X World 5

 


*🕊️X WORLD🕊️*

_Duniyar shahara_


_Last Free page_

        _0 5_

_Daga Wannan page din Free page ya ƙare , ga masu buƙatar wannan littafin Regular payment₦500 vip group₦1000 spc₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932_


*MAMAN TEDDY*


https://youtube.com/shorts/LnnDPlVt5Hk?feature=share

Kuyi Subscribing channel din mu Domun samun sababbin littafan mu .


**

Suna tsaka da Wannan mamakin ne na ganin Allah da ikon shi Wato su Zahra ma basu san inda suke zaune ba . Kallo Ɗaya Adnaan yayi masu Zahra ya kai hannun sa yana gyara Bakar Gilashin idanun sa . Wuce su yayi yana nufar Gate ɗin wanda tun da Su Zahra suke Basu taba Sanin nan barikin Sojoji bane.  Don duk yawon su bai taɓa kawo su nan ba . Nufar Gate ɗin yayi wanda Ganin haka yasa Zahra sheƙewa da Dariya tana cewa " Makaryata kawai , to Wancen mai ji da kan ya tafi kuma sai ku Bama mutane Wuri . Tsayawan Da yayi ne yasa Zainabu dake Gyefe ita dai ta fara tsorata musamman Ganin Wrist watch din Hannun Adnaan Na Sojoji ne ,wanda ita Kan Zahra Sam bata lura da Hakan ba . 

Wani irin gigitaccen Tsawa Wani kurtu ya daka masu wanda yasa Hantar cikin su Kaɗawa guuuurrr . Kallon Su Adnaan yayi yana basu command da cewa " Ku shigo mun dasu ciki . Ihu Zainabu ta fasa tana kirar sunan Baba Kamin ta Cigaba da cewa " Zahra kece kika ja mana , Ina ta Miki magana Wallahi Sojoji ne kawu nan mu zasu harbe yau wayyo Mama na . Jikin Zahra ne ya dauki Rawa da makerkyata kar³ . Zainabu da Gaske sojoji ne mun shiga uku wayyo Ni Zahra . Mu gudu...! Tayi maganan da Ƙarfi tana kama hannun Zainabu Wacce ta kusa fitsari a tsaye.


Tako biyu Wa'annan Kurtun suka yi Suna tarar Gaban su ,amma har a lokacin Zahra kafiya da Taurin kai sai ta ƙara Riƙo Hannun Zainabu tana jan ta wai su Gudu . Abun ka ga Soja da zafin Rai Daya daga cikin su ne y daga hannu yana Wanka mata Mari wanda sai da ta kame ƙyammm ganin ta da jin ta na  Ɗaukewa na yan Daƙiƙu . Wani irin uban Ihu ta kwarma tana Gigif tare da ƙirar Sunan Inna Salame tana kwarma ihu iya ƙarfin ta . Wuce mu shiga ciki ...! Suka kuma daka masu Tsawa wanda a wannan lokacin babu musu ko tirjiya suna kuka ita da Zainabu suka shige cikin Barikin Sojojin . Hannun Zahra dai a saman Kuncin ta yake har a lokacin bata Sauke ba .


**

Sauke Tafashen Naman Ragon Neesa tayi tana Cigaba da taya Ammie Girki don yau Daddy General Sufyaan Jamawa zai Dawo . Amma Aneesa naga kun dawo da Wuri Bayan a ƙalla kuyi kaman six mount kuna ...Ammie ba komai kawai nice na ƙosa na dawo Gida Nigeria Cox nafi jin Dadin zaman nan . Neesa ta katse Ammie tana murmushin nan nata Irin na gogaggun mata . Mashaallh Ƙwarai naji Daɗin jin haka daga Gare ki , da yanda naga kuna zaman lafiya a tare daku . Allah kuma ya kawo maku zuri'a Ɗayyiba masu Albarka. Ƙirjin Aneesa ne ya buga dam, maganan Ammie ya tuno mata da wani magana da Likitan su ya taɓa faɗa mata a lokacin da ta zubda ciki na huɗu yake sanar mata tayi Hattara Mahaifar ta ya fara samun matsala . Yanzu ma da yiwuwar ko ta kuma samun ciki ya zauna . Gumi ne ya fara tsatstsafo mata . Cike da kawar da komai kaman ba damuwa a tare da ita tace " Ammie Amin ya rabbi . A ina za'a zuba naman .? Zuba a cikin miyar Ɗanyar Kuɓewan Kin san Daddyn naku da son ciman Gargajiya . Dan Darawa Aneesa tayi kamin tace " Ƙwarai fa Ammie yau Daddy zai yi matukar farin ciki da ganin Irin wannan best dishes din da yafi So.." Gashi ba zamu hadu ba Zan koma gida . 


Kallon ta Ammie tayi tana gyara Tuwon Semo ɗin Hannun ta tare da cewa " Me yasa .? Aiko zaki tsaya ku hadu yaga bakin America. 


Ammie kin san Dai Muhammad idan yace Abu to kawai fa ayi masa shine zaman lafiya . Yace mun na koma gida arround kin ga yanzu har 2:pm . Shiyasa nake Sauri Naci Tuwon Ammie sannan na tafi . Dariya Ammie tayi tana cewa ' Kwarai fa Ai Juyewan Muhammad mai iya zama dashi sai ke Da din . 


**

Baba ne ya shigo Gida da misalin karfe biyu na Rana don yanzu suka rabu da mahaifin Zainabu a masallaci. Salamatu..! Sallamatu...!! Ya kira sunan Inna Salame wanda tayi saurin fitowa daga madafi tana faɗin Sannu da Dawowa Malam . Amsa ta yayi yana cewa " Wai ina Fatsima ce ? , Yanzu Malam Garba mahaifin Zainabu yake mun maganan wai tun safe suka bar gida har yanzu ba su dawo ba . Idanun Inna ne ya fito wai dama bata na Gidan su Zainabu ba tun safe.? . Ina kuwa yaran nan suka nufa ne haka .? Shiru malam yayi irin nasu na manya kamin ya nufi Ɗakin sa yana cewa " To Allah ya dawo dasu lafiya duk inda suka je . 


Juyawa Inna Salame tayi tana kallon Talatu wacce suna Haɗa ido ta cabe baki tana cewa " To ai gatan kenan Inna , bakya bari ayi ma Zahra Koda Tsawa yanzu to gashi nan wa take wahalarwa.? Ko yayyun ta bakya yarda suyi mata fada . Murmushi Inna Salame tayi cike da salɓi irin nata don ba zafi take dashi sosai ba ,ita dai fushin ta indai kaga tayi to akan an taba Autan ta ce Zahra . Ayya Talatu In ban SO Uwa ta ba wa zan so ,ina zan bari a taba mun Mama na . Humm ai Shikenan . Ke Hannatu tashi maza Zo na aike ki gidan mai Adashi  ,ki dawo kiyi shirin islamiyya .  Ki natsu ki kama kanki yanzu ke budurwa ce ba zan ɗauki Shashanci ba . Tun da yanzu har sallama ake yi dake a kofar Gida . 


Girgiza Kai Inna Salame tayi tana komawa cikin Madafi don tasan duk wannan Abin da Talatu take yi da ita take yi akan Zahra ita da babu natsuwa makarantar ma tayi dambe da malaman har tana fasa mawa malaman nasu baki . Allah dai ya taimaka Abin yazo da sauki albarkacin Girman Malam da Ake gani . Haka ta zauna Shiru a kitchen kunsan Uwa da Ɗan ta , Tun zaman ta take tunanin Zahra tana addu'a a Zuciyar ta a ko ina suke Allah ya tsare su ya dawo mata dasu lafiya .

**

Barikin Su Adnaan kuwa Zaune suke a inuwar bishiyoyin barikin gyefe guda can nesa sojoji ne fareti yayin da shi da Shureim da Abdullahi suke zaune suna kallon yanda su Zahra ke up and Down . Sai kuka suke yi sun fi awa Uku a haka . Gumi kuwa yanda kasan Ana watsa masu Ruwan Sanyi. Yallaɓai Soja don Allah kayi Haƙuri mun tuba Soja .! Tana maganan tana matso ƙwallah ga zafin rana gana Wahala kan ta wani irin zaɓaɓɓen ciwo yake yi mata . Babu wanda yabi takan ta ko ya tanka su sai Muryar Wani Kurtu suka ji yana ce mawa Adnaan lokaci ya cika . Kallon su Adnaan yayi yana cewa " kuyi tsallan ƙwado daga inda kuke zuwa can ku kai ku dawo Sau Hamsin . Innalillahi wayyo Inna ta wayyo Inna ki taimake Ni kafana zai tsinke yabar jiki na . Kuyi hakuri Wallahi taimakon rai muka fito yi taimako zamuyi bamu Sani bane mukayi maku rashin kunya bamu san ku sojoji bane . Kallon Adnaan Shureim yayi Wanda sai a yanzu yasan laifin da su Zahra suka yi ma Adnaan yake masu wannan horon. 


Taimakon mene zaku yi..? Shureim ya tambaye su yana kallon su . Zahra ce ta fara basu labarin yanda suka yi da Mubarak Ƴaron dan Me kunu , tare da shuga gidan Tsaiba da tayi tana ji tana kururuwa ,kallon su tayi tana cewa " Shine naji zai kashe ta. Haɗa ido Adnaan da Shureim suka yi kana Adnaan yace " Wannan yarinyar raina mana Hankali zata yi ,me take nufi .? Nufin ta bata san Aure ba?. Shureim ne yayi masa kallon karya take yi . Yayin da Adnaan yace " maza ku fara .


Cikin Muryar kuka Zahra ke fadin Ni nasan anan zan bar duniya don izayar nan taki halaka mu zata yi .amma ku taimaka ku ceci baiwar Allah Tsaiba .  Ga Recording din da nayi zan kaimawa Manya don a cece ta muma a cece mu . Kurtun Gyefen ta ne ya amshi Wayar yana danna Recording din da tayi saving yana mika mawa Adnaan tare da ƙame masa irin tasu na soja .  A hankali suka fara Saura , Yayin da Zahra ta fara tsallan kwaɗon don dole suna rera kuka kaman wake . Sukan su Adnaan Sam basa ta kansu sauraren Recording din suke yi ,suna sheƙewa da Dariya irin na shahara . Oga Da gaske fa Wannan yarinyar bata san Meye Aure ba , ita kuwa daga Wani kauye ta fito haka .? Cewan Shureim yana daɗa kecewa da Dariya . 


Wayyo Zahra ,Zahra ki buɗe idanun ki Zaharaaaa....! Zainabu ta kwarma ihu tana jijjiga Zahra da t fadi anan Wurin tana sanƙare masu a sume . Saurin Miƙewa Su Captain  Adnaan suka yi suna isowa inda take . Ganin yanda kumfa kebin  bakin ta tamkar wacce tasha guba yasa shi saurin kai Hannun sa yana Daukar ta cak cikin sassafa ya nufi moton sa yana saka ta tare da kallon Shureim yana faɗin " Ina zuwa yanzu . Sam kan sa ya dau zafi tunanin sa kar yar mutane ta mutu ba zai so hakan ba ,musamman a dan zaman su na a wanni sai yake jin nishaɗin yaga yana kuntata mata tana kuka wannan yasa shi kin dakatar dasu . Cikin wani irin mahaukacin Gudu yabar cikin barikin kan sa na masa zafi sam ya rasa ma ina zai kai ta wannan yasa shi nufar Gidan sa da ita ,don yasan Aneesa Matar sa Likita ce...........!*To laifin daɗi ƙarewa💃🏻😄*

*Anan na kawo ƙarshen free page dina masu buƙatar cigaba regular group ₦500 VIP group ₦1k SPC ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*


*#MAMANTEDDY*

No comments

Powered by Blogger.