Yar Aikin Karuwai 36-40

 


🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼

     LITTAFIN KYAUTA NE

            36-40

Official

By

AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_nfection_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_


_Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*08089965176*

*07084653262*




Page naku ne


Ruky

Kukuwa

Maman Khadija Abj

SummynDaddy

Fatimalawan600

Maman Twins

Ammey laylah

Umminnas

Serdieycute

Wuta(Golda)

Hafsat I Atiku

Khairiyya Ahmad

Darlin Queen

~Umme


Gingina ga

BINTA UMAR ABBALE

UMMIN SADDIQ

MHIZ AWWAL






        Sabreen tana Jin Dadi na gudu da kaina sai ganinmu tayi ya dawo dani tace wlh baka Isa ba bazan zauna da Yar iska ba ni da kaina zanyi maganinta,ban kulata ba shima bai kulata ba ya shirya ya bar gidan ya wuce gidan Khaleel,Ina zaune zuwa yamma ban San komai ba wasu kartai su biyu Suka fado min daki,hannayensu dauke da manyan bulalai,Sabreen ce ta shigo tace Na'alhaji ku cika Mata aiki yanda nace kudi Zan biya,Ina zaune Ina kallon ikon Allah,mikewa nayi tsaye,Sabreen tace ke ba Yar iska ba wlh baza ki zauna min a gida ba ai ba gidan ubanki bane,Cikin kartin nan Daya ya kamani da igiya a hannunsa Muna kokawa Ina cewa ka sake ni zanci uwarku shegu tsinannu Allah ya Isa a Haka Suka daureni da igiya Kamar goro kowanne a cikinsu da bulala Suka Fara zubaba min ita Kamar daga sama aka basu umarni,Ina ihu amma Sabreen cewa take ku karawa shegiya sai ta daina motsi gobe ai baza tazo gidan wata ba,tunda Naga zasu cuceni yanda tace sai na daina motsi ai Ina Jin haka da Suka sake tsula min uku sai nayi suman karya na daina ko motsi tare da dauke numfashi na, Sabreen ta tuntsire da dariya tare da cewa ku barta haka ta Suma muje na biyaku,Suka juya Suka fice sannan na saki numfashi na amma dukansu dukane bana Wasa ba gadon bayana yayi rudu rudu ya farfashe,na fashe da kuka nace wlh sai na rama,Ita Kuwa biyansu tayi Suka tafi Ina nan kwance a kasa sun daureni sun tafi,inda Allah ya taimakeni na dinga ihu ban daina ba cewa nake wayyo Allah azo a taimakeni har Nawwar ya dawo yaji ihuna a daki da gudu ya shigo ya ganni a daddaure da igiya,na saki kuka me karfi,yace waye ya Miki haka nace Sabreen cikin kuka,reza ya dakko ya yayyanke igiyar na tashi zaune da kyar nace kalli bayana na zuge Masa zip yaga yanda bayana yayi rudu rudu bulala Uku kawai wani wajen har da jini abinka da Fara dama,waiyazubillah ya furta ya fita a fusace,Ni Kuwa wayata na jawo na Kira Seraline tana dagawa na fashe da kuka nace ku taho za a kashe ni matar saurayina tasa Yan Iska sun min dukan tsiya sun fasa min jiki kuzo gidan na fada Mata Adress,Seraline Wayar ta ajiye daure take da guntun towel daga wanka ta fito ma taji wayata da ihu ta fito tana kwalawa karuwan Kira harda Yan daudu su biyu,matan Suka zo su wurin goma tace an taba Mana Yar uwa,Yar uwar mu tana can Rai a hannun Allah matar Saurayinta ta kawo Yan Daba sun Mata mugun duka.


   Santana dan daudu yace ahayye an tabo jarabar duniya yau za aga bala'i ya rike haba yace oh Kinga star ku dakko makamai,Nima ga Nawa ya suro wani dogon ludayin juya miya,Daya dan daudun yace yau nake Jin jaraba shike nan sai a nemi illata Mana Yar uwa laifinta ko na mijinta ita Miracle sabo da Allah Ina ruwanta service fa aka dauketa ya tafa hannaye biyu yace kuzo mu kaddamar musu ke Yar uwa kiji samun waje dan Allah ya dakko almakashi yace aski zanwa shegiya a local government dinta sai na samu tsuliyar shegiya na aske ta kwal kwal Zan Mata muje,Star tace yau idan na dinga zubawa Yarinyar mari sai ta tafi gidansu a kafa, Wise ma daga wanka ta fito,itama Yarzabil haka,Manduwa da Star sune da wata matsiyaciyar shiga domin manduwa mini skert ne a jikinta sai half vest,ita kuma,da sauran karuwan duk ba me shigar mutunci su goma cif Suka hadu zasu je,wasu Suka taho Suma Suka ce ai dole Suma suje su kwatowa Yar uwarsu yanci,mutum biyar harda yare Suka karu,kananan mota uku taxi uku Suka cika su Sera dukkansu daure da towel su uku a haka Suka tafi sauran Kuma Babu me shigar mutunci ga Yan daudu mutum biyu.


    Suna zuwa kofar gidan masu taxi dinma nasu ne Yan duniya ne harda zana kwabo a kofar gidan Suka danne horn ba dagawa fiiiiiiiii suna zaga wajen da mota wasu da makamai wasu babu,Kuma sunci sa'a ba securities yau a gidan sai me gadi Kara da hayaniya tasa Sabreen data buya a daki gudun Kar Nawwar ya daketa ta fito Jin ihun da karadin tasan ba lafiya ba,har compound ta fito taga an banko kofar gate suna dukan gate karaf kararaf...wata Igbo a ciki tace who is she da karfi,Seraline daure da dan towel tace gata can Suka rugo gidan gaba daya suna durawa Sabreen ashar tsoro da firgici yasa Sabreen ta kasa motsi da kyar take daga kafarta tana ja da baya,Seraline ba jira tana zuwa ta cakumi wuyan Sabreen ta kwada Mata mari,ta sake kwada Mata mari tace dan uwarki Yar uwarmu Zaki sa a daka ta sake wanke ta da mari,Star tazo ta hankada Sabreen ta timata da kasa Suka Zo dukkansu Mata Suka dinga jibgarta,Yan daudu ihu Kawai da zage zage sukeyi suna shewa da tafi, Sabreen ihu babu damar Yi sai ta Fara basu hakuri tace wlh bazan sake ba babu ruwana da Yar uwarku daga yau,Wise ta make Mata Baki sai da jini ya fito ko a jikinsu Yarzabil harda fisgowa Sabreen nono ta kurma salati tace ko a bariki shegiya baza ki samu kudi ba,wannan a kwalta ba me zabarta bata da nono,Seraline ce tace ku kyaleta haka Naga jikin Yar uwarmu da sauki ganina na fito Ina dingishi,Sai lokacin Nawwar yaji hayaniya yaki karewa ya zaci ma securities dinsa ne suka dawo ya leko ta sama ya hango Sabreen kwance a kasa jina jina da ita ba Dan kwali rigar ma ta yayyage,jini ta baki na fita,jikinta duk rauni,Me gadi ma yana kwance a kasa Yan daudu sunci ubansa sun kwantar da shi a kasa Santana ya Dora kafarsa daya a ruwan cikin me gadi yace da dayan Miko min mudubi a jakarka na duba fuskata ko ta baci,Nawwar ne ya fito da sauri ya daka musu tsawa wannan wanne irin haukane zaku zo min gida ku daki matata,wanne irin hauka ne haka,Seraline tace Matukar za a taba Mana Yar uwa to wlh baza mu Bari ba, ba a taba irinmu a kwana lafiya,baiwa ce ka dauka wallahi duk ranar daka bari aka sake dukanta wallahi abinda zamuyi sai yafi wannan,tsawa Nawwar ya daka musu ya nuna musu hanya yace get out ko yanzu nasa a kamaku gaba daya,Wisa tana gyara daurin towel dinta tace dama ai ba Zama zamuyi ba dole zamu tafi mudai aka taba Mana Yar uwa baza mu kyale ba ko sojoji ka zuba gidan nan wallah sai mun tarewa ko waye Hanya mun Saba Masa kamanni,Ina ji nace ya Isa haka Wise kuje tunda Kun rama min ana Kara tabani zan kiraku kuje,Suka tafi abinsu Suka sake tashin motocinsu Kamar zasu kashewa mutum dodon kunne,Suna barin kofar gidan ya juyo ya kalleni yasan Yana masifa Zan gudu can bariki yace me yasa bakya ji? Me yasa kike da taurin kai? Lokacin Sabreen ta bude idonta tana kuka wiwi tana kallonmu, nace ya za ayi tasa karti maza su min duka daya ya rikeni ya daureni,Ido ya zaro yace ya rikeki nace ae sai da ya rungumo kirjina sau uku Yana taba min nono Kuma itace tace su taba na banza ne na karasa da kuka na fada jikinsa na rungume shi nace shi yasa nace gwara kai ka dinga tabawa tunda kana biyan kudi,Tsaki yaja ya janye jikinsa da sauri ganin Sabreen tana gani, tana daga kwance tace ta tabbata wallahi Karuwarka ce yau gidan ubana Zan kwana,duk dukan da taci haka ta mike Yana tsaye taje ta hado kayanta ta fito tana tafiya da kyar ta shiga motarta,ihu nayi Ina dariya nace bye bye,Me gadi da ya tashi tuni Yana uzurinsa ya bude Mata gate ta fice a tsiyace, Nawwar ya kalleni yace kinji dadi shike nan? dariya da farin ciki ya kamani nace ae mu indai za a taba mu to fa uwarsa baza tayi bacci ba ko waye in ka gaji ka maida ni bariki na ka huta ni banga abin takura ba a nan duk inda Naga Sabreen sai ta San fada damu ba dadi.


      Ido ya lumshe a hankali tare da juyawa ya koma Palo ya fada saman kujera Yana huci zuciyarsa tana Masa zafi ciki na koma nima na zauna Muka Yi shuru ni da shi,ba a fi 15mnt ba sai ga Kiran Baffansa,sai da yayi tunani dama ya daga Yana dagawa yaji ashar sabo da shi babban mutum ne amma Babu Kalar zagin da baya yiwa yaro sai da ya kutuntuma Masa ashar iri iri karshe yace to Dan uwarka Dan ubanka kazo gida Ina nemanka,to kawai yace ya tashi bazai iya driving ba yau driver dinsa na ya tukashi zuwa gida.


    Kowa ya zauna yayi Shuru Yana saurare Nawwar yana kusa da Maminsa, Iyamami itace ta Fara magana tace wallahi Nawwar ka bani mamaki ka bani mamaki tirrr da hali irin naka,Mami a ranta tace ba tirr ba ban haifi dan tirr ba wlh Allah yayiwa dana Albarka Inshaallah sai yaga dai dai,Iyamami tace dama wannan lusarar uwar taku ai ita ke zuga ku wato Kai ka girma mace daya ta maka kadan sai ka Kara da karuwa,to bari kaji ko zaka Kara aure sai dai a dangi a samo maka wacce aka sani aka San iyayenta da asalinsu,Muna wannan gari Wanda ya tara baki garin kazo nazo ace ka hadu da wata ka aura bazai yuwu ba ko bana raye Matukar da sauran yarana a duniya baka Isa ba,idan Karin aure kake so ka koma can danginmu Shuwa ka Nemo Yar dangi idan Kuma baza ka iya ba ka bamu zabi,Kuma ba yanzu ba sai Sabreen ta tara iyali,Mamin Nawwar ce tayi magana tace idan Allah ya rubuta ya zakuyi wannan fa hurumin Allah kuke shiga,laaaaaa......Iyamami ta dafe kirji kunji Salamatu abinda take fada min wato ke ba a Isa ayi magana akan yayanki ba sai kin shiga kin tare musu shi yasa Suka taso basu da tarbiyya basa ganin kowa da mutunci

    Papa ne yace dan Allah ku kalli jikin Sabreen 'yata Daya tilo tace gaba daya matan tsirara Suka Zo da Yan daudu sunfi su talatin Suka Mata dukan tsiya,Sabreen da bakinta yake a kumbure da idonta daya ya kumbure tace ai iya Yan daudu sunfi sunfi su goma,Nawwar ya kalleta tare da furta kiji tsoron Allah lokacin dai kin ji jiki bakya gani dai dai,Baffa ne yace rufe min baki yanzu kalli Yar uwarka kalleta matarka wata banza ta Mata haka idan baka Yi Wasa ba sai na tsine maka,Mama tana gefe tace ato a dauki mataki wallahi idan wani Abu ya samu yata tilo baza aga dai dai ba duk da nima Yar uwa ce amma ai Da baifi 'Ya ba,Sultana ce tace wlh Namiji yafi 'ya ko a gado ba daya bane,Baffa ne ya kifa Mata Mari ta dafe kunci yace uwata tana magana kina magana,Iyamami kuka ta fashe da shi tace dama yaran Salamatu basa ganina da mutunci sun tsaneni ta gama zuga su,Amaryar Baffa Yar gaban goshinsa sai yanzu tayi magana tace ato gwara ku gani da idonku nima da yarana biyu ne rak basa kaunata basa kaunar yarana Kuma jini daya muke dadin abin dai mijin ko kwana baiyi a dakinki sai dai ki dafa Mana a matsayin baiwa kike shi yasa ban damu ba,Iyamami tace ita take jawa kanta da kuturun iyayinta,Baffa ya kalli Nawwar yace ka tabbatar ka gyara kuskurenka idan ba haka ba ga shedu kar ku ce ban fada ba duk abinda na maka kaika ji,Kuma ka tababbatar ko wacece ta bar gidan nan Kuma Kar najita a Daya daga cikin gidajenka Zan dinga bincikawa Kuma Kar a kawota gidana ko bangaren uwarka ta koma barikinta kaji me nace? Nawwar yace naji,Sabreen tace Saura Maganar dazu Baffa,yace Ina sane ai tace dama baka kwana tare da ita Kuma kana da lafiya,idan da kana muamular aure da ita ai da mun ganta da ciki,Nawwar ransa ya Fadi da Sabreen har wannan zancen ta iya fada kwafa yaja a ransa,sai da Suka gama fadansu sannan Suka sallami kowa,Mamice ta Fara mikewa yaranta kaf Suka tashi Iyamami ta furta idan aka zagemu aka ci Naman mu Allah ya Isa munafukai duk kin lalata yara Anya Kuwa wannan jinin mu ce,tafiyarsu Suka Yi Suka barsu suna ta magana akan Mami da yaranta.


     Mami sama ta haura bedroom dinta,yaran gaba Daya Suka shiga Nasira da Hamra ta Fara Kora tace kuje kuyi Assignment dinku ayi Sallah Kuma,Sultana ta kalla tace kije kiyi Sallah ki shiga kitchen kiyi girki tace to ta wuce shi kuwa Autan nasu sarkin ball ya wuce dakinsa tuni,Nawwar kwanciya yayi a gadon Mami ita Kuma tana zaune a gefe a hankali tace wacece? Nawwar yace Mami ba fa wata bace,bana son karya me yasa baka ji Nawwar me yasa kake son sani a masifar mutananne? tunda kasan halinsu Kawai kabi umarni a zauna lafiya,Mikewa yayi ya zauna yace Mami kin san fa tsarin Allah dole haka rayuwarka zata bi,Kuma wlh ni nayi Niyyar taimakonta bazan fasa ba,Ido Mami ta zaro tace sonta kake Yi? da sauri yace haba Mami so Kuma Allah ya kiyaye bata layin Kalar matan Dana ke son aure ma,ni da nake son Ustaziya kullum a hijab Yar Shuru Shuru saliha bana son mace Yar duniya,nafi son me addini da hankali, Murmushi Mami tayi tare da cewa Allah ya baka to,yace Ameen,to fada min tunda kace ba sonta kake Yi ba me zakayi ka taimaketa Kuma wacece ita? yace ni so nake Kawai ta sanadina ta shiryu yanzu dalilin kawota gidana so nake na raineta na bata tarbiyya sannan na aurar da ita,au ashe yarinya ce ma shekarunta Nawa? Mami ta tambaya,yace 22yrs take,dariya Mami tayi tace Dan Allah Nawwar bana son Wasa 22yrs sabo da rainin hankalinka kace Wai zaka raineta ka bata tarbiyya ka aurar da ita,to ki bari Mana kiji labarinta Mami ba kya cin ribar zance


    Kunne Mami ta Miko Masa tace to Ina ji,Murmushi yayi yace to ki daina kallona ma kunyarki nake ji,yau kuma,dariya yayi yace I'm serious,Ina ji,yace Kinga Mami bana boye Miki Abu karki ce nayi rashin kunya, lokacin Sabreen tana min wulakanci Ina nemanta bata yarda ko naje na iske tayi bacci Kuma baza ta tashi ba,lallai maganin Iyamami yayi aiki,idonsa ya rufe Wai kunyar Maminsa yake ji,tace uhum Ina ji,shine naji haushi na gaji Kuma a lokaci Ina cikin yanayi na bukata,Mami tace Allah sarki My son Sannu,dariya ya sake saki yace Mami kunyarki  fa nake ji,to na daina Ina jinka,yaci gaba sai nace bari ma na fara Neman Mata na dinga bin titi shine na ganta,a lokacin ta Yi maka ka dakko ta ko? Mami ta tambaya yace ae,Amma ba abinda ya faru banyi komai ba,Mami Hannu ta daga sama tare da furta ya Rabbi na gode maka Ina Addua Inshaallah yarona bazai lalace ba na sani,daga nan ya bawa Mami labarina kaf da komai har labarina dana bashi cewar Ni Yar tsintuwa ce da labarin Dagaci inda na taso,Mami tana gama ji tace ya sunanta? Rabiah,tace duniya kenan idan kaji halin da wani ke ciki sai ka godewa Allah Kai.


  Abinda mutum zai Fara godewa Allah akai da aka Yi auren sunna aka haife shi ya taso cikin asali da dangi,idan aka jefar da Kai ko akasi yasa kazo a Dan tsuntuwa baka San kowa ba shike nan Kai baka da asali da nasaba,Babu dangi bare uwa da uba baka San kowa ba a duniya sai Kai kadai wannan kadai ya Isa a tausayawa yaran tsuntuwa da Wanda ke gidan marayu Allah sarki kaga rashin iyaye da dangi shi ya taba wannan yarinya da ace ta fada Hannu na gari da shikenan, idan aka samu akasi baka fada Hannun na gari ba to fa ka shiga Uku,a wannan Zamanin wa Yana zina da kanwa,Kani yayi da yayarsa,kanin uba ya Nemo Yar Kaninsa ko Yar yayansa ana samu uba me Neman yarsa to bare mariki Dagaci Wanda ya rike yarinya ganin bata da kowa irinsu Kuma Allah Yana musu baiwa da ba kowa ke samu ba sabo da Allah baya hadawa mutum biyu


      Wannan marikin nata yaci Amana matuka Kuma na tausaya mata,yanzu kaga Wanda ya riketa yaci amanarta ya koreta amma karuwai sun karbeta har fada suke akanta suna daukar Mata fansa,suna kiranta da Yar uwarsu su basu kyamaceta ba Zama ya hadasu na banza Amma sun dauki kansu Yan uwan juna ne,ga masu hankali Wanda basa shashanci sun tsani junansu Kuma suna Yan Uwa musulmai,wani ya taba musu ita sunzo sun daukar Mata fansa Allahu Akbar,kaima gashi Allah yasa maka ita a ranka,a'a Mami nifa ba so ne ba Kawai naga ta lalace ne da yawa shi yasa nake kokarin taimaka mata,Mami tace ka taimaketa da duk abinda zaka iya da karfinka da dukiyarka ka taimaka mata amma kayi da iyawa sabo da mahaifinka idan ya gane Kuna tare zai dauki matakin da baka zato kasan halinsa ita Kuma matarka bata da hankali ka sani Sarai zata sake fada musu,Amma yau Zan bika naje na ganta ashe itace Hamra take cewa kazo da wata ziza kyakyawa Sam bata Yi Kalar Kauye ba,yanzu kaje kayi Sallah in yaso sai muci abinci muje,no Mami bazanci abinci ba nasan ta dafa yanzu Yarinyar fa tana da Yar biyayya abinda nace tana Yi she is so caring, Sabreen bata bani abinci tunda na aureta naci banci ba babu ruwanta amma ita har rokona take yi sai naci dole,Mami kin gani har durkusawa fa,a haka tasan idan Ina Fushi kiji dan Allah dan lokaci kadan ta karance ni she is so brilliant,Mami tace kaji Yar baiwa Kudirar Allah,yace dama sunanta ne Kuwa Kamar kin sani Miracle ake ce Mata,ya sake furtawa,  Mami ki tashi kiyi Sallah tace to ko bakya Yi yau ne?  Slifas din dake kafarta ta dauka tare da jefa Masa ya fita da gudu,Tsaki Mami taja tace kaji min yaro dan Allah Kai yaran zamani Allah ya shirya ta kwanta Kuma bata Sallar Kamar ya sani.bai samu Sallah ba tasa yayi ya dawo gida a Hanya Suka hadu da Iyamami ta fito daga wajen danta tace au hararata kake Yi Nawwar gaba kake dani ko,bai kulata ba cikin takunsa ya shiga sashen Maminsa ya ganta a main Palo suna cin abinci fuskar Mami ya kalla ya ganta da kwalliyarta alamun ba a sa ruwan Alwala ba,sake lekawa yayi tace lafiya wai, Murmushi yayi yace ba komai,Sultana ce tayi magana tace Mami na koshi ni,Zama Nawwar yayi Yana latsa waya yace Wai Yarinyar nan Mami naga yanzu wani yanga take ji kalli tafiyarta,Sultana tasan tana magana zai ci ubanta Shuru tayi,Mami tace ai an Fara Zama Yan Mata baka gani tayi candy,baki ya tabe a ransa yace Mami baki San Yan Mata ba sai karuwai gasu nan kyawawan Yan Mata wata in kaga tana bariki sai kaji Takaici komai Allah ya bata amma ta watsar da kyan a bariki,a fili kuwa bai ce komai ba,Autansu ne ya shigo sanye da 3qtr da Riga armless,Hannu ya mikawa Nawwar harda cewa bros ya gida ya akaji da iyali,dariya Suka Yi gaba daya


    Ko a jikinsa ya zura hannaye biyu a aljihunsa yace me aka dafa? gashi ka gani jullof din taliya bazan ci ba indomie Zan ci ni, okay ka sa kwai kaji Autana,Nasira tace wlh kina biyewa Autanki Mami,sai da Mami ta gama ta dakko mayafinta na Arabian gown din Dake jikinta maroon da hand bag dinta tace tashi Kai mu tafi,Su Hamra Suka ce a dawo lafiya Yaya ka gaida gida,yace to,suna Fitowa akan idon Mama ai da gudu ta fada bangaren Iyamami tace taso ki gani da idonki uwar za a tafi wajen bokaye Yan tsubbu,an tafi wajen masu Juju tsafi Kinga sabo da yau an musu fada sunji basu samu nasara ba,Iyamami ta fito da sauri harda labewa tace anyi uwar banza me watsa yayanta dama nasan aikinta kenan,ai da gani ba sai an fada ba to li'ilafi wallahi,Mama ta rike baki tare da furta ta Kare a kansu sai gobe Sabreen zata koma,Iyamami tace Allah ya kaimu.


Ni Kuwa tun fitar Nawwar  nayiwa Seraline ta kawo min dogayen riguna haka dai na dan mutunci cikin kayana ta dan zabo kala hudu ta bawa Wise tunda ita tana da mota ma itace ta kawo min domin a motarta na koyi tukin mota itace ta koya min ta koyawa wasu ma da yawa,tana zuwa tace Ina shegiyar? nace ta tafi gidansu shima sun Kira shi,tace to idan ya koreki ki min waya nazo na daukeki ai da gatanki kina da mu babu Wanda zai taba Daya a cikin mu ko waye wala arne ko musulmi face mun dauki mataki,nace Wise kin San dai bani da mutunci ko? tace ah sai dai na bawa wani labari,na sake furta kin San dai bani barin ko ta kwana idan fada akace za ayi sai dai a mutu Kuma Ni fada dani baya karewa,Wise tayi ihu tace ai bama cin Kan jaki badai mu ba,na sake nuna kaina da yatsa nace Kuma kin san bani da kunya cikakkiyar fitsararriya ce ni wannan karuwancin ban shige shi da Wasa ba da karfina da komai nawa na tattaro na shiga Kuma na Fara kenan ba fita,wise tana ihunta tace yes ooooo mu mutu a ciki,center table na daka da hannuna Ina tsaye Ina zaga palon nace to an taro match wannan Yarinyar sai na hanata Shan ruwa ko wace ci uwarta dan burar....wise ta kundumo ashar nima na lailayota na dura nace ba dai sabo da Namiji take wannan haukar ba sabo da bana ko rike Masa hannu a gabanta shine take wani ae yane to wannan show din dole ya shigeta na girgiza gashina nace zata ga tsiya,Wise tace tasan Kuwa su waye masu siyar da gidan kashi,duwawu fa muke siyarwa ka shiga ka fita ka biya,a mazan ma me ta sani ba a cinyewa shegiya duwawu shi yasa  Zama nayi na tattale kafafuna sosai na baje tare da furta na tabbata bai taba nacking nata sosai ba,Muka kyakyace da wata mahaukaciyar dariya irin ta Yan duniya Muka tafa,Wise tace me Zan Miki yanzu Yar aikin Karuwai a da,nace a ai yanzu original karuwa ce cikakkiya ,tayani gyara gidan nan please mu canjawa furniture din nan wajen Zama yayi local yanda aka saka su baiyi making sense ba..kafin na rufe baki sai ga Yarzabil da Star Muka dinga iya shege gaba Daya Suka tayani Muka hadu Muka gyara gidan nan neat ko Ina Yana sheki da kamshi na musamman,dakinsa Dana Sabreen ne bamu gyara ba,Suka ce dakin ogan fa? Nace zanyi da kaina yanzu,sallama Suka min Suka tafi abinsu,Ni Kuma ban taba shiga dakinsa ba sai yau na shiga na gyara ko Ina Kal Kal har toilet dake gadon me turawa ne sai na canja mishi position shima komai na gyara yayi wani mugun kyau na turare da kamshi, na kunna ac na rufo dakin,a gurguje nayi wanka da sallar Isha sannan na shirya cikin wando tight fari tas da wata rigar material sharara daga kirji zuwa ciki an Mata landing bangare daya yayi tsayi sosai har kasa rigar take tabowa gefe Daya Kuma iyakarta gwiwa,grey color ce tayi kyau rigar sosai ba karamin kyau nayi ba dake dan jikina dumi dumi yake da Yar kibata kadan,baza ace dani ramammiya ba Kuma baza kace dani me kibaba, gashina da yaci gyara jelarsa na yawo a gado bayana na daura wani Dan mitsil din dankwali me santsi Wanda yanzu aka dawo da yayinsu grey Kalar rigar nayi kyau ainun Ina kamshi na Shiga kitchen na Fara shirya girkina na musamman kamshin turaren dakin da kamshin girkina ya gauraye palon a haka naji dirin motar Nawwar..


      Parking yayi a gidansa ya fito ya zaga tare da budewa Mami ta fito suka Shiga ciki,kofar yaji a kulle door bell ya Danna,hannuna na wanke nazo da sauri na Danna code din kofar palon na bude,Yar matashiyar dattijuwa na gani me Kama da Nawwar da gani ba tambaya mamansa ce,Murmushi nayi nace oh Sannu da zuwa kuyi hakuri wlh Ina kitchen aiki nake,Mami ta saki baki tana kallon wata princess a gabanta a ranta tace kyakyawar gaske ce gaskiya,Murmushi Mami tayi tace ba komai Suka shigo,Mami ta kalli cikin palon ko Ina ya canja ba yanda tasan shi ba ga tsafta ga kamshi ta ko ina ga Kuma girkin kamshin ya Isa,bayan sun zauna durkusawa nayi har kasa nace Ina yini,ta amsa da lafiya lau,na sake cewa ya gida ya yara? tace duk lafiya tana Murmushi,Nawwar na kalla Muka hada Ido nace Sannu da zuwa hope dai ba a maka komai ba ko ka tafi Ina ta tunani,yace ba komai,girkina na tuna akan wuta na mike da sauri nace girkina na shige kitchen da guduna Wanda ya bawa Mami dariya,ruwa da lemo me sanyi na kawo Mata a tire me kyau na tsuguna tare da tsiyaya Mata a glass cup nace kiyi hakuri ban San wanne Kika fi so ba Kawai na dai dakko na Mika mata,Mami ta karba tana cewa ba komai ta Sha, na koma kitchen na dakko Mata snacks din da nayi da rana na kawo Mata nace gashi kafin na Gama girkin kiyi hakuri,Murmushi Mami tayi,Nawwar yasa Hannu zai dauka caraf na rike hannunsa nace bafa naka bane,hannunsa ya janye da sauri Yana hararata nace ai Kuwa sai dai ka harareni ma na Mama ne,yace ke Wai sa'anki ne ni, baki na turo na murguda Masa baki, Mami tana kallo,Tsaki yaja,na koma kitchen na dawo na zauna a kasa ganin Mami na kujera ban zauna kujera ba,tace   nice Maman Nawwar,nayi Murmushi tare da cewa Sannu Mami,tace yawwa naji labarinki ya bani...kafin ta rufe baki nace wlh ya za ayi kin San kowa da sana'arsa to ni tawa kenan Muna dan siyar da idon garin ni tunanina ya fada Mata karuwa ce ni shi yasa,Kunya ta Kama Nawwar ya min wani mugun kallo yaci sa'a Kuwa mun hada Ido nace ai gaskiya ce a fada Mata gaskiya ta sani,Mami tace uhmmm ta jinjina Kai tace Allah ya kyauta, nidai dama cewa zanyi dan Allah karki shiga Harkar Sabreen kiyi hakuri ki kyaleta Kinga ko wace dole taji kishi da haushi a kawo Mata budurwa irinki gida,Nace Mami wannan bata son Nawwar ba wani kishi da take Kawai tana da dalilin tsanata,kin San ni nasan rayuwa ce mu duk irin wannan mun San shi muna karantar mutum,Kuma da alamu tana shaye shaye Kawai dai baku gane bane,to koma mene dai Ina rokonki dan Allah karki sake nace to Inshaallah Mami,mikewa tayi ta fita tare da Nawwar


    Suna fita tace Nawwar wannan Kuwa zata shiryu naji har alfahari take yi da karuwancin nata, Inshaallah Mami zata daina yanzu ai bata yi tunda Muka hadu bata sake kula kowa ba,to shike nan ka dai kiyaye Banda kebewa da mace wacce ba muharramarka ba kaji na fada ma,yace to ya tuka mota ya maidata gida suna ta shawarwarinsu Yana kaita ya dawo gida lokacin na gama girkin na gyara kitchen Ina jerawa a dining ya shigo da sallama na amsa, Dining ya karaso nace wanka fa? Kallona Kawai yayi yace Ina ruwanki abinci Zan ci,okay Zama yayi nayi serving nasa na zauna ni ban zuba ba,Yana cin abincin sai Naga Yana dan tunani nace akwai matsala ko? an maka fada sosai? Kai ya girgiza min a hankali Wai no,nace to meke faruwa ko nice,bai kulani ba,nace then sai na tafi gidanmu gobe...wani mahaukacin kallo ya min Wanda yasa nasa hannuna daya na rufe bakina da sauri.


     Yana gama cin abinci ya tashi na zauna kallon film Ina latsa sabuwar wayata dana siya da kudina iPhone me tsada,Wayar hannuna ya kalla ya iske Ina dannawa bai kula na siyi waya me tsada ba sai yanzu ta bayana ya tsaya na shiga WhatsApp group dinmu na Yan gidanmu karuwai Ana ta turo Xvideos yanda ake sex different style latest idan ya shigo gasu nan sunfi Hamsim tarrrrrrrrr yaga suna shigowa ban zaci Yana bayana ba ma,Wayar naji an fisge a hannuna na juya da sauri Naga shine, yace dama abinda yasa Kika siyi Wayar kenan,ya zaro sim Dina ya jefo min Yace idan baza ki rike karama ba keypad to ki bar rike waya ki zauna haka,nace Dan Allah ka bani na daina bazan sake ba please nace dubu dari uku na siya fa to ka biyani kudin Yana taka steps yace Zan Miki transfer


    Washe gari ranar Kwanan Mami ne abinci tayi ta Kai Ma Baffa part dinsa ta dawo sabo da baya bata kwananta ta rigada ta Saba zata Yi girki amma sai dai Amarya ta kwana da shi,dakinta ta koma sai ga Baffa ya shigo Yana fada gaba daya kin bata min Yara baki iya tarbiyya ba wayarta tana hannunsa Yana dannawa Mami tace me nayi Kuma,Kamar Sultana ce zata shigo wajena na bata kudin shopping amma yarinya tana hararata kece Kika koya musu amma ba komai Zan iya kwashe yarana na kaisu inda za a basu tarbiyya tunda ke baki iya tarbiyya ba ai Ina da wata matar sai na Kai su can,gaskiya ka isheni Kuma abinda ake a gidan nan ya ishe ni fa cewar Mami,au na isheki ma Kika ce? Mami tace ae ka isheni yanda nasan Nima na isheka da sauri ya furta kwarai kuwa kin isheni nima kin addabi rayuwa ta ya buga tsaki tare da kade babbar rigarsa ya bar part din Mami,Mami kwanciya tayi a saman bed tare da furta tabbas da kayi kuka a cikin jirgi gwara kayi farin ciki a Napep ga kudi ga gida har gida babu farin ciki amma ga wasu talakan suna Jin dadinsu.


    Zuwa Yamma Mama da kanta ta maida Sabreen suna shiga sanyi da kamshi ya dake su,palon Suka bi da kallo yanda komai yake shining,Mama ta kalli Sabreen da mamaki tace badai itace tayi aikin ba? itace ai Yar wahala ce sosai,baki ta tabe ta sake cewa naji kamshin girki na tashi ko itace a kitchen? Sabreen tace itace ai Yar wahala ce,sallama Mama ta sake kwalawa na fito rike da wuka da albasa a hannuna nace Sannu da zuwa Mama,Mama tace Kan uwarki ce Maman,kaga Yar iska ohhh wato yanka mu Zaki Yi ko ki sare mu da wuka shi yasa Kika fito Mana da wuka ,lallai duk abinda aka ce kinyi Zaki aikata ashe gawurtacciyar Yar daba ce bayan karuwancin,Ni na zaci me gidan Yana gida ma shi yasa nayi sallama ke kin Isa na Miki sallama karuwa,ohhh dama bai daukeki daga gidan nan ba,tambadaddiya me bin mazajen wasu,to wallahi tun wuri ki Fara hada kayanki ki bar gidan nan, baki na washe tare da furta Laaaaaaa ashe kin San ni karuwa ce,bari na sake tabbatar miki me dattin dankwali cikakkiyar karuwa ce ni na dade a cikinsa ki godewa Allah gidan Mijin yarki na zo ba gidanki ba gwara ki rufawa kanki asiri idan ba haka ba gobe da mijinki zan kwana,Ubana yafi karfinki wlh banza Fasika me bin maza cewar Sabreen,wani kallon banza na musu na furta a haka Kuma na kwace Miki miji tunda yana cinye min duwawu ya daki ta baya ya daki ta gaba ya daki center, Mama baki ta rike tare da sakin salati magana ta inganta,nace au da Wai tantama kike? to bari ki gani na wuce ta Gaban su na haura sama nayi knocking kofar sa lokacin Yana ciki Yana fesa turare ya shirya cikin wani yadi me tsada ruwan kwai Ina daga bakin kofa ko dakinsa ban shiga ba nace kazo kayi baki,kofar ya bude Muka jero Muka sakko kasa Mama tace kayi asara Nawwar,Nawwar Fuska ya bata yace nifa ba wani abu nayi ba na sabon Allah ba Kuma Naga dai gidana ne,Mama kuka ta saki tace shike nan Nawwar an Masa asiri yanzu ni surukarka kake zagi sai ta juya tana kuka ta fita driver ya ja ta sai gida.


     Sabreen ta kalle shi tace kaji dadi uwata ta tafi da kuka,yanzu uwata zaka ciwa mutunci akan Karuwa sai itama ta haura sama ta fada saman gadonta tare da fashewa da kuka,Nawwar dai ya rasa me ya musu, kitchen ya sameni yace Gama abincin muci sai na canja Miki gida,to nace Ina hawaye,fuskata ya leka Jin Ina shesheka,kuka kema kike yi to ke Kuma me nayi miki,a hankali cikin muryar kuka nace ba komai dan Allah ka kyaleni na koma inda nafi wayo inda babu Wanda zai takura min,Tsaki ya ja ya juya tare da barin gidan gaba daya,gidan Khaleel yaje a garden ya same shi babu kowa sai aiki da yake da system saman carpet din ya zauna tare da furta wajenka fa nazo,Khaleel System din ya ture gefe tare da furta Ina jinka,Nawwar labarin irin halin da yake ciki ya bashi,Khaleel Yana gama ji yayi dariya yace dama na fada maka wallahi Matukar aka sani baza ka kwashe lafiya ba,gashi Baffa yace ba gidansa bare a kaita wajen Mami Ni Kuma dangina basa kusa bare a kaita gidanmu,Kuma gaskiya ko wacece tsakani da Allah Dole baza ta yarda a kawo Mata sankaceciyar budurwa irin Rabiah ba,Kuma baza ka fita daga zargi ba a wajen mutane dole za a ce Karuwarka ce tunda har alfarhari take da karuwancinta dole a zargeka nace ka kyale Yarinyar kaki ji ance sonta kake Yi kace a'a ni gaskiya ban san me zance ba a Kai shawara guda ce ka aureta Kawai Kuma kafin hakan ka Kama Mata gida haya Wanda ba Wanda ya sani ga Baba kulu Yar Aikinmu mu baka aronta su zauna tare ka dinga kula da komai nata


     Nisawa yayi yace Ina tsoro gaskiya Kar ta dinga guduwa,Khaleel ya Bude bude Baki tare da furta to Kai Dan Iska sai kace wata Yar uwarka,Nawwar yace Zan gwada hakan ya zanyi amma wanne gidan za a sata yace wannan ai normal akwai gidan Dana gama a Nmandi Steven Estate karami 2 bedroom flat sai Palo da kitchen ai na gama biyan kudin gidan Rannan ma Maman Aabid tace na zuba furniture Kuma na zuba dama tunani nake na bawa kanin Babanmu ya zauna a ciki naga gidansa ya lalace amma yanzu ta zauna anan idan ta tashi sai nace su koma kawai,Nawwar yace ba damuwa a tura Baba kulu ta gyara gidan anjima sai na kaita,Khaleel yace idan ka dakko ta ka biyo ka dauki Baba kulu sai ku tafi gaba Daya sai su hadu su biyu su gyara gidan dama ai ba wani dirty,Nawwar yace thanks a Nan suka rabu Nawwar Yana tunanin Kawai ya auri Rabiah








AsmaBaffa

08061929616

No comments

Powered by Blogger.