X World 4

 


*X WORLD*

_Duniyar shahara_

_(Temptations Erotic and comedian story)_


          Free page

              0 4

*AYSHATOU MAMAN TEDDY*


_Littafin X World na kuɗi ne kaman yanda kuka sani a next page Free page zai ƙare labari ne short story mai ɗauke da darussa da salo na daban . Ga masu buƙatar cigaba da karanta lbrn Regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ku tura ta Wannan number 09061466409 duka evidence of payment din ku zaku tura ta Wannan WhatsApp number 08081202932 thank you_


*The Novel is only for matured , idan kin san You're under 🔞 don Allah kar ki karanta .*

**

Wani irin farin ciki ne mara Misaltuwa ya mamaye Zuciyar Asmeey Saurin juyawa tayi tana neman Su Zee don ta basu kyaƙyƙyawar Labari don ita a jikin ta take ji Shureim ne wanda suke jin labarin su ɗaya daga cikin Star Gang na matasan Sojojin nan masu fama da Rashin ji da girgiwa . A hankali ta Dafa zee dake ta rawa kaman mazari babu Alamun Gajiya don a haka suke for more than 1hr . Bakin ta takai kusa da ita tana raɗa mata magana kaman Haka " Zeee Dakata kiji nayi fa nitso yanzu haka na kamo Babban Kifi. Saurin kallon ta Zeee tayi tana maida Hankalin ta sosai kan Abin da take cewa". Ke Asmeey ban gane ba. Wa kika samo mana .? One of the Star gang . Asmee tayi maganan tana Sakin murmushi . Eh Asmee A ina kenan .? Wa'annan da basu Ƙasar London basu Thailand basu America ta ina kika same su.? Ai wannan Wurin yayi masu Kaɗan koda Ma A shaharar ne . Star Gang fa Basu kusan Biyar bane. Eh nafi jin sunan mutane biyu dama daga Ciki Na Ɗaya Shine Muhammad Wanda ake kirar sa da Adnaan na biyu sai Shureim kaman haka ne . Zeee ne ta saki Ajiyar zuciya kamin tace ' kwarai fa su Nima nake jin sunan su sosai ,Adnaan Da Shureim . Wani irin Dariya Zeee ta saki Kamin tace " Kice Zamu Fantama iya yanda muke so kudi ai kam yanzu sai dai mu koma Rabon shi . Chilling sai inda ya tsaya ,zamu koma fita kasashen Turai da Sauran su .


Kallon Anya kin san me kike yi Asmee ta Watsa ma Zainab kamin tace " ke raba Ni , Ai nayi nadamar ma yanda ya Ganni Anan . Cike da Rashin Fahimta Zee tace me yasa .? Gyara Hannun Half vest din jikin ta tayi tare da cewa " Ai yanzu ne nake jin na samu mijin Aure . Kin kuma san Gang din su ba sa'an mu bane . Amma sai na ga na mallake shi ko ta halin kaka nafa samu miji . Ai irin wa'annan baka bari suna kubce maka . Zee ce ta bude baki zatayi magana dai dai Seeyah na isowa . Me kuke tattaunawa Haka .? Humm kedai Seeyah bari Abin nema ne ya samu . Cewan Zee tana Zaiyana mata labarin duk yanda suka yi da Asmeee . Kai Haba.! Wai da Gaske .? Allah kuwa nima kaina na ruɗe kaina ya dau chaji cewan Zeee tana saka hannun ta tare da kama Kan ta . Wani irin Dariya suka kece mata dashi kamin Seeyah ta kalle su  duka tana cewa " Back to Our business ya muke ciki .? Ta yaya zamu kama fatsan .? Zeee ne ta furta " Ai mun kama ma ,mu abun da ya rage namu sanin yanda zamu gudanar da tafiyar har mu gan mu a inda muke So . Don kinganni nan inada Labarin rayuwar ɗaya bayan Ɗayan su.  Mahaifiyar Adnaan kuwa Ita idan kika ganta baiwar Allah ce sosai . Ita bata Cikakken Wata shida a Nigeria tana Sa'udiyya don haka Hijab Zan koma sakawa Don na mallake shi , na kama Wannan . Kallon ta Su kayi suna saka Dariya tare da Cewa " Shi da akayi masa Aure ,ko bakiji labari bane .? Wanda ya Aura Cikakkiyar Mayawaciya ce Ta gama shagalanta Sannan aka liƙa masa don Dole . 


Shiru Zeee tayi kamin ta saki Murmushi mai manifofi tana cewa " Dole a yanzu Gidan sa babu zaman lafiya . Don ko Dan iska yana son Auren kintsatstsiya . Don haka zan Amfani da Wannan daman don Ganin na shiga daga ciki Nima . In yaso sai a Cigaba da bandarwan Dani ba komai duk masifa indai zanci me kyau nasha me kyau . A tare suka sheƙe da Dariya kamin Aseeyah tace " ya kamata mu fita daga Waje ne sai mu tattauna da kyau yanda abun zai tafi mana . 


Suna Wannan maganan ne Asmee taji Hannun Wani yana lalubar ta sam bata san lokacin da tace " Kai bawan Allah rabu Dani ,barni naje na nema ma kaina mafita ,na samu Wanda na dade ina Marari wanda banyi zaton zasu neme Ni Ko a karuwanci ba .  Don haka rabu Dani zuwa nan ya kuma kare daga yau .! Ta ƙare maganan tana angaje yaron , Dariya suka fashe dashi su Zeee Suna juyawa tare da fara sauka Stairs din suna fadin Kin mana dai dai . 

**

Cikin Wani irin yanayi Na rashin Jin Dadin dawowa Kasar Nigeriya Take kallon mijin nata Adnaan kamin Neesa ta Furta " Yana ga Muna daukar Hanyar da ba gidan mu ba .? Nan fa Gidan Ammie zamu je kenan da Wannan tsalelen Daren .? Yanzu ba zamu sauka a gidan ka ba sai Gidan Ammie to me zamu yi a can Adnaan .? Duk magaanan da take masa banza yayi mata don dama tasan hali ba lallai ya tanka ta ba . Takaici Ni ya ishe ta Wannan yasa ta yin shiru zuciyar ta na mata ba Daɗi . Don ita ba haka taso ba sam .


Tafiya suke yi sosai ba ta ƙara masa magana ba haka shima bai da alamun tanka ta ko ya bata Amsa akan tambayoyin da take masa. Ear phone din sa ya gyara yana receiving call . No Shureim ka koma mun kusa Isa Gidan Ammie da Safe ma haɗu A Barack . Ba tare da ta ji mene Shureim din yace ba ta taji ya basa Amsa da Okay yana mai Cigaba da Driving ɗin sa a Hankali . Wani irin mahaukacin katafaren Gida ne suka isa . Inda Ko ina tun daga Farkon gidan har bayan shi Sojoji ne Masu Bama Gidan tsaro da kariya . Ko ba'a faɗa maka ba Gidan babban Soja ne wanda ya amsa Sunan shi . Cikin Arrogant Muryar sa irin na Sojojin nan marasa Kirki ba tare da ya Juyo ya kalle ta ba ya Kira sunan ta Da " Neesa ".  

Juyowa tayi tana kallon sa tare da amsa shi tana faɗin "Na'am Adnaan. Neesaa Wai yanzu bakya jin kunya na Har kike iya kallo na da Buƙatun ki ?, Bakya jin kunyar a matsayin ki ta mace yar shekaru 28 baki kawo mun mutuncin ki ba gidan mijin ki .? Ke bakya jin komai ne na damuwa ko nadama.?  


Kallon sa Tayi tana Sauke Farar Gilashin Idanun ta kamin tace" Adnaan Mutunci fa kace ?, Wani mutunci ne ban kawo maka ba Tarbiyya ce bani da shi ko iya kula da miji ne ban iya ba . Iya Girki ko sanin yanda zan gyara komai nawa dana miji na naga ya zama safe . Ko kuwa wani Abu budurci ne ban kawo ba wani tantani shikenan sai Ka kasa yafe mun duka ina da Wa'annan Qualities Din ka manta dashi . 

Wani irin Tsawa ya daka mata Don ya lura shashasha ce Aneesa . Ke rufe mun baki ." Shiru Aneesa tayi tana raba Idanu Jin motsin ana Ware masu Gate ɗin Gidan yasa Ta mai da Hankalin ta Gurin tana mantawa da duka ɓacin ran nasa . Shiga da moton nasa yayi zuwa Farfajiyar gidan Tun kamin su fito Sojojin ke Kamewa suna sara masa don sun san tsauri da zafin Rai irin na Adnaan . 


Hannu tasa tana Kokarin bude Murfin Moton ta fito kawai sai taji ya riƙe Hannun ta yana cewa " Zan yi magana dake . A hankali ta Juyo tana cewa " Yes Ina sauraren ka . Bana Son Ki faɗa ma Ammie komai kawai mu muka yi deciding mu dawo Nigeria . Sannan Ni da Safe zan Wuce Barack , wuraren 11am zaki iya tafiya Gidan namu .  Jin furucin sa kan Abun da take SO yasa ta Sakin masa Murmushi tana cewa " Ok Half World. 


**

Tun ƙarfe 9:am na Safe Zainabu ke Gidan su Zahra tana Jirar tashin daga barci amma itace har kafe 11am sannan ta fito tana tukuki tamkar Wanda aka yi mata Wani Abun That's her behavior duk idan ta tashi haka zaki ga tayi ta fushe² tana cuno baki na tsananin Tsiwa . Inna Salame ce tace " Auta na Ga Kawa nan ta zo Wurin ki tun ɗazu take Jirar ki baki ta shi ba . Juyawa Inda Zainabu take Zahra tayi inda taga Cikin Sauri Zainabu tayi mata alama Da Ido wanda Ganin Haka yasa Zahra fahimtar Akwai Wani Abin mai muhimmanci . Bara ina zuwa yanzu . Juyawa tayi Ɗakin Inna Salame Tana Ɗauko Hijabin ta tare da kallon Zainabu tana cewa " Zainabu taho muje daga Waje . Kallon Inna Salame tayi tana cewa " Inna Bara mu je waje mu dawo . 


Kamin Inna Salame tayi magana ne Talatu ta katse su wacce take Fitowa daga Banɗaki tana aje butan Hannun ta tare da cewa " A'a Zahra Ina kuma zaku je haka.? Wai makarantar bokon kun aske shi  ne yanzu bakwa zuwa ?. Kallon ta suka yi suna ficewa da Sauri daga Gidan yayin da Zahra ke fadin " Baba na nan kar ta jaza mana . 


A bakin layi ne suka tsaya Zainabu na cewa " Ke Zahra wai kin ji labarin za'a ba Ɗan me kunu Sarauta?  Yaje ya saya gari ya gari Har Zazzau . Kama Baki Zahra tayi cike da mamaki tare da cewa " Dan me kunun.? Kwarai kuwa .? Zainabu tace tana kallon Zahra Ido cikin ido . Mai lalata yaran ne zai amshi sarauta.? Ta na ina kenan.? 


Ke na Layin mu mana shine za'a naɗa shi Sarautar . Tab Aiko ba zai yiwu ba . Ni wallahi ba zai zama shugaban mu ba ,bayan kowa yasan halin sa . Don dai yana da Dan Rufin Asiri ? , Bara ki gani kina da Kudi a hannun ki?. 


Zainabu ne tace " A'a wallahi daga Ni sai Naira hamsin . 


Ke Nima bani da Sisi amma kin ga Wayar nan tawa itace mun hujja zan kunna aji halin sa yanda za'a ji a soke wannan Sarautar nasa . Menene Hujjar taki Zahra?. 


A'a kedai mu tafi kawai Ai yau ko a ƙasa ne sai munje Zazzau mun Kai korafin sa Fadan me martaba . Jin hakan yasa Zainabu cewa " Ai ko mu tafi idan munje Wuraren Kawo kila mu samu na Allah ya ƙarika da mu . Kin ga kuwa idan munje can Sukaji mun kawo masu irin wannan Karuwa Ai kudade zamu samu Wuce na Moto ma . Tafiya suke yi zaf² suna barin layin tare da fara deban Hanya . 


Tafiya ce da yayi tafiya Hamsin din Zainabu suka sayi masara na Arba'in da Ruwa . A can Wani gabar hanya suka ga Wani babban Gida bayan sun wuce kawo babu moton kyauta . Zama suka yi a gyefen Hanya Suna cin masarar Zahra na masifa tare da cewa " Ai Dan me kunu ya Shiga uku daga yau ya gama ƙwartanci . 


Fitowa Adnaan yayi daga Barack din sanye take cikin shigar sa Wanda baka ce Soja bane in ba kaga Alamu ko ya faɗa maka ba . Fuskar sa cikin baƙar Tabarau bayan sa Sojoji ne maza Biyu suma da kayan Su bana sojoji ba . da'alama yaran shi ne . Ɗaya daga cikin su ne ya daka masu Zahra Tsawa yana cewa " What are you doing Here.? Juyowa Su kayi suna kallon saurayin da fuskar shi yake bakin kirin .  Taɓe baki Zahra tayi tana juyawa tare da kallon Zainabu wacce suna haɗa ido suka sheƙe da Dariya ji kake Hehehe . Sai kuma ta furta " Baƙi fentin Allah wani Dariya suka kuma sawa yayin da Wannan Soja ya fusata . Ashe inda suke zaune Wurin zaman manyan su ne , Irin su Adnaan Shureim da Sauran su . Kai baku san nan Wurin zama Sojoji bane .? 

Kallon su Zahra tayi tana Sauke idanun ta akan Adnaan da bai yi magana ba yana jin dai yanda suke Yi tsakanin su yana kuma mamakin Rashin kunya irin na Zahra da Ƙawarta Zainabu . Don har gwara Zainabu da taji ance Wurin zaman Sojoji ta ɗan tsorata tayi shiru tana raba Idanu . Ita kuwa Zahra kallon Zainabu tayi kamin ta juya tana ce masu " Ai ashe Wurin zaman Soja ne ,yanzu ma fa sai kuce ku sojoji ne mu baku Wuri ko?. Fusata Dayan Sojan yayi tare da cewa " Kin ga mun kama Miki da wasu ne bayan Sojoji ne?. Tazo mu ji ta makarya ta kawai ,kun debo Ranan ku kuzo kuna neman inuwa ku dame Ni na baku Wuri, Wallahi babu inda zan motsa Gwara ma kuyi tafiyar ku , don kar ku nuna mun tijara saboda na fi ku iyawa.....!
*Tirƙashi.😂*

*To jama'a na free page zai ƙare a page na gaba maza hanzarta Wajen mallakar taki regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*

No comments

Powered by Blogger.