Yar Tsakar Gida 7


 *🛖ƳAR TSAKAR GIDA🛖*

*Romance love and Sympathetic Story**Story and Written by Aisha Mamanteddy*


_Page 0 7_


*Littafin Ƴar Tsakar gida na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 Special payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932... Idan VTU transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409*


Kallon su Amrah keyi sam ta rasa fahimtar inda maganan su ya nufa , abun ka ga karamin yaro Hausan har a lokacin koyan ta ake yi,wannan yasa ta kallon Baba Zuwai tana cewa " Wallahi Baba.....yi mun shiru...!! Ta daka mata Wani irin gigitaccen Tsawa tana mai Cigaba da cewa " Nawa Ɗaya shine ki bani Kuɗi na casss Don Ƙwandala ya ɓata sai na sauya Miki kamanni da Duka a cikin gidan nan . Cikin Rawar Jiki Amrah ta miƙa ma Baba Zuwai kudin ,jikin ta ko ina Rawa yake yi ,tsoron ta ɗaya kar yazo kudin bai kai ba . Muryar Baba Zuwai ne y katse ta tana faɗin " Allah ya cece ki sun cika , wuce Ki Dauki bokiti ke debo ruwa ki zo ga kwanuka can ki Wanke su . Tom Baaba . Amrah tace tana Saurin wucewa ɗakin Ikilima don anan yanzu Amrah ke kwana ita Ɗaya ,don ikiliman bata nan . Duk da A wannan shekaran zata dawo Gida Shikenan kuma an gama Sakandire . Aje uniform din nata tayi tana saurin fitowa tare da Ɗaukar Bokiti da Wannan yammacin tana nufar makoton su inda suke da rijiya don ta debo Ruwan wanke wanken  .

**

Akwana a tashi babu Wuya shakuwa da soyayya tamkar yaya da Kanwa ya shiga tsakanin Nurain da Amrah ,wacce a yanzu take cikin zakukwuran yaran Ajin nasu . A farkon Term din tayi na Goma wanda a jarabawa na gaba tazo na Uku . Sam a yanzu bata damuwa da Fitinan cikin gidan su da tsangwaman da take sha , Don idan sun ɓata mata tana fitowa zata shige Gidan Su Nurain , Anan zai Amsa kayan tallahn ta ya rabar suyi hira tayi barci idan ta huta sai suyi karatu . Sosai kokarin Amrah ke basa mamaki don kullum a zuciyar sa cewa yake " An kashe product anan , Don bata yi sa'an Iyaye ba ,duk da a yanzu ya san ita marainiya ce . Wannan yasa shi sosai yake bata kulawa ,ya zama mata tamkar uwa uba bango majingina . A yanzu har yakai ya kawo sunan ta a makarantar ƙanwar Nurain ,don da yawa wasu suna mata kallon ƙanwar sa ce . 

Ihun Ɗaliban ne yasa Nurain Wanda a yanzu suke SS 3 kuma yana da muƙamin Headboy saurin juyowa shi da duka abokanan nasa suna kallon inda Yaran primary din suke a layi . Sunan Amrah ne ashe da aka kira a matsayin wacce tazo na uku yasa Ɗaliban ihu suna kiran sunan ta Da Fine Girl fine girl don sunan da suke kiran ta dashi kenan . Tsayawa yayi yana murmushin nan nasa yana gani Amrah ta fita cike da karsashi da gwarin Gwiwa ta ta amsa Kyautar nata tana juyawa tare da kallon Ɗaliban tana mai ɗaga masu cike da fara'a . Juyawa Nurain yayi yana kallon Abokanan nasa suna barin Wurin don ita Amrah bata Gansu ba ma .  A cikin Ajin su babu wacce Amrah ke shan Wuyan ta irin Naana bata da kirki ,kullum aikin ta kenan bin ajijuwan tana cewa " Ai Amrah yar talakawa ce har tallah take yi , basu hada komai da Nurain ba . Duk tana faɗin Wannan maganan ne saboda Tasan Familyn Nurain . Don da mahaifiyar ta da Momyn Nurain ƙawaye ne sosai . Don a bakin Naana Mommyn Nurain ta fara jin sunan Amrah da Halakar su da Nurain . Kallon Marian tayi tana dalla mata harara tare da kallon Amrah wacce ta dawo inda suke tsaye . Bakin ciki ya ishi Nana do mun kuwa ita ce ke daukar positon din da A yau Amrah ta dauka , ita kuma tayi baya don na Huɗu tazo . Humm Wacce kike ne ? Amrah Ko? , Kar ki manta Wacece ke , Haka zalika kullum talaka a kasan mai Arziki yake , Ki daina farin ciki don a yau kin zo na Uku a gobe ina nufin a kwana a tashi Ni zan zama ta gaba dake , sannan ke matsayin ki ba zai wuce mai mun shara da goge goge ba .  Mtswwwww...! Saurin buɗe baki Marian tayi zata yi mata magana sai Amrah ta riƙe ta tana Girgiza mata kai Alamun ta rabu da Naana don ita bata son tashin hankali gaba Ɗayan ta ,sannan kuma sam bata ji zafin maganan Nana ba ,don dama tasan Naana ba tsaran ta bane . Duk Hutu suna Abroad kin ga ba zata hada kan ta da ita ba . Idanun ta sun ciko da ƙwallah sosai Amma sai ta maidasu tana lallashin Zuciyar ta daba kan ta Haƙuri .

**

A hankali take kutsa kan ta Izuwa Falon Gidan ,cike da Sanɗa wai a dole tana so tayi surprising din sa . Yanda taji Muryar nasa ne yasa ta saurin ƙarikawa inda yake , Sakin Takardar da kyautan nata tayi a ƙasa Ganin Hawaye na bin Kuncin Nurain , Jarumin Namiji wanda ko karaya bata taɓa Gani a idanun sa ba ,amma a yau taga Hawaye . Cikin nuna damuwa ya furta " Please Mommy ki bari na kammala SS 3 ɗin After all sai na dawo America, idan na tafi Wane zai kula da Amrah.? . Wacece Amrah ? , Muryar Daddyn shi ya katse shi cikin zafi ,wanda da'alama mutum ne mai zafi , gobe zan sa a zo dauke ka , jirgin 11am zaku biyo zuwa America. Tare aka haife ku da ita yarinyar ne ? , Ƙanwar Nusaiba tana SO ta ganka duk ta damu , yau ne fa karin Shekarun haihuwar ka ,amma baka sai dai muyi ta kallon hoton ka . Shiru Nurain yayi a zuciye cike da sangarci irin na yaran Hutu ya Datse kiran yana cilli da Wayar can Gyefe . Kallon sa Amrah tayi a hankali ta kira sunan sa da " Nurain ...! Ɗago da sexy eyes din sa yayi yana kallon ta kamin yace " Na'am Amrah . Meke faruwa ? Tafiya zaka yi ? Zaka koma America ne inda Mommy da Nusaiba suke kaima?.  Duka a lokaci daya take jero masa tambayoyin nata . Cike da son kawar da damuwan sa ya kalle ta yana kafe ta da idanu,kawai sai taga ya zaro mata idanun sa yana tsora ta ,saurin bata tayi ,nan take ya hau yin mata Dariya yana faɗin " Matsoraciya . Taho muje kasa palour . Bin bayan sa tayi tana faɗin " Nurry ka daina tsorata Ni da yawa haka . 


Me hoto ta gani a tsakiyar falon , yayin da Nurain ta kalle ta yana cewa " Amrah today I'm + 1 . Wow Happy birthday Nurry . Murmushi yayi yana rike hannun ta tare da furta " Thank you Amrah . Cake din da Mama Nanny ta kawo masu ne Amrah ta kallah kamin ta tsinkayi Muryar sa yana cewa " Mama Shigo Mai Photograph yana jira a dauke mu duka . Rungume Nurain Amrah tayi a tare suka dau hoton wanda yawan su yafi talatin fiye da Ashirin suna tare daga ita sai shi suka yi shi . A wannan rana sun wuni cikin nishaɗi har wuraren yammaci . A farfajiyar Gidan ne ta kalli Nurain tana cewa " Nurry ina keken ka yake.? Juyawa Nurain yayi yana kallon Can Gyefen Garden kamin yace muje can ki gani . Kai tsaye suka nufa Garden din Nurain na fiddo da keken sa Taho ki hau . Yayi maganan yana kallon Amrah don yasan Abun da take so kenan . Kallon sa Amrah ta tana masa dariya tare da cewa " yeeee tana saurin hayewa ta gaban shi yana fara juyi da ita a keken suna kaiwa da komowa a tare . Su kan su basu san mintunan da suka ɗiba a hakan  Amrah ..... Taji Muryar sa ya kira sunan ta. Ɗaga idanun ta Tayi tana kallon sa fuskar ta cikin matsanancin fara'a ,Kiyi Haƙuri kinji..." Uhmm mene kayi mun Noory.? Murmushi taga yayi mata yana Girgiza kan sa tare da cewa " ba komai . Kallon sa Tayi tana jin akwai wani Abu kamin tayi masa magana Muryar Mama Nanny ya katse su tana faɗin " Dare fa ya fara yi , Amrah ta tafi Gida haka . Sauka Amrah tayi daga keken tana kallon Sa tare da daga masa hannu tana faɗin " Sai da safe.  Ba zan jira ka ba gobe makaranta xan tafi ,idan ina jiran ka Zango daya ke wuce ku kullum . Idan kazo school ma haɗu . Juyawa tayi da gudu tana barin Wurin . A hankali Nurain ke sauke Numfashi don ji yake tamkar zuciyar sa zata tarwatse.  Idanun sa na fidda Hawaye masu zafi da raɗaɗi . 


Kama hannun sa Mama Nanny tayi tana nufar palour dashi . Nurain kayi hakuri Kabi maganan iyayen ka , ko mun daɗewa wata rana zaku hadu da Amrah . Tafiya ba mutuwa bace ba . Mama yanzu ba yanda za'a yi Amrah tabi Ni mu tafi America,ko na roƙi Baba Adamu ?. Cikin Sauri Mama Nanny tace " A'a Ba zai yiwu ba ,ko itama Amrah ba zata bika ba . Rintse idanun sa yayi yana cewa " ki haɗa mun kayan da zan tafi dasu . Gyada masa kai Mama tayi kurum tana gani ya wuce ciki ,a zuciyar ta hamdala take yi daya amince da tafiyar nasa do mun kuwa bakaramun fada ta sha ba a gurin mahaifin sa , a cewan sa tayaya ta bari har Wata mu'amala ta shiga tsakanin sa da yar talaka...? 

**

Zama yayi a kasan tiles din yana bin gift din Amrah da sakamakon jarabawar nata da kallo . A hankali ya kankafe yana yo kasa dasu tare don yaba Mama ta sanya masa a jakar tafiyan sa .


Safiyar Alhamis . 

Zaune Amrah take a cikin Ajin suna fira da ƙawayen ta . Kaman Ance ta juya idanun ta ya sauka akan Naana dake mata wani irin Dariya . Humm sauke Numfashi tayi a hankali tana Cigaba da Rubutun ta a haka har aka Tashi break . Marian ina zuwa ko zaki rakani Secondary Section . Hahaha....Uban me zakiyi a secondary section din.? Muryar Naana ya katse ta , takowa tayi gaban Amrah tana faɗin " Nasan Wurin Nurain Zaki je ? Shin baki da labarin Nurain ya koma America da zama. ? Kirjin Amrah ne ya buga daaam . Ai ba zaki ƙara ganin Nurain ba ya Miki nisa nisan da ba zaki taba iya cimmasa ba . Kallon Naana Amrah tayi kawai sai ta juya da Gudu tana nufar Section din su . Voting ta tadda Sunayi na sabon Headboy wanda Ganin haka yasa Zuciyar ta kare karyewa . Juyawa tayi tana ware ware tare da kallon Yan Class din nasu . Amrah ...! Taji Muryar saif ya katse ta . Cikin sauri ta Juyo tana kallon saif tare da cewa " Ina Nurry yake ? Don Allah ka faɗa mun yana ina..? . 


Kallon Amrah saif yayi cike da daurewar kai yace " A'a bai faɗa Miki zai koma America da zama ba ? , Ai yanzu ma haka jirgin su ya Ɗaga nake tunan.... Kamin ya ƙarike Maganan ta juya da Gudu tana nufar Hanyar Gate . Me Gadi dai yaga yarinya ta felle ne ta gudu wannan yasa shi kiran sunan ta da Ƙarfi Amma ko waiwayowa ba tayi ba . Gudu take yi iya ƙarfin ta wanda sam bata tsaya ba sai a bakin Gate ɗin Gidan su Nurain.  Baba mai Gadi ta gani a kofar gidan ,Wannan yasata ƙarisowa cikin haki take fadin " Ina Noory.? . Kallon ta ya tsaya yana yi wanda Ganin irin kallon da yake mata yasa ta fara zubda Hawaye . Da gaske ne kenan ya tafi.? . Girgiza Kai Baba mai Gadi yayi cike da Tausayin Amrah kana yace " Kiyi Haƙuri Amrah , kuskuren naki ne tun farko kin shiga jikin wanda yafi ƙarfin ki , sanadin ki mahaifin sa yasa shi don dole sai ya koma America, Saboda baya son hulda da talaka . Yaji labarin ki , kuma ko da kika ga Nurain a nan layin mahaifiyar sa ce taso hakan ,ba tare da mahaifin sa yasan a cikin talakawa yake zaune ba . A yanzu ina so ki manta da Nurain domin gidan nan ko kin shiga babu kowa cikin ta ya sallami kowa,sannan Nima yanzu ina hada kaya na ne xan koma Garin mu ta buzaye . Karan motocin da Amrah taji ne yasa ta Saurin juyawa tana kallon Wasu irin manyan motaci irin na rusau din nan . Hawayen idanun ta karuwa suka yi . Baba mai Gadi Nurain ya tafi kenan . Amrah kalli kiga wannan motocin sun zo ne don rushe Gidan nan , saboda Mahaifin sa baya son alakar ku Dawowan Nurain ba yanzu ba . Kuma ko ya dawo Nigeria ba lallai ya gane inda kike ba . Saboda rushe gidan nan za'a yi inda ya zauna ma ba zai gane ba . Idan kuwa aka rushe nan da shekaru uku Ba za'a gane komai ba ,bare kuma ya kai ga Shekaru goma . Kiyi Haƙuri ki manta da komai ,ki manta da kin san Nurain .!  Ɗauke Wuta tayi tana kasa ce masa komai ya juya yana barin ta anan tsaye don baya da bakin da zai Fahimtar da ita .


A hankali take daga ƙafan ta tare da Nufar can Gyefe tana gani aka fara rushe gidan yayin da bata motsa ba har aka maida wurin flat .zama tayi a bakin hanyar tana wani irin kuka mai ban tausayi da raunana zuciya . 

**

Akwana ta a tashi Wahalan nata na karuwa amma a haka take girma ,tana manta komai a rayuwar ta amma ta kasa mantawa da Nurain wanda a yanzu gidan su ya zama Wani karamin kasuwar layin don fili ne aka maida shi na Al'umma ,wannan ya tabbatar mata da cewa " Mahaifin Nurain wani babban ne a Nigeria.  A yanzu sun kai Primary 5 inda a yanzu hanya ta biyo don an ce tazo da kuɗin zana jarabawar shiga Js 1 . Sannan scholarship ɗin nata ya ƙare yanzu sai dai ta biya kuɗi idan tana son tafiya Ajin gaba ko ta sauya makaranta . A Tsakar gidan taci karo da Baba Adamu wanda shima a yanzu yana jin jikin sa halin rayuwa kudin ma babu kwatakwata . Sannu da Jiki baba . Yauwa Amratu ,yayi maganan yana kokarin ficewa . Nufar dakin Baba Zuwai tayi sam ta kasa tambayar baba Adamu . 


To maza a sauya kaya azo a dauki tallann Awara . Kallon Baba Zuwai tayi kana tace " Tom Baba , Baaba An Koro ni kudin jarabawa Zamiyi exam . Don Allah Baaba ki biya mun ,idan banyi ba ba Zanje Matakin gaba ba . 


Wani irin Kallo Baba Zuwai tayi mata kamin tace " Alhamdulillah, Na huta da Wannan shegen karatun naki , Ni asara ta haife Ni na biya Miki kudin makaranta,koda kuwa kudi na zuba mun ai ba zan baki ba . Don haka Shikenan . Daga nan kin gama karatu har Abada kuwa.  Wasu irin Zafafan ƙwallah ne suka zubo mata . A hankali take tunawa da maganan Nurain . Ki mun Alƙawari ko dani ko bani Zakiyi karatu . Me kike so ki zama for your future life.? Rintse ido tayi tana tunano da maganan tasu . Ina so na zama babban mutum kaman kai . Dallah dauki Awara ki fita ki zaga mun makota . Saurin daukar Roban awaran tayi tana ficewa daga Dakin . Tun daga nan Amratu bata ƙara karatu ba ta hakura ta aje komai da ya shafi karatu sai Wahala na cikin gidan kawai . Kamin nan kowa yasan ta a ƳAR TSAKAR GIDA.


*2023................*

Amrah......! Amrah.....!! Baba Zuwai ke kwaɗa kiran sunan Amrah tana Fitowa da Dakin Inna Larai . A hankali ta sako kafanta tana fitowa daga Dakin Yaya Ikilima . Kara murje idanu na nake yi ko dai sune basa Ganin mun dakyau . Wow...wow wow . Amrah ce ta zama Wata irin kyaƙyƙyawar Karshe kyawunta ta ko ina ya bayyana. Farin ta ya Fito Tassss. Idanun ta kuwa sun kara yin dulu².  Smiling face din nan nata yana nan , don ta haka ne na hango simple din ta da suka loɓa daga tsakiyar Kuncin ta . Doguwa ce amma matsakaiciya  . Tana da dan dogon hanci sannan siriri,bakin ta kuwa baka ce spoon yana shiga ba . Ga cikar gashin ido dana Gira. Komai sai dai muce Mashaallh, Yanda ta cika ka rantse ta kai shekaru Ashirin , Ga Albarkatun sama da ƙasa.Harara Baba Zuwai ta Watsa mata tana watso mata dubu takwas din Aikin nata kamin tace " Ba kin ce za'a kara maku Kudi a wurin aikin naku ba? Ya nake ganin dubu Takwas...........!
to yanzu labarin zai fara ....mu haɗu a next page ...........


```Tallah```

Assalamu alaikum mata yan uwana namaku kunyimun Allah ka bar zumunci ya shiryar mana da zuri'a ameen


Dafari kuma san idan *buxuwa empire* da ta doso kunsan taimako ya kawo ta Allah ka taimakamana ameen Hmmm 😗 to mata nasan dacewa kuma kun sani duk wata mallakar da takai bakin mallaka ko dadai tarihi baya canjawa kan cewa indai mijinki ya shiga list din aikin buxuwa empire topah hajiya ya riga da ya gama mallakuwa sai kuma Allah  he is sorry 😐😐 Allah ka mana jagora ameen


Mallakar lilin kaza 


Mallakar rushii


Mallakar gaban da namiji 


Mallakar masai 


Mallakar kwai 


Mallakar ayoyi da sirri na surorin mahaliccin mu 


Mallakar da muke samun hanta muja da sunansa danaki a dake da magungunan hadin mu 


Farin jinin warwaro mai kaman kiranyen


Kiranyen toxali mai kamar bita zaizai


Kiranyen bakin Ruwa


Mallakar dauji,ko kiranyen saurayi ,ko macen da bata da cikakkun samari masu ajii to inkinga kawarki dawannan to aikin cikin dajine masu yi dawanda nayomasu sunsan yanda yake yi kamar yankan wuka topah hajiya bazama😒😒😑😑


Kitaho Gurin Hajiya *buxuwa empire* da tayi maku wannan kalolin aikin da zarar kinbini pc please 🥺 kifadi abun da kk so direct Saboda mutane sunyi mun yawa Allah Matar da tashirya aure ko kinason amsar kudi wajensa ko kina buƙatar ayi masa farraku da yammata ko wacce mace ,mallaka 


Masu bukatar kayan da'a available suke cikin price mai saukin gaske masu aiki da marasa aiki available zaku iya yin mana mgn ta wannan number kamar haka:08139762831


Muna godiya ga mata bakiɗaya masoya a ko ina ngd🥰🙏🙏🙏🙏🙏🥰🥰🥰🥰🥰🥰

No comments

Powered by Blogger.