Soldiers Family 5-6
Page 5&6
__"tafiya sukeyi suna firarsu kamar wasu mutane, Sam basu kula da sunfara shigowa gari kawai seji sukayi wani ya ƙwallah ihu, Yana faɗar munshiga ukku 🙆 jama,a zakuna agari tareda fallawa dagudu Dan ceton
ranshi ihu yake Yana gudu Yana fad'ar zakuna jama,a kowa yayita kanshi zakuna sunshigo shinkafi Zaki jama,a wlh kowa yayita kanshi....habawa ai ko bakinshi baya rufewa ake rufamai baya aduk inda yasamu gungun mutane...sudai su bibibo sukallansu Amma ko a jikinsu balle uwar gayyar dataketa tikar dariya.Wani shayine a hanya irin shayinnan na buzaye, wanda ake sayarwa a keke da ƙatuwar butarshi taruwan zafi yanata sallamar mutanen da suka siya kamar daga sama sukaji ana ihu ana fad'ar Zaki, ga mutane nata runtumawa aguje ai besan sanda ya wantsalo daga kan keken shiba, yayi tullu ya fad'a gefe tare da arcewa batare da ya bi takan butar shayinshi tare da wankewa wasu daga cikin masayan jikinsu ba, se ihu sukeyi suma ga azabar ruwan zafi gatashin hankalin Zaki ya shigo gari.
A fadar sarki kuwa tuni labari ya kai cewar zakuna sun shigo gari, Amma sam me gari da muƙarrabansa basu yadda ba, inda sukace shirmen bazane. Dan a furgita mutane...liman yace ai wannan zancen banzane zancen wofi hakan aikeyi domin ahana kowayin abun gabanshi shima watarana, Yana sallah agonarshi kawar yaranshi sukace, "Wai kura tashigo" duk suka watse yace, "hakan naci gabada sallata duk da a wannan lokacin dagaskene kurar ta shigo hakan ta zagani tawuce Ni ko kallo Bata isheniba balle hankalina yatashi tinda nasan naci dubu se ceto kowa yanutsu yakwantarda hankalinshi koma zakinne dayazo yaganni anan zekomane domin Allah yasakawa dabbobi da aljanu Jin tsorona sabida Allah yabani ilimin hallakasu.." yak'arasa zancen Yana gyaran babbar rigarshi.......to kunji tunda ga liman kowa yanutsu Dan Allah kundaiji abunda yace.."eh munji rankaya Dade wasu daga ciki suka fad'a yayinda wasu kuwa cikinsu ya ɗuri ruwa saboda azabar tsoro ciki kuwa hadda kawo ila...kowa yayi shuru anajiran ganin me zai faru?.
Kamar daga sama suka fara jiyo gurnanin Zaki da ihunshi yafara ciki ilahirin garin irin gurnanin daya keyi Idan yafito farauta yanajin yunwa wani irin gurnani sukeyi me ban tsoro da tada hankali...cikin tashin hankali fad'ar megari aka fara kallan kallo kamar nasu jiran katt su arcee.
Malam liman kuwa wata zuface ta wanke mai fuska tun daga kanshi take tsatstsafowa se shareta yakeyi da babbar rigarshi, Yana gyara zaman rawaninshi Yana zare Ido...to me garimadai hakan ce takasance domin in banda murɗawa, ba abunda cikinshi keyi tuni ya cire rawani Yana fifita dashi yanata famar zare ido...duk Wanda ke wurin a mutukar tsorace yake saboda wannan gurnanin da zakokin keyi domin daji kasan ba Zaki d'aya bane Kuma sekara yawa gurnanin keyi Yana k'ara tinkarosu..gashi kamar way'anda akad'aure kowa yakasa Koda kwakkwaran motsi balle yunk'urin gudu inbadan zarar Ido dashare gumi ba,abunda mutanen wurin keyi.
Acan kan hanya kuwa cikin nishad'i mama ke kallan k'awayen nata dasuketa famar hargowa suna zahayeta itako se dad'i takeyi ahakan suka dumfari fad'ar megarin.....wani irin zaro Ido lilwanu yayi yaron baba lado Yana nuna ibunda adonshi ke hango mashi Yama kasa bud'e Baki yayi magana ganin abunda yakeyi yasa kowa juyawa Yana kallo abunda lilwanu kenunawa atare duk Wanda ke wurin ya k'walalo idonshi waje jikina karkarwa suke kallon mama dake tafe cikin farin ciki da muk'arabanta gasu se tinkarosu sukeyi Kuma suna wannan gunjin....dayawa daga wurin wasu sunyi suman wuccin gadi wasu kuwa tuni fitsarin tsoro ya suɓuce musu domin dai Shi kawo ila ya riga kowa sako fitsari awurin Yana wani marmar da Baki Amma yakasa magana megari kuwa tuni yak'ame yayinda malam liman in banda k'ugi ba,abunda cikinshi keyi Kuma abun kamar wasa kowa yakasa Ko da motsawa daga inda yake...ahakan mama da aminanta suka karaso wurin inda tuni wasu sun cijima aduniyar somammu.
Tsayawa sukayi Dede tsakiyar fad'ar suna zagaye mama tareda Dan lasar k'afar fa itako se murmushi takeyi Amma aranta tana mamaki kawota fad'ar megari da sukayi sunjima suna zagarenta kamun su d'anja baya kad'an suna suna d'aga kohotansu sama...cikin sauri mama tak'arasa inda suke tana rungumo k'awarta tareda manna Mata kiss akai kana ta juyo tana shafa gashin bayan bibibo shima tamanna masa kiss d'in tana doka murmushi...suko baya sukaja tare da yin wata irin girgiza mehad'e wannan gurnanin nasu me ban tsoro Wanda seda yakarad'e ilahirin k'auye hakan Kuma yayi Sana diyyar farfad'owar Wanda suka suma kamun subude idanuwansu suna k'arewa mutanen wurin kallo cikin alamar gargad'i suna bud'ar bakinsu nakusan minti 5 kamun suka juya aguje suka nausa cikin jeji.
Ai kamar jira akeyi sud'aga kana kowa yasamu kanshi cikin wani irin tashin hankali aka fara ihun neman d'auki da gudun ceton Rai shidai kawo ila dayawa mutane akanshi sukabi suna ihu ciki kuwa hadda wasu y'ay'ansa yayin da megari yamik'e yakai sau ukku ana koma durk'usarda dashi tsoro yanashi yin gudun da yake sonyi adurk'uso na hud'u ne ya fad'a akan malam liman dake kusanshi ak'anme seda tayi tullu tukunnah yacika rigarshi da iska ya fad'a gida yayin da malam liman yaji megari akanshi akan ya farfad'o akuma Dede wannan lokacin cikinshi dake d'ure ya facce hakan yasaki wani Masha hurin zawo me shegen wari kamun Mike a 360 yayanki hanyar barin garin Baki d'aya gudu yakeyi zawo nazuba...megari kuwa Yana fad'awa gida bega kowaba awaje hakan yasa banka k'ofar d'akin asabe yafad'a in da labulen k'ofar ya tad'eshi ya fad'a cikin kwallar furar datake damawa kamun sume da k'ofar surufe gammm😂
Eggo kuwada tinda ta hangi mama da wayannan zakunan hankalinta yatashi Kuma duk abunda suke itada aminan nata eggo na kallo hakan bakaramin Kara daga Mata hankali yayiba sanadin hakan yasa tashiga wani mugun shock Wanda yahanata Koda kwakkwaran motsi seda yanzuda kowa yawatse mama tarink'ata tana fad'ar eggo mike faruwa ne tashi muje gida kowa Babu agun...arazane eggo tajuyo tana kallan mama kamun tajanyo da k'arfi tarungume tana dudduba jikinta kamar mene man wani abun..can Kuma tamik'e dasauri takama hannunta suka nufi gida itadai mama tana biye da eggo tana mamakin wannan Al,amarin..!
Dubai
Yau jumu,a Kuma kowa a part d'in habibbty zeyi breakfast dinner dakuma lunch...cike parlourn habibbty yake da zaratan samarin jikonkin nata da yammata se iyayensu Wanda idanda perlon bayada girma to baze tab'a daukarsuba...Yaya suhaif ne yashigo Yana turo kujerar da ammy ke kai yayin da kannenshi ke takemai baya sallama sukayi kowa ya ,amsa kana yasamu wuri kusada iyayen nasu Mata ya,ajiye ammynshi kana yaje gun habibbty yaringoneta Yana gaidata suma duka su Al,Hassan hakan sukayi kana suka shiga kaida iyayen nasu abbu suka fara gaisarwa sa,annan Abba se dady da uncle A kana iyayen mata..daganan Yan uwansu suka shiga gaisawa da juna...seda kowa yanutsu bayan anga gaishe gaishen kana suka fara cin abunci in da suhaif ya fara bawa mahaifiyarsu Amma hajiya suhaima tahana tahanyar karbar abuncin daga hannunshi ta shiga bata hakan kuwa bakaramin dad'i yayi musuba duk da in da sabo sun saba, muddin akazo cin abuncin nan part d'in habibbty to d'aya daga cikin iyayen nasu matane zata Bata...bayan angama cin abuncin ne masu aiki suka gyara wurin kamar yadda aka Saba d'aya daga cikin samarinne yamik'e me suna muhufas yashiga had'a wata katuwar computer dakenan perlon habibbty seda yagama had'a komai kana yamik'e yakoma wurinshi tareda d'aukar wayar habibbty yashiga contact d'inta yadannwa wata nomber Kira ta WhatsApp seda tayanke aka sake Kira kana Wanda ake Kiran yad'aga d'auke da sallama abakinshi yayinda Kuma ya bayyana awannan katuwar computer mekamar Rabin bagon perlon... murmushi yayi kamun yayi magana habibbty tace jalaludeen kana lpy? Cikin far,a da farin cikin ganin ahalinshi jalaludeen yace lpy qalau habibbty kana ya gaisar da iyayen nasu sake wurin bayan kowa ya,amsa cikin farin ciki k'anen nashi suka shiga fad'ar Yaya jalal barka da safiya duk acikin larabci suke maganar Yana amsa musu seda duk suka gama gaisawa kana yadubi alhusain yace little bro yajikin ammy? Amma d'auki Yaya jalal...to allah yabata lpy...duk suka ammasa da ameen kana yammata suka shiga zuba mishi tab'ara Yaya jalal kasiyomun Yaya jalal kayimun kaza hakan sukayita seda iyayen suka gaji kana sukayimashi sallama aka riwani...jalaludeen duka shine babba acikin ahalin gidan Kuma shima sojane sedai Shi Yana aikine a Nigeria acikin garin Abuja.
Bayan ankashe aka Kira Zaid shima hakan akayita yi mishi duk da be cika sakewa kamar Yaya jalal ba bayan anshene aka Kira wata number, Amma me wannan number seda akayi masi Kira hud'u kana yad'aga, Yana zaune cikin office d'inshi atake kyakkyawar fuskarshi tabayyana sedai ad'aure take tamau ba wani walwala atare dashi kallanshi habibbty tayi nadan lokaci kum tace *ALYASAT* kana lpy? Lumshe kyakkyawan idanuwanshi yayi kamun yasake bud'esu cikin so da k'aunar kakar tashi yace lpy qalau habibbty ya k'arfin jikinki? "" Alhmdllh alyasat y aikin? Shiru yayi kamar bejitaba kamun yabud'e baki kamar bayaso yace alhmdllh sa,annan ya shiga gaishe da iyayen nasu dakyar domin jinyakeyi gabaki d'aya ya wahala wannan Yar maganar dayayi danshi baya k'aunar Friday d'innan tazo sabida kiraye2 Nan
Nan shima kannenshi suka shiga gaidashi Amma hankalinshi na kan ammy daketa dokamai murmushi..seda duk suka gama wayar harzeyanke domin yagaji wlh sekawai yaji ance yaya sat I miss you..atake duk anunrin fuskarshi tad'auke yak'ara take fuskarnan sosai kamun yakashe wayarshi kawai...itako muhibbat dataga yayi Mata hakan se kawai tasaka kuka cikin Jin haushi mama Billy tabige Mata Baki karma wani yaji bayasan Kuma ta makaraba domin d'ay d'ayku ne kawai Basu ganiba.
kamun asake Kiran wani hakan akayita Kiran yaran gidan d'aya bayan d'aya duk akagaisa da way'anda basa gari kana akayanke wayar kowa ya fito zuwa wurin aikinshi bayan Al, Hassan ya maida ammy part d'inta tareda damk'arta hannun anty ayame.
Ahakan motocinsu sukabar gidan ajere kamar yadda suka Saba.
Ba,afayikomaiba yanzune asalin cankalen zefara💃
*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500 kacal ka duk me buk'atar complete kuma 700 Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124
Leave a Comment