Saran Boye 71


 No. 71


..............Saurin zaro ido waje Rabi tayi tana mai girgiza kanta. “Wlhy ba haka bane ranki ya daɗe. Mizaisa na aikata hakan ga Nu'Aymah. Bayan sikari da Lipton sai ruwan dana dafashi da shi ne kawai a ciki”.

       Wani irin tafasa zuciyar Yoohan takeyi daga can, ji yake kamar ya ziro hannu ya shaƙo wuyan Rabi ta cikin system ɗin, sai dai babu dama.

        

     Little bee zatai magana Bily ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Inaga ku maidata inda aka ɗakkota tukkunna”.

       Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu. Sai tasa ƙeyar Rabi da aka saka wani jami'i yay tana kuka aka maidata inda aka ɗakkota.

      Bayan fitarsu ajiyar zuciya bily ta sauke tana rubuce-rubuce. Kusan mintuna biyu kafin ta ɗago ta kalli Yoohan da zuciya ta kume daga can.  “I'm sorry Dear wannan case ɗin duk yanda kuke tunaninsa ya wuce haka. Akwai wani abu dana fahimta dangane da wnanan matar wanda sam na kula ku duk baku gansaba. Kodai ya kasance amfani akeyi da ita a gidan batare da ita kanta ta sani ba. Kokuma tana kan sani ta fi yarda ta shanye duk wata azabar data fuskanta anan danta rufama wancan asiri. Kokuma an mata gargaɗi mai girma da tsoratarwa akan sanarwa tun ba yanzuba.

         Dole wannan wayar tata na buƙatar sabon bincike. Sannan waɗannan voice recording ɗin suma zamu sake bincike sosai a kansu, idanma har ba'ita ɗin bace zamu gano ainahin mai muryar insha ALLAHU”.

     Dukansu sun fahimceta. Hakan yasa Yoohan tabbatar musu da shima zai shigo Nigeria zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma harda Nu'aymah. Dan ya fahimci lallai wasan na gaske ne.


_____________★★


           Tunda ya shigo gidan yau taketa faman binsa da kallon mamaki. Dan tun randa ya dawo daga 9ja ta kasa gane kansa gaba ɗaya. Kullum yana cikin ƙunci da tunani, baya son yawan magana, sai su yini su tashi har dare magana sau biyar bata shiga tsakaninsa da shi ba. Tayi tambayar harta gaji tayi fushi ta ƙyalesa. Daga ƙarshe ma sai ya koma fita asibiti. Idan ya tafi tunda safe sai tayi barci zai dawo. Ta fahimci yana hakane duk dan karta cigaba da masa tambaya akan abinda ke damunsa. Dan idan ya fita yata yawan kiranta kenan wai yaji yaya take ita da Unborn ɗinsa.

     Hakan data ƙara fahimtane ya sata sake tattare maganar damuwar tasa ta watsar gefe. to shinefa aɗan kwanaki ukun nan ya fara sakin jikinsa yana kuma dawowa gidan kafin tayi barci. Yau kuma abin mamaki sai gashi kusan ƙarfe uku ya shigo mata.

       Yanda batai maganaba shima baiyiba. Sai dai kallonta yake cike da tausayawa a gareta. Tana zaune ne a kujera ta miƙe ƙafafunta bisa centre table ɗin falon. Sai filo ƙarami a cinyarta ta ɗora lap-top a kai tana sauraren lecture da akeyi daga can school ɗinsu.

    A ɗan kwanki goma sha huɗu ɗin nan duk ta rame saboda damuwarsa da itama ke damunta. Hakan yasa cikin nata ɗan watanni bakwai sake fitowa sosai gamai kallo. Musamman yanzuma da take sanye da skirt na atanfa da t-shirt mai ƙarancin girma. Sai dai ta ɗara waɗanda take sawa a da kafin samuwar cikin da girmansa. plate ne a cinyar tata shima gab da cikinta ɗauke da green apples a kai, sai ɗaya dake a hannunta da ƙaramar wuƙa tana yanka tana ci a hankali.

     Sassanyan numfashi ya sauke da lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta. sai kuma ya shiga takowa har inda take dan ganin taƙi daina kallonsa. Gefenta ya zauna daf da ɗora hannunsa akan fuskarta ya juyar mata da kanta ta koma kallon lap-top ɗin.

         Cike da sanyin murya yace, “K da kike ɗaukar Lecture miye na zubamin ido kuma?”.

       Uffan batace masa ba, sai iska data furzar daga bakinta. Itama da sanyin muryar tace, “Lafiya naga ka dawo da wuri haka?”.

      Ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu, ya dora kansa a kafaɗarta tare da kamo hannunta dake riƙe da yankan apple ɗin ya kai bakinsa. Bata musaba ta saka masa itama. Sai da ya tauna ya haɗiye yana kallon lecturer ɗin shima sannan yace, “thanks you Sweet girl” ya ƙare maganar da kaima kuncinta sumbata, ya kuma tura hannunsa a rigarta yana shafa cikinta cike da ƙwarewar likitanci.

       Kamar koda yaushe kuwa sai ga cikin na motsi. Dan duk sanda zai masa irin wannan shafar sai kaji ya motsa. Har mita Aymah ke masa akan ita miyasa cikin baya mata haka sai idan yaso motsinsa da kansa yakeyi. Kokuma idan tanajin matsanancin yunwa nanma yana motsawa.

       A hankali yace, “Sheikh ɗin Daddy ga daddy ya dawo gida. Ina fatan bakai fushi da canjawarsa ba?. kana kuma cikin ƙoshin lafiya zinarin zuciyata”.

     Fuska Aymah taɗan taɓe tana ɗauke kanta ta maida ga lecture ɗin da sam yanzu ma ba fahinta takeba ita. 

     “Jealous ɗin ya motsane madam?”. Yoohan ya faɗa a cikin kunnenta cike da neman tsokana.

          Hannu tasa ta ture nasa da zuba masa harara. “Tunda Jealous ɗin nakeyi mizai hana a ciremin na huta”. Gimtse murmushin dake neman kufce masa yayi yana taɓe baki da ɗage gira ɗaya sama. “Silly girl, ai idan kinga mun barki sai mun cika watanni tara da kwanaki tara ciff insha ALLAH. magajin Uncle na zuwa kuma wata ƙwallon zata kuma faɗawa rag.....”

     Lap-top ɗin da take shirin saukewa a jikinta yay azamar riƙewa dan yasan sotake ta gudu. “Oh am sorry sweetheart wasa nake fa ni. Mu mun isa miki gadara bayan yanzu kece boss ɗin gidanma, kammu bisa wuya Mie-mie. Nifa namazo miki da wani albishirne mai daɗi”.

      Batare data tanka masa ba ta sake yunƙurawa zata tashi. “ALLAH seriously Sweet girl”.

      Ajiyar zuciya taɗan sauke kaɗan. Sai kuma ta kallesa, “To ka bari naje na kawo maka ruwa”.

      “Okay harda abinci. dan yunwa nakeji”.

    “Ai baka da kaso anan gidan malam”.

  Tai maganar tana shigewa kitchen. Murmushi yayi mai faɗi daya jima ba'a gani a fuskarsaba. Ya jingina da kujera yana furzar da zazzfar iska. Shi kaɗai yasan mi yakeji a ransa. Yana daurewa ne kawai saboda fahimtar halin da yake ciki na ƙuntata ta itama. Shikuma bayason haka kodan yanayin da take ciki........

      “Uhyimmm! An tafi tunanin ko?”.

Saurin dubanta yayi yana ƙoƙarin canja yanayin fuskarsa, Aymah da idanunta suka cika da ƙwalla ta ajiye tiren data ɗoro masa plate ɗin abinci  da ruwa sai kofin lemo ɗaya. Saurin riƙota yayi ganin zata gudu. Ya ɗorata a cinyarsa duk da tanata ƙoƙarin ƙwace kanta ga hawayen sun fara sauka a kumatu da gudu. Matseta yay da ƙyau ya lumshe idanunsa, tun tanason ƙwatar jikinta harta haƙura tayi luf a jikinsa tana shashshekar kuka da sauke ajiyar zuciya.

      “Am sorry Zeeynab. I'm very sorry. Nasan tabbas ina ƙuntata rayuwarki da laifin da banakiba. Nima bada son raina bane, ina cikin tashin hankaline mai tsananin ruɗani Nu'aymah.......”

     “Shine ka zaɓi ka ɓoye min saboda ni banda matsayin sanin sirrinka? Amma ni har sirrin daya kasance na family ɗina mun baka dama ka shiga tsundum saboda baka darajarka, sai ni da.......”

       “Shiii!!!. Wlhy bani da wani sirri a duniyar nan sai ke Nu'aymah. Da ana buɗe zuciya ma'abocin kallo yaga sirrin dake cikinta dana buɗe miki tawa kin gani Zeeynab. Da kinsan wacece ke a gareni da dukkanin tasirin da kikayi a rayuwata da bazaki taɓa yin tunani irin wannan ba. Amma kiyi haƙuri nasan da laifina. Laifina shine ɓoye miki damuwata. Bana ɓoye miki dan baki isa bane, na ɓoye miki ne saboda al'amarine mai girma a gareni. Ki tayani da addu'a ke dai kinji. Ki kuma cire komai a ranki, ki yarda ke ta dabbance ga mijinki. Bakiga duk yanda kika rameba, hakan na tayarmin da hankali.....”

      “Yah Yoohan amma ai......”

“Oh my Cutie karkice komai Please. Yanzu dai mu ajiye wancan batun bashi da wani muhimmancin cigaba da hargitsa mana rayuwa da tunani ok?. Ina miki albishirin zuwa Nigeria gobe insha ALLAHU ”.

       Duk da kewar ahalinta da ɗokin son zuwa garesu da takeyi sai taji kamar tafiyar bata lafiya bace, musamman da tasan yace itada 9ja ɗin sai ta shiga watan haihuwa lokacin sun sami hutun ƙarshen shekara da Christmas.......

     “Tunani again baby?”.

Numfashi ta kawo tana kallonsa. Kallo irin na tambayoyin da baki ya gaza furtawa.

      “To ko a fasa nayi tafiyata kawai ni kaɗai”.

      Da sauri ta girgiza masa kanta alamar a'a. Ya ɗan murmusa da sumbatar laɓɓanta. “Karfa kisa komai a ranki surprise ne kawai”.

       Duk da bata yarda da shiba haka ta shanye abinta a rai. Sai dai ta masa maganar karatunta yace babu damuwa ko suna a can zata cigaba da ɗaukar lectures ta online ɗin. Daga haka suka fara shiri a ranar, duk da daima bawani sun haɗa kaya bane dan bama zasu tafi da kayanba tunda akwaisu acan babu buƙatar hakan.

     A dai ranar duk wani abu da zai iya lalacewa sun fitar da shi. Suka ɗan fita shopping na abinda zata iya buƙata saboda lalurarta. Ranta cike yake da ɗokin Isa ga ahalinta bayan rabuwa da su tsawon watanni tara. A gefe kuma cike take da fargabar sakamakon abinda zataje ta tarar.


*_WASHE GARI_*


        Washe gari safiyar juma'a jirgin su Nu'aymah ya sauka a ƙasar haihuwarsu batare da kowa yasan da zuwan nasuba. Sai da taimakon Yoohan ta sakko a jirgin saboda ƙafafunta da sukai mata tsami da kumburi. Sai faman taɓe fuska take kamar zatai kuka. Shi kam dai ga tausayinta ga dariya na cinsa a rai. a zuciya ya ayyana, ‘Abufa yazo ga ma'iya’.

        Bayan shigarsu texi taji yace a kaisu hotel. Ai babu shiri ta kallesa, “Hotel kuma Yah Yoohan? Gidan papa ɗin fa?”.

      Cikin jin zafin dake taso masa a rai ya girgiza mata kansa. “Zamuje, amma yanzu muje ki huta ko?”.

       Hankalinta tashe akan tunawa da hoton nan da sauri tace, “A'a ni dai gaskiya inba gidan papa ba sai dai ka sani a motar kano na wuce. Yaya gamu da gidan iyaye mu kama raɓe-raɓen hotel kamar wasu marasa galihu. Kayi haƙuri gaskiya ni dai bazanje hotel ba”.

      Duk yanda yaso lallashinta akan suje hotel ɗin dan shi bayason zuwa gidansu. Ko sha'awar kallon fuskar Momy bayayi sam. Amma Nu'aymah ta tubure duk da bawai dan tanason zama gidan bane itama. Tana son sujene saboda hoton nan. Gara suje tun a yau ta ɗauka kafin papa ya farga suna ƙasar tunda ya bada kwangilar kasheta. Daga lokacin da matsaloli suka fara kuma ai maganar hoto sai tasha ruwa.

     Badan Yoohan yaso ba dole yasa mai taxi ɗaukar hanyar anguwarsu dan kuka Aymah ta sanya masa rirus babuko kunya. Sam baya buƙatar damuwarta a irin wannan lokacin. Dan yama fahimci jininta yayi sama saboda wannan tafiyar mai nisa da sukayo. Daga haka kuwa bai ƙara maganaba, sai dai ya sakata a jikinsa kawai yana shafa bayanta alamar lallashi. Saiko faman cijar lip ɗinsa na ƙasa yake da ƙoƙarin danne abinda ke taso masa a rai.

         Har ciki mai taxi ɗin ya shiga dasu, koda maigadi ya leƙi yaga Yoohan sai ya koma da sauri ya buɗe gate ɗin ransa fal murnar ganinsu. Da taimakonsa Aymah ta fito yanzunma. yayinda gaba ɗaya Guards ɗin gidan suka rufu musu a ka suna kwasar gaisuwa bakin kowa a washe na murnar ganinsu. Zuciya kam fal gulma ganin Nu'aymah da ciki. Musamman ma Solomon daketa faman zare ido.

      Solomon ɗinne ya amshi ƴan kayansu dake a trolly ɗaya sai lap-top bag ɗin Yoohan. handbag ɗin Aymah kuwa tana a hannun Yoohan ɗin ɗayan hannunsa kuma riƙe da nata.

      Da Gebrail suka fara cin karo zaune a dining yana lunch ɗin daya makara baiyiba. Idonsa na sauka a kansu kuwa ya sarƙe da abinci har sai da Blessing ta fito daga kitchen a guje dan jin mahaukacin tarin da yakeyi. Ko kallon inda yake kuwa Yoohan da Aymah basuyiba.

     Wani bala'in waro idanu Blessing tayi tare da daka tsalle gefe hannayenta duka a saman kai tace, “Heeyyy!!! Ahhhhhh!! Emiiii!!!”.

     Dariya ta bama Aymah sosai. Hakan ya sakata darawar kuwa. Yoohan kuwa daya zaunar da ita a kujera ko kallon Blessing ɗin baiyiba. Sai durƙusawa yay a gabanta ya kama ƙafafunta ya zare takalman da take sanye da su masu taushi, amma saboda tsabar hawa da ƙafar tayi sun manne mata har sunyi mata sayi. Matsa mata ƙafar ya farayi a sannu-sannu ransa fal tausayinta duk da yasan bawai wata matsala bane. Yanayine kawai da wasu masu cikin kan shiga.

       Ihun Blessing ne ya fito da Joy da Miracle daga ɗaki suma a guje. Sai ga Victoria dasu Favour da har yanzu su suna abuja basu koma ƙauye ba. Makaranta ma Yoohan yace zai duba musu anan, sai kuma aka samu akasi wancan matsalar ta faru Yoohan yabar ƙasar babu shiri.

         Da gudun bala'i su Destiny sukayo kan Nu'aymah da itama take kallonsu fuskanta washe da dariyar Blessing data gama kwasa... 

     A wani zabure Yoohan ya miƙe yana dakatar dasu, amma ina sukam idonsu ya rufe yau saboda farin cikin ganin auntynsu da kullum suke nacin son dawowarta. Gata kuma da ciki zata haifa musu baby a gida.

      Goshi kawai Yoohan ya dafe yana faɗin, “Oh GOD!”.

          Itako Aymah da dama ba hankalinne ya gama isartaba oho. Tuni ta tarbi ƴan yaranta da suka nuna mata ƙauna zalla a gidan babu algus. Sai da Yoohan yaga lamarin nasu bana ƙare bane yasa hannu ya fara ɗagasu ɗai-ɗai daga kan Nu'aymahr. 


       Ihun su Destiny ne ya farkar da mama debora a barcin da takeyi. Ta fito jikinta na rawa dan ta ɗauka wani abunne ya faru da yaran. Kaɗan ya rage bata bangaje su Joy da Miracle tai suman gigitaba ta tarota. Kota kansu batabiba ta fara sauka a benen da gudu zane a hannu.

     Wani bala'in waro ido tayi akan Nu'aymah tana faɗin, “Jesus John matarka ne da ciki? Cikin jikana ɗanka. Kaima zaka haifi yaronka John ?”. Sai kuma ta nufeta cike da Sassarfa. A take annurin fuskar Aymah ya ɓace ɓat, hakama Yoohan kallon kakar tasa yake yaga mizatayi. A mamakin kowa sai mama debora ta fashe da kuka tana rungume Nu'aymah. Sai kuma ta durƙusa ƙasa ta ɗaura hannunta akan cikin Aymah tana sambatun zance da yare wanda sam Aymah ba ji takeba. Sai dai yanda taga Yoohan ya langaɓe kai yana kallon kakar tasu fuskarsa da murmushi ya sata fahimtar ba mummunan abu mama debora ke faɗi akan gudan jinin nasu ba. Tabbas duk wanda ya kalli mama debora a wannan lokacin yasan farin cikine na gaske tattare da ita. Ba komai yay silarsaba kuma sai cikin jikin Nu'aymah ɗin. Dan kanta batasan yaya akai ƙaunar cikin ta saukar mata ba lokaci ɗaya tare da Nu'aymahn kanta. (Nace Ƙarfin addu'a ce mama debora). 

     Tana faman sharar ƙwalla ta kamo hannun Yoohan ta zaunar a kusa da Nu'aymah. Ta haɗa hannayensu cikin na juna sannan tai Kneeling a gabansu tare da rufe idanunta duka ta ɗaga hannaye sama ta fara raira waƙar addu'a da yare tana hawaye, ganin hakan yasa su Victoria ma durƙusawa tare da Blessing suka fara tayata suma duk idanu a rufe.

      Cike da zaro idanu Nu'aymah ta kalli Yoohan kamar zatai kuka. Dariya taso kufce masa. Amma sai ya gimtse yay murmushi kawai. A cikin kunnenta yace, “Karki damu addu'ar kariya sukema baby dakema ALLAH ya saukeki lafiya cikin ƙoshin lafiya”.

     Duk da tasan su ba musulmai bane ta ɗanji sanyi a ranta tunda ba wani tsafi baneba dai. sai kawai ta ɗora kanta a gefen hannunsa tana mai addu'a a ranta itama ALLAH yasa sunada rabon musulinci. Dan tabbas yau taji gaba ɗaya haushin mama debora da takeji ya kwaranye. Dama ance mai ɗa wawa.

     Bayan sun gama addu'arsu sun zauna, mama debora nata wani ji da Nu'aymah. Ita dai abin har dariya yake bata. Hakam Yoohan dariya kakar tasa ke basa da gaske. Ta dungure masa kai tana faɗin, “Mara mutunci. kasan matarka nada ciki baka taɓa faɗama kowaba. Yarinyata watansa nawa?”. Ta maida maganar kan Nu'aymah bayan ta zubama Yoohan dake kumbura mata fuska saboda mangarar masa ƙeya da tayi harara.

      Haka kawai sai Aymah taji nauyin faɗa. Sai Yoohan ɗinne ya bata amsa. Sai kawai ta tashi ta kama rawa tana waƙar yarensu irinta tsoffi.

      A wannan yanayin papa da Madam Chioma da basa gidan suka shigo suka samesu. Gaban Nu'aymah yay mummunan faɗuwa. Da sauri ta shiga karanto addu'a a cikin ranta. Sannan ta yunƙura ta miƙe kamar yanda taga Yoohan ya miƙe fuskarsa a tsuke saboda ganin Momy.

      Da wani irin kallo papa kebin Nu'aymah da cikinta. madam Chioma kam Yoohan take kallo kamar wata tsohuwar mayya. Dan sam hankalinta bai kai kan Aymah ba tukkunna.

    Cike da farin ciki Mama debora ta nufi papa tana rera waƙarta da ke nuna tana a tsantsar farin ciki na haƙiƙa, hannunsa ta kamo ta nufi inda Nu'aymah take. Da sauri Madam Chioma takai dubanta inda mama debora ta nufa da Papa. Aiki idanunta sukai mata mummunan gani. Da tsanin gigita ta furta, “What??! Impossible!. Na rantse da ALLAH impossible!!!”. 

      A kusan tare kowa dake a falon ya kalleta, sai kawai ganinta sukai a ƙasa ta sulale sumammiya.

      A guje su Destiny sukayi kanta da papa. Yoohan kam fuska ya kauda gefe cike da ƙunar zuciya. Nu'aymah da tasan ba sonta madam Chioma keyiba dama can sai bata ɗauki hakan komaiba face ƙiyayyar da take nuna mata dama can.

     Mama debora kam wani irin taɓe baki tayi da faɗin, “Aiko Chioma zaki mutune a haifamin jikana duniya. Kujimin yarinya da baƙin halin baƙin ciki. Ke sanda kika haifi John nayi miki hassada ne? Bandama inada zuciya me ƙyau ai saina saka ayar tambaya a kanki dan Yoohana baya kama dake, nayi shirune kawai dan yana kama da yarona, amma kekam ai kamarma ba ɗanki ba. Sai shi yanzu zaki baƙin ciki matarsa zata haifa masa ɗa. Kema sai kinji abinda naji na rabani da ɗana da kikayi......”

      A guje Blessing ta kawo ruwa aka yayyafama Madam Chioma. Tako fasa wata razananniyar ƙara da miƙewa zaune tana nuna Nu'aymah. “Wannan ba cikin yarona bane, kufitarmin da ashawo ɗinnan a gida, na rantse da ALLAH john wannan ba cikinka baneba. Dan hakan bazata taɓa kaswncewaba. Idan baku fitarmin da ita a gidaba zan kasheta. Ku kaita can ta nemo uban cikinta dan bana John bane. Darling narsantse damfararmu yarinyar nan zatayi cikin nan bana John bane. Sun tsafemin yaro sun rabani da shi. Yanzu zasu manna masa cikin kuma da ba nasab.......”

        Yanda take surutan zaka ɗauka bata da hankalima sam. Yoohan da takaici ya kume yaja hannun Nu'aymah suka haye sama abinsu batare da yayi ko tariba. Mama debora ma wani dariya da ihu ta sanya tana tafa hannaye. “Chioma kishi da matar ɗanki yasa kin haukace gaskiya. Tunda ni kakar John na yarda cikinsa ne koke da goshpower kukaƙi yarda nasan kishi ne. Yanda nasha baƙin cikin rabani da ɗana da kikayi kema sai kinsha fiye da wannan baƙin cikin na rabuwa da John. Wuuuuuuu!!! She she Shem!!! Wuuuuuu!!!! Hhhhhhhh!!!! Anji kunya uwa mai kishi da matar yaronta!!!!”.


        Hankalin papa ya sake tashi da abinda mahaifiyarsa keyi. Dan har cikin zuciya shima a kiɗimen yake game dayin tozali da wannan cikin da ko a labari bai taɓa sanin akwaishi ba.  Lallai wannan shine lokacin daya kamata a fara yaƙin na gaske. Dan tura takai bango anzo dai-dai wajen.

     Madam Chioma kam ihu takeyi da kururuwa har su Yoohan dake sama na jiyota.

       Idanun Aymah da a yanzu sam batason yawan hayaniya cike da ƙwalla ta kalli Yoohan daketa kai da kawowa a cikin falon. “Yah Yoohan Please ka barni na wuce kano kawai zaifi. Wannan wane irin tashin hankaline? Maimakon ciki ya zama abin farin ciki sai kuma a maidashi tashin hankali? Kayi haƙuri mahaifiyarka ce, amma ina tsoron ta cutar dani nikam gaskiyar magana”.

        Kallonta kawai Yoohan yake ransa na ƙara zafafa. Sai dai sam baiji zafin kalamanta ba, dan yasan gaskiyarta take faɗa. Shi kansa a yau ɗin nan ya sake shiga ruɗani dangane da halin mahaifiyar tasa. Wace irin uwace ita? Miyasa halayenta suka banbanta dana sauran iyaye? Tunba yanzuba wasu abubuwan nata suke dama masa lissafinsa da zurmasa a yawan tunani. Sai dai bai taɓa zaman musu fashin baƙiba saboda karta munana a cikin idanunsa. A wannan karon kam yaji bazai iyaba, dolene ko yanaso ko bayaso yasan dilin da yasa mahaifiyar tasa zafafa abubuwa akansa bayan kuma bashi kaɗai bane gudan jininta........

       “Yah Yoohan maganafa nake”.

Nu'aymah ta dawo dashi hankalinsa saboda riƙe masa hannu da tayi. Nannauyan numfashi ya sauke tare da rungumota jikinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Sunkai tsahon mintuna uku a haka sannan ya ɗagota, fuskarta cikin tafin hannayensa yana mai kallon ƙwayar idanunta data cika da hawaye. “Nima nafi aminta da tafiyarki Kano baby love, amma ina roƙonki kiyi haƙuri da safe idan ALLAH ya kaimu sai mu wuce kinji. Karkuma ki damu da zantukan Momy babu abinda zatai miki ɓacin rai ne kawai yasata faɗinsu itama kinji Heartbeat ɗina”.

      Duk da bata gamsu baneba sai ta ɗaga masa kanta dan babu abinda take hange a cikin idanusa sai tsantsar tashin hankali da damuwa, itakuwa indai akan iyayensane bazata bari ya shiga tashin hankaliba insha ALLAH.

     Yaji daɗin yanda ta nuna ta amince. Dan haka ya zaunar da ita duk da akwai ƴar ƙura a falon. Fita yay da kansa. Bai iske Momy ba da papa a falon, da alama sun shige daga ciki. Sai mama debora dake waya tana masifa da alama da ɗaya a cikin su momy Destiny take wayar, dan tana faɗa mata abinda ya farune. 

      Baibi takantaba itama yay kiran Blessing dasu Destiny suzo su musu gyara. Tare ya koma dasu, ya zauna yana mammatsama Aymah ƙafa daya tarar tana matsawa, su kuma suka fara aikin gyaran.


        Koda suka kammala ɗakinsa ya janyeta sukai wanka a tare. Suna fitowa babu jimawa Blessing tai knocking. Jallabiya ya zura ya fita danya duba wanene?. Samunta yay tsaye da ƙaton tire ɗauke da abinci. Hanya ya bata ta shiga. Ta ajiye tiren a dining sannan ta fita kanta a ƙasa. Ƙofar ya maida ya rufe, yaje ya ɗauki tiren ya nufi ɗakinsa da shi. 

        Nu'aymah na kwance a gado ko towel ɗin jikinsa ta kasa cirewa saboda gajiya da barcin dake ci mata idanu. “Kefa yanzu kin zama raguwa Sweet girl. Tashi to ga abinci”.

      Tashi tai zaune fuskarta da murmushi itama. Tace, “Duk ba ɗanka bane ya maidani hakan? Nida naci burin duk randa nazo 9ja yawo sai inda ƙarfina ya ƙare. Amma gashi tun ba'aje ko inaba lalaci ya fara mamayeni”.

     Ƴar dariya yayi yana miƙa mata t-shirt ɗinsa mai girma sosai. Ta amsa ta saka sannan tazo inda yake zuba abincin. Tasan Blessing ce tai girkin shiyyasa zataci. Da taimakon Yoohan kuwa taci ta ƙoshi tai nak, shima ta bashi yaci sai dai kaɗan yaci dan sam zuciyarsa bata cikin jin daɗi. Yana dannewane kawai danya ƙarfafa Nu'aymah. 

     Suna gamawa gadonsa ta haye ta kwanta saboda uban barcin dake cimata idanu. Bai hanataba, saboda shima yafi buƙatar tayi barcin a yanzu. Babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay gaba da ita.


_________★


      Tunda Blessing mai kawoma Omar rahoton gidansu Yoohan ta kirashi ta sanar masa da abinda ya faru game da isowar su Yoohan ɗin hankalin Umar yay ƙololuwar tashi. dan shi kansa da yasan Yoohan gidansu zai wuce da Nu'aymah ba hotel ba ko kano da bazai bariba. Dolene shima yau ya kwana abuja kuwa dan harga ALLAH lamarin papan Yoohan yanzu tsoro yake bashi harma Momyn, bai ƙara tsinkewa da al'amarinsu ba sai akan abinda ya faru tsakanin Yoohan ɗin da Momy. duk da su hasashe sukeyi tunda su su Blessing bawai sunga komai baneba akan idonsu.

       A take ya bincika ko akwai jirgi mai tashi zuwa abuja. Yakoyi sa'ar samun mai tashi nanda sa'oi biyu, dama shekaran jiya ya baro Abujan ai. Bai kira Yoohan ba, dan yafi son ya gansa tsulum kawai a bazata.


___________★


        Shiko Yoohan yana samu Aymah tayi barci saiya fito zuwa sashen papa.  Zaune ya samesa a falo yana waya. Yana ganin sa kuma ya yanke wayar. Ko a jikin Yoohan, dan ba wannan ne ya kawosa ba.

     Zama yay a kujera, batare da ya dubesa ba yace, “Good afternoon”.

      Papa ya danne abinda ke a maƙoshinsa da ƙyar ya amsa masa. Ya ɗora da faɗin, “Saukar yaushe haka babu labari. Aini nazata yanzu ni narigada na haifama Sheikh Sooraj ne kai?”.

       Shiru Yoohan yayi baiyi magana ba. Hakan sai ya ƙara harzuƙa papa matuƙa. Cikin tsagwaron masifa yace, “Ina magana da kai kamin banza. Wato na fahimci dama nika maida ɗan iska game da cewar wani aiki kakeyi akansa. John dolene yau insan minene tsakaninka da Sooraj?”.

        A matuƙar ɓacin ran da Yoohan shima baisan dalilinsaba, cike da suɓutar baki yace, “Papa nima inason sanin shin da gaske Momy itace ta haifeni? Dan ban taɓa jin mai halin uwa irintaba. Inhar ka amsamin wannan tambayar ni kuma na maka alƙawarin sanar maka alaƙata da Uncle Soorajidden Hashim jibiya. Sannan kama matarka gargaɗi, wlhy inhar wani abu ya samu cikina ko matata a gidan nan komaima zan iya aikatawa..”

     Yana kaiwa nan ya miƙe fuuuu ya fito yana huci. Da sauri madam Chioma dake bakin ƙofar tsaye tai baya ta bashi hanya cikin matuƙar rawar jiki da tsagwaron tashin hankali. Dan taji komai daya gudana tsakanin papa da ɗan nata.

         

       Wani irin zufar tashin hankalice ta shiga karyoma papa. Jikinsa na rawa ya zamo ƙasa daɓas kan carpet ya zauna. Gaba ɗayama duniyar sai take juya masa. Yau John ɗinsane ke kallan cikin idanunsa yana faɗa masa magana irin haka babu kunya babu tsoro. To tayaya hakan ta faru? Minene kuskurensa? Karfa ace lokacin da yake jira domin nasara ne ke shirin masa juyen ruwan hadarin da ba'a tsammaci zuwansa ba. cikin rawar jiki ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa batare da ya kula da madam Chioma dake a tashin hankalinba itama. A gurguje yay shiri ya fito daga ɗakin. Idonsa a rufe ya sake bangaje madam Chioma ya wuce dan harga ALLAH bai gantaba yanzuma, idanunsa har wani yana-yana suke masa saboda jirkicewar ƙwaƙwalwa dana tunani...........✍

      

No comments

Powered by Blogger.