Tabarmar kashi 2

 *H U G U M A*




*_TABARMAR ƘASHI_* 💔

_Arewabooks:Huguma_

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 02

*_1988_*


         Cikin madaidaicin falon matsakaicin gidan,wanda bai cika da wani kayan ado da qawa na rayuwa ba,saidai tsananin tsaftar data bayyana kanta jikin kowanne loko da saqo na gidan zai matuqar burgeka tare da daukar hankalinka,har kayi sha'awar matsakaicin gidan.


            Kyakkyawar macace fara sol,irin farin da zai iya daukan hankalinka,tare da alamta maka cewa lallai mutum yana da nasaba da wani yare cikin yarukan nigeria zuwa afrikaans da kowa yasan fatar duk wani dan yarensu farace,koda akwai baqaqe suna wahala qwarai. Duka duka shekarun haihuwarta a ido ba zasu haura ashirin ba. 


          A gurguje take sakawa yaron dake tsaye a gabanta uniform dinsa,tana gyara masa kwalar rigar uniform din,lokaci guda kuma tana jijjiga yarinyar dake goye a bayanta daketa faman tsala kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta.


          Kana kallonta zakasan a rude take,uwa uba kuma alamu sun nuna sauri takeyi sosai,fadi takeyi cikin yanayin damuwar dake shinfide akan fuskarta


"Yi shuru......yi haquri yanzu zamu wuce kyasha iska a hanya" ta fada fana durqusawa tana qoqarin sanyawa kyakkyawan yaron da sumarsa mai yawa da santsi ke sake kwantowa gaban goshinsa saboda duqawar da yayi zai karba safar da take qoqarin saka masa


"Zansa da kaina ummee"


"Bari na dauko maka lunch box dinka da hijabina saimu wuce,kaima ka kusa makara yau" tayi maganar tana miqewa,dai dai lokacin da aka bankada labulen falon aka shigo.


           A nutse ta daga kai ta kalli matar,wadda zasuyi kusan sa'anni da ita,idanma ta girme mata duka duka baifi ta bata shekara daya ba. Ita dinma ita ta kalla suka hada ido,saita dauke kai tana yatsine fuska,ta kuma tattara dukka bacin ran duniya ta azawa fuskarta,ba tare data ko kalli sassan da matar gidan take ba,ta wuce kanta tsaye zuwa kitchen din gidan.


          Wani abune yazo ya tsaye mata a wuya,duk da cewa idan da sabo yaci ace ta saba da mummunar hali da dabi'ar ta,amma akance,duk mutumin da yasan daraja da martabar kansa baya iya jurewa cin xarafi daga wajen ko waye,tana da dukka hanyoyin da zata cusguna mata ta hanata jin dadin zaman tarensu,to amma wannan ba shine muradinta ba a halin yanzu,don haka tayi qoqarin share wannan daga ranta,ta wuce kitchen din tana dan bubbuga goyon nata data samu ta lafa da kuka zuwa yanzu.


            Tsaiwa tayi turus tana dubanta cikin kitchen din,lunch box din yaron da tazo dauka tuni ta budeshi,ta kuma zazzage duka soyayyen chips da indomie din data dafawa yaron,wanda su kenan sukayi saura cikin gidan nasu,sai yau da take sanya ran samun albashi take tunanin ta biya kasuwa ta taho masa dasu.


         Ba yau ne karon farko data fara yi mata irin hakan ba,saidai na yau din yafi na ko yaushe bata mata rai da quntata matuqa,idan a baya tanayin hakan ta qyaleta ta debo wani ta dafa masa,yanzun basu da sauran abinda zata dafa masan,don haka cikin muryarta data cika da bacin rai tace


"Wanne irin abune haka?,bakisan abincin waye bane da kika juye kina ci?" Cikin gadara ta waiwayo,ta watsa mata wani banzan kallo da ya sake tunzurata matuqa


"Ko abincin me gidan ne ina da right din naci qarewa ma kenan,tunda dai yaya na ne ya kawo,guminsa ne,saboda haka banga wanda ya isa ya dinga yimin shamaki ba" wani mummunan bacin rai ya yunquro mata,taji ya tsaye mata a wuya,kamar ma da qyar take zuqar numfashi,har batasan sanda ta isa gareta ba ta tankwabe plate din abincin ya warwatse a qasa ba. Itama abun yazo mata a bazata,don bata taba tanka mata ba,duk da ire iren wadan nan abubuwan da take mata masu yawan gaske.


          Da yatsa ta nunata tana kafeta da idanunta da suka canza launi


"Wannan abincin dama saurana binciccikan da kike zuba rashin mutunci da rashin tarbiyya a kansu to ba yayan naki bane ya kawosu ba,gumi na ne ke dashi duka kuke ci,kuma daga rana irin ta yau kinci iya rabonki kenan,duk ranar da kika qara saka hannu kika taba min wani abu dana ajiiye cikin kitchen dina,bama kitchen dina ba gidana ma gaba daya sai nayi maganinki naga uban daya tsaya miki" tuni ta miqe tsaye,gabanta yana faduwa saboda ta tsorata da yadda ta ganta,ta jima tana burin wannan ranar dama


"Ni kika zaga?" A fusace ta daga kai daga kwashe lunch box din yaron ta dubeta


"Muddin wannan shine zagi to na zagekin,kiyi duk abinda kika iya"


"Wallahi wallahi sai na sakaki kinyi nadamar wannan abun da kikayimin,zakiga iya matsiyina a wajen dan uwana"


"Na nawa kuma?,annamimiya?,wadda ta sanadinta na rasa duk wani walwala jin dadi da fahimtar junan dake tsakanina da mijina kuma me yayi saura?,ai ba abinda ya rage sai abu daya......"


"Wannan abu dayan shi zan ida" ta fada idanunta carr a tsaye cikin nata. Haka kawai ta samu kanta da faduwar gaban fitar lafazin daga bakin FAUZIYYA,amma saita gyada kai


"Karki fasa shashasha wofi" kai ta jijjiga da qarfi,sanna tabi takan indomie din da tayi kaca kaca a qasan kitchen din ta fice.


           Kasa tsayawa ta tsaftace gurin tayi,sai ta juya kawai ta fice ta saka yaron a gaba zasu fita,har taje tsakar gida ta dawo,ta laluba maqulli ta datse qofar falonta ta wuce da key din,abinda bata taba yiba tsahon zamansu da fauziyyan.


             Tun daga cikin gidan harta isa titi,bus ta iso suka hau kwanyarta empty take,babu abinda yake mata kai kawo sai zallar illar da zaman fauziyya cikin gidanta tayi mata,ta jima da sanin cewa FAUZIYYA annoba ce cikin gidanta,tun daga randa ta tsoma qafarta cikin gidanta bayan rasuwar mahaifiyarsu......komai ya fara jagule mata,makira hatsabibiya kuma annoba,wadda ta kwashe dukkan wani walwala da jin dadi gami da fahimtar juna dake tsakaninta da mijinta da sukayi auren soyayya.....tayi amfani da matsananciyar qaunar dake tsakaninsu ta jini daya,uwa daya uba daya,take juya akalar gidan,take kuma juya komai yadda taga dama.


           Bata taba damuwa da furucinta ba,amma a yau abinda ta fada din ya tsaye mata a rai,har ta sauke yaran bayan ta siya masa biscuit da drink ta hadashi dashi,ta kuma wuce zuwa nata gurin aikin.


          Sukuku ta wuni,har zuwa lokacin tashi aiki yayi. Tana tsaka da tattare kayanta kira ya shigo wayarta,a mamakance ta dakata tana duba number,number makarantar yaronta ne,gabanta ya yanke ya fadi,to me ya faru?,saita koma ta zauna tana rungume yarinyarta a qirji ta amsa wayar.


            Tayi mamaki sosai jin cewa har yanzu yaron yana makaranta fa ba'a zo an daukeshi ba,mamaki ya cika kwanyarta,ta sani abbansa baya wasa ko jinkirin zuwa daukarsa,to amma a yau din meye ya faru haka?,sai ta katse tunanin ta soma laluben layinsa.


           Sau uku tana kira ana rejecting,zuwa sannan mamakin dake qasan zuciyarta ya gaza boyuwa ya bayyana har saman fuskarta


"Anya kuwa lafiya?" Ta yiwa kanta da kanta wannan tambayar,irin hakan bai taba faruwa ba,don haka ta sake gwada kiran nasa a karo na hudu,amma sai take yankewa kafin ma takai ga shigar,alamun dake nuna anyi blocking dinta,ko akwai qaqqarfar matsalar network,don haka ta katse dukka wasu wasi wasi nata,ta hada komai nata a gurguje a jaka,ta dauki yarinyar ta baro office dinsu.


           Tana gab da bakin gate taji ana matsa mata hon,a dan hanzarce ta waiwaya,matashiya ce data kusa shekarunta zaune cikin motarta,suka hada idanu saita sakar mata murmushi yadda fuskar waccar din take shinfide da murmushi,duk da bata shiryawa hakan ba.


            Abokiyar aikinta ce kuma qawa a gareta,duk da ita din tana dan jan jiki da qawancensu,ganin cewa akwai tazara me yawa a tsakaninsu cikin gidan auren kowaccensu,amma tsananin kirkinta da kulawar da take bata ba zata iya sanya hannu ta tankwabe ba


"Yauma guduwa zakiyi,to Allah ya kamaki,shigo na saukeki" murmushi ta sake sakar mata,duk da cewa ba'a nutse take ba


"Ayyah,ba haka bane wallahi,yau din ba gida na nufa kai tsaye ba,saina tsaya na dauko yaro a makaranta" harara tadan jefa mata


"Shi din ba yarona bane nima?,ki shigo kawai muje"


"Na gode" ta fada tana zagayawa daya side din,batason zancan ya tsawaita,don hankalinta ba'a jikinta yake ba,gaba daya yana kan yaron. Suna hanya tana janta da hira,saidai gaba daya bata da wanna sukunin,lokaci lokaci tana sake gwada number wayar data kira dazu,amma sam taqi shiga ko sau daya ne.


           Da gudu ya taho ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya,farar fuskarnan tasa tayi ja,kwantaccen gashinsa duka ya hargitse,bai taba dogon zaman jira irin haka ba,yana cikin sahun daliban da mahaifansu ke fara daukarsu saboda yadda ya damu da al'amuransa.


            Har qofar gida ta ajjiyeta,ta fito rungume da babyn,yaron yana dauke da jakarta,ta zagaya ta bakin window tayi mata godiya sosai


"Wai meye a ciki?,ai mun zama daya" qaramin murmushi ta saki tana juyawa zuwa cikin gidan,cikin Zuciyarta cike da mamakin karamcin matar,da yadda take sonta,yaron yana biye da ita yana mata qorarin yunwa yakeji


"Abinci zan fara dafa muku in sha Allah"ta fada tana jin tausayinsa na tsahon zaman da yasha,gashi bai samu tafiya da abinci ba,tasan dole kuwa yasha yunwa.


           Zaune yake a tsakar gidan saman kujerar plastic daga dai dai bakin qofar falon,shi din ta fara gani,sai a sannan ta tuna cewa ta kulle falon,bata bar masa key din baa,kuma koda wanne lokaci yana iya dawowa tunda bashi da tartibin lokacin fita ko dawowa,tun bayan da ibtila'i ya fada masa.


"Subhanallah" ta fada a ranta,sai tayi sallama a nutse tana sake qoqarin karantar yanayinsa,kai ya cira a hankali ya sauke kallonsa a kanta.


            Mummunar faduwa gabanta yayi,wani irin hargitsatsen kallo daya watsa mata shi ya sanyata cikin rudani,batasan me tayi masa banda kulle qofa da tafiya da key din,kallon daya watsa mata yafi qarfin wannan laifin,kallo ne na zallar qasqanci da kuma tsana,tasan dai ranar yau lafiya qalau suka rabu,ya fita cike da murna zai karbo upper dinsa aiki ya samu,suna ta murna dukkansu tare da saka ran fita daga tsanani zuwa sauqi,sai dukka gwiwarta tayi sanyi da irin nau'in kallon da yake jefa mata.


         Kafin ta qaraso ainihin tsakar gidan sai wulgawar fauziyya ta gani,wadda kanta ke daure da bandeji da yayi tsatstsafar jini gaba daya daga samansa,ta nufeshi a gigice ta cukuikuyeshi tana neman mafaka a bayansa,bakinta na wani irin rawa na zallar tsoro da firgici take cewa


"Na shiga uku akh,gata nan ta dawo,don Allah ka boyeni,kada ka bari ta qaraso,wallahi zata qarasa illatani kamar yadda taci alwashi" tayi maganar tana wani irin haki da tawar jiki,kamar wadda tayi gudun kwana da wuni.


            Baki kawai ta saki galala tana kallon fauziyya,qwaqwalwarta gaba daya ta rikice,me take nufi ne?,saita maida dubanta ga bandejin kanta tana mamakin me ya sameta daga fitarta


"Bata isa tayi miki komai ba,a yau qarshen al'amarinta yazo,muguntarta a kanki kuma ta qare!" Muryarsa mai zurfi dake fita da amon fushi ta fusgi hankalinta,saita maida dubanta kansu gaba daya,kwanyarta na sake rikicewa da salon maganganunsu da ba ganewa takeyi ba.


_uhmmm,me karatu bari mu tsaya a nan,bazance komai ba_



FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070


VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥

No comments

Powered by Blogger.