Yar Aikin Karuwai 91-95

 


🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼

    LITTAFIN KYAUTA NE              91-95
Official


By

AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA


Page naku ne


Mum Amatullah

Pharteema Muhammed

Hajiya Hauwa

Ummu Shureim

Hassana Habeeb

Zainab ashiru Adamu

Saudatu Abdullahi

Ammin Airah


       Malam kunya ta Kama shi bai taba ganin irin wannan rashin kunya ba,Wise ce ta mikawa Santana Hannu Suka kawo zasu tafa sai Suka janye tare da hada Baki suka furta ba kyau kowa ya maida hannunsa, ana Mana babin wanka Mandula tace ai ni bana wani gaggautawa da cuccudawa ai kawai Malam na kwara da roba na wuce wajen to Yar

degree faranti ce ni, Santana da su Star harda shewa,Star tace ashe a ruwan ma akwai me tsarki da tsarkakewa to idan Mata da miji suna wanka fa amma dai shi ba matsala,Malam dai yace ai Yana da kyau sunna ce wanka da matarka,Wise ta rufe baki tana kunshe dariya tace Malam to kaima kana Yi wai,yace ae Alhmdllh Muna dan tabawa,Ido Muka zaro ai mun zaci banda ustazai yo Ustaz yayi ma bare tubabbun karuwai Papa kaga ta kanka cewar Wise ,Star ta kalli Malam tace Abul khairi Mazarawi? Yace naam dariya tayi tare da kifa kanta a saman cinyoyinta tace ya amsa wlh gaskiya Ina sonka ni Kaine ka birgeni da gani dai dai dani kake tana karewa wandon Malam kallo tace amma Malam daga wajejen Isra'ila kake ko, Malam ya Sha kunu Kawai irin ba Wasa, nidai Nace Malam ni Ina da aure ya  mazaunin mace yake idan tana yiwa miji kukan shagwaba,Malam yace ba laifi wannan Abu ne me kyau duk cikin kara dankon kauna ne,nace tab Nawwar ka shiga Uku Malam yace da kyau,ya daina Wasa yaci gaba da biya mana Muna ta iya shege ya gama da sauri ya sake Mana nasiha sosai sannan yace gobe cikin darasi harda tarihin annabawa,Star tace toooo an kusa zuwa Suratul Yusuf suna ta murna Ina jinsu Dan ni na fisu ilimin addini da Wise ma tana da nata ba laifi,Malam ya tafi da yamma Me English tazo,tace banda hausa a nan ta Mana darasi Muna ji,tana ta Mana iyayin turanci,tace zamu Fara da Noun,nace now ta yanzu yanzu ko kuwa wata Hajiya Now din ce daban,Wise ta dinga dariya da malamar ma haka,munyi nisa da karatu Nawwar ya shigo a mota yayi parking cikin jerin motocinsa,a fili nace Excuse Zan karasa Ilimina a can tare da dafe kirjina nace My life ya dawo,Malama tace karatu muke fa,baki na bude nace Man of the world fa ake ce miki,My Hero,My Star haba malama ko daga birtaniya kika zo ai kya saurara min,tashi nayi na wuce abina,fitowarsa kenan na taho da gudu na fada kirjinsa nace I wanna be in your life,dariya ya saki yace ko karatun ne ya Fara aiki,dariya nayi nace a street na tsinta, daukana yayi kamar Baby a haka Muka wuce part dinmu 


     Bedroom na tayashi ya cire kayansa ya fada toilet,lekowa yayi yace Miko min key din can,daukowa nayi na Mika Masa ya damko Hannu na tare da jawoni cikin toilet din,nace yanzu fa nayi wanka,ai tayani zakiyi Yana min rada a kunne haka na hakura Muka yi wankan tare yana Wasa da sassan jikina haka Muka Gama muka fito tare da shiryawa,ya sa Kaya marasa nauyi sea blue ni kuwa guntuwar gown na saka peach and green me kyau sannan na fita kitchen na kawo Masa abinci,nice na ciyar da shi Yana danna waya har ya gama ci Muna hirar masoya, yace jibi zanje Abuja,murna nayi sabo da dama na gaji da irin yanda baya barina na huta,nace ai kuwa sai muyi ta karatunmu Allah ya dawo da Kai lafiya,Kallona yayi ganin Ina ta Jin dadi,kwafa ya ja wato murna ma kike yi to na fasa kuma ma Zan iya tafiya dake ai kina da ilimin addini, wani dukul naji yace ki hada Mana kayanmu sati zamuyi amarci sabo,tagumi na zuba haka na kumbura baki tare da cewa to,Murmushi ya shiga yi,Ashe tsokanata yayi dama ban sani ba haka na shiga hada mana kaya yace Wasa nake Miki,nace Allah ba matsala muje ko da gaske ne ai kana so Ina son abinda kake so,tsokanarki nayi tsakanin kafafunsa na dawo na zauna tare da maida kaina da gadon bayana saman kirjinsa, Wayar dake hannunsa ya ajiye gefe ya shiga Wasa da jikina sai da ya murzani son ransa sannan ya kyaleni lokacin malama ta gama darasinta har ta tafi ma,suna part dinsu sun saki kida sai cashewa suke yi Kamar basu ji Nasihar Malam ba Santana Yana can Yana ta faman murguda duwunsa Kamar na dan tsako.


   Baffa kwana biyu ya rasa inda zai ga Mami Kawai sai ganinsa nayi a gidan yayi knocking Ina Budewa na ganshi na kalle shi Muka hada Ido kallon palon yayi ko Ina Kal Kal Yana zuba kamshi yace Yana nan Kuwa? Nace ae,shigo Mana,ya shigo ya zauna na durkusa na gaida shi sai kunyata yake ji ya tuna sanda ya kaini hotel,nace Baffa ya kawata Kuwa Star, har gumi yake yace dan Allah ki rufa min asiri karku fadawa iyalina da yarana ki rokar min kawar taki ta rufa min asiri,nace wlh ya wuce har abada baza mu fada ba amma idan ka daina fa,da sauri yace wallahi daga Sanda nasan kina tare da dana ban sake ba Kuma na tuba sahihin tuba bazan sake ba har abada Inshaallah,nace to ka dauka komai bai faru ba dan Allah ya wuce har abada Allah ya Kara kiyayewa ya Kare mu ya shirya mu,yace ameen Yar Albarka sai yanzu nasan Zina bata da amfani,ga zunubi,ga zubar da mutunci dama Indai sana'ar mutum kenan to Watarana sai yaji kunya zai iya Neman yarsa ma bai sani ba,nace wlh ai mu Kam Allah ya Kare mu yanzu ma duk su Star sun dauki hanyar tuba Nawwar ma ya samo Mana malami Yana koya Mana yaki da jahilci,Baffa yace madalla kaji Dan Albarka Allah yasa wannan ya Zama shine silar shigarsa Aljanna,nace Ameen Ameen Baffa Inshaallah damu daku a Aljannar ma a GRA muke,yayi dariy tare da furta ameen ameen,nace da anyi mashahuriyar Yar giya a aljanna,Baffa ya dinga dariya yace kin San inda Mamin Nawwar take kuwa? Nace Baffa ya akayi haka ta faru har saki uku kayi ganganci wlh uwar yaranka guda,Baffa yace to ba a kaunata a gidanmu shi yasa aka kyale ni babu me fada min gaskiya gashi nan yanzu kullum 'yata sai nayi kuka,dariyar Baffa ta kamani Kamar ba surukarsa ba sabo da a bariki Muka hadu shi yasa,nace kaga ko ni ban San inda take ba wlh Amma Watarana tana zuwa nan,Baffa yace kiyi amfani da damarki a wajen dana ki samo min inda take dan Allah Hakuri Zan bata Kawai ta yafe min tun kafin hakkinta ya kamani Allah yasa dai tayi aure da wuri mijin Kuma ya saketa ta dawo wajena,Nace Baffa ai ko ba'a saketa ba sai mun kaddamarwa mijin dole ya sako maka matarka,Baffa yace da kuwa bani da kamarki a duniya Allah ya Miki Albarka bana so ma ta fito ta hanyar da ba daidai ba Indai Allah yayi za'a saketa ne again Kinga dama kuskurena nake so na gyara,cikin magana kasa kasa nace an gama Inshaallah zata dawo muyi ta Addua Kuma zan tsaya maka iyakar iyawata Baffa ai Kai namu ne tun a baya,Baffa Yace daina tuna min na tuba wlh, Nawwar ne ya sakko daga sama ya iske mu Ina zaune Baffa ma Yana kujera a zaune Muna ta hira, yaji dadi a ransa sosai ya rasa alakarmu da Baffa da muke hira sosai, Yana zuwa na mike na kawo Baffa kayan ci da sha,Kuma ya zage yaci ya koshi,Nawwar sai mamamaki yake Suka gaisa da Baffa,yace yau ziyara na kawo muku,shi dai Nawwar yasan ko Sabreen bai taba zuwa gidan ba sai Rabiah da baya son auren.

   Haka shima ya zauna Muka dinga ta hira,ya Dade a gidan sannan ya tafi,Yana tafiya Auta Nawaf yazo tsabar tsaurin Ido na yaron nan mota ya dakko ba a sani ba da kyar yake kallon gabansa haka yazo har gidanmu na fito zanje part din su Star na ganshi harda jakar kayansa, Nawwar ya fito zai fito shima ya ganshi yace Kai motar ubanwa ka dakko motar Baffa fa yaushe ma ka iya ganin gabanka? Auta yace Yaya Ina kallon gabana Mana idan naje fitsari,dariya ta kamani Nawwar harda min dakuwa ya min ambola Yana dariya,Jakar Auta na karba nace wata daya zanyi Aunty,Nace oyoyo muje ciki muka koma na Kai Masa jakarsa part din Sabreen data bari ya Sha gyara,yana zuwa harda cire agogo ya ajiye a saman gado yace kawo min shinkafa ni idan banci shinkafa ba bana Jin dadin duniya,kawo Masa nayi da ruwa da lemo wai yace ki kawo min fresh milk nace wannan Kuma baka Isa ba sai dai kaje da kanka,Zan fita yace Ina kawayenki ne Aunty? nace ai suna gidan nan an basu part guda amma wasu duk sun mutu na bawa Auta labari yace Allah sarki Allah yaji kansu fatan dai ba wannan Wise din ni kin San ita nake so,Kai Amma da tsaurin Ido kake Nawaf tafi karfinka ai nawa kake,yace wallahi da za a aura min ita Zan iya Zama Kuma na riketa tsaf nifa a SS2 nake fa ai na Isa aure,to girman aji ne aure,ke dai ba ruwanki ki hadani da ita, nace Indai itace gata gaka ba ruwana idan ka Sha mari.


   Part din su Wise na Shiga Ina dariya na basu labarin Nawaf,Wise tace kaji shegen yaro sai dai ubansa,nace ke karki zagar min uba wallahi uban miji uba ne,to Allah ya baki hakuri Mrs Nawwar nace Ameen Ina masifa,Wise tace wannan Ina zai iya dani, Wai ba yaron nan da yazo da biki ba? Nace ae Suka Yi dariya Sera tace karki kawo shi wallahi yaro haka Kawai a koya Masa fitsara nace hauka nake Nawwar yace mun lalata Masa kani domin bakin nan naku da babu sakata,shi kuwa Auta Yana Gama cin abinci sai ganinsa mukayi a part din ya shigo yayi sallama yana wani iyayi,su Star sai kunshe dariya suke,Wise tace Dana yau kazo,Auta yaji haushi yace a ransa wannan ta Isa ta haifi kamata ita din wa,a fili kuwa ya basar ya zauna a gefe,Santana ya fita baya gida ya tafi kasuwa Wai girki zai musu a part dinsu na musamman su Star duk zaman da suke kenan su ci girkin Santana ya kware da girki.


    Wise tace Nawaf Naga kana hamma,yace bacci nake ji Yana ta kallonta ta dakko zanin Atamfa tare da furta zo dan ubanka na goyaka na jijjiga ai Kai a wajenmu jariri ne,Nawaf harda harara ance za a goya shi da zani ana maida shi yaro tashi yayi ya fice ya tafi kallon ball wai yayi fushi,Mandula tace yau Naga balagaggen yaro,wlh Yana Isa aure suyi Masa Kar ya lalace cewar Seraline.


    Dagaci kullum ramewa yake Yana tumburewa sai dan ciki kwajaja a gaba wuya Kamar Sandar kiwo,Gwaggo ma duk sun rasa sukuni,suna haka manyan garin kowa yaji asirin Dagaci ya tonu an gama gane gaskiya yanzu,su Star da shigigi har kotu Suka je a kano,ni naji suna yawan tafiya kano ashe Kara suka shigar akan abinda Dagaci yayi min ni Rabiah,aka Nemo hukumar gidan reno da su ake zuwa kotu har garin Suka je Suka ji gaskiyar labari abinda ya faru da yarsu nan da nan aka fara kawo labarin karar a gidajen Radio,sakayya ni ban San me akeyi ba sai ji nayi kotu na nemana a Kano lokacin Suka bani labarin komai suna cewa wlh baza su kyale ba, da Nawwar Muka je sai da Muka halacci kotu sau biyu sannan aka samu sarki da Kansa yasa aka tugewa Dagaci rawani aka sauke shi daga sarautarsa tare da cinsa tara ta kudade masu yawan gaske,Haka ya siyar da gonakinsa kusan gaba daya gonarsa ta gado ce kawai ta rage,ya bani kudi ni Kuma ba mutunci na karbe na Kai tallafi gidan marayu gaba daya kudin, Dagaci harda cewa Rabi babu tausayi? Ki tausaya min,nace Ni Sanda kuka min mugunta tun Ina yarinya Kun tausaya min ne,abinda Zan iya muku Kawai yafiya ce amma ni bani da hadi da ku bani ba ku kuje Kuma abinda kuka min kanku kuka yiwa,gashi ban fasa ci gaba ba na juya Muka tafi ,Gwaggo tayi tsumu tsumu itama, da kotu cewa Suka yi za a kaita prison nice na nemar musu Alfarma aka kyale su a haka.

   Dagaci fa duniyar ta Masa zafi Aunty Amarya Kuma sun daura gaba da Gwaggo kullum basa zaman lafiya,Dagaci ya Gaji ya saki Aunty Amarya, da Gaji da Gwaggo Suka nada Mata dukan tsiya ta fito zata tafi Suka bita da duka ko kunya basa ji har gefen babban titi suna kokawa mota tazo wacce birkinta yaki tsayawa Kawai ta banke su gaba daya har Gaji.


   Mutane Suka cika wajen aka kwashe su zuwa asibiti,Dagaci ya tafi asibitin Yana kuka abubuwa sun Masa yawa Yana zuwa ya samu Aunty Amarya tayi karaya wajen biyar itama Gwaggo karaya ta Kai hudu,Gaji Kuwa Allah yasa motar kadan ta shafeta bata karye ba.

    Me chemist din kuwa da Gaji Suka je Suka sashi ya min sharrin ciki gaba daya yanzu bashi da kasuwa duk da ba a San me yayi min ba babu Wanda ke saurar chemist dinsa sabo da an bude sababbin chemist,Ni Kuwa Nawwar nasa ya bawa Bala Babban jari ya tura Masa dubu dari uku ya ja jari sai godiya yake min kamar ba gobe.


     Tsabar son abin duniya na Papa kullum sai ya Kira Wise tun Yana Kira yace ya Kira ne ya gaisheta har ya saba da hira,Yau da dare cikin dare suna kwance da Maman Sabreen ya lallaba ya tashi ya barta ya fito Palo ya Kira Wise bugu Daya ta dauka da muryar bacci,yace Sorry na tashe ki ko kiyi hakuri na riga na Saba da ke nifa Ina ganin kamar mun wuce matakin da muke na gaisawa ni gaskiya sonki nake Yi Kuma aurenki zanyi idan kin amince, Wise tayi Murmushi a hankali tace gaskiya anya Kuwa to ka bani dai lokaci nayi tunani yace na baki farin cikina,kece ruhina,Wise tana jinsa tace ji mutumin banza Yar cikinka a fili tace na gode yace dan Allah ki soni karki ce a'a na Riga na baki Amanar zuciya....Amanar zuciyaaaaaaa yaji Mama ta fito tana tambaya uban wa ka bawa amanar zuciyarka? Dama abinda kake kenan kullum tsakar dare sai waya waya haba Yusuf Ashe amanata zaka ci kace baza ka min kishiya ba ka tuna Alkawari fa kayi min,Papa yace na karya shi yau shike nan bazan Kara aure ba ance idan ka Kara aure kofofin budi zasu Kara bude maka shike nan so kike nayi asara tsaki yaja yaci gaba da wayar,Wise tace Uwargida ce ne? Yace itace take min ihu,tace kyaleta kishi ne ni gaskiya Zan fasa auren naka yace kiyi Hakuri Dan Allah kyale wannan tsohuwar hakorinta fa sun Fara cirewa,nace Allah sarki bata da hakora yace ai duk na gaba sun zube tsufa ya kamata da gaske, Wise tace gaskiya kana bukatar sabuwar zuma,dariya ya saki Hahahahaha shi yasa kike birgeni,Mama tayi sororo tana ji yace kiyi mafarki na sannan ki gaishe min da kudadenki, Wise Ido ta zaro tace amma wannan ya cika mayen kudi har kudin Nawa ma na gaishe Masa da su,Yana Gama wayar Mama tace yanzu Yusuf ni zaka cewa hakorana sun zube kayi min sharri,Tsaki ya ja ya mike Mama ta cakumo shi ta kafa Masa hakoran a gadon baya tana cizonsa Yana ihu,tace wannan mene kace sun zube,ranar sabo da bala'in Mama basu yi bacci ba.


     Jamcy ce taci kwalliya ta shigo gidan Nawwar a motarta tana parking ta fito ita ga tsagera tana tauna chewgum tana taku,taci sa'a su Star suna palona gaba dayanmu ta shigo ko sallama,Yar zabil tsawa ta Mata ke koma kiyi sallama,ubanki ma yayi kadan bare ke cewar Jamcy,Ina shegiyar da akace ta gagari kowa ba wacce ta Isa ta auri mijinta gani ni na zo Kuma sai na auri mijinki Nawwar na dade Ina sonsa,Star basu ce Mata kala ba Suka maidata banza ta gama zage zagenta Shuru,Wise ce ta dakko sabuwar hira ya dinkunan Kuwa kin karbo? Nace sai gobe Inshaallah,Jamcy bata hakura ba tace ana magana Kun maida mutum mahaukaci nan ma Shuru basu ce kala ba sai hirarmu muke ta zubawa Muna tafawa,taci gaba da cewa idan Kun hana Sabreen Zama ni nafi karfinku baku Isa ba,Nan ma shewa mukayi muka tafa Muna hirar mu,Jamcy ta kule Kamar ta hadiyu zuciya tayi tsokanar tayi Shuru sabo da bata da abin fada,Tsaki ta ja tace karuwan banza karuwan wofi Yan Iska duk Wanda yake ba dan sunna bane ai dole yayi haka,idan Kun haifu kuyi magana banzaye karuwai,Ni dariya ta bani Kawai kizo ba gaira ba dalili ki dinga tsokana,ba Wanda ya kulata duk magana intayi sai mun saki shewa wannan yafi Mata ciwo ta juya ta fice tana Jan Tsaki,ko da ta tafi ko zancenta bamuyi ba hirar mu Muka ci gaba,Wise tace Allah yasa ta dawo yanzu mun Mata abinda yafi komai ciwo to nan gaba jini da majina zamu hada mata.


    Baffa kwance yake a dakin Iyamami saman gadonta ya sata gaba ya hanata sukuni,yace gaskiya ni a san yanda za ayi dani dan ni gaskiya ku Nemo min matata ai da zugarku yasa na sake ta kune kuka dinga zugani,Iyamami ta juyo da masifa tace kai kaci ubanka yau naga marar mutuncin yaro abinda kake ko Auta bazai Yi ba,Nema kake ka susuce ta ja tsaki,Baffa yaki tafiya yace Allah sai Kun Nemo min matata ba inda zanje ai da Yusuf ne da tuni kuna tausayinsa Ni shike nan kamar bare an ware ni ba a so na ya karasa da muryar tausayi,Nawwar ne ya shigo bayan sun gaisa Baffa yace Nawwar wato baza ka fada min inda uwarka take ba ko? to ai kafin a sameka ni ta sani ita na sani yanzu kazo sabo da uwarka ce ka fini zakewa,Nawwar shi kunya ma yake ji abinda Baffa ke yi, Ya hana kowa sukuni tashi yayi zai bar dakin Baffa yace sai na talauce tukun zakuyi bayani tunda so kuke ku ganni na zama abin Allah sarki a gari,Nawwar tafiyarsa yayi ya bar Baffa da Iyamami suna ta fama.


   Satin Mairo biyu a Kaduna rannan sunje kasuwa da Sadiya kawarta ta sake ganin Rufaida Cele a kasko tana ta yiwa me shago masifa wannan waken suyar kace wani naira dari ta karu akai sabo da tsadar rayuwa ni a awarar tawa nawa ce ribata eyyeee Zan daina zuwa siyayya wajenka Dan Allah jibeka gaba Daya kamannin Yan Tanzania ne da kai,Haka tana mita me shago Yana dariya yace Cele tsiyarki yawa gareta,sai da ya gama zubawa ta dakko biscuits Kato me tsada tace alakoro na Sha shayi da shi,ta dauki kayanta tana juyawa taga Mairo a bayanta ta kafeta da Ido,tace baiwar Allah wai lafiya da wata fuskarki Kamar anyi kilishi da biri, Nuna Mairo tayi da yatsa ke dai da gani koko da miyar kuka sunyi saukar ungulu a fuskarki,Sadiya ta kalli Cele sanye take cikin tsohon leshi riga da zani tace ke wai ke bakya Shan kokon ne aikin banza,Cele tace Kutmar....ta duro ashar ta ajiye ledar wake taci kwalar Sadiya tace wa ya fada Miki Cele tana magana ana maida Mata da martani,karki ganni a Haka kina ganina Kinga Kalar shayi jikina duk shayi ne kwakwaran juyi nayi sai dai kiga Lipton da citta da kaninfari suna zuba kasa shegiya me kunnen bera ta sake jijjiga Sadiya,Sadiya ta shaku sosai sai kakari take,Mairo tace dan Allah kiyi hakuri ta raba fadan da kyar,Cele ta sake kallon Sadiya tace ke dai wlh ko bilget ne ya aureki karewar kudi baza ki taba gyaruwa ba baza ki kyau ba,juyawa tayi Kan Mairo ta nunata da yatsa tace ke Kuma wallahi duk ranar da Muka sake haduwa dake a hanya Kika kirani da Rabi sai....sai...ta zaro slifas dinta ta kwalawa Mairo a goshi tace sai naci uwarki,suna kallo ta dauki Wakenta ta Kara gaba a shegiyar tsohuwar Vespa dinta tana cewa kowa ya matsa ba mutunci,baki bude Mairo Suka bita da kallo.


   Cele wata unguwa ta shiga ta talakawa futuk,gidansu wani mugun tsohon gida ne me dauke da daki biyu sai bandaki a tsakar gida sai kitchen,da alama gidan babu matar aure daga Ita sai tsoho Kakanta,Zuwa Yamma likis ta fito da awarar da ta rigada ta dafa ta yanyankata a kofar gidansu ta kunna wuta tare da dasa kasko ga dankalin hausa shima a yanke a wanke ana soyawa,tun kafin ta Fara suyar ana ta kawo kudi wajen ya cika da samari matasa babu digon Rahama a fuskarta,tana fara suya tace Kai Safiyanu zo dalla ka karba tana cika tana batsewa,Safiyanu ya matso Yana cewa ai sai Cele,bata ko kulashi ba ya tafi,tana soya wata tace Nasuru matso kusa shegen baki Kamar damusa na hamma aka sheke da dariya,su matasa sabo da kyawun Rufaida gata budurwa yasa samari ke dandazo duk bala'inta,tanayi ta kwala Kira Bashariiiiii...ta dari uku ko? Kuma du zaka cinye? Yace ae tayi min kadan ma wlh manage zanyi,tana suya ba tare data kalle shi ba tace amma salka ce a cikinka ko kake tarawa?in ba haka ba Ina tunbinka zai dauke sai dai ko Allah ya maka wata jaka daban ma'adanar abinci ungo ni karbi,ta soya wata ta zuba a Leda tace Hamisu ta hamsin ko yace ae tace uhmm sarkin tsumulmula wannan matarka ta shiga uku kullum ta hamsim Anya Kuwa kana bawa budurwarka kyauta ungo gayyar tsiyarka karbi jeka karka isheni,dankali ta soya na dari biyu tace Usyyyy.. yazo ya karba tace amma Kai kadai kake kwana a daki ko yau akwai banka tusa ungo basir salamu Alaykum dinka,a haka ta sallami matasa da yara ta juyo Kan wani yaro yasha kwalkwabo tace zo Kai ya mato yaro karami tace Miko min shegen kan nan naka duk kwal uku,ya miko kuwa tasa hannu ta zuba Masa rankwashi tace jeka naci ladan aska,yaro ya fara hawaye tace zan karyaka na tatsile ma wuya bar nan dan uwarka asabe me Miya Kamar yawun kaza ta Mika Masa tasa ya tafi sum sum tace Yan banza Wanda iyayenku basu iya gayu ba basu San wanka ba su samu yaro a salle Masa Kai sai kace Shedan,Kaka ne ya dawo da kekensa tace Sannu da zuwa Kaka yace yawwa Jikalle ta a zubo min awarar Nima na lasa,ta soya ta Mika Masa a Leda tace Kaka ka Mana jullof din taliya,in Banda abin Rufaida wannan tsoho Haka shi zai iya wani Jollof cewar wani saurayi da zuwansa kenan,tace Masa'udu Ina ganin mutuncinka kasan hali na tam Kaka ba girkin da bai iya ba Rannan ma cewa nayi wallahi sai yayi Mana fried rice na siyo kayan yi a kasuwa sai da na koya Masa, Kuma watarana Indai nace yayi ya kasa sai nayi sati guda Ina gaba da shi,Masa'udu ya kwashe da dariya yace Cele na gode jiya naje wajen kawarki da Kika hadani da ita,tace Allah ya kuka Kare? Yace mun Sha love,Rufaida tana kallonsa tace kace har abin nan ta maka me Kama da tsaki,yace me? tace kamarsu daya da tsaki dai ,yace oh wai kiss? tace ae mana shi,yace bata min ba ai sai an saba,to Indai tayi maka shi na daina kula Hajara bani ba ita wannan ai Iskanci ne soyayyar Shan minti ku dama samarin yanzu halinku kenan daga Fara soyayya sai tabe tabe da matse matse bada ni ba shi yasa ba ruwana da soyayya idan ka min Zan aureka to ba wani zance go Straight to the point Kawai a daura aure amma wannan Iskanci bada ni ba,Rannan Sailuba tace tayi saurayi kirjinta karmar zai cire,to ba ruwana ni harda dukan cinya taci gaba da suya.


    Zuwa dare bayan ta gama tana zaune tana irga kudi tace Kaka gobe geron yin Rufaida yogourt zai Kare sai naje kasuwa gobe,Dattijon yace Allah ya kaimu ta dakko jullof din taliyarta da Kaka ya girka gata nan a cabalbale tana ci aka yi Sallama ta amsa


    Wani yaro yace wai ance Cele a kasko tazo,zanyi masifa Kaka ta furta yace dan Allah jikalle kije ko alheri ne,dan Kawai kasa baki ne wlh ko wanka fa banyi ba,Haka ta fita tana zuwa ta samu wani Alhaji yazo da motarsa katuwa dama ga haske a kofar gidan ya kasa magana sai kallonta yake Yana kallon kirjinta duk kuwa da cewa Hijab ne a jikinta,ta kalli Alhajin taga ya zura Mata Ido tace Kai idan kirjin kazo kallo dan Allah fisge ka tafi da shi gidanka ka dinga matashi da shi Kawai,wannan da ganinka gwauro ne kai Allah ya kaimu watan azumi sai nasa an maka kidan gwauro, tana Gama fada tayi juyawarta gida ta bar shi nan tana balbalin bala'i,Kaka Yana kwance a saman tabarma a tsakar gida to wa ya taba min ke ne haka? Yo Kaka kirjina yazo kallo ashe shine dalilin Kiran shi yasa na dawo,Kaka ya dinga masifa zai lalata min jika da Ido tambadadde ya tashi ya dakko Sanda ya fito Yana tambaya Ina munafukin yake algungumi lokacin mutumin ya tafi ma tuni,sai da ya gaji da masifa sannan ya dawo gida.

  Washe gari da sassafe Rufaida ta dama kokonta na siyarwa cikin bitikin painti uku ta fita kofar gida da shi,kokon da take damawa ta siyar shine samari Suka sa masa Rufaida Yogour din Cele


   SAUDIYA


    Hamshakin balarabe ne Kyakyawan gaske Wanda ko a larabawan ba karamin Handsome bane haifaffen dan Makkah ne amma a birnin Riyad yake da matarsa,balaraben matashi ne bazai wuce sa'an Nawwar ba zai Kai 30 zuwa 32yrs,sanye yake cikin kayan likitoci Mai kudi ne Kuma gashi likita ne da Shirin fita ya fito Yana sauri ,matarsa Balarabiya ce itama usul me Yar kiba kyakyawa da ita Mashaallah itama ta fito sanye da kayan likitoci domin itama kwarariyar likita ce ta bangaren Mata,Dining Suka nufa Wanda yake shake da kayan abinci irin nasu na larabawa Wanda me aikinsu wata Yar kasar Bangladesh ta gama shirya musu,suna cin abinci suna magana akan matsalar dake damunsu ta rashin haihuwa gashi shi zai iya haihuwa amma matarsa mahaifarta baza ta dauki ciki ba, an auna su akan hakan matarsa Kuma Zafin kishi gareta baza ta yarda ya auri wata ba,Kiran Sunansa tayi tace Ahsan cikin harshen larabci tace bazan iya sharing miji da kowa ba Kawai mu samu wata a Mata dashen ciki ta haihu tunda maniyyinmu zai iya bada yaro Kawai mahaifata ce baza ta iya daukan ciki ba, mu samu a masu zuwa aiki kasar nan a samu wata,cikin larabci yace haba Maheerah ni bazan zalunci kowa ba wannan zalunci ne ko da Zan iya yarda sai mace wacce ta haifi Kamar Yara uku ta Saba da wahalar ciki da dawainiyarsa sannan sai da yardarta Kuma biyanta zanyi kudi me yawan gaske,Maheerah Kuwa tana daga cikin larabawa marasa tausayi da imani sannan akwai nuna kabilanci,a fili tace ba matsala hakan yayi a ranta Kuma tace ta karfi ma zan samo wata ba ruwana wala budurwa wala bazawara Kawai dai ni na samu yaro jinina jinin mijina,suna Gama cin abinci shi da Kansa yayi driving matarsa wurin aiki asibiti sannan sabo da wahala shi kuma ya Kira driver ya kaishi nasa kamar yanda yawancin larabawa ke yi matarsu da kansu zasu kaita unguwa,ga Wanda kudinsu ya kai driver Kawai shi zai tuka.


    Wise Wasa Wasa sosai alakarsu tayi nisa da Papa har Nawwar ya shirya ranar da zasu je garin su Wise a daidaita da iyayenta ta koma gida kafin biki, kullum Kuma suna karatu Wanda Watarana malamin ji yake kamar ya ajiye koyar dasu idan Suka kwabo Masa tambaya,ga Star ta sa Malam gaba kullum yazo karatu sai tayi ta zana Masa hoton love ta dinga nuna Masa a littafi,tun Yana sharewa har ya Fara basarwa.


   Yau Muna zaune Yana Mana Karatu Star suna hada Ido da Malam sai ta kashe Masa Ido tana Masa wani kallon kauna,shi kuwa Malam wannan kallon na Star shi yake tafiya da imaninsa sai Yana cikin karatu sai aji yayi duf ya shagala da kallon Star,yanzu ma yana biya Mana Tafsir na Qur'ani dake daga kasa ya fara yana cewa Suratul Iklasi...surar Khadaituwar  ubangiji,a maka aka saukar da ita,tana da ayoyi hudu,kalmomi goma Sha biyar harufai arba'in da arba'in da bakwa...da ba...daaaaaaaaaaa Yana can suna ta signa da Star  shi da ita,su Muka zubawa Ido muna kallon ikon Allah,Wise ce tayi gyaran murya tace Malam Abulkhari Kalli gabanka da sauri ya dawo hayyacinsa ya fuske Yana basarwa Antaina har ta mike a wando ana gani kuru kuru dake wani yadi ya saka me karamin dinki,Muna ta dariya kasa kasa a boye,ya bata rai ya cukule yana mazewa.


     Kwana uku tsakani Star kafin ta fito karatu sai ta zauna tana ta faman tsala gayu duk Muna can anyi nisa a karatu Muna ta bada hadda,Malam wajen zamanta yake ta kalla Yana so ya tambaya Yana Jin kunya can dai ya gagara daurewa yace Wai Ina nutsatsiyar Yarinyar nan ne? Muka Fara kalle kalle Muka hada baki har Santana Muka ce Malam ai duk cikinmu ba Nutsatse mu,yace akwai Mana wacce tafi kowa nutsuwa wannan me hankalin me sunan tauraro,dariya Muka kece dama mun San Star yake nema matar da tafi kowa Iskanci zai ce nutsatsiyar cikinmu,Yar Zabil tace mugun ciwo ya Kama Malam,Mandula tace ahayeeee Muka saki guda ayyiriririri ganin Star ta fito cikin gayu,Sera tace Malam ga wankan ka nan,Malam harda sosa keya,nace yau Nawwar sai yaji labarin nan Mun rinjayi Malam,Ina karyar malinta a guji sharrin mata,Wise harda waka karuwa tayi rana...karuwa tayi rana....Malam ya daure Fuska Kawai yaci gaba da karatunsa irin ba raini.

Masu Shari wlh Kuna birgeni

AsmaBaffa

No comments

Powered by Blogger.