The Sexy Boss 4

 


*D*

*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip

group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*

*D*



*Littafin THE SEXY BOSS na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun ba tare da kin biyani haƙƙi na ba... Regular group ₦300...Vip group₦500... Special ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko kuma ki tura katin MTN ta wannan number 08081202932 Idan VTU transfer zakiyi ki tura kai tsaye ta wannan number 09061466409*



Kuka Umaima ta juma tana yin shi mai ban tausayi na narkar da zuciya , a yau ta gama nadamar Son kuɗin ta ,wanda duk son ka dasu wata rana dole zaka mutu ka bar su , a yau gashi ta jefa rayuwar ta cikin watangariri , tasa rayuka da zukata da dama cikin tashin hankali ,akan son ranta kawai . Kuka take tana ƙarawa har da ƙyaƙyatawa kana ta ɗaga hannayen ta biyu sama tana Addu'oi ,don Muryar ta baya fita saboda tsaban sheƙewa da maƙoshun ta yayi don kuka . Kusan awa biyu ta ɓata bata ko iya motsi ,jin ta take ta zama kaman wata konho fiyau take jin kan ta ,kaman a iska . Tunani take ta ina zata iya miƙewa ma tsaye ,don tsoron hakan take ji , kasantuwar ji da take kaman a iska take ,babu komai da take ji mai nauyi a jikin ta . Ƙafarta ta motsa tana ƙoƙarin saukewa daga saman gadon zuwa ƙasan tiles Nan ta Saki wani irin azabtaccen kuka ,na wahala ,wayyo Umma ,Hajiya Hajiya na shiga uku ya gama da rayuwa ta.! ALLAH ya isa na mugu azzalumi , wallahi sai ka gani Inshaallh ". Ta ƙare maganan kuka na cin ƙarfin ta . A haka tana kuka take motsa ƙafan kaman wanda yayi mata tsami , sai kuma ta dura a saman ƙafafun nata ,tana fara jan jikin ta tare da rarrafawa ta nufi inda taga ya fito don tafi tunanin nan ne toilet ɗin . Da rarrafawa ta shiga don ta kasa takawa da ƙafafuwan ta a haka ta shiga bathroom ɗin . 



Sauke ajiyar zuciya tayi ganin komai na wurin fari ne ƙal ,bin ko ina take da kallo , kamin a zuciyar ta tace " Anya nan Toilet ne kuwa? , Idon ta ne ya sauka akan baf da squater yasa ta girgiza kai a hankali tana faɗin Toilet ne . Tsawon lokaci ta dauka ta rasa ta yanda zata yi amfani da komai ,don tsoron tabawa take ji , a tunanin ta shima kar yazo yana laɓe yana kallon ta itace bata sani ba . Wannan yasa ta juyawa tana komawa inda ta fito , a wannan karon bata nufi gadon ba , Blanket kawai taja tana ƙwanciya a saman sofa cushine tare da lumshe idanun ta da suka sauya daga fari zuwa jajaye . Fuskar ta da idanun ta duk a kumbure suke . A hankali take tuno da rayuwar ta na baya . 


Ƙiirrrrr taji motsi kaman na ƙararrawar ƙofa. Cike da mamaki take kallon Shatin Shadow Kaman na wata mace .! A Hankali ta furta mecece wannan ai , dama aƙwai mata a gidan nan . Banza tayi tana komawa tare da lumshe idanun ta , can jin ba'a bata umarnin shiga ba ,yasa Badi'a ɗaga wayar ta tana kirar Sir Umair . Ohk Umaima taji matan tace tana danna wasu nombobi a jikin glss door ɗin sai gashi ya buɗe , cike da natsuwa take takowa zuwa inda Taga Umaima ƙwance , Sunkuyawa tayi a hankali a matsayin ta na Nurse tana dafa saman goshin Umaima da taji shi zafi rau . Sorry dear . Sir Umair ne ya turo Ni ,na duba ki tare da baki magunguna da zai rage maki zugi . Wani irin kallo Umaima ta watsa mata ,tana daga ƙwancen da take. Cigaba da magana Badi'a tayi da cewa " Yanzu zakiyi iya watsa ruwa ki gasa jikin ki ,ko Ni na taimaka miki?. 



A matsayin ki na wace kenan? . Umaima tayi maganan tare da muskutawa tana miƙewa daga zaune ,don kirar sunan Umair da akayi nan taji ciwon nata ya tafi mata don haushi da takaici . Cike da rashin fahimta Nurse Badi'a tace " Eyya Doctor Umair ya turo Ni. Ga lunches ɗin ki can ,idan nayi maki allurai sai kici abinci ki ƙwanta. Ke baiwar Allah tattara ki fita ki bani wuri. Idan kuma kin ƙi duk abun da nayi maki ,ki sani ki kuka da kanki. Ki koma ki ce masa Ni Umaima nace " In shi ya isa yazo yayi mun duk abun da kika lissafa zaki mun ,ina jiran shi ,fita ki bani wuri...... Tayi maganan a tsawa ce ,wanda yasa cikin sauri Nurse Badi'a ta aje mata basket ɗin tana cewa " Ohk ma". Ɗaukar ƴar box ɗin ta tayi cikin sauri tana fichewa daga Bedroom din , a zuciyar ta tana tunanin wacece Umaima? Kodai Umair yayi aure ne dama? Ko kuma already yana da matar sa ce ,sune basu taɓa sani ba. 



Bayan Nurse Badi'a ta fita ne Umaima ta kalli Basket din dake  shaƙe da different types na dishes kala kala , ƙamshi duk ya cika ta , amma bakin ta ba dadi ,wani irin ɗaci ma takeji . Ƙwallah ne ya ciko idanun ta ,tuno da ada baya yanda take ,cin abinci kaman ita ce tayi kan ta . Kullum a haka take ,bata ma iya sana'a indai bana ci bane . Sauke ajiyar zuciya tayi tana tuno da malaman Maths ɗin su , da tana shigowa idon ta akan Umaima yake , don tasan a tauna take kullum ,nan cike da masifa zata ce fiddo da abun bakin ki. Don dole Umaima zata fiddo da komeye take ci ,ta wurgar ta Window ,sannan malaman zata rabu da ita . Allah sarki Malama Ko tana ina Oho .


***


A hankali take takowa tare da shigowa office din Sir Umair ,Wanda Jin ƙamshin Ru'aifa kaɗai yasa shi saurin ɗagowa don yasan tabbas yayi sabuwar baƙuwa . Zama tayi tana bin sa da kallo ido cikin ido ,duda shima bai sauke nasa tsayayyun idanun ba . Sunana Ru'aifat.! Ehemm?? Yayi maganan yana maida hankalin sa sosai akan ta.  Gyara zama Ru'aifa tayi tana kallon sa tare da sakin masa wani irin murmushi na ƴan duniya tana ciza laɓɓan ta na ƙasa tare da cewa "  i hope ka fahimci inda na nufa. Murmushi yayi mata hushiryar sa na bayyana ,yana sa hannun sa tare da shafa sajen fuskar sa . Lumshe idon ta tayi da take ƙara ƙankantasu a dole ga Sexy eyes tana gyara zaman ta. Gani tayi Umair yakai hannun sa tare da ɗaukar wani dan Remote Yana latsawa . Sai ga security ya shigo . Sir". Yace tare da maida hannun sa baya . Fitar mun da ita . Ke tashi ki bani wuri. Cikin sauri Ru'aifa ta ɗago tana kallon sa . First in her history ,tazo wurin namiji ya koreta ya nuna baya buƙatar ta . Wani irin ciza yatsa tayi na takaici zufa na karyo mata ,a lokaci guda idon ta yayi jah. Kar ka ƙara barin ko wa ya shigo ina buƙatar hutu. Ohk sir. Security n yayi maganan tare da shirin tasa Ru'aifa . 



Kai da Allah ɗan dakata ,da ƙafana na shigo da ita zan fita . Dakatawa secutin yayi ganin ta miƙe tana shirin fita ,sai kuma ta ja ta tsaya , juyowa tayi tana kallon Umair kana tace " I will be back soon Umair". A sauka lafiya.! Yace mata tare da maida hankalin sa kan computern gaban shi .  Har sun kai kusan daf da zasu bar office din ne ,Umair yayi kirar security n . Amm Nurse Badi'a Zata zo ,ita ka barta ta shigo.  Jin haka yasa Ru'aifa saurin juyowa tana takowa cikin sauri zuwa inda yake. Kai tsaye tace " Me yasa ita zaka barta ta shigo? Ohk itace dadiron naka?. Kaman ba zai bata amsa ba ,don ya lura yarinyar bata da kunya , tabbas inda badon yau yana cikin annashuwa ba ,da babu abun da zai hanna shi hukunta ta . Ba ita ce dadiro na ba , matata itace cikakkiyar dadiro na , taje ta duba mun lafiyar ta ne , fuche ki bani wuri. Wani irin bugawa ƙirjin Ru'aifa yayi ,cikin sauri ta juya tana fichewa , wanda kamin ta bar farfajiyar asibitin ta fara kirar Hajiya Turai... 



Cike da annashuwa da farin ciki Hajiya Turai ta ɗaga kirar don tasan haƙar su yakai ma gaci. Hello". Hello Hajiya anya kuwa kin san komai game da Umair kuwa? Har yana da mata ne baku taba sani ba ? Kuna ina hakan har ta faru , to  Umair yana da Aure yana da mata ,kuma tunanin da muke akan sa sam ba hakan bane . Ke wannan wani irin shashanci ne? Shi ya faɗa maki? Ko kuwa labari kika ji ? To ƙarya ne wannan ba gaskiya ba. Hajiya Turai tayi maganan kan ta tsaye . Yanzu nan yake shaida mun da bakin sa fa.! What??? Hajiya Turai tayi maganan tare da tashi daga kishingiɗen da take . Oh ALLAH , ke Ru'aifa ki sani Ni ban yarda ba sam da wannan batun naki. Uban sa fa nake Aure. Idan Umair yayi Aure dole zan sani , don haka kar ki dawo sai kin san gaskiyar komai . Don nafi tunanin ba Aure ne yayi ba , indai shi ya faɗa maki Yana da mata ,to aƙwai wacce yake harin Aure ,kuma dole na dakatar dashi daga yin hakan . Yau Alhaji Ahmed zai dawo ƙasan nan ,zan tare shi da maganan Auren nasa , dole Ni zai bai mawa wuƙa da nama... Nisawa Ru'aifa tayi kana tace " To Hajiya zan cigaba da shiga jikin shi har na gano gaskiya ,ki bani ƙwana uku . Yowa...


***


Kallon Nurse Badi'a yake jin yanda take labarta masa Abun da Umaima tace , har tana cewa itace nan Umaima. Cikin rashin fahimta yace " Wacece Umaima?? Wurin matana Fah nace kije .! Yass Sir itace tace hakan ,wai itace Umaima. Shiru yayi yana tunani a zuciyar sa yana cewa " Ohk itace Umaima , wato dama sunan ta Umaima kenan. Ohk yanzu bari zan koma na rarrashe ta ,ki koma office ɗin ki. Ohk sir tayi maganan tare da juyawa , a zuciyar Badi'a cewa take " Gaskiya wannan tayi dacen duniya da har ta samu Dr Umair a matsayin miji , gashi ko ba'a ce ba kasan yana jin ta a ransa sosai , tun da ba haka yake mawa watsatstsun matan da suke sheƙe ayar su ba. Ko da yake ai ita matar sa ce . A haka ta fice tana tunani daban daban . Da ƙarshe ne ta furta gaskiya Sir Umair yafita ƙyau .


Bayan fitar Nurse ɗin ne ya miƙe tare da tarkata abubuwan buƙatar sa , don tun da ya baro gidan hankalin sa ke akan Umaima , duba time yayi wurin to 5 kenan , a sarari ya furta me be ma bata motsa daga inda take ba. Keys ya ɗauka yana fichewa cikin sauri , moton sa ya nufa , ƙirar wane yaro , yana shigar ta tare da ficewa daga farfajiyar asibitin . Yana kan driving ne wayar sa ta hau ruri , a hankali ya ɗau wayar yana furta sunan " Julayb. Hlo mutumin kana ina badai ka dawo ba?. Yas Ina  cikin garin Lagos yanxu haka , a gidan ka daka saba holewa. Dariya Umair yayi fahimtar inda yake . Ammm tunanin Ya tsaya yi na Umaima tana wani hali yanxu , sai kuma a zuciyar shi yace " me yasa kake wani damuwa da ita ne?. Shareta..! Ohk Julayb ina zuwa zan ƙariko yanzu. 


No comments

Powered by Blogger.