Yar Tsakar Gida 9

 


*🛖ƳAR TSAKAR GIDA🛖*

*Romance love and Sympathetic Story*

*Story and Written by Aisha Mamanteddy*


_Page 0 9_


*Masu tambaya na complete na wannan littafin don Allah kuyi hakuri ku sani wannan littafin sabo ne yanzu nake rubuta shi ba complete , yanzu nake rubuta labarin nawa . Sannan kuma littafin na kuɗi ne a next page 10 Free page zai ƙare . Maza ki hanzarta don ki mallaki naki ki kuma yi karatun ki cikin Aminci da Kwanciyar hankali*

*Littafin Ƴar Tsakar gida na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 Special payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932... Idan VTU transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409*


Yanda Naana ta Daka ma Amrah Tsawa yasa ta a hankali takawa tana nufar inda take tsaye . Zama a ɗaya daga Kujerun Dinning ɗin tayi tana daura kafa Ɗaya kan Ɗaya tana Girgizawa . Ɗaukar Plate Amrah tayi tana kokarin buɗe Rice bowl  din ne taji Muryar Naana tana cewa " Kama ta yayi kome zaki yi ki tambaye Ni bakiyi gaban kan ki  ba ,ko kin manta matsayin ki ne na tuna Miki.? Ɗan kallon ta Amrah tayi kana ta motsa laɓɓan ta a sanyaye tace " Kiyi Haƙuri, mene kike buƙata a farko .... Ohh My daughter Ina Nusaiba take.? Muryar Daddy ya katse ta Wato Alh Mubashshar . Juyawa Naana tayi tana murmushi kana tace " Daddy...ganin Momy a gyefen shi ashe tare suka ƙariko yasa ta cewa " Daddy , Mommy yanzu zata Sauko . 


Ja ma Daddy kujera Amrah tayi cikin sauri yana zama yayin da Mommy ta zauna a Gyefen shi .  Ga sabuwar mai aiki fatan zakuji daɗin Abincin ta . Hummmm To Mommy bari mu dai muci muji. Barkan ku da dare . Amrah tayi maganan jiki ba kwari , murmushi Mommy tayi tana cewa " Thank you my dear , Zaki iya tafiya Bara Ni nayi ....No mommy ita fa mai aiki ce just allow her to Do her Work ,wannan Aikin ta ne fa . Cewan Naana tana bin Amrah da Wani irin kallo na Wutan Ƙiyayya . Amma naga tayi kokari ai duka wannan ita tayi shi , at least she need to be rest . Ba Aikin ta bane ? , ki barta tayi Aikin ta , ai shi iyayen ta suka turo ta tayi , to Meye ma Abin tausaya ma Talaka ? , Mutanen da zaka yi masu Rana suyi maka Dare . Bana son ƙara jin haka daga Bakin ki . Muryar Daddy ya katse su , wanda daga ji kasan mutum ne kosassan tsohon dan boko , wanda basu dauki talaka da Wani ƙima ko daraja ba . Hasali duk idan suka ga Talaka to ƙiyayyar su a kan su baya ɓoyuwa . 


Shiru Mom tayi tana jin ba dadi sam , A hankali Amrah ta fara Aikin ta tana aje masu Abin da suke buƙata wanda tana haka Nusaiba ta ƙariko inda suke . Mamaki ne ya kama Amrah Ganin yarinyar bata da banbanci da Yaran Turawa wanda basu san darajar kan su da jikin su ba . Ashe Naana shigar mutunci ne a jikin ta , ita kuwa Nusaiba irin Ƙaramin Matsatsen Wandon nan ne a jikin ta iya cinya . (Bom short) . Sai normal rigar ta iya Qugu . Kunnen ta maƙale cikin Head phone , hannun ta dauke da Wayar ta kirar Iphone 14. Jan Kujerun tayi tana zama yayin da Amrah ta ke Tambayar ta Abun da take buƙata ,a maimakon ta bata Amsa sai A wulaƙance ta daga mata hannu tana dakatar da ita  . Humm Sauke Numfashi tayi a hankali tana ja baya tare da yatsawa tana mai jiran Umarnin su . Kunun Ayan Naana ta fara zubawa a Glass cup tana kaiwa bakin ta Muryar Nusaiba ya katse ta tana cewa " Daddy Ya Nurain Nan da Kwana Biyu zai dawo . Saurin Ɗagowa Amrah tayi tana kallon Nusaiba ,yayin da bakin ciki ya tokare Zuciyar Naana . A fusace su dai kawai sun ga ta sheƙa ma Amrah Ragowar Kunun tana Fadin banza dabba ,wannan Wani irin Abu kika yi ma mutane ba Daɗi ba daɗaɗawa ?. Wani irin Ajiyar zuciya Amrah taja mai ƙarfi da sanyin Kunun har bargon ta . Nan take idanun ta suka fara Fidda Hawayen, jikin ta ko ina Rawa yake yi karrrr³ . Uhmmm Uhummm . Nusaiba tayi maganan tana dan kallon Inda Amrah ke tsaye tare da bin ta da kallon sama da ƙasa kana tace " Mom wannan yarinyar yaushe ta fara Aiki .? Tun da ba ta iya abincin ba ta koma bangaren masu shara da goge² mana it's Will be simple .  Juyawa Hajiya Sa'adah tayi tana kallon inda Amrah ke tsaye gaba Ɗaya Naana ta gama tsuma mata jiki . Amrah zaki iya tafiya Gida yanzu sai gobe ko.? . Cikin Sauri Amrah ta juya tana barin Wurin yayin da Daddy ya mike yana kallon Naana yana cewa " Idan basa buƙatar Girkin ta Acan masu wata mana .? Ok . Mom tace tana kallon yaran mata su biyu . Barin Dinning room area din yayi yana nufar Under ground inda Apartment din shi yake . A hankali Nusaiba ta fara zuba kunun Ayan tana sha , wanda kurba daya ta ɗago tana kallon Naana cike da mamaki tace " Naana Wai Meye kike ce ba daɗi ? ,Ohh Mom Sha kiji mommy dadin gaske wallahi ,ban taba shan Wannan abu mai dadin wannan ba . Kallon Ta Hajiya Sa'adah tayi kana ta kalli Nusaiba wacce take cin Abinci tana yamutsi sam bata tanka Nusaiba . 


Gaskiya Naana ina tunanin may be daga bakin ki ne , amma Wannan ai daɗin shi yayi yawa . Tsakanin Mom da Naana babu wanda ya tanka Nusaiba wacce ta janyo jug din gaban ta tana sha hankalin ta kwance. 

**

Mom Cruzita ne ta kalli Amrah cike da masifa take cewa " Duk ranan da kika kara missing wani Aikin ki , to abu biyu ne zai hada Ni dake , ko na Kore ki ,ko na baki Half Salary a watan . Na lura dake kwana biyu kin maida mutane kaman dodon Ni . To kin san Aikin ki ba sai na tuna Miki ba Gaskiya, Ni kawai Abun da yasa kika ga ina tura ki cleaning saboda yanda mutane ke son ki a lokaci guda zan ji suna firar ki wannan shiyasa . A yanzu a aikin ki na ƙara Miki duk safe kina rinƙa zuwa Office din Doctor Zaid kina masa Aikin sa . Yanzu Rana tayi kalli Lokaci Amrah ? Sha daya na rana sai yanzu nayi ido dake ? , Na tura masa Su Hajara yace yafi yabawa da Aikin ki , ko mun rana idan kinzo kije kiyi masa . Don haka kiyi sauri ki tafi yanzu ,idan kuma kin gama kizo ina son ganin ki . Cike da Sassanyar Muryar ta tace " Tom Mam Cruzita amma don Allah Kiyi Haƙuri...A'a No next time bani Zaki yi ma laifi ba , Oga ne ,don kin ji dai Cleaning din ki yake so ba na kowa , so You have to maintain . Ok mah... Amrah tayi maganan cikin sauri tana juyawa tare da nufar benen da matakalan shi kadai ya isa ya sarar da mai tafiya akai . Wannan yasa Wasu suke bin lifta don Asibiti ne yanda kasan a Turai haka yake . Amma su cleaners dole su bi matakala ko mun tsayin shi .


A bakin Office din ta tsaya tana kai hannun ta tare da murɗa Handle Door ɗin . Muryar sa taji yana fadin " You no what ? Na haɗu Wata fine girl, which really love her ba wasa ...shigowan Amrah yasa Zaid Aje wayan sa a Gyefe yana kallon ta , sam ta kasa hada ido dashi don kallon Wani irin Ƙwarto take masa . Haka shima ya gagara dauke idanun sa daga Kallon ta . Excuse me Sir. Tayi maganan tana dan Ɗagowa tare da kallon sa . Hummmm Wani irin gwauron Numfashi ya sauke kamin ya miƙe daga Zaunen da yake yana kallon ta tare da cewa" me yasa jiya bakiyi taking Excuse kaman haka ba? Kika faɗo mun Privacy ? , Fatan dai kin iya barci ,abun da kika gani bai hanaki barci ba ko.? Tsammm Tayi tana ƙasa basa amsa  mintuna uku yana expecting yaji wani Abu daga bakin ta but she make silent ,Amma sai tayi shiru ,hakan yasa shi Fahimtar tana Miskilance...hummmm . Ya numfasa kana yace " Oya zaki iya fara Aikin ki . Sum.sum tayi tana wuce shi tare da nufa inner Room ɗin shi . Ba laifi yau bai watsar da komai kaman jiya ba . Nufan Bakin gadon sa tayi tana kokarin sauya Bedsheet din a zuciyar ta tana cewa " Oh wai nan Asibiti ya dauka ko Gida.? Motsin shigowan sa yasa ta saurin juyowa , kallon kallo suke ma juna yana Sakin mata Wani Murmushin da ta kasa fahimtar menene manufar sa na yin hakan . Tun karo ta yake yi yana takowa zuwa inda take . Nan take Amrah ta rasa inda zata nufa ,wannan yasata nufar Hanyar Fita da gudu ,wanda tana isowa yayi caraf ya riƙe ta . Mutsu² take yi tana kokarin kwace kan ta ,amma nan taga ikon Allah hannu daya yasa yana kama hannayen ta duka biyun wanda motsi ta kasa . Sai fara masa kuka da tayi . Don Allah,don Allah ka rabu Dani ....Ka rabu .....Wayyooo naaaa.....Maganan ta ne ya Datse ganin yanda ya wurga ta saman Gadon sa yana haye mata tare da jan rigar aikin nata yana yagawa ƙyaaaaaaaaaaaaaaa.............!*Kuyi hakuri posting din yau ba yawa , muna biki ne sai mun hadu Posting din gobe wanda kuma zai zama last Free page , daga shi ba zaku kara ganin pagen kyauta ba . Sai an biya kudi nasa ka mutum a group .ga masu ɓukatar yin payment regular group  ₦500 Vip group ₦1000 SPC ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*


       *Aysha Mamanteddy*

No comments

Powered by Blogger.