Yar Aikin Karuwai 11-15

 


🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼

      LITTAFIN KYAUTA NE



               11-15



Official


By

AsmaBaffa

08061929616




SADAUKARWA ZUWA GA DUK YARAN TSUNTUWA







Page naki ne 

MARYAM T BALIYA








        Nawwar a gurguje ya fito cikin shiri yasha wankan wani danyen yadi milk shara shara,gashinsa yaci gyara na gogaggun matasa kamar wani bature Yana zuba kamshi,agogonsa me azabar tsada yake daurawa yana sakkowa daga steps wani Yaronsa ne ya fito Masa da Yar karamar jakarsa wacce ya shirya kayansa da sauran abin bukata ya wuce Masa da ita ya saka a boot din mota,Sabreen tana dining tana breakfast sanye cikin kayan bacci tana ganinsa ta dauke Kai Wai ita me aji, kallo ma bata isheshi ba,har yanzu bai duba inda ya ajiye kudinsa ba bare yasan ta ebi wasu ba,Zama yayi ya hadawa Kansa tea yana Sha Yana cin chips sai da ya koshi sannan ya dauki wayarsa yace na wuce Kano Ina da meeting a can har na 2weeks,shekeke ta kalleshi ko a dawo lafiya babu tace to Kawai ta mike tare da haurawa sama,baki Nawwar ya tabe ya daga Kiran wani abokinsa Khaleel suna waya Yana fada Masa ya tafi kano,fita yayi ya shiga mota ya kame a baya securities a mota uku suna take Masa baya,gidansu ya fara zuwa tare da yiwa Maminsa sallama sai yaje ya samu Papa Yana gida har dakinsa ya shiga bayan sun gaisa Mama tace kaga dana ga iya wanka ga kyau,Murmushi Nawwar yayi ba shiri,Papa yace ai Yar mu ta dace,Sumarsa Nawwar ya shafa sannan yace Papa dama Kano zanje Ina da meeting da wasu turawa sunzo daga Finland akan business dinmu zanyi sati biyu,Papa yace a'a to Allah ya bada sa'a ubangiji ya ida nufi,Mama ta furta Allah ya tsare hanya yace ameen ya mike yace na tafi sabo da jirgi ya musu sallama ya fito direct part din Iyamami ya nufa kakarsa kenan,zaune ya isketa a kujera ta tasa katuwar tv gaba tana kallo tana tauna goro,Dan Nema sai yau aka ga damar zuwar min dama nasan ni ba kaunata kake Yi ba sai kayi sati ban ganka ba auren ma bana Yi na sake ka,Murmushi Nawwar ya saki yace dama ni me zanyi da tsohuwa ga matata sabon jini dama sallama nazo na Miki zanje Kano Ina da wani meeting, Iyamami tace aikin kenan to Allah ya tsare na zaci da matarka zaka tafi ma,ai ba dadewa zanyi ba,to Allah ya bada abinda ake Nema yace ameen tare da zaro kudi da yawa ya bata yace ga kudin cefanenki tunda na bawa Amarya karki ce na zalunce ki,dariya ta dinga Yi tayi godiya ya wuce Suka wuce airport.


     Bangaren su Mama Kuwa Yana tafiya Papa yace bar shege ya gama tara Mana mu gaje dukiyar,wani ma yaji cewar Mama.

    Nawwar yana zuwa Kano wani Yaronsa yazo da mota ya kaishi green palace hotel inda aka sauki turawan kuma a nan hotel din zasuyi meeting din kullum har a Gama,bai ko zauna ba kayansa Kawai ya ajiye yaje inda zasuyi meeting din dama shi ake jira,Yana zuwa suka Fara basu gama ba sai bayan Sallar Isha,wanka yayi da Sallah sannan ya zari motar da aka bar Masa ya fita dan zaga gari sanye cikin farar jallabiya me tsada.


   Rabi ina sauka a Kano ban San inda nake ba haka na samu wani lungu na fito da yagaggen Hijab dina ja,ya gama fatattakewa haka na saka nace Neman Sadaka yo ai sai anyi Kalar tausayi sosai a kasar nan basa ba da Sadaka sai anga mutum ya kusa mutuwa sabo da wahala,ni Rabi ina maganganuna ina canja kamanni nace gani jajir ai dole na Zama Yar dukununu na nemo gawayi a hanya da kyar na samu na dandaka da dutse na dan shafa kadan a fuskata Kamar me shafa powder nayi wani duhu,hakorana ma duk na goga musu bakin sukayi Kamar sunyi tsatsa in ka kalli Rabi Kamar ba ni ba,tafiya nayi me uban nisa ga rana tayi sosai sai da na samo wata makaranta wacce babu gate ta gomnati ce na shiga na samu saman baranda na ajiye kayana a nan sannan na fito gefen titi tare da shanye hannuna Daya ya dawo Kamar me shanyayyen hannu ina tafiya ina cewa a taimaka min sabo da annabi a taimakeni na samu abinci, na koma dai dai wajen danger inda motoci ke tsayawa jiran a basu hannu su wuce ina bi ta tsakiyar motoci ina a taimakeni sabo da Annabi,dan me Mana ruwa da iska abinci ya gagare mu,wani ya sauke glass zai siyi charger naje wajen ina Alhaji adubi girman Allah Allah ya kaika gida lafiya canjin ishiri ya mika min ni Rabi na karbe ina Allah shi Albarka,matarsa dake Gaban mota tace na tsani almajiran Nan duk su damu mutane wasu ma sunfi ka kudi da gatansu sabo da mutuwar zuciya sai su fito bara,mijin yace ai baka San wa zaka taimakawa ba a haka wasu ne Suka bata wasu,wasu da kike gani dole ce ta sasu bara baki San mene dalili ba.


    Na hada uwar zufa sosai amma daga goma sai biyar sai ishirin yinin ranar gaba daya kudin abinci naci dasu zuwa Yamma na koma makarantar inda kayana suke naci sa'a Kuwa lokacin Yan makaranta suna hutu sai na fito wasu gidaje dake kusa da makarantar na lallaba na leka wani gida na talakawa sosai ai Kuwa a zaure na iske wani dan baho karami na dauke shi na gudu tare da komawa makarantar na ebi ruwa a tuka tuka din na duba jakar kayana na dakko sabulun wankina na zaga bayan aji tunda ajujuwan a rufe suke me gadi ma ya tafi hutu abinsa a can a tsorace nayi wanka na canja Kaya sannan na Kara Nemo gawayi na mulke Fuska ta na kwanta a barandar Ina hutawa bacci ya sace ni sai bayan Sallar Isha na farka,a gurguje nayi Alwala tare da Sallah sannan na sake Fitowa cikin dare ko zan dace,ko da na fito ban iya bara ba sai yawo Ina ta kallon birni ko Ina haske Kamar Rana Yan Mata da samari da Yan gayu ana ta lailaya Kan mota gaba Daya kallo ya dauke min hankali Ina ta yawona har nazo bakin wani hamshakin Hotel na tsaya Kawai Ina kallon haduwa motoci sai parking suke wasu a ciki wasu a waje,Yan Mata Kuwa Subhannallahi ana ta shiga dasu da manyan Alhazawa wasu ana sauke su a napep,wasu sunyi gayu suna zaga wajen masu so suna samu suna Shiga dasu ciki,sai zare Ido nakeyi Ina kallo.


    Ina nan tsaye wani kamshi ya daki hancina Wanda ban taba Jin irinsa a duniya ba,kafin nayi motsi wani azababben matashi ya wuce ta gefena,Nawwar kenan hannunsa dauke da ledojin take away,wayarsa ce tayi Kara ya Fara lalubota ya zaro Wayar ya daga tare da shigewa cikin Hotel din, Wallet dinsa ce ta Fadi bai kula ba sabo da ga waya ga ledoji a hannunsa har ta Fadi bai sani ba,Ina kallo da sauri na karasa kanta na dauka tare da budewa ATM card ne kala sun Kai biyar a ciki sai wasu kudin Amurka dollars amma dake ni Yar Kauye ce ban San Mene ba sai na tabe baki nace aikin banza babu abin arziki a ciki ma bari na jira ko zai fito ya amshi abarsa,waje na samu nesa da wurin na zauna a jikin wata bishiya,shi Kam bai San ma ya jefar da wallet dinsa ba wanka yayi ya kwanta bacci abinsa,Ni Kam a jikin bishiyar bacci ya kwashe ni sai farkawa nayi Naga rana a kaina,tashi nayi da sauri na koma makarantar da masaukina yake Alwala nayi nayi Sallah wallet din tana wajena,itacen bishiya na balla na zauna na goge bakina tas na kuskure da ruwa,Fitowa nayi Ina dubawa har naje wajen da mutane suke sosai da manyan shaguna ga me kosai a wajen na siyo cikin kudin barata na jiya,na siyo bredi da shayina ba Madara aka zuba min a Leda na dawo makarantar na zauna naci na koshi,na sake shafa bakina a Fuska duk nayi Mata dabbara dabbara da bakin gawayi na saka yagaggun kayana na bara na fito rike da wallet a hannuna


    Ina tafiya Ina kalle kalle Ina zare idanuwa wani ne ya tare ni a hanya ganin Kamar ko zararriya ce ni,yace ke...a gabansa na tsaya Ina kalle kalle,gashina na sosa na kasa tsayawa kyam,kana ganinsa kaga kamili yace Ina Zaki je? nace ai Almajira ce ni,kai ya jinjina yace kina zuwa makaranta Kuwa? Murmushi na saki nace tab ai ni Jahila ce bani da ilimin komai yanzu ma littafi da karatu bazai Shiga kaina ba,galala ya kalleni yace kina so ki iya? da sauri nace ae,yace Okay da zaki iya zuwa dakina da na koya Miki dole sai karatu ya shigeki da yatsansa ya nuna kirjina yace idan bai shiga ta kanki ba dole zai shiga ta nan idan bai shiga ta nan ba to Dole zai shiga ta nan ya nuna gabana da yatsa,nace har ta nan karatu Yana shiga kaji karya,to Malam Iskanci aka ce ana yi da wajen,Kai baka sani ba Iskanci fa akeyi da wajen ba ruwana wajen Iskanci ne,na ja tsaki na juya nayi tafiya ta abina Ina masifa ya dauka bani da wayo zai taba min wajen Iskanci na Allah ya kiyaye.


   Direct hotel din nan na koma ko zanga mutumin jiya gashi bazan ma ganeshi a Fuska ba sai dai ko idan naji kamshinsa na dade Banga alamar shi ba na bar wajen na tafi barata yau ma iya kudin abinci na tara, Wasa Wasa kullum Ina zuwa Hotel har da dare ban sake Jin me irin kamshinsa ba har na kwashe kwana biyar,shi Kuma Nawwar bai ma duba wallet dinsa bata nan ba,yau da dare na sake komawa nace wallahi daga yau Matukar ban ji me kamshinsa ba bani sake zuwa, ranar Kuma Nawwar ya nemi wallet dinsa ya rasa musamman atm card dinsa sune Suka dame shi, Fitowa yayi ko zai iya gani a cikin motarsa Nan ma ya gama dubawa babu, Fitowa yayi dake da duhu a wajen ko fuskarsa ban gane ba nidai naga hadadde ya wuce,Yana wucewa wani kamshi ya dakeni naji Kamar irin kamshin Wanda ya jefar da wallet dinsa jiya,Ina juyawa Naga ya Dan min nisa da karfi nace Malam....tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba da gudu na fyalla naci wawan birki a gabansa Ina haki na zaro wallet din tare da Mika Masa nace t...taka..ce? Yau sati guda kenan ka jefar da ita na ganta kullum sai nazo ko zan ganka,kasan irin hatsarin da na Shiga a hanya sabo da zan kawo maka abarka ai Saura kadan wani ya taba min wajen Iskancina,wai dan Allah karatu ai baya Shiga ta wajen,Nawwar bai gane me nake nufi ba ko saurarar zancen nawa baiyi ba, farin ciki ya Kama Nawwar cikin muryarsa me dadin saurare yace ta ya Kika ganeni? Nace kamshinka yasa kawai danni ko yanzu in za a kasheni bazan ce ga fuskarka ba sabo da duhu,karbar wallet din yayi Ina kallo ya duba komai nasa Yana ciki inda suke ya fito da dalolin masu yawa ya irga ko wacce dala dari dari ce a ciki ya zaro guda Uku yace gashi na gode


  Baki na turo nace Hmmm uhm jam ni me zanci da wannan takardar ai gwara ka bani dari biyar,dariya ta kamashi yace kudine fa idan Kika canja sunfi dubu dari nace wallahi bana so kaji mutum dama can baka yi Niyyar kyautata min ba in hakane ka bani dubu daya mana,Nawwar ya buga buga nace wlh bana so,yace to jirani a nan Ina tsaye a wajen ya koma cikin hotel din sai gashi da kudi Yan dubu dubu ya Mika min Yace gashi dubu talatin Kika samu ba cash a hannuna da yawa,da sauri na karba nace Allah ya shi Albarka za kaga daidai a rayuwarka bukatunka sai sun biya da iznin Allah na juya na take da gudu,yace jita Kamar yarinya da bakar Fuska kamar bayan tukunya Kai wannan da baki take,ni kuwa ko gane fuskarsa banyi ba nasan dai fari ne sosai dan dogo haka ,baki ya tabe ya juya ya koma ciki Yana cewa Kai amma tana da Amana a Zamanin nan.


    Ni Kuwa cike da murna na kwana da sassafe Ina idar da Sallar Asuba wanka nayi da ragowar sabulun wankina na wanke fuskata tas duk da na dan canja sabo da yawon bara a rana,kayana dana jiya na wanke su tas jakata na dauka Yar wayata na Kira   Saratu kawata tana shiga Kiran duniya ba a daga ba,nace ya zanyi haka Zan tafi Kawai,sai dana jira 8am tayi na samu na karya sannan na tambayi wani me Napep inda ake shiga motar su Anambra ya kaini Kuwa har can irin inda ake shiga mota haka Ina zuwa aka saka ni a motar Onitcha direct duk haka Ina ta Kiran Wayar Saratu amma taki dagawa Kuma tasan number ta haka mota ta ja Muka tafi,mun biya kudin mota tuni harda Yar ragowar kudina na adana abina cikin aljihun doguwar rigata domin sanye nake cikin doguwar rigar wani material orange rigar harda aljihu shine a kayana me Dan dama dama Yana min kyau,na yafa dan karamin mayafina,tunda muke kwarara tafiya nake uban bacci na farka na koma cike nake da nishadi Kamar ba gobe, sai tsakar dare Muka Isa Wanda mafi yawa a tasha muka kwana,in Banda turanci da Kuma pidgen English sai yaren Igbo shi Kawai ke tashi,gaba daya a tsorace nake,na matsu na ga Saratu nace yanzu Saratu dan masifa ta iya Zama a garin nan ko tsoro bata ji Kar fadan arna da musulmi ya barke a halakasu, gashi bana Jin turanci,Fitowa nayi daga tashar ba Wanda ya saurareni kowa Harkar gabansa yake yi, Napep na gani na tare iya sunan street din na iya fada masa yace you be Hausa? Yana cewa Hausa na washe baki na daga Kai sama kamar naga Dan uwana bahaushe,shiga nayi ya Fara tafiya Naga haduwar birni gidaje na gani na fada Muna tafiya Ina ta farin ciki,a fili nace yanzu nasan nazo birni, Birni na shigo,Yan Kudu gani sunana Rabi ae Rabi me zamani dariya na saki hahahaha kamar sabon kamu,nace wuhuhu kuturun dosan uwa ana bala'i a kudu, na nuna wasu Yan Mata da yatsa nace kalli cinyoyi Kai cinya a waje haka da Dan wando gajere wasu da mini sun Sha takalma masu tsini,na saki ihu nace yehoho ana tsiya nayi tafi da hannayena nace naga waje.


     Munzo wucewa ta wata GRA nace wuhuhu Kai Saratu lallai kinci gaba haka Zan zauna a katon gidanki,bani ba Arewa dole sai nayi kudi inzo inyi ta aikina in tara kudi ba inda zanje naga waje,Kai Rabi kin dace Ina magana da karfi Ina dariya Ina zazzare Ido Ina nunawa da yatsa Ina ta kallo,Me Napep bai San me nake cewa ba, tafiya mukeyi kamar zamu bar gari tafiya taki karewa tun Ina nishadi har na gaji nace Allah dai yasa yasan unguwar da nace,tafiya akeyi na gaji ma tun Ina magana har na gaji nayi shuru ga yunwa na cina,cikin birnin naga mun bari munzo wasu unguwanni Ghetto area unguwar talakawa da Yan jagwal badan ginin bulo bane da yawa sai nace kauyenmu yafi nan komai da komai.


     Sai da muka zo daidai wani lalataccen gida yayi parking Yana min alama da na fito,Ina mamaki na fito dauke da jakata a Hannu nace ya za ayi ka kawoni kauye ni da nace birni dan mugunta sai da ka wuce duk wurare masu kyau sanna ka kawo ni lalataccen wuri ni nasan wacce nazo wajenta baza ta zauna a nan ba Yar gayu ce me kudi tace Mansion ta gina a birni wata ce ta karaso wajen tana Jin hausa da alama ma bahaushiya ce itace ta tambaye shi da turanci meke faruwa? Yace shi bai San me nake cewa ba,tace ke meke faruwa? Ina masifa nace Odimgbe Street nace ya kawoni shine ya kawoni kauye Kuma wajen kawata nazo Saratu Amma kamar ana kiranta da Seraline,nan take matar ta sheke da dariya tace nan ne Abeg dauki jaka ki Shiga ciki kice a nuna Miki dakinta ki jirata, Ni dai nace Yar gayu ce fa me kudi ce kawata matar ta sake shekewa da dariya tace bawa me Napep kudi dalla malama kinzo mansion din Sera,Ina mamaki duk na hada zufa na biya me Napep kudi na Shiga ciki,matar ta rakani wani dan daudu ya shigo Yana karairaya yace wannan fa daga Ina haka? key zaka bata na dakin Sera zata jira ta bakuwarta ce,shewa Dan daudun yayi tare da furta ahayye daga Kauye amma wannan za'a kwashi gara,nidai mamaki nakeyi Dan yanda Naga Saratu ta hadu bazan taba yarda a irin wannan gidan take ba, gidane baida Fadi sai tsayi zururu daki daki sunfi ashirin ko wacce kofa na facing wata kofar dakin,tsakar gidan siminti duk gidan Kuma bandaki guda daya ne tal dakunan Kuma harda Yan daudu mutum uku a gidan,duka layin unguwar Haka gidajen suke unguwa ce ta karuwai arna da musulmai da duk wani yare a kwai a unguwar, kidane iri iri ke tashi Mata ta ko Ina gasu Nan da kyawawa da munana duk da shigar banza wasu sabo da kyau sai kace mene ma ya fito dasu amma haka aka bude min dakinta na shiga.


   Dakin nake karewa kallo da tiles dinsa sai katuwar katifarta da fanka irin ta kasa sai akwatunan kayanta a gefe,can barin Kuma Gas ce karama da duk wani kayan girki na bukata akwai shi,Babu wutar nepa Sanda na shiga sai zafi kamar zai kashe ni na jike da zufa haka na zauna na buga tagumi Ina kallon hoton wani katon gida me kyau manne a bangon dakinta,Daya barin Kuma katuwar poster ce ta batsa Namiji ya rungume mace babu Kaya a jikinsu ni dai kunyar hoton ya kamani na daina kalla na sadda kaina kasa,gajiya nayi da Zama na fito waje na samu a tsakar gidan wasu suna shan giya,wasu sunyi group kayan maye suke sha,wasu suna ta busa wiwi,wasu Kuma suna ta buga chacha sai bina suke da kallo suna kus kus gasu duk matane sai Yan daudu a cikinsu da wasu tambadaddun mazan,Ina juyawa wani yace Kai ji Duwawu dan Allah bakuwar Sera ce,wata inyamura ta kalleni tace Ohh Jesus see her back nidai fita nayi daga gidan da ko kofa babu bare a rufe a jikin wata bishiya na tsaya Ina kallo yanda karuwai ke hada hada wasu suna rawa kamshin girki sai tashi yake,inda nake tsaye Me POS ne wani tattirin dan duniya hancinsa ya saka barima har waje uku,kitso ne a kansa kana ganinsa kasan ya gogu da bariki,yace ke ya sunanka? Yana Jin hausa amma ba sosai ba dake Wai ya zauna a Jos,na kalle shi nace sunana Rabi,ahaa yace yaci gaba da harkarsa,Ina tsaye wata karuwa tazo ta bada dubu dari ya tura Mata a accnt, yace oh lallai Lili jiya an daki harka har dubu dari ko da Alhaji Kika hadu? Tsaki Lili ta ja tace Munafuki Abeg send  my money,aikin banza tana tauna chewgum, sai Suka Fara fada,me POS yace see your head mango head,with your toothpick hand idiot,suna ta cece kuce Ina tsaye Ina jinsu sai ga wata mota hadaddiya tayi parking Saratu ce ta fito daga motar taci uwar kananan kaya wani bumshort ne a jikinta sai yar riga bingila komai nata a waje ga takalmi me shegen tsini da jaka ta rataya komai da ta saka blue and white ne sun Mata masifar kyau.


     Tana ganina ta saki Murmushi naje da gudu Ina murna na rungume ta tace kawata kece nace ai tun dazu nazo Ina jiranki dariya tayi tace Ina can wajen aiki muje ciki muka tafi cikin dakinta sai kallonmu akeyi anyi sabuwar bakuwa, muna shiga na hau Saratu da fada nace Saratu Wai Ina hadadden gidan naki ne Dan Allah mu bar nan gidan na tsane shi mu koma can,Saratu Tsaki ta ja tace karki sa min ciwon Kai idan zaki zauna ki zauna nan ne gidana gidan da nake fada Miki ban gama gina shi ba,ihu na saki tare da dafe kirji nace Saratu la'ilahaillahu ashe haka kika iya karya kalli gidan da kike a waje marar kyau kalli dakinki sai zafi yanzu a nan kike rayuwa wlh gidan Dagaci yafi wannan sau dubu ke kauyenmu yafi nan layin naku kyau,gidanku ma yafi nan tsari haba Saratu ashe duk karya Kika je Kika yi Mana a kauye na gama ganowa yanzu dama karya ce motar ma naki da ita Kika je Mana data aro,Kinga Rabi idan Zaki zauna ki zauna idan baza ki zauna ba ki koma kauye,badan wlh ke bace baki Isa ki tsaya a gabana ki dinga fada min magana ba,Hannu na shiga tafawa Ina karewa Saratu Kallo nace kalli cinyoyinki kalli duwawukan ki cibi a waje ashe a nan tsirara kike yawo Saratu,tsaki Saratu ta ja tace wai Kinga me ma ya kawoki ne kike fada min magana haka? haka nayi shuru,zama mukayi na bawa Saratu labarin komai na gidan Dagaci,Saratu ta tausaya min tace Yar uwa nasan wasu wahalar da Kika Sha tun Muna yara me yasa baki kai Kara hukuma ba tunda sai da aka cike Miki takardu da komai sannan aka damkawa Dagaci ke tunda yace Yana so ai hukuma bata bashi Kawai dan ya zalunceki ba,nace da a baya Ina karama kin San hukumar gidan raino suna zuwa duba ni Dagaci ya dinga tsarasu ya fada musu karya Kuma suna ganina shar shi yasa ma tunda na girma Suka daina zuwa,idan na Kai Kara ya fini power ta ya za a kwato min hakkina a kasar nan tamu da zukatan mu sun gurbace,sannan ki duba fa Allah ne ya kwace ni Saura kadan ya fasa ni ya lalata min rayuwa Allah ne ya tsare,Saratu tace yanzu uba mahaifi ma neman yarsa yake a Zamanin nan bare ke Yar tsintuwa Allah ya kyauta yanzu kafin nayi girki kinsha wahala bari na bayar a siyo mana abinci me zaki ci? nace ah Ina kudu ai a kawo min Sakwara da miyar Agushi ,Saratu tana yanga ita a dole wayayya ta bawa wani dandaudu kudi ya tafi siyo Mana abinci Muka ci Muka koshi daga nan hirar Kauye ta barke muna ta labari,tace ya labarin saurayinki Kutama? nace Allah sarki Alhaji Kutama ,baki Saratu ta tabe tace ke dalla manta da shi ki fara sabuwar rayuwa,rayuwar yanci rayuwa me dadi ki samu aikinyi Wanda Zaki dogara da kanki,Farin ciki ya kamani nace yawwa Saratu dan Allah ki samamin aikin Yi kinji,karki damu Zaki samu aiki amma sai kin canja suna,Ido na zaro nace na canja suna Wanda aka yanka min rago aka rada min Rabiatu sai na canja suna,Kinga kamar ni Seraline ake ce min ki samu sweet name na Yan gayu irin su cutie,princess,sweet pussy etc,Ido na zaro nace ah Saratu bazan iya ba Ina laifin ma a kirani da Miracle din Kawai, Okay Miracle din ma yayi ai cewar Saratu,duk tunanina wani aiki ne babba.


    Ban fahimci inda aikin nasu ya nufa ba sai da dare yayi naga kowacce har mazan suna ta faman daukan wanka ko wacce ta sa Kaya matsiyata Wanda tsirara Kawai suke,naga wasu matan Wanda zasu kwana da wani me kudin sun shirya anzo an dauke su a manyan motoci wasu Kuma sun shiga Napep sun tafi,Wanda Basu da wani Kuma suna shiri zasu fita gefen kwalta me son kwana da karuwa ya dauka ya biya,na kalli Saratu nace Saratu badai wannan sana'ar itace aikin da Kika ce kina yi ba? Ba kunya tace shine Ashawo work aikin siyar da Pussy kasuwancinmu kenan ka biya ka ci,baki na bude a tsorace nace Saratu kiji tsoron Allah kin cuci iyayenki tunaninsu Kuna tare da Yar uwarku aikin restaurant,ba kyau Saratu ke a karuwancin ma mafi Muni kike yi na kwalta haba Saratu karki biyewa arna akan abin duniya ki tuna addinin mu,tsawa Saratu ta buga min tana duba mudubi sanye take cikin Yar ficikar gown bata fi rabin cinya ba Blueblack ta sa hular gashi me tsada,tace karki dameni idan baza kiyi ba ki kyaleni bana son wa'azi aikin banza local girl,dan bakina na turo gaba nace ni dai bazan yi ba,Ina kallo Saratu ta Sha takalmi me tsini ta fice,sai da safe Suka dinga dawowa,a Haka na kwashe sati biyu har na Saba da kowa da mutanen layin kowa ya sanni Muna mutunci har idona ya fara budewa nima na fara dan zama tsagera sabo da Zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai,Ina daki a zaune bani da ko sisi Saratu tace 


   Rabi ki bude kunnenki kiji zaman da kikeyi a karkashina ya Kare zan hakura mu zauna daki Daya dake amma fa ba kyauta ba dole ki dinga kawo kudin haya rabi Nima na kawo rabi mu hada mu biya,sannan daga yau na gama ciyar dake da kudina sai kema ki fara neman kudi ki dauki nauyin kanki da kanki sabo da haka na baki nan da wata guda ki kawo kudi dubu hamsim nima na kawo mu biya kudin haya,sai abinci ki nemawa kanki daga yau,na rasa me zance ma gashi bani da wajen zuwa,nace to a nan gidan Kinga ni dai bazan iya siyar da gabana ba bazan yi karuwanci ba idan akwai masu daukana aiki zan dinga musu shara da wanke wanke,Saratu tace akwai 'yarzabil kaf layin nan tafi kowa kudi,akwai wise itama tana da kudi ta Dade tana Neman Yar aiki a gidan nan, ga Star itama duk nasan zasu yarda ki musu girki,wanke wanke da shara da mopping,idan duty na wanke bandaki yayi na kowacce ke Zaki wanke musu haka sharar compound kaf gidan nan kullum da duty kowa so Zan musu magana,nace to ai suna da kirki ma ki fada musu Kinga na samu aiki idan na samu miji me sona nayi aure na,Saratu baki ta bude tace aure lallai Zaki kashe kanki yarinya tab, amma rayuwarki ce.


    Nace Saratu karki dameni da iyayi na sanki kin sanni me zaki boye min,yawwa idan na samu Miji aure zanyi yawwa ehe yanzu tsadar rayuwa tayi yawa ga tsadar abinci sabo fa da tsadar abinci yanzu Mata masu ciki sun daina Amai,Saratu ta kwashe da dariya tace ke makaryaciya inji uban wa? nace baki da labari ke? Dariya Muka dinga yi Saratu tace to bari na baki shawara tunda ke soyayya kike so kiyi aure idan zaki fara soyayya ki tabbatar kinyi photocopy na zuciyarki ki ajiye Original din a gida Kinga idan an samu matsala dama zuciyar taki photocopy Kika bayar sai ki dawo gida ki dauki Original din,dariya nayi sosai muka tafa nace kawata har yanzu baki bani shawara ba fa akan yanda zan kula da budurcina a gidan nan naku na karuwai.

    Saratu zama ta gyara tace karki yarda da Namiji ko waye musamman idan Kika ji Yana kiranki da Sexy Nan gaba zai iya cire Y din yayi Sex dake daga karshe ya cire S din ya kiraki a Ex-girl friend ki Zama wise Kar wata ta Miki wayo ta hadaki da Namiji ta samu kudi tunda ke kin zabi aure no problem,mun dade Muna hira.


   Washe gari dake da asuba na fito nayi wanka da Alwala,na fito Kawai naga Mata da maza sun kafa layi kamar layin banki ashe Wai toilet za a Shiga ake wannan uban layi,kowa yazo sai ya hau layi,da sauri na koma ciki nace Saratu yanzu akan za ayi kashi aka kafa uban layi haka? shi yasa nace ai ke tunda kina Sallah ki tashi kafin ayi Sallah Kuma fatan kin wanke bayin kafin kiyi amfani da shi? nace sosai ma ai baki ga na dauki Hypo ba,tace to ta juya taci gaba da baccinta babu Sallah ba salati,ni na gyara Mana dakin na Mana abin kari, bayan kwanaki sosai na kara sabawa da gidan kowa ya sanni nasan kowa, mutum uku Seraline ta hadani da su Suka daukeni aiki a gidan zasu na biyana duk wata 'Yar Zabil ta dauke ni,Wise sai Star tun kafin ma na Fara aiki suka jibgo min kwancen Kayan sawa kana nan Kaya da namu na hausawa masu kyau da tsada,harda takalma Suka bani abubuwa na ras,a ranar na fara musu aikinsu kullum ba fashi sai abinda suka ce,gashi duk canji in ya ragu bar min sukeyi,Muna haka kullum idona sai budewa yake Ina Kara gogewa sannan bakina ya bude yanzu surutun masifa gareni Kamar naci aku,kana taba ni ba mutunci ga fada dana koya,ga rashin kunya Nima Jin Iskanci da kalamai na batsa yasa na iya wasu nima bana Jin kunyar fadar magana duk girmanta,Nima su rawa da su whot game da ni akeyi a gidan idan ba caca akeyi ba,Ina cikinsu na koyi saka shegun Kaya baza kace na hada Hanya da muslunci ba Kawai abinda ban taba shine fita titi neman customer Ina nan a virgin dina ban taba Iskanci ba sai dai Kawai nasan mazan gidan da Yan daudu mun Zama kawaye kuma kusan duk arna ne Muna rungume juna da su Kamar kawaye mata,gashi pidgin English Ina ta koya a hankali yanzu na Fara iyawa ba laifi gashi abin haushin kudin idan na samu a cikina nake cinyewa sai kudin haya da sauransu babu kudin da zan iya tarawa ma sam sabo da basu da yawa,Amma sutura da komai a gidan duk su Wise sunfi mutum ashirin bani Kaya suke har na kwashe watanni shida.


    Yau Star ce ta sani girki da yamma likis Ina girkina a dakinta itama komai akwai a dakin na more rayuwa nata dakin ba irin na Saratu ba harda ac ya hadu itama Yar zabil haka da wise su suna samun customers sosai, ina ta juya stew sai ga Star ta shigo a gajiye ta fada saman katifarta tana wash,na kalleta nace hala jiya customer ya baki wuta? Star tace ke dai bari mutumin hariji ne baya gajiya sai da ya more kudinsa kaf guy din ya daki harka yayi ta front, back da center babu ta Inda baiyi ba,nayi tsuru Ina kallonta Ina mamaki bada kansu da suke yi nace wai Star ni kuwa abin nan da Dadi? Star tace wa ya fada Miki karuwa na enjoying sex ai karuwai irinmu badan Dadi muke ba sai kana son mutum ko Yana birgeka kake jin Dadi ai Kawai mu bude maka zamuyi ka daki harka yanda kake so ka bamu kudi,in Kinga yanda muke dagewa Muna sarrafa maza zaki mamaki Kuma mafi akasiri ba Jin dadin muke ba sabo da Kawai muja hankalinsa ya Zama babu wacce yake so yayi sex da ita sai mu,shi yasa muke kwacewa Mata mazajensu wasu sun tsaya kunya da shirme mu Kuwa zamu yi maka yanda baka ma tunani dole a nace mana,nace ah gwara da Kika fada min idan nayi aure kice na dage? Star tace ki dage sosai ki fahimci mijinki me yafi so yarinya ki gyara kanki karki Wasa da gyara ki kashewa jikinki kudi,Kinga dai irin magungunan da muke siya masu mugun tsada,da ace zaki samu Wanda kike so ki gwada kiji dadi, sai naji Ina so Nima nayi sex din yanda kullum a wajen karuwan ke kwadaita min dadin shi, so suke su rinjayeni na fada harkar nima amma naki,Auzubillahi na dinga ja Ina Neman tsari a raina,dama kullum bana Wasa da addinina ga Karatun Qur'ani kullum Ina yi Allah ya tsareni,Ina ta girki Muna hira daga ita sai pant da bra a haka wani katon Arne Igbo yazo ya sameta da gani kasan ba karya akwai kudi a kugunsa,Yana shiga dakinta ya fada kanta a haka Suka fara kissing a gabana inda sabo na saba gani ko a jikina Ina jinsu suna ta fama har ya rabata da kayan jikinta tsirara take shima daga shi sai sai boxers ta cire Masa Kaya,Condom ta saka Masa da kanta nishinsu na dadi Kawai nake ji,Allah yasa na gama gas na kashe da sauri na bar dakin suna ta masha'a dinsu,Ina Fitowa Wise ta dau wanka zata unguwa da karamar akwatinta me kyau tace Miracle zo ki rakani gidan saurayina,dakinmu na shiga na saka Yar riga doguwa me siririn hannu Kamar hannun best daga sama ta dan tsuke kasa ta bude yar kanti ce brown me adon golden cikin kayan da suke bani.


     Mayafina karami nayi rolling brown nasa flat shoe dina brown na Fara gogewa fa gani kyakyawa ajin karshe Fara sol dani ko Ina sai ayi ta kallona, Jakarta na dauka Muka shiga napep,Wise duk tafi yanga da wulakanci ni kaina bana Mata wasa sabo da halinta gata kyakyawa da ita,wani katafaren gida Muka Isa,knocking tayi gate man ya leko Yana ganinta da alama ya Santa ya bude Yana washe baki,kallona yayi yace small madam how far?Fuska na bata nabi Bayan wise tun kafin mu shiga ciki ya leko wani fari Igbo kyakyawa ne amma katon arne ne,glass cup ne dauke da juice a ciki yaci wanka cikin kana nan kaya yan ubansu gashi matashi,yana zuwa ya kalleni nace good afternoon sir, yace Good day Yana Murmushi tare da rungume Wise,tana shafa sajensa tace Baby I miss you,yace miss you more,let's go upstairs and have fun,hannayensa ya maida saman kugunta Suka haura sama ta juyo tace ya bani kudi na koma gida,ai Kuwa 5k ya bani sai Murna nakeyi na karba Ina godiya na wuce gida nace daga rakiya 5k guda yau akwai zazu,Ina komawa gida Seraline tana gida yau hutawa takeyi tana Jin kida Ina shiga na dinga cashewa Ina karkada Mata 5k sabo da yanzu duk na fetsare ban taba rawa ba sai a nan gidan duk na koya kullum sai nayi rawa tun Ina hauka har na fara gogewa.


   Saratu dariya takeyi tace akan 5k kike wannan rawar da ace aiki nake fita rana daya Zan iya samun dubu dari ma,na kalli Sera nace ba shegen da zai shigar min local government ku dai da kuke ashawo Kobo kobo 2thausand Kuna rabawa kyauta kuje ayi ta ketara muku local government ni duk shegen da ya shiga local government dina to dole yayi loosing Election,Baki ga Dagaci ba tuni sun rasani,dariya Seraline tayi.


   Su Gwaggo tunda na tafi ko a jikinsu Kawai murna sukeyi suna Jin Dadi Gwaggo tace yanzu sai mu zauna mu taru akan yaranmu su samu mazaje masu kudi suyi aure,Aunty Amarya tace yau wajen wata shida da barin Yar banza gida har gidanmu yayi dadi duk ta tare Mana waje,Dagaci ne ya shigo da abincin kajinsa dakin dana bari kaji masu kwai ya zuba Yana kiwo a ciki duk da ta bangaren aikin gida sun rasa me yi sai dai suyi da kansu gashi Gaji da Mairo basa aikin gida kazamai ne sai dai Iyayen suyi,ana haka Katsam Gaji ta hadu da wani me kudi a kasuwa ya biyota har gida Yana da kudi Alhaji Kabiru Danbinni murna wajen Gwaggo da Dagaci ba'a magana sai abinda Alhaji Kabiru yace, sai da ya bari sun Saba sosai Yana kashe musu mahaukatan kudi sai ya fara fita da Gaji yawo yana siyo Mata kayayyaki, yau Sunday zance yazo yayi parking da arniyar motarsa Gaji taci gayu ta Sha kyau ta fito tana taku dai dai Farin ciki ya Kama Alhaji Kabiru tun kafin ta karaso ya fito a motar ya tsaya Yana Kare Mata kallo sanye take cikin Material Maroon Wanda shi ya dinka Mata ba karya tayi kyau ta ko Ina dama su Gaji anyi school a waye suke,Yana kallon Gaji yace sai naji kamar na rungume ki,Murmushi ta saki yace Allah dama ace yanzu tare zamu kwana da zan more, Gaji Ido ta rufe sabo maganganun Alhajin nata,yace ki daina kunya yara kanana ma yanzu Jin dadin rayuwarsu suke yi bare ke da girmanki,ki bari na dan motsaki ki Dan kawo yau kiyi bacci me dadi kin tsaya Kamar Yar Kauye haba Gajina,wallahi da ace kin yarda dani Kawai romance ba sex ba babu abinda bazan baki ba,komai zan siya Miki Zan Miki komai,I will take care of you


    Gaji tace ni dai bana son Sex sai munyi aure,wayancewa yayi haba ya za ayi na lalata Miki rayuwa ai bazan ma iya ba Kawai romance amma ya kamata ace munje inda yake da privacy waje me sirri inda zamu saki jiki sosai muji dadi ai romance dinma yafi Sex,Ni mota ma zan siya Miki kwana nan in kin yarda,Gaji taji mota tace to muje amma dan Kaine yace ko kefa ai yanzu rayuwa sai ana Jin dadi ana dan motsawa amma duk kin bari kinyi mugun tsatsa,dariya tayi tace tsatsa Kuma yace yes kinyi tsatsa,gida ta Shiga tace Gwaggo Alhaji yace naje zai kaini na siyo Kaya,Gwaggo tace sai kin dawo tunda ai mijin aure ne ba damuwa ai aure zakuyi nan kusa a dawo lafiya Dagaci Yana ji yace mutumin kirki kenan Alhaji Kabiru Danbinni ba abinda zamu ce Masa,Gaji dai ta fice ta shiga gaban mota ya ja sai cikin birni tunda Suka taho yake Mata maganganu na batsa,yace da alama zakiyi ni'ima,zakiyi dadi,sannan Wanda ya sameki ya dace zaki dade ana sex dake baki gajiya ba,gaki da alama jarababbiya ce ke kina da karfin sha'awa,Gaji tace ta ya ka sani? Yace af baki san wani littafi ba me suna Surah inda aka siffanta dukkan kalolin Mata to ke me surarki haka aka ce a littafin,ai ya kamata muje na sha dadi ko ya kika ce.


    Zaune muke a tsakar gida Muna game din whot ban wani iya sosai ba sai cinye ni akeyi,Munfi mu shida Sera,Wise,Star,Yarzabil, Mandula,Manduwa sai dan daudu Santana,Star tana yi tana bulbula sigari,Seraline itama kunnawa tata wuta tayi tana sha,Wise kuwa bata Shan komai na hayaki sai kwaya ita, sai yarzabil yar Syrup ce ita Kuma,Mandula Kuwa ba abinda bata sha,duk na goge nima har yanzu kallon baki waye ba suke min,Muna fama sai nishadi mukeyi,Santana ya kalleni yace Miracle ki taimakawa kanki ki nemi kudi Ina baki shawara kin zauna kina ta talauci shegen pussy din ai ba gutsira za ayi ba kin zauna Wai ke aure a nan gidan zaki samu mijin aure ko balagaggen dan bariki zaki aura a nan,kin San dai kaf layin nan yan Iska ne,Nima da Zan samu Wanda zai aureni ai da naji dadi,dariya ta kamani nace kalleka ko kunya baka ji kana Namiji ka maida kanka dan daudu Wai da zaka samu Wanda zai aureka Namiji fa kenan stupid karka isheni me suffar Condom,dariya su Wise Suka dinga yi, Yar aikin Karuwai lallai kinci abinci cewar Yar Zabil dama yawanci duk gidan Yar aikin Karuwai suke ce min.

   Anjima fa akwai gala a gidan nan,dama unguwar kullum sai anyi gala iri iri mawaka suna zuwa suyi show Yan gala,akwai bangaren gala a unguwar  yau can zasu kusan kwana,da dare da ni aka tafi can wajen Yan solo duk munyi gayunmu,Su Wise suka dinga lika musu kudade ranar Karuwai sun zubar da Naira,Nima mawakin ya birgeni mawakin hausa ne Wanda ke tashe kudin dake hannuna dubu uku da na riko a hannuna na hau step naje na lika Masa su,na dawo kida na kwasata na ranci dubu biyar wajen Seraline naje na Kuma lika masa,mu indai Harkar banza zakayi a gidan babu me hanaka sai dai ma a goya maka baya.





Sharhi fans




AsmaBaffa 

08061929616

No comments

Powered by Blogger.