Saran boye 52


  No. 52


............Motar tayi shiru, bakajin komai saina fitar sassanyan ac da sautin karatun al-qur'ani daya saka can ƙasa. A hankali yake tuƙin kamar baya so. Fuskar nan babu ko alamun yasan minene ma murmushi. Duk da Aymah tasan shiɗin ba mutum bane mai

fara'a aɗan zaman da sukayi, sai duk tajita a takure da yanda yay matuƙar tsuke fuskar.

       Sake lafewa tai abinta cikin kujera ƙamshin motar da sanyin ac na kuma saka mata kasala. A zahiri zakace idanunta a rufe suke, sai dai sam ba haka bane. Ta ƙasan ido take ƙare masa kallo daki-daki kamanin balarabiyar nan ta hoto na sake bayyana tattare da shi. A ranta kuwa rayawa take, ‘Dolene kayi ƙyau, ashe kanada alaƙa da larabawa. Ga papan ma duk da kasancewarsa ɗan African, Africa ɗin ma Najeriya, Najeriyarma kudanci shiɗin ƙyaƙyƙyawa ne tabbas’.

      Yoohan dake ji a jikinsa kallonsa akeyi ya ɗan juyo ya kalleta. Duk da idanunta a rufe suke ya fahimci ba barci take ba. Dan inba ita ɗinba babu wanda zai kallesa tunda a mota suke, motarma mai tinted glass. Baice komaiba ya cigaba da tuƙinsa kamar baya son suje inda zasu ɗin. 

          Sun isa haɗaɗen shagon sayayyar da Abujawan da kansu keji da shi, (bazan faɗi suna ba, danni na dainama masu shaguna talla yanzun🙄, duk maison a ringa saka sunan shagonsa a littafi yazo ya biya kuɗi koda baturene😎😏). 

            Sai da ya gama dai-daita fakin ya buɗe motar zai fita sannan Nu'aymah ta buɗe idanu. Batasan wannan cinkushe fuskar dan haka cikin neman tsokanar data iya tai saurin faɗin, “Ni dai gaskiya bazan shiga da kaiba wani yazata kidnapping ma'aikatan mukazoyi”.

        Jin abinda ta faɗa ɗinne ya hanashi zura ɗayar ƙafar da yay niyya dan har ya sauke ɗaya a ƙasa. Juyowa yay yana kallonta. Ta cika kumatu da iska tana tura baki. “Yoni ka daina kallona da waɗan nan idanun iya gaskiyata na faɗa. tayaya dan ALLAH zan bika, kaga fuskarka kuwa? Yasin kamar ta shekau na dajin sambisa. Dan haka yi gaba zan biyoka a baya”.

      Duk yanda yaso daurewa ya gaza, ya kauda kansa gefe murmushi na suɓuce masa. A ransa yana jinjina rashin jin yarinyar nan da rashin tsoro. A fili kam sai ya ƙarasa fita  yana faɗin, “Silly girl sakko, kafin in jehoki ƙasa”. 

         Baki ta murguɗa tana buɗe ƙofar ta fito. Cikin ƙunƙuni tace, “Kaima dai nakusa fara kiranka Silly boy ɗin nan daka ishi mutan da shi”. Ta ƙare maganar tana ƙarasawa inda yake tsaye yana gyara p-cap ɗin da a yanzu itadai ta gansa da ita. Dan da suka fito kansa babu hula. Kallonsa tai ta ɗauke kanta, a ranta kuwa tana yaba yanda p-cap ke masa ƙyau idan ya sanya. Musamman a yanzu da komai na jikinsa ya kasance baƙi, hularce kawai fara. 

        “Malama kallon da kikemin ya isheni”. Taji maganarsa a bazata. Sai dai yayi gaba kamar bashine ya faɗa ba. Murya taɗan ɗaga kaɗan yanda zai jita tace, “Kai da wane idon kasan ina kallonka?”.

         Tsayawa yay tare da juyowa gaba ɗayansa. Ita kuma ta riga da tazo gab da shi sai tai ƙoƙarin yin baya ganin zasuyi karo. Tako tafi gaba ɗayanta zatasha ƙasa. Da sauri ya bita ya tallafo ƙugunta ta dawo jikinsa. A yanda ƙirjinta ke bugawa ya tabbatar masa taji tsoron faɗuwar sosai. Samun kansa yay dajin dariya na taho masa. Ya ɗanyi kamar zai saketa, tai wani uban tsalle ta mamuƙesa zata saki ihu yay azamar danne bakin da ɗayan hannunsa yana kallon yanda tsirarun mutane dake shiga da fita cikin wajen suna kallonsu. Wasu na dariya wasu na gulma.

      Idanunsa ya rumtse da sauri yana faɗin, “Shikenan kin tara mana mutane hankalinki ya kwant...” Ai baima kai ƙarsheba ta fincike jikinta tana turesa. Sai kuma tai saurin komawa bayansa ta ɓuya ganin da gaske kallon nasu akeyi. Gaba ɗaya kunya ta dabaibayeta kamar ta nutse ƙasa takeji.

        “ALLAH ne ya rama min”. Ya juya da wani salo yana yin manar a cikin kunnenta kamar bashi ya faɗa ɗin ba. Da sauri tabi bayansa tana tura baki gaba. Sai dai da alama bakin tsuwar ya mutu kam. 

       Kamar yanda ƙa'idar shiga wajen take sai da akai bincikesu sannan suka shiga, sai dai yanzu kam a jere suke tafiya gwanin sha'awa. Batare da ya kalleta ba yace, “Mizaki saya?”.

     “Duka shagon”. Ta bashi amsa itama batare data kallesa ba.

      Shima da yake ya iya baƙar maganar sai cewa yay, “Okay sai muje a saidama Shekau ɗin da kikace Kano muzo musai shagon da kuɗin”. 

       Babu shiri taja birki harda riƙe ƙugu. Shima tsayawar yay ya tura duka hannayensa cikin aljihun yana kallonta fuska a ciskule. “Ai wlhy sai dai a saida garinku, dan kano tafi ƙarfin shekau”.   

       “Trouble maker”. 

Ya faɗa yanayin gaba. Bayansa tabi tana ƙunƙuni, sai dai bajin abinda take faɗan akeba. A haka suka shiga wajen kayan ƙwalam da maƙulashe. Irin kalolin biscuits da kayan ƙwaɗayin dataga ya tara a gida yaketa ɗiba yanzun ma, hakan yasa ta dinga binsa da kallo kawai tana gulmarsa a cikin zuciya, (wai maƙwaɗaici ne🤣).

       Sai da ya kusan cika keken sannan ya kalleta. “Kifa ɗeba naki, dan ba ƙara cimin nawa zakiyi ba yarinya”. Idan ba ita datasan shine yayi maganarba babu yanda za'ai ace shi yayita. Dan ya ɗauke kansa ya cigaba da harkar gabansa.

       Leɓe Aymah ta ciza, a ranta take raya ‘zakaga mugunta kuwa yau ɗan balarabe’ komawa baya tayi itama ta jawo nata keken. Ta shiga lodar chocolates da kayan ciye-ciye iri-iri. Wanima ko saninsa batayiba balle tasan zaiyi daɗi ko bazaiyiba. Saida ta cika kwandon nan dam da kayan ƙwaɗayi kawai har tana turawa da ƙyar tsabar mugunta. Tana a layin ƙarshe zata ɗauki wani roban chewing gum taji ƙamshin turaren da ya sakata waige-waige da sauri. Cikin kwandon ta jefa chewing gum ɗin tai saurin fitowa a lungun tana leƙe. Babu ko mai alamarsa, sai dai tabbas wannan ƙamshin shi kaɗai ta sani da shi. Duk da zuciyarta na ayyana mata wanine bashi ba ta kasa aminta. Sai ƙara kutsa kai take kowanne layi dan dubashi. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta yayi jin an riƙo mata hannu. Ta waigo da sauri sai taga Yoohan ne. 

       “Miye kike nema haka?”.

   Yay maganar babu wasa a fuskarsa. Sannan muryarsa a kausashe kamar wanda yake cikin fushin da ɓacin rai. Kanta ta girgiza masa tana ƙoƙarin maida ƙwallar da suka cika mata ido. Bai sake cemata komaiba yaja hannun nata suka bar wajen. Duk da taga bai maidata wajen kayanta data bariba, ba tai magana ba. A mamakinta saita hangi kayan can wajen bada kuɗi ana loda musu a ledoji. Suna isowa matar fuskarta faɗaɗe da murmushi tace, “Doctor ATM”. Zarowa yay a wallet ya miƙa mata batare da yace komaiba. Ta amsa idanunta akan Nu'aymah dake sake waige-waigen ko zata gansa anan. 

      “Amaryar Doctor Good evening ”. Maganar matar ta maidota hankalinta. A taƙaice ta amsa mata duk da ta fahimci akwai sanayya tsakaninta da Yoohan ɗin. Ta ɗan dubesa lokacin da ma'aikatan wajen ke kwashe ledojin zasu kai masu mota. Har yanzun fuskarsa babu sauƙi. Gashi ya wani riƙe mata hannu gam kamar za'a saceta. ATM ɗin ya amsa yaja hannunta suka fita.

           A can wajen motar da sukazo taga anata loda kaya harma da wanda bataga sanda aka sayaba ita dai. Batayi magana ba dan bataga fuskaba. Saima buɗe mata murfin yayi yay mata alamar ta shiga. Tana shiga ya maida ƙofar ya rufe mata. Ta mazauninsa ya zagaya, taga ya buɗe lokar motar ya ciri kuɗi ya maida ya rufe. Batasan waya bamawa ba, sai dai bai jimaba ya dawo suka fice a wajen.

      A lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Gudu yake yanzu sosai, kai tsaye anguwar su Abban Abdallah ya nufa. Daɗi ya kama Aymah sai dai ta haɗiye abinta a ciki har suka isa. Anata hada-hadar shiga sallar magriba a massallacin ƙofar gidan. Horn ɗaya kuwa yayi maigadi dake ƙoƙarin fitowa zaije salla yay murmushi yana komawa ya buɗe musu. Shiga Yoohan yay da motar har ciki yay fakin Aymah nata mamakin ƙarfin halinsa.

      “Kije ciki zanje nai salla”. Yay maganar yana buɗe motar ya fita. Ai tuni ma ta rigashi fitar. Sai hangota yay ta tsilla da gudu hanyar shiga cikin gidan. Da kallo kawai ya bita harta buɗe ƙofar falon ta shige. 

      Ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe yana nufar hanyar fita gate ɗin da hanzari jin za'a tada salla.


       Da uban ihu Nu'aymah ta shiga tana ƙwalama su Amal kira. Aiko kamar jira suma sai gasu da gudun sun fitowa suna ihun murnar ganinta. Momy na salla take jiyo ihun nasu. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka sarara. Ɗakin Amal ɗin suka nufa inda Yusrah da Adawiya dataƙi fitowa suke hutunsu da basusan dalilinsa ba balle ranar komawa kano.

         Duk da idon Aymah ya ga Adawiya dake kwance a kan gado tana danna waya sai tai tamkar bata ganta ba ta cigaba da biyema su Yusrah dake mata sherin wai ta canja saboda daɗin aure ko sun sami baby ne?. Shaƙiyanci sukaitama juna suna sheƙa dariyar dake sake ƙullar da Adawiya. Dan suma su Amal ɗin ta ishesu. Kullum haka take yini a gidan cikin ɗacin rai, bata shiga sabgarsu basa shiga tata. Momy tayi faɗan harta gaji ta zuba musu idanu. 

           Sallar suma sukayi, kafin su idar Adawiya tabar ɗakin ta koma falo. Bayan sun idar cikin dabara Aymah take tambayarsu Amal yaushe Yusrah zata tare tunda taga Yah Ab bai koma ba. Da mamaki sosai Amal tace, “Yah Ab ɗin da ya koma Saudia tun randa aka ɗaura miki aure. Kuma Yusrah ai tace bazata tare a gidansa ba saboda fitinar Adawiya”.

          Bayanin Amal ya matuƙar ɗaure kan Aymah, dan ita dai tabbas-tabbas tanaji a ranta da Yah Ab sukai gamo a inda suka baro. Sai dai batasan dalilinsa na ɓoye mata kansa ba. Danne wannan tunanin tayi a zuciyarta ta fuskanci Yusrah datai kamar bataji mi suke magana a kai ba. 

         “Yusrah! Miyasa baƙya son zama da Yah Ab wai dan ALLAH?”.

       Murmushi Yusrah tayi tana ƙoƙarin miƙewa daga wajen gaba ɗaya, Aymah tai saurin maidata ta zauna. “ALLAH babu inda zakije sai kin amsamin tambaya ta”. 

        “Humm Aymah kenan, ba amsa tambayarki bace mai wahala, hujjar amsata. Ni bancema kowa bana son Yah Ab ba ai. Kawai dai zaman aurene banason yi da shi. Fatan da nakeson muyi ni da ku kawai shine ya maida Adawiya ɗakinta. Indan ba hakaba kuwa tsugunne bata ƙareba a family ɗinmu wlhy. Adawiya na son Yah Ab sosai duk da nasan tabbas Nu'aymah kin fita sonsa. Amma ke yanzun wannan babin ya shafe a gareki dan dama ƙaddarace tazo muku da wannan yanayin”.

          “Amma Yusrah.…..”

“No Aymah karki sake cewa komai dan ALLAH. Mu ajiye wannan maganar haka kawai. Ku tashima muje dan ga kamar momy can ta fito”.

      Badan Nu'aymah taso ba tai shiru. 


  A falo kam zaman Adawiya babu jimawa Abba da Yoohan suka shigo falon Omar biye da su. Ɗago kanta tayi da nufin yima Abba sannu idanunta ya sauka akan Yoohan da shi koma kallon inda take baiyi ba. Ganin har zasu wuce batai magana ba Abbah yace, “Adawiya baki iya gaisuwa ba ne? Ko bakiga mijin ƴar uwarkiba Nu'aymah?”.

       Da gaske gaban Adawiya sai da ya faɗi. Bakinta na rawa ta gaida Yoohan. Sau ɗaya ya amsa tare da mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Binsa da kallo kuwa ta cigaba da yi harya shige falon Abbah. 

       A fili tace, ‘Dama Aymah ba ƙabila akace ta aura ba? Naga kuma balarabe?’. Bata da mai bata wannan amsar dan haka tai shiru tana saƙe-saƙenta a cikin zuciya har Momy ta fito tana tambayarta ihun mi takeji ɗazun. Tana cikin sanar ma Momyn ne su Aymah suka fito. Zuwa Nu'aymah tai ta rungume Momy cike da murna.

       Momy dake dariya tace, “Ja'ira, an girma ba'asan an girma ba”.

         Dariya ta sakeyi su Amal na taya ta. Adawiya dai tai muƙuy kamar bata falon abin duniya ya gama isarta a rai game da ganin mijin Nu'aymah..

          Tura Amal momy tayi ta kira Uwaliya mai aikin da aka kawoma Nu'aymah daga kano. Ashe dama ita suka biyo ɗauka batare da Yoohan ya sanar mata ba. Ba wata tsohuwa bace ba. Zata iya kai kimanin shekaru talatin da bakwai dai. Sun gaisa da Nu'aymah momy tai musu bayanin juna. Har cikin zuciya Aymah taji son zama da Uwaliya kuwa. Dan haka cikin jin daɗi ta miƙe domin zuwa falon Abbah ta gaidashi shima.


          Basu bar gidanba sai goma saura. Sun tafi da Uwaliya. Su Amal ma sun mata alƙawarin zuwa next week dan dama Abbah ne ya hanasu wai karsuje su tada mata hankali. Amma yanzu daya ganta babu wata damuwa yace zai barsu suje ɗin amma sai weekend insha ALLAH.

          Papa kawai suka samu a harabar gidan zaune. Sai su Solomon da suma ke tasu hirar acan gehe. Ita dai tana gaida papan ciki suka wuce da Uwaliya. Shi kuma ya nufi inda papan yake zaune.

         Basu sami kowa a falon ba. Gidan ma shiru alamar duk sun kwanta. Ta fahimci ɗabi'arsu ce barcin wuri, musamman ma yaran saboda makaranta. Da kuma su ɗin kansu daya kasance duk suna fita aiki da safe. Uwaliya nata kalle-kalle ita dai har suka ƙarasa sashensu. Sarai Aymah taga Momy acan ƙofar sashenta zaune. Amma sai tai kamar bata ganta ba suka shige abinsu.

        A falo suka yada zango. Kusan zaman mintuna ashirin sai gashi ya shigo tare da su Solomon da suka kwaso kayan. Anan tsakkiyar falon duk suka zube komai suka fita suna musu sai da safe.

      Batare da Yoohan ya zauna ba ya dubi Aymah yana faɗin, “Ki kaita ɗakin kusa da sashen nan anan zata zauna”. Kamar Aymah zatai magana sai kuma tai shiru ganin ya juya abinsa ya nufi hanyar ɗakinsa. Ta fahimci har yanzu ransa a ɓace yake dai, kamarma an sake tunzurashi ne yanzu da suka shigo. Tashi tai ta raka Uwaliya ɗin, ɗakine babba da katifa a ciki da kwabbot na kaya da toilet ɗinsa kamar kowane ɗaki. Hakan yasa hankali Aymah kwanciya. Itama Uwaliya sai faman washe haƙora takeyi ganin ita da aka kawo tai aiki amma irin wannan aljannar duniya haka.


_________★★★★_________


              Washe gari da yamma tana ɗakinta bisa gado ta baje littatafan ta na islamiyya tana dubawa ya shigo. Batare data ɗago ba ta amsa masa sallamar da yayi. Sai da ya zauna a bakin gadon tare da ɗaukar littafin gabanta na SAHIH AL-BUKHARI da take dubawa sannan ta ɗago. 

      Idanu ta ɗan zaro tana kallon abinda ya ke ci. Ta tsuke fuska iya gaskiyarta tana faɗin, “Tab wannan ai chocolate ɗina ce, naga kaine kace kowa yaci abinda ya sayo ai ɗazun da safe ko?”.

          “Oh ashe babu daɗi hajjaju, ni da kika tasamin biscuits a gaba kika cinye banyi maganaba, sai ni danna sha wannan chocolate ɗin da ko wani daɗi babu”.

       Ture buks ɗin tai gefe ta miƙa hannu zata warce a hannunsa. “Tunda babu daɗi bani abuta”.

        Hannun ya riƙe yana wani kafeta da narkakkun idanunsa. Yayinda yake ɗan motsa bakinsa a hankali yana cinye wadda ya gutsira. Ƙara matsowa tai tasa ɗayan hannun zata warce again, dai-dai zai kai bakinsa.

      Fisgota yay gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa. Yay baya shima suka faɗa saman gadon. Zabura tai tana faɗin, “Malam kana shigarmin hanci da yawa wl......”

        Bai bari ta ƙarasa ba ya juyata ta koma ƙasa shi ya koma sama. Sai dai rabin jikinsa ne a kanta, a hakanma bai sakar mata nauyinsa ba dan a ganinsa bazata iya ɗauka ba. Amma tsabar ragwantaka na Aymah sai ta wage baki zata masa ihu. Hannu yay saurin ɗorawa akan bakin nata yana ɗan waro idanunsa waje. “Idan kikai ihun nan na ratse sai na haɗiye bakin kinnan yanzun nan”. 

         Hannu tasa ta ture nasa hannun tana faɗin, “Tunda kai maye ne basai ka haɗiye ba mugani”. 

       “Kema zaki koma mayyar ai”

Yay maganar yana saka idanunsa cikin nata yanda ta kasa magana ta kuma kasa janye nata idanun saboda tsabar yanda ya sarƙeta da nashi.

        Cikin wata irin kasalalliyar murya yace, “In sammiki chocolate ɗin?”.

       Duk yanda taso buɗe baki tayi magana ta kasa. Dan yanda yay maganar gab da fuskarta, ga idanunsa cikin nata sai taji kamar ya mata wani ɗaurine da igiyoyi. 

          Chocolate ɗin ya kai bakinsa ya sake gutsira kaɗan, har yanzu idanunsa na a cikin nata bai janye ba. Ya sake matsar da bakinsa gab da nata. A hankali cikin maganar raɗa yace, “Buɗe bakin”.

       Kamar wadda ake juyawa da remote Aymah ta motsa laɓɓanta kaɗan idanunta dake cikin nasa na cikowa da ƙwalla. Bata ankara ba taji laɓɓansa akan nata, a tare suka lumshe idanu, sai dai ita wasu hawaye da batasan na minene ba suka shiga silalo mata saman kumatu da gudu. Yayin shi kuwa Yoohan yake juye mata narkakkiyar chocolate ɗin daya narkar da yawunsa......


    (Kai zafafa fans wannan bada cakuleti na Yoohan yafi ƙarfina, bara naɗan fita na barsu su sarara😱. Amma zan leƙa muku ta kafar mukkuli🏃).


         Gaba ɗaya Nu'aymah ta kasa fahimtar kanta balle abinda Yoohan yake mata. Shi kansa da yake aikatawar yayi masifar shafa'a da wadda yake tare. Sai da labari ya nema canja salone ƙwaƙwalwarsa ta fara aikin masu hankali. Da ƙyar ya iya janyewa daga jikinta ya koma gefenta ya kwanta rufda ciki. itama saurin juyawa tayi ta koma can gefe taja bargo ta ƙudundune jikinta na wata irin karkarwa.

         Sunja tsahon mintuna goma a hakan kafin Yoohan ya buɗe idanunsa dake a rufe da ƙyar. Ya cija lip ɗinsa na sama tare da sake lumshe idanu ya sake kuma buɗewa akan Aymah dake a cikin bargo har yanzun. Tsaf yanayin ya shiga dawo masa a cikin kai. Duk da cikinsa daya ƙulle hakan bai hanashi tashi zauneba da sauri jin ajiyar zuciyar da Nu'aymah ke saukewa. Ya matsa inda take tare da jan bargon data kudundune a ciki har kanta.

     Cikin muryar da bata taɓa saninsa da itaba yashiga kiran “Zeeynab! Zeeynab!”.

        “Hasbunallah” tai saurin ambata akan laɓɓanta jin zuciyarta na neman faso ƙirjinta ta fito waje. duk da ba yaune karan farko da aka kirata da wannan sunanba sai taji tamkar na yau ɗin ya banbanta dana kullum. musamman daya faɗa a saitin kunnenta kuma cikin wata irin shu'umar murya. Gashi da wani irin style ɗin daya banbanta da harshen duk masu kiranta da sunan saboda hausa bata ishi nasa harshen ba.

          Ganin duk yanda yaso yaga fuskarta ma taƙi yarda ya sakashi ƙyaleta, dan cikinsa ya ƙulle matuƙa. Idan kuma ya cigaba da zama a ɗakin za'a samu matsala. Da ƙyar yace, “Okay na fita”.

        Duk da tana jinsa batako motsaba. Amma muryarsa ta sakata jin tsoro. Dagaji kasan baya cikin ƙoshin lafiya. Ƙarar rufe ƙofa kawai taji, daga haka bata sake jinsaba sai da daddare wajen sha ɗaya saura ya shigo lokacin tana ƙoƙarin hawa gado ta kwanta.

          Tanajin ƙamshin turarensa tai saurin ƙoƙarin jan bargo zata lulluɓa. Sai dai tayi rashin sa'a dan harya rigada ya shigo. Ta bashi dariya amma sai ya gimtse. Bakin gadon ya ƙarasa saitin inda ta saka fuskarta. Ya ajiye ledar hannunsa yana faɗin, “Ga wayarki nan, da sassafe zan wuce UK. Please banda jan faɗa wa kowa”.

         Duk da tana jinsa bata motsaba. Sai dai tana kallonsa ta cikin ƴar ƙofar data bari kaɗan kasancewar bata kashe wutar ɗaki dama ita. Daga haka bai sake cewa komaiba ya juya ya fita. Da kallo ta bisa tana mamakin yanda duk yay wani laushi duk da fuskar a matuƙar tamke take ma fiye da yanda ta sani.

      Tanajin ya fita ta yaye bargon da sauri. Mikewa tai tsaye a saman gadon ta dirgo ƙasa. Ta nufi ƙofar da gudu ta murza key kamar ance mata zai dawo. Sai da ta tabbatar tayi gam sannan ta dawo wajen wayar da yace. Ledar ta buɗe cike da doki, sai ko ga waya mai azabar ƙyau ta kamfanin Apple ta bayyana ƴar yayi. ai batamasan ta dirga wani uban tsalle da ihu ba ta ɗane gadon. Sai kuma ta miƙe ta hau rawa duk a saman gadon harda kwaso shoki ta manna a ido duk tana kallon kanta ta mirrorn ɗakin dake kallon gadon.

       Sosai Aymah tasha rawarta da ihun daɗi akan wannan waya kafin ta zauna ta fara dubawa. Komai na cikin wayar yana akwalin dan sabuwace fil. Sai dai a mamakinta anyi caji full, sai dai sim card guda biyu duk suna jikin ƙashinsu bai ɓalleba. Ta ɗauki ƴar guntuwar takardar dake ciki ta karanta abinda ya rubuta.

         _Ki shirya Gebrail zai kaiki kiyi register ɗin layukan duk sanda kike buƙata. Zanyi kwanaki goma ne ko sati biyu. Please banda tsokana, dan an tabbatar min kece kika karyama Miracle ƙafa ranar._

        Da sauri ta zaro idanu waje tana faɗin, ‘La'ila wane shugaban ƴan sherin ne ya faɗa masa? Tab ashe gidan bayan masu shegen kallo da rawan kai akwai magulmata ma. Indai suna son karna shiga harkarsu nima karsu shiga tawa. inko ba hakaba na rantse da gemun baba malam nata karya ɗiyan jama'a a gidannan ana kaima likitoci ɗorinsu’.

     Daga haka ta murguɗa baki tana miƙewa taje ta kashe wutar ɗakin ta dawo ta kwanta tana ƙanƙame wayar a hannunta. Tace, ‘Tab, ai wlhy dake zanyi barci ko sauron ɗakin nan sai dai yayi shawagi a bayan hannuna ya wuce’.

       Da wannan shiriritar tai addu'a tai barci...............✍

No comments

Powered by Blogger.