Saran Boye 65

 


No. 65


..............A hankali soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ta cigaba da shiga tsakanin ma'auratan masu banbancin yare da yanki cike da birgewa. Yayinda Aymah ke matsayin malama ga Yoohan a ɓangaren ilimin addini shima sai ya zame mata malami a ɓangaren sanin soyayya da rayuwa. Dan sosai yake yawo da ita a lungu da saƙo na ƙasar Austria har wasu jihohinma suna zuwa yawon buɗe ido.

      Tun tana tsoro da masa raki a shimfiɗa harta fara sakin jikinta da sabawa. Dan jarumin nata namijin gaskene babu wasa. Baya takura mata yanda zata wahala. ba kuma ya barinta ta shagala.

      Sai ga Nu'aymah tai wani irin murjewa da ƙibarta na dawowa, (kunsanfa wannan harkar na gyara wasu matan harma da mazan🙈, shiyyasa da yawa amare farkon aurensu zakaga sunyi ɓulɓul da su🏃). To ga Nu'aymah ma dai an dace. Balle abin ya haɗa da kwanciyar hankali data samu, babu mai hantararta babu mai damun rayuwarta. Abinci saita zaɓa. Kullum zatai waya ko video call dasu Umm. Ga lafiyar jikinta Alhmdllh sai ƙaruwa take ƙarayi dan tana shan maganinta da ƙa'ida kasancewar Yoohan tsaye yake akanta da tsantsar kulawa.

      Takanji yana waya da papansa da momynsa (Madam Chioma) sai dai yanda bai taɓa cewa gashi su gaisaba itama bata taɓa nuna sha'awar hakanba. Garama Momy ranar ta kira yana wanka har sau uku. Ganin wayar na wajenta ya sakata ɗagawa suka gaisa. Sai dai yanda Momyn ta amsa mata a daƙile ya sosa ranta. Dan ta fahimci har yanzu da sukai nesa da juna ba ƙaunarta takeyiba. Su Momy Destiny ne dai ta gaisa dasu kusan sau uku-uku harda su Victoria. Amma su tom and jarry mama debora ko yaya jiki basu taɓa aiko mata da shiba balle suce zasu gaisa da ita a waya. kuma taji ranar duk sai da suka gaisa da Yoohan. Gebrail nema ta lura idan ya kirashi baya ɗagawa, daga bayama sai taga ya sakashi a black list.

  

         Gaba ɗaya ta hana Solomon musu gadi. Dan yanzu duk inda zasuje tuburewa take akan itadai bazataba inhar sai Solomon ɗin ya bisu. Hakan yasa Yoohan ya yanke shawarar kawai ya sallamesa ya koma Nigeria, dan baiga amfanin kisan kuɗin da yake ba a dalilin zaman Solomon ɗin tare da su.

       Randa ya samu Solomon da maganar komawa Nigeria hankalinsa yayi matuƙar tashi. Ya kira iyayen gidansa ya sanar musu da hukuncin Yoohan ɗin. Hakan yasa papa kiran Yoohan ya nuna masa bai amince da dawowar Solomon gidaba. Dan bazai yarda ya barshi shi kaɗai yana yawo ƙasashen duniya a cutar masa da shi ba.

       Yanda Aymah ta tubure kuma akan indai Solomon zai cigaba da kasancewa da su sai dai ita ta koma Nigeria wlhy yasa kan Yoohan ɗaukar zafi. Yayima Aymah lallashin duniya akan tabar zancen Solomon tunda papa ya dage amma sam taƙi saurarensa. har takaisu dayin ɓacin rai ranar akai barci kowa na ƙarshen gado. Washe garima taƙi kulasa shima ya shareta. Sai daga baya yaso su shirya taƙi. (A raina nace hummm Yoohan bakasan kafiyar Aymah bane ba). 

        Wannan tuburewar tata ya ƙara bashi haushi. Harya yanke shawaran ta shirya ta koma Nigeria tunda bazataji lallashinsa ba.

      A mamakinsa kuwa sai yaga ta hau haɗa kayanta. Dan itafa tabbas tayi alƙawarin bazata sake zama inuwa ɗaya da Solomon ba. Dan tsaf ta gama fahintar wannan nanema Yoohan ɗin da yakeyi akwai wata a ƙasa. tabbas da gaske akwai abinda su papa suke ɓoyewa game da Yoohan ɗin. Inba hakaba minene na nana masa guard a duk inda yake. Sannan sau biyu tana kama Solomon na waya da papa. Na farko yare taji yanayi sai turancin daya saka kaɗan ya sakata fahimtar papa ne. na biyu kuwa da turanci sukai magana. Hakan ya sata jin komai akan duk wani motsinsu Solomon yana sanarma papa. Dan a ranar shi papan har maganar ya kamata ta koma Nigeria yayma Yoohan. Amma shi Yoohan ɗin ya nuna baya bukatar yana wani ƙasa matarsa na wata ƙasa. A ransa kuwa ya ɗau alwashin Aymah bazata ƙara zama a gidanba baya kusa saboda Gebrail. Dan ba ƙyalesa yayiba. ya ɗau alwashin duk randa ya dira Nigeria sai Gebrail ya yabama aya zaƙinta.

      Ganin da gaske shirin tafiyar take ya sakashi sakkowa daga fushinsa shi. Ya fara lallashinta amma taƙi saurarensa. Saima kuka da take masa mai cin rai. Daga ƙarshe dai dole ya kira baba malam akan dan ALLAH ya lallasar masa ita. Dan shikam a yaune ya kuma tabbatar da borin Aymah bana wasa bane. Dan ko abinci taƙi ci, taƙi shan maganinta. ta birkice masa ita kawai ya kaita airport ta wuce gida kokuma ta tafi da kanta.

       Murmushi baba malam yayi kawai yana girgiza kansa. kafin ya sauke ajiyar zuciya ya farama Yoohan nasiha. Daga ƙarshe ya koma masa faɗa akan sakacinsane ai ya saka Nu'aymahn iya bijirema umarninsa. Dan haka ya nutsu sosai wajen riƙe gidansa da ƙyau. dan su mata wani lokacin zuma ne sai da wuta. Sannan wutar kara ne sai da iji. Ba'a sakaci da su sannan ba'a musu tsauri da yawa. ana riƙesune tsaka tsaki sai a samu jin daɗin duniya.

     Sosai Yoohan yaji shawarar sirikin nasa. tare da ƙarajin ƙaunarsa a cikin zuciya da ɓargo. Daga haka ya haɗashi da Nu'aymah kamar yanda ya buƙata.

        Zata fara masa kuka baba malam yay mata jan ido. faɗa sosai yay mata akan tashiga hankalinta mijinta ba abin rainawarta bane. Idan batai wasabama sai yazo har Austria ɗin ya hukuntata. Sai da ya tabbatar tayi laushi sosai da faɗansa sannan ya koma yimata nasiha. Daga baya kuma ya buƙaci jin dalilinta na takurawa akan Solomon ya barsu.

           Kasancewar Yoohan yana koyon hausa a wajenta ya sakata yin amfani da manya-manyan hausa wajen yima baba malam bayani akan abinda ta fahimta da zaman Solomon tare da su. Ta kuma bashi labarin abinda ya faru akan maganar hoto, harma da videos ɗin da Omar (Richard) ya nuna mata kwanakin baya da suka shuɗe. shi kansa baba malam ɗin hankalinsa yayi matuƙar tashi. sannan zarginsa ya fara zama gaskiya kenan. Albarka ya saka mata sosai da faɗan rashin sanar masa zance hoton da tayi tun a wancan lokacin. Duk da ya fahimci mijinta take son bama kariya akan matsalar da gajeren tunaninta ya kasa faɗaɗa mata. Yace,

      “Mamana yanzu ina hoton yake?”.

Hawayenta ta share da jan majina. Tace, “Abba yana nan Nigeria a cikin kayana”.

       “Masha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Saka wani ya ɗakkosa bazai yuwuba. Dan haka zamuyi haƙuri har ku dawo ƙasar sannan musan ta inda zamu ɓuloma al'amarin. Batun Solomon kuma bata hanyar rikici zaki yakicesa a jikin mijinki ba. Cikin hikima da wayon da ALLAH ya baku na mata da tarbiyyar Umm ɗinki zakiyi amfani wajen sakashi ya sallamosa. Ko kin taɓa ganin muna rikici da Umm ɗinki ne a gidannan?”.

     Kanta ta girgiza masa tamkar tana a gabansa. Sannan tace, “A'a Abba”. 

      “To amma shine ke zakije kina rikici da mijinki. har yana taroki kina ƙwacewa? Wannan shashanci ne ai. Sannan kina zubar mana da kimar tarbiyyar da muka baki. Mu mazafa da kike gani munada wuyar sha'ani dason nuna mulki a gidajenmu, shiyyasa duk macen data fahimci haka ta iya zama damu mutane suke ganin kamar ta mallake mijintane  nanko ba haka baneba. juriyace kawai da iya zama da mijin tayi. Ki kula da ƙyau. Mahaifiyarki abin koyice a gareki akan zaman takewar aure. Babu wanda zaice ga Jannat da wata matsala a gidan aurenta. da daɗi babu daɗi ta jure ta shanye komai. Yaya muka kwana yaya muka tashi ta jurema ranta. har takai wasu na ganin tsorona takeji da yawa. Nanko ba hakan bane. Mune muka san sirrin kammmu fiye da duk wanda ke zagaye damu. Karna ƙarajin haka kinji ko?”.

       Nu'aymah na sharar ƙwalla tace, “Insha ALLAHU Abba bazaka sake jiba”.

       “To Alhmdllh naji daɗin hakan kuwa. ALLAH yay miki albarka keda mijinki damu baki ɗaya”.

      Cike dajin kunya ta amsa da amin. Daga haka suka ajiye wayar. Ta ɗan saci kallon Yoohan dake kwance ciki sofa idanunsa a lumshe tamkar mai barci. Tashi tai a hankali taje ta ajiye masa wayarsa a saman ciki batare datace komaiba.

     Shima buɗe idanu kawai yayi ya bita da kallo harta shige toilet.


_________★★


        Batare da tasan yaya zancen Solomon ya kasanceba washe garin da suke cika sati biyu. ta kama randa zasu bar ƙasar kenan. Bayan sun kammala shirinsu tsaf sukaje asibiti aka ƙara tabbatar da ingancin lafiyarta, sukai sallama da su Dr Sophia kuma. Yoohan ya ƙara siya mata sauran magungunanta suka nufi airport cike da kewar ƙasar Austria da garin Vienna. Harma da mutanen cikinsa.

           Yanzunma suna nane da jelar tasu Solomon. Sai dai kuma suna zuwa Airport ta fahimci Solo Nigeria ya nufa. ita da shi kuwa U.S zasu wuce dan Yoohan ya koma hutu. Zai kuma gudar da wani aiki a ƙasar United states ɗin, da wani taron manyan likitoci da zasuyi kuma insha ALLAH.

        Duk da basu shiryaba har yanzun ita da shi sai da ya ga farin cikin komawar Solomon 9ja a fuskarta. Shidai hakan na bashi mamaki. dan ya gaza fahimtar ƙiyayyar dake tsakanita da Solomon. Shi kansa Solo ɗin ya kula baison Aymah. Sai dai baya iya nunawa a gabansa saboda shakkarsa da yakeyi. shi kuma bai taɓa nuna masa ya fahimta ɗinba dan yanason aje inda zai taka masa birki akan matarsa.

      Shi kansa Solomon sai da sukaje airport ya fahimci Nigeria zai komai. Gashi babu damar kiran papa ko madam Chioma dan suna a tare. Sai dai zuciyarsa na ƙara jin zafin Nu'aymah. Dan ransa ya basa itace sanadin komawar tasa tabbas. Musamman da yaga yanda taketa faman moso. Dan ya fahimci kwana biyun nan daga ita har ogan suna cikin rikicine ko damuwa oho bai gama tabbatarwaba dai.

      Jirgin su Solomon ne ya fara tashi zuwa Dubai. daga can zai hau Jirgin Nigeria. Ya tafi cike da alkairin da Yoohan yay masa da takaicin Nu'aymah da tsana mai tsanani. Dan shi baimasan ina zasujeba a yanzu haka. Solomon na wucewa da kamar mintuna ashirin da biyar suma nasu jirgin ya ɗaga zuwa U.S. yana ta wajen Window tana gefensa a cikin jirgin. Sai dai ya ɗauke fuska a binsa gashi ya ɗaureta tamau. Daga ƙarshema saiya kunna lap-top da liƙa earpiece a kunne ya hau kallon film. Duk da ran Nu'aymah ya sosu saita fuske tai kamar bama tasan da zamansa a wajenba. Koda akazo tambayarsu mi zasuci catai bata buƙatar komai. Shi kuma yasa aka kawo masa coffee da biscuits.

         Lokacin da jirginsu ya sauka a U.S Nu'aymah barci takeyi. Hakan yasaka Yoohan shafa mata fuska. Sai dai tana buɗe ido ya ɗauke kansa tamkar bashine ya aikataba. Itama duk da ta fahimci shine ya tadata sai ta watsar da shi ta basar. Handbag ɗinta ƴar ƙarama kawai ta ɗauka tai gaba. Shi kuma ya jawo trolly ɗinsu sai lap-top bag ɗinsa a hannu. Yana biye da ita a baya. Sai dai da suka sakko dole ita ta koma bayan nasa dan ba sanin hanya tayiba. Da wannan damar ta ware ido tana kallon airport ɗin daya amsa sunansa airport. Sai dai ta haɗiye mamakinta a rai wai kar Yoohan ya rainata da ƙauyanci😂.

      Taxi ya ɗauka musu drop. Koda suka shiga nanma dai kanta naga Window tana kallon birnin da mutanen cikinsa. Daga haka suka isa wani haɗaɗɗen gida daya amsa sunansa gida. A tunaninta gidan nasa ne. sai dai batasan haya ya kama musu ba dan a yanzun baya buƙatar zaman hotel ɗin da ita. sannan yanason barinta anan U.S ɗinne dan yasan bazai yuwu yayta gantali da ita duk inda yakeba. Inba wajen daya san zai iya yin sati biyu kwana goma ko sama da haka ba. Amma kamar tafiyar kwana uku ko biyu zuwa sati ɗaya zai iya barinta yaje ya dawo. Inba dai buƙatar tafiya da ita taga duniya tasa suje tareba.

      Komai da zasu buƙata na gida akwaisa a cikin gidan. Shopping ɗin abinci kawai zasuje suyi da kansu saiko suturar sakawa da sukazo da kayansu. Harga ALLAH gidan ya matuƙar burge Aymah harta kasa ɓoye shauƙin hakan a zahiri.

       Duk da yaji daɗin yanda tai farin ciki sai ya basar bai nuna mataba. Ya fara shiga ko'ina ya duba gidan da ƙyau. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata tamkar yanda ya gani a yanar gizo daya kama gidan sannan ya shiga wanka.

      Yana fitowa Nu'aymah dake kwance a gado ta miƙe itama ta shiga dan wankan take buƙata itama saboda gajiya. Koda ta fito zaune ta samesa a bakin gadon yana musu order ɗin abincin ta wayar landline. Da alama dai gidan abincin yana kusa da sune, kokuma yanada alaƙa da masu gidan abincin dama can.

     Sai gashi kafin ta gama kimtsawa tai sallar magriba da lokacinta ya shiga an kawo abincin. Shine ya fita ya amso. Sai dai bai dawo bedroom ɗinba yay zamansa a falo. Sallama acan yay abinsa.

         Wani mahaukacin yunwa Aymah takeji. Hakan yasa bayan ta idar da salla ko hijjab bata cireba ta biyosa falon. Dan bazata iya basar da cikintaba ta halaka a banza a wofi. Turus tayi tana binsa da kallon mamakin ganin yanda ya baje yana ɗora abinci a cikinsa. Ta kumbura baki ƙwalla na cika mata idanu. Cike da fushin data koya kwana biyun nan ta juya zata koma bedroom ɗin. Sai dai kuma caraf taji an riƙi mata hannu. Ƙoƙarin fisgewa ta farayi hawayen da take riƙewa na zubo mata a guje saman kumatu.

      Ɗaukarta yay gaba ɗayanta ya dawo da ita a falon. duk yanda take watsal-watsal da faɗin ya sauketa bataso bai kulataba. Ya zauna cikin lallausar zagayayyar kujerar da aka ƙawata falon da ita kalar royal blue tana a jikinsa. Cikin hawayen da takeyi ta shiga kaimasa ƙananun duka a ƙirji da faɗin ita ya saketa bataso. Tunda yabar sonta yaje ta haƙura ta barma duniya dasu Miracle dake addabarsa da text massege kullum shi. 

         Zancen nata yaso bashi dariya. Dan haka ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa akanta yana ƙoƙarin riƙe hannayenta da take kaimasa duka a ƙirji. A ransa kuwa yana sake jinjina rikicinta. Duk da ransa na raya masa wani abu game da saurin fushinta na kwana biyun nan. Sai dai bai tabbatarba dan ya san inma shine to ƙaramine kuwa sosai.

     Bakinsu ya haɗe waje guda. Tun tana turesa harya samu nasarar maida mata jiki laƙwas ta fara bashi haɗin kai. Da ga ƙarshe ya ɗauki abarsa cak suka shige bedroom inda zaiyi lallashi ɗan gaske na zallar ƙauna da babu gaurayen algus a cikinta😵. Saiga mutuniyarkun muna funfun dake faɗin zata barma duniya dasu Miracle tai luf kamar bata gidan😏😧.

            (Su Aymah babu aji🏌😑)


Sai da suka gama wadata juna da farin ciki yanda ya kamata. Yoohan ya kalli Aymah dake lafe a jikinsa idanu a lumshe alamar barcin nata na ƙa'ida zai ɗauketa. Dan duk sanda hakan ta kasance a tsakaninsu sai tayi wannan barcin. Shiyyasa yake kiranta raguwa.

        Guntun murmushi yayi da lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta tare da ja mata hanci. “Silly girl! Babu abinda ta iya sai jan mutane faɗa”.

      Lumsassun idanunta da basu gama washewaba ta buɗe a kansa. Sai kuma ta tura masa baki tana maidawa ta rufe tare da tirza ƙafarta dake jikinsa tace, “Tab, kai wama ya kaika iya neman mutane faɗa”.

       Sake jawo bargon data zazzame da ƙafa yayi ya lulluɓesu da ƙyau yana ƙara sakata jikinsa. “Nine ma mai neman faɗan kenan?”. 

     “Sosai ma. Tunda ai kaine dai kasa akayi wannan faɗan”.

         Dariyar data bashi ce ta sakashin yin guntun murmushi. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta yana sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu. “ALLAH na gode maka daka mallakamin ƴar rigimarnan tawa. Tare da mai ramamin gashinan yazo”.

         “A ina?”.

Tai tambayar cikin yanayin barcin daya figeta.

        “Mi kikeci na baka nazuba, zaki gani ai”. Ya faɗa yana miƙewa zaune da ita a jikinsa. Cike da shagwaɓa tace, “Ni wlhy barci nakeji”.

      “To muje ayi wanka, sai kizo kiyi Sweet girl ɗin Yahya”.

      Da taimakonsa sukaje akayo wankan. Dan barcin da bataiba na bayan lobewa ne cike da idanunta. Suna fitowa kuwa ta zube a gadon ta fara. Kayan barci ya ciro mata yazo bakin gadon ya zauna yana kallonta na tsayin mintuna uku. Hannunta ya kamo ya na kallon tafin, kafin ya juya ya tsurama yatsun idanu suma na kusan minti ɗaya. Ya miƙe inda ƙafafunta suke ya durƙusa a gaban gadon yana kallon yantsun suma na tsayin mintuna. Sassanyan murmushi ya sauke da ajiyar zuciya, ya sumbaci ƙafafun duka biyu sannan ya dawo kusa da ita ya zauna. Sake tsirama fuskarta ido yayi na tsahon wasu mintunan cike da so da ƙauna, kafin ya ranƙwafa kanta yana sumbatar bakinta da kumatunta, idanun har wuya. (Ni mai ɗauka muku rahotonma sai yaban dariya. Dan na kasa fahimtar inda ya dosa😂😑).

      Kayan barcin ya sanya mata, ya gyara mata kwanciya, shikuma ya koma bayin ya ɗauro alwala ya dawo yay zaman karatun al-qur'ani. Dan tunda suka fara rigimarnan ta Solomon kota ɗora masa karatun ba fahimta yakeba da ƙyau. Haka yake kwata-kwata bayason damuwa. Koyaya irin haka ta faru da shi duk sai ya fita hayyacinsa. Ya jima yana duba al-qur'anin da sauran buks ɗin kafin ya miƙe zuwa fallo ya tattaro abincin da yaci ya rage dan yasan saita tashi cin abinci tunda yunwar takeji. Kwana biyun nan haka take, batama abinci sauƙi. Kodan jinyar da tasha ne oho. Sallaya ya hau ya kabbara sallar isha'i, bayan ya idan bai kwantaba ya ɗauki wayarsa da tun ɗazun yake ganin tana haske, ya tabbatar kuma kiransa akeyi dan a silent take.

      Ilai kuwa missed calls ne na papa har guda takwas, sai na Momynsa biyar. Sai na Omar (Richard) biyu. Sauran kuma duk ba important bane a garesa dan haka baibi takansuba dan harda mayyarsa Miracle.

        Kiran papa da Momy yasan bai wuce saukar Solomon Nigeria ba. Dan haka yay kiran Omar (Rich) kawai da shima yana Nigeria. 

       Sallama kawai Omar (Richard) ya amsa masa, ya shiga masa shaƙiyanci wai yanzu soyayya tasa sai ya gadama yake amsawa mutane kira a waya. Su G-boy ma jiya suka gama masa tsogumi a wajen birthday ɗin Osin da akayi a garin Lagos. Kai abokan suma da yawa sunyi wannan complain ɗin duk da dama sunsan shi Yoohan fa bai cika ɗaukar kiran da zuciyarsa ta raya masa mara amfani bane, saboda yanayin aikinsa da duk ya maidasa busy a gaba ɗayan rayuwarsa. Sai dai idan yana a cikin hutu da kansa yake bin abokan mu'amulat nashi masu muhimmanci ya kirasu su gaisa koda bazai zauna hira da kai ba. Musamman ma daya musulinta ɗin nan ya ƙara sanin darajar zuminci.

      Murmushi kawai yayima Omar (Rich) ɗin da cewa “Humm ka samin ido da yawa”. Dariya kawai Omar yayi da ga can. Dan ya fahimci ƴan miskilancinne a kusa yau. Ajiye maganar wasan yayi suka fara tattaunawa kamar haka.

       “X-man duk yanda muke tunanin aikinan bazai kasance mai sauƙiba. Amma dai na turo maka dukkan bayanan dake a hannuna yanzu ta Email ɗinka. Ni dai yanzu shawarar dana yanke, mizai hana mu sami wani amintaccen jami'in tsaro da zai taimaka mana akan case ɗin nan. Dan tabbas sai munyi kutse a cikin wayoyin mutanen gidan saboda fahimtar da nayi case ɗin babba ne dan yanada tushe”.

     Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke yana bin Nu'aymah da ta tashi zaune da kallo. Ya juya harshensa zuwa yare. “Tunaninka mai ƙyaune Omar. Inaga kuma babu wanda zai iya taimakonmu akan aikin nan sai Dawood, sai yay mana hanyar ganin bawan ALLAH nan dana taɓa baka labarin ya taɓa buƙatar na duba matarsa akan matsalar cancer ɗin mahaifa da sukai zargin tana da ita, sai dai hakan bata samuba a wacan karon sai haɗasu nai da wani likitan.. So dole zan shigo Nigeria kwanan nan, tunda kaga akwai aikin da zanzo nayima anan Lagos. Kuma shi mutumin babban jami'i ne zaifi dawood tsaya mana sosai”.

         “To shikenan, sai mu bari sai kazo ɗin saimu tattauna, insha ALLAH madam ma zata dawo nextweek tunda kuna nan”. 

      “Idan kayi hakan kuwa zaka taimaka min, dan zaman Zeeynab a ƙasar nan yana buƙatar samun wanda zasu shaƙu. Inason samar mata admission ma ta fara karatunta insha ALLAH. Dan tanason karatu sosai na fahimta. Sannan tanada brain, sai dai shiriritanta yayi yawa wlhy”. Ya ƙare maganar yana satar kallonta, dan tana zaune ne tana cin abincin da yunwa ta hanata barcin nata yay tsaho.

      Dariya Omar yayi daga can yana faɗin, “Ai da sauranta ne. 18years fa. bandama hausawan nan babu ruwansu ina ƴar 18years ina aure. Sai dai kuma yanzu ni tsarinsu birgeni yake. Indai madam ta haihu min baby girl nima tana gama secondary zan mata aure”.

     Dariya zancen ya bama Yoohan. Dan haka ya murmushi yana bin Aymah da wani narkakken kallo. Itako ta zuba masa harara ta ɗauke kanta. Dan tana takaicin idan suna tare taji ya canja harshe yana magana. Sai taga kamar gulmarta akeyi🤣. Shiko tunda ya fahimta ma har yi yake danya takaleta suyi faɗan nasu.

            Cikin ɗauke kai yace, “Saina faɗa mata duk abinda ka faɗa”.

     “Kai! Kaifa baka da kirki wani sa'in dude. Ni karka ɓatamin suna wajen ƙanwata dan kaga dai tace yanzu nine yayanta, idan ka mata laifi zata kawomin ƙara na hukuntaka”.

       “Kai kuma kaji daɗi ko? Shege mai shiga hancin masoya sai anjima. Wuce ka tafi wajen Juliet ɗinka dare ne anan inan buƙatar ɗumin baby na”. Kafin Omar yace wani abu Yoohan ya yanke wayar ƙitt.

          Matsowa yay kusa da ita ya amshi spoon yana faɗin, “Wannan fake yayan naki yana takuramin da yawa Sweet girl”. Sai da ta buɗe baki ya saka mata abincin daya ɗebo sannan ta bashi amsa cike da kasalar barcin da takeji. 

       “Ai shine zai dinga saitomin kai idan ka birkice. Dan kaima rigimammene silly boy”.

        Goshinsa ya shafa zuwa saman ido yana murmushi. Ya cigaba da bata abinci batare da yace komaiba. Ta fahimci yau dai halinne ya motsa, shiyyasa itama tayi shiru ta cigaba da karɓar abinci da yake bata. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan shina ta amsa zata fara bashi. Cikin marairaicewa yace, “Na ƙoshi Sweet girl. Karkisa naita ƙaton ciki kizo kina kasa ɗaukata dama gaki da rakin tsiya”. 

      Murmushin da batayi niyyaba ta saki. Ta kwanto a gefen hannunsa tana lumshe ido da faɗin, “Duk ƙaton cikinka zan iya da kai malam”.

      “Oh wow!!. Da gaske?”.

    Miƙewa tai zata gudu yay saurin riƙota ta faɗo jikinsa. A cikin kunnenta yace, “Yarinyar nan kinfa ƙware wajen guduwa ba'a gama magana ba”. 

         Da sauri ta taune lip ɗinta na ƙasa tana dariya ƙasa-ƙasa. “Ni kaga barci nakeji ALLAH. Ka barni na kwanta kona maka barci a jiki”.

       “Ai jikinki ne baby”. Ya bata amsa yana miƙewa ɗauke da ita suka haura kan gadon. Fitilar ya rage musu yana gyara mata kwanciya a jikinsa da ƙyau. Kanta ya sumbata suka sauke ajiyar zuciya. Ɗagowa itama tayi ta sumbaci laɓansa da shafa kwantaccen sajensa. Cikin sauke murya sosai tace, “I'm sorry. Nayi alƙawarin bazan sake ba insha ALLAHU”.

       “Thanks you sweet angel. ALLAH yay miki albarka. Nima kiyi haƙurin ɓata miki rai da nayi. Insha ALLAH bazan ƙaraba humyim?”. Ya ƙare maganar da cusa kansa a wuyanta yana shinshina. Ƙanƙamesa tayi dan salonsa a kullum mai wahalane a gareta.....


______________★★


         *_ABUJA NIGERIA_*


      Isowar Solomon Nigeria shi kaɗai yayi matuƙar tadama papa hankali. Duk da baice dasu komai ba saboda darene anan 9ja sanda ya iso ɗin. Amma sai papa ya kasa haƙuri ya shiga antayama Yoohan kira a waya. A lokacin shi kuma bai kulaba dan wayar na'a silent ne. Itama Madam Chioma tashin hakalinta ganin Solomon ɗin shi kaɗai babu Nu'aymah babu Yoohan ɗinne ya sakata kiransa taji su kuma suna inane? Amma sai yaƙi ya ɗaga. Daga ƙarshe ma sai suka daina samun layin nasa gaba ɗaya. Da wannan tashin hankalin suka kwana. Duk da ma barcin nasu rabi da rabi sukayisa. 


        Aiko gari na wayewa suka nemi Solomon da shima dai kiran nasu dama yake jira. Dan shima ɓacin rai bai barsa yayi isashen barcinba. Kwana yayi yana mafarkin Nu'aymah da tsanarta ke ƙara hauhawa masa a rai a kowane daƙiƙa na rayuwarsa. 

       A falon papa ya samu Momy da papan. Bayan ya gaishesu suka buƙacin bayanin dawowarsa babu su Yoohan. Tsaf ya kwashe komai ya faɗa musu harda ƙarawa da ƙarya. A take ransu ya ƙara ƙololuwar tashi. Papa ya miƙe a fusace yana faɗin, “Lallai yarinyarnan ubanta dama ya turota gidan nan ne bisa wani dalili. Darling bani keys ɗin sashen John. Dole na bincikima ɗakin yarinyarnan yau..........✍


(Munga idi hotonmu😱🏃).

No comments

Powered by Blogger.