Saran Boye 74


 No. 74


............“Dabarata ta jingina ciki ga Nu'aymah, da kawo hotonta ita da Yoohan shine burina Sooraj yay fushi yace sai Yoohan ya auri Nu'aymah. Ta hakanne kawai aurenta da Abdallah ko Naseer zai gagara. Duk da bana zargin Nasir da komai, amma inhar shi Nu'aymah zata aura tsugunne bata ƙareba kenan. Amma indai ta auri Yoohan inada yaƙinin zai bata kariya.

Saboda alwashinsa na ranar da aka kirashi akan wannan batun ya birgeni. Ko bayan babu raina ina fatan ya zama garkuwa ga ahalin Firdausi. Sannan Nu'aymah ma zata samu lafiya ta dalilinsa tunda shine likitan da dama aka basu Number sa muka sace ni da Lurwan. Alhmdllh naci nasara, dan kuwa da bakinsa ya furta son auren Nu'aymah, duk da Sooraj bai bashi goyon bayaba a lokacin saboda jin nauyin ƴan uwansa akan su Abdallah na tabbatar yanason bashi. Lurwan ya shiga ruɗanin ganin zai rasa dama ta biyu, hakan ne ya sakashi sake dawowa gareni mu haɗa kai a wannan karonma. Ya kuma bani haƙuri da tabbacin zaisa Abdallah ya maida aurensa da Adawiya da zarar anyi aurensa da Nu'aymah. Na nuna masa na amince dan na samu a gama maganar auren Nu'aymah da Yahya cikin kwanciyar hankali. Daga haka na cigaba da gayama ALLAH dan agareshi kawai nake hangen samuwar nasarar kubutar da Nu'aymah daga tarkon Lurwan. Hidimar aurar da ƴaƴa kawai nake a zahiri, a baɗini kuwa ba wannan bane a gabana sam, shiyyasa na samu Firdausi da shawarar duk yanda zatayi tayi kar Sooraj ya bama Abdallah ko Nasir Nu'aymah, gara a auramata Yahya bisa wasu dalilan dana lissafa mata a lokacin waɗanda Alhmdllh sunyi tasiri a gareta. Sai da ina shirin fitowane naga Sooraj tsaye bayanmu alamar yaji komai da muka tattauna kenan. Hakan yamun dadi, dan insha ALLAHU koba komai inada yaƙinin samun nasara”.

      Ta share hakawayenta ga murmushi a fuskarta. Cigaba tai da faɗin,

       Jin tabbatuwar ɗaura auren Nu'aymah da Yahya shine nasarata ta farko da kobayan nabar duniya inason ƴaƴana su tuna suyi farin cikin aikin alkairi dana taɓa ƙullawa a rayuwata ta zaman gidan nan. Ko murnanr aurar da ƴaƴana guda biyu a ranar banyi murnarsa da tsananin farin ciki ba kamar yanda nayi na Nu'aymah. Amma a baɗini nabar wannan nasarar tawa. A zahiri kuwa na shiga jerin masu shiga ƙololuwar tashin hankali kamar su Abdallah da Lurwan da rayuwarsu ke a gigice. Dan wlhy aranar da aka ɗaura wannan auren kaɗan ya hana zuciyar Lurwan bugawa a gidan nan. Ya kuma sake ɗaukar alwashi kala-kala akan koma ta halin ƙaƙa saiya samu cikar burinsa. Wannan furici nasane ya sakani saka ƙanwata bin ƴan tawagar kai amarya. Sai da na tabbatar Nu'aymah ta shiga ɗakin mijinta lafiya ta hanyar ji daga gareta sannan hankalina ya kwanta. Duk da na tausayama yarinyar inda ƙaddara ta jefata. Amma sai nai mata fatan samun kariyar UBANGIJI da nasarar canjasu dalilin shigowar tata cikinsu. Daga haka na cigaba da ɓoyayyar jiyyar da mijinane kawai yasan inayi da duƙufa neman gafarar UBANGIJINA ko zan samu sassaucin raguwar zunubaina. Abinda yasa nabiku Austria ganin Nu'aymah saboda kozan samu na nema gafarartane. Ban saniba ko kafin ta dawo ƙasar ni na rasa raina. Ta ɗayan gefen kuma inason sakama Lurwan idone. dan a yanzu na daina sanin komai daga shirinsa saboda ya fahimci bana tare dasu a yanzu. Ko amincewa da zaman Adawiya da nai gidansa tanamin aikin sakamasa idone. Dan duk wani motsinsa itace ke kirana tana sanarmin batare da ita kanta tasan aiki takeminba dan ban fito fili na sanar mata manufataba”.

      Wannan shine labarina, shine ƙaddarata, shine kuma son zuciyar SARAN ƁOYE dana aikata muku Firdausi, nasan bazaki taɓa yafeminba ke da zuri'arki, shiyyasama bazan matsaba wajen neman yafiyarku. Kai koma ke kin yafemin ALLAH bazai yafemin ba, dan nasan na cutar daku iya matuƙar gaya ta hanyar SARAN ƁOYE. na aminta ku kaini kowace irin kotu a yankemin hukuncin daya dace dani kafin naje na fuskanci babbar shari'ata ga babban alƙali”.

     Ta ƙare maganar da fara tari mai tdanani. Sosai yanda take tarin guda gudan jini na faɗowa ya tada hankalin kowa a falon. Umm ta matsa gareta ta riƙeta sosai jikinta tana kuka. Da ƙyar aka samu tarin ya lafa. Duk da Yoohan najin zafinta har yanzu, dan shi baiji wani tausayin taba, duk da ƙoƙarin ƙulla aurensa da tai da Nu'aymah a ƙarshen ɓarnakun data tafka, amma sai ya bada shawarar a kwantar da ita zata samu sassauci daga yawan tarin. Da shawararsa akai amfani wajen kawo ƙaramar katifa aka kwantar da ita ɗin. Aiko sai tarin ya lafa sosai.

     Murmushi tayi tana kallonsa, murya na rawa tace, “Nagode Yahya, ALLAH ya azurtaku da ƴaƴa nagari da zasuji ƙanku, ALLAH ya sauki Nu'aymah lafiya naga gudan jininku kafin nabar duniya”.

     Uffan baiceba, baima nuna yaji mita faɗaba, amma jama'ar falon sun amsa mata da amin, duk da wasuma irin zuciyar Yoohan garesu basuji tausayin nataba.


          Abban Abdallah da keji kamar ya tashi ya ƙarasa rayuwarta saboda zuciya data kumesa ya yunƙura zaiyi magana Hajjo ta dakatar da shi ta shanyar ɗaga masa hannu. Dole kuwa ya koma ya zauna yana zare idanu.

        Tai gyaran murya sannan ta gyara ƙafarta mai ciwo da dubansu ɗaya bayan ɗaya ta fara faɗin, “Karma ka wahal da kanka wajen ƙaryata abinda duk Fauza ta faɗa Lurwanu. Idan bakai tunanin ana kallonku ba yau zan sanar maka cewar na jima da fahimtar kai da ita su wanene a cikinmu. Na barkune saboda na muku talalar zuwan wannan ranar. Na jima ina zargin akwai wani abu a zuciyar Lurwanu game da ɗan uwansa, dan yasha kawomin sukarsa akan miyasa kaza da kaza dole sai da umarnin ɗan malam akeyi a gidan nan?, sai dai ina nuna masa ɓacin rai. Amma ban sake tabbatarwa ba sai bayan tsaida ranar auren Abdullahi da Zainabu. Da kunnena naji dukkan abinda kuka tattauna akan soyayyar da Adawiya kema Abdullahi, tare da shirinku na bayan mutuwar Zainabu zai aureta. Hankalina ya tashi, dan zan iya cewa wannan shi e sanadin girmama samuwar hawan jini na ma. Na riƙe komai a raina na kasa faɗa har ƴar uwata tazo diba ni (Ananah) banso faɗa mataba. amma na fahimci dolene na samu shawara daga wani kafin lokaci ya ƙure. Dan wannan abune mai matuƙar sarƙaƙiya. haka na samu lokaci a wani dare mukai maganar. Itama hankalinta yayi ƙololuwar tashi dajin wnanan zance. Itace ta kawo shawarar ai tunda SARAN ƁOYE kukeyi muma yakamata mubi ta ZAGON ƘASA mu kamaku a hannu dumu-dumu. Itace ta kawo shawarar sace Zainabu ranar daren aurenta, dan hakanne kawai zai wargaza auren cikin sauƙi. A cikin shirinmu Ameer ya shigo rayuwar Zainabu matsayin abokin Abdullahi. Ameer kuwa abokin Naser ne, dan Naser shine mukaba aikin a hannunsa. Nice da kaina na shiga na haɗo kayan Zainabu a ɗakinta, na kuma jajjefa wasu ta taga. Ina cikin yi Yusrah ta shigo ɗakin da alama banɗaki zata shiga. Na tabbatar taga mutum, sai dai ban saniba kota gane waye ko bata ganeba. Abdullahi yaso lalata mana shiri a ranar saboda jan ra'ayin Zainabu da yay tayi akan suyi hira. Sai dai kuma ta dalilin Adawiya hirar batai tsaho ba. Naser ya samu damar ɗauke Zainabu ya kaita wani gida. Bamu dawo da itaba sai bayan sati biyu. Daga haka muka cigaba da bibiyar duk wani taku naku. Hatta da sace Number likitan da zaima Zainabu aiki naji a raina wani a cikinkune ya saceta, sai dai banida hujja shiyyasa nai shiru. Ina kan sani na amince da aurama Abdallah Adawiya saboda ɗana tarkon farko a gareku, inason kuma tabbatar da hannun Abdallah akan shirinku, kokuwa kuna amfani da shi ne kawai batare dashi kansa ya sani ba?. Na kuma hana Yusrah tarewa dan dama bazan yarda ta tare ɗinba. Tafiya da Zainabu Umrah yanada nasaba da son sake tabbatar da komai. Na kuma tabbatar ɗin. Waya da aka ɗagama Khadijah na hana Abdullahi zuwa Nigeria duk a cikin shirinmu ne. Munsa Nasiru ya dawo rayuwar Zainabu ne daman dan ya sake wargaza magar auren da Abdallah keta naci da son sake ganin ya ƙullu tsakaninsa da ita. Da kuma sanin da nai duk cikin shirinkune”.. 

        “Maman Aaida data zama ƙawar Adawiya a saudia duk a cikin shirinmune itama. Mune muka sakata samun kusanci da Adawiya da ɗorata mataki-matakin kasancewa da Abdallah, a tunaninmu ko zaku dawo hayyacinku ku yarda da ƙaddara. Amma sai kuka sake tura kanku a cikin ramuka. A tarayyar maman Aaida da Adawiya ne ya bamu damar sake fahimtar bada sanin Abdallah kuke wani abunba. Dan ba komai kuke sanar masa akan shirinku ba, sannan lallai da gaske yana son Zainabu duk da ya raba hankalinsa biyu akan soyayyarta da dukiyar mahaifinta da kuka ƙwaɗaita masa a rai. Ta kuma hakane muka fahimci banzar sana'a da Abdallah yake ƙoƙarin jefa kansa a ciki. Amma Alhmdllh munyi ƙoƙarin maidosa hanya ta dalilin mijin maman Aaida ɗin, wanda ta hannunsa mukejin duk wani motsin Abdallah a yanzu haka. Maganar cikin Zainabu shine ya hautsina min tunani, saboda batare kukai aikinba yasa ban fahimci komaiba a ciki ba, duk da ina zargin kuɗinne duk da haka. Koda na tabbatar Zainabu takai mutuncinta gidan aure wannan ruɗanin na maganar ciki bai barniba sai yanzu da Fauza ta warware komai akan samuwar ciki da fitarsa. Na kai Uwaliya aiki Abuja ne dama dan Lurwanu yay yunƙurin yin amfani da ita kamar yanda Nasiru ya gano mana hanyar da sukebi wajen aamfani da Rabi itama. Na tabbatar alwashin da yahya ya ɗauka akan gano ko wanene bazai tashi a banzaba. Bakuma zai samu sauƙin ganowarba sai da wani a tsakani. Shiyyasa na tura Uwaliya ta fara sauka gidan Lurwanu ta kwana biyu sannan aka kaita wajen Zainabu. Ita kanta batasan amfani zamuyi da itaba, na ɓoyene saboda fahimtar idanunta a buɗe suke dasan kuɗu itama. Ko nawa Lurwanu ya bata lallai zata amince tai masa aikin daya buƙata akan Zainabu. Ankoyi sa'a shirinmu ya tafi dai-dai saboda Nasiru ma mutumne mai ƙwaƙwalwa da hikima. Hatta da yawan shigowa Najeriya da Abdallah ke yawan yi suna ganawa da Lurwanu duk mun sani dan duk inda yasa ƙafa Nasiru na biye da shi batare da yasani ba. Kai hatta binmu da Abdallah yayi ƙasar da akaima Zainabu aiki nasani. Dan ko a randa Yahya ya gansu suna magana shi da Lurwanu nima na gansu, sanin da nayi babu ta hanyar da zasu iya cutar da Zainabu saboda tsaron da take samu a wajen yasa na watsar da al'amarinsu. A yanzu haka mijin maman Aaida shine ya taso mana ƙeyar Abdallah zuwa Najeriya harya halarci wannan bikin duk da yazone a makare”.

       Ta ƙare maganar da nuna inda Abdallah ke zaune kansa a duƙe tamkar munafuki. Harga ALLAH da yawan mutanen dake falonma sai yanzu sukasan da zamansa a falon. Hajjo ta sake gyara zamanta tana duban kowa.

       “Nasan wasu zasuce miyasa duk nasan wannan amma na ɓoye matsayina na mahaifiya ga waɗan nan yara su duka?. Amsarku itace duk da ni mahaifiyace a garesu fitowa da lamarin kai tsaye dasa sabuwar fitinace da zatafi wadda muke ciki girmama. Dan inhar da tun a wancan lokacin na fiddo komai zasu kare kansu akan ba haka bane, su jefa zuciyarmu a ruɗani mu duka kokuma su canja salo, ko komai ya ɓaci duniya tasan halin da muke a ciki maƙiyanmu dake a waje su sami ƙofar yin kutse cikin wannan zuri'a su ƙarasa ɓarar da sauran abinda ya rage daga garemu. Ƙyaƙyƙyawar rayuwar da aka gina tsahon shekaru zata wargatse ta lalace kowa ya fita a hayyacinsa. Idan hakan ta kasance banci riba ba. Sannan wahalar da malam ya sha akan son gina zuri'arsa baici riba ba kenan shima. Dukansu ni na haifesu, tun a ƙuruciya nasan halin kowannensu. Dama can Lurwanu hatsabibine tun yana ƙanƙaninsa, a cikin ƴan uwan nan nasa babu wanda baisha wahalarsaba. Kaifin addu'a ne kawai ya ladabtar da shi, sai kuma kawaici da iya zama da su da ɗan uwansu yayi. Na yarda inhar ka samu ƙyaƙyƙyawar tushiya a cikin yabanyarka da izinin ALLAH zaka azurta da ƙyaƙyƙyawar albarka. Kasancewar ɗan malam ɗa nagari, mai haƙuri da kawaici, mai juriya da riƙe girmansa matsayin babba ga ƴan uwansa shine ya taimaki wannan zuri'a da kaiwa haka batare da mutanen waje sunyi tunanin samun ɓarakar shigowa cikinmu su wargazamuba. ALLAH yayima ɗan malam baiwa da ƙyautar abubuwa da yawa. Ilimi, hankali, dattako, dukiya, sanin ya kamata, nasaba. Sai dai hakan ba yana nufin zai more rayuwarsa ɗari bisa ɗari ba tunda ya haɗa komai. Shiyyasa ALLAH ya jarabcesa da atsabibancin Lurwanu dana matar ɗan uwansa Mustapha. Suka dinga wajiga rayuwarsa saboda UBANGIJI ya gwada ƙarfin imaninsa. Koni da nake mahaifiya a garesa inajin sha'awar koyi da halayensa na haƙuri da juriya duk da zuciyarsa na ƙonuwa shi da matarsa da ƴaƴansu. Wannan kawaicin da uziri shine ya kaimu ga matakin nasarar da a yau gashi su da sukecin dunduniyar sane a gabanmu suna faɗin tsiyatakun da suka aikata da bakinsu, miyafi wannan nasarar daɗi ga bawa kuwa?”.

       Abban Adawiya ya share hawaye da fadin, “Babu inna, wlhy babu makamancin wannan nasara kuwa, dan hakan yana nuna mana duk mai haƙuri da tsayawa akan gaskiya, da adalci gana ƙasa da shi, ma'abocin bautar UBANGIJI, ALLAH bazai taɓa taɓar da shi ba, ALLAH bazai taɓa ƙasƙantar da shi ba. ALLAH bazai taɓa wulaƙanta rayuwarsa a hannun azzalumai ba. Ni shaidane akan hakan, dan Lurwan yaso jan ra'ayina sosai akan lamarin Yaya, kullum zancensa shine Yaya cutarmu yake a ɓoye. wai tayayama za'ai ace a raba mana gado tare, amma yazo ya fimu komai. Yafi kowa kaso mai tsoka a duka kamfanonin mu. Ga wasu harkoki da yakeyi kuma a gefe masu bala'in bashi kuɗi. Sannan kuma wai ai muduka munada ilimin addini amma tayaya za'ace kowa yafi sonsa da ƙaunarsa dajin maganarsa. Hatta mahaifiyarmu sai abinda Yaya yace takeyi a gidannan. Acewarsa wai Yaya ya asirce kowane kawai amma yake fakewa da malanta. Da farko na fara bin ra'ayinsa. Sai dai ba'ai nisaba ALLAH ya soni da rahamarsa ya fargar dani, danni dai ban taɓa ganin wani abu saɓanin ƙyautatawa ga yaya ba. Da kuɗinsa na gado ya tsaya mana mukai karatu duk da kuwa muma muna dasu. Da kuɗinsa na gado ya dinga mana hidimar rayuwa tamkar mahaifi. Idan mukai kuka shima sai kaga ƙwalla a idanunsa. Idan mukai ciwo shima sai kaga raɗaɗin a fuskarsa. Idan mukai dariya sai kuga tashi fuskar faɗaɗe da murmushi mai tsada. Shine ya nuna mana hanyar tashi mu nema na kanmu, dan shine ya fara shan wahalar kafa dukkan kasuwancin da ayanzu sune suke riƙe da duk wani motsinmu. Shine ya tsaya akanmu mukai karatu tuƙuri bayan ya tattare martabar mahaifinmu ya riƙe mana bai bada ƙofar da zamuyi sakacin da zata kufce mana ba. To miyasa son zuciya zaisa zamuyi sakaci ya sargafe tunaninmu?.  Hakan yasani janye jikina daga wannan mummunar a ƙidar naita istigifari akan zargin da aka sakani nai masa babu gaira babu dalili. Ashe ya koma sun ƙulle da matata suna cutama yaya da zuri'arsa da basujiba basu ganiba. Minene laifin waɗan nan ƙananun yaran da basuma gama sanin rayuwarba balle daɗinta. Basai nace komaiba, dan Fauza azabarma da kike ciki ta isheki. kai ko Lurwanu ka jira naka sakamakon kaima, dan duk wanda yaci zalin gwani rabbi zai saka masa da alkairi a duniya ko a lahira”.

        Abba Musbahu yace, “Tabbas haka zancenka yake Yaya Mustapha. Dan koni ma yaso jan ra'ayina. Sai dai fa ka sanni ni, a zuwan farko na shata masa layi duk da kasancewar sa yayana. Shine dalilin da yasa zama waje ɗaya a Lagos ya nema gagararmu sai da yabi ya lallaɓa yaya malam ta ƙarƙashin ƙasa aka maidasa Abuja aka buɗe masa company wanda ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnar da yake a cikinsa shi da abokan aikin nasa. Domin a duk lissafin ƙarshen shekara idan mukayi sai mun tsamo yawan cuwa-cuwa da akai da kuɗaɗen company. Shi Yaya cayake daga ma'aikatanne. Niko nasan Yaya Rudwan ne dama wlhy. Nayi shiarune kawai dan ina fatan Yaya Malam ya kamashi da hannunsa dumu-dumu. To ashe aikin nasama ba anan ya tsayaba duk bala'in da ake kunnama Yaya malam da ƴan ƴaƴansa biyu da suka rage yanada hannu aciki. Wlhy ko alhakin ƙananun yaran nan bazai barku ku zauna lafiya ba balle kuma haƙƙin yaya malam da Umm-Muhammad da a kullum burinsu su ƙyautata rayuwar ƴaƴanmu a gidan nan. Kaɗanma kuka fara gani yanzu kuma”.

          Momyn Abdallah daketa kuka tun ɗazun tace, “Lallaikam yanzu suka fara gani Musbahu. Wannan wace irin cin amanace haka? Wane kalar son zuciya ce?. Ba yaya kaɗai kuka cutarba ai, muma kammu iyalanku kun cutar damu, kun shiga haƙƙinmu. Wace irin ni'ima ce ALLAH bai baku ba a rayuwa amma ku gaza gode masa har sai kun ɗaura ɗammarar shiga haƙƙin wani. Alhalin dukiyar da kukema zarin ma kunfi mai ita amfana da ita ku da iyalanku. Wai miyasa ɗan adam ɗin da ALLAH yayma ni'ima shike fin tsaurin idon rashin gode masa? ALLAH ya baku ilimi alhalin ga wasu can jahilai ko yanda zasu bauta masa basu saniba. Ya baku lafiya, ga wasu can a gadon asibiti kwance basu da kuɗin neman lafiyar. Ya baku muhallin zama. Ga wasu can suna raɓe-raɓe basu da ko kangon da zasu raɓa. Ya muku sutura. Ga wasu can tufafin da zasusa su rufe tsiraicinsu bai wadacesu ba. Ya baku mutunci da daraja a idon duniya, bayan akwai dubunku da suka fiku shekaru a ƙasƙance. Ya baku dukiyar da bama kuda iyalanku ba, waɗanda suka raɓu da ku zaku iya ciyar da mutum sama da ɗari a kowanne yini. Ga wasu can iyalansuma basa iya wadatawa. Ya azurtaku da ƴaƴa maza da mata,  ga wasu can suna nema da miliyoyin kuɗaɗe basu samu ba. Ya azurtaku da iyaye na gari, bayan ga wasu can iyayen nasu a gidajen baɗala. Duk waɗan nan ni'imon kuka gagara godema ALLAH a kansu, to mikuke jira UBANGIJI ya muku kafin ku gode masan? Mi kuke nema kukuwa a duniya bayan duk waɗan nan tarin ni'imomin da yay muku. Bafa kunfi waɗanda basu da shi bane, ba kuma tsoronku yasa aka baku ba. Ba kuma ƙoƙarin ibadar kuce tasa aka baku ba. Kai jama'a kaicon hannu mai butilcin amsa ga mai bashi. Kaicon zuciya mai baƙin cikin cigaban mai ƙyautata mata, Kaiconku Rudwan, tabbas bazan yafe muku ɗoramin yaro akan mummunar aƙida da kukayiba........”

      Kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana. Shi dai Abban Abdallah ya kasa koda ƙwaƙwaran motsi, kansa duƙe a ƙasa ya gagara kallon kowa. hakan yasa babu wanda zai iya cewa ga a yanayin da yake.

       Baba malam ma dai kansa a ƙasa yake duƙe. Babu mai shaida yanayinsa. Umm kam ganin al'amarin take tamkar a mafarki zuwa anjima zata farka. Zuciyarta ta kasa gaskata komai akan Abban Abdallah da Fauza. Mutanen da sukafi kowa kusanci da su a gidan. Kai jama'a duniya ina zaki kaimu?.....

      Jin kowa bai ƙara cewa komai ba yasa Jay yin gyaran murya. Kusan duk kallonsa sukayi. Ya furzar da numfashi na takaici da faɗin, “To inaga idan kun gama da su zamu kaisu station mu haɗa bayanansu sai mu miƙasu kotu su amshi hukunci kamar yanda shari'a ta tanadar”.

       Tari Addah ta fara kaɗan-kaɗan, hakanne ya saka baba malam ɗagowa ya kalleta ya maida dubansa ga Jay. “Muhammad Jawaad mubar zancen zuwa kotu kaji. Ita wannan kuma miya rage mata a duniyarma gaba ɗaya. Ai wannan izayar da take ciki kawai ta isheta izina. Sai dai mu taimaketa mu miƙata asibiti kawai....”

     Murmushi Jay yayi yana jinjina kai. “Duk da haka malam ai ya kamata su fuskanci shari'a kodan hakan ya zama ilimi ga ƴan baya masu sha'awar sake aikatawa. Duk da tana cikin halin ciwo bashi ke nuna zata mutu ba, mutuwa ta ALLAH ce, takanzo a sanda taso ga wanda taso. Dan haka zamuje asibitin taga likita amma bisa ƙarƙashin kulawar hukuma. Shi ko zamu wuce da shi station”. Ya ƙare maganar yana nuna inda Abban Abdallah yake zaune.

      Baba malam zai sake magana Hajjo ta katsesa da cewar, “Ɗan malam hakan shine dai-dai kuma ya kamata. Kaga idanma da mai sha'awar aikatawa a nan gaba sai ya bada himma”.

      Tarin Addah daya ƙara ƙarfine ya sakasu duk maida hankalinsu gareta. Da wannan damar Abban Abdallah ya samu ya sulale a hankali yabar sashen. Sauran jami'an dake a waje basusan yaya aka ƙareba shiyyasa basu hana Abban Abdallah bi ta gabansuba ya wuce sashensa yaje ya haɗa duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci ya zuba a ƙaramar jikka ya fito. A gaban jami'an ya shiga motarsa maigadi ya buɗe masa gate ya fita batare da shima yasan mike faruwa ba. 

       Daga ciki ma babu wanda ya farga da rashinsa sai bayan an fito da Addah daketa faman zuba aman jini aka saka a mota domin kaita asibiti. Suna wucewa su Jay suka koma kan Abban Abdallah sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye. A take suka hau cigiyarsa a lungu da saƙo na gidan, sai daga baya sukeji daga bakin maigadi cewar ya fita a mota tun kusan mintuna talatin da suka shuɗe.

      A razane Jay yace, “What?!!, shine kuka barsa saboda baku da hankali?!”. Yay maganar wa yaransa. Duk rawa jikinsu ya kamayi suka hau rantse-rantse su basusan mai laifi bane. Ai kota kansu Jay baibiba ya shiga motarsa shi da Bily da Little. Suma duk suka shiga a wacce sukazo. sai da suka tambayi maigadi motar daya fita a ciki da lambarta sannan suka fice a guje.

      Wayar Jabeer Jay ya kira, yana ɗagawa ya ce, “Jabeer inason a baza zami'ai a kowacce hanyar fita garin kano domin tsaidamin mota mai Number..... Ruwan toka”.

     Jabeer na amsa masa ya yanke kiran, C.P ya kira shima dan ya taimakesu.


__________★★


       A gidan su Nu'aymah kam musalta muku halin da suke ciki ɓata lokacine. Dan motocin su Jay na fita a gidan Umm ta yanke jiki ta faɗi. Hakama Malam ƙarami shiɗe musu yayi. Ga kukan da su Adawiya keyi ya taru ya ƙara ɗaga musu hankali. Baba malam kansa dauriya kawai yakeyi dan gaba ɗaya jinsa yake kamar kansa zai tarwatse dan ciwo. Gashi su Yoohan sun wuce da Addah asibiti. Hakan yasa dole aka kwashi su Umm ma zuwa asibitin.


   Ɓangaren Abban Abdallah kam tunda ya fito anguwarsu kai tsaye hanyar Katsina ya ɗauka, shi kansa baisan mi yake shirin aikatawaba. Ceton kansa ko gudun kunya? Ko tsoro?. Gudu ya ke na hauka babu wasa a cikinsa. Musamman daya kasance ta gefe-gefen gari yake tafiyar, dan bai yarda yabi ta cikin gariba sam. Yana fara ɗaukar hanyar Ktn bayan ya gota Dawanau kaɗan ko mintuna goma baiyiba ya ga motar ƴan sanda na binsa a baya. A take ya ƙara ƙarfin gudun motar tamkar ya manta da kasancewarsa Dattijo. Abu kamar a film suka fara rere tsakaninsa da jami'ai.

       ALLAH sarki rayuwa, duk iyawarka baka isa zarce ƙaddarar UBANGIJI ba. Dan kuwa dai wannan ƴar tsere na Abban Abdallah da ƴan sanda sunansa gudu akan igiyar ƙaddara. Dan kuwa bisa tsautsayi sukau taho mu gama da wata mota dake nufo cikin kano. A take waccan tayi gefen titi, shiko ta Abban Abdallah sai ta kife ta fara wuntsil-wuntsil daga titi ya gangara cikin gona. Tun suna jin yanda yake neman ɗaukin UBANGIJI har sukaji tsit, motar kuma ta bugi bishiyar dalbejiya ta tsaya cak.

      Cikin sauri ƴan sandan da dama tuni sun fito a mota suka nufi motar domin bashi taimako. Da ƙyar kuwa akayi kama-kamar ɗaga motar aka zarosa a ciki. Gaba ɗaya jikinsa yayi face-face da jini har ba'a iya gane inane ya bugu koma yanada rai ko ya mutu. Kasancewar sun kira sun sanar sai ogansu ya basu umarnin maza su ɗakkosa su dawo cikin kano asibiti. Bisa wannan umarnin ya sakasu ɗakkosa suka juyo a guje.

    Kai tsaye babban asibiti suka nufa, cikin amincin ALLAH kuma akai sa'a can aka kai Addah da su Umm suma. Su baba Malam na tsaka da tashin hankalin abinda ya faru sabon labari akan haɗarin Abban Abdallah yazo musu. A take na gida dana asibitin suka sake harmutsewa. 

     A yanda Yoohan yaga al'amarin ya kasance sai da yaji nadamar shigewa gaba wajen wannan bankaɗe-bankaɗe. Sai gashi da idanunsa ya ga baba malam na rusar kuka. Nu'aymah kam ai sai allurar barci ya danna mata saboda yanda ta birkice kamar dai ƙwaƙwalwar ta bata gama dawowa dai-dai ba.

      Lallai wannan ranace da waɗaɗan nan ahali bazasu taɓa mantawa da itaba a jerin tarihinsu. Sauƙinsu ma har yanzu ainahin labarin bai fita kunnuwan jama'ar gariba. Sai dai kawai ana maganar Sheikh Rudwan Hashim jibiya yayi Accident a hanyarsa ta zuwa Ktn yanzu babu jimawa. A take mutane suka shiga jera masa addu'ar ALLAH ya tashi kafaɗa, musamman ma mabiyansa.

      Zan iya ce muku yanda wannan ahali sukaga yinin wannan rana haka sukaga dare. Duk da kuwa Alhmdllh zuwa dare an tabbatar da Abban Abdallah bai rasuba. Ya dai samu karaya a kafaɗunsa duka biyu da kafafu. Sai manyan raunika da sukai masa kaca-kaca da jiki. Itako Addah barci suka sakata yi. Umm ma Alhmdllh ta farfaɗo ita da malam ƙarami. Hakama Nu'aymah ta farka.

         Sai kusan tara na dare suka bar asibitin, ba kuma a barsu sunga Abban Abdallah ba dai. Yoohan da kansa ya fiddo Nu'aymah da ga ɗakin office ɗinsa daya sakata barci. Ananah ta taimaka mata suka ƙarasa shiga mota. Baba malam yaso su Yoohan su bisu can gidan su kwana amma suka bashi haƙuri akan zasu zauna anan asibitin ne. Badan yaso ba ya barsu.


       Yoohan na ganin motocinsu sun gama wucewa ya sauke ajiyar zuciya mai kauri, A ɗaya daga kujerun dake a waje ya zauna hannayensa duka dafe da kansa. Sai yanzu komai ke dawo masa a ƙwaƙwalwa tamkar almara. Dan ɗazun su Addah na bayani ne little na fassara musu shi da Umar, duk da shi yana ɗan jin hausarma kaɗan-kaɗan yanzun. 

      Kusa da shi Umar yazo ya zauna shima yana sauke nasa ajiyar zuciyar. Yoohan bai motsaba balle ya kallesa. Shima sai bai damuba ya fara magana a hankali. “Haka mafi yawancin mutanen da suka samu ɗaukaka suke. Sai kaga na nesa da su na matuƙar sonsu da begen kasancewa da su. Amma waɗanda ke tare da su mafi yawancinsu ba son gaskiya suke musu ba. Ƙaso ɗaya bisa uku a ciki zaka samu suna musu ƙauna ta tsakani da ALLAH. Kaso biyun kuwa sai kaga suna raɓe da sune bisa wannan ɗaukakar da ALLAH yay musu. A zahiri kuwa su zugasu da nunama duniya babu kamarsu, a baɗini sune masu musu SARAN ƁOYE. lallai waɗanan mutanen masu zagon ƙasa suna ɗaya daga cikin jarabawar masu mafi yawan ɗaukaka”.

      Ajiyar zuciya Yoohan ya sake saukewa. Ya ɗago ya dubi Umar a karon farko, idanunsa sunyi jajur. Ga barci ga yunwa ga gajiya. Shi kansa Umar ɗin a galabaice ya ke. “Zancenka haka yake Umar, bazan ɓoye makaba al'amarin mutanen nan ya sake saka tsoro a zuciyata gaba ɗaya, nasake jin tsoron halin mutum da ayyukansa. Wannan wane irin bushewar zuciya ne haka? Su da ya kamata su zauna suyita godema ALLAH bisa ni'imar da yay musu ta rayuwa, su dinga ibada sai suka zama masu butulcewa ta hanyar cutar da wanda shi ya kusan ƙare tasa rayuwarne a ƙyautata tasu da ta ƴaƴansu. Umar wai miyasa ɗan adam keda manta alkairi da yawan butulci ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda da biyayya wa huɗubar shaiɗan akan dokar ALLAH ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda ya zama mai samu bamai sadaukarwa ba?  Miyasa mafi yawan mutane sunfi sha'awar cutar da wanda suka ƙyautata musu amma sunajin tsoron mai munanasu?. Ko addu'a mutum zaiyi, sai kaji yace ALLAH ka tsareni daga sharrin masu sharri. To miyasa bama addu'ar ALLAH ya karemu da aikata sharri ga masu ƙyautata mana ne?”.

       “Wannan shine halin ɗan adam ɗin da ake faɗa Dude, munada son kanmu, duk kuma mutum mai son kasa zakaga shine kullum a cikin wahalar nema da faɗuwa. Dan bazai taɓa doguwar nasara ba. Daya samu take kufece masa. Amma saboda bushewar zuciya gobe ma sai ya koma sake neman sa'a. Kowane addini akwai na banza akwai na gari. Irin waɗan nan mutanen suke ja ana zagin addinin islama bayan shi kuma addinine mai koyar da ƙyawawan ɗabi'u. Ko shekara banyi da shiga musilinci ba, amma wlhy Yoohan na fahimci babu wani addini dake gogayya da shi akan koyar da ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Komai musilinci ya haɗa. Amma ka duba su da keda ilimin sani a tsahon shekaru sunfi zaɓar su saɓama ALLAH bisa son zukatansu”.

     Sosai zukatansu Yoohan suka ƙara rauni da wannan al'amari. Imani da tsoron ALLAH ya sake shigarsu a zuciya da ɓargo. Suma kansu dai a wannan dare sunyi barci ne kawai badan jin daɗi ba.


*_WASHE GARI_*


        Washe gari aka bama su baba malam damar shiga su duba Abban Abdallah. A lallai duniya abin tsoro. Bawa daina cikama rayuwa baki kai ba komai bane. Duk damar da kaga ka samu a rayuwa da ga rahamar ALLAH ne. Amma wlhy idan yaso ko ƙyaftawar ido baka isa gittawa ba. A jiya iyanzu shine zaune tare da ƴan uwa da iyalansa. Amma yau gashi babu ko ƙyan gani a fuska saboda tsabar jigata da rayuwarsa tayi. Ita kanta Addah jikin nata babu daɗi.

    Duk wanda ya shiga duba Abban Abdallah sai kaga ya fito da kuka. Hakan yasa dama Yoohan bai bar Nu'aymah a wajenba. Suna zuwa ma ya jata wai tazo suje wajen awo. Bata fahimci wayo yake mataba ta bishi. Sai ya kaita office yasa aka kawo mata abinci. Duk da tace masa ta ƙoshi, dan basu fitoba sai da Umm ta bata abinci ya dage sai taci. Dole taci kaɗan dan ya barta. Sauran kuma ta bashi dan ta fahimci shima yana buƙatar a tsaresa yaci abincin.

         

     Zuwa ranar dai dukan ahalin gidan sunsan halin da ake ciki, ƴaƴan Addah dake aure da ƙannen Abdallah ma duk sunzo. Ansha sabon kuka dai kam yau ma. Daga ƙarshe baba malam dake ta ƙoƙarin danne tasa damuwar yay musu nasiha da nuna musu muhimmancin ƙaddara. Ya tabbatar musu da cewar hakan jarabawane. Dan bazai yuwu dama a rayuwa a rayuwa babu jarabawa ba. Ya hana kowa kakkausan lafazi akan su Addah, dan kuwa shi a take ranar ya tabbatarma da kowa cewar ya yafe musu. Sai su cigaba da musu addu'ar ALLAH ya basu lafiya kawai.

     Baba malam ya ƙara kima a idanun iyalan Addah da Abban Abdallah. Musamman ma Abdallah da har ran yakejin tsanar mahaifinsa da Addah. Sunso su gurɓata masa tunani ALLAH ya hana hakan. Dan bayan Addah ta ɓale a cikinsu Abbansa sake zaunar da shi yay ya ɗora masa sabon karatu akan maido da Nu'aymah rayuwarsa koda ta ƙarfin tuwo ne. Wannan shine dalilin da yasa dinga bibiyar rayuwarta. Ko a randa ya bisu shopping mail ɗin nan da nufin kidnapping Nu'aymah ya je. Sai akai rashin sa'a Yoohan ya gansa tun lokacin da suke faɗansu da Aymah harta faɗa a jikinsa. Dai-dai lokacin da yake cemata ta tara musu mutane idonsa ya sauka akan Abdallah ɗin. Har suka shiga mail ɗin kuma yana sane da shi. Sannan yana akan sani yabar Aymah a wajen ita kaɗai dan yaga mi Abdallah zaiyi?.

     Lokacin da Nu'aymah taji ƙamshinsa da gittawar mutum Abdallah ne, yana gab da isa gareta Yoohan ya jasa baya da ƙarfi ya toshe masa baki suka koma ta bayansu. Cikin fushi Abdallah ya hakaɗe Yoohan ɗin yana faɗin. “Kai shasha minene haka?”.

     Murmushi Yoohan yayi sannan ya haɗe fuska. Cikin ƙanƙance ido ya nuna Abdallah da faɗin, “Idan ka bari gangancinka ya ɗora zuciyarka bisa dokin shiga gona ta. Na rantse da ALLAH Abdallah sai na dawwamar da rayuwarka a dana sani. Na fika hatsabibanci fiye da yanda kake tsammani. Dan haka ka kama kanka kafin na ajiye mutuncin ahalinka da nake gani gefe na ɓata rayuwarka. Karka zata bansan wanene kai ba da ubanka. Ka kiyayeni kona fallasaku duniya ta sanku da aiyyukanku akan ahalinku”.

     Yana gama faɗa yabar wajen, shine yaje yaja Aymah suka wuce wajan biyan kuɗi.

      Tabbas kalaman Yoohan sun girgiza Abdallah. Hakan yasa ya janye daga bibiyar Nu'aymah. Dan dama can shi mutum ne da a rayuwa bai son yawan matsawa kansa, sannan baison fitina sam. Wannan halayyar tasa tasa lokacin yana yaro ake ganinsa matsoraci a cikin yara ƴan uwansa. Dan da gaske tabbas yanada tsoron faɗa a rayuwarsa. Dai-dai da film ɗin faɗa Abdallah baya zaman kallonsa sam saboda baya ra'ayin fitina, daya zama saurayune ma dai ya fara canjawa. har zuciyar tasa tai tauri saboda zuciyar gidansu ta gado.

      Ƙin faɗama Abbansa zancen yayi. Amma yayi ƙudirin janye jikinsa daga bibiyar Nu'aymah. Daga bakin Abbansa yaji samuwar Uwaliya, dan a randa aka kawota a ranar Abbansa ya tattauna da ita tun a office kafinma a kaita gidansa. Uwaliya akwai son kuɗi. jin maƙudan ƙuɗin da Abban Abdallah ya tabbatar mata zata samu akan kaso masa auren Nu'aymah da kawo musu dukkan bayanai a kanta yasa ta amince zatayi. A ranar ya bata rabin kuɗin, sauran kuwa sai aiki ya kammala.

      Tasha murna a ranar, ta kuma tabbatar da lallai ta shigo Abuja da ƙafar dama. Yo ko Yoohan ɗin sukace ta bibiya akan waɗanan kudin ai ta halakashi kuwa.

       Wannan shine dalilin da yasa ta fara musu aiki. Sai dai abinda bata saniba suna amfani da wayar Rabi da muryartane idan suka kirata.

     Lokacin da aka wuce da Nu'aymah Austria da gaske Abdallah yaje dubatane saboda son da yake mata. Sai dai baiso Yoohan da su baba malam su gansa. Shine yaso su fara haɗuwa da Abbansa. koda suka haɗun Abban ya dinga masa faɗan da har zancen Nu'aymah ya shigo ciki saboda Addah da tazo taga Abdallah ta zata cutar da Aymah zasuyi. Anna ne Yoohan yaji da Hajjo sukaji, abinda kuma basu saniba shine baba malam ma ya gansu, ya kuma jisu. amma sai bai taɓa nunawa ko da Umm ba balle su..........✍  


No comments

Powered by Blogger.