau kike, ae ni ban ma so kiyi kwalliyar yanzu, don banson ki rikita samarin gidan nan, mu rasa wa zamu ba acikin su,'
"BABBAN YAYA' ta faɗi acikin zuciyarta a fili kuma tace "Mai rabo," dariya azmee tayi tana cewa "Toh Allah yaba mai rabo sa'a time kawai zamu jira muga wanene wannan in da rai da lafiya,'
Murmushi kawai sehrish ke saki, suna cikin wannan tsayuwar motocin su suka shigo atare mai ɗauke da jiniya, azmee tace "Alhamdulillah shikenan ma, tun da kin shirya in suka shigo ki tabbatar kin kaima Babban yayansu dinner dinsa tare da Omar, yanzu ma na kammala jera na dining din basu kai ga saukowa sunci ba, dama Twins ne da suka dawo bada jimawa ba sai Junaid da HAROON, just zanji da sauran kawai,'
ta ƙare bayanin tare da kama hanyar fita daga ɗakin tana nanata mata,
Sehrish ta amsa mata da "toh insha Allah,"
cikin sauri ta koma wurin window dinta ta janye labulan ta zuge glass din tana hangensu,
kowannansu agajiye ya fito daga cikin Motar, Abbansu ne tare da marshal Omar sai SGR, Abbansu na sanye cikin kaki, haka SGR army trouser ne ajikinsa sai shirt light green mai gajeran hannu sun ɗame jikinsa, Omar kuma Shigar dazu ce ajikinsa wadda yayi shirin Zuwa Kaduna dazu,
tunda Armstrong ya buɗe masa mota ya fito yake faman lumshe ido hannunsa ɗaya na acikin sumar kanshi yana yamutsa ta, kallon shi Abban su yayi tare da cewa "Ko dae saina taimaka na goyaka ne? Naga alamar baka iya tafiya," ɗago da eye balls dinsa yayi ya kalli Abban nasu sannan anatse yace "Dad kenan, ni da kai wa zai goya wani? kai ma ka sani,"
Yayi maganr tare da soma tafiya abban nasu kam dariya yayi yana cewa "Oh kana jin kanka Tamkar giwa ko? Ae ba abun mamaki bane kaga na sa6eka abayana, in banda ma yanzu daka zama jibgege haka ga tsayi nan nan nake ɗaukarka kana yaro har goya ka nake yi," duk Omar na jinsu yana murmushi kawai saboda atare suka jera suka nufi cikin gidan,
ɗan gyaran murya yayi tare da cewa "Abba yanzu ae sai dai ka goya grandchild dinka masu zuwa," Omar ya faɗi,
Abban su yace "hmmmm taya hakan zata faru bayan ƴan bukulu sun hana ruwa gudu, burina kenan kullum kamar yadda na haifa nima nawa su haifa amma abun takaici duka ya'yan nawa babu wanda ya ajiye ko budurwa bayan ni tun ina 20 years aka sanƙamamun aure muka sha soyayya gaba ɗaya,'
Omar yace "Kada ka damu Abba, Insha Allah burin ka zai cika, in har hakan zaisa ka farin ciki, kawai acigaba da yi mana addu'a,'
Jinjina kai abbansu yayi yana ɗan kallon SGR dake gefensa shiru tamkar baya jin me suke cewa,
Ruko hannunsa yayi cikin nasa sannan yace "kai fa Son, Naji baka ce komai ba ? Ko baka son farin ciki na ne?
yatsina fuska yayi tare da cewa "In dai yaron da zaka goya ne zan kawo maka shi,'
"Uwar fa"? Abban ya tambaya adai dai lokacin da suke shiga babban falon SGR yace "Babu," dariya omar kawai yake yi.abbansu kuwa baki sake yace "Shege zaka kawo min,'?
"Ko baka so ne"? Sgr ya tambaya shima da zolaya,
Abbansu yace "Ae da babu gwara ba daɗi, akawomin inaso,"
Omar yace "So funny wlh, abba son jikokin harya kai haka, to. Insha Allah ba shege acikinsu, Original zaka samu daga gurin kowan nan mun, ' cike da nishaɗi suke fira kamar bazasu iya rabu ba, wuce wa Abbansu yayi part dinsa, shima SGR tare da OMAR suka wuce Uptairs nasu parts din,
💪
Tun da Omar ya shiga bedroom dinsa ya rage kayan jikinsa toilet yashiga ya yi wanka, yafito ya zura kayan baccinsa, har cikin ransa yaso ya kira Aunty babba don abasu Hosana yaji Muryarsu amma ransa yana bashi cewa yanzu sun isa suyi bacci, wannan dalilin ya hana shi calling ɗinsu,
Fitowa parlor dinsa yayi yasamu wuri saman sofa yazauna hannunsa ruƙe da wayarsa, sai lokacin yake dana sanin rashin daukar su hosana da jahad hoto ya ajiye acikin wayar shi koya samu na rage kewarsu, yana cikin wannan tunanin wayarsa ta soma ruri karatun kur'ani Ne ringin tone dinsa duba sunan daya bayyana a screen dinsa yayi nan take sunan*ABUSUFYAN*ya bayyana muraran,
Cikin hanzari ya ɗaga ya kara a kunnansa "Assalamu Alaikum Uncle Sufyan yau an tuna dani ne"?
On ther other hand ABUSUFYAN yace "Ko da yaushe cikin tunawa nake yi dakai Omar, nayi trying number dinka dazu baya shiga, kuma na jaraba ta RAFAYET tana ringing amma bai ɗaga ba,'
Omar yace " Kash ! rashin sani ɗazu ne na kashe wayar muna aiki ne shiyasa,"
Abusufyan yace "Dama inaso na maka magana ne About wannan yaran da goggon katsina ta ƙaƙabamun a matsayin ya'ya na"?
Murmushi Omar yasaki kamar yana agabansa yace "Ae ko ɗazu da safe ta kira ni awaya, kusan kullum ne sai ta mun Complain akan ƴa'ƴan abusufyan ɗinta,'
Abusufyan yace"Allah sarki, Nima tana kira na tana mun complain akan nasa ka mayar mata da ya'yana wuri ta, ynx ina yaran suke ne? Ya tambaya yana jiran amsa
Omar yace "A gidan general ishaq suke da zama, can na kaisu,"
"Ina iyayen su suke ne"? Ko yan uwan matar ishaq din ne? Ya tambaya
Omar yace "A'a Uncle yaran fa basu da kowa kamar yadda suka sanar mun, na haɗu dasu ne a asibiti cikin mawuyacin hali tagwaye ne baza su wuce 17years ba Suna buƙatar taimako,
Ajiyar zuciya abusufyan yasaki kafin yace "Meyasa ba zaka dawo dasu nan ba cikin abuja kusa da kai ba"?
"Uncle kaima ka sani, zaman su anan bazaiyi yu ba, maza ne mu duka duk ba wannan ba AMMI bazata ta6a lamuntar wani bare ya zauna acikin jinin ta ba,especially su da suka kasance basu da asali,' bayani yake masa tamkar yana agabansa
ɗan gyaran murya abusufyan yayi kafin yace "Listenin to me OMAR! kana da kyakkyawar niyya akansu, inaso ka kaddara aranka cewa waɗannan yaran jinin ka ne, kasanya wa ranka cewa Ƴa'Ƴa na ne, ya'yan ƙanin mahaifin kane *ABUSUFYAN* ina so ka basu kulawa Omar ! Dan Allah kada ka bari su wulaƙanta kayi mun wannan alƙawarin.......
Jikin Omar ne yayi mugun sanyi jin abun da Uncle Abusufyan ke faɗamasa, yanayin sautinsa da yadda yake yin kalamansa haƙiƙa ya ta6a Zuciyar Omar sosai, tunani omar yashiga yi aransa har sai da Abusufyan yace"Naji kayi shiru OMAR,"
Cikin sauri yace "Insha Allah Uncle i wll take care of them more than u think, nima inajin su araina sosai Uncle, ina ƙaunar yaran har cikin raina,
yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar Abusufyan alamar hankalinsa ya kwanta kuma yasamu natsuwa da bayanin Omar,
ABUSUFYAN yaci gaba da cewa "OMAR! INA SO KA DAWO DA YARAN NAN GIDA NA DAKE ANAN SU CI GABA DA RAYUWA, KA SANYA MUSU SECURITY TARE DA MAI AIKIN DA ZATA KULA DASU, INA SO SU RAYU ACIKIN GIDA NA, KAYI MUN WANNAN ALƘAWARIN!!!"
runtse ido Omar ya ɗanyi yana jinjina kalaman Uncle din nasa daga bisa ni yace "Insha Allah Uncle zanyi komai kake so, zan dawo dasu nan acikin gidan ka kamar yarda kake so,"
Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama, ya ajiye wayar yana mai tunani iri-iri aransa, yana ji aransa in ya ɗauke su hosana daga gidan aunty babba tamkar baiyi mata adalci ba don ya Lura tana son yaran kuma sun saba dasu anya kuwa zai iya cika alƙawarin Uncle Abusufyan Na dawo dasu hosana cikin Abuja da zama!!? 😟
Yana cikin wannan tunanin Sehrish ta shigo da sallama, batare da ya ɗago ya kalle ta ba ya amsa mata sallamar, sam ransa ajagule yake uncle dinsa ya ɗan ruɗa masa brain ɗinsa
Tray na a hannunta ƙarasawa tayi tare da gaishe shi "ina yini ya Omar," ƙiris ya rage omar ya ɗago ya kalle ta saboda Voice dinta tayi mashi kama da ta JAHAD, amma yabar Abun a matsayin muryar mai aikinsu ne ya koma masa ta Jahad Saboda kewarsu da yayi sosai
Amsa mata yayi da cewa "Lafiya lou"
Ajiye masa tray din tayi mai dauke da food stuffs dinsa asaman table Din dake a front dinsa sannan ta juya takama hanyar fita tana jiyo shi yana furta "ngde,"
Sauƙin kan MARSHAL OMAR yana matuƙar burgeta, babu ruwan shi ba kamar SGR ba, yana da IZZA ta wani bangaren kamar abinci muddin takai masa sai tayi saving ɗinshi, amma Omar sam baya buƙatar wannan kawai daga an kaimasa shi yake zuba abunshi yaci,
Saukowa tayi down a lokacin har su Twins da kanal yusuf Sun hallara suna cin dinner dinsu, tayi mamakin ganin babu Abbansu da junaid may be yana a part dinsa azmee takai masu acan
Gaishe su tayi gaba ɗaya suka ɗan dago suna kallonta, Kanal yusif ya amsa mata da sakin fuska amma Ayaan da jahan kuwa sai dai suka bita da ido,😡
Har bugun zuciya take ji in ta gansu cikin hanzari ta shige kitchen ta shirya ma SGR dinner ɗinsa ta fito ɗauke da tray ahannu ta nufi hanyar upstairs dinsa,
Da sallama ta shiga palor dinsa baya aciki, ƙarasawa tayi ta ajiye masa kayan abincin saman table dinsa, sannan ta ɗan dakata ko zai fito amma shiru babu alama,
. yanke shawarar zuwa bedroom dinsa tayi a bakin ƙopar shiga ta tsaya sannan tayi sallama, daga ciki taji ya amsa mata ƙasa ƙasa kafin ya bata permission ɗin shiga ciki,
A hankali ta zura ƙafa ta shiga ciki jikinta na ɗan kerma Hango shi tayi daga shi sai bathrobe ajikinsa kwance abaje saman gadonsa, alamu sun nuna cewa baiji ma da fitowa daga wanka ba, ya kwanta gajiya ce tayi masa yawa, idonsa na'a lumshe yace "Wanene ne,"
sehrish tace "mai aiki ce dama dinner ne na kawo maka yana a palor naga baka fito ba,
Jim yaɗanyi kafin yace "Tea kawai nake buƙata,akawo mun nan,'
Amsa mashi tayi da toh, sannan ta fuce ta koma palor dinsa ta ɗauko kayan tea din dake acikin tray din da ta ajiye anan sannan ta shigar masa dashi,
har gab da gadonsa ta ajiye masa saman madai-dai cin table din dake a wurin ta matsa masa dashi jikin gadonsa,
bin shi tayi da kallo saboda bai buɗe idonshi ba kuma baiyi yunƙurin tashi ba, yayi wani fresh dashi,
Ganin alamun fa zai iya zarcewa da bacci yasa tace "Na kawo maka Tea ɗin,"
"I knew," ya bata amsa, jinjina kai tayi ashe yasan ta kawo ɗin, wahalar tashin ce kawai yake ji, kusan 15 mins sannan ya ƴunkura ya miƙe tare da sauko da ƙafafunsa ƙasa, rigar iya guiwar ƙafarsa ta tsaya, saukin yasa shorts daga ciki amma chest ɗin shi a buɗe yake fari kal,
Zuba mishi ido tayi tana kallon ikon Allah wani irin bacci ne ke fusgar shi, ga uwar yunwa yana ji, ji take tamkar ta bashi tea ɗin abaki yasha, cikin sauri ta haɗa masa tea ɗin a cup ta ɗan tura masa agabansa tace "gashi nan,'
buɗe blue eyes ɗinsa yayi a hankali sannan yakai hannu daker ya ɗauki cup ɗin yakai bakinsa yana ɗan kurba da zafinsa, ya sha ba laifi kusan sau biyu tana ƙara masa yana shanye wa,
Bayan ya kammala tace "kayan dinner ɗin fa na mayar dasu"? Ta tambaya cike da jin tsoran amsar da zai bata,
"In akwai fruits ki haɗo mun," ya faɗi tare da mayar da jikinsa ya kwantar akan pillow,
Tattara kayan tea ɗin tayi sannan ta fuce dasu ta ajiye su a tray din dake ɗauke da warmers na abincin sannan ta ɗauke shi ta fita dashi kitchen ta shiga ta ajiye su, sannan ta ɗebo mashi fresh fruits acikin fridge,
A plate ta zuba mashi su sai da tafara yayyanka mashi su sannan, tana ƙoƙarin fita suka ci karo da Haroon tsaye abakin ƙopar kamar aljani,
Da ƙarfi ta furta "A'uzu billahi minashshaiɗanin rajim,'
Haroon ya fashe da dariya tare da cewa "Ni ne shaiɗan ɗin, ko kin ga ƙaho akaina ne?
"Eh," ta bashi amsa,
Yatsina fuska yayi yana bin jikinta da kallon frm up to down kafin yace "Haɗaɗɗiyar Sura,"
tace "Tubarkallah masha Allah,"
Murmushi yaɗanyi kafin ya kuma cewa "ki dai bi ahankali naga kamar zakiyi rawar kai Kada kici ka zaƙewa mana domin kuwa har yanzu fa baki da wani matsayi acikin gidan nan, duk inda za'aje adawo bakya wuce ƴar aiki, sannan na lura kina shisshige ma wancan ifritun ko? to inaso ki sani wancan dashi da dutse duk ɗaya suke indai agame da feelings ne, mace bata gabansa koda zai kula matan ma bana tunanin irin ki, ae ma zaren ba kalar yadin bane iska ce kawai zata wahalar da mai kayan kara.........
tun da yasoma magana idon sehrish suka soma ciccikowa da kwalla amma bata bari hawayen sun zuba ba, ganin zai bata mata lokaci yasa ta bi ta gefensa ta fuce da sauri, tana jiyo dariyarsa sam tarasa gane ma haroon, batasan mai ta tsone masa ba,
time ɗin da tashiga bedroom ɗin SGR samun shi tayi yana ta faman sharar baccinsa alamu sun nuna cewa ma tunda tasa ƙafa ta fuce ya fara baccin, tsayawa tayi akansa tana kallonshi hannunta na riƙe da fruits ɗinsa,
Yayin da idonta Suke cike da hawaye saboda kalaman haroon ita kanta tasani tabbas SGR ba tsaran yinta bane kwata-kwata bama haɗi, jinjina kanta tayi aranta tace "nasani kafi ƙarfina nesa ba kusa ba, kuma nasan cewa kafin ni akwai wanda suka ruga ni faɗawa wannan tarkon bila adadin, Amma inaji araina babu wadda zata soka dan Allah kamar yadda nake sonka, tun bansan ya kamannin fukarka suke Ba, da sunanka kawai nakamu da tsananin ƙaunarka kuma zan cigaba da addu'a akan hakan koda bazan ci nasara ba aƙarshe...Ana ahabbuk kasiran BABBAN YAYA.........❤💘
Wani irin juyi SGR yayi har sai da Sehrish ta ɗan tsorata gudun karya farka ya ganta, gyara kwanciyar shi yayi, yadda yake sakin numfashi anatse yana bacci ba ƙaramin tafiya yayi da ita ba,
Ajiye fruits ɗin tayi saman table sannan ta matsa a hankali cike da fargaba ta janyo lallausan blanket ɗinsa jikinta na ɗan kerma ta samu ta hayo dashi jikinsa ta lullu6a masa har zuwa neck ɗinsa,
Murmushi ta ɗan saki ganin ta kammala batare da ya farka ba, juyawa tayi ta tattaka izuwa inda makunnin hasken ɗakin yake ta kashe mashi shi, nan take ɗakin ya soma kyalli yana bada wani irin haske har sai da ta ɗan razana, ashe furnitures ɗin dakine masu wannan sparkling light ɗin launi daban daban suke badawa, aduk time ɗin da aka kashe hasken ɗakin Yayi dark gaba ɗaya su kuma sai su soma bada nasu hasken mai launuka, fuska ɗauke da murmushi sehrish ke kallon wannan ikon Allan Bin su take yi da kallo tun daga Bed ɗinsa da bedside table ɗinsa, drawer ɗin da ke ɗauke da mirrow jerin wurin Closet ɗinsa gaba ɗaya sun ɗau hasken nan, sai taga ya ƙara yi mata kyau sosai,
Lalla6awa tayi ta koma inda yake kwance tana kallon fukarshi yadda eye lashes dinsa suka fito radau zira zira dogaye kasancewar idon na'a rufe, sun kwanta luf,
Addu'ar bacci tashiga yi mashi saboda tasan cewa bai samu damar yi ba ayarda ya kwanta ɗin nan agajiye ta jima sannan ta ɗan tattofa masa ajikin bargonsa, kamar karta bar ɗakin haka take ji
(Nace ba mai zai hana kawai ki kwana anan Ehen 😂)
hannu tasa ta ɗauki Kayan marmarin dake acikin plate ɗin sannan ta fuce dashi bakowa a babban falon Dama tun fitowar farko da tayi duk sun kammala dinner ɗinsu sun shige cike aranta tace "Allah sarki su fawan hada rashin su yasa yanzu basu cika haɗuwa atare suna cin abinci ba ko zama a palor suna fira, ko yaushe zasu dawo? Duk da ina tsoran abunda zasu ce in suka ganni a
Matsayin mace, Especially fawan nasan halinsa sosai baijin magana shine ya ta6a bani horo harna galabaita," ta ƙarasa zancen zucin nata , bedroom ɗinta ta wuce da fruits ɗin saboda dama itama bata ci komai ba, asaman gadonta ta zauna tsakiyar gadon ta lankwashe ƙafa tana shan fruits ɗin tass ta shanye su sannan ta ajiye plate ɗin asaman side drawer ɗinta, dama empty yake tunda ta rotsa ma haroon fitilar saman shi akai, bata sake ajiye komai asaman wurin ba,
sauko wa tayi tashiga toilet saboda bata yi sallar isha'e ba, alwala tayi sannan ta dauko hijab ta zura bayan ta shimfiɗa carpet ta gabatar da salla,
Tana gama wa ta naɗe carpet ɗin ko addu'a bata tsaya yi ba, ta tura su cikin wardrobe sannan ta haye saman gadonta taja bargo ta kwanta daker tayi addu'a kafin bacci 6arawo yayi awon gaba da ita.................(Shin ko kun lura cewa Sehrish ta manta dasu hosana da jahad bakamar da ba? hmmmmm rayuwa kenan baka ta6a sanin asalin ya mutun yake sai yasamu wurin zama koya samu abun duniya nan zaka ga zahirinsa😥)
_____________________🌹🌹🌹____________________
In midnight Hosana tafarka da matsanancin Ciwo, wani sabon raɗaɗin ciwon ne ya taso mata agigice tafarka tana kuka tana zabga Uban ihu tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihiraji'un , La'ila ha illallah muharammadur rasulillah Wayyo Allah na, mutuwa xanyi, gaba ɗayansu suka farka hankali atashe tun daga jahad har hafsat dake kwance saman Sofa sai da tafarka a tsorace,
taruwa su kayi akanta jahad na faman yi mata addu'a tana tofa mata cikin kuka take faɗin "Hosana ki daina magana ciwon bakin ki zai ƙara raunata, dan Allah kiyi haƙuri innalallahi bansan ya zanyi ba,'tafaɗi tare da fashewa da wani sabon kukan itama, dama sai da ranta yabata cewa raɗaɗin ciwon hosana zai iya dawo wa sai gashi ya dawo, fuskar tayi suntum la66an sun kumburo hancinta ma yayi girma, idanunta ma sun kumbura duk kwantsa ko buɗe su bata iyayi saboda sun datse sosai, ita kaɗae tasan azabar da take sha ga haƙoranta suma nasu Zogin daban, ko'ina ciwo hakanne yasa ta haukace taita faman zabga salati tana kiran Sunan Allah da manzon sa 😭*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
*EPISODE 11-12* Ita kan ta Hafsat ba ƙaramin tashin hankali tashi ga ba ganin halin da yarinyar ta shiga, da alama ma raunukan nata sun ɗuri ruwa dole sai an fitar da ruwan Ya Salam, Yarfa hannu kawai take yi tana zabga uban kuka, hankali atashe JAHAD ta kalli hafsat tare da cewa "Aunty dan Allah ki taimaka mu mayar da ita asibiti aduba ta.....' ta ƙare maganar tana faman zubda hawaye,
Ita kanta hafsat tunanin da take yi kenan can ne kawai mafi ta, ta shi tayi jiki na rawa ta ɗauko hijab ta zura sannan ta ɗauki mukullin motarta da ta bari a saman mirror,
da kanta ta cuccu6i hosana daker ta ɗauko ta a kafaɗarta, ta fuce da ita cikin sauri itama jahad tabi bayanta a babban falon suka samu aunty babba saman Sofa hannunta ɗauke da plate ta dafa taliya sai faman ci take a tsiya ce saboda yunwar da ta taso ta, duk ihun da hosana take yi a kunnanta amma batayi yunƙurin tashi ba, balle taje ta dubo meke faruwa,
Ganinsu afujajen yasa ta miƙewa tana cewa "Hafsat ina zuwa cikin daren nan? Ina zaki kai ta?
Batare da hafsat ta kalle ta ba tace "Zan mayar da ita asibiti ne," hankali atashe aunty babba tace "Saboda me !! Acikin daren nan ! Ki barta kawai inyaso gobe dr yazo ya duba ta har gida,"
tsoki hafsat taja dama a ƙule take da Mommyn nata saboda duk ita taja mata halin da suke ciki,.
Wuce ta tayi tana cewa "da yake ba jikin ki bane ae dole ki ce haka,'
Bin su kawai aunty babba tayi da kallo har suka fuce, abayan mota hafsat ta kwantar da hosana, sannan suka shiga gaba ita da jahad, taja motar da gudu ta fuce da ita a wani privet hospital takai ta, cikin sa'a suka karbi hosana kuma nan take suka shiga bata taimakon gaggawa,
Yayin da hafsat da jahad suka samu wuri suka zauna nan waje suna jira saman waiting chairs, runtse ido kawai jahad ke yi tana faman karanto addu'a, tsigar jikinta har tashi take yi saboda jin yarda ihun hosana ya cika asibitin gaba ɗaya baiwar Allah, ita kaɗai tasan azabar da take sha,
Ita kanta hafsat dake gefenta jikinta duk ya gama mutuwa haƙiƙa taji tausayin Yarinyar fiye da tunanin mai tunani,
Jim kaɗan suka ji tsit babu kukan hosana babu alamar shi, jin hakan yasa jahad yin zumbur ta miƙe ta tunkari ƙopan ɗakin da suka kwantar da ita, tsoranta kar ace hosana ta mutu ne shiyasa suka ji shiru,
turo ƙopar Nurse tayi ta fito cikin sauri jahad ta tare ta tana cewa"dan Allah sister ya jikin nata yake? ta tambaya a ɗan ruɗe
Nurse ɗin tace "Alhamdulillah, kada ki sa damuwa aranki, jikinta da sauƙi sosae anyi mata dressing na raunukan nata sannan Mun taimaka mata da pain relievers yanzu haka allurar bacci mu kayi mata, addu'a kawai zaku ci gaba da yi mata,' tana faɗin hakan ta wuce gaba,
Ajiyar zuciya jahad tasaki har hankalin ta ya kwanta sosai, komawa tayi ta zauna gefen hafsat wadda ke ta faman yin gyangyaɗin bacci,
Rufe idonta kawai tayi tana faman ci gaba da yiwa hosana addu'a, bata jin zata iya runtsawa a daren nan,
tsawon awanni suna anan jugum time ɗin hafsat ta jima da yin nisa a baccin ta, jahad kuwa na nan ido buɗe, kamar daga sama taji hosana na kiran sunan ta ƙasa ƙasa da farko tayi tunanin gizau muryarta keyi mata amma daga baya ta tabbatar da cewa ita ɗin ce ke kiranta,
Cikin hanzari ta miƙe ta shiga ɗakin samun ta tayi ta tashi zaune saman gadon, ba ƙaramin farin ciki bane ya cika jahad, ganin yadda fuskar hosana ta sa6e an matse mata ruwan anyi dressing ɗin wurin ga bandage nan a forehead ɗinta da saman hancinta, duk da fuskar ta canza sosai kamar ba ita ba, idanuwanta sun buɗe sosai tana ganin jahad takama Murmurshi 😥
Faɗawa saman gadon jahad tayi ta rungumo ta sosai ajikinta tana faɗin "Allah sarki hosana ashe kin farka ban sani ba kina ta kiran suna na, ya jikin naki? Akwai inda ke miki ciwo yanzu"? Tayi tambayar tana janye jikinta daga na hosanar,
Daker ta iya cewa "Naji sauƙi sosai jahad ba inda ke mun ciwo yanzu, amma magana tana mun wahala,Kuma ina jin jikina kamar ba nawa ba"
hannu jahad tasa tana shafa gefen fuskarta tace "Insha Alah zaki dawo dai-dai hosana, yanzu hankali na ya kwanta tun da naga kina murmushi nasan cewa sauƙi ya samu, yanzu ki faɗamun wanene yayi maki wannan bugun mutuwar?'
turo baki hosana tayi tana cewa "Wannan mara imanin, saboda nazo na same ta, ta shaƙe maki wuya kamar zata kashe ki, na bata haƙuri ta ƙyale ki ta ƙiya shine na gartsa mata Cizo a hannun, wannan ne fa kawai yasa ta kamani ta jibga ta faffasa mun fuska..........," shessheƙar kukan da take yi ne ya hana ta cigaba da maganar
Cikin sanyin Murya jahad tace "ashe duk don saboda ni ne tayi maki wannan bugun, babu komai akwai ALLAH ! , Zai bi mana haƙƙin mu duk wanda ya zalunce mu Allah zai saka mana insha Allah!
Jinjina kai hosana tayi tana share hawayen ta tace "Yaya Omar bazai ƙyale su ba, duk sai sun gane kurensu.....
ta faɗi wit angry face can kuma ta sake cewa "Jahad komai yasa yaya Omar har yau baizo ya duba mu ba"?
Jahad tace "muyi mashi Uziri hosana, ni nasan cewa yana sane damu kuma zaizo nan very soon,'
Sun jima suna yin fira atsakanin su, ita kanta jahad tasan cewa hosana juriya kawai take yi tana yin surutu, daker tasamu hosana ta koma ta kwanta, itama a gefenta ta ra6a ta kwanta, lokaci guda bacci ya kwashe su su duka,
Ba ƙaramin bacci suka sha ba, don kuwa har sai da gari ya waye rana ta fito sannan jahad tafarka, hosana kuwa nata faman sharar baccin ta, ganin yadda hosana ke bacci anatse ya ƙara tabbatarwa da jahad cewa tasamu sauƙi sosai, tashi tayi ta cire hijab ɗin dake jikinta, ta shige toilet ɗin dakin Alwala tayi sannan ta fito ta ɗauki hajiabin ta zura, tana faman tunanin in da zata samu tayi sallah don babu carpet,
Fitowa tayi don ta duba hafsat samu tayi bata anan inda tabar ta jiya babu ita ba alamarta a wurin, sai taji hankalin ta ya ɗan tashi tsoranta kar ace guduwa tayi tabarsu a asibitin,
Hankali atashe ta fito harabar asibitin ga mutane nan nata wuce wa wasu na shigowa wasu na fuce wa, sai faman waige waige take yi tana neman hafsat, har wurin ajiye motoci taje taga ko zata ga motarta amma babu ita, hakan na nufin tabar asibitin kenan, da alama ma tun asubahi tabar asibitin, tuni jikin JAHAD yayi mugun sanyi,
Koma wa tayi tasamu wurin inda taga wasu mata zazzaune suna fira, tayi musu sallama suka amsa mata da fara'a
Tambayarsu tashiga yi idan suna da abun sallah su ara mata, nan wata daga cikin su ta miƙa mata sallaya ɗinsu da suka zo da ita, anan harabar jahad tayi sallah bayan ta kammala ta mayar masu da dardumar sannan ta koma ciki a kasalance, bakowa tafi ji ba face HOSANNA, yanzu in da gaske hafsat tafiya tayi tabarsu yaya zasu yi? Ina zasu dosa? bakomai ma yafi damunta ba face Hosana in tafarka ta son dole akwai yunwa atattare da ita, gashi ita ba ta da ko sisi balle ta siya musu abunda zasu samu su Ci,
Gefen hosana tasamu ta zauna wadda ke kwance tana faman sharar bacci, tagumi ta zabga tare da zuba mata Ido tana kallonta, in taƙaice muku tsawon lokaci ba hafsat ba alamarta 😧😳 Gashi in sunce zasu kai kansu gidan duka ba wanda yasan hanyar da zai bi, saboda da daddare ne kawai suka fito daga gidan baza su iya shaida kwatancen gidan ba, gashi ko Sunan unguwar basu Sani ba, ajiyar zuciya jahad tasaki aranta tana jin cewa hutu ne yazo musu, zasu ci gaba da rayuwarsu ne kawai akan titi,
_____________________SEHRISH__________________
Around 8 Ta farka kai tsaye kitchen ta wuce har time ɗin rigar jiya ce ajikinta da rolling ɗinta, a kitchen ta samu Azmee harta kusan kammala breakfast din gaba ɗaya, bayan tayi sallama ta shiga suka gaisa da junan su, Daga bisa ni azmee tace "Ina fata jiya kin kai ma SGR dinner ɗinsa ko? don na shigo na taras da kayan abinci a warmers ko ta6a su ba ayi ba,'
Sehrish tace "Na babban yaya ne, Jiya bai samu yaci ba dana kai masa, Tea kawai yasha daga baya yace mun yana buƙatar fruits, shine kafin naje na kawo masa har bacci ya ɗauke sa,'
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Allah sarki da alama jiya sun sha aiki ne that's why harya gaza cin abinci, Yanzu bari na shirya miki breakfast ɗinsa ki kai masa da sauri saboda nasan dole ya tashi da yunwa,'
Sehrish ta amsa mata da Toh, ta tsaya tana jiran ta shirya mata kayan breakfast ɗin nasa,
Shiru tayi tana tunano maganar da HAROON ya faɗa mata jiya, akwai abunda ya tsaya mata arai take son fitar dashi
"Aunty azmee dan Allah me ake nufi da ZAREN BA KALAR YADIN bane? ta tambaya tana kallom azmee dake shirya abinci cikin warmers asaman kitchen drawers din dake jere,
Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace "idan aka ce Zaren ba kalar yadin bane, a tunani na ana nufin kamar abunda bai dace da wani ba, a misali kamar ace kina son wani wanda yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, bari na baki wani misali ma kamar yanzu ace mace tana Son Namiji wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi ne ko mai mulki ga ilmi ga kyau gashi prominent dae, ke kuma ace kin kasance ƴar talakawa ce koma kina aiki a ƙasan shi baki da duk wani abu daya mallaka da zaku zo ɗaya dashi kin ga kuwa ba sa'an yin ki bane,wannan shi ake nufi da Zaren ba kalar yadin bane......'
Jinjina kai sehrish tayi aranta tana cewa "Wato abunda haroon yake nufi kenan hmmm,"
Sannan a fili tace "To Aunty azmee me ake nufi da cewa ISKA NA WAHALAR DA MAI KAYAN KARA,!"?
Har sai da azmee ta ɗanyi dariya jin wannan, ɗan gyaran murya tayi kafin tace "Kamar mutun ya yi ta wahalar da kansa akan abunda bazai ta6a samu ba, yanzu in mutun ya sanya kayan kara ana iska shin kayan zasu zauna ne batare da sun tarwatse ba?
Sehrish tace "Eh hakane kuwa,"
"Yawwa ma'anar kenan, mutun yasanya wa ransa abunda bazai ta6a samu ba, kin ga zai tashan wahala ne,"
ta ƙarasa maganar tare da cewa "Zo ki ɗauki breakfast ɗin ki kai masa na kammala,"
ƙarasawa sehrish tayi ta ɗauki tray ɗin duk jikinta yayi sanyi ga me da abunda Azmee ta fassara mata yanzu, amma taci alwashin duk runtsi duk wuya zata jaraba Soyayyarta Agare shi ba fashi 💔
Fuce wa tayi ta miƙi hanya kamar daga sama taji muryar haroon a kunnanta yana cewa "ƴar Shila barka da safiya fatan kin kwana cikin ƙoshin lpy,
Shiru tayi bata bashi amsa ba, yana tsaye ruƙe da ƙugu daga shi sai gajeran wando ajikinsa,
Ci gaba da magana yayi "Dole kisha ƙamshi baby, an fa samu Freedom dole a hura hanci, hallau dae bari na ƙara tunasar miki, shisshigi da kutsi ba zai kai ki ga cin nasara ba akan wancan Babban kayan da ki ke hari, ke bama shi ba ko junaid dana ga kina shisshige mawa wlh yafi ƙarfin ajin ki, kwara ma ni zan iya yin maneji na lalla6a ki mu rufa wa juna asiri, ke ƴar aiki ni kuma ɗan masu gida Fantsararre,,,
takaici ya hana ta cewa komai wuce wa kawai tayi upstairs,
Tun da ta nufi part ɗinsa take jin tashin ƙamshi ya gauraye ko'ina Har cikin hancin ta direct masu daɗin ƙamshi,
Bayan tayi sallama tashi ga, babu kowa a palor ɗinsa ƙarasawa tayi ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗinsa, tsayawa ta ɗanyi don ta jira fitowarsa,
Tana cikin tsayuwar nan wayarsa da ya bari asaman hannun Sofa ta soma ringing da ƙarfi har sai da sehrish ta ɗan yi firgit da ido, kai idonta tayi a inda wayar take hada sa hannu tana dafe kirjinta, matsawa tayi a ƙoƙarinta na ta ɗauki wayar takai masa,
Adai-dai time ɗin yafito cikin sauri Don ya ɗauki wayar saboda Kira ne mai mahimmanci agare Sa yasan dashi
Jin motsin mutun yasa sehrish ɗagowa takai ido a kansa, aikuwa a tsananin firgice ta ɗanyi wani sauti tare da yin Hanzarin juyawa cikin tsananin farga ba,
Sam baisan da mutun ba, fitowa yayi daga shi sai ɗan pant a jikinsa gaba ɗaya halittar jikinsa ta bayyana,
bin bayan ta yayi da kallo mamakin sa ganin yarda ta razana kamar taga wani dodo, wuce wa yayi yasa hannu ya ɗauki wayarsa sannan ya shige ciki yana amsa kiran a kunnansa,
Juyo wa sehrish Tayi jin alamar ya koma ciki sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, gaba ɗaya duk ta firgice ta gigice ta tsorata da yanayin da tagansa,*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
_🔥The Father Of Soldiers🔥_
Story & Written
By
*BOSS BATURE*
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·*Episode 13-14*•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
Tsawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, after some minutes sai gashi ya fito jikinsa sanye da jeans da t-shirt, hannunsa ruƙe da wayarsa ya samu wuri ya zauna saman Sofa, cikin sauri sehrish ta gaishe shi "Barka da safiya, fatan ka tashi lafiya," a tunaninta bazai amsa ba amma sai ji tayi yace "Alhamdulillah Am well," murmushi ta ɗan saki, kafin ta shiga haɗa masa Tea a cup mai ɗan xafi ta tura masa agabansa, hannu yasa ya ɗauka yakai bakinsa yana kur6arsa a hankali, ci gaba da saving ɗinsa sehrish tayi, kamar daga sama taji yace "Meyasa jiya ba'a kawo min fruits dana buƙata ba"!?
Murya na rawa sehrish tace "na same ka kana bacci ne lokacin dana kawo maka," ta ƙarasa maganar tana kallon fine face ɗinsa,
Bayan wasu mintina ya kuma cewa "daga yanzu inaso a rinƙa kawo min Coffee or Tea wit fruits around 12 pm,"
Cikin hanzari ta amsa mashi da cewa "Insha Allah," jinjina kansa ya ɗanyi yayin da yake ci gaba da cin pancakes ɗin data haɗa masa da Zuma,
tsayawa sehrish tayi tana jiran ya kammala ta zuba mashi wani abun,
Wayarsa dake ajiye a gefensa ta soma ringing cikin sauri takai hannu zata cirar mashi tissue ya goge hannunsa adai-dai lokacin shima ya miƙa hannunsa zai cira karaf suka haɗa hannunsu cikin na juna 😌 zaro ido sehrish tayi cikin tsananin jin tsoro tana ɗan kallonsa,
Shi kuwa bin hannun Yarinyar yayi da kallo sam ba'a yi masa irin haka amma yayi mata Uziri ne saboda da alama batasan ko shi wanene ba, gata kuma ƙaramar yarinya,
"Am sorry,...' sehrish ta furta aɗan tsora ce yayin da ta janye hannunta, shi kuma ya ciri tissue ɗin a natse yace "Don't repeat that mistake again,"
Cikin sauri tace "Insha Allah," goge hannunsa yayi sannan ya ɗauki wayar ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnansa, taso taji mai zai ce acikin wayar amma sai dai kash cikin wannan harshen taji yana magana wato Espanol da alama yafi jin yaren sosai ko kuma shi ya taso yana ji,
Zuba mashi ido tayi tana kallon shi tun daga shafaffen cikinsa har zuwa saman wide Chest ɗinsa haɗaɗɗiyar ƙira, maganar haroon ta tuna dayake cewa Zaren ba Kalar yadin bane Iska ce kawai zata wahalar da mai Kayan kara, tabbas kuwa yayi gaskiya amma in ta tuna wannan karin maganar da ake Cewa *DUK KYAN TAKALMI ƘAFA CE ZATA TAKA SHI* sai taji wata irin natsuwa tazo mata, tana tunani tana ci gaba da kallon fuskarsa yadda yake Moving pink lips ɗinsa yana magana tamkar baison yi, da kuma yarda yake faman lumshe sexy blue eyes ɗinsa ba ƙaramin Yanayi yake jefa ta ba,
"Allah yasa bada budurwarsa yake waya, koda yake aunty azmee tace baya soyayya, To Allah yasa dai bada mace yake waya ba," ta faɗi acikin zuciyarta saboda ganin yarda yake ta faman lumshe idonsa kamar wanda ke waya da mace cikin shauƙi,
tana cikin yi mashi wannan kallon ƙurullan nata ya kamata, adai dai time ɗin ya ɗan ware idonsa direct suka sauka kan na sehrish dake faman Zuba masa ido tana kallonsa abunda ya tsana arayuwarsa ba, sam bata lura daya kamata ba saboda idonta na akan Sumar kansa, har sai da ya ɗanyi gyaran Murya cikin sauri ta wurga kwayar idonta kan tashi aikuwa har sai da ta ɗan Razana ganin ya aza idonsa acikin nata Unexcepted,
ƴar harara ya wurga mata sannan yace "Stop looking at me, i don't like,' ya faɗi tare da cigaba da yin wayarsa,
Sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunyar Kamatan da yayi tana masa kallon kurulla, amma wannan hararar daya sakar mata ba ƙaramin kashe mata zuciya yayi ba, ya jima yana wayar kafin ya kammala ya ture ta gefensa, sehrish ta cigaba da saving ɗinshi harya kammala cin breakfast ɗin nasa sannan ta tattare komai ta fuce dasu kitchen ta ajiye agefen Kitchen sink yadda in tadawo wankewa kawai zatayi,
Daker ta iya fitowa daga kitchen ɗin saboda taga duk sun Hallara suna yin breakfast, tunkarar su tayi gabanta na faɗuwa saboda ganin hada HAROON zaune ga kuma Twins duk suna zazzaune, tunkan ta isa junaid na ganinta yasoma sakin murmushi kamar gonar Auduga, sallama tayi masu suka amsa sannan ta kalli Abbansu wanda keta faman sakar mata murmushi tace "Ina kwana Abba, fatan kun tashi lafiya," Abban nasu yace "Alhamdulillah My Only daughter, yanzu nake tambayar azmee take cemun kin shiga kaiwa Babban yayanku Abinci,"
"Eh hakane," ta bashi amsa sannan ta juya ta kalli sauran ta gaishe dasu duk suka yi tsit sai kanal Yusif daya ce "Ae nayi tunanin bazaki gaishe da yayyen naki ba, yanzun nan nayi fushi dake,"
Murmushi sehrish tasaki tana mai mamankin hali irin na kanal Yusuf sam bakamar na sauran ba,
"Samu wuri ki zauna mana," Abbansu ya umarce ta kujera taja ta zauna zuciyarta na ɗar ɗar, tana a jerin inda Abbansu yake gefensa junaid daga shi sai ita, a ɗayan side ɗinta kuwa haroon ne tabbas tasan dole ya hantare ta, ga kuma AYAAN Da JAHAN da take facing ɗinsu duk ta tsargu saboda tasan halinsu suna jere tare da kanal yusif,
azmee da kanta tayi saving ɗinta acikin plate ta buɗe saving dish ta zuba mata Chicken pper soup
Sannan ta haɗa mata da Cofee acikin Cup☕ Sehrish ta kalli azmee tare da cewa "nagode aunty amzee"
hararar ta amzee tayi alamar cewa bata son godiyar,
..a hankali take kurbar coffee ɗinta duk da kermar da hannunta ke yi, muryar haroon taji a ƙunnanta yayi ƙasa ƙasa da Voice ɗinsa don kada wani yaji yace"Su acici mala'ikun tauna, an fa samu wurin zama, to adai ci ahankali kar a shaƙe," banza tayi dashi batace komai ba, amma sam tarasa cin chicken ɗin dake agabanta shaƙe cikin plate,
Sanyayyiyar muryar junaid ce ta ratsa kunnanta da cewa "Sehrish ya akai naga yanayin ki ya canza? ko breakfast ɗinki baki fara ci ba,"
tace "bakomai junaid kawai bana jin daɗi ne, inaji kamar na tashi na tafi ɗaki kawai,"
cikin sauri junaid yace "a'a reesh pls kada kiyi haka ki daure kawai ki ci, kinji My sister," murmushi tasaki jin sunan da junaid ya kira ta dashi, ɗan ɗagowa tayi da idonta karaf suka sauka kan na Jahaan da Ayaan da suka ɗago atare, shiru tayi tana ɗan kallonsu, atare suka yatsina fuska suna yi mata wani irin kallon Tara saura kwata,
ƙasa da murya Jahan yayi tare da cewa "Ayaan kalli yarda junaid ke fira da wancan yarinyar, shi junaid kowa nasa ne, baya tsoran mutane sai sunyi masa Illah," yayi maganar cikin nuna damuwa
Ayaan yace "ba kai kaɗai ba jahaan, ni ma abun na damuna wlh, shiru kawai nayi amma na lura da yadda suke shiri, bazan ƙyalesa ba dole na buga masa warning Allah,
Jahan yace "gasky kam, janyo shi yakamata muyi a ɗakin mu, muja masa kunne tunda shi shashasha ne kowacce baƙuwar fuska shige mata yake yi, sai kace ba Jinin mu ba,"
Ayaan yace "kwarai kuwa, ae shi junaid da kake ganinsa half cast ne, ruwan Abba ne dana Mommyn mu ya ɗauko, mu kuma ruwan mommy ne kawai ajikin mu, banda na daddy," Wannan maganar ta Ayaan tasa kanal yusuf fashe wa da dariya ashe duk yana jin firar tasu saboda shine kusa dasu a jere, ɗagowa su kayi suna kallonsa dukansu hada Abban nasu da junaid da sehrish da azmeee,
Abban nasu yace "in ce dai ko lafiya? Kanal yusif yace "babu komai Abba, gasu nan su Ayaan da jahan ne suke fira su faɗa maka abunda suke cewa ka ji,"
tunkan Abbansu ya tambayesu suka haɗa baki wurin cewa "Babu komai Abba, firar wani film muke yi,'
girgiza kai kawai Abbansu yayi, Haroon kuwa cewa yayi "Allah yayi wa ɗan iska uwa koda ta kara ce," ya faɗi yana kallonsu salon jan faɗa kawai, Babu wanda ya tanka masa miƙewa Ayaan da jahan su kayi tare da yiwa Abban su sallama suka fuce,
💪 Fito wa marshal Omar yayi daga upstairs yana saukowa down jikinsa sanye da jallabiya ash colour sai faman ƙamshi yake yi, tunkaro su yayi Abbansu na ganinsa yafara fara'a yana cewa "Omar sai yanzu ka tashi? tun ɗazu nake ta faman waige-waige naga ta ina zaka 6ullo,
Ɗan ƙayataccen murmushi yasaki tare da cewa "Gm Abba ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya,"
"Alhamdulillah Son, Samu wuri ka zauna na baka abinci a baki," cikin zolaya yayi maganar su kuwa sauran dariya su kayi, ɗagowa OMAR yayi tare da gaishe da Azmee ta amsa mashi, sannan su kuma Su kanl yusif da junaid suka shiga gaishe shi, Haroon yace "Barka da fitowa Damusa mai maganin ƙananun ƴan iska,"
ɗan harararsa Omar yayi tare da cewa "Zaka fara wannan tsokanar taka ko? To ka shiga taitayin ka ko yanzun nan na saita maka waɗannan haƙoran naka, don naga ba'a jere suke ba,' shima da zolaya yayi maganar ayayin da yake zama azmee kuma ta soma zuba masa breakfast ɗinsa,
Mayar da idonsa yayi kan JUNAID dake ta faman sakar masa murmushi yace "My shagwa6a boy, irin wannan kallon haka da kake mun ko kana buƙatar wani abu ne?
Cikin jin kunya junaid yace "Babu komai ya Omar kawai inaso inta kallon ka ne, aduk lokacin danayi kewarka,"
Murmushi Omar yayi kafin yace "Ae da ka sani jiya ka shigo bedroom ɗina mun kwana tare,"
Junaid yace "ae Abba bazai bari ba, Kishi yake yi," gaba ɗayansu suka fashe da dariya jin abunda junaid yace,
Abban nasu kuwa murmushi kawai yayi tare da ɗan jinjina kai yana kallon junaid ɗin,
Haroon yace "Ae na Lura da yadda Abban mu ke ji dakai, kamar kai kaɗai ya haifa bayason komai ya same ka,'
Junaid yace "Yaya haroon ka ta6a ganin inda mutun ke wasa da bugun zuciyarsa? to aeni zuciyar Abban tamu ce gaba ɗaya shiyasa Yafi sona," yayi maganar wit proud,
ta6e baki Haroon yayi yana kallonsa, MARSHAL OMAR yace "Ae bama Abban mu kaɗai ba Haroon, Junaid farin cikin kowan nan mune acikin gidan nan, bamu son wani abu ya same shi domin tamkar mu yasha fa, JUNAID BUGUN ZUCIYAR FAMILY ɗin mune gaba ɗaya,"
Kanal yusif ya ƙara da cewa"Maganarka gaskiya Ce Yaya OMAR, Ni kaina aduk lokacin dana aza idona akan na baby junaid wlh farin ciki ne ke ziyarta ta, kuma aduk lokacin da wani ya 6ata mun rai junaid ne ke lallashi na da kalaman sa masu kwantar da hankali, tabbas shi Yaro ne amma yana da baiwar iya sarrafa harshe wurin farantawa mutane,"
Har cikin zuciyarsa yake wannan bayanin, junaid kuwa farin ciki ya hanasa idasa shan cornflakes ɗin dake agabansa, haka zalika Abbansu murmushi ne a fuskarsa saboda bai da Burin daya wuce yaga ana yabon Jininsa, kuma ma Junaid,
Haroon kuwa tuni zuciyarsa tayi baƙiƙƙirin ji yayi bazai iya ci gaba da zama ba, don haka da hanzari ya miƙe tare da fuce wa daga babban falon gaba ɗaya, sam ba wanda ya damu dashi bare su son halin dayake ciki,
Duk fa wannan abun dake faruwa a kunnan Sehrish tana sauraron su, sam tagaza gaishe da Marshal Omar tsoran ta kada ya ƙi amincewa da ita duk da ta lura bazaiyi Tsauri ba,
Sai da tabari duk sun natsu wuri ya ɗanyi tsit sannan ta ɗanyi gyaran Murya tare da cewa "YAYA OMAR ina kwana,"
Jin Muryar mace yasa shi saurin ɗagowa yaga wacece karaf fararen idanuwansa suka sauka akan na SEHRISH, ae baisan lokacin da ya fesar da Tea ɗin daya kur6a abakinsa ba, hankali atashe yake kallonta, Ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tare da miƙewa tsaye idonsa akan na sehrish wadda ta gama tsorata dashi ganin yadda ya firgita da ganinta kamar yaga wata ALJANA, tuni jikin sehrish ya soma kerma, ita kanta azmee ta tsorata da ganin reaction ɗin Omar akan Sehrish haka zalika Abbansu kanal yusif da junaid duk mama ki ya ɗaure musu kai
Nuna ta da hannu Marshal Omar yayai tare da cewa "Keeeee !!!!!!!!!! " gaba ɗaya ya razana da ganin yarinyar, ganin haka yasa kowannan su ya tashi tsaye suna kallonsa,
Abbansu yace "Omar meya faru ne? Na manta ban faɗa maka ba game da yarinyar nan ba, ƴa Ce Allah yabani daga sama....
.kallonsa Omar yayi a ruɗe kafin ya mayar da idonsa kan Sehrish wadda tuni idonta sun cuccuko da kwalla saboda tashin hankali,
da hanzari OMAR ya bar dining ɗin yayi saurin haye wa upstairs part ɗinsa, zuciyarsa a cunkushe sam yagaza gane ma Idonsa dayake yi masa Gizan Fuskar Hosana da Jahad a fuskar wannan yarinyar daya gani a yanzu,
Bedroom ɗinsa ya shiga hannu yasa ya ɗauki wayarsa daya ajiye asaman pillow, cikin hanzari ya daddana layin aunty babba ya buga mata Call, kusan 3 times yana kira bata shiga, numbar Hafsat ya kira itama tana ringing ba'a ɗagawa,
Wurgi yayi da wayar saman gadonsa, tsayawa yayi yana faman sauke ajiyar zuciya, hannu yasa ya dafe kansa tamkar wanda ke fama da ciwon kai, tabbas ransa na basa cewa Ba fuskarsu hosana bace a fuskar yarinyar, ya sawa ransa cewa tsananin Son da yake yi ma yaran ce da ƙaunar da yake yi musu da kuma kewarsu da yayi ya sanya Fuskarsu keyi mashi gizau afuskar yarinyar daya gani ayanzu, tabbas Omar yayi Confusion ɗin kansa, ya rikita tunaninsa bazai ta6a yarda da abunda idonsa ke nuna masa ba akan Waccan Yarinyar................
Ajiyar zuciya yasaki aransa yana ƙara jin cewa bai kyauta musu ba da baije ya dubo su, amma ya shirya zuwa gobe domin ya duba su,
Yana gama wannan tunanin ya dawo Downstairs da sauri ya sauko a lokacin Sehrish harta gudu zuwa ɗakinta saboda ta tsorata,
Abbansu na ganinsa yace "Omar wai lafiya meya faru ne? Naga duk ka rikice lokaci ɗaya ko don saboda wannan yarinyar ne da ka gani yanzu,"
Zama Omar yayi yana cewa "No ba haka bane Abba just there's something that confused me but am ok now,"
Ajiyar zuciya Azmee tasaki jin yace babu komai, ci gaba da yin breakfast ɗinsa yayi anatse but still his brain was confused,
Zuwa wani lokaci kowa ya Kammala breakfast ɗinsa sai daga bisani Sehrish ta fito suka shiga gyara gidan ita da azmee,
______________________________________________Farkawa hosana tayi da wata irin matsananciyar yunwa don hada kukan ta dama ita bata da jumurin yunwa ko kaɗan, hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda hosana ke ta faman rusa kuka gashi sai faman lallashinta takeyi amma sam taƙi yin shiru sai ta runƙa cewa "baki ji yadda nake ji bane, babu komai acikina kamar zan mutu," runtse ido jahad tayi sam tarasa abunyi, yanke shawara tayi kawai tafita waje taga ko zata samo mata abinci, tun da taga akwai visitors dake zuwa wurin marasa lafiya wata'kil ko Allah ya haɗa ta dana gari su sam mata abinci taba Hosana, tashi tayi cikin sauri tana cewa "Hosana ki jira dan Allah ki daina kukan nan, yanzun nan zan dawo," shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,
fita jahad tayi tana faman zarya a asibitin wurin nema musu abincin da zasu ci, taimako yayi ƙaranci a arayuwar nan domin kuwa duk wanda jahad ta tunkara da niyar ya taimaka musu sai suce suma bazai ishe su ba, ga abinci nan tana gani haje-haje agaban wasu sun baje suna ci amma tarasa wanda zai taimaka musu koda da rabin plate ɗaya ne,
A ƙarshe da ta gaji da yawon neman taimakon abinci sai ta samu wuri abakin wata bishiya ta zuƙunna tare da kifa kanta tana faman shesshekar kuka, babban tashin hankalinta yarda zata tunkari hosana tace mata bata samo masu komai ba, 😥
tana cikin wannan zuƙunnan Motar hafsat tashigo asibitin da gudu tayi parking ɗinta a harabar ajiye motocinsu, fito wa tayi fess da ita tayi wanka ta canza kayan jikinta yanzu tsadaddiyar atampha ce riga da skirt ajikinta sun bi shape ɗin jikinta very tight, ta ɗaure kanta da ɗan kwalin sannan ta yafa veil a shoulder ɗinta, ƙarasawa tayi ta buɗe back seat ɗin Motar hannu takai ciki ta ɗauko kwando mai ɗauke da kayan abincin da tazo masu dashi, bayan ta rufe motar ta wuce ciki sam bata lura da Jahad ba, haka itama jahad bata ɗago ba balle taganta,.
tana ƙokarin shiga cikin ɗakin da aka kwantar da hosana dr yafito suka ci karo, ganin ta yasa ya saki fara'a yana cewa" ke ce mai kula da wannan patient ɗin ko"?
Hafsat tace "Yeah its me,"
Dr yace "yawwa tun dazu take faman kukan yunwa gashi naga ba kowa tare da ita, amma tun da kin zo yakamata ki kula da ita, sannan idan ta kammala cin abincin akwai magungunanta dana ajiye wanda za'a bata,"
hafsat ta amsa mashi da cewa "Shikenan dr ngde ssae," tana faɗin hakan ta wuce ciki shi kuma ya nufi cikin asibitin,
Samun hosana tayi tayi kukan tayi mai isarta har ta gaji, tana zaune saman gadon ta kife kanta saman guiwowinta, jin muryar hafsat yasa ta ɗagowa cikin sauri,
Ae tana ganinta ɗauke da food stuffs a basket nan take jikinta ya soma rawa kaf-kaf kamar kura taga nama,
Da murmushi hafsat ta isa ta zauna gefen gadon kusa da Hosana tana cewa "Ya jikin naki"? Murya na rawa Hosana tace"da sauƙi sosai" ita burinta tafara zuba ma cikin ta abinci,
Ajiye basket ɗin hafsat tayi ƙasa, sannan tasanya hannunta ta curo flask mai ɗauke da haɗaɗɗen ruwan tea ta ajiye sa, Cup ta curo guda biyu ne a haɗe, ɗaya ta ɗauka ta bude flask ɗin ta tsiyaya mata shi sannan ta zuzzuba mata madara da bornvita aciki har sai da yayi kauri, sannan ta miƙa ma hosana, kar6a tayi takai bakinta tana sha da hanzari har wani sauti maƙoshinta keyi kwat-kwat , kusan sau 3 tana shanye wa hafsat na ƙara mata, bayan ta kammala ta ciro kula mai ɗauke da Chips haɗi na musamman, ta zuba mata a plate, miƙa mata tayi tana cewa "ki ci a hankali saboda ciwon ki," hosana ta amsa da "toh" Turawa kawai take yi abaki kamar zata haɗa da plate ɗin duka, bayan tagama dashi hafsat ta zuba mata fruits a plate ta bata, shima tashiga sha kamar kamar me,
"Ina Ƴar uwarki take ne ban ganta ba"? Hafsat ta tambaya yayin da take kallon hosana,.
Hosana tace "tun ɗazu ta fita tace na daina kukan yunwa na jira ta, har yanzu bata dawo ba,"
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Nasan bai wuci taje nema muku abunda zaku ci bane, May be tayi tunanin na tafi nabarku ne,"
suna cikin magana jahad ta turo ƙopar a galabaice take tafiya saboda tsabagen yunwa, ƙafafunta har harɗewa suke yi tana tafiya kamar wadda tasha Codine,
shigowa tayi tana faɗin"hosana sai dai kiyi haƙuri wlh bansamu komai .........' ganin hafsat yasa ta dakatawa da maganar cikin mamaki take kallon su, hannu tasanya tana murza idonta don ta tabbatar wa kanta cewa ba mafarki take yi ba, sakin hannunta tayi tana ƙare masu kallo, Expecially hosana data gani sai faman cusa fruits takeyi abakinta wanda hafsat ta zuba mata,
Wani irin farin ciki ne ya cika jahad har batasan lokacin da ta fashe da kuka ba Don tsabar murna,
tashi hafsat tayi ta ruƙo hannunta tana cewa "Kukan ya isa haka, tun da gani na zo ko? Halan kinyi tunanin na gudu ne nabarku shiyasa kika fita nema muku abinci"? ta tambaya tana kallon jahad dake faman shesshekar kuka tace"Nayi tunanin kin tafi kin barmu ne shiyasa na fita, ashe zaki dawo,".
ɗan murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Am so sorry nayi laifi ban sanar muku ba, da asuba na tafi gida, nayi sallah bacci ya kwashe ni without my knowing bayan na tashi ne kuma na wuce kitchen na shirya muku breakfast dana kammala shine nayi wanka na fito,"
bayani take yi jahad na kallonta tsananin mamaki ne yakamata ganin yadda lokaci guda Hafsat ta canza musu gaba ɗaya tamkar ba ita ba, tazama wata mutuniyar kirki lokaci guda ANYA?
jan hannunta hafsat tayi ta zaunar da ita gefen hosana sannan tashiga saving ɗinta abincin tare da miƙa mata, sannan ta haɗa mata tea itama, bayan ta kammala ta samu wuri saman plastic chair ɗin dake facing gadon da suke tana kallonsu,
A hankali Jahad ke kurbar tea ɗin tana ɗan kallonta, bakomai take jin tsoro ba fa ce kada ace Hafsat tasanya musu POISON acikin abincin da takawo su,tun da dama tasan sarai neman hanyar da zasu kawar dasu suke yi, kuma wannan ce hanya mafi sauƙi, yadda hafsat ɗin ke kallonta ido cikin Ido yasa Jahad ƙara jin wani irin Tsoro aranta nan take hannunta ya shiga yin kerma kaf!kaf!kaf! 😳😳😳
Wani shu'umin Murmushi Hafsat tasa ki tana cewa "nasan mai ki ke tunani JAHAD, tabbas abunda kike tunani gaskiya ne, POISON nasanya muku a abincin saboda wannan ce hanya mafi sauƙi da zamu kawar da ku acikin arayuwarmu, kuma zaku huta da wahalar zaman duniya,"
Hankali atashe Jahad ta Zazzare ido waje jikinta na kerma tace "POISON!!!!!!!!!!!!!! "*🪩🪩🪩ABBAN SOJOJI🪩🪩🪩*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·15-16•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·
____________(✪)____________
Story & Written by *BOSS BATURE*
Firgit jahad tayi daga zurfin tunanun da ta shiga tana faman sauke ajiyar zuciya, ɗagowa ta ɗanyi ta kalli hafsat samunta tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "Tun ɗazu na lura da kallon da kike yi mun Jahad, na menene?
ɗan sunnar dakai jahad tayi tace "Babu komai kawai ina mamakin yarda kika canza mana ne ba kamar da ba, kin nuna tausayi agare mu, ba muyi tunanin haka ba,
Hafsat tace "Nima kaina nayi mamakin yarda na canza wurin nuna muku tausayi, bayan ba hali na bane gaskiya, tun ina yarinya bani da tausayi ko kaɗan kuma bana son mutun mai tausayi, ban sani ba ko kunayin addu'a ne shiyasa Allah ya kawo muku sauƙi ta 6angare na.....' ta ƙare maganar tana kallonsu,
Jinjina kai Jahad tayi jin abunda hafsat tace, Lallai ne Allah ne ya amshi addu'arsu ya kawo musu sauƙi ta wurin hafsat,
Ajiyar zuciya Jahad tasa ki tare da juyawa ta kalli hosana wadda ke zaune wuri da ido, taci ta ƙoshi tayi hani'an,
Hafsat tace "Ga maganin da dr yace abaki, tun da kin kammala cin abincin bari na baki ki sha, sannan zuwa anjima insha Allah zamu koma gida,"
jahad tace "Allah ya kaimu lafiya,"
"Ameen," ta amsa mata sannan tasanya hannu ta ɗauki ledar maganin,
ta shi ga fiddo su tana duba su, kafin tasanya hannu cikin basket ɗin da tazo dashi ta ɗauko robar ruwa, ta buɗe ta bayan ta ciro maganin ta miƙa ma hosana tare da ruwan tana kar6a tana sha, haƙiƙi su Hosana da jahad ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, saboda sun ga tausayinsu ƙarara a fuskar Hafsat kuma da alamun zasu samu sauƙi ta 6angarenta,
*Shin Ya maganar matar da ta ba Hafsat miliyan shidda don ta zubar mata dasu Jahad? Kuna ganin zata fasa wannan aikin ko kuwa*? 😳
*AUNTY BABBA* 😈
Sam ta gaza samun natsuwa hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda hafsat ta fara damuwa da twins ɗin da OMAR ya kawo, tabbas dole ta ɗauki mataki akan hakan, kuma haryanzu tana akan bakanta na sai tasa an zubar mata dasu Hosana da Jahad,
*Tabbas dole na ɗauki mataki akan hakan*
tayi maganar tare da dakatawa daga zirga zirgar da takeyi acikin ɗakin nata, fitowarta kenan daga wanka, ta zumbula doguwar rigar Buba ta Material, hannu takai ta ɗauki wayarta dake ajiye saman stool dake agaban mirror,
cikin hanzari ta shiga contact ta dannawa wata number kira wadda tayi saving ɗinta da *BABA ALAMU*
Nan da nan kiran yashiga wayar ta soma ringing zuwa wani lokaci mai numbar data kira ya amsa wayar,
Cikin sauri tace "Assalamu Alaikum,"
daga can 6angare wata murya kakkausa ta gawurtattun ƴan iska ta amsa mata da cewa,"Hajiya Laila manyan gari, ashe kuna neman mutane? Ae nayi tunanin daga in da amfanin mutun ya ƙare a wurinki yazama shara......'
dakatar dashi Aunty Babba tayi da cewa "Baba Alamu ! mu aje wannan gefe, wlh ina cikin tsananin damuwa ne, tunawa dakai yasanya na kira ka domin nasan kai kaɗai ne zaka iya yi mun wannan aikin.....' ta ɗan dakata tana jiran amsar da zai bata ,
Baba Alamu yace "Ae dama ke ba'ki ta6a neman mutun sai in buƙatarki ta taso, tun da ansan muna da amfani ae a rinƙa ɗan kiran mu ana bamu hasafi don tafiya tayi kyau ko?, yanzu dai faɗa mun me kike so in aiwatar kawai ! Wa kike so akashe miki har lahira? Ko wa kike so In Naƙasa Miki kasusuwansa ajefar bayan Duniya?😳
Dariya aunty babba tayi cikin jin daɗi tace "Yawwa Mutumina, dama nasan kaine kawai zaka iya share mun hawaye na, abunda ke faruwa wani ƙanin Mijina ne wlh ya tsinto wasu ƴan mata tagwaye ya kawomin a gida na, na tsani yaran nan ko ganin su bana son yi, saboda zasu tarwatsamun target ɗina abunda nakeso kawai so nake kazo ka ɗauke su Ka fitar mun dasu daga gidan nan ka kai su can bayan gari ka jefar mun dasu Can cikin ƙurmin daji wanda zasu rikice su gaza gane hanyar da zasu fita daga cikin shi,"😳
tamkar tana agabansa haka take masa bayani tana faman cizon la66a, 😠
fashe wa da dariya baba Alamu yayi daga bisani ya tsagaita yace "Ƙaramin aiki kenan, ni nama yi tunanin wani za'a kashe maki ne yanzun nan mu kai shege lahira, amma tun da wannan ne kada ki samu damuwa, yanzun dai bana nan kinsan naje lagos ƙarƙashin gada amma maƙo mai zuwa bi iznil lahi, aikin ki zai kammalu, ƴan Canji kawai zaki tanada "
Aunty Babba tace "in dai wannan ne an gama, zanyi maka biya na musamman babban kaso mai tsoka,
Baba Alamu yace "Shikenan sai kin jini, da zarar na dira kaduna zan zo da rugwagwar mota ta na kwashe Maki Sharar azubar abayan gari,'😂
Jinjina kai aunty babba tayi har wani sauke ajiyar zuciya take yi jin burinta zai cika na kawar da su Jahad,
Sun jima suna waya da baba Alamu kafin daga bisa sukayi sallama, ta ajiye wayar saman mirror tana cewa "Yanzu abunda ya rage mun shine, na dakatar da Omar don nasan zai iya zuwa yace zai tafi dasu na lura da hakan I ave to do something ❗‼ .........!👷wani irin shu'umin murmushi tasa ki, saboda plan ɗin da ta tsara,
*********
Sai wuraren bayan Sallar La'asar sannan dr yayi discharge ɗinsu daga asibitin kamar yadda hafsat ta buƙata don bata son zaman su a asibitin gudun kada Omar yayi musu Dirar Mikiya, duk da dr yaso ya ƙara ma hosana Jini amma ta hana hakan sai dai tayi alƙawarin cewa zata mai do ta asibitin Next time,
A hankali take driving ɗinsu acikin motar, hosana na'a a back seat kwance sai faman sharar bacci take yi, yayin da jahad ke agefen hafsat dake driving, adai-dai wani Store ta tsaya da motar, sannan ta kalli jahad tace "Ki kula yanzu zan dawo,"
Jahad ta amsa da cewa "Toh Aunty"
Shiga cikin wurin tayi bayan wasu mintuna tafito hannunta ruƙe da leda, ta buɗe motar ta shiga miƙa ma jahad ledar tayi tace "Ruƙe wannan a wurin ki,"
Amsa jahad tayi ta ƙanƙame ledar a hannunta, sannan hafsat taja motar suka tafi gida kai tsaye,
Bayan tayi parking suka fito daga motar daker jahad tasamu hosana tafarka ta ruƙe hannunta suka nufi ciki hafsat na biye dasu, sai faman jin fargabar haɗuwa da Aunty babba suke yi,
Aikuwa suna shiga suka same ta zaune a babban falon saman sofa tana faman danna wayarta,
tana ganinsu ta miƙe tsaye tare da cewa "Sannun ku da dawowa, Allah sarki hosana da jahad kuyi haƙuri ban samu damar zuwa asibiti ba na dubo ku, Ya jikin naku"? ta faɗi cikin nuna tausayin su,
ai ba su jahad da hosana ba hatta hafsat tayi mamakin jin abunda Momyn nata tace lokaci guda ta canza tamkar ba ita ba, tsayawa sukayi suna kallonta baki asake,
Ganin hakan yasa aunty babba ƙarasawa ta ruƙo hannun kowannan su , sannan cikin sanyin murya ta wanda yayi nadama tace "Haƙiƙa nasan na cutar daku sosai, Allah ma ba zai yafe mun ba, tabbas jiki na yayi sanyi, nayi danasanin abun da na aikata muku dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun........'
Hawaye ne suka soma saukowa daga idon aunty babba fuskarta duk a yamutse tana kallonsu,
cikin mamaki hafsat tace "Shin mafarki nake ko gaske!? Mom are u serious about what are u sanying? Ko dai kin sha wani abu ne bayan na fita? kece dakan ki kike danasani hada neman gafara a wurinsa?
ɗago ido aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace "Shin ni ba mutun bace kamar kowa daba zanyi laifi na nemi gafara ba"? na zauna nayi wani tunani menene riba ta idan na cuci waɗannan bayin Allan? Allah fa dakansa ya haramta ma kansa zalunci kuma ya haramta shi atsakanin mu, kuma yace kada muyi zalunci, amma ni na kansance mai son zuciya..........'
Sam ta kasa ƙarasa maganar saboda shessheƙar kukan da tafara, juyawa hafsat tayi ta kalli jahad yayin da ita kuma jahad idonta na akan Hosana wadda ke kallonta, gaba ɗayansu mamaki ne ke ɗawainiya dasu, shin taya zasu gasgata tuban da Mommyn hafsat tayi? Anya ba wata ƙullalliya bace?
"Naji kunyi shiru baza ku yafe mun bane? In har baku yafe mun ba bana ji zan iya bacci adaren nan,"
Cikin sauri Jahad da hosana suka haɗa baki wurin cewa "Aunty mun yafe miki, Allah ya yafe mana gaba ɗaya,"
Murmushi Aunty babba ta saki tare da sa hannu ta haɗa su duka ta rungumesu ajikinta, tana faman ci gaba da basu haƙuri akan kuskuren da tayi masu na jibgarsu da tayi,
Jikinsu duk yayi mugun sanyi, gaba ɗaya kwalwarsu ta rikice sun rasa gane dawa zasu YARDA? SHIN HAFSAT ko MOMMYNSU? Taya hakan zaiyiyu ace lokaci guda sun canza musu izuwa mutanen kirki masu tausayin su?
Bayan aunty babba ta janye su daga jikinta ta mayar da idonta kan na hafsat tace "daughter daga yau inaso ki ɗauke su tamkar ƙannen ki, ni kuma insha Allah zan ɗauke su tamkar nice na haife su, zan basu duk wata kula daya dace uwa tabawa ya'yanta, "
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Insha Allah mommy as from now hosana da jahad sun zama ƴan gida, zasuyi rayuwar ƴanci acikin gidan nan, babu wanda zai sake cutar dasu acikin mu,"
Jinjina kai aunty babba tayi sannan tace "ina so daga yanzu su koma ɗakin Ladi mai aikin mu da kwana,"
Hafsat tace "a'a Mommy, mattress ce kawai acikin ɗakin, gaskiya ni nafison su dawo bedroom ɗina da kwana yadda zanfi basu kulawa,"
Aunty babba tace "hakan ma yayi, yanzu yakamata ku shiga ciki ku huta, sannan hafsat ki taimaka ma hosana tayi wanka da ruwa mai ɗumi ko taji daɗin jikinta,
Hafsat tace "insha Allah mommy," sannan ta mayar da idonta kansu hosana tace "mu shiga ciki," hannun su cikin na juna suka bi bayan hafsat har izuwa cikin bedroom ɗinta,
Da taimakon hafsat hosana tayi wanka ta canza kayan jikinta izuwa doguwar riga mara nauyi, bayan ta kammala hayewa kawai tayi saman gadon hafsat, tana jiran zuwan jahad wadda ta shiga toilet yin wanka itama, Ajiyar zuciya kawai hosana ke saki amma tana jin fargabar canjin da su ka gani wurin hafsat da Mommynta, sam bata amince dasu ba, kuma taci Alwashin muddin YA OMAR yazo ƙafarta ƙafarshi sai ta bishi, 😠
**********SEHRISH**************
A gajiye ta shiga cikin bedroom ɗinta bayan sun kammala gyare-gyaren gidan, sai lokacin tasamu damar yin wanka tare da alwala tafito ɗaure da towel, agaban dressing mirror ta zauna saman kujera tana Shafa mai ajikinta, bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare, sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗin kayanta, ta ɗauko dogon skirt brown color ta zura sannan ta sanya t-shirt fara, daga nan ta zura hijab tare da shimfiɗa carpet tayi sallah anatse, tun kafin ta kammala azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo, wuri ta samu gefen gadonta ta xauna,
bayan sehrish ta kammala sallar ta naɗe dardumar ta mayar da ita cikin wardrobe tare da hijabin, sannan ta juya da fara'a tana gaishe da azmee "Ina yini aunty azmee,"
Azmee tace "lafiya lou sehrish, zo ki zauna,"
Ƙarasawa tayi ta samu wuri kusa da ita ta zauna, azmeee tace "sehrish wai ina wayarki take ne? Na lura tun ranar dana baki ita, ban sake ganinta a hannunki ba, kodai baki so ne?
zuru sehrish tayi don ita tuni ta manta da zancen wata waya, kuma ba kowa bane yaja mata hakan ba face haroon, shine silar damuwar da tashiga harta manta in da ta jefe wayar
"Ina sauraron ki ina wayar"? Azmee ta ƙara nanata mata, cikin en ina sehrish tace "Aunty azmee tun....ranar...da...kika...ban...ita..na manta inda na ajiye...ta,'
ta ƙarasa maganar tana ɗan kallonta azmee tace "Sehrish kenan kin cika shiririta yanzu wayar mai tsada ita kika 6atar? To ina so ki nemo ta yau ɗin nan duk inda take, in ma saman ceilling kika turata ki hau saman ki fiddo ta, Ki kawo min ɗaki na ina jiranki,!" tana faɗin hakan ta tashi ta fuce........
tafa hannu sehrish ta shiga yi tana tunanin ta ina zata fara neman wayar, ita kanta abuƙace take da wayar ko don ta rinƙa ɗebe kewar zama ita kaɗai aɗaki,
Tashi tayi cikin ƙanƙanin lokaci ta hargitsa ɗakin wurin neman wayarta, duk ta zabure har ƙarƙashin gado ta leƙa, ta bincika cikin laundry basket ɗinta, gaba ɗaya ta zazzago kayan wankinta dake cikinsa babu komai, agajiye ta mayar da kayan, zarya tashiga yi tana tunanin ina ta wurgar da ita, ci gaba da neman wayar tayi, a ƙarshe tayi deciding zuwa ɗakin junaid ta roƙesa ya kira layin wayar ko tayi ringing,
cikin hanzari ta ɗauki mayafinta dake ajiye saman bed ɗinta, ta yarfa shi a head ɗinsa, sannan ta fita cikin sauri babu kowa a babban falon direct upstairs ta wuce da ƙarfi take tattaka stairs ɗin ko kallon gabanta batayi burinta kawai ta isa bedroom ɗin junaid,.
Kamar daga sama taji ta bugi wani abu da ƙarfi nan take wani irin jiri ya kwashe ta, agigice tasaki wata irin ƙara ganin yarda ta tafi gaba ɗaya zata faɗi amma ina tuni yayi mata wani irin kwakkwaran ruƙo da hannu guda ya tallabo waist ɗinta,
Zazzare ido sehrish tayi cikin Jin tsananin tsoro yayin da take faman sauke ajiyar zuciya,
gabanta ne ya soma faɗuwa saboda tuna hannun wa take a ruƙe, sam tagaza ɗago ido ta kalle sa, ae tun daga ƙamshin turaren nan nasa ta shaida kowane ne,
ɗago da ita yayi ta tsaya da ƙafafunta sannan ya wuce abunshi, juyawa sehrish tayi cikin sauri tana kallonsa ba ƙaramin wanka ya ɗauka, har sai da ya fice daga babban falon sannan ta kawar da idonta sannan ta ƙarasa haye wa upstair ɗin, har time ɗin jikinta wata irin kerma yake yi hannunta na dafe da ƙirjinta,
A hankali tayi knocing ƙopar ɗakin junaid tana buga ƙopar a slow saboda zuciyarta dake tariyo mata abunda yafaru yanzun nan,
kusan 3 times tana knocking sai daga bisa tajiyo muryar junaid yace "Come in,"
Ashe door ɗin a buɗe take, tana zura ƙafarta ciki karaf taci ido dashi gaban mirror daga shi sai short towel a waist ɗinsa sam baisan cewa sehrish bace, ta cikin mirror ya hangota, aikuwa cikin sauri yace "dakata !! Kada ki shigo! Ja baya," dariya sehrish tayi sannan taja da baya ta tsaya jikin ƙopar tana cewa "Junaid yaushe ka fara jin kunyata har haka"?
daga cikin ɗakin tajiyo muryarsa yana cewa "tun ranar dana gane cewa ke maca ce.....,'
Murmushi ta saki tana faman sauke ajiyar zuciya har time ɗin temperature ɗin jikinta yayi mugun zafi ba don komai ba sai don abunda yafaru da ita yanzun nan,
"Come in Sehrish," junaid ya faɗi,
Shiga ciki tayi a lokacin harya zura jallabiya ash colour ajikinsa yana gyara hannun rigar,
wuri tasamu agefen gadonsa ta zauna tana cewa "Junaid dama wannan wayr tawa nake nema narasa inda na jefar da ita, shine nazo ka taimaka ka kiramin layin dake cikinta, may be in tayi ringing in gano ta,
Murmushi junaid yasaki kafin yace "shikenan zan kira maki ita, amma under one condition? Ya faɗi ayayin da ya tsaya agabanta ya ruƙe qugu, sehrish tace "Menene sharaɗin?
Junaid yace "Tun ran nan nake ta fama dake ki nunamin gyaran gashin ki kin ƙiya, to yau indai kina So na kira layin wayarki sai kin cire mun nagani" ya faɗi yana murguɗa mata baki,
Yamutsa fuska tayi tare da cewa "look junaid yanzu ba lokacin wannan bane, am not in mood Just ka kiramun wayar,' ta faɗi tana tsuke baki,
Bin shi tayi da kallo ganin ya ɗan ɗaure fuskar shi alamar baiji daɗi ba,
Cikin lallashi tace "junaid are u angry with me? Am sorry pls ni bazan so naga king of smile ya koma king of Angry ba,' tayi maganar da ɗan zolaya,
Ɗan sakin fuskarshi yayi sannan yace "its ok, go back to ur bedroom i wanna call u righ now,"
Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "yawwa mutumi na, Allah yabar mun kai," ta faɗi tare da miƙewa ta wuce bedroom ɗinta cikin sauri,
Junaid kuwa acikin ransa yace "Ameen sehrish Allah yabarmun ke till the end of my life,' sannan yasa hannu ya ɗauki wayarsa dake ajiye saman mirror, contact yashi ga tare da lalubar nombar sehrish da yayi mata Saving da*FUTURE DREAM* sa'an nan ya danna mata kira,
tunkan sehrish tashiga ɗakinta ta rinƙa jin ringing ɗin wayar da ƙarfin gaske, tura ƙopar ɗakin tayi ta shiga ciki tana bin inda sautin ke fitowa, ashe tana cikin bedside drawer ɗinta, duk wannan uwar wahalar da tasha, cikin hanzari ta janyo drawer chest ɗin gida na farko, sai ga wayar ajiye sabuwarta kusan 1 month kenan tana ajiye bata mutu ba, saboda ruƙon chargyn ta, ajiyar zuciya sehrish tasaki tana shasshafa screen ɗin wayar da hannunta,
. .........................tuna da azmee dake jiranta yasanya ta fice da wayar cikin sauri ta isa ƙopar ɗakin azmee knocking tayi daga ciki taji azmee tace "in kin son bada wayar kika zo ba ki koma," wato har ta gane ce sehrish ce ta kwankwasa mata,
Gyaran murya sehrish tayi tare da cewa "Tare da wayar nazo aunty azmee,"
Azmee tace "shigo ciki,"
Tura kopar sehrish tayi ta shiga, samun ta tayi kishingiɗe saman gadonta, ganin sehrish yasa ta tashi zaune tana cewa "yanzu naji magana,"
Murmushi sehrish tasaki tare da samun wuri gefen azmeen ta zauna sannan Ta miƙa mata wayar tace "Gata,"
Azmee ta kalli wayar tare da cewa "dama ba wani abu zanyi da ita ba, ke nake so ki runƙa amfani da ita akai-akai takasance tare dake, saboda daga yanzu duk wani mai buƙatar wani abu ke zai kira kai tsaye a waya yasanar miki," jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa da bayaninta,
Sannan azmee taci gaba da cewa "nikam inaso na tambaye ki, shin kin ta6a yin makaranta ne before?
ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta a wani irin yanayi kamar wani abu yaɗan sosa mata zuciya, shiru tayi na wani lokaci kafin tace "eh nayi primary bayan nan nafara secondry karatun duk ashiriri ce ƙarshe ma muna gab da zamu shiga ss3 nadaina zuwa gaba ɗaya......' ta ƙarasa maganar asanyaye
Azmee tace "yanzu kina da burin ci gaba da karatun ne ko kuwa a'a? Ta tambaya tana kallonta,
Sehrish tace "ina so mana sosai, ina so nayi Ilmi saboda wata rana nima nazama abun alfahari, kuma wannan burin mahaifiyarmu ne, tun lokacin da ta haife mu takance Sehrish zata zama Achitecture, Hosana kuma Doctor, Jahad kuma Nurse haƙiƙa inaso nacika mata wannan burin nata.......................' idonta ne suka cuko tab da kwalla sunnar da kanta tayi ƙasa tana kallon wayar dake hannunta,
Cikin mamaki azmee ke kallonta ita kanta sehrish batasan me take cewa ba, ci gaba da magana tayi kawai tana cewa "Allah sarki a lokacin ni nafi kwarewa wurin yin zane, hosana ce mai ƙoƙari acikin mu amma yanzu bata da cikakken hankali tun lokacin da ta duro daga saman window mai tsayin gaske ..........ban......ban.......
Kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da yazo mata nan take ta fashe da matsanancin kuka,
Gaba ɗaya hankalin azmee ya tashi sam tarasa gane ma sambatun da sehrish ke yi, cikin ruɗu tace "sehrish wai meke faruwa ne? Su wanene waɗannan kike magana akansu ne? ƴan uwanki ne?
ɗaga mata kai tayi alamar "Eh" jinjina kai azmee tayi tare da cewa "share hawayenki daina kuka ya isa haka, duk da bansan Labarin ki ba amma ina da tabbacin cewa wani mummunan abu yafaru acikinsa wanda ke yawan saki cikin damuwa, don haka zanso naji labarinki sehrish amma ba yanzu ba aduk lokacin da muka samu free time sosai zamu zauna ki bani shi tun daga farko har ƙarshensa,'
"Insha allah aunty azmee na yarda dake sosai baxan 6oye maki komai ba," ta faɗi ayayin da take share hawayen ta,
Bayan sun samu natsuwa su duka azmee taci gaba da cewa "Zaki fara zuwa school insha Allah....'
Cikin mamaki sehrish ta ɗago ta kalle ta tare da cewa "Makaranta? Ni kuma? Aunty azmee taya za'a ɗauke ni a school bayan ko takardun kammala primary ɗin bani dasu na rasa su,'
"Kada ki damu sehrish wannan ba wata damuwa bace, komai za'a iya yi maki shi insha Allah, kuɗi ne kawai ke magana, kuma ni zan tsaya maki harki samu don nasan muddin na tuntu6i koda kanal yusif ne da maganar zai iya sama maki hanya, bama shi ba junaid zai iya yi maki wannan hanyar cikin sauƙi ki fara daga ss1 daga baya kin zana Jsce in time ɗinta yayi,'
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish har tagaza rufe bakinta, aranta tana cewa nan bada jimawa ba nima zan fara zuwa makaranta kamar kowa ?Alhamdulillah 😇
Hannu azmee tasanya ta kar6i wayar hannun sehrish tana cewa "ina fata junaid ya nuna miki komai ko?
"Eh harma ya tura mun wasu apps ɗin da zanyi amfani dasu,"
Azmee tace "okey, idan kina so kiyi amfani da data ko wurin yin browsing da sauransu just Wi-fi kawai zaki kunna, '
Jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa, sun ɗan jima suna fira kafin daga bisani ta sallame ta, komawa bedroom ɗinta tayi cike da murna koba komai in tafara zuwa school zata haɗu da friends irinsu Hafsat Bature Domin ɗebe kewa 😇
Sehrish first day at school 😮 Can't wait to see 💃💃💃💃
Ga wanda ba suyi payment ba su hanzarta su biya before end of this week👍 Yanzu littafi Zai fara 🔥🔥🔥 (08103884440) ayimun magana direct
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 17-18
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️
*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• bayan Jahad ta kammala wankan ta canza kaya ixuwa doguwar riga, hawa tayi itama saman gadon kusa da hosana suna daf da juna tace "hosana me kike tunani game da hafsat da mommynsu? Anya ba wani abu suka shirya mana ba? Kada fa ace so suke yi su kashe mu ko su zubar damu shiyasa suka tsara mana hakan,' tayi maganar cikin nuna damuwa a fuskarta,
Hosanna tace "jahad ni nasan abunda mommynsu hafsat ta shirya mana, fuska biyu tayi mana wlh, so take ta nuna mana kulawa sosai don mu saba da ita yadda in yaya Omar yazo yace zai tafi damu muƙi binsa saboda sun nuna mana kulawa.........' dakatawa tayi da maganar jin alamun tunkarowar mutun ɗakin da suke ciki,
Hafsat ce ta shigo ciki fuskarta ɗauke da murmushi tace "sannunku My sisters ya jikin naku"? Ta tambaya ayayin da take samun wuri saman room sofa ɗin tazauna,
"Alhamdulillah da sauƙi" suka bata amsa atare, mayar da idonta tayi gefen kujerar da take zaune leda ce ajiye wadda taba Jahad ta ruƙe mata bayan ta fito daga store, hannu tasa ta ɗauki ledar tana cewa "Lahh Jahad wannan ae naku ne na siya maku, Chocolate ne da sweet ko bakwa so ne"? ta tambaya tana kallonsu,
Suka haɗa baki wurin cewa "muna so," sannan jahad ta sauko daga saman gadon tasanya hannu biyu takar6a tana fadin "mungode Aunty hafsat,"
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Naji daɗin sunan nan da kuka kira ni dashi, amma nafison ku kira ni da Sister Hafsat akan aunty hafsat zanfi jin daɗin hakan,"
Murmushi su kayi su dukan su, kafin daga bisani Jahad ta curo musu chocolate cookies ɗin data siya musu, guda biyu ta curo ta ɗauki ɗaya sannan ta miƙa ma hosana suka 6are suna sha,
Har lokacin idon hafsat na akansu kallonsu takeyi gwanin burgewa, dama tun ranar farko data fara cin karo dasu sun burgeta kawai baƙin hali ne irin nata yasa bata nuna ba,
Ɗagowa su kayi jin alamar shigowar mutun, AUNTY BABBA ce ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi tana kallonsu tace "Ya jikin naku My daughters?
haɗa baki su kayi wurin cewa "da Sauƙi Alhamdulillah,"
Jinjina kanta tayi kafin daga bisa ni ta kuma cewa "Yakamata ku fito mana kuzauna a palour ko kallo ne kuyi zai ɗebe muku kewa kuma zaku samu nishaɗi,"
Amsa mata sukayi da "Toh" sannan suka sauko daga saman gadon hannun jahad ruƙe da ledar choculate ɗinsu,
A falon suka samu wuri saman gujera mai mazaunin mutun biyu su ka zauna tare da mayar da hankalin su Wurin kallon shirin da akeyi a tashar Bollywood, tuni kallon ya ɗauke musu hankali saboda daɗin dramar da suke yi ta india, dama kuma ga chocolate ɗinsu suna sha sai abun yaƙara nutsar dasu gaba ɗaya,
AUNTY BABBA kuwa wuri tasamu ta zauna agefen gadon tana fuskantar hafsat tace "Sannu Madam,"
tashi hafsat tayi zaune tana cewa "Mommy dama ina son magana dake! Wannan canjin dana gani a tattare dake shin dagaske ne? Ko duk shiri ne? ta tambaya tana kallonta don jin amsar da zata bata,
ɗan ƙayataccen murmushi AUNTY BABA tasaki tare da cewa "Hafsat kenan ! Ke naso ki fara faɗamun gaskiyar lamarin nan shin dagaske ne yanzu kin fara jin tausayin yaran nan?
"Mommy da gaske ne, natausaya musu sosai saboda bugun rashin imanin da kika yi musu, kuma ayanzu bana son wani yaƙara ƴunƙurin cutar dasu daga ni har KE !
Ajiyar zuciya aunty babba tasaki tana mai jinjina kai tace "Shin ya maganar matar da kika amsar ma kuɗi kusan miliyan shidda? Mayar mata su zakiyi kenan.....?
Hafsat tace "wannan ni tashafa mommy, zan san yarda zanyi da ita, in ma bazaiyiyu ba just zan mayar mata da kuɗinta ne,"
ɗan ta6e baki AUNTY BABBA tayi daga bisani tace "Shikenan Daughter but lemme remind u something, kin manta da uban bashin da Ake bin ki kenan u ave to think about it, how can u pay all ur debt? Dole ki buƙaci kuɗi ....................tana kai ƙarshen maganarta, ta tashi ta fuce tana faman sakin shu'umin murmushi aranta tana cewa "Yarinya kenan! Naki wasa ne,"
**********💪💪💪***************
misalin ƙarfe 5 da rabi na marece a lokacin suna dab da kammala aikace-aikacen su na girki, sai ga OMAR ya shigo cikin gidan kai tsaye kitcen ya nufa in da suke, Hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba ganin OMAR don atsorace take dashi,
bai shiga kitchen ɗin ba tsayawa yayi daga waje ba tare da yace komai ba,
Sehrish ce tace "Aunty Azmee ga yaya Omar nan," azmee na jin haka cikin sauri ta fito izuwa inda yake tsaye da murmushi a fuskarta tace "Omar ashe kaine ina fata lafiya dai ko,"
Jinjina kansa ya ɗanyi ayayin da idonsa ke kallon sehrish wadda ke acikin kitchen taƙi ɗagowa su haɗa ido dashi, har time ɗin ya gaza gasgata abunda idonsa ke nuna masa,
ɗan gyaran Murya yayi tare da mayar da idonsa kan na Azmee yace "Sannuku da ƙoƙari, ina fata dai ban katse maku aikin ku ba"
Azmee tace "A'a wlh Ae ma mun kammala girkin gyaran kitchen ɗin ne kawai ya rage mana yanzu,"
OMAR Yace "Okey, dama aiki ne nake son kuyi mun ke da waccen Yarinyar ta cikin kitchen,'
Jin hakan yasa sehrish ɗan ɗagowa suka haɗa ido dashi cikin sauri ta sunnar da kai ƙasa,
Azmee tace "Wane kalar aiki kenan Omar?
"Zan baku makullin gidan Uncle ABUSUFYAN so nake Kuje can ku duddubamun gidan duk wani abu da ake buƙata kawai inaso ku rubuta mun shi,"
Murmushi azmee ta saki tare da yin ƙasa² da murya tana cewa "To fa, kodai Abusufyan ne zai dawo nigeria da zama ne?
Kamar daga sama taji muryar Omar yace "Bashi bane zai dawo, wasu marayu ne nake son zubawa aciki, so inaso agyara mun gidan da duk wani abu na more rayuwa da mace zata buƙata acikin Sa, sannan bayan kun kammala wannan aikin inaso ku shirya zuwa Yi masu siyayyar kayan sawa da sauran abubuwan buƙata na mata,'
Azmee tace "wannan ai aikin lada ne, insha Allah Omar zamu yi komai yadda kake so,"
"Hakan yayi mun, bari na ɗauko maki key ɗin gidan ku tabbatar kunje yau, zansa Junaid ya kai ku a motarsa," ya yi maganar yayin da yake wuce wa izuwa sashen Abbansu,
Hannu yasa ya ciro wayarsa daga cikin aljuhun wandonsa, contact ya shiga tare da dannawa Abban nasu kira, kamar jira yake omar ya kira sa awaya sai gashi ya ɗauka,
Ƙara wayar Omar yayi a kunnansa yana cewa "Abba gani nashigo bedroom ɗin naka, wurin ina key ɗin yake"?
"Ka duba cikin side drawer ɗita gida na tsakiya suna anan ciki makullan na zuba su,"
"Ok to ngde Sosai Abbana, take care of your self for me,"
yana jiyo sautin muryar Abban nasu Mai haɗe da Murmushi yana cewa "Nima haka ka kulamun da kan ka,"
"Insha Allah," Omar ya faɗi tare da rejecting kiran, ya mayar da wayar tasa cikin aljihunsa,
Kai tsaye inda Bedside drawer ɗin Abban nasu take ya ƙarasa tare da zuƙunnawa ya janyo gida na tsakiya acikinta, Sai ga makullan sun bayyana hannu yasanya ya ɗauka sannan ya fito daga ɗakin nasa,
Kitchen ya nufa azmee na ganinsa ta fito, ƙarasawa yayi tare da miƙa mata key ɗin yana cewa "Ga shi nan ku tabbatar kunyi aiki mai kyau, yanzun nan zan ma junaid magana yazo yakai ku can gidan,"
Azmee ta amsa masa da cewa "Toh insha Allah," sannan Omar ya fuce daga main palour izuwa filin buga ball ɗinsu tunkan ya isa yake faman kwalawa junaid kira wanda ke acikin filin kwallon sai faman buga ball suke yi su uku shi da wasu daga cikin security ɗin gidan,
Jin kiran Omar yasanya shi dakatawa da yin kwallon ya wurgar masu da ita sannan ya fice daga cikin ragar izuwa inda Omar yake,
tsayawa yayi agabansa tare da zuƙunnawa ya dafe guiwarsa sai faman haƙi yake yi daker ya iya cewa "Yaya Omar gani,"
Hannu omar yasa tare da bugun bayan junaid yace "Bana hana ka buga ball dayawa har haka ba? Tun fa ɗazu dana shigo nasame ka, cikin waɗancan gardawan sai faman wahalar mun dakai suke yi,"
Murmushi junaid yasaki tare da ɗagowa tsaye yana cewa "Yaya Omar zandaina ne, amma yanzu tana sanya ni nishaɗi sosai,"
Jinjina kai Omar yayi tare da dafa kafaɗarsa yace "ko don saboda lafiyarka junaid, yakamata kadaina yawan buga kwallon ɗin nan da kuma yawan yin guje-guje,'
Cikin girmamawa junaid yace "insha Allah yaya Omar zandaina,"
dafa kafaɗarsa omar yayi sannan yaci gaba da cewa "ka shiga ciki ka shirya zaku fita tare da Azmee da wannan Yarinyar inaso ka kaisu Gidan Uncle Abusufyan, zasu yi mun aiki ne kaima sai ka taya su,"
Cike da zumuɗi junaid yace "To shikenan yaya Omar, bari naje yanzun nan nashirya nakaisu,"
"Yawwa My boy," Omar ya faɗi tare da wuce wa gaba,
Shige wa junaid yayi da gudu cikin babban falon kamar ba wanda aka gama ja ma kunne akan yin gudu ba,
A lokacin azmee da sehrish sun kammala gyara kitchen ɗin, kowan nan su ya wuce ɗakinsa domin kimtsawa,
Da gudu yake tattaka Matattakalar benen adai-dai lokacin SGR ya fito shima yana ƙoƙarin saukowa down, jikinsa na sanye da jallabiya fara mai gajeran hannu abun ba'a magana,
tsayawa yayi yana jiran isowar junaid Domin yayi masa kyakkyawan ruƙo, sai da junaid yakai ƙarshe sannan ya lura dashi, ɗan zaro ido yayi tare da dakatawa da tafiyar gabansa na faɗuwa, sarai yasan cewa sun hana shi gudu shi kuma abun ajinin sa yake yadda kasan wanda aka sanya Ma battery haka junaid yake,
Tun kafin Babban yayan nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa "Bazan ƙara ba wlh, na daina" ya faɗi yana ɗan raku6e fuska yana kallonsa wuri da ido,
Sgr yace "Junaid na ta6a sa hannu na ajikinka, da sunan zan buge ka ga?
Girgiza kai yayi tare da cewa "a'a babban yaya, baka ta6a ba kuma bana fata, ai nasan ma bazaka ta6a buguna ba," ya faɗi da murmushin nan nasa,
Sgr yace "meyasa kake tunanin cewa bazan iya bugunka ba,"?
ɗan cizon red lips ɗinsa tare da cewa "Because.......You love me so much......' ya ƙarasa maganar tare da wuce wa cikin sauri yana dariya, bin shi da kallo kawai Sgr yayi, tunawa yayi da wata magana da aka ta6a faɗa masa cewa
*Kowa ne ɗan adam yana da lagwansa, kaima haka ga lagwagonka nan, wato ƙanin ka JUNAID, Yakamata ka kula dashi sosai, Saboda duk wanda zai kawo maka hari acikin maƙiyanka, to ina da tabbacin cewa zasu 6ullo maka ne ta wurin JUNAID, So you've to be very careful,"!
Jikinsa ne ya ɗanyi Sanyi amma ta wani 6angaren yana jin cewa bazai ta6a barin hakan ta faru ba A matsayinsa na SURGEON GENERAL RAFAYET,
A babban falon ya zauna saman doguwar kujera mai mazaunin mutun uku, ya kishingiɗa tare da ciro wayarsa yana daddanawa,
Shigowa Omar yayi cikin babban falon ganin SGR yasa shi sakin fara'a yana cewa "Ashe kana ciki yaushe ka shigo,"
tashi zaune Rafayet yayi jin muryar omar,
Kallonsa yayi tare da cewa "ban jima da dawowa ba, what of u ,"? ya tambaya yana kallonsa,
Zama Omar yayi saman Sofa ɗin da sgr yake suna ɗan fuskantar juna yace"Nima yanzun nan nashigo, bansan kana aciki ba ae dana shigo, dama inaso nace kunyi waya da EVA? tana so tayi magana dakai sosai tayi mun magana ɗazu, its better ka kira ta if not kasan halinta ƙaramin aikinta ne kaganta a Nigeria,"
ɗan ta6e baki sgr yayi tare da cewa "naga missed Calls ɗinta, na manta nabi kiran nata that's why,"
Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa "Har yanzu baka yanke shawara bane game da ita? Pls bro kodan saboda Uncle Donald yakamata ka sassauta mana....'
Wani irin kallo Sgr yake binsa dashi kafin yace "Uncle ya riga da yasan tsarina, ko shi kansa ya tsawatar mata akaina amma taƙi ji so ni banson ya zanyi na fahimtar da ita ba,"
Omar yace "matsalar kenan, ni abunda yafi damuna taurin kanta, in banda ƙarfin hali irin nata taya zata ce dole sai kai zata aura? a ƙalla EVA ta baka kusan 10years aduniya, har yaushe ne zata daina wannan mafarkin? ya tambaya yana kallonsa,
Sgr yace "Omar da ace zan iya canza ra'ayi na akan mace ,to ina mai tabbatar maka da cewa ita ce mace tafarko da ta cancanta ta mallake ni, saboda kusancin dake a tsakani na da ita..................."
Karaf!! Maganar Sgr ta sauka a kunnan Sehrish wadda fitowarta kenan ta nufo cikin babban falon, har ta kammala shiryawa tsaf, ta zumbula jalbaba ajikinta har ƙasa maroon colour, hannunta na ruƙe da hand bag, ƙafarta kuma na sanye da flat shoes launin hijab ɗinta, fuskarta sam babu makeup ƴar hoda ce kawai ta shafa sai ta murza man baki a la66anta, amma ba ƙaramin kyau tayi ba, tsayawa tayi jiki amace tana sauraron firar tasu sam tagaza motsi, har sai da Marshal Omar ya ɗago da idonsa ya kalle ta, gabansa ne yaji yayi mugun bugu sam yagaza ganewa wannan ruɗanin dake a fuskar yarinyar nan, Sehrish bata lura da kallon da Omar keyi mata ba, juyawa Sgr yayi don yaga me Omar yake kallo ne karaf idonsa suka sauka ana sehrish wadda itama idon nata na akanshi, from up to down ya kelle ta kafin yace "Ke zonan," gabanta ne taji ya faɗi rass tayi firgit tana kallonsu, hankali atashe ta tunkare su gabanta na ɗarr!ɗaarr ta ƙarasa inda suke dab da Babban yayan nasu daya kira ta, Hannu yasa tare da ruƙo jalbabar dake ajikinta, saboda tsananin tsoro sai da sehrish ta kusa sakin fitsari tuni jikinta yasoma kerma kaf!kaf !!kaff!
cikin sanyayyiyar muryar nan tasa ta natsastsu yace "Menene wannan haka ajikin ki,"? Ya tambaya in serious matter batare da ya aza idonsa akanta ba,
Murya na rawa sehrish tace"hi..hij..hijabi ceeee...'
"Masallaci zaki je ne"? Ya tambaya yana jiran amsa,
"A'a fita zamu tare da aunty azmee,"
Cire hannunsa yayi tare da nuna mata hanya yace"maza ki koma, ki cire wannan abun, bana son sake ganin shi," cike da mamaki Omar ke kallon sgr har dai yagaza yin shiru yace "Rafayet nan fa ba Us bane Nigeria ce, kuma wannan shine best outfits da yace mace musulma tayi, Domin rufe surar jikinta daga jan hankalin mutane akanta saboda tsaro,'
girgiza kai sgr yayi tare da cewa "ban yarda da wannan shigar ba, shin Omar taya mutun zai iya motsi acikin wannan abun"? Ya tambaya yana nuna hijabin jikin sehrish,😂
Fashewa da dariya Omar yayi kamar kamar me, ganin yarda Sgr ya haƙiƙance akan hijabin dake ajikin yarinyar, shi a ganinsa takurace kuma mutun bazai iya motsi acikinta ba, daƙer ya dakatar da dariyar tasa ya kalli sehrish tare da cewa "Ki faɗa masa yarda kike motsi acikinta may be ya fahimta,"
ɗan murmushi sehrish ta saki ita kanta abun ya gama ɗaure mata kai, ɗagowa da hannayenta tayi tare da cewa "Ga hannun hijabin nan, tun da na fiddo da hannun acikinsa lafiya lau nake motsi acikinta," ta ƙarasa bayanin tana kallonsa
Jingina bayansa yayi ajikin sofa ɗin tare da cewa "Its Okey, u can go,' har ta juya zata tafi Omar yace "Ya Sunan ki ne?
Juyo wa tayi ta kallesa da murmushi a fuskarta tace"SEHRISH"
Omar yace "masha Allah suna mai daɗi, amma menene ma'anarsa? ya tambaya yana kallonta,
*kyawawan halayyu na mutun,"
ta bashi amsa,
*ina fata zaki nuna mana waɗannan kyawawan ɗabi'un acikin gidan nan, har ma ki zama alkhairi agare mu," omar ya faɗi da ɗan murmushi a fuskarsa, duk Sgr na sauraronsu duk da ya ci gaba da dannar wayarsa,
Sehrish ta amsa masa da cewa "Insha Allah," sannan ta wuce
Sai lokacin Sgr yace "Ashe kana surutu har haka Omar?
Kallonsa Omar yayi tare da cewa"Yarinyar ce tana tattare da wani abun al'ajabi a fuskarta shiya sanya Na sake mata,"
"Ba kowace baƙuwar fuska yakamata ace kana sakemawa ba irin haka ba, Mata Basu da tabbas they're trouble makers," acewar Babban yaya,
ƴar dariya Omar yayi batare da cewa komai ba,
Sehrish kuwa kitchen ta wuce ta zubo musu coffee tare da snacks a plate Cikin tray sannan tadawo inda suke tare da ajiye masu saman Table, Omar yace "thank u miss Sehrish,"
Murmushi tayi masa sannan ta juya ta nufi ɗakin azmee tunkan ta ƙarasa ɗakin nata sai ga Azmee ta fito itama ta kammala shiryawa cikin atampha ja, ta aza babban mayafi milk colour launin takalminta ƙafarta, atare suka fuce suna jiran isowar junaid,
Ba da jimawa ba sai ga junaid ya fito daga upstairs yana saukowa down sai faman zabga murmushi yake yi, jikinsa na sanye da haɗaɗɗiyar shadda gezner blue colour mai maiƙo sai faman ɗaukar ido yakeyi kai kace wani sabon ango ne, shaddar tasha aiki a wuyanta tsantsararre, hannunsa na ruƙe da wayarsa haɗe da key ɗin motarsa,
Lokacin daya ƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin, gaba ɗaya Marshal Omar da Sgr suka bishi da kallo,
Zagayawa yayi inda babban yayan nasu yake yana isa ya manna mashi kiss agefen fuskarsa sannan yace "Zan fita, saina dawo," ko amsa bai jira ba cikin sauri ya lalla6a ya fuce yana cewa "yaya Omar kayi masa bayani, mu mun wuce ,"
Girgixa kai kawai SGR yayi sam ya kasa magana, wato junaid yasan cewa zai iya dakatar dashi daga fita shine yayi dabarar tserewa,
Murmushi Omar yasaki tare da cewa "Junaid kenan ! komai nasa na burgewa, ya cika ƙiriniya ga shegen wayon tsiya, saboda kada ka hana shi fita shiyasa ya gudu bai jira amsarka ba," yayi maganar yana kur6ar coffee ɗin da sehrish ta kawo masu a cup,
"Ina zasu je ne"? Sgr ya tambaya yana kallonsa, Omar yace "Gidan Uncle Abusufyan na aikesu, inaso zanyi amfani da gidan ne akwai wasu marayune da zan zuba acikinsa kwanan nan,"
Sgr yace "Omar kenan, meyasa baka sanarmun ba? ko ni ba'a buƙatar gudummuwata ne? ya faɗi yana kallonsa,
Murmushi Omar yasaki dama sun saba indai irin haka ne, muddin akace aikin lada yasamu, to har rububi suke yi wurin bada taimakonsu, kowa burinsa ace da dukiyarsa za'ayi amfani wurin bada tallafi sam basa gajiya da irin wannan (Kaji masuyi don Allah) Shiyasa dukiyar tasu kullum hau hawa takeyi kamar kamar me, a ƙalla su kansu basu son adadin gidajen marayun da suka buɗe ba a kasashe daban daban kuma suke ɗaukar ɗawainiyarsu da komai, Manyan asibitoci kuwa da suka buɗe ba iyaka, wanda suma duk kyauta ne ake duba marasa lafiya acikinsu, ga makarantu na marayu da marasa hali da suke dasu ba adadi, wannan ba komai bane ba, kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke yi na taimako, Ya Allah ka bamu arziƙi mai albarka wanda zamu amfana dashi kuma ƴan uwanmu musulmai suma su amfana dashi, ba irin arziƙin da mutun zai mallaƙe ba, ka ga ko cikin gidansa fama ake dashi basa ciyuwa balle na waje su samu😧
*****GIDAN ABUSUFYAN*******
Haɗaɗɗiyar daula, Aljannar duniya tun daga kan Tanƙameman gate ɗin gidan Golden colour & brown sehrish ta saki baki tana kallo Ikon Allah, Ba don daga gidan Abban sojoji ta fito ba da sai tace wannan gidan a dubai yake, tsayar da motar junaid yayi abakin gate ɗin sannan ya fito daga cikin Motar, ya nufi jikin gate ɗin, tunkan ya isa ya danna madannin da ke ajikin key ɗin gidan a hankali gate ɗin ya soma zugewa da kansa daker daker yake tafiya saboda gidan ya jima ba'ayi amfani dashi ba tunda Abusufyan yabar Nigeria a fusace gidan yake ahaka garƙame, ganin zai 6ata musu lokaci yasa junaid sanya hannunsa yana ƙoƙarin turasa da ƙarfinsa don yayi saurin f
Buɗewa, aikuwa nan take zufa tasoma wanko masa kamar wanda aka watsa ma ruwa a fuska dama jiki bana wahala ba, muryarsa kamar zaiyi kuka yace "Aunty Azmee wai bazaku fito ba mu tura, Wlh ban iyawa ni kaɗai,"
Jin hakan yasa su fitowa daga cikin motar suna faman tikar dariya, azmee tace"Haba junaid wannan fa ƙaramin aiki ne, sai kace ba Namiji ba haba karka ban kunya mana, Be a Man,'
Kallon azmee yayi yana faman sauke haƙi yace"In dai saina tura wannan jibgegen gate ɗin zan zama namiji, to Allah abarni a jinsin mace yafi mun,"
Fashewa da dariya sehrish tayi har tana dafe ciki jin abunda junaid yace, harara ya watsa mata yana hura hanci,
Azmee na isa jikin gate ɗin tace"Matsa ka gani junaid, ni bari in zama Namijin, ni kaɗai zan tura sa,"
Jin haka yasa junaid matsawa suka bata wuri don ta jaraba, gefen Sehrish ya tsaya suka zuba ido suna kallon azmee,
Hannu tasanya sannan ta soma tura gate ɗin nan take ya tafi da gudun gaske ya ƙarasa zuge kansa,
Zaro ido Junaid da sehrish su kayi cikin tsananin mamakin ƙarfi irin na AZMEE,
A ruɗe junaid yace"Aunty azmee taya hakan ta faru? Ni nakasa turasa amma ke kina aza hannu gate ɗin ya buɗe,"
Murmushi azmee ta saki tare da nuna masa damtsen hannunta tace "Tsohon ƙashi kenan! ba irin naku ba na ƴan shila,"
Fashewa su kayi da dariya su duka kafin daga bisani suka koma cikin Motar, junaid ya shigar da ita cikin gate ɗin kai tsaye yayi parking ɗinta a harabar gidan
*Shin Kuna tunanin Cewa Omar zai samu damar ɗauko su hosanna da Jahad daga gidan Aunty babba*?😟
Ku hanzarta yin payment 300 ne ga acct 3196407426 Bature Hafsat Muhammad first bank, sai aturomin shaidar biya ta numberta 08103884440, idan kuma recharge sai ayimun magana ta numberta,👍👏
[9/9, 4:03 PM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 19-20
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️
*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•
bayan sun fito daga motar kai tsaye suka nufi hanyar da zata sadaka da babban falon gidan, Sehrish sai faman bin ko'ina take da kallo aranta tana cewa"tab ! Mace ta samu wannan amatsayin gidan aurenta, ae kawai ta bi mijinta sau da ƙafa, tabi da addu'a don ni gaskiya na mallaki wannan hamshaƙin gidan amatsayin gidana, ko ƙofar gida bana leƙawa sai in ta kama,'
sai faman zancan zuci take yi har suka ƙaraso wurin wani bene mai kanannaɗa, hawa junaid yayi sannan azmee tabi shi, itama sehrish tabi bayansu, sai faman jinjina kai take yi tana cewa"lallaine Aljanna ta mai rabo ce,"
daker take tattaka matattakalar benen saboda gajiya don yana da ɗan tsayi, bayan sun kai ƙarshensa, wata haɗaɗɗiyar ƙopa ce wadda kai tsaye in ka bi ta zata sauke ka upstairs inda main falo ɗin gidan yake,
key junaid yasanya yabude ƙopar sannan suka shiga cikinsa,wurin ya haɗu an ƙawata shi ahaka ma wai ba furnitures acikinsa, to inaga ansanya mashi kujeru da sauran abubuwan ƙayatarwa,
Batare da 6ata lokaci ba, sehrish ta buɗe handbag ɗinta, memo ta ciro tare da biro, junaid da azmee suka dunga dudduba falon suna karanto mata abunda za'a buƙata acikinsa, ita kuma tana rubutawa acikin memo ɗin hannunta, bayan sun gama da falon kaf sun lissafa duk wani abu da za'a sanya mashi,
Sannan acikin babban falon akwai bedrooms guda biyar ƙofofinsu na acikin falon, ciki suka shiga suna dudduba ɗakunan masu girman gaske, nan ma azmee ta faɗa ma sehrish duk abunda za'a buƙata na furnitures ta rubuta, daga nan kuma suka sauko downstairs stairs shima bene ne zai biyo dakai ƙasan,
Agajiye sehrish ta kalli junaid tare da cewa "dan Allah wannan wane irin gidane haka junaid? Nafa rikice wlh, mun shigo ta Upstairs yanzu kuma ga mu a downstairs yanzu ta ina zamu bi mu fita? Ba dai sai mun koma upstairs ɗin ba don wlh ƙafafuna a sanƙare suke hawa stairs ko wahala,
Junaid da fuskarsa tayi jawur ya gama cika ya 6atse saboda uwar yunwar da yake ji, ga gajiya duk ta baibaye shi, daker ya iya cewa "wannan ne damuwarki, Ni ta cikina nake yi yaushe har muka kammala muka koma gida ni daga nan ma, ba abunda zan ƙara yi Allah, ku je ku ƙarasa sauran aikin in kun kammala kuyimun magana,"
Wuri yasamu a sitting room ɗin dake a downstairs saman wani benci ya zauna, da alama tun lokacin da akayi ginin gidan aka barsa, don akwai tarkacen kayan aikin da aka bari acikinsa,
Acikin sitting room ɗin akwai ƙofofin bedrooms guda biyu, sai kitchen mai girman gaske, sunsha aiki kaf sai da suka zagaye gidan bayan sun tabbatar sun bincika ko'ina sun dudduba abunda ya dace duka kaf sehrish ta rubuta a memo ɗinta, Ana cikin kiran Sallar magrib suka bar gidan kowa agajiye,
Suna ƙarasawa gida daga babban falon kowa ya wuce ɗakinsa, shaf shaf junaid ya tu6e kayan jikinsa ya faɗa toilet donyi wanka, haka itama sehrish tana shiga ɗakin nata bayan tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado tare da memo da biron duka, kai tsaye ta tu6e Jalbab ɗin dake ajikinta, ta cire rigar jikinta, cikin sauri ta faɗa toilet wanka tayo tare da Alwala, tana fito ta ɗaure da towel ta bude wardrobe ta ciro wata doguwar rigar mara nauyi ta zura, daker tasamu tayi sallah bayan ta kammala ta baje saman gadonta, bata ƙara sanin meke faruwa ba sam ta manta da batun jera abinci adining, gana babban yaya da zata kai mashi bacci kawai take kwasa,
Azmee ce kawai tayi ƙoƙarin fitowa bayan ta canza kayan jikinta, tunda ta leƙa tasamu sehrish na jan minsharin wahala, bata tashe ta ba kitchen kawai ta wuce ta shirya masu abincin dinner ɗinsu ta dunga kaiwa a dining tana jerawa harta kammala,
Daker junaid yasamu ya fito sai da yaci ka cikinshi sannan ya wuce masallaci yin sallah,
Sai bayan sallar isha'i sannan sehrish tafarka tana faman zazzare ido, agogon bangon ɗakinta ta duba kusan ƙarfe goma da rabi cuf, arazane ta miƙe tana faman dafe ƙirji tuna cewa bata kaima SGR dinner ɗinsa ba, cikin sauri ta ɗauko mayafi a wardrobe tayi lagensa a kanta, sannan tafito dakin azmee tafara wuce wa don taji ko takaimasa, kwankwasawa tayi sannan ta jira ta buɗe mata,
A lokacin azmee bacci takeyi jin bugun ƙofar sehrish yasanya ta, farkawa daga baccin nata, tasowa tayi ta buɗe mata ƙofa,
Ganin sehrish yasa ta cewa "ashe kin tashi daga baccin? Lafiya naganki ko akwai wani abune?
Sehrish tace "dama babban yaya na manta bacci yaɗauke ni ne, bankai masa ɗina ɗinsa ba, shine nazo na tambaya naji ko ankai masa,"
Azmee tace "Ae basu kai ga dawo cikin gidan ba Shi da Omar, pls kada ki koma bacci ko kuma ki sanya alerm na wayarki in sun dawo ki tabbatar kin kai masu abincinsu, sannan kada ki manta ki bama Omar list din da mukayi masa acikin memo dinki,'
Sehrish ta amsa mata da cewa "to shikena insha Allah zan bashi, mu kwana lafiya,"
Tayi ma azmee sallama sannan ta fito ta wuce nata ɗakin, gefen gado tasamu ta zauna sannan ta miƙa hannu ta ɗauko handbag ɗinta, wayarta ta ciro daga ciki sannan ta shiga dannata, Tunawa tayi da maganar Azmee da tace mata in zatayi amfani da data, wi-fi kawai zata kunna, Cikin sauri tasanya yatsanta ta janyo top of the screen din wayar ta, danna wi-fi ɗin ya kunnu, tsayawa tayi tana tunanin me zata fara yi da wayar yanzu, tana cikin tunanin nan taji ƙarar shigowar motocinsu cikin gidan kusan ƙarfe 11-30 na dare, mayar da wayar tayi saman bedside drawer ɗinta ta ajiye asamanta, miƙewa tayi tana jiran su kammala shigowa sai taje ta kai masu, sai da tabari 12 tayi dai-dai a lokacin tasan sun kimtsa kowannansu na a bedroom ɗinsa,
Sannan ta fito ta wuce kitchen ba ƙaramin daɗi taji ba ganin azmee ta kammala zuzzuba musu komai na dinner ɗinsu, a cikin tray guda biyu ta jera masu asaman table na kitchen ɗin,
Hannu kawai tasanya ta ɗauki tray ɗaya ta wuce dashi sashen marshal Omar sallama da ƙarfi tayi saboda yaji ta da kyau, kasancewar yana acikin bedroom ɗinsa bayan tajiyo Muryarsa yana amsa mata sallamarta ta, sai ta shiga cikin falon nasa ta ajiye masa tray ɗin asaman table, sannan ta fita cikin sauri tunawa da Memo ɗin da azmee tace ta bashi, bedroom ɗinta ta shiga ta dauko memon data bari asaman gadonta, sannan ta koma part ɗin nasa a lokacin har ya fito jikinsa sanye da jallabiya ash, wuri yasamu yazauna saman sofa fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi ganin Sehrish,
Ƙarasawa tayi inda yake tare da gaishe shi "Yaya Omar barka da dare, ya gajiyar aiki," ?
"Alhamdulillah miss Sehrish, ya maganar aikin dana saku? Ina fata komai ya tafi dai-dai, sannan ya gajiya nasan kun kwaso ta ko?
Murmushi tasaki tare da miƙa masa memo ɗin hannunta tace"Gashi nan, mun dudduba gidan duka kuma mun rubuta duk wani abu na furnitures da za'a buƙata acikinsa,"
Jinjina kai Omar yayi bayan yasanya hannu ya kar6a yana duddubawa yace "Very good, naji daɗi sosai gaskiya kunyi ƙoƙari, insha Allah zuwa gobe zanyi oder na duk wannan abubuwan da kuka lissafa ana buƙata acikin gidan, zuwa dai next week zan sake tuntu6arku,"
Sehrish tace "toh Allah ya kaimu lafiya,"
Har ta juya zata tafi ya kuma cewa "kina zuwa school ne? Ko baki fara ba?
Sehrish tace"a'a ban fara ba, amma aunty azmee tace zan fara cikin kwanan nan,"
Omar yace "Owk, inaso ne suma yaran da nakeson kawo wa cikin gidan can, su fara zuwa school amma zan jira naga wadda zaki fara zuwa, in yaso suma saina sanya su amakaranta ɗaya dake,"
Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "mata ne suma? ta tambaya tana kallonsa a lokacin harya fara cin abincinsa yace "Eh ƴan mata ne, kyawawan gaske inason yaran sosai tun dana ganki sai na ga fuskarki tana koma mun irin tasu, nasan saboda son da nake masu ne da kuma kewarsu da nake yi,......' ya ƙarasa maganar asanyaye,
Hakanan sehrish taji gabanta ya ɗan faɗi raaasss! amma batasan dalilin faɗuwar gaban nata ba, taso ta tambaye shi sunayen su amma tunawa da cewa ba ta kaima babban yaya abincinsa ba yasa ta saurin cewa "Allah sarki yaya Omar Allah yabaka ikon Kula dasu, yasa su zama alkhairi agare ka,'
Ya amsa mata da "Amin,"
Sannan cikin sauri ta fuce ta koma kitchen sai da tafara haɗa masa yankakkun fruits acikin madai-daicin plate ta azashi asaman tray ɗin sannan ta fuce hannunta dauke da tray ɗin acikin babban falon suka ci karo da haroon wanda fitowarsa kenan daga part dinsu, night dress ne ajikinsa riga dai-dai guiwa, kawar da kanta tayi tare da miƙar hanya tana jiyo shi yana cewa "a rinƙa haɗawa da sallar dare ko an samu adace asamu shiga,"
Murmushi sehrish tasaki batare da tace komai ba bayan ta isa part ɗinsa da sallama tashiga, baya acikin falon nasa ƙarasawa tayi ta ajiye masa asaman table dinsa, sannan ta tattaka izuwa bedroom ɗinsa tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin nasa, sallama tayi masa amma shiru babu amsa hakan na nufin yana cikin toilet ko kuma bacci ya ɗauke sa ne, aranta tace "Allah yasa baiyi bacci ba,"
ɗan sa ƙafarta tayi cikin ɗakin nasa ta shiga ciki sai uban ƙamshi ke daker hancinta kamar wadda tashiga gonar turare, samun shi tayi baje a saman gadonsa daga shi sai Short ajikinsa, ji tayi gabanta ya faɗi rass saboda yadda surar shi ke ɗaukar idonta,
sam tarasa me zatayi ta tashe shi don tasan dole akwai yunwa atattare dashi, kuma in ya tashi da safe yaga ba'akai masa abinci ba zai iya tuhumarta,
Shawara ta rage ma mai shiga Rijiya, tana cikin wannan tsayuwar abakin ƙopan ɗaki nasa ƙafarta har ta soma rawa saboda gajiya da tsayuwa,
Wani irin Juyi taga yayi daga saman gadon nasa gaba ɗaya ya tafi dukansa zai faɗo daga saman gadon, agigice sehrish ta watsa ciki da gudun gaske ta ƙarasa tare da kai hannu zata tarbesa sai gashi ya buɗe blue eyes ɗinsa kuma nan take yasanya hannusa ɗaya ya dafe ƙasan yarda bazai faɗi ba,
Tsayawa tayi tana faman sauke haki tare da sauke ajiyar zuciya, matsawa yayi tare da cire hannunsa ya gyara kwanciyarsa saman bedmattress ɗin sannan ya ɗan ware idonsa akan Sehrish dake atsaye, mamaki ne ya kamasa ganin ta tsaye dab da gadonsa me hakan ke nufi badai tazo bane don ta hanasa faɗuwa ba, ƙarfin halin ta yabashi mamaki shin ko ta ina zata iya ruƙoso daga faɗuwar da ya kusan yi? tabbas da ace sehrish takai hannunta da nufin ta dakatar dashi daga faɗowa daga saman gadon,ƙarshenta ya faɗa mata ajikinta ya danneta tagaza tashi don kuwa ko kusa sehrish bata da ƙarfin da zata iya taimakonsa daga faɗuwa,'
Sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya sam tarasa gane ma kanta, ita dai kawai burinta karya faɗo ƙasa yaji mummunan rauni shiyasa tayi yunƙurin tarbosa,
Kasalalliyar muryarsa ce ta ratsa ta da cewa"Sannu da ƙoƙari, amma kada kiyi attempting cewa zaki ruƙoni next time, if not jikinkin ki nei zai gaya maki,"
Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"kayi hakuri bazan ƙara ba,"
Shiru yayi tare da mayar da idonsa ya lumshe su, yana faman sauke ajiyar zuciya,
ɗagowa ta danyi tare da kallonsa tace "dama......na kawo maka dinner ɗinka ne, yana a falo na ajiye,"
Kusan minti 5 da yin maganarta ta sannan yace"Shigomin da fruits tare da Coffee, su kawai nake buƙata,"
Juyawa tayi cikin sauri ta koma cikin falon hannu tasa ta ɗauki plate ɗin dake dauke da fruits ɗin ta shigar masa dashi saman front table ɗim gadonsa ta ajiye masa, sannan ta koma ta dauko masa hadaɗɗen Coffee din dake acikin Cup ta dawo ɗakin nasa a lokacin har ya tashi zaune ya sauko da ƙafafunsa ƙasa,
a gefen plate ɗin ta ajiye masa sam yagaza buɗe idanunsa da alama ba ƙaramin bacci yake ji ba, sai faman cizon pink lips ɗinsa yake yi,
Ita dai burinta ya buɗe idonsa yafara shan fruits ɗin kafin ta tafi, don batason ya kwanta bai ci komai ba acikinsa 😒
Muryarsa taji yace"What are u waiting for? Ko zaki ban abaki ne? ya faɗi a time din yaɗan ware idanunsa masu ɗauke da bacci,
Cikin sauri sehrish tace "a'a sai Allah yakaimu, mu kwana lafiya,"
ta fadi tare da juyawa cikin sauri ta fuce daga ɗakin nasa sai da tafara tsayawa ta dauki food stuffs din dake acikin tray ɗin da ta ajiye masa sannan ta fuce dasu, a kitchen tasamu wurin ta zauna saman dining table ɗin ciki, buɗe kayan abincin tayi tazauna ta shaƙe plate tana ci, bayan ta kammala ta koma bedroom ɗinta sai da tafara yin sallar isha'e sannan tayi addu'ar yin bacci taja bargo ta lullube jikinta cikin wani irin yanayi na abunda yafaru tsakanin ta da SGR,
***************AUNTY BABBA**********
Da kanta ta girka masu hosana da jahad lafiyayyen abinci ta kuma jera masu shi adining, su duka suka halarta suna ci jahad na kusa da uosana polyayin da Hafsat ke kusa da mommynta dama mai 4 seats ne,
Duk sun kasa sakewa suci Abincin saboda fargabar da suke ji aransu, kwarama hussana tasamu tana shan kakkauran tea ɗin data haɗa mata tare da bread wanda yaji butter ajikinsa,
ɗagowa Aunty babba tayi ta kalli jahad tare da cewa "My daughter me yake faruwa ne? Naga tun ɗazu sai fama juya cokali kike yi acikin plate, yakamata ki fara cin abincin ko saiya huce"? ta tambaya cikin nuna kulawa,
murya na rawa jahad tace "babu komai Aunty zanci ne yanxu,"
Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa "kwara dai kici ta da zafin ta, saboda in ta huce baza tayi maki daɗin ci ba,"
Jahad ta amsa da toh sannan ta soma cin taiyar pasta din dake agabanta,
Mayar da idonta tayi kan na hussana tace "Yawwa my daughter, ae ke na lura bakya wasa da abinci da alama, kamar ni kike, shiyasa gani nan kamar buhun masara sai uban auki,"
Jin abunda tace yasamu fashe wa da dariya su duka banda hafsat dake satar kallon mommyn nata, abun ɗaure mata kai yake ganin yadda lokaci guda Mommynta ta sakewa yaran aranta tana cewa "gaskiya Mommy ba ƙaramar ƙuruwa bace wurin iya tsara tuggu, ta iya shu'umanci Allah kaɗai yasan me take shirya wa, koma dai menene nidai ina nan ina zuba ido in gani......👀
Murmushi Aunty babba tasaki tana kallonsu ganin yarda tasanya su nishaɗi aranta tace "haka nake so don kutmar ubanku a hankali zan canza muku tunani har na cimma burina," a fili kuma ta washe baki tana cewa "ku hanzarta ku kammala ci dare yayi sosai yakamata ace yanzu kun kamma yi nisa a bacci, sannan jahad kada ki manta kafin ku kwanta ki tabbatar kin ba Hussana maganinta,
Jahad ta amsa mata da "toh,"
Bayan sun kammala yin dinner ɗin nasu suka wuce bedroom din hafsat bayan hussana tasha maganinta sannan suka kwanta, bacci mai nauyi ya ɗauke su.............
Kallon Hafsat aunty babba tayi a lokacin itama idonta nakan Mommyn nata,
"tun ɗazu na lura da satar kallona da kike yi shiru kawai nayi," aunty babba ta fadi tana kallonta
Hafsat tace "hmmmm mommy kenan ni so nake ki faɗamun abunda kike shiryawa game da twins ɗin nan yakamata na sani,"
Dariya aunty babba tayi kafin tace "bai da amfani koda kin sani hafsat ! ki ma daina tambayata domin kuwa bazaki ta6ajin mutuwar sarki abakina,!"
Jinjina hafsat tayi tare da miƙewa daga kan dining ɗin tace "Shikenan Mommy kwarama ki ruƙe sirrinki, yarda in asiri ya tashi tonuwa ke kaɗai zakiji jiki ban dani, ni dae nayi nan," tana faɗin hakan ta wuce cikin bedroom ɗinta,
Saman Sofa ta kwanta tare da jan bargo ta lullu6e jikinta,
Shu'umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa "Yanzu wasan ya soma, " 😳 Nikuma nace Allah yaba mai rabo SA'A
***********AFTER 1 WEEK*********
BAYAN SATI ƊAYA
Acikin waɗannan kwanakin Jahad da hussana ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, sun samu ƴanci sosai acikin gidan jikinsu yayi kyau ba laifi sun ɗan murmure, gashi hafsat bata gajiya da ɗawainiya dasu har fita takeyi dasu yawan shaƙatawa, su fita shan ice cream ko kuma ziyarta gidan friends ɗinta, Aunty babba dae ta zuba ma sarautar Allah Ido burinta kawai Baba alamu ya diro Garin kaduna kafin Zuwan Omar, don tuni Baba Alamu yasanar da ita cewa suna kan hanya yau Litinin zasu sauka kaduna, 😳
A 6angaren Sehrish kuwa tana cikin farin ciki matuƙa saboda makaranta da zata fara zuwa, an riga da an kammala yi mata komai hatta Uniform ɗinta an kawo mata su kusan kala 3, ga sandals ɗinta masu kyan gaske, ga jibgegiyar school bag ɗinta da aka siya mata tare da textbooks na amfani da sauransu, abunda ya rage mata yanzu shine fara zuwa makarantar acikin satin nan, 😇
Tuni Marshal Omar yayi oder na haɗaɗdun furnitures made in dubai, kamfanin da yayi siyayyar kayan su da kansu, suka tsara mashi gidan wa'iyazubilla wurin kyau ba'a magana, komai sabo fal acikin gidan, kayan kitchen ne kayan ɗaki kayan falo komai fa wannan an zuba acikinsa ba abunda ya bari, bari in taƙaice muku zance hatta wannan kayan store na abinci yasa an jibge masu shi, duka freezer ɗin dake acikin gidan yasa an cike masu shi da Kayan marmari dana sha, komai fa Omar ya tanadar musu na jin daɗin Rayuwa, dama abunda ya hana shi zuwa kaduna kenan saboda yafi son saiya fara gyara masu gidan ya sanya musu komai na more rayuwa acikinsa sannan ya je yaɗauko su, kuɗi sosai Omar yaba Sehrish da azmee don suje yi musu siyayya, koda suka tambaye shi size dinsu na kayan da zasu siya masu gudun kar ayi kuskure, sai yace musu komi zasu siya irin na Sehrish saboda yana da tabbacin cewa tsayinsu da komai na jikinsu bazai wuce na SEHRISH ɗin ba, da sukayi masu siyayyar kaya masu yawan gaske kamar irin na sehrish amma nasu yafi yawa saboda su biyu ne, ƙarshe sai dai motar kamfanin da su kayi siyayar ta kawo musu kayan har gidan Abusufyan saboda motar junaid bazata iya kwashe su duka ba, saboda shine ke ɗawainiya dasu duk in da zasu fita, finally dae komai ya kammalu,👍
Ga masu karantawa a facebook indai kuna son Cigaba da kawo muku littafin Abban sojoji to ku hanzarta yin payment recharge card zaku tura ta wannan numbar 08103884440, 200 ne saura 3 pages free ya qare, Ga masu acct gashi nan 3196407426 first bank, Bature hafsat Muhammad, wanda sukayi payment ina sane dasu kuma kuɗinsu bazai tafi abanza ba🙌
[9/12, 8:44 AM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 21-22
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️
~Story & Written~
*BossBature*
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•
Ringing ɗin da wayarta ke faman yi ne ya tashe ta daga guntun baccin daya ɗauke ta, farkawa tayi tana faman yin Hamma, hannu ta miƙa tare da ɗaukar wayarta dake ajiye saman side drawer, duba screen ɗin wayar tayi don taga wanene ke kiranta, lokaci guda gabanta ya faɗi rass ba arziƙi ta miƙe zaune saman gadon tana duban sunan mai kiram nata, sam tagaza sa hannu ta ɗaga kiran saboda tasan mai zai biyo baya,
Kusan sau uku kiran nashigowa cikin wayar ta ta, amma taƙi ɗagawa daga bisa ni mai kiran nata yadaina kira,
Can sai ga ƙarar shigowar Message cikin sauri tasa hannu ta buɗe sakon ta soma karantawa kamar haka
_Babu buƙatar yin Sallama! Malama hafsat kin ban mamaki,Na kwashi uban kuɗi nabaki donki gudanar mun da aiki na, amma sai gashi Labari ya risƙeni cewa Anganki kina yawo dasu agari,Don haka ina so ki mayar mun da kuɗina yau ɗin nan in ba haka ba kotu ce zata raba ni dake_!!!!!!!!
Wata Irin nannauyar Ajiyar zuciya Hafsat tasaki afili take furta "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un, ni sam na manta da maganar wannan matar ashe tana sane da kuɗinta, gashi har na fasa su, yanzu dole ne na biya ta kuɗinta ko na samu salama, tabbas zata iya ja mun bala'e Ya zanyi ni! Gashi Yau Daddy zai dawo in yaji wannan abun tabbas Nashiga Ukuna!
Yunƙurawa tayi cikin sauri daga saman gadon jikinta na sanye da dogon wando baƙi sai ƴar Riga fara mai dogon hannu ajikin rigar an rubuta *I Love Paris*
Hannu tasa ta ɗauki ribbom ɗinta da ke ajiye saman mirror, ta ɗaure sumar kanta dashi sannan ta fito cikin hanzari, a babban falon tasamu Jahad da hussana zaune saman 3 seater suna kallo a plasman dake facing ɗinsu, jin alamar tafiyar hafsat yasa su ɗagowa tare da haɗa baki wurin cewa "Barka da fitowa Aunty hafsat," daker ta iya yi masu murmushin yaƙe tace "Yawwa My Twins," sannan cikin sauri ta wuce upstairs direct izuwa bedroom ɗin aunty babba,
tun kafin ta shiga ɗakin nata take faman kwala mata kira Mommy!mommy!!Mom!!"
Aunty babba da fitowarta kenan daga bathroom waist dinta daure da farin towel tana faman tsane gashin kanta da karamin towel tace"daughter lafiya kike mun irin wannan kiran na tashin hankali !!!," Shiga ciki hafsat tayi tana cewa "Mommy akwai matsala wlh! Dakatawa da tsane gashin kanta tayi sannan ta juyo ta kalli hafsat tare da cewa "Matsala kuma ta me kenan"?Cikin tashin hankali hafsat tace "Mommy wannan matar data ban kuɗi don na zubar mata dasu hussana da jahad, wlh itace ta kira ni yanzu, ban ɗaga kiran ba shine ta turo mun saƙon cewa na biya ta kuɗinta ko kuma ta haɗa ni da hukuma!!Ta ƙarasa maganar tana jira taji mai Aunty babba zata ce, abun mamaki sai taga ta fashe da dariya mai sautin gaske....... Cikin ruɗu hafsat tace "Mommy na faɗa maki tashin hankalin da nake ciki maimakon ki tayani jimami amma sai naga kina dariya saboda me!? tsagaitawa da dariyar Aunty babba tayi sannan tace"Hafsat kenan to ni menene ruwa na aciki? Ki mayar mata da kuɗinta mana shine kwanciyar hankalin ki," Muryarta tamkar xatayi kuka tace "Amma mommy sarai kinsan cewa nariga da na ta6a kuɗin nan kusan dubu ɗari takwas nayi amfani dasu aciki, Bani da kuma hanyar da zan biya su shiyasa nazo wurin ki saboda nasan akwai kuɗinsu Jahad wanda yaya Omar ya bayar ayi masu hidima, Inaso ki bani su don na biyata kuɗinta," Turusss ! aunty babba tayi kafin tayi Uwar shewa tace "Ahayyeeeee ! Anzo wurin dana fi so !! tabbas don kuɗi akwaisu kuwa suna kwance cikin bank account ɗina suna bacci, Ko sisi wlh baxan baki ba !! Har ni zaki watsa ma ƙasa a ido saboda waɗancan tsintattun yaran da ke da kan ki kika ce zasu iya zama nakiyar da zata tarwatsa mun plan ɗina, amma sai gashi akan idona kike nuna masu soyayya don ki 6atamun rai Ko?, don haka kije kiji da matsalar ki ! Ni babu ruwana acikin lamarin ki!!! Ido cike taf da kwalla hafsat ke kallonta cikin tsananin 6acin rai da ƙuna har ta nufi hanyar fita daga ɗakin ta tsaya tare da juyowa ta kalle ta tace "Mommy naji duk abunda kika ce ! Nayi mamakin yarda kike tada jijiyoyin wuya akan kuɗin da bada gumin ki kika same su ba! Kuɗin nan Mallakin Su hussana ne! saboda su Omar yabada ayi masu hidima, ke kuma kika kwamashe su Saboda son zuciyarki, don haka muddin kika ce zaki hanani kuɗin nan, zan kira yaya Omar ne na tona maki asiri game da duk irin cin Zalin da kika yima Twins ɗinsa.............' dakatawa tayi da maganar tana faman haƙi, Aunty babba kuwa wani irin shu'umin murmushi tasaki kafin tace "and then So What Hafsat! Go ahead ki faɗa masa wlh ko ajiki na! Ni nasan yarda zan fidda kaina wlh, kece a ruwa bani ba, Ni dan Allah fuce mun daga ɗaki............ tayi maganar tare da nuna ma hafsat hanya alamar ta fuce mata daga ɗakinta, murmushin takaici kawai hafsat tasaki kafin tasa kai ta fuce daga ɗakin, cikin tsananin jin 6acin rai Fuuuuu ta wuce izuwa downstairs ta wuce bedroom ɗinta, wuri ta samu gefen gadonta ta zauna cikin tashin hankali tana cikin wannan tunanin message ya sake shigowa cikin wayarta data bari saman gadon,Hannu tasa ta ɗauki wayar tare da buɗe saƙon ta karanta kamar haka
"ina tsammanin jin alert ɗin kuɗina, a yau ɗin nan in ba haka ba, nasamu labarin cewa yau general ishaq zai dawo wato Abbanki, kai tsaye zanzo har gidan ku, adai-adai lokacin dana tabbatar cewa ya iso gari zan shigo na tada maki 6alli"
Shiru hafsat tayi gabanta na wani irin faɗuwa tuni idonta sun canza launi, bata da wata mafita daya wuce ta koma ma mommyn nata, ta lalla6a ta tasamu tabata kuɗin ta mayar ma jarababbiyar matar nan, ko sun rabu lafiya, Zumbur ta miƙe tashi ga yin sintiri acikin ɗakin nata cikin tsananin damuwa, Sallamar Jahad ce ta katse mata dogon tunanin da ta shiga, "Jahad har kun gama kallon"? ta tambaya yayin da take ƙaƙaro murmushi a fuskarta, Jahad tace "A'a aunty an fara kiran sallar la'asar ne shine nashigo nayi sallah," Hafsat tace"Allah sarki, na lura bakya wasa da sallah Jahad, da zarar lokacinta yayi komai kike saina ga kin dakatar dashi don yin ibadah,"Murmushi jahad tasaki tare da shige wa ciki tana cewa "aunty babu abunda yakai sallah muhimmanci acikin dukkan aiyuka, babu wani jin daɗi na duniya da zai sanya na manta da yin ibadata abisa lokacinta..........' Wayar Hafsat da tayi ringing ya hana jahad ƙarasa jawabin nata, cikin sauri hafsat taƙarasa ta ɗauki wayar tare da dubawa, ganin numbar matarnan ce tsanya ta, yin wurgi da wayar, hankali tashe ta fuce daga ɗakin......... Shiru jahad tayi cikin mamamki ganin yarda hafsat tayi wurgi da wayarta ga fuskarta da alamun damuwa hakan na nufin wani abu na damunta, "Ya Allah ka yaye ma aunty hafsat damuwar dake damunta, ka kawo mata mafita Alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W)," ta faɗi acikin ranta sannan tashige cikin toilet donyin alwala,kai tsaye Hafsat ta koma ɗakin Aunty babba, lokacin da ta shiga har ta kammala shirya kanta cikin atampha Embellished mai tsadar gaske da kyau, tana zaune saman stool agaban mirror tana shafa jan baki abakin ta, Hafsat ta shigo, wuri tasamu gefen gadonta tazauna tana kallonta,Juyowa Aunty babba tayi ta kallota tare da sakin Murmushi tace "My daughter, Look at my face how do i look? Kinsan yau Abban ki zai dawo, Shiyasa na taƙarƙare ina masa kwalliya, yau inajin kaina tamkar sabuwar amarya," Fuska a ɗaure hafsat tace"Kinyi kyau,"Aunty babba tace "Ae ko baki faɗa ba, nasan cewa ni kyakkyawa ce, tun da gashi nan ke ma albarkacin kyau na kin samu har kinyi ɗan haske da dogon hanci ga gashi har kina taƙama," Hafsat tace "hmmm mommy kenan, amma dai kinsan cewa Hanci na ba irin naki bane ko? kuma da kike maganar kyau kar ki manta Abbana fa kyakkyawa ne hausa fulani," Tsoki aunty babba tasa ki tana cewa "Menene wani hausa fulani, Jinin Larabawa ake magana, kowa yasan mu da kyau babu jinsin da suka kai mu kyau aduniya kaf," ɗan guntun murmushi hafsat tasaki kafin tace"Ae shi kyau mommy ba'a fuska yake ba, ko a Surar jiki, a zuciya yake!! Duk kyan mutun muddin zuciyarsa baƙa ce, to ya tashi abanza mummuna ne shi,'Jin abunda hafsat tace ne yasa ta ajiye jan bakin dake hannunta tace "Tashi ki fuce mun daga ɗakina ! Bansan ma uban me yakawo ki ba," Shiru hafsat tayi batare da ta motsa daga inda take ba, illa kawai ta zuba mata ido,"baxaki fuce mun daga ɗaki na ba"? ta faɗi fuska aɗaure, Sassauta murya hafsat tayi tare da cewa "Kiyi haƙuri mommy in na 6ata maki rai, zuciyata ce bata mun daɗi........' Aunty babba ta katse ta da cewa "don zuciyarki bata maki daɗi shine kika zo na wanke maki ita? Ko me? girgiza kai hafsat tayi tare da cewa "kusan hakane mommy, ni yanzu zuwa nayi ki taimaka mun na mayar ma matar nan kuɗinta, ta addabe ni da kira, narasa ya zanyi," Murmushi aunty babba tasaki tare da juyowa sosai tana fuskantar hafsat tace,"Na Amince zan baki kuɗin ki mayar mata, amma bisa wasu sharuɗɗa! In kin bi muzauna lafiya daga ni har ke!? jinjina kai hafsat tayi tace "ina sauraronki, wasu sharuɗɗa ne? aunty babba tace "Inaso ki amince da maganar Fitar da yaran nan daga cikin rayuwarmu !!!!!! ɗagowa hafsat tayi aɗan razane tana kallonta..............Murmushi Aunty babba ta saki kafin taci gaba da cewa "Abun da nake son ki fahimta hafsat, ko da mun bar Omar ya ɗauki yaran nan ya tafi dasu can gidansu, wlh baza su ta6a samun kwanciyar hankali ba, domin kuwa Ke kinsan wacece Ammi ta tsani mutumin da bai da asali ya ra6i jinin ta, koda Omar yakai su can wlh ba zasu tsira ba!domin kuwa Ammi na zuwa zatasa a Kore su daga gidan! don haka yakamata kiyi tunani akan hakan kwarama cikin ruwan sanyi mu rabu dasu Lafiya,
Shiru Hafsat ta ɗanyi na wani lokaci kafin tace,"Yanzu mommy Idan na Amince, su kuma yaran Yaya rayuwarsu zata kasance?ina za akaisu? Ina tsoran Rayuwarsu ta salwanta !
Aunty babba tace "Hafsat don me zaki damu akan haka? ni in dai kin Amince zan sa akai yaran gidan marayu acan zasu samu kulawa, kuma dama can yafi dacewa dasu, in yaso sai mu runƙa zuwa muna kai musu Ziyara tare da tallafi koya kika ce?
shiru hafsat tayi na wani lokacin sannan tace"Shikenan Mommy na yarda da hakan, Amma yaya Omar fa? In yazo yaya zamu ce mashi in ya tambayi twins ɗinsa?
ɗan murmushi aunty babba ta saki ba ƙaramin daɗi taji ba jin yarda hafsat ta amince yanzu komai zai fi zuwa mata da sauƙi,
taci gaba da cewa "Hafsat duk yarda zamuyi kada mu bari Abban ki yasan da yaran nan har izuwa gobe, Akwai wanda nayi ma magana zai zo gobe insha Allah, Shi zai kai su gidan marayun, Sannan maganar Omar tunda har yakai yanzu bai zo ba, inajin cewa tabbas akwai abunda ya tsaida shi wannan ba matsala bace kibar mun komai a hannuna ni nasan yarda zance mashi ya yarda..................
Jinjina kai hafsat tayi jikinta a matuƙar mace saboda sabon da tayi da Su hussana da jahad sam batason rabuwa dasu amma kuma babu yarda zatayi this is the Only solution !!!
Ajiyar zuciya ta saki tare da kallon Mommyn nata tace "Shikenan Mommy, ni zan wuce ɗaki sai naji ki ............ Muryarta na rawa take magana cikin sauri ta ƴunƙura tare da miƙewa ta nufi hanyar fita ɗakin tana jin Muryar Aunty babba tana cewa "Yanzu zan tura maki da kuɗin ki mayar mata abunta, kar taja mana bala'e
Hafsat bata ce komai ba saboda yanayin da ta shiga, cikin sauri ta fuce kai tsaye ta shiga bedroom ɗinta,
Lokacin da ta shiga ta samu su hussana da jahad zaune saman darduma suna karatun Al'qur'ani da kansu, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya, cikin sauri ta faɗa toilet tare da rufo ƙopa tana faman shessheƙar kukan rabuwa dasu.........................................
__________________SEHRISH__________
Sam bakin ta yaƙi rufuwa don Murya, tun ɗazu ta shimafiɗa uniform ɗinta saman gadonta tare da sandal ɗinta da kuma school bag ɗin duka, ta tasa su gaba sai kallonsu take yi,bakomai take tunani ba face yarda zata fara shiga school gobe Talata, irin wankan da zata ɗauka,tana daga zuƙunne saman gadon nata sae faman sakin murmushi takeyi, hannu tasa tare da shafa uniform ɗin data jera tana cewa "daga gani zasuyi mun kyau,oh ni reeshi yanzu zanyi new friends a makaranta, da na banza da na kirki, Allah dae ya haɗa ni dana gari, ba wanda zasu canza min tunani na ba, ina ƴar talaka dani," ta faɗi da ƴar dariya,
Turo ƙopar Azmee tayi tare da shigowa tana cewa "Da alama yau sehrish kin manta da shiga kitchen ko? kin barni da aiki narasa dalilin dayasa kika zubama kayan makarantar nan naki ido,sai kace ba mallakin ki ba"?
tayi maganar yayin da take ƙarasawa ciki, ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta fuskarta washe tace "Am sorry aunty azmee, Yanzun nan nake shirin fitowa wlh, na kammala salla ne shine nake ɗan ƙara binsu da kallo,
girgiza kai Azmee ta ɗan yi kafin tace "maza ki tattara kayan nan, ki mayar dasu cikin wardrobe, Kizo maza mu kama aiki,'
Sehrish ta amsa mata da Toh sannan ta miƙe cikin sauri ta sauko daga saman gadon, Tattara kayan Uniform ɗin tayi takai su cikin wardrobe, bayan ta kammala ta ɗauki mayafinta saman gadonta, tayarfa shi akanta dama riga da skirt ne ajikinta,
Cikin sauri tabi bayan Azmee suka fuce izuwa kitchen,
Cikin hanzari suka soma shirye shiryen fara girkin dare, suna cikin aiki Azmee nagaban gas tana tafasa nama, yayin da sehrish ke ta faman fere kayan lambu asaman Chopping board,
Faɗowa junaid yayi cikin kitchen ɗin jikinsa na sanye da Kayan ball yellow sai faman zufa yake yi da alama shigowarsa kenan daga wurin ball, sam yagaza rufe bakinsa sai faman murmushi yake yi,
"Wlh harka ban tsoro junaid, yarda ka faɗo suddenly,jibi jikin ka sai faman zufa kake yi," Sehrish ta faɗi tana nuna sa da wuƙar dake hannunta,
Juyowa azmee tayi tana kallonsa batare da tace komai ba,
"Zuwa nayi in tunasar maki cewa, gobe ni zan kai ki school da mota ta," ya faɗi yana faman sauke ajiyar zuciya,.
Sai lokacin azmee tace "Salon wahalar da kai junaid, ka bari tahau school Bus mana,ƙwara tasa ba da bin motar makaranta tun yanzu, amma in kace zaka runƙa kai ta ɗawainiyar zatayi yawa, kuma kasan sarai Babban yayan ku baya so kana fita ko?.ta faɗi tana kallonsa,.
turo baki junaid yayi tare da ɗan buga ƙafarsa yace "Nidai Aunty azmee zan kaita, just for tomorrow cos this is the first time da zata fara zuwa school ɗin yakamata tasan wasu abubuwan inaso zan nuna mata ne, tun da ni nasan school ɗin sosai...."
gaba ɗaya kallon shi suke yi yarda yake magana cikin shagwa6a, yana faman bubbuga ƙafa
Dariya azmee tayi don ta Lura rigimarsa ce ta tashi, dama aduk lokacin daya buga ball sosai yagaji alokacin rigimarsa tafi tashi,
Sehrish tace "Shikenan junaid gobe kai zaka kaini school, amma yanzu kana buƙatar yin wanka ka ɗan huta,,"
ɗan murmushi yayi jin abunda tace "Amma ina jin yunwa fa sosai," ya faɗi yana kallonta
"Shikenan kada kadamu yanzun nan zan kawo maka abinci,"
"Yawwa My lovely sis," ya faɗi tare da kama hanya ya wuce upstairs room ɗinsa,
A tray ta shirya masa coffee tare da snacks, sannan ta fito ta wuce upstair domin takai masa, tana hawa saman stairs ɗin sai ga SGR shi da Marshal Omar suna nufo stair ɗin, ganin su zo dab da benen yasa ta saukowa gaba ɗaya don tabasu wuri su wuce, dukansu suna sanye da jean da t-shirt, sai faman sauri suke alamar akwai wani Uzuri dake gare su, suna ƙarasowa inda take tsaye tayi saurin cewa "ina yinin ku," Omar ne kawai yasamu damar Amsa mata, amma shi SGR sam ko kallo ma hasalima baisan da mutun a wurin ba, gabanta ne ya faɗi don alamu sun nuna cewa ba ƙaramin abubane ganin yanayin fuskar kowannansu Especially Omar da ta sani, Kullum cikin sakar mata fuska yake duk in suka haɗu amma yau dakyar ya amsa mata gaisuwarta,
Bin su tayi da kallo, yayin da suka wuce kai tsaye hanyar fita falon suka nufa, har sun kusa fita Omar ya juyo ya kalle ta, bakomai yasa Shi juyowa ba fa ce tuna Hussana da jahad yau tsawon wata kenan baije ya dubo su, saboda busy ɗin daya shiga, yana da burin zuwa ɗaukosu amma aiyuka sun hana shi, Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da kansa suka sa kai suka fuce,
sam sehrish tagaza yin motsi da ƙafafunta, hakanan ta dunga jin gabanta na faɗuwa, bata kai ga hawa benen ba, taji dirar motoci cikin gidan nan take ta sake jin faɗuwar gaba, cikin sauri ta haye upstairs ɗin da hanzari ta shiga bedroom ɗin junaid a lokacin yana cikin toilet yana wanka, ajiye masa tray ɗin tayi saman table, sannan tafito da sauri-sauri ta fito daga babban falon ta tsaya abakin ƙofar shigarsa, .
Kamar dai ranar da SGR da Omar suka zo Nigeria tare da uban security guards na sojoji haka yau ma, tsoro ne yakama sehrish gudun kar ace US zasu koma,
Tana ganin lokacin da suka shiga cikin motocinsu kuma nan take motocin ajere suka nufi dogon titin da zai fidda ka daga cikin gidan,
Komawa ciki tayi da gudun gaske ta faɗa kitchen tana faman kwalama aunty azmee kira, a ɗan razane azmee ta juyo ta kalle ta tare da cewa "Sehrish lafiya kuwa kike ta faman kwalamun kira haka!?
Cikin tsananin tashin hankali tace "Aunty azmee meke faruwa ne? Yanzun nan naga Babban yaya tare da Yaya Omar, sun fito fuskokinsu ba annuri kuma ga tarin motoci can sun fita dasu,"
tsayawa azmee taɗan yi jimmmmmmm tana ɗan tunani kafin tace "Tabbas ina hasashen cewa Us zasu tafi Saboda ɗazu da safe naji ƙishin-ƙishin ɗin cewa Momynsu matar Uncle ɗinsu donald tana fama da blood cancer, To ina da tabbacin cewa kodae ta rasu ne...........'
Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali take furta "Innalallahi wa'inna ilairaji'un Allah yasa bata mutu ba, Yanzu shikenan in suka koma ko yaushe zasu dawo.....'
Murmushi Azmee tayi kafin tace "naga kin tayar da hankalin ki, nasan saboda Tafiyarsu Rafayet ne bawai don jin mutuwar ba,
Hannu sehrish tasa tare da rufe fuska saboda hawaye da taji sun tafo mata,
bin ta da kallo kawai azmee tayi cike da mamakin ganin tana shessheƙar kuka,
Matsawa tayi kusa da ita tare da dafa ta tace"Sehrish !! Wannan kukan na menene? Ba dai don tafiyarsu bane?
shiru kawai tayi batare da tace komai ba, ita kaɗai tasan me take ji aranta, gaba ɗaya fuskarta ta damuje da hawaye,
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Ki koma ɗaki ki kwanta kawai,"
Cikin kuka sehrish tace "a'a aunty azmee zanyi aikin,"
Azmee tace "a'a banaso ki tafi kawai zan ƙarasa abuna,"
Juyawa sehrish tayi tare da fuce wa daga kitchen ɗin ta koma bedroom ɗinta, saman gado tafaɗa tare da cigaba da kukan, To fa sehrish komai yasata yin kuka? Allah wa'alamu,
Azmee kuwa ta jima tana mamakin dalilin kukan Sehrish tarasa gane mata, aranta tana cewa "Badai saboda tafiyar SGR take kuka ba? Don ta lura da yadda sehrish ke matuƙar ƙaunarsa, sam bata iya fira batare da ta, Amabaci sunan shi ba ita dae kawai tafison jin Ana maganarsa,nan zakaga sakewarta,
"Lallai ne akwai Babbar Matsala, muddin abunda nake zargi ya tabbata,ya zama dole in ja ma Sehrish burki, don gujema kamuwa da CIWON ZUCIYA,"!! Azmee ta faɗi acikin ranta,
_______________________
Sehrish kuwa Tuni wani Irin zazza6i taji ya rufe ta lokaci guda, jikinta har kerma yake yi wurin janyo bargonta dake asaman gadonta ta lullu6e jikinta dashi, tana faman fidda numfashi mai zafin gaske, sam tarasa ina zata tsoma ranta ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta
Har wuraren Sallar Magrib sehrish bata motsa ba, tana nan yarda take ƙudundune cikin barko,tamkar mai bacci alhalin nan Idonta biyu jikinta ne kawai da bayayi mata daɗi, Acan ciki kuwa fitowa junaid yayi bayan yasha baccin sa, ya sauya kayan jikinsa izuwa riga da wando, lokacin daya sakko down yayi mamakin ganin Azmee ita kaɗai tana faman jera masu dinner a dining, ƙarasawa yayi cikin sauri yana cewa"Aunty Azmee ina sehrish ɗin ne? Ita bazata fito ta tayaki ba? Azmee ta ɗan ɗago ta kallesa tare da cewa "Junaid ni kaina bansan meke damun Sehrish ba, Lafiya lou fa muke aiki da Ita, amma tunda tazo ta tambaye ni game da babban yayanku da Omar da taga sun fito fuskarsu cikin wani irin yanayi, kuma taga Sun fita tare da motoci dayawa, shine nake ce mata may be Us zasu je, tunda ɗazu da safe naji ƙishin ƙishin ɗin cewa Matar Uncle ɗinku donald tana fama da blood cancer may be ta rasu ne.....shine fa kawai sehrish takama kuka har nace mata ta koma ɗakinta kawai ni zanyi aikin," ta ƙarasa maganar cikin damuwa, Junaid kuwa shiru yayi hankalinsa ya rabu gida biyu, sam ya rasa gane inda maganar Azmee ta dosa, cikin mamaki yace "Us kuma? Taya babban yayan mu zaibar ƙasar nan batare da sani na ba? Anya kuwa aunty Azmee am just doubting about it bana tunani Us zasu je, kuma Matar uncle donald bana tunanin ta rasu gaskiya, tunda da naji ko a wurin Abban mu ne, Ni dai Allah yasa ba wani abu bane ya faru mummuna," ya faɗi cikin tashin hankali kafin ya wuce yana cewa "Bari naje wurin Sehrish ɗin naji meke damunta,"
Azmee tace "to shikenan,"
A hankali ya tura ƙopar ɗakin yashiga da sallama, tsayawa yayi yana kallonta yarda take ƙudundune cikin bargo, A hankali ya kira sunanta "Sehrish..........' shiru bata amsa masa ba, ƙarasawa yayi izuwa gab da gadon nata yaɗan zauna gefe tare da sa hannu ya yaye mata bargon dake jikinta, dogon numfashi taja tare da cewa "Junaid ka mayar mun da bargona, Sanyi nake ji," Junaid yace "Reesh wai meke damunki ne? Aunty azmee ta faɗamun cewa kinbar kitchen kina faman kuka? Cikin kuka tace "Junaid wai dagaske ne cewa Babban yaya da Yaya Omar us zasu koma yau? Sakin baki junaid yayi yana kallonta cikin tsananin mamaki amma bai kawo ma ransa komai ba sai cewa yayi "Sehrish dama akan wannan kika shiga damuwa? to ki kwantar da hankalin ki, Yaya Omar da yaya Rafayet bana tunanin sun bar ƙasar nan ne, Aunty azmee ce kawai tace maki hakan a hasashen ta, just calm down ur mind My lovely sis... . ...........jin abunda junaid yace yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa zaune daga saman gadon tana cewa "ngde da jin hakan junaid, naji ma anata kiran sallar magrib bari naje nayi alwala," junaid yace "to shikenan nima bari naje nayi salla,pls reesh karki ƙara sa damuwa irin haka, kuma in kin kammala sallar, ki fito muyi dinner atare," Murmushi ta sakar masa tare da cewa "Ok my lovely bro, da zarar nayi sallah zan fito nima," lumshe ido junaid yayi tare da buɗe su akanta fuskar nan ɗauke da Murmushi, sai da yaga sehrish tashiga toilet sannan yafuce hankalinsa a kwance..........................❤
remain 2 pages free su ƙare, wanda baiyi payment ba ya hanxarta Yi, Abban Sojoji 300 ne, discount da nayi na Abbban sojoji fans group ne kawai 200, Vip kuma 700, bank details ɗin da za'a tura,3196407426 First bank, Bature Hafsat Muhammd Evidence of payment 08103884440
[9/13, 11:08 AM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 23-24
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️
*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• Fitowa tayi tana faman yarfar da ruwan alwalar dake hannunta,hijab da sallaya ta ɗauka a wardrobe, ta shimfiɗasu tare da kabbara sallah,bayan ta kammala tabar darduman anan saboda in an kira isha'e, hijab ɗin ta cire tare da ajiye shi saman gadon sai ta ɗauki Mayafinta, ta yafa shi akanta,
Fitowa tayi kai tsaye ta wuce dining, a lokacin junaid ma yana a wurin tare da Haroon sai kanal Yusif duk suna zaune, yayin da Azmee ke faman ɗawainiyar Zuba masu abinci,
Ƙarasawa tayi tare da cewa "Sannu da aiki Aunty Azmee,"
Juyowa azmee tayi tare da kallonta tace"Yawwa mutuniyar sarkin kuka, Lamarinki naban mamaki kamar me iska,"
Sunnar da kai Sehrish tayi tana ɗan Murmushi kafin daga bisani ta gaishe da Kanal yusif da fara'arsa yace "Our Princess,duk yau ban saki a idona ba, Yakamata ace kina sakewa da ƴan uwanki sosai,"
Murmushi kawai Sehrish tayi tare da zama kusa da junaid suna facing ɗin kanal yusif da haroon ta hannun dama,
Zuba mata abinci azmee ta soma yi a plate, junaid dake a gefenta yace"Da ace baki fito ba ko, da bazanci komai ba Allah,"
Kafin sehrish tace wani abu haroon yayi saurin cewa "Saboda ciki ɗaya kuka fito ko? murmushi junaid yayi tare da cewa "Yaya Haroon yadda na ɗauƙi Sehrish ta wuce haka a wurina," ta6e baki Haroon yayi yana kallonta, Harara Sehrish taɗan wurga masa tare da murguɗa masa baki, jinjina kansa yayi tare da cewa "An fa samu freedom of sitting the same table da Ƴa'ƴan masu gida dole ayi iya shege,
Jin wannan maganar ta Haroon ta sanya junaid ɗaure fuska lokaci guda yace "Yaya haroon me kake nufi da hakan?
Haroon yace "Abunda ranka yabaka"
Dakatawa kanal yusif yayi daga cin abincin da yakeyi ya ɗan bubbuga plate ɗin dake gabansa da cokalin hannunsa ya bada sauti sannan ya aza idonsa akan na Haroon, Ganin irin kallon da kanal yusif ya jefa masa ne yasa shi, yin tsit ya shiga taitayinsa,
Mayar da idonsa yayi kan Sehrish yace"Sister Yaushe ne zaki fara zuwa school ɗin? yayi hakan ne donya mantar da ita maganar haroon, ganin yarda tayi sanyi lokaci guda,
daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa "Gobe ne insha Allah,"
Kanal yusif yace "Masha Allah,A matsayina na yayan ki, akwai wani jan hankali da nakeso nayi maki, kin ga gobe zaki fara zuwa, kuma zaki fara haɗuwa da sababbin ƙawaye iri-iri,akwai good friends waɗanda zasu dunga ƙarfafa maki guiwa akan karatu ta hanyar baki shawarwari masu kyau,bayan su kuma akwai bad friends gur6atattu waɗanda majority ɗinsu ba karatu ya kaisu ba,Asarar kuɗin iyayensu kawai suke yi, basa karatu ƴan abi yarima asha kiɗane,babban ma tashin hankalin yanzu majority na irin waɗannan ƙawayen ƴan Lesbian ne,fitsararru marasa kunya waɗanda suka gagari iyayensu da malamansu, burinsu kawai su 6ata tarbiyyar wasu, bana so ki kasance ɗaya daga cikin irin waɗannan ko kusa, dayawa wasu suna kuskuren yin abota da irin waɗannan bad friends ɗin, sai suce ae basu suke aikatawa ba,sun manta cewa zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai,to koda gigin wasa bana so ko fira ta haɗaki da irin waɗan gur6atattun balle harku ƙulla Abota, Ina gargaɗin ki akan hakan ! And i want u to know that Ke yanzu kina ɗaya daga cikin Mutuncin gidan nan!! Kuma kinsan yarda sunan family ɗinmu ya karaɗe ko'ina, ba inda ba'asan Jinin SALAHUDDEEN HUSSEIN ba, don haka yazama dole ki kiyaye mutuncin family ɗinmu da kuma ƙimarsa, ina fata kina fahimtar abunda nake cewa"? Ya tambaya yana kallon sehrish wadda ta natsu tana sauraronsa cikin sauri tace "Ina fahimtar duk wani abu da kace yaya yusif, kuma insha Allah zan kiyaye faruwar hakan,kuma naji daɗi sosai harma baxan iya misaltawa ba,saboda na samu ɗan uwa nagari wanda yake mun nasiha akan na tsira da mutunci,babu wanda ya tunasar dani akan hakan sai kai, kuma insha Allah bazan ta6a baku kunya ba, zan kasance ɗaya daga cikin abun Alfaharin gidan nan,"
taƙarasa maganar yayin da idonta suka ciko da kwalla, gaba ɗaya Azmee da Junaid sun kasa kunne suna sauraron maganar tasu, dukansu babu wanda baiji daɗin maganar Kanal yusif ba, Illa mutun ɗaya Wato Haroon wanda ke ta faman tur6une fuska yana faman hura hanci aransa yana cewa "Insha Allah ni kuma bazan taba barin ki ki xama abun alfaharin gidan nan ba, balle har ki samu matsayi acikinsa, saina san yarda zanyi in tarwatsa komai har inyi sanadiyar korarki acikin gidan nan," ya faɗi yana kallon sehrish rai a6ace yana faman tura dambun nama abakinsa har yana shaƙewa,
Kanal yusif kuwa murmushi ya saki sannan yaci gaba da cewa "Allah ya yarda Sehrish,Nima inason ki zama Abun alfaharin mu gaba ɗaya," ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu ya ɗauki glass cup dake ɗauke da Lemu mai sanyi yakai bakinsa yana kur6a,
ƙasa-ƙasa da murya junaid yayi tare da cewa "sehrish nima fa naso nayi maki nasiha akan zuwanki makaranta, amma kash sai gashi Yaya yousouf ya riga ni, amma duk da haka ban makara ba, don Allah sehrish karki canzamun koda kin fara zuwa school don nasan zaki ƙara wayewa sosai..........'
Murmushi sehrish ta saki jin abunda junaid yace, kafin tace "Insha Allah junaid hakan baxata ta6a faruwa ba,mu aminnan juna ne zamu kasance atare ako wane hali na rayuwa, kaine abokin shawara na,"
ajiyar zuciya junaid ya saki aransa yana ƙara samun kwanciyar hankali jin bayanan da sehrish tayi masa,
wayar haroon ce dake acikin aljihunsa ta soma ringing taken waƙar nan da ake cewa "ɗan duniya hayaƙin taba," jin ringing ɗin wayar yasa kanal yusif girgiza kai tare da cewa "Allah ya shirya ka,"
Haroon yace "Ameen don son Annabi," sannan yayi saurin tashi daga dining ɗin yakama hanyar fita daga falon yana zaro wayar daga aljihun wandonsa, ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnansa yana cewa "Shegen bisa ashe har ka isa hotel ɗin, ae ko gani nan zuwa Yanzun nan Allah yasa ka taho mana da harkar nan..........' ya yi maganar da dariya a fuskarsa kafin yasa kai ya fuce,
Bayan sun kammala dinner ɗin junaid suka wuce masallaci tare da kanal yousouf jin ana kiran isha'e,.
Itama Sehrish bayan ta kammala dinner ɗin tare da azmee suka kwashe kayan da sukayi amfani dasu izuwa kitchen, Sehrish ce ta wawwanke su tare da jerasu a ma'ajiyarsu,
Bayan ta fito suka ci karo da azmee tace " Inaso naje na kwanta,pls kada ki bari bacci ya kwashe ki, idan Twins sun dawo ki tabbatar kin kai masu dinner ɗinsu, Shima Abbansu pls ki kaimasa nasan ƙila sai wurin 12 zasu shigo,.
Sehrish tace "To aunty azmee insha Allah baxanyi bacci ba, zan kai masu in sun dawo,"
daga nan azmee ta wuce ɗakinta, itama sehrish bedroom ɗinta tashiga, sai da tafara shiga toilet ta kuskure bakinta, dama da alwalarta,
Fitowa tayi ta ɗauki hijab ɗinta da ta ajiye saman gadonta, ta kabbara sallah
_________________________________________________
Tuni General ishaq ya iso gidan ya cika tab da mutane tare da jami'an sojoji da suka rakosa, su Aunty babba sai faman rawar kai akeyi miji ya iso gari, a lokacin hafsat har ta shirya kanta itama tsaf ta kimtsa cikin haɗaɗɗen cord lace Ash colour mai adon duwatsu,rigar mai dogon hannu sai skirt ba ƙaramin kyau kayan su kayi mata ba, gashi dama takware wurin iya kashe kallabi, tare da Mommyn nata da wasu daga cikin abokanan aunty babba da suka zo dana hafsat suke taimakawa wurin tarbar baƙi da abunsha dana ci,
"Jahad ya Omar shiru kodai ya manta damu ne"? Hussana ta faɗi fuska tamkar zatayi kuka tana kallon jahad suna zaune dab da juna daga gefen gadon hafsat,
"Hussana bana tunanin hakan, Ya Omar yana son mu sosai ni ina da tabbacin yana sane damu,kuma zaizo ne insha Allah," acewar jahad
Hussana tace "Ni inajin tsoron a rabamu da ya Omar, wlh banso banso....'
Kamar daga sama suka ji Muryar Aunty babba tace "Saboda ƙanin ubanki ne ko? ta faɗi ayayin da take shigowa, arazane suka miƙe tsaye su duka suna kallonta, su biyu suka shigo cikin ɗakin ita da wata hajiya, amma ita ta tsaya daga baya
Kusa dasu taje sannan tasoma magana "Ko da gigin wasa bana so wata daga cikin ta leƙo da kanta daga cikin ɗakin nan ! Saboda Mijina ya dawo kuma banaso ya gan ku, ina fata kun gane?
Cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Insha Allah aunty bazamu fito ba,"
ta6e baki tayi sannan ta juya bayanta ta kalli matar da suka shigo tare tace "Hajjaju gafa yaran nan da nake faɗa baki, Omar yakawo min cikin gidana,"
ƙarasa shigo wa ciki matar tayi jikinta na sanye da shadda gezna green colour tasha uban aiki a wuyan rigar, tayi ɗaurin ɗan kwalin ture kaga tsiya sannan ta yarfa gyalenta a kafaɗarta,
Alokacin da matar ta ƙaraso Jahad taganta nan take gabanta yayi wani irin bugu zaro ido tayi tana kallonta saboda son tuna inda tasan fuskarta,
Hajjaju kuwa tana ganin su hussana da jahad farat ɗaya ta gane su, a ɗan razane ta dafe ƙirji tare da cewa "Kaiii !!!" taja maganar da ƙarfin tana kallonsu cikin mamaki da al'ajabin wannan Ikon Allahn,
tuni aunty babba tagama ruɗewa ganin yadda hajjaju ta razana da ganinsu, da kuma yarda jahad ta firgita itama wannan alama ce dake nuni da sun san juna kenan ko yaya,
Cike da mamaki Aunty babba tace "Wai meke faruwa ne hajiya rabi? kinsan su ne?
Cikin sauri hajjaju tace "A'a bansan su ba, Kamar dae nata6a ganin mai kama dasu ne,"
tayi maganar tare da ruƙe hannun Aunty babba taja ta, suka fuce daga ɗakin,
Kallon jahad hussana tayi tare da cewa "Jahad wacece wannan matar? Naga kin razana da ganinta,"
"Nima so nake na tuna inda nasanta," Jahad ta faɗi tana faman cizon akaifar hannunta da takai abakinta,
Hajjaju kuwa da taja Aunty babba suka fuce can suka nufa wurin kitchen suka tsaya, ga mutane sai faman shige da fuce suke,.
"Dan Allah ki faɗamun gaskiya hajjaju raina na bani cewa kinsan yaran can ko? Aunty babba ta tambaya tana kallonta cike da son jin ƙarin bayani daga wurinta,
Jinjina kai Hajjaju tayi tare da cewa "Yau naga ikon Allah, Lallai ne duk zakaran da Allah ya nufa da cara,to fa sai yayi ta, haƙiƙa nayi matuƙar mamakin yarda akai har Allah ya haɗa Omar da waɗannan yaran , kai kaga wani ikon Allah nan ! mai matuƙar ban mamaki da Al'ajabi?
Hajjaju tayi maganar cikin nuna mamakinta,
Aunty babba kuwa cewa take yi "Hajjaju kin barni acikin duhu, wlh har kinsa hantar cikina ta kaɗa dan Allah kisanar dani me kika sani agame dasu?
dariya hajjaJu tayi tare da tafa hannayenta tace "Ana bura'uba a lagos! yo ke laila da kike cewa zaki sa a zubar maki da waɗannan yaran don ki nisanta su da Omar, idan Kin toshe wannan hanyar to ita waccen ɗayar hanyar da ta ruga isa inda bakya so ya zakiyi da ita?
gaba ɗaya fa Aunty babba ta gama rikicewa da bayanin hajjaju, cikin tashin hankali tace "wai me kike nufi ne hajjau, kiyimun bayani mana yadda zan fahimta !!!
ta faɗi tare da ɗan jan guntun tsoki, Murmushi hajjaju tasaki sannan tace "Ni baza kiji mutuwar sarki abakina ba!kawai abunda nakeso ki sani shine babu wanda ya isa ya hana ruwa gudu sai Allah! Bakin alƙalami dai ya ruga daya bushe, Amma fa waɗannan yaran da kike gani wlh ikon Allah ne su, tunda har Allah ya haɗasu da Omar aikuwa magana ta ƙare, Yakamata kisan abunyi,'
Hajjaju tayi maganar tare da wuce wa ciki tabar Aunty babba tsaye abakin kitchen baki asake, lokaci guda taji ta ƙara tsanarsu hussana da jahad tabbas suna tattare da wani abu yaran, duk da bata fahimci inda maganar hajjaju ta dosa ba,
ranta ya gama 6aci tsoki ta buga tare da cewa "ta tsaya tayimun bayani amma ta tsaya yimun wasu sambatun banza dana wofi,ni duk tasa hankalina ya ƙara tashi, kuma wlh goben nan zansa a Kwashe mun su aje can azubar dasu tsakar daji, sai dae abunda bangane ba acikin maganar hajjaju wacece ɗayar hanyar da take nufi wadda ta isa inda banaso!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!? ta tambayi kanta sai dae kash babu amsa hakanan ta koma ciki tana faman sambatu aranta,
Zumbur !! Jahad tayi tare da kallon husana tace "Wlh nasanta!! Nagane ta !! Itace matar da ta taimaka mana a asibiti har ta biya kuɗin gadon Ki husana, wlh itace matar da tasama ma SEHRISH aiki, hakan na nufin ta son inda sehrish take.....!!
Cikin tsananin farin ciki jahad tayi maganar, hussana ma aɗan raxane tace "dagaske jahad itace tasama ma sehrish aiki? Ke nan itace kawai zata iya faɗa mana inda ƴar uwarmu take kenan,.
jahad tace "eh itace, nagane ta yanzu ya za'ayi muyi magana da ita, gashi aunty ta hanamu fita, amma ni dae inason magana da ita kodan saboda ta faɗa mana inda sehrish take,' jahad tayi maganar fuskarta tamkar zatayi kuka,
Cikin sanyin murya hussana tace "Jahad kada ma musa rai don nasan bazata faɗa mana ba, ita fa ƙawar Aunty ce, kuma kinsan muguwace idan halinsu ɗaya fa? Bazata ta6a faɗa mana ba, Ni tsorona ma kada ta faɗa ma wannan muguwar auntyn inda sehrish take, suna iya zuwa su cutar da ita, Allah yasa sehrish tana lafiya banaso wani abu yasame ta.........'" tayi maganar cikin shessheƙar kuka,
"Da gaskiyar hosana,Nima ina tunanin hakan Allah yasa karta faɗama auntyncan inda ƴar uwarmu take, amma dai ni inason naga matar na roƙeta akan ta faɗa mana inda sehrish take,yakamata musan inda take, wane hali take ciki, gashi yanzu sai mutuwa akeyi Ya Allah kasa sehrish tana araye har mu haɗu," tayi maganar idonta cike tab da hawaye,
daga bisani ta kalli hosana tace "ki zauna hosana kada ki fito bari ni naje nayi magana da matar na roƙe ta, ta faɗamun inda rishi take,"
Hosana tace "toh," sannan tasamu wuri ta zauna gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya,
Cikin sanɗa jahad ta futo daga kopar ɗakin ta tsaya tana ɗan leƙa kanta, mutane tagani gasu nan sai faman zarya sukeyi acikin babban falon,
A hankali ta miƙi hanya ta soma tafiya tana faman waige-waigen neman hajjaju, ta ɗanyi nisa a tafiyar ta ta, tajiyo magana daga bayanta ana cewa "Nasan cewa ni kike nema ko"?
Cikin sauri jahad ta juyo bayanta, hajjaju ce tsaye tana kallonta fuska ɗauke da murmushi,
Ajiyar zuciya jahad ta saki sannan itama ta mayar mata martanin murmushin tare da gaishe ta, hajjaju ta amsa mata da cewa "Nayi mamakin ganin ku, anan gidan ko ba'a faɗamun ba nasan cewa kunsha wahalar rayuwa don nasan Laila sarai muguwace bata da Imani,kuma tana sanar dani game daku a waya sai dai bansan cewa ku bane,"
Jinjina kai Jahad tayi tare da cewa "Munsha Wahala sosai tamkar ba zamu rayuwa ba,dan Allah ki faɗa mana ina Sehrish take? Munyi kewarta sosai, rabon mu da ita, tun da ta tafi aikin nan da kika sama mata,bayan wasu kwanaki hosana ta 6atar mana da wayar da muke amfani da ita wurin kiranta, shikenan rabuwarmu da ita......' jahad ta ƙarasa maganar idonta cike tab da kwalla,
ɗan shuru hajjaju tayi tana kallonta gwanin ban tausayi kafin tace "Kiyi haƙuri, amma bazan iya shaida a ina sehrish take ba nikaina,saboda nasaba hulɗa da yara ina sama musu aiki, bazan iya tuna a wane gari nakai sehrish ba, bazan iya tunawa ba......'
Jin hakan yasa Jahad fashe wa da kuka mai cin rai, matsawa hajjaju ta ƙara yi gab da jahad tasanya hannunta tare da dafa kafaɗunta tace"kiyi haƙuri Jahad, ina mai matuƙar jin takaicin gaza taimaka maku akan halin da kuke ciki, haƙika kun ga rayuwa, amma ni abunda nakeson sani taya akai kuka haɗu da Omar? bayan naji labarin rasuwar tsohuwa ya gigita ni matuƙa, sannan naji labarin cewa ana zargin cewa kune kuka bata poison amma bansan ya ƙarshen labarin yake ba,'.
Cikin shessheƙar kuka jahad tace "bayan tsohuwa ta rasu, mutane suka ce mune muka kashe ta alhalin mu bamu da masaniya akan mutuwarta, shine aka kaimu police station, munsha Wahala sosai saboda bamu da sheda, ana shirye shiryen za'a miƙa case ɗinmu kotu, hussana tayi rashin lafiya shine dalilin dayasa ƴan sanda suka tafi da ita asibiti tare dani, Acan ne Allah ya haɗamu da yaya Omar shine ya kwace mu daga hannun police ɗin kuma ya kashe case ɗin gaba ɗaya......' ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya,
Murmushi hajjaju tasa ki tare da cewa "Allah sarki Omar mutumin kirki ne sosai, yana da tausayi inama ace tunfarko ba nan ya kawo ku ba, wlh da kun more rayuwarku,amma sai dai kash yayi kuskuren jefa rayuwarku cikin haɗari batare da sanin shi ba, Amma insha Allah Laila bazata ta6a cin nasara akanku ba,'
Jinjina kai kawai Jahad ke yi, bayan sun ɗanyi shiru hajjaju tace "Muje ɗakin da kuke,ina son ganin ƴar uwarki danaji kin kirata da hussana, bazan manta ba itace a lokacin kwance saman medical bed ansa mata oxygen tana shaƙar numfashi cikin mawuyacin hali, Amma yanzu naganta taji sauƙi sosai jiki yayi kyau,' hajjaju ta faɗi da ɗan murmushi a fuskarta yayin da suke nufar ɗakin hafsat atare,
Suna shiga suka samu hussana atsaye sai faman zirga-zirga take yi burinta kawai jahad tadawo kusa da ita,
Tsayawa tayi ganin sun shigo tare da matar, Murmushi hajjaju ta sakar ma hussana tare da ƙarasawa inda take ta rungumo ajikinta, tana ɗan bubbuga bayanta tace "nasan ke baki sanni ba,sabosa lokacin kina kwance rai hannun Allah, amma ni nasan ki saboda naganki a lokacin, naji daɗi sosai dana ganki cikin ƙoshin lafiya,
Hajjaju ta ƙarasa maganar tare da janye hussana daga jikinta, ita dai hosana kallonta kawai take yi don batasan ta ba, mayar da idonta tayi kan jahad tace "ta faɗa maki inda sehrish take?
Jahad tace "a'a hosana, tace itama ta manta inda takaita aiki saboda ta saba kai yara aiki bazata iya tuna inda takai su ba,"
Jin haka yasa Hosana fashewa da kuka tana cewa "..yanzu shikenan bazamu ƙara ganin sehrish ba....
Hajjaju tace "Ki daina kuka hosana,wayace maki bazaku sake ganin sehrish ba? Ki daina wannan tunanin Insha Allah zaku haɗu da ƴar uwarku, abunda nakeso daku kawai ku cigaba da addu'a insha Allah zaku dace,"
Jahad tace "kullum muna cikin yin addu'a,Kuma zamu cigaba da yi har illa masha Allah"
Murmushi hajjaju ta kuma yi sannan tace "Ni zan wuce,Ku kula da kan ku,Allah ya Albarkanci rayuwarku, yaci gaba da tsare ku aduk inda zaku kasance arayuwar nan,"
Suka amsa mata da "Amin," sannan tasa kai ta fuce tana mai jin rashin daɗin gaza taimaka masu da tayi na ƙin faɗa masu inda ƴar uwarsu take, bayan ta son inda take,
Komawa sukayi atare suka zauna jikinsu amace, Shin mai zai biyo baya?😥
Bayan wasu lokutta, duka baƙin da suka zo suka tafi gidan yayi tsit ba hayani, suna cikin wannan zaman na jimamin Ga samu ga rashi, na hajjaju da suka haɗu da ita yau, sun son itace kaɗai zata faɗa masu inda Sehrish take gashi itama tace bata sani ba, hakan ba ƙaramin kashe musu zuciya yayi ba, daker suka samu bacci ya ɗauke su,
_______________________
Fitowa daga wanka general ishaq yayi jikinsa sanye da gajeran wando, Closet ɗinsa ya nufa tare da sa hannu ya buɗe ya ɗauko jallabiya ya zumbula ajikin shi, Sarai yasan cewa tana ɗakin Amma sai yayi tamkar bai ganta ba, sai da ya kammala kimtsa kansa sannan yace "Ya Rashin Ji"? Ya tambaya yana kallon kansa acikin Mirror, mamaki ne ya kama aunty babba jin abunda yace, tana zaune daga gefen gadonsa tace "Nifa ce ba hafsat ba," ta faɗi tana kallonsa
Ishaq yace"Nasani ae, dake nake magana, duk rashin jin hafsat ae bata kai ki ba, kefa tamkar 6eran gida kike wurin 6arna da rashin ji,"
ɗaure fuska tayi jin abunda yace rai a6ace tace "Alamu sun nuna cewa ba kayi kewata ba ko? shiyasa kake gayamin magana, ko da yake dama kai ae ba ka iya soyayya ba, Iya ruƙe bindiga kaɗae ka sani,"
......juyowa Ishaq yayi yaɗan kalle ta tare da ta6e bakinsa yace "ban iya soyayya ba, amma gashi nan har kin haifi hafsat dani ko? Naga wannan ma ae wani sashe ne na soyayya,"
ya ƙarasa maganar tare da wuto wa ya haye saman gadonsa ya kwanta yana cewa "Idan kin tashi fita daga ɗakin kada ki manta, ki kashe mun hasken inaso nayi bacci,"
a ƙule aunty babba ke kallon shi, can kuma ta miƙe fuuuuu ta nufi hanyar fita har takai bakin ƙopar ɗakin ta kuma tsaya tare da juyowa tana kallonsa, abun mamaki sai ta same shi yana ta faman tiƙar dariya,
Bakomai yasa ta tsayawa ba face tsananin son kasancewa dashi da take yi,
dakatawa da dariyar yayi sannan yace "nifa ba korarki nayi ba, zaki iya dawowa kiyi zaman ki,"
murguɗa masa baki tayi aranta tace "shashasha dama nasani ae dole ka buƙace ni,"
shi kuma aransa yace "Mayya, Jibi yarda take ta hau hawa kamar buhun harawa, duk an cinye mun abincin gidana," 😂
Kamar taji mi yace ta ɗan kallesa tare da jinjina kanta tace "bari na kawo maka Tea,"
"Ok i wll be waiting for u," ya faɗi yana faman yin dariya ƙasa-ƙasa, general ishaq kenan tamkar Abbansu haka yake indai wurin iya zolaya ne,
******************************
A 6angaren sehrish kuwa, sam taƙi bari bacci ya ɗauke ta sai faman gyangyaɗi take yi tana zaune asaman kujerar dake gaban mirror burinta kawai su twins su dawo ko tasamu ta kai masu abincinsu, sune kawai suka rage mata takai mawa, domin kuwa ta jima da kaima Abbansu nashi tunda ya dawo,
Basu tashi dawo wa cikin gidan ba sai wuraren ƙarfe Sha biyu da rabi suka shigo suka shigo cikin falon kai tsaye ɗakinsu suka wuce, shaf shaf suka shiga rage kayan jikinsu, sai da ya rage daga su sai shorts ajikinsu, sannan suka shige toilet donyin wanka, sun jima aciki kafin daga bisa ni suka fito kowannansu ɗaure da towel a waist ɗinsa, closet ɗinsu suka buɗe jerin kayansu ne ajere komai iri ɗaya, kamar yadda suke tagwaye haka komai nasu yake iri ɗaya, kimtsawa su kayi cikin sleeping dress riga da wando milk colour,
faɗawa su kayi saman gadon Su tare da rungume junansu suka ci gaba da abunda suka saba, kamar injina haka suke sam basa gajiya,abun ya zamar masu jangwangwam,
Kwankwasa ƙopar bedroom ɗinsu akayi, kusan sau uku basu ji ba, sai ana huɗun Jahan yace "Wai Uban wanene yake buga ma mutane ƙopa? Atunaninsa Sehrish ce tazo kawo masu dinner ɗinsu,
Amma sai yaji akasin hakan Muryar haroon yaji yace "Ubanka ne shege, zoka buɗe mun ƙopa in shigo," Uban tsoki Jahan yasaki tare da ƙara ƙanƙame Ayaan ajikinsa yana cewa "wlh bazan buɗe masa ƙopar ba, bansan uban me yakawo shi bedroom ɗinmu ba,"
Ayaan yace "Amma sweet heart baka tunanin wani abu mai mahimmanci ya kawo shi"? ya faɗi yana faman lumshe idonsa akan Jahan,
guntun tsoki jahan yaja tare da cewa "Wlh bazan buɗe masa ba, yazo yayi disturbing ɗinmu ne kawai,"
duk abunda suke cewa a kunnan haroon dake tsaye abakin ƙopar ɗakin nasu, Jinjina kansa yayi yace "Yara kenan dani kuke magana," hannunsa ya tura cikin aljihunsa tare da zaro wayarsa yaci gaba da daddanata na wani lokaci, daga bisani ya mayar da wayar cikin aljihunsa sannan ya ɗaga murya tare da cewa "tunda bazaku buɗe mun ƙopar ba, ku duba wayoyin ku acikin whatsapp ɗinku na turo maku wani saƙo mai mahimmanci,"
Jin hakan yasa su dakatawa gaba ɗayansu cikin sauri jahan ya zura hannunsa asaman side drawer ya ɗauko wayarsa da hanzari ya miƙe zaune, whatsapp ɗinsa yashiga mamaki ne yakamasa ganin Numbar da yayi saving da yaya Haroon ya turo masa Video, cikin sauri yashiga chat ɗin tare da danna video ɗin ya buɗe...........lokaci guda jahan yayi wata irin Zabura sai gashi tsaye saman gadon hannunsa na kerma gaba ɗayama jikinsa, nan take kuma wata irin Zufa ta shiga wanko masa duk da sanyin A.c in dake ɗakin, Zazzaro idonsa yayi hankali a matuƙar tashe yace "AYAAN MUN SHIGA UKU!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
jin hakan yasa Ayaan tasowa shima ya miƙe tsaye yana cewa "jahan menene ya faru na ga duk ka razana,"
Miƙa masa wayar yayi batare da yace komai ba, amsa Ayaan yayi yana duba video ɗin, porn video ɗinsu ne shida Jahad, gasunan kwance saman gado a ɗakin hotel ɗin da suka kama, tsantsar mamaki ne a fuskar Ayaaan a ruɗe yace"Jahan taya yaya haroon ya samu wannan video ɗin?
"Nima shine abunda ban sani ba," Jahan ya faɗi cikin tashin hankali,
Muryar haroon ce ta dakatar dasu da cewa "Oya, azo abuɗe mun ƙopar,"
A hanzare suka diro daga saman gadon tare da nufar ƙopar suka buɗe masa,
shigowa yayi yana faman sakin shu'umin murmushi yace"Ƴan duniya, fararen Balbelu tun yaushe kuka fara wannan harkar bansani, ahhh gaskiya wannan anyi mun nisa
har suna haɗa baki wurin cewa "yaya Haroon ba yin kan mu bane, dan Allah ka rufa mana asiri,"
atsiyace yabi su da wani irin kallo kafin yace "taya kuke tunanin zan iya rufa muku asiri hakanan siddin ragadan ku ci banza!!? nifa dama nasani duk kaf zuri'armu babu fasiƙai irin ƴa'ƴan mommynku, masu jaza mana bala'e acikin zuri'armu,' yayi maganar fuska aɗaure yana kallonsu
Jin wannan magana ta haroon ya sanya su jin wani irin ɗaci aransu,
Ci gaba da magana haroon yayi "kai nifa tunda Mommynku ta nuna ta tsane ni bataso na, Nima naji cewa bana ƙaunarku! bama wannan ba adalilin ku yasa abba yadaina so na kwata-kwata nazama abun ƙyara acikin gidan nan, don hak wannan babbar dama ce agare ni, Idan har na ɗaura wannan videon a Social media, Abban mu ya gani to tabbas nan take zuciyarsa zata buga ya mutu! idan kuma babban yayan ku ya gani hohohoho ku kunsan mai zai faru, Idan Ammi tagani shikenan zata rabaku da mahaifinku ne na har Abada dama ba sonku take ba, tabbas wannan babbar dama ce agare ni !!! Ya faɗi da dariya a fuskarshi
tuni Ayaan da Jahan sun zube agabansa saman guiwowinsu idonsu cike tab da hawaye, tabbas sunyi mamakin Kalaman haroon yadda ya nuna irin tsanar da yayi masu tamkar ba jininsu ba,
cikin tsananin ƙunci suke cewa "Yaya Haroon pls ka rufa mana asiri dan Allah, kada kace za kayi amfani da wannan damar wurin tarwatsa farin cikin gidan nan, kaifa ɗan uwan mu na jinin mu dan Allah yaya haroon ka dubi girman Allah kada kayi mana haka,"
Fashewa da dariya haroon yayi yana binsu da wani irin kallo na ƙasƙanci yace "Au haba? Ashe nifa jinin ku ne? Amma taya akai bamu kama? Ikon Allah sai yau kukasan da hakan? kaiiiii ! Ni saima yanzu na lura wai yau ƴa'ƴan Alexandra ne durkushe saman guiwowinsu agabana suna neman afwa hada matsar kwalla kodai mafarki nake yi ne?
Yayi maganar tare da sa hannunsa yana murza idanunsa wai donya tabbatar ba mafarki yake yi ba,
shiru su kayi gaba ɗaya jikinsu ya mutu sai uwar zufa dake wanko masu, ga jikinsu dake ta faman kerma yayin da idanunsu suka ciko tab da kwalla, gwanin ban tausayi
Murya na Rawa Ayaan yace "Ka faɗi komai kake so za muyi maka donka rufa mana asiri,"
Haroon yace"yanzu naji magana, Anzo dai-dai wurin dana fi so,"
ya faɗi tare da ƙara gyara tsayuwarsa yace "Abu biyu nake buƙata muddin kukayi mun hakan to shikenan zamu raba jaha daku,".
Cikin sauri suka amsa masa da cewa "muna sauraronka,"
wani irin bazawarin murmushi ya saki kafin yace "Nima fa kwararrene a irin wannan harkar taku! gashi kuma dama na jima ina sha'awarku musamman junaid, Kai yaron akwai sirrin kyau atattare dashi kuma daga gani zaiyi ni'ima sosai........'
a firgice jahan ya daka masa tsawa tare da cewa "Ya isa haka!! Komai za kayi ka tsaya a iya kan mu kawai, amma koda gigin wasa kada ka ƙara kiran Sunan junaid da waɗannan munanan kalaman naka! saboda ba zaka ta6a samun abunda kake so agame dashi...........' cikin sauri Ayaan ya rufe ma jahan baki muryarsa cikin kuka yace "Jahan dan Allah kayi shiru, kada ka ƙara ja mana wani bala'en, ka bari muji da wanda muke ciki," shiru jahan yayi yana faman sakin Huci ji yake tamkar ya tashi ya shaƙe wuyan Haroon,
Hannu haroon yasa abaki irin mamakin nan yace "Wow wai meyasa kowa yake ma junaid irin wannan zazzafar soyayyar har haka? Gaskiya anyi mun nisa kaina na cikin duhu, farin jinin junaid yayi yawa ina kishi da hakan," ya faɗi yana dafe saitin zuciyarshi
. Ayaan yace "Ba son junaid muke ba, Ƙaunarsa muke yi saboda shi ɗin jinin mu ne,"
ta6e baki haroon yayi tare da ɗan jinjina kai yace "hmmmm ni wannan ba damuwata bace ba, abu biyu nake buƙata daga gare ku, inaso ku gamsar dani acikin daren nan, saboda inji irin naku salon, Sannan abu na biyu kuɗi nake so kimanin naira miliyan 50, in kun mun hakan zaku zauna lafiya,
Wani irin kallo suke bin shi dashi, Jahan yace "50m fa kace? Ina zamu same su? ka ruga da kasan iya salary ɗin mu, kuma ba tarawa muke yi ba, kashewa muke yi,"
haroon yace "Wannan ba damuwa ta bace, in kun so there's many way da zaku samu waɗannan kuɗin ! Yayan ku fa billionare ne! Mahaifiyarku ma billionaire ce, yadda take son ku ɗin nan, da zarar kun mata waya kunce kuna son Ƴan silalla zata turo maku,"
Murya a sanyaye Ayaan yace "mun ji zamu samu kuɗin mu baka amma dan Allah kada kace zaka aikata wannan abun damu, wlh bazamu iya ba, iya mu biyu ne kawai ba kowa muke bi ba, ka faɗi mashi jahan kada ya cutar da rayuwarmu bazamu iya jurewa ba........................"
bugun ƙopar da akayi ne ya hana Ayaan ƙarasa maganarsa, Cikin sauri Haroon yayi tsalle yashige bayan labule ya 6oye,
tashi su kayi atare suna faman sa hannu suna goge hawayen dake fuskarsu, sannan jahan yayi ƙoƙarin cewa "Wanene?
Sehrish dake tsaye ruƙe da tray a hannunta tace "Ni ce sehrish,"
Ayaan yace "Shigo ciki,"
Tura ƙopar tayi da tray ɗin hannunta mai ɗauke da food wermers tare da kayan tea ta shiga ciki, tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki ganin yadda fuskokinsu sukayi Jawur, idanunsu sun Canza launi alamar sunsha kuka,
Muryarta na rawa tace "Dama.............' bata ƙarasa ba Jahan ya katse ta da cewa "Ki barshi kawai, bazamu iya cin komai ba, ki koma da kayan,"
Shiru tayi aranta tana mai mamakin jin yadda Jahan ke mata magana cikin sanyin Murya, shi da kullum atsiwace yake mata magana,
Jinjina kai tayi tare da yin juyi zata futa karaf idonta suka sauka kan ƙafafun haroon dake 6oye bayan labule, tana ganinsu tagane cewa ƙafafunsa ne kamar na shebur haka suke, tsananin tsoro da mamaki ne suka kamata daker ta iya fuce wa daga ɗakin,
Kai har ta futa tana waiwayen ɗakin nasu, cikin mamaki take cewa "Meke faruwa ne? Naga fuskar Ayaan da jahan jawur alaman sunsha kuka, kuma menene yakai ƙafafun haroon ɗakin, hakan na nufin shine 6oye bayan labule? ko uban me yakaisa ɗakin hada su 6oyewa abayan labule, gaskiya akwai wani mummunan abu dake faruwa, Nashiga ukuna Allah yasa dae Haroon kada ya cutar dasu don nasan halinsa ba ƙaramin shaiɗani bane...........' ta ƙarasa zancan Zucin nata ayayin da take saukowa down daga saman stairs ɗin,
Kitchen ta shiga ta ajiye tray ɗin, sannan ta wuce bedroom ɗinta cike da zullumin abunda tagani,
A daren ranar haroon sai da ya tabbatar ya wulaƙantar da rayuwar Ayaan da jahan domin kuwa har sai da Ayaan Ya sume sannan ya ƙyalesu ya fuce yana ƙara jaddada masu maganar kuɗinsa, bayan ya fita jahan ya fashe da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali yana jijjiga jikin Ayaan dake sume aƙasa 😭
[9/15, 9:20 AM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
~🔥The father Of Soldiers🔥~
*Episode 25-26*
*Story & Written by*💫
*Hafsat Bature Moh'd* *BOSS LADY*
cikin sauri Jahan ya miƙe fitowa daga ɗakin yayi ya sauko down kai tsaye freezer ɗin dake a babban falon nasu ya tunkara, buɗewa yayi tare da zura hannu ya ɗauki robar ruwa mai sanyi, sannan ya juya ya koma ɗakin nasu, bayan ya buɗe robar ruwan ya ɗebo ya yayyafa masa a fuskarsa, wata irin doguwar ajiyar zuciya Ayaan ya saki tare da buɗe idonsa da sukayi jawur dasu yana kallon jahan dake zuƙunne agabansa, ganin Ayaan ya farka yasa jahan faman sauke ajiyar zuciya, yayin da hawaye ke sintiri a fuskarsa yana kallon ɗan uwan nasa,
Buɗe baki Ayaan yayi zaiyi magana, nan take wani irin yunƙurin amai yazo masa, a hanzarce ya zabura ya miƙe duk jikinsa ba ƙwari da gudun gaske ya faɗa toilet agaban basin ya tsaya yana faman kwarara aman, biyo sa jahan yayi cikin toilet ɗin tsayawa yayi kusa dashi ya sanya hannunsa yana ɗan bubbuga bayan Ayaan cikin muryar kuka yake cewa "Ayaan kayi haƙuri ina mai takaicin wannan ranar, naji natsani kaina Ayaan saboda nagaza ceton ka a hannun wancan fasiƙin, tabbas Haroon bai da Imani ko misƙala Zarratin kashe mu kawai yake son yi, ni ina kokwantan cewa Anya haroon JININ MU NE !!!!!!!!!!
dakyar Ayaan yasamu ya dakata da Aman hannunsa yasanya yana tarbo ruwan dake kwararowa daga jikin fanfon yana kuskure bakinsa, bayan ya kammala ya kashe Tap ɗin,
Sannan ya ɗago da shanyayyun idanuwansa ya kalli jahan yace "Haroon bai da Imani, Ƙazamin banza mugu macuci kuma Azzalumi wlh Allah bazai ta6a ƙyalesa ba sai ya bi mana haƙƙin mu, Jahan ni sam bana jin kunyar videon tsiraicin mu ya fita, babban abunda nake jimawa shine Mutuncin mahaifin mu da kuma na Babban yayanmu, jahan dole mu nemi mafita akan wannan Baƙin Shaiɗanin...........' ya ƙarasa maganar yana faman sakin Numfashi mai zafi, don tuni zazza6i yakama jikinsa,
Jahan yace "yanzu dare yayi Ayaan,Gobe sai musan Abunyi amma gaskiya bazan ƙara bari haroon ya ƙara kusantar ɗaya daga cikin mu ba, ko nawa yakeso muyi ƙoƙari mu biyasa shine kawai !!!
Sun jima suna jimamin abunda yafaru dasu kafin daga bisani suka sake sabon wanka don tsarkake jikinsu, bayan sun fito suka zura jallabiya ajikinsu, sai da Jahan ya canza musu bedsheet sannan suka kwanta, sun juma idonsu a buɗe kafin daga bisani bacci ya ɗauke su 😥
(Arayuwa kowa da irin tashi jarabtar, babu wanda Allah baya jarabta, kuma bawai don baya son mu bane a'a face don ya jaraba imanin mu)
**************Morning***********************
tun da sassafe sehrish ta farka daga baccin da ta koma na asuba, fuskar nan awashe yau zata fara shiga school, jiki na rawa ta faɗa toilet shaf-shaf tayi wanka ta fito jikinta ɗaure da farin towel,
Uniform ɗinta ta curo daga cikin wardrobe duka ukun, ta jera su saman gadonta tana tunanin wanne zata sanya, duk kala ɗaya ne amma na farkon riga ce da mini skirt ɗan dai-dai guiwa shafa su tayi tare da girgiza kai tace "Ba wannan zansa, basu son cewa ni musulma bace, taya zansa wannan gajeran skirt ɗin cinyoyi awaje kamar ƴar christiana," tayi maganar tana yatsina fuska, buɗe na biyun tayi riga ce tare da skirt pencil ba ƙaramin ɗame jikin mutun zaiyi ba,
"Kamar dae wadda zata club," ta faɗi tana ƴar dariya, na ƙarshen ta buɗe riga ce tare da dogon wando, duka uniform ɗin suna da Top wadda ake sanyawa daga sama bayan an zura rigar sai kuma guntun hijab wanda daƙyar ya dire kafaɗa,
"Kwarama wannan zasu fi dacewa dani," ta faɗi tare da hanzarin komawa gaban mirror sai da ta kammala shafe jikinta da body oil tabi ta feshe shi da turare ko'ina yakama ƙamshi sannan ta koma gaban gadon tana zura uniform ɗinta, lokacin da ta kammala zura kayan duka ta kalli kanta a mirror sai da taji gabanta ya faɗi saboda yadda kayan suka hau jikinta su kayi mata wani irin kyau,
Rigar white colour ce wandon kuma Maroon colour launi ɗaya da Top ɗinta, jujjuyawa tayi agaban mirror ɗin sannan ta sakarwa kanta murmushi, sai da tagama shiriritar sannan ta ɗauko takalmanta,
tsayawa tayi tana ƙoƙarin zura safa a ƙafarta, ta aza ƙafar asaman kujerar gaban mirror tana gyaggyara safar, Azmee ta shigo ɗakin da sallama tana yin arba da sehrish ta soma washe baki tana cewa La!la! Irin wannan kyan haka, Masha Allah gaskiya uniform ɗin nan ba ƙaramin kyau su kayi maki ba Sehrish sai kace donke akayi su,"
Murmushi kawai Sehrish ke saki tana ɗan kallonta a lokacin ta kammala sa safar da takalmin a ƙafar daman ta, saura ta hagun zata sanya mawa,
"aunty azmee ina kwana fatan kun tashi lafiya," ta faɗi tana aza ɗayar ƙafar saman kujerar ,
Azmee tace "Lafiya lou Alhamdulillah, naga sai faman shiri kike yi, maganar breakfast ba?
"Aunty azmee lokaci zai ƙure ne, idan nadawo zanci," ta faɗi tana zura safa a ƙafar hagunta,
Azmee tace "Kin ta6a ganin inda akaje ɗaukar karatu da yunwa? gaskiya bazaiyiyu ba, akwai sauran miyar jiya na ɗumamata saina haɗa maki da dankalin dana soya kici, bari na kawo maki"
ta fadi tare da juyawa ta fuce cikin sauri bayan wasu mintina sai gata ta dawo hannunta ɗauke da plate, soyayyan dankalin ne aciki tare da jar miya, ajiye mata tayi asaman side drawer ɗinta, sannan ta koma ta ɗauko mata kayan tea don ta haɗa tasha,
"Nagade sosai Aunty azmee da kulawarki," sehrish ta faɗi a lokacin ta baro gaban mirror ɗin, wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana cin breakfast ɗinta, yayin da azmee ta fuce tana cewa "ki hanzarta ki shirya kafin Junaid ya fito,"
ta amsa mata da "Toh,"
A can ciki kuwa tuni junaid ya farka saboda ya tashi da wuri ya sanya alerm a wayarsa, shaf shaf yayi wanka ya fito ya kimtsa cikin pakistani riga da wando farare amma anyi masu ado da stone launi daban daban ajikinsu, ba ƙaramin kyau yayi ba, bin jikinsa yayi ya feshe shi da Spice bomb, sannan ya gyara sumar kanshi, gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa yace "Nima kaina nasan cewa Ni kyakkyawa ne, Son kowa ƙin wadda ta rasa, Allah kaɗai yasan ƴan matan da suke crushing akaina," ya faɗi yana tsumbula yatsansa na tsakiya a dimple ɗin fuskarsa daya Lotsa,
daga bisani ya ɗauki key ɗin motar shi tare da wayarsa ya fito daga ɗakin, cikin hanzari ya sauko down babu kowa saboda duk basu tashi daga bacci ba, wuri ya samu asaman Royal sofa ɗin dake a falon mai mazaunin mutun 3 ya zauna yana jiran fitowar sehrish, wayarsa ya shiga daddanawa, message ya tura mata cikin wayarta, na cewa yana jiranta ta fito,
a lokacin ta kammala kur6ar tea ɗin data haɗa, message ɗin junaid ya shigo mata karantawa tayi "Am waiting for u reesh,' murmushi ta saki cikin sauri ta miƙe tare da ɗaukar guntun hijabin ta zura ajikinta, sannan ta ɗauki School bag ɗinta ta ɗan sagala hannun jakar a kafaɗarta, sai da ta ɗauki wayarta sannan ta fito daga ɗakin, kai tsaye ta nufi falon tunkan ta ƙarasa junaid ke kallonta baki asake,
Ganin hakan yasa ta sakin dariya, ƙarasa wa tayi wurinsa tare da tsaya agabansa ta ruƙe waist ɗinta tace "Nayi kyau,"?
Cikin mamaki yace "Reesh irin wannan kyau haka? Anya karfa malaman makarantar su rikice? innalallahi," ya faɗi tare da aza hannunsa akansa,
ɗan bubbuga ƙafarta tayi tare da cewa "ka tashi mu tafi junaid har 8:30 fa tayi,"
Mamaki tayi ganin yarda yake kallonta hannunsa yakai tare da cafko wutsiyar gashinta da ta sauko har tsakiyar bayanta yace "Sehrish jibi fa? Babu wani dogon hijabin ne sai wannan? Taya zaki bar gashin nan haka bainan nasi? Kowa ya kalla?
Sai lokacin ma ta ankara sam ta manta bata sanya ribom ba ta ɗaure gashin, dafe kanta tayi tare da cewa "kash ! Wlh mantawa nayi ban ɗaure gashin ba, kuma fa in na sanya ribbom gyaran gashin da akayimun zai 6ace,"
tashi junaid yayi tare da ruƙo hannunta yace "Mu shiga cikin ɗakin na ɗaure maki shi, nasan yarda zanyi batare dana 6ata maki gyaran gashin ba,"
bin shi tayi suka wuce ɗakin nata, duk wannan abun dake faruwa akan Idon haroon sam basu ankara dashi ba, tun fitowar sehrish yake tsaye ruƙe da qugu daga shi sai gajeran wando fuskar nan a murtuke kamar ta shanu, jinjina kansa yayi tare da cewa "Wato ni waccen ƴar shilan zata raina ma wayau, in na ta6a jikinta taita ƙyamata amma gashi junaid har wani ruƙe hannunta yake yi, hada su shiga ɗaki ko uban mi zasu yi aciki,"? Ya tambayi kansa can kuma ya saki wani irin shu'umin murmushi yace "Wannan babbar dama ce agare ni ! Zanyi amfani da ita wurin gur6ata sunanta acikin gidan nan, Zan ƙala mata sharrin cewa ta koyama junaid lalata, kuma na kama su hannu dumu-dumu, " fashe wa yayi da wannan mahaukaciyar dariyar tasa kafin ya juya ya nufi hanyar komawa dakinsa yana cewa "Yarinya kin gama yawo acikin gidan nan, sai kin gane baki da wayau !," yana tafiya yana sambatu har ya shiga ɗakinsa,
Junaid kuwa bayan sun shiga ɗakin sehrish ta cire hijabin nata agaban mirror suka tsaya, ribbom ɗinta dake ajiye saman mirror ta ɗauko tare da miƙa masa, hannu yasa ya kar6a sannan yashiga kiciniyar tattara gashin kanta donya ɗaure mata,
Murmushi ta dunga saki saboda jinsa yadda junaid ke faman nishi aranta tace"junaid ba ƙaramin rago bane, yanzu gashin kan nawa ma yagaza ɗaure wa, shi dai sai kace ba namiji ba, sam babu wannan karsashin na maza atattare dashi......
Muryarshi ce ta katse ta da cewa "Gulma ta kike ko"? Cikin sauri tace "a'a ni na isa,"
Murmushi kawai yayi, daƙyar yasa mu ya tattara sumar kan sehrish ya ruba ta biyu ya haɗa ya ɗaure," sannan ta mayar da hijabin nata,
"Gaskiya junaid ka iya dabara, gashi nan yanzu babu gashin bai leƙo ba,"
ruƙo hannunta yayi tare da cewa "Mu tafi ko," cikin sauri ta bishi suka fito da hanzari suka fuce,
Buɗe mata motar yayi ta shige sannan shima ya zagaya yashiga ciki, yana a driver seat ita kuma tana a gefensa, tayar da motar yayi sannan suka fuce daga gidan,
A natse yake yin driving ɗin sehrish na satar kallon shi tace acikin ranta "koya akai ya iya driving yanzu yadda yake shagwa6a66an nan karfa wata rana ya tunkari babban mota damu kwatsam ta rotse damu duk mu mutu.....'
"Matsalar ɗan nigeria kenan, duk wani bala'e shike fara kira ma kansa, yanzu ko menene na wannan tunanin"? Cikin mamaki tace "Acikin Zuciya fa nayi maganar" ta faɗi tana kallonsa
Junaid yace "Eh nasani, ae muddin zaki yi gulmata acikin zuciyarki to fa saina ji don haka ki kiyaye," ya faɗi yayin da yake shan kwana dasu,
Shiru tayi tun daga lokacin bata sake maganarsa ba acikin zuciyarta amma fa tayi mamaki don ita tasan cewa acikin zuciyarta tayi maganar amma gashi yaji,"
Tunkan su ƙarasa sehrish ke hangen katafariyar makarantar motoci sai shiga suke yi ciki suna sauke ɗalibai, tsayawa zayyana kyawun makarantar 6ata baki ne, gashi bani da isasshen lokacin yin wannan bayanin 😆
A parking space dinsu junaid ya sauke sehrish tare da cewa mun iso, atare suka fito gaban sehrish ne ya faɗi ganin tsala-tsalan ƴan mata young ladies irinta sun ɗau wanka, ƴa'ƴan masu kuɗi wayayyun gaske tun daga shigarsu zai tabbatar maka da cewa An sangarta su da yawa, saboda majority ɗin matan Mini skirt ne ajikinsa sai santala santalan cinyoyi awaye, kuma mafi yawancinsu babu hijab ajikinsu gyaran gashi ne kawai iri-iri, wasu kuma skirt ɗin nan ne ajikinsu waton pencil yabi shafe ɗin jikinsu, iya guiwar ƙafarsu ya tsaya,
waro ido waje sehrish tayi tana cewa "kai!kai!!kai!!! Junaid mu koma gida, gaskiya bazan iya zama a school ɗin nan ba, wannan sunfi ƙarfi na Allah,"
Fashewa da dariya junaid yayi ganin yarda sehrish duk ta dabarbar ce, hannunta na kerma ta ruƙo rigarsa tana 6oyewa abayansa tana faman yi masa sambatun su koma gida, abu kamar wasa har hankalin wasu students ɗin suka dawo kansu ganin yadda Yarinyar ta ƙanƙame jikin dan uwan nata hada su hawaye a fuskarta,
Shima kansa junaid sehrish ta rikita shi hankali atashe yake cewa "dan Allah sehrish ki daina, karki bani kunya mana kalli yarda hankalinsu yafara dawowa kan mu innalallahi, yanzu da ace school bus ce ta kawo ki bansan ya zaki ƙare ba,"
"Junaid nidai mu tafi gida, Allah bazan zauna anan ba" ta faɗi tana shesshekar kuka 😆
dariya kamar zata kashe junaid ba shi kaɗae ba hada wasu daga cikin ɗaliban dake a wajen,
Wasu gungun ƴan mata ne suka ƙaraso kusa dasu, ɗaya daga cikinsu tana cewa " Wow friends kalli wani handsome guy nan ya burgeni sosai,"
Jin hakan yasa sehrish dakatawa da kukan tana ɗan kallonsu kai kana ganinsu kaga jarababbu,
Murmushi ta gefenta ta saki tare da cewa "Kamar nasan shi a tiktok fa, zanso ko na tuna sunan shi daga gani cele ne shi sosai,"
Sai faman surutu suke yi suna yaba kyan junaid,
"Kai nifa bazan iya jure ba, sai nayi ma shi magana," ɗaya daga cikinsu ta faɗi atare suka iso dab da su junaid da sehrish, su uku ne matan
junaid yace "Sannun ku fa," suka amsa mashi da "Yawwa," sannan ɗaya daga cikinsu tace "Kamar na sanka,"ta faɗi cikin rangwaɗa
Junaid yace " Sunanki Parveena," zaro ido su kayi jin yadda junaid ya faɗi sunan ɗaya daga cikinsu kai tsaye, Nuna ɗayar yayi ta tsakiyarsu yace "ke kuma Sunanki Amrish ta ƙarshen kuma sunanki Naja'at," ya faɗi da murmushi a fuskarshi, su kuwa sai faman yarfa hannu suke yi suna kallon shi cikin mamaki jin yadda ya zayyana sunayen su gaba ɗaya,
Cikin mamaki wadda ya kira da Amrish tace "Dan Allah ya akai kasan sunayen mu"?
Ta tambaya cike da zumuɗin son jin amsa,
Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan sehrish wadda ke ruƙe da rigar junaid taɗan la6e abayansa,
Junaid yaci gaba da cewa "Ban son ku ba nima kawai abunda nasa ni ke Amrish kece kullum kike isarmu da surutu a group, ke kuma parveena baki da aikin yi sai turo hotunan Chacolate iri-iri, Sannan ke kuma Naja'at kinfi kowa iya turo hoton abinci duk in zaki ci sai kin turo mana hotansa,"
Gaba ɗayansu suka saka ihu da sowa har suna haɗa baki wurin cewa "Wai dama kaine ! junaid romeo ko?
Murmushi junaid ya saki tare da cewa "Ni ne, bamu ta6a haduwa ba amma muna yin chat sosai ta whatsapp a group, na ruƙe fuskar kowannan ku da sunayen ku,".
Ba ƙaramin farin ciki su kayi ba, Amrish ta nuna sehrish tare da cewa "wannan fa? sister ɗinka ce"?
Junaid yace "Eh, younger sis ɗina ce, new comer ce yau tafara zuwa,"
Parveena tace "No wonder, that's why naga tana hiding kanta abayanka, amma kamar batason mutane ko? Naga ko son kallon mu bata yi,"
Junaid yace "No just kin gane shagwa6a6iya ce, Last born ɗin mu ce bata saba shiga cikin mutane ba kullum tana a gida, so aduk lokacin da aka fito da ita cikin mutane tana ɗan razana,"
tunda ya soma jawabi sehrish ke kallon shi baki asake, jin irin ƙaryar daya zuƙa mata nafarko yace ƙanwarsa ce ita, kuma ya laƙwafa mata sharrin cewa tana shagwa6a bayan shine shagwa6a66e, jinjina kanta kawai takeyi,
Amrish tace "Ayyah na tausaya mata but she's so cute kuma ta fito daga babban gida yakama ace tana shiga mutane,"
ta6e baki sehrish tayi tana ɗan kallonsu, 6an6aro hannunta junaid yayi daga jikin rigar shi, sannan ya miƙa ma Amrish yace "Gata nan dan Allah amana na baki ita, ki tafi da ita ba ta son komai ba da yake ita ɗin rainon kakarmu ce, sai ahankali," 😆
Murmushi Amrish ta saki tare da kar6ar hannun Sehrish tace"aikuwa na gode sosai da wannan kyautar, kuma zan ruƙe amana,"
Cikin raha sukayi sallama da Junaid yayin da suka shiga ciki da Sehrish duk ta zama tamkar mutun-mutumi , suna tafiya tana waiwayon junaid shima kansa sam yagaza tafiya kallonta kawai yake yi, sai yaji duk kewarta ta kama shi daker ya ɗaga mata hannu tare da yi mata bye-bye,'
Sannan ya buɗe motarsa ya shige, yayi mata key sannan yaja ta da gudu yabar makarantar, sai da yayi nisa da driving ɗin sannan yayi parking ɗin motar agefen titi yana shesshekar kuka yana cewa "ko na minti ɗaya bana son rabuwa dake sehrish kewarki nake yi," yayi maganar tare da curo handkerchief ɗinsa daga front pocker ɗin rigarsa yana faman share hawayensa, ya jima acikin motar duk kasala ta dabaibaye shi daker ya iya tayar da motar yaci gaba da driving ya miƙi hanyar komawa gida 😥
Parveena da Naja'at Class ɗinsu suka wuce, Amrish ce tayi ɗawainiya da Sehrish ta raka ta har Admin ɗinsu wurin principal ɗin makarantar, maca ce hamshakiyar gaske tun da taji sunan sehrish tagane cewa daga Family ɗin Salahuddeen Hussein take, hakan yasa ta sake mata sosai har tana jan ta da fira, daga bisa ni taba ma Sehrish Sunan Class ɗin da zata zauna, Science department ne kuma an ci sa'a Class ɗinsu ɗaya da Amrish SS1 science C, Madaddalar ƴan iska ba 😂
(Nima Science C nayi a school ɗinmu wlh basa jin magana, dama anyi ittiƙafi babu wanda yakai ƴan C rashin jin magana)
Hannunta na ruƙe dana Sehrish suka tunkari benen da zai sadaka da Upstairs ɗin makarantar, anan Classes ɗin suke akwai kuma na down,
sehrish dae sai bin ko'ina take da kallo makarantar ta haɗu kamar ba wurin ɗaukar karatu ba saboda tsaruwarta ga wuraren shaqatawa,
shiga Class ɗin sukayi mutun goma ne a cikinsa a ƙa'ida kowane class mutun 12 ne kacal acikinsa maza 6 mata 6, idan aka haɗa da Sehrish da Amrish 12 kenan student ɗin cikin sa,
gaba ɗaya Ido yadawo kan Sehrish kowa da irin kallon da yake yi mata, Mazan class din kuwa tuni sun soma sakin baki suna cewa "Wow so beautiful, so hot, She looks so sexy,"
Gabanta ne ya faɗi kowa da irin abunda yake cewa, Matan kuwa wani irin kallo suke binta dashi irin kallon hadarin kajin nan,' ƙara ƙanƙame school bag ɗinta tayi daga tsayen da take,
Amrish ce ta soma magana" Hello Class we ave a new comer today, She's from awesome family, i hope zaku bata hankalin ku domin tayi mana Introducing kanta,"
ta ƙarasa maganar tare da kallon Sehrish tace "Pls introduce ur self,"
ɗan gyaran murya Sehrish tayi sannan ta soma cewa "am....Sehrish Salahuddeen Hussein by name, 17years old.... Alhamdulillah I love the Way i am,"
Wannan bayanin na sehrish yasa su gaba ɗayansu Clapping hands ɗinsu suna tafa mata, musamman ƙarshen maganarta ta ƙayatar dasu,
Sun mata kyakkyawar tarba duk da akwai waɗanda tunda ta shigo ma basu ɗago da kansu ba daga saman desk sun kife shi kamar masu bacci,
Kowane seat mutun ɗaya ne, Amrish ta sama ma Sehrish gurbi a Middle Roll na Class ɗin 0a Second seat Amrish kuma na'a First seat, sai da tafara neman alfarma wurin asalin mai seat ɗin na sehrish akan tabar mata, kuma cikin sa'a ta amince shine har tasamu gurbi abayanta, komai yazo mata cikin sauƙi kuma ba ƙaramin daɗi taji ba na haɗuwarta da AMRISH 💃
******************AUNTY BABBA***********************
tun da sassafe suna kwance wayarta ta soma ringing a firgice ta farka jikinta na sanye da kayan bacci brown colour, leƙa fuskar Ishaq tayi taga koya buɗe ido samun shi tayi sai faman Sharar baccin sa yake, don haka a hankali ta lalla6a ta sauko daga saman gadon cikin sanɗa,
Bayan ta sauko ta ɗauki wayarta data ajiye saman side drawer ɗin shi, sannan ta lalla6a ta shige cikin toilet ta duba mai kiran nata mutumin da tayi tsammani shi ta gani wato*BABA ALAMU* murmushi ta saki cikin sauri ta ɗaga kiran ta kara a kunnanta tun kafin tayi magana baba alamu yace "Na faso gari fa, tun jiya da daddare inata kiran layin ki baya shiga,"
Aunty babba tace "wlh bansan ka kira ba, dayake nabar wayar acikin ɗakina sai da asuba na ɗauko ta, tun jiya nima nake jiran kiran naka mutumina,"
Dariya baba Alamu yayi sannan yace "Ae ke baki sani ba, jiya muna dira gari na kwaso rugwagwar motata na shigo unguwarku don in sanar maki kawai sai naga waɗannan Masu fuskar shanayen tsaitsaye ruƙe da bindiga ae ba arziƙi naja motata na koma,"
Fashewa da dariya aunty babba tayi tace"Ae mijina ne yadawo jiya shiyasa kaga sojoji nan,"
Baba Alamu yace "Oh to ashe angon ne yadawo, yanzu dae ya za'ayi wurin fitar da yaran kinsan fa wlh shegen tsoran Soja nake, don kwanaki sun ta6a tarar mu a hanya suka sanya mu tsallen kwaɗi a tsakiyar titi da rana tsaka,"
Aunty babba tace "Ae basu da Imani, musamman in suka ji su acikin kakin nan sai su dunga ɗaukar kansu tamkar wasu dodonni, yanzu abunda za'ayi kana ina ne?
Baba alamu yace "yanzu haka na fito da mota ta ina kan hanyar zuwa unguwarku amma fa bazan shigo ciki ba sai dai ki san yarda zakiyi a fito da yaran,
Aunty babba tace "Shikenan ka jira ni, zaka ga kirana yanzun nan bada jimawa ba,".
bayan ta kammala maganar ta kashe wayar sannan ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sanɗa ta lalla6a ta fuce daga ɗakin,
Kai tsaye ta nufi ɗakin hafsat ta shiga, tsayawa tayi tana kallonsu hussana da jahad dake ta faman sharar bacci baje saman gadon hafsat, yayin da ita kuma hafsat ɗin ke kwance saman doguwar kujerar ɗakin tana bacci, da alama dukansu daga tashin asuba suka koma bacci,
jinjina kanta tayi sannan ta ƙarasa dab da hafsat ta ɗansa hannu ta bubbuga ƙafarta, a dan firgice hafsat tafarka tana cewa "wanene,"
Murya ƙasa ƙasa aunty babba tace "ke ki taso inason magana dake,"
Bin ta da kallo hafsat tayi tana yamutsa fuska Alamar bacci bai ishe ta ba, daker tasa hannunta ta janye bargon data lullu6e rabin jikinta da tashi sannan ta miƙe tsaye tabi bayan aunty babba, suka fito daga ƙopar ɗakin suna fuskarta junansu hafsat tace "Meya faru mommy naga kin tashe ni ina tsaka da bacci na? Aunty babba tace "Mutumin fa wanda zai kai su hussana da jahad gidan marayu ya ƙaraso....,"
jin hakan yasa hafsat canza fuska tuni tace "Mommy yanzu dole sai kin raba ni da yaran nan? Wai me suka tsare maki ne? Dan Allah mommy kibarsu suyi rayuwarsu cikin salama, sun sha wahala fa baki tausayin su?
tsoki Aunty babba ta buga tuni ta tamke fuska tace "Tausayin Uban me? menene alaƙata dasu? ke bana son zancen banza mun riga da mun gama magana dake don haka ! Ke nake so ki fidda yaran nan daga cikin gidan nan!! In yaso zan baki numbarsa in kin fitar dasu acikin motarki sai ki kira shi ki bashi su ya tafi dasu can Orphanage home ɗin,"
Murya asanyaye hafsat tace"shikenan mommy amma ina so ki sani haƙƙinsu ba zai ta6a barin mu ba! Sai Allah ya saka musu duk wani cin zalinsu da mu kayi,!!!!!!!!!!!!!!!! tana faɗin hakan ta juya tare da shigewa cikin ɗakin,
wani irin matashin murmushi aunty babba tasa ki tare da cewa "Komai zaki ce ki ce, nidae in dae burina zai cika ba abunda bazan iya aikatawa ba ehen,"
acan ciki kuwa bayan hafsat ta shiga wuri tasamu gefen gadon ta zauna maimakon ta tashe su sai kawai tafashe da kuka mai cin rai
Sautin kukanta ne ya farkar da jahad a firgice ta tashi zaune hankali atashe take cewa "Subhanallahi Aunty hafsat meya faru naga kina kuka? Meya same ki? jahad ta tambaya fuskarta cike da nuna alamun damuwa,
Ci gaba da kukan hafsat tayi sam ta gaza cewa komai jikinta har wani jijjiga yake yi, jahad ta kuma cewa "dan Allah sister hafsat ki daina kuka, ban ta6a tunanin zanga wannan ranar ba, idan wani abu ke damunki, zan taya ki addu'a Allah ya yaye maki
jin wannan maganar ta jahad yasa hafsat ƙara sautin kukan nata, ɗagowa tayi ta kalli jahad idanunta jawur suna fitar da zafafan hawaye tace"Jahad ba saboda kaina nake wannan kukan ba, face saboda ku ! Ina tausayinku, Nasaba daku zan iya cewa akanku nafara jin tausayin wani ɗan adam aduniyar nan !!
tun da jahad taji hakan gabanta ya faɗi Rasssss !! Duk da hafsat bata fito fili ta faɗa mata kai tsaye abunda yasa ta kuka ba,
miƙewa hafsat tayi tana faman sharar hawaye tace "Ki tashi hussana ku shirya inaso zan fita daku,"
Jiki a mace jahad tace "Toh," cikin sauri hafsat ta fuce daga ɗakin,
Jahad kuwa jikinta har kerma yakeyi saboda tsoran inda hafsat zata kaisu, daker tasamu hussana ta farka daga bacci sannan ta sanar da ita cewa ta tashi su shirya Sister hafsat zata fita dasu,
Batare da sunyi wanka ba, tsaka tsami kawai su kayi acikin toilet sannan suka fito suka shirya, jahad ta zumbula doguwar riga Orange colour ta yafa mayafi launin fari akanta, ita kuma Hussana riga ce Square neck green colour, sai Skirt Ethnic maxi ta sanya ajikinta yana da dan faɗi ya bude da ƴar bazarsa, ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, Mayafi tasamu launin skirt ɗin black colour mai ɗigon fari² ajikinsa, tayi rolling ɗinsa tamkar yadda Jahad tayi,
Kallon hussana kawai jahad keyi kallon tausayi don ita ranta yana bata cewa lokacin barinsu gidan ne yayi, yanzu kuma zasu fuskanci wata ƙaddarar !!!
lokacin da suka fito daga ɗakin hannunsu ruƙe dana juna, Aunty babba na'a falon sai faman zagaye zagaye take yi, tana ganinsu ta nufo su cikin sauri gudun kada ishaq ya farka daga bacci ya fito yagansu,
Tana ƙaraso wa inda suke tace "Ku biyo ni," sannan ta juya ta miƙi hanyar fita daga falon, bin bayanta su jahad su kayi gabansu na faɗuwa, suna fitowa daga falon a harabar gidan tuni hafsat ta fito da motarta, buɗe musu motar aunty babba tayi tana cewa "Maza ku shiga ciki, ku jira hafsat yanzu zata zo, Allah ya kiyaye hanya," ta faɗi tana faman tiƙar dariya sannan ta rufe musu motar,
Kusan minti goma sha biyar suna zaune jigum cikin motar gaba ɗayansu babu mai magana duk jikinsu yayi mugun sanyi ganin yarda Aunty babba ke faman yi musu dariya, tun daga haka suka gane cewa ba lafiya," 😳😳😳
_wannan na jiya ne da banyi ba, da Anjima zan saki next page insha Allah kuma shine, Ga masu son cigaba da karanta Littafin Abban Sojoji su tuntu6e ni ta wannan numbar (08103884440)
[9/16, 2:19 PM] 💋BOSS LADY💋: 💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋
The father Of Soldiers Story & Written by_*Boss Bature*
page 27
Fitowa hafsat tayi hannunta janye da trolley ba komai bane aciki ba fa ce kayansu jahad, ɗayan hannun nata kuma na ruƙe da basket na breakfast dinsu data haɗo masu, 😥😥😥
Tana isowa ta buɗe boot ɗin motar ta saka trolley ɗin sannan ta rufe, duk aunty babba na tsaye ruƙe da qugu tana sakin murmushi,
Bude back seat ɗin hafsat tayi inda su jahad ke zaune ta miƙa musu basket ɗin, hannu na kerma jahad ta kar6a,
Sannan ta rufe musu murfin motar, har tasa hannu zata buɗe gaban motar ta shiga ta juyo ta kalli aunty babba idonta jawur tace "Baki bani numbar mutumin ba, wanda kika ce zai kaisu Orphanage home ɗin,"
cikin sauri aunty babba ta ɗago wayarta dake hannunta, tashiga contact numbar baba alamu ta lalubo, sannan ta shiga karanto ma hafsat ita kuma tana rubutawa a wayarta, bayan ta kammala sa numbar tashige cikin motar kafin ta rufo ƙopar ta aza idonta akan aunty babba tace "Ina fata kin ji daɗi mommy, yau hussana da jahad zasu bar miki gidanki, sai ki zuba ruwa a ƙasa kisha don murna,"
tana faɗin hakan ta datse motar tare dayi mata key, ta juya sitiyarin motar tayi baya² da ita sannan ta karya kwana ta juyar da ita direct ta nufi gate ɗin gidan ta fuce da motar aguje,
Lumshe ido Aunty babba tayi afili tace "Alhamdulillah na kawar da wannan matsalar, yanzu abunda ya rage mun shine zuwa wurin boka domin gudanar da target ɗina na gaba," tana faɗin hakan ta nufi cikin gidan fuskarta washe yau ta rabu da alaƙaƙai,
sai da ta ɗan yi nisa da motar ta fito bakin titi sannan ta dakatar da driving ɗin, wayarta ta ɗauko dake ajiye agefe, Lambar baba alamu ta danna ma kira, bayan ya ɗaga ta sanar dashi kwatancen inda motarta take,
bayan ta katse kiran ta ambaci sunan Jahad da Hussana, atare suka amsa mata da "Na'am," juyo taɗanyi ta kallesu da idanunta waɗanda suka canza launi, cikin sanyin Murya tace"kun san inda za'a kai ku"?
Har suna haɗa baki wurin cewa "A'a,"
Shiru taɗanyi kafin taci gaba da cewa "Gidan marayu !!!!!!!'
Zaro ido su kayi gaba ɗayansu hankali atashe suna kallonta, hussana da tagaza jurewa tuni ta soma kuka tana cewa "Yaya Omar fa? dan Allah kar akaimu can ku bari yaya Omar yazo ya ɗauke mu mana, ni bana son mu rabu dashi,"
Murmushin takaici jahad ta saki tare da cewa "Aunty hafsat ba wai gidan marayun ke bama so ba, kawai ni so nake naji da sanin yaya Omar za'a kaimu can"?
girgixa kai hafsat tayi tare da cewa "Jahad bada sanin shi ba, kuma nima ba da son raina ba na amince da hakan, amma ina so ku sani can shine zaifi muku zama cikin salama, saboda shi kan shi ya Omar ya manta daku tun da gashi ko kira a waya yadaina yi, babu tabbacin cewa ma yana ƙasar tunda dama banan yake zaune ba, don haka ku Cire tsammani da shi, kawai ku rungumi ƙaddara, kuyi haƙuri³," har kusan sau uku tana maimaita masu kalmar suyi haƙuri,.
Hussana dae bata dakata da kukan da takeyi ba sai ma sautin da ta ƙara, jahad ta jinjina kai idonta acikin na hafsat tace "Shikenan Aunty hafsat, kada ki sa damuwa aranki, mu kan mu bamu ta6a tunanin zamu kawo wannan lokacin araye ba, amma gashi mun kawo da ran mu da lafiyar mu, wannan alama ce dake nuni da cewa Allah yana sane damu !!! Kuma shine zai kare mu aduk inda muka kasance a faɗin duniyar nan! mun gode sosai da kulawar da kika nuna mana," daga haka jahad tayi shiru idonta na zubar da hawaye hussana kawai take kallo wadda ke ta faman shessheƙar kuka,
Jikin hafsat ya gama yin sanyi sam tagaza yin kwakkwaran motsi, suna cikin wannan Yanayin Motar baba Alamu ta ƙaraso dab da tasu, wata tsohuwar jeep ce ta ragwaggwa6e ta fita hayyacinta, kai wannan motar ko kyauta aka bani ita wlh na kwammace in ƙaraci yawona da ƙafafuwana saboda muninta, gaba ɗaya fa glass ɗin motar ya faffashe kana hangen cikin motar, babban abunda zai ɗaure maka kai shine yadda yakeyi wurin tayar da motar domin kuwa babu wurin zura mukulli atada mota, sai dae wasu wayoyi gasunan birjik su yake haɗawa sannan ya tashi motar,
hankaɗa murfin motar yayi sannan ya fito, wani irin Matsolan mutun ne ramamme sai uban ƙasusuwa gashi baƙi wulik kana ganinsa kaga cikakken ɗan duniya, fuskarsa yana da wasu irin tsaguna waɗanda zasu tabbatar maka da cewa Magobiri ne, yadda kasan kwarya haka tsagunan fuskarsa suke, yana da kwalakwalan idanuwa kuma jawur dasu, ga wani irin fankacecan hanci harya so yafi ƙarfin fuskarshi, haƙoran bakinsa kuwa sunyi jawur dasu saboda Cin goro, a shekaru zai iya zarce shekara hamsin, jikinsa na sanye da wani tsohon yadi wanda yausha rabon da yaji dutsen guga tun 1960 😔
fitowa hafsat tayi ita kanta da ta ga mutumin sai da gabanta ya faɗi saboda muninsa, shi kuwa washe baki ya shiga yi yana cewa "Yarinya ta girma ! komai yaji dai² nasan baki sanni ba, amma ita jatumarki kullum tana bani labarinki,"
ɗaure fuska hafsat tayi zuciyarta har wani tashi take yi, hannunta na kerma ta buɗe masu hussana motar, fito wa Su kayi atare da jahad duk jikinsu ya gama mutuwa, musamman da su kayi arba da baba alamu, sai duk suka firgita jiki na kerma Hussana ta ƙanƙame jahad saboda tsoro,
Buɗe boot ɗin motar hafsat tayi tare da curo masu trolley ɗin kayansu ta miƙa ma jahad ta kar6a, sannan ta ɗauko masu food basket ɗinsu da suka manta, ta miƙa ma hussana daker ta kar6a,
Cikin kuka Hussana ke cewa "Aunty hafsat dan Allah kada ki tafi kibarmu a hannun wannan mutumin !!"
rigima sosai hussana ta sanya, hafsat kuwa tsananin tausayinsu duk ya kamata, purse ɗinta ta ɗauko cikin motar, sannan ta ƙirgo kuɗi kusan dubu 30 ta miƙa ma Jahad tace "Ki ruƙe wannan a wurinki nasan za suyi maki amfani, ni zan wuce,"
Bin ta da kallo kawai jahad ke yi idonta na zubar da hawaye duk yadda hussana ke faman rusa kuka tana rurruƙe mayafin jikin hafsat amma hakan bai hanata tafiya ba, cikin sauri ta shige motarta, taja ta da gudun gaske tabar wurin,
Mayar da idonsu su kayi kan Baba alamu wanda ke ta faman bin jikinsu da kallo yana sakin wani irin shu'umin murmushi,
hannu yasa ya buɗe masu motar yace "Maza ku shiga ciki,"
Amsar trolley ɗin yayi ya bude boot ɗin motar ya wurgar dashi ciki sannan ya datse shi, shiga ciki su kayi gabansu na faɗuwa zuciyarsu nayin wani irin bugu mai sauti,
dawowa yayi ya shige gidan gaba sannan ya jona wayoyin nan take motar tayi wata irin ƙara ƙirrrrrrrr bakin hayaƙi ya soma fita ta baya, sannan yaja motar da gudun gaske ya miƙi hanya dasu,
******************
tun jahad tana ganin gine-gine da gifcin mutane har ta soma ganin dajijjika, hakan yasa hankalin jahad ya tashi ganin ya fidda su cikin gari bayan cewa Hafsat tayi zai kai su gidan marayu, zazzare ido jahad ta soma yi gabanta na wani irin bugu, juyawa tayi don taga wane hali hussana ke ciki, abun mamaki saita samu hussana sai bacci take shara hannunta ƙanƙame da kwandon abincin su,
Kai tsaye baba alamu ya kutsa dasu cikin dajin mai uban bishiyoyi da ciyayi ba gifcin mutun acikinsa sai dabbobi dake shawagi,
Murya na rawa jahad tace "Bawan Allah ina zaka kaimu ne !? Ba gidan marayu akace zaka kaimu ba,"? Ta tambaya idonta cike taf da hawaye cikin tsananin tsoro,
fashewa da dariya baba alamu yayi sannan yace "A sanin ku ba, amma ni ba gidan marayu nayi da ita hajiyar zan kaiku ba, ce mun tayi in zubar mata daku acikin daji,"
Cikin kuka jahad tace "Dan Allah kada ka cutar damu , ka sauke mu kawai anan,"
Baba alamu yace "Yarinya kenan ki daina wannan tunanin, ae tunda idanuwa na suka yi arba da surar jikinku na kwaɗaitu da son kasancewa tare daku, don haka zan kai ku gidan gonata dake acikin dajin nan don na runƙa rage zafi daku," ya ƙarasa maganar da wata irin shaƙiyar dariya,
Jahad kuwa neman hanyar fita take yi daga cikin motar amma ta gaza buɗe murfin motar saboda ya datse shi sosai, duk wannan tashin hankalin da ake ciki hussana bata sani ba, saboda baccin da takeyi,
jahad bata haƙura da ƴunƙurin buɗe motar ba sai da ta sanya iya ƙarfinta na ƙarshe ta tunkuɗe murfin motar ya buɗe aikuwa nan take baba alamu ya girgiza motar da mugunta, hakan yasa jahad ta faɗo ƙasa timmmmm ! ta gangara Ta bugi wani dutsi nan take goshinta ya fashe,
Shi kuma yaja motar da gudu ya tafi da hussana acikinta, hankali a matuƙar tashe jahad ta ɗago daga jikin dutsen jini na zuba a goshinta, miƙewa tayi da gudun gaske tabi motar tana kuka tana ambaton sunan HUSSANA, muryarta har wani shaƙewa take yi saboda yadda take kwala mata kira ga uban gudun da takeyi don ta taddo motar, amma ina tuni yayi mata nisa ga tafin ƙafarta da ƙayoyi suka sossoke ta duk ƙafar ta fashe, jini nata faman gangarowa a ƙarshe data gaji da bin motar jiri na kwasarta nan take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya acikin korayen ciyayin dake a wurin, 😭
Kiran ƙarshe da jahad ta kwalama hussana kafin ta sume har cikin zuciyarta taji shi tuni ta soma ƙoƙarin buɗe idanunta wanda ke cike da bacci, a lokacin har baba alamu yashiga da ita gidan gonarsa ƙopar katako ce ke gare sa tamkar ɗan gate, bayan ya shigar da motar ya fito ya rufe ƙopar gidan gonar da kwaɗon dake ajiki,
Sannan ya koma tare da buɗe murfin motar inda hussana ke zaune tana faman lullumshe ido alamar bacci bai isheta, so take ta buɗe Idonta taga ina jahad take amma sam bacci ya hana Ta,
hannu baba alamu ya zura tare da ɗauko hussana ya sa6ata a ƙafaɗarsa ya miki hanyar wata ƙopa inda ya dosa ya buɗe ta ya shige da ita ciki sannan ya sauke ta ƙasa har tana yin tangyaɗi zata faɗi, sai da baba alamu ya datse ƙopar ɗakin gam yadda bamai shigowa sannan ya juyo yana kallon hussana tare da washe waɗannan haƙoran nasa marasa saiti,
A lokacin Hosana ta dawo cikin hayyacinta baccin yabar jikinta, bin wurin tayi da kallo ɗakine mai faɗin gaske babu komai aciki sai jarkokin ruwa da bulo bulo, da wani ajiyayen genarator tsoho, sai sauran tarkace, wurga idonta tayi akan baba alamu dake tsaye agabanta yana washe mata baki, nan take ta buga uban tsalle taja da baya tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga uku, Ina jahad take! Wayyo Allah na Me zaka yi mun meyasa ka kawo ni nan ! tayi maganar tana ja dabaya a tsorace
Baba alamu ya kashe mata ido ɗaya tare da cewa "daɗi zan baki, kiyi shiru da bakin ki kada wani yaji mu, indai kina son ganin ƴar uwarki to ki bani haɗin kai muyi mu gama cikin salama,'
Yayi maganar tare da kai hannu zai shafa fuskarta a firgice taja baya tana girgiza masa kai atsorace take cewa "Dan Allah kada ka cutar dani, ka ƙyale ni bani da lafiya, idan ka ta6ani mutuwa zanyi," ta faɗi tana faman zazzare ido, ga wata irin zufa dake wanko mata dakyar take haɗiyar numfashi,
"Ba zaki mutu ba, bada zafi zan miki ba kaɗan kaɗan, in dai baki bani haɗin kai ba zan ƙwata ta ƙarfi kuma naƙi nuna miki inda ƴar uwarki take,"
Cikin kuka hussana tace "a'a nidai kada ka cutar dani bana so, kadaina matsowa kusa dani, wlh Allah bazai barka ba kuma yaya Omar ma bazai ƙyale ka ba sai ya kashe ka,"
fashewa da dariya Baba alamu yayi tare da gwalo ido yana mata gwalo yace "Wanene wani Omar kuma? babu kowa anan daga ni sai ke ! Kuma yanzun nan zan kawar da sha'awata tare dake," yayi maganar tare da yin kwakkwaran taku ya fusgo mayafin jikin husana nan take ya zame ƙasa, watsa wa tayi da gudu ciki tana kuka cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da bulo ƙafarta ta harɗe ta kife ƙasa gaba ɗaya.........................
dariyar mugunta baba alamu ya saki ganin abun yazo mashi cikin sauƙi, nan take ya shiga kwance zariyar wandonsa,
daker hussana take jan numfashi saboda buguwar da tayi wani irin ciwon kai yafar mata lokaci guda, jin motsinsa dab da ƙafafunta yasa ta dumbuzar ƙasa a hannunta, ta daddage ta tashi zaune tare da watsa mashi ita a fuska, nan take yashiga yin tsalle yana faɗin "kai ! Kai!! Kai !! Don ubanki ni kika watsa ma ƙasa a ido! aiko bazan ƙyale ki ba, saina wulaƙanta rayuwarki,
Jin hakan yasa hussana zabura tare da miƙewa tsaye zata gudu batayi wani aune ba taji yaja rigar jikinta nan take ta soma yage wa, juyowa tayi tare dasa hakoranta ta gartsa mashi Cizo, azaba da raɗaɗi suka sa shi sakin ihu, kuma hakan ya ƙara fusata shi, a fusace yabi ta tare da damƙo gashin kanta ya janyo shi da ƙarfi ta dinga sakin ihu tana kuka tana kiran Sunan Jahad,
Matse ta yayi ajikinsa tare da sa hannun shi biyu ya ƙarasa yage rigar jikin hussana gaba ɗaya, hankali a matuƙar tashe husana ta watsa mashi miyau afuskarsa biji-bijin daya daya fara gani ne yasa shi ɗan dakatawa, hannunta ta sanya tare da ingije shi da ƙarfin gaske gaba ɗaya baba alamu yayi taga² zai faɗi ƙasa,
Cikin sauri hussana ta tattare rigarta ta kare kirjinta da ita, hanyar fita daga ɗakin ta nufa da gudun gaske tana kuka burinta kawai ta isa kopar ta buɗe ta fuce
tana cikin gudun nan baba alamu ya taso a matuƙar zuciye ya nufe ta da sauri yakai hannunsa tare da jan rigarta data rufe jikinta da ita, gaba ɗaya ya 6an6are rigar daga jikinta ya cire ta gaba ɗaya ya ruƙe a hannunsa,
Wani irin kuka hussana ta saki mai matuƙar cin rai ganin yarda ya cire mata rigarta, gashi ko brazier bata sanya ba, ƙirjinta gaba ɗaya sun fito, hannunta ta sanya ta tarbesu tana kuka kuma hakan baisa ta daina tunkarar ƙopar ba,
Bin ta baba alamu yayi da gudun gaske saboda ya ruƙo ta jikinsa don ya idasa nufinsa,
Sai dae ina kafin yayi wani kwakkwan yunƙuri tuni anyi ma ƙopar ɗakin wani irin kwakkwaran Naushi nan take katakon jikinta ya farfashe gaba ɗaya ta buɗe,
A tsorace baba alamu ya dakata yana faman zazzare ido don son ganin wanene wannan ya faɗo masa cikin gidan gonarsa !!!!!!!!!!!!
Ita kanta hussana ta firgita tsayawa tayi jikinta na wani irin kerma ga zazza6i daya lullu6e ta, har lokacin hannunta na tarbe da ƙirjinta,
Duro ƙafarsa yayi cikin ɗakin tamkar damusa wani irin kakkarfa ne mai ban tsoro, jikinsa na sanye da Jacket baƙa daga ciki kuma farar t*shirt ce wadda ta bayyana ƙirar ƙarfinsa, Sai dogon wando baƙi,
bai bamu damar muga fuskarsa ba domin kuwa tana sanye cikin face mask baƙi, idonsa kuma na sanye da baƙin glass,
gaban hussana ba ƙaramin faɗuwa yayi ba duk ta gama tsorata, baba alamu kuwa murya na rawa yashiga cewa "kai...Wai Wanene kai ! daga ina kake? Mai ya kawoka gidan gonata ! ya tambaya yana tada jijiyoyin wuya,
Har lokacin bai da alamar yin magana, a hankali ya sanya hannunsa tare da ruƙo jaket ɗin dake ajikinsa ya cire ta gaba ɗaya yayi wurgi da ita, sannan ya mayar da hannun nasa ya tu6e t-shirt ɗin dake ajikinsa ya rage babu riga ajikinsa,
Hankalin baba alamu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin irin damtsen hannunsa a murmuɗe ga ƙirjinsa dake motsi abun gwanin ban tsoro,
tuni zuciyar hussana tayi wani irin bugu nan take ta tafi zata sulale ƙasa, da Hanzari ya tarbota jikinsa gaba ɗaya tafaɗa a faffaɗan ƙirjinsa,
hakan ya bashi damar zura mata t-shirt ɗinsa ajikinta donya rufe mata jikinta, bayan ya kammala sanya mata rigar,
ya buɗe bakinsa ta cikin face mask ɗin yayi fito mai sautin gaske har saida baba alamu ya firgita yana faman kwalala ido,
Da gudun gaske wani Saurayi ya shigo ya tunkare sa, batare da yace komi ba ya miƙe masa Hussana, cikin sauri yasa hannu ya ɗauketa tare da azata a kafaɗarsa ya fuce da ita,
sai lokacin Yasa hannu ya cire glass ɗin fuskarsa tare da yin wurgi dashi, Azazafe ya sanya kyawawan idanuwansa waɗanda suka Canza Launi izuwa ja saboda tsananin 6acin rai, gadan gadan ya tunkari Baba alamu wanda ke shirin guduwa, hannunsa yakai tare da damƙar wuyan rigarsa ya ɗaga shi sama, ya dawo dashi ƙasa ya buga kansa jikin bulo nan take haƙora biyu daga bakin sa suka fito Jaga-jaga da Jini, saboda tsananin azaba da raɗaɗi ya sanya Baba alamun sakin futsari a wando yana cewa "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un na bani na 6atare na lalace nashiga uku, Dan Allah ka ƙyale ni wlh nabi Allah nabi manzonsa .,...........
tsawa mutumin ya daka masa tare da cewa "Kasan da Allah kake ƙoƙarin aikata ma ƙaramar yarinya faɗe tsofe tsofe dakai!! mutun mara imani da tausayi irinka wanda baisan darajar ƴa' mace ba Sam bai cancanta daya cigaba da rayuwa ba,'
ɗagowa baba alamu yayi yana ja da baya da baya idonsa jawur, jini na kwaranyowa daga bakinsa yana cewa "Dan Allah kada ka kashe ni ! Kabarni a haka naji jiki sosai, ina da ƴa'ƴa da mata in ka kashe ni zasu shiga wani hali.....' bai bari ya ƙarasa maganar ba, yakai masa wata irin mahangul6a da hanunsa nan take yasake fasa ihu,
"Karka kuskura ka sake buɗe wannan ƙazamin bakin naka da sunan zakayi mun bayani ! Bani da lokacin sauraron jawabin Ka, har kana da bakin da zakace mun kana da ƴa'ƴa da mata, don ubanka su yaran daka ɗauko donka lalata ma rayuwa daga sama suka faɗo? Ko su basu da dangi ne da zasuyi kuka in sun rasa su? Idan ka lalata masu rayuwa kana da tabbacin zasu ƙara numfashi ne ko baza suyi ba ? Ka yi tunanin hakan? ! idan wani ya lalata rayuwar ƴarka yaya zaka ji? Ka ƙiyasta yaya raɗaɗin yake azuciya............yana faɗin hakan yasa hannu ya rarumesa tare da wujijjiga shi ya sake buga kanshi ajikin bulo ɗin nan take kansa ya fashe jini ya soma kwaranya, ko shurawa baiyi ba nan take ya mutu a mace............
(Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar? Ka mutu kana aikata irin wannan mummunan zunubin batare da ka shiryu ba? Shin mai zaka ce ma Ubangiji? mutum baison lokacin mutuwarsa ba, shiyasa ake so koda yaushe mutun ya kansance cikin shiri kuma ya kasance yana aikata abun kirkiri, sam baba alamu baisan cewa yau wa'adinsa zai cika ba, Ga yarda ƙarshem shi takasance Ya Allah kasa muyi kyakkyawan ƙarshe, kuma ka kare mu daga aikata aikin dana sani 🙏😥
duk da ya mutu amma hakan bai masa ba saboda raɗaɗin da yake ji azuciyarsa, hannu yasa ya rarumi ƙaton dutsin dake ajiye a ƙasan wurin zai rotsa masa kai, cikin sauri matashin nan daya fita da husana ya faɗo ɗakin ya tunkaresa tare da hanzarin ruƙo hannunsa yana cewa "Yalla6ai kabarshi haka mana, ya riga daya mutu," fisge hannunsa yayi yayin da idonsa ke cike tab da hawaye da wani irin huci yake cewa "Kabarni kawai na tarwatsa kansa ko zuciyata ta samu salama, kasan yarda nake ji acikin zuciyata kuwa, tamkar ana rura garwashin wuta acikinta saboda tsantsar baƙin cikin da nake ji, WANNAN MUTUMIN YA SHIGA HURUMINA !!!!!!!!!!!!!!!!!!!! ⁉❗‼❗❓❓❓❓❓❓
*SHIN WANENE WANNAN MUTUMIN DAYA FARMAKI BABA ALAMU ACIKIN GIDAN GONARSA AYAYIN DA YAKE ƘOƘARIN KETA HADDIN HUSANA*❓⁉
*WANENE SHI*❓❓
_*amsar tana a wurin hafsat Bature muhammad Boss Lady domin son sanin wanene wannan sai ku antaya kuɗinku naira 300 kacal Vip kuma 700 a wannan acct number ɗin 3196407426 first bank Bature hafsat Muhammad ku tura shaidar biya ta wannan layin da kuma masu tura recharge card 08103884440 kada ku bari abaku labari , masu karantawa ta facebook masu ƙaramar waya Recharge card zaku tura koda digits ɗinsa ne 200 only in kun daure kun biya da dama zaku cigaba da samun posting insha Allah Ku fara biya da hanzari daga yau zuwa monday, har yanzu dae nice dae Hafsat Baturen da kuka sani mai sauƙin kai, ban canza ba, kaɗanne kawai zasu fahimce ni👍👏*
Alhamdulillah finally na kammala free pages
Leave a Comment