Saran Boye 56

 


No. 56


.............A hankali Yoohan ya ringa buɗe idanunsa da ke ganin wanda ke zaune a gefensa dishi-dishi. Hannunsa ya ɗaga da ƙyar ya kamo na Richard wasu zafafa hawaye na silalo masa daga cikin idanu. Cikin rawar murya yace, “Da gaske ta na rasata ko Rich?”.

        Ƙasa Richard yay da kansa shima hawaye na ciko masa idanunsa. Ya zare hannunsa da ga cikin na Yoohan zai miƙe. Saurin riƙosa Yoohan yay yana girgiza masa kai. “Please Richard faɗamin gaskiya”.

      Kai Rich ya girgiza masa. “Basu ce mana komai ba har yanzun Yoohan. Tun da aka kawoka nan suka sake komawa ɗakin har yanzu basu fitoba kuma”.

        Da sauri Yoohan ya yunƙura zai tashi. Sai dai ya dafe kansa da hannunsa saboda tsananin sara masan da yayi. Saurin riƙosa Rich yayi yana faɗin, “Please cool down.

      “Bazan iya ba Richard, Karka damu dani, ina bukatar ganinta”.

       Duk yanda Rich yaso Yoohan ya haƙura yaƙi sauratensa sam. Dole ya taimaka masa suka fito a ɗakin yana dafe da kansa. Sai dai dole a ƙofar ɗakin suka tsaya dan dokace bazaiyi knocking ba ba kuma zai shigar musu kai tsaye ba. Yadai danna wani ɗan abu dake a jikin Computer ɗin dake maƙale a bangon ɗakin. Bayan kamar mintuna biyar ƙofar ta zuge ya shige.

         Da ƙyar ya iya ringa ɗaga ƙafarsa ya shiga saboda tsabar fargaba. A tare duk Doctors ɗin suka juyo suna kallonsa, fuskokinsu ya dinga bi da kallo ƙirjinsa na bugawa da sauri-sauri. Yama gama yarda ya rasata kawai. Dan haka ya juya zai sake fita hawaye na gangaro masa a saman fuska. a hankali Dr Sophia Tace, “Dr Yoohan!”. Cak ya tsaya da ga yunƙurin fitar tasa. Sai dai ya kasa juyowa. Sai da yaja kusan mintuna biyu sannan ya juyo a hankali yana kallon fuskokinsu da a yanzu suke ɗauke da murmushi.

     Kafin ya nema ba'asi Dr Liam Yace, “Smiles”. Yay maganar da ɗora yatsunsa biyu a gefen bakinsa alamar Yoohan yayi murmushin. Da gaske kuwa sai ga murmushin ya suɓuce masa ga hawaye. Ya tako da hanzari inda aka saka Aymah cikin wata na'uwar glass.

      Su kansu yanda yayi ɗin sai da ya basu tausayi da dariya, ta cikin Computers ɗin ya tabbatar da gaske Nu'aymahn sa nada ranta. Sai dai tana a halin suma haryanzu. Zuciyarta dai tana harbawa. Ƙafafuntane kawai a waje zuwa gwiwa, sauran jikin duk yana a cikin glass ɗin. Ya koma wajen ƙafafun ya riƙesu duka cikin hannunsa ya sumbaci tafinsu sau kusan uku-uku. Ga hawayen daɗi yanzu na sakko masa.

      Kamashi Dr Liam yazo yayi ya miƙar. Ya rungumesa yana masa Congratulations, aiki yayi kyau, sai kuma fatan farfaɗowarts da addu'ar kartai loosing memory ɗinta. Suma sauran duk sun masa Congratulations shima yayi musu, sannan suka tattaro suka fito dan sai zuwa nanda awanni goma sha biyu za'a fiddota daga ɗakin a maidata wani inda nanma zata share wasu awanni goma sha biyu daga nan ake fatan farfaɗowarta gaba ɗaya kuma.


        Su Yoohan na fitowa Rich ya nufosu, rungume juna sukayi yana tambayar tana da rai ne? Saboda ganin farin ciki tattare da Yoohan. Fuskar Yoohan washe da irin dariyar da shi kansa Rich ɗin bai taɓa gani ba yake tabbatar masa aiki yayi ƙyau. A take farin cikinsu ya ƙaru har Solomon. Dan shima Yoohan ɗin rungumesa yay.

        Baba malam Yoohan ya fara kira ya sanarmawa. sai kuma Papa dake tare da Momy dan ya koma Nigeria yau da safe. A wayar dai kam ya nuna murnarsa. amma yana katsewa yaja wani shegen tsaki mai nuna tsantsar takaici. ba haka ya soba sam. Dan game da aikin nan da za'aima Aymah a mutuwar da sukai fatan zatayi harsun gama tsara komai game da aikinsu akan baba malam.

      Ransa a ɓace ya ɗauki waya ya kira Dr Mateo. Domin kuwa sunyi da shi lallai Nu'aymah bazata tashi ba. Dan zaiyi duk abinda zaiyi su kasheta tun a wajen aikin. Sai dai har wayar katse Dr Mateo bai ɗaga masa kira ba. Maida kiransa yay ga Solomon. Shi kuma a lokacin suna tare da Yoohan da Richard shiyyasa ya kasa ɗagawa dan yasan dalilin kiran papan tunda a gabansu Yoohan ya kira ya sanar masa anyi aiki kuma an dace.


      Ba ƙaramin sake haukacewa Papa yayi ba kuwa. Ya ringa zazzaga bala'i Momy na tayasa itama duk da ba komai ta sani game da shirin papa ɗinba. To amma itama wannan ranar itace fatanta tun a daren auren Yoohan da Aymah da papa ya sanar mata matsalar Aymah da aikin da Yoohan zai fita da ita bayan auren. Wanda yana ɗaya daga dalilan yin auren da gaggawa. Shine dalilin sakankancewarta tabar Aymah miƙe ƙafa a gidanta tana zuba iskancin data gadama. To yanzu kuwa inhar Aymah bata mutu a wajen aiki ba lallai game ɗin zai canja salo kenan. Dan babu wata mace a duniya data isa raɓar Yoohan inhar tana a raye tana numfashi. Shiyyasa ma ta ɗauki mataki a kansa tun shekaru da dama ta kashe masa mazantakar tasa. Wannan yana ɗaya daga abinda ya sake assasa rashin damuwa da mata ga Yoohan, dan akan Nu'aymah ya farajin feeling makamancin hakan bayan shekarun farkon balaga da suka shuɗe masa lokacin yana farkon shiga University. Dan yanayinsa ya fara masa yanada ƙarfin sha'awa, amma ko a wancan lokacin yayi ƙoƙarin riƙe kansa dan shekararsa sha tara kacal, sai dai abin mamaki kafin suje level 2 sai yaji sam matanma basa burgesa. Kizo ki gama taɓararki a gabansa da nuna masa jiki ko a kwalar rigarsa bayajin komai ko a ɗanyatsan ƙafa kuwa. Rashin kula ta hanashi fahimtar akwai damuwa tattare da shi, sai ma sake ƙaimi da yayi akan harkar karatunsa fiye da farko. kuma shine dalilin saka masa rashin barci yake ɗaukar tsahon kwanaki, a dabarar bokan nata wannan galabaitar da zaiyi zai sakashi shan wani abu ya fita hayyacinsa. Ita kuma sai tai amfani da damar wajen kusanta kanta da shi har ta dinga biyama kanta buƙata.


     Sai dai kuma shi UBANGIJI alhakimu ne. dan hakan data aikata sai yazam kiyayewa ga Yoohan bai taɓa aikata zina ba. saboda tayi a sirin ne a dai-dai gaɓar da girmansa ya kai zai iya sha'awar kasancewa da macen.  Dalilin rashin barci kuma bai sakashi shan giya ko kayan maye ɗinba, abinda ma bata saniba ba aikinta bane ke hana Yoohan rashin barci. Wani kuma ƙullinne daban, ga wanda batai zatoba da ita kanta bata fahimtaba. Duk da kuwa tun yana yaro tasa akai masa wannan asirin.


To masu karatu sai muyi fatan samun lafiyar Aymah dan muga yaya wannan wasan zai kaya tsakanin madam Chioma, uwa ga Yoohana da   kuma Madam Nu'aymah mata ga Yoohana. Ga Papa ga baba malam, ga kuma Yoohan ga Abdallah dan tabbas idan mun tuna abinda ya faru ranar shopping  hakan na nufin akwai zazzafan wasa a ƙasa. Tsakanin Ayma da papa ma akwai game, hakama tsakanin Yoohan da family ɗin Aymah akwai game. Sai kuma Nasir da Abdallah. Tabb gyama-gyamanfa na da yawa. Kuma da alama samun lafiyar Nu'aymah ne kakar buga wasannin sai muje zuwa muga yanda za'a kafta wasannin😋😸😉🏃🏃.


________★★★★________


       Washe gari kamar haɗin baki su baba malam da papa a tare suka taho ƙasar Austria a jirgi ɗaya kuma. Suma basu fahimci hakaba sai da suka sauka kowanne yaga ɗan uwansa. Kallon kallo akaima juna tsakanin Papa da baba malam, Umm da madam Chioma. Sai dai baba malam ne ya fara kauda shirun da miƙama papa hannu. Itama Umm sai tai ɗan murmushi tana kallon madam Chioma da ke jinjina ƙyawu da kamalar mahaifiyar Nu'aymah. A ranata tace, ‘Ashe anan yarinyar nan ta ɗakko ƙyau kamar ƴar aljanu’.

      Itako Umm mamakinta yanda babu wani kamannin Yoohan da madam Chioma kamar yanda tai tunanin gani.

           Sun gaisa kowa yana ƙoƙarin danne abinda ke cikin ransa. Richard da Solomon dama sukazo ɗaukarsu, dan shi Yoohan sarai yasan a jirgi ɗaya zasu taho amma yaƙi sanarma kowannensu.

        Tun a wajen su Rich suka sakejin labari mai daɗi daya sake saka musu nutswa a zukata. Sai dai na papa da madam Chioma iya kan fuska ne kawai. Sai da aka fara kaisu masauki da Yoohan ya tanada musu, Rich yace su huta nanda awa uku zaizo suje asibitin dan ko sunje yanzu baza'a bari suga Aymah ba tunda ba'akai ga fiddota daga wancan ɗakin ba har yanzun. Duk da kodama sun fiddotan da wahala subar wani shiga inda take sai dai likitocin kawai.

       Su baba malam basu damuba. Dan mutanene masu tawakalli da kawaici. A ganinsu kuma tunda har suka iso ƙasar ai magana ta ƙare kuma.


        Papa dai kam bai zauna ba. Yana tabbatar da Rich sunbar hotel ɗin ta hanyar Solomon ya shirya shima ya fito zuwa inda sukai zasu haɗu da Dr Mateo, Sai da ya isa wajen shan coffee ɗin da kusan mintuna goma sannan Dr Mateo ya iso.

           Gaisuwar arziƙi Papa bai bari sunyi ba ya rufesa da jarabar miyasa yasan bazai iya aikinba ya amsa zai masa har kuma yama biyasa maƙudan kuɗaɗe?.

           Dr Mateo dake kallon papa a yatsine yace, “Na kula ƙwalwarka bata aiki da ƙyau Mr Goshpower. Wannan ƙasar tamufa ba irin africa ɗinku bane da kuka ɗauki ran mutum ba abakin komaiba. Sannan mutanenmu ba wawaye bane irinku da suke abu da ka babu wata ƙa'ida. Duk da aikine mai haɗarin gaske amma na gwada son ganin na aiwatar dan in faranta maka. Sai dai matsalar da aka samu bani kaɗai nayi aikinba. Kuma duk Doctors ɗin da mukayi aikinnan tare suna bala'i-bala'in ganin mutuncin yaronka Yoohan, dan yanada mutunci da karfi a wannan asibiti saboda yayi mana manyan ayyuka da ko gwamnatin ƙasarnan bazata manta da shi ba balle asibitin kansa. So Please kayi wani tunani akan kisan yarinyar ta wani hanyan amma ba wannan ba. Dan koni kaina yanda na fahimci Dr Yoohan nason yarinyar bazan iya kasheta ba dan ina girmama soyayya sosai”.

         A rikice papa yace, “Ban gane bazaka iya kasheta ba. Kana nufin kaci kuɗina a banza kenan?”.

       “A wofi ma kuwa Mr goshpower, dan na gwada maka aikin daka bani nasarace kawai ba'ayi ba, saboda yarinyar ƴar baiwa ce. Sannan ka yarda da shawarata kar kayi wani gangancin koda na saka wanine ya kasheta a cikin asibitin nan, asirinka zai tonu. Dan koshi ɗan naka bazai barka ka kuma zuƙar iska ba a duniya inhar ya fahimta. Ni kaina dasun fahimci nine naso ɓata musu aiki har Dr Yoohan ya tsorata ya suma da baka ganni anan gabanka ba. Abu na karshe dazan sanar maka kuma shine zagaye take da securitys ta ko ina saboda girmamawa ga Dr Yoohan akan hidimarsa. Dan tunda kowa ya fahimci matarsace kaf Doctors ɗinmu sun sake ninka kulawarsu fiye data farko a gareta. na barka lafiya”. Ya kare maganar da wani kaɗa masa yatsunsa da kashe ido yana wani shegen murmushi.

       Tamkar wani soko haka Papa yabi Dr Mateo da kallo harya tare taxi ya shige. Jiyay kansa ya masa wani irin shegen nauyi, ya ɗauki butar da aka zubo musu coffe a ciki ya tsiyaya a karamin kofi. Duk da turirin da yakeyi bai damuba haka ya kafa kansa ya hau kwankwaɗa yana ƙona masa baki da maƙogwaro. Wato lallai ya fahimci baturen likitan nan ɗan iska ya maidashi kawai. Duk yasan da wannan dokar amma ya amsar masa kuɗi ya kuma amsa masa zaiyi aikin?. Ɗaga kofin yayi kamar zai rotsa da ƙasa sai kuma ya fasa ya ajiye ya miƙe a fusace ya baro shagon shan coffe ɗin yana kumbura kamar wani kububuwa😁😜.


      Nannauyan numfashi Richard dake kujerar bayan su papa ya sauke, tsabar kaɗuwa da tattaunawar papa da Dr Mateo ta sakashi cire p-cap ɗin kansa ya hau fifita da ita. Miƙewa yay da ga shagon coffe ɗin shima ya fice zuciyarsa na bala'in masa kai kawo.


******


          A ɓangaren su Baba malam kuwa awanni uku na cika sai ga Solomon ya dawo ɗaukarsu. Ya iske papa baya nan dan haka ya tafi da su su uku tunda yasan inda papan ya tafi. Sun isa asibitin dai-dai da fitowar Yoohan daga wani aiki da sukai shi da wasu likitoci. Dan dama akwai yarjejiniya tsakaninsa da asibitin akan zasu taimakesa aima Nu'aymah aiki, shima kuma zai taimakesu wajen duba musu nasu patients ɗin da sukasan yanada basira a kai. Ya kuma amince zaiyi, dan haka bayan an kamalama Aymah shima ya maida hankali wajen cika musu nasu alƙawarin duk da kuwa duk abinda yakeyi hankalinsa na a kanta.

         Cike da murmushi ya tarbi su baba malam. Kamar yanda suma suke nasu ƙayataccen murmushi. Madam Chioma kam kallonsa take kamar ta hadiyesa. Ta buɗe masa hannayenta alamar yazo gareta. Daga shi sai ita ma baya iyawa balle yanzu akwai baba malam a wajen. Kafaɗarsa ya maƙe mata tare da cigaba da takowa zuwa gaban baba malam. Shi ya fara gaidawa da girmamawa. Baba malam ya riƙo hannunsa yana murmushi sukai musabaha. Daga haka ya gaida Umm itama data amsa masa cike da kunyar surukuta. Shima dai ya kasa dubanta da ƙyau dan tana masa tsananin kwarjini ainun.

       Juyawa yay ga Madam Chioma data cika tayi fam da takaici da kishi. Bai damu da yanayin nata ba ya kamo hannunta ya sumbata yana murmushi. Danne zuciyarta tai da ƙyar ta nuna masa kulawa da tambayarsa yaya daughter ɗinta. Cike da kulawa a gareta da nuna jin daɗi ya sanarmata suna fatan nasara ga farfadowar dota ɗin tata.

      Daga haka yay musu jagora zuwa zuwa ɗakin da aka maida Nu'ayma mintuna talatin da suka shuɗe. Basu shiga har inda takeba. Dan hakan dokar take ba'ason motsin komai a inda take. Hatta da takalmansu duk sai da suka cire suka saka na roba duk da kuwa ba ainahin ɗakin zasu shiga ba. Ta cikin glass ɗin daya raba tsakanin inda suke da dakin da Ayma ke a ciki suka lekata. Dolene mai imani ya ganta yaji tsananin tausayinta, dan bata da maraba da gawa a kwance, na'urorine kawai ke aiki a jikinta ta ko ina. Sun mata addu'oin samun lafiya a zukatansu suka baro wajen Umm na share hawaye. Baba malam ma dai dauriyace kawai da jarumta.

        Office ɗin da Yoohan yake suka koma, anan yay musu bayani sosai akan nasarorin da aka samu a wajen aikin da wanda suke fatan samu idan ta farka. Sunji daɗi sosai, sunata kuma godema ALLAH. Madam Chioma dai murmushi kawai take wanda yafi kuka ciwo. A haka papa yazo ya samesu shima.

       Shima dai sai da aka rakasa yaga Nu'ayma dan ya dage cike da nuna damuwa da alhini kamar har cikin zuciyarsa ne.

          Lokacin da zasu koma masauki tare suka tafi da Yoohan dan zaije yay hutun awanni biyar kafin ya sake dawowa asibitin.


★★★★★


           Ƙarfe takwas da rabi na dare agogon ƙasar su Yoohan suke saka ran farfaɗowar Nu'aymah. Amma sai bai sanarma su baba malam ba dan basu san mizai biyo baya ba. Yafi son sai sunga komai yanda suke fata kafin yay musu albishir. Daga shi sai Rich nema sukazo asibitin, Solomon ma sun barshi a masauki. Yauma sai da yay salla raka'a biyu da addu'ar neman nasara kafin su shiga ɗakin da Nu'aymahn take. Duk da ransa cike yake da tsoro haka yaketa ƙarfafa kansa suna ƙoƙarin janye duk wata na'ura dake tare da jikin ta.. Sai da suka cire komai aka barta da na'urar numfashi kawai kafin Yoohan ɗin da kansa yay mata wata allura. Daga haka suka koma gefe suka zubama sarautar UBANGIJI idanu kuma.

         Mintuna sha biyar da suke jira ta cika Aymah bata motsa ba. Suka sake ƙara biyar suma suka shuɗe shiru. Sha biyar suka ƙara nanma babu labari. Dukansu babu wanda tsoro da fargaba bata riskesa ba, musamman Yoohan da ruɗaninsa ke neman fitowa fili. Dr Sophia ta bada shawaran ko zasu sake mata allurarne dan dama ta fahimci jininta nada matuƙar ƙarfi. Duk sunyi na'am da hakan tunda sunsan ba illa bane. A ƙa'ida ma za'a iya yimata sau uku. Daga hakane idan bata farfaɗo ba sun tabbatar mutum ya mutu kenan.

         A yanzun kam Yoohan bashi yay alluranba dan bazaima iyaba. Koda suke maganarsu zaune kawai yake yana kallonsu bai saka bakinsa ba. Hakama har akai allurar bai motsa daga inda yake ba. Yanzu dai mintuna talatin suka bata na jira.

      Cikin amincin UBANGIJI minti ashirin da bakwai na cika tai wata irin mahaukaciyar zabura. Sai jikinta ya kama rawa har gadon kansa na jijjiga. Gaba ɗayansu suka rufu a kanta kowa na nuna farin cikinsa. dan kuwa dai ta wuce mataki na biyu kenan. Wanda kuma yafi kowanne haɗari dama a aikin. Matakin ƙarshe shine abubuwan dake a ƙwaƙwalwar ta zasu dawo ko zatayi loosing ɗinsu. Kasancewar ta yarinya ƙarama basu cika damuwa da wannan ba dan a ganinsu tanada sauran isashen lokacin da zata koya duk abinda ta rasa. Sai dai ga Yoohan sam baya fatan haka. Burinsa komanta ya kasance tare da ita musamman karatunta na addini koda kuwa zata manta da sauran abubuwan ciki harda shi kansa.

       Dukkanin taimakon daya dace shi suke bata cike da ƙwarewar aiki. A awa guda suka dai-daita komai Alhmdllh. Allurar barci aka sake mata da bama Nurse ɗin da zasu goge mata jiki dama. Amma sai Yoohan ɗinma yace su barshi. da kansa ya gogemata jikin ya canja mata kaya sannan aka maidata ɗakin da zatai jiyya.

          Farin cikine sosai tattare da Yoohan. Dan yanaga komai ya dai-daita tana sauke numfashin barci da ajiyar zuciya a kai akai sai ya fito ya koma masauki dan ya sanarma su baba malam wannan daddaɗan labari.


        Aiko basu kaɗaiba hatta da su hajjo ƴan Nigeria dake can cike da fargaba da alhini duk sun kaure da farin ciki da murna tamkar ance Aymah ta miƙe a kan ƙafafunta. Hajjo ta kuma sakawa akai abinci mai yawa akai sadaka da shi. suka kuma shirya ita da kaf ƴan gidan sukaje asibiti sukai ziyarar marasa lafiya da bama masu buƙatar taimakon tallafi.

      Suma anan daga su baba malam har Yoohan sunta nafilfiline suna nunama UBANGIJI godiyarsu akan wannan ni'ima da yay musu. Washe gari kuma suka tashi da azumi a bakinsu na sake jaddada godiyarsu ga ALLAH. Sun kuma je sun duba ta suma hankalinsu ya sake kwanciya da samun nutsuwa fiye da farko.

     Shi kansa Yoohan yau yini yay yana barci cike da kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya tare da daddaɗan mafarki.

          Su papa dai baƙin ciki fal ransu. Dan a ranarma sukace zasu koma tunda ta farfaɗo. Daga Yoohan harsu baba malam basu kawo komai a ransu ba game da hakan. Sai ma godiya da sukai musu tare da rakkiya har airport. Shima Yoohan ɗin a ganinsa zaifi samun sakewa da su baba malam ɗin a yanzu fiye da su papa na tare da su.


       Aiko hakance ta kasance. Dan suna dawowa daga rakkiyarsu Umm ta koma ɗaki, shiko shi da baba malam wani wajen hutawa suka zauna a cikin hotel ɗin suka shiga hira mai daɗi tamkar ɗa da uba. Dan idan ka gansu bazaka taɓa ɗaukar ba shine ya haifesaba. Yoohan yana bala'in sakin jiki da baba malam fiyema da papa da ke amsa sunan mahaifi a garesa.

         A haka Rich daya tashi a barci yazo ya samesu shima. Da farko ya zaunane kawai dan yanajin zafin baba malam da kuma son fahimtar ta wace hanya suka dilmiyar masa da ɗan uwa ya fara salla. Sai dai hirar batai nisaba Rich ya farajin nutsuwa da baba malam ɗin. Harma yake jin hirar na masa daɗi da basa wani irin farin ciki.

       Baba Malam kam tsaf ya fahimci Rich najin zafinsu tun isowarsu ƙasar. Sai dai baisan akan wane daliliba. Amma kasancewarsa mutum mai zurfin ilimi da hikima sai ya dinga mu'amulantar Richard ɗin cike da kulawa. Har i zuwa yanzun da suke zaune a tare. 

       Yoohan duk yana lura da yanda Rich ya fara sakin jiki da baba malam saɓanin farkon zamansa a wajen. Murmushi kawai yakeyi a cikin ransa, yana mai roƙon UBANGIJI ALLAH yasa abokin nasa nada rabon shiriya shima kamar yanda ALLAH ya cidashi ya tsamosa da ga DUHU zuwa HASKE.

        Sunja lokaci mai tsayi suna hirar kafin su koma ɗakunansu. Shi dai Yoohan shiri yay ya tafi asibitin dan akwai abinda zaiyi. Kuma lokacin gogema Nu'aymah jikima yayi


____________★


            Alhmdllh, yau kwanaki biyar kenan da yima Nu'aymah aiki. Sai dai zamuce har yanzun ba sanin inda kanta yake tai ba. Dan kullum a cikin barci take. A bisa ilimin likitanci ake bata taci ake bata ta sha ta allurai da sauransu.

       A komai Yoohan ne ke tsaye a kanta. Dan duk abinda ya dace shine kema matarsa da a kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin tausayinta da tsantsar kulawar da yake bata akan fuskarsa. A yau ne ake shirin barinta ta dawo hayyacinta gaba ɗaya. Dan haka tun sha biyu na daren jiya babu wata allura da aka ƙara mata. Duk wata na'ura dake tare da jikinta kuma an janyeta.............✍


*_Hummm. Ashe haka kuke da tsoron mutuwa dama? Tofa inhar a ranku kunajin jaruman littafi bai kamata su mutuba sai ku daina ƙalubalantar marubuta nasaka rayuwar littafii daya wuce kima. Idan kuma har kun shirya karɓar littafi dai-dai da zahirin rayuwa dolene ku shirya amsar ƙaddarar cikinsa itama dai-dai da zahirin rayuwa. Mutuwa dolece akan kowanne bawa. Dan haka jiya na tunatar da ku muhimmancinta dan shima littafin bazai zama kullum farinciki ba. inhar mutuwar jarumar littafi zata iya ɗaga hankalinku irin haka harda masu iya buɗe baki su zageni bayan sunama karantawa ne basu biyaba😂, to lallai ku ji tsoron zuwan mala'ikan mutuwa mai ɗaukar rai a zahiri ranar da babu tsumi babu dabara, sannan kuji tsoron cin haƙƙin abinda koda ɗaukarsa kuke ba komaiba. Muguji son ziciya dan ƙarshe ɓacin zuciya take zamarwa mai ita. Kai da karantawa kake kaji zafi a ranka dan an rubuta saɓanin abinda bashi kaso ganiba harka furta ALLAH ya isa. Mu kuma da muka ɓata awanni muna rubutawa kika fitarmana, ke kuma kika gani kika karanta da yaƙinin kin samu bati, bayan mun haɗaku da Girman ALLAH mi kake tunani koda bamuce da ku komai ba?. Kunbi kun ruɗar da kanku koma fahimtar bayanin nawa bayi kukaiba😸, nace karku sare, kar kuma ku saka rai, amma shine harda masu rusar kuka😂, da masu kirana suna kuka🤣, kai jama'a gaskiya jiya kun sani dariya kun kuma sakani hawaye saboda tausayin kammu, saboda tunawa da muma mutuwar nan tana tafe a garemu duk daren daɗewa, sannan wasu a cikinmu ma an zare mana mutane masu muhimmanci a rayuwarmu a yau babusu tare damu😭😭. ALLAH ka gafarta mana baki ɗaya. Wannan itace makarantar JIKI MAGAYI bisa gaskiyar zancen Nu'aymah_*😭🙏🏻.


No comments

Powered by Blogger.