Saran Boye 46-50


 46




         Saida komai ya kammala azeez yana tare da mai martaba,abinda ya rage kawai ya wuce zuwa ciki inda akewa manyan mutane irinsa nasu screening din,idanuwan azeez na biye dashi sanda yake wucewar,duk da ranshi a cushe yake amma hakan bai hanashi jin qaunar mahaifin nasa ba,tare da ayyana abubuwa da dama tattare dashi.



       Wani irin mutum adali,wanda bai dauki duniya da zafi ba,inda shine ke riqe da ragamar rayuwarshi,yake kuma bibiye da al'amuransa sabanin ammi abinda ya faru dashi zaya farun?,ya jefawa kanshi tambayar da baya da amsarta,saiya kada kai,abinda ya sani kawai shine,qaunarshi ta rufewa ammi idanu,har take ganin duk abinda takeyi saboda shine,kuma bisa dai dai take,amma sai yaushe ne al'amura zasu gyaru?.



       Ajiyar zuciya ya sauke yana shirin dauke idanunsa daga inda maimartaba ya wuce wanda tuni ya bacewa ganinsa.



      Karaf idanuwansa suka sauka a kanta,cikin kaduwa mamaki da bazata ya qanqantar da idanun nasa yana son tabbatar da gaskiyar abinda suka gano mishi,naci ya sanya sosai tare da sake matsawa kadan daga inda yake tsaye don kuma tabbatar da zarginsa.



       Itace a tsaye ana duba passport dinta,sanye cikin doguwar riga saqar qasat dubai mai matuqar kyau da daukar idanu,duk da yalwar rigar amma hakan bazai hanaka hango cikinta daya bullo ta cikin rigar ba,yakuma zauna sosai bisa jikinta,idanunta itama nakan passport din kamar yadda idanun me dubawar yake,bai ankara ba yaga ya miqa mata passport din da dukka sauran kayanta wanda hakan ke nufin xata wuce kenan,zata wuce ciki inda babu lallai ya ganta,idan ta wuce ina take shirin tafiya?,wacce qasa zata?,bai sani ba,amsar daya baiwa kansa kenan,amsar data sanyashi zabura cikin matuqar zafin nama da karsashi ya durfafi wajen,duk bashi da tabbacin cimmata kafin yakai wajen saboda 'yar tazara da dan cunkuson jama'a dake wajen.



       Kamar wanda ya fice a hayyacinsa haka ya dinga kutsa jama'a yana neman hanya,wanda hakan ya ja hankalin mutane da dama suka dinga binshi da kallo,wasu da yawa daga cikinsu sunsan wayeshi,sunsan matsayinsa,hakan ya sa ya suka dinga mamakin abinda yakeyi din,saidai shi sam ba wannan bace damuwarshi,damuwarshi ya samota kafin ta bace,damuwarsa ya cimmata,damuwarsa ya ganta a gabanshi,damuwarsa suyi magana,damuwarsa cikinsa dake jikinta,ya tabbata cewa yayi dashe kenan a tattare da ita.



        Saidai ko kodan burinsa bai cika ba,domin yana ganota sanda aka bata boarding pass ta bace masa kamar yadda mai martaba ya wucewa ganinsa,duk da hakan bai fasa niyyarsa ba,har yaso tsallake shingen da aka sanya,wanda hakan yaja hankalin jami'an tsaro cikin mamakin ko babu lafiya suka taso suka dakatar dashi suna tambaya,wanda tambayar ya dinga jinta kamar wani qarin bacin lokacin da datsewar burinsa ne,ya dinga fidda numfashi mai zafi yana son su matsa mishi yakai gareta.



   

       Hannunsa da daya daga cikin manyan hadiman mai martaba ya riqe shiya sanyashi maida hankalinsa jikinsa,ya waiwaya ya dubeshi cikin girmamawa da rusunawa yace,murya qasa qasa ta yadda shi daya zaiji

"Allah ya taimakeka dukka idanuwa suna akanka,ko meye kayi qoqarin daidaita yanayinka,saboda girma da qimar masarautar kaisa,da kuma gudun bacin rai fulani" wannan maganar ta sanyashi sauke nannauyar ajiyar zuciya wadda yakejin kamar anyi ajiyar dutse ne a qirjinsa,yanajin tamkar ya bangaje duk wanda ke tsaye a gabanshi ya ganshi ya cimmata,babban burinsa kenan,bai damu da dukkan wanda zai kalleshi ba,amma maganar data fito daga wane sashe na zuciyarsa ta sanya bai aikata hakan ba

"Ganinta anan din tamkar wata nasara ce a gareka,kuma haske ne da zai kaika ga inda zaka cimmata", da wannan kalaman jami'an suka samu suka tafi dashi xuwa wani kebantaccen daki,suka soma bashi kukawa ta musamman kafin su nemi jin damuwarsa.



        Sam bai damu da ababen sanyin da aka ajjiye masa ba cikin katafaren office din,gaba daya hankalinsa ya karkata ne kan wanda ke binciken list na sunayen passingers din da suka tashi yanzun bada dadewa ba,wanda dama duka duka a yau din jirgi biyu ne kacal ya tashi,biyu ya sauka,ji yake kamar ya finciki na'urar zuwa gabanshi,gani yake kamar baya sauri,haka ya dinga dunqule hannunshi waje daya yana tausar kanshi da gayawa kanshi ya nutsu,yabi komai a hankali.



      Tsahon wasu mintuna da suka biyo baya kafin mutumin ya dago daga allon na'urar,ya zauna sosai yana duban yarima azeez da kuma shugabansa dake zaune gefe shima,a ladabce yace

"Cikin jirgi na biyu daya tashi yanzun tabbas akwai mai suna bilkisu,kuma kusan ita kadai ce ma mai sunan....."

"Wacce qasa ya nufa?" Azeez yayi hanzarin tambayarshi ba tare daya barshi ya kammala jawabin nasa a karan kanshi ba,don ji yake dukka wani bayani da mutumin yake kamar bata lokaci ne,kamar bashi da amfani.



      Ganin yadda yanayinsa yake a qagauce yasa shima ya bashi amsar tambayarsa kai tsaye

"Ethopia"

"Ethopia?" Ya samu kanshi da tambayar kansa da kansa,idan yace zai tsananta tunanin abinda zataje yi can din tabbas ya yaudari kansa ne,bai gama sanin wacece ita din ba totally balle yace yasan wani abu daya shafeta,wanda zai bashi hasken tana da alaqa da canne ko 'yar can ce,abu guda daya ne da yakejin zai zame masa mafita shine,ya yanki ticket yabi dukkan wani jirgi da aka samu zashi qasar daga yanzu zuwa kowanne lokaci

"Qasar ethopia nada girma da fadi,bawai qaramin gari bane qwaya daya da zakace kana sauka zakaga wanda ya santa koya hadu da ita ya nuna maka inda take,idan kaje ina zaka dosa?" Zuciyarsa ta antayo masa da duka wadan nan bayanan da rudu yasa yaso mancewa dasu,yanaji cikin zuciya da gangar jikinsa cewa zai iya qarar da dukka numfashinsa wajen nemanta koda baisan inda take ba,to amma hanya mafi sauqi da kwanyarsa ta yi masa hasashe shine,gidansu nan ne muhalli qwaya daya tak da xai samu sahihin inda zai sameta acan inda ta tafin ba tare da jinkiri ko bata lokaci ba,jinkirin da yakejin duk bayan shudewar wasu mintuna kamar yana shudewa ne da farincikinsa,walwalarsa da kuzarinsa,yanajin kamar bashi da dukkan wata jarumta da yasan kanshi da ita.



       Da wannan shawarar ya miqe,ya miqa godiyarsa garesu cikin qasaita ya soma barin office din,yana jin wannan karon koma meye zaya faru saidai ya faru,amma babu shakka zai nemo ladingo a duk inda take,zai kuma sanyata ta nuna mishi gidan mahaifan bilkisun,bayajin zai iya jurewa wannan asarar cikin rayuwarshi,idanuwansa sun gane mishi gaskiya da sahihancin abinda ammin ke kokwanto akai,me kuma yayi saura?,har cikin zuciyarsa yana jin wani feeling idan ya tuno fuskarta da cikinsa dake zaune a jikinta,yana jin wani irin yanayi mai nauyi da wuyar fassara idan ya tuna fuskar macen data taba masa sunan matarsa da kuma cikin dake amsa sunan dansa jininsa ne kwance a wajen.



       Tunda ya koma gida bai yadda ya hadu da kowa ba,tsarinshi duka shine inda za'a nemo ladingo duk inda ta shiga a masarautar kaisa,sam yama mance da batun bar mishi kula da qasar shida waziri mahaifin abdulrashid da me martaba yayi,don hankalinshi ba'a jikinsa yake ba.



       Kwana guda da wuni guda kafin a lalubo mishi itan cikin sirri da boyewa,baya son batun yakai kunnen ammi bare ta samu damar dakatar dashi,yana son kome zai faru ya faru bayan ya cimma gaci.



       Tunda masu tahowa da ita zuwa sashen nashi suka risketa gaba daya jikinta yayi sanyi qalau,gabanta ke dukan uku uku,tasan cewa kashinta ya bushe,kuma tata ta qare kenan,saboda bata manta da gargadi da kuma jan kunne da babbar murya da fulani tayi mata ba,bayan ta sauya mata sashe ta dauketa daga cikin gidan sarautar gaba daya,to amma matuqar yarima ke buqatar jin wani bayani daga bakinta tasani cewa akaran kanta bata da zatin da zata iya jaa da kwarjininsa,bare har ta musawa buqatunsa,da wannan tunanin suka iso cikin sassan azeez cikin duhun bayan isha'i,suka ajeta a inda ya buqaci ganawa da ita kafin ya fito,taci gaba da zaman jiranshi cikin fargaba da rudani,ko ina na jikinta rawa yake kamar kazar da aka tsoma cikin ruwan qanqara aka ciro.



        Takunshi kawai ya isa ya sanya dukkan wani dake wajen ji a jikinsa,a jininsa yake kuma halittarsa ce,tarin kwarjini da haiba wanda mutane da yawa kan camfa,wasu suce siya masa akayi,wasu suce akwai kalar dabbar da yake ci wanda hakan ke qara masa kwarjini kulli yaumin.



        Tun baiyi magana ba ta sake rusunawa sosai tana miqa gaisuwa cike da tsantsar ladabi,kanta a qasa bakinta yana rawa,bai amsa mata ba,saidai ya baiwa dukkan wani mahaluki dake wajen umarni da ido nasu basu waje,cikin qiftawa da bismillah wajen ya zamana daga shi sai ita,ya gyara tsaiwarshi sosai yana dubanta na wasu sakanni,sannan kai tsaye ya jefa mata tambayar data zama silar zuwanta wajen

"Idan kin amsa min babu qarya ko boye boye to ba shakka kin kubuta,ki cire dukkan tsoron wani daga zuciyarki ki bani amsar tambayoyina dai dai,wannan shine kawai mafita a rayuwarki"

"Allah ya taimakeka.....ya qara maka nisan kwana sarkin gobe.....ya qarawa mai martaba daraja da daukaka.....ya qarawa fulani lafiya.....ba shakka kome zaka buqata daga wajena....nidin me biyayya ce ga umarninka" kai ya jinjina yana sauke numfashi,cike da sarauta yace

"Kece mutum daya tak da kikasan gidansu....ina ne gidan mahaifanta?" Ko bai fito baro baro ba tasan wa yake nufi,zuwa yanzu tana jin kamar gudawa zata qwace mata,ko bai gargadeta bama ba zata iya musu dashi ko yi masa qarya ba,tasan cewa wutsiyar raqumi tayi matuqar yin nesa da qasa

"Tana nan unguwar hayin malam amadu Allah ya taimakeka" shuru yayi yana hasashen unguwar da sunanta,bazai iya tuna wacce unguwa bace,mutumin da baiyi cikakkiyar rayuwa cikin masarautarsa bama ina zai san wasu anguwanni cikin qasar tasu,saiya katsewa kansa wahal da tunaninsa da yakeyi yayi magana ta qarshe da ita yana mai takawa yana barin wajen

"Ki zama cikin shiri" iya abinda ya gaya mata kenan ya wuce zuwa ciki.



        Cikin dare saiya dinga ganin dare yayi masa mugun tsaho,tamkar gari ba zaya waye ba,kamar safiya ba zatayi ba,wani irin dare ne daya cika fal da mafarkinta da kuma tunaninta,uwa uba kuma tunanin cikin dake jikinta wanda yayi imanin babu tantama ko kokwanton cewa nashi ne.



       Baiyi barci ba sai daya kira abdulrashid ya shaida masa komai da kuma aniyarsa na zuwa gidan gobe da kanshi,gami da neman rakiyarsa

"Ko baka fadi ba yarima zuwa ya zama dole"

"Amma inaso mu tafi da mota daya zuwa biyu,itama idan da hali daga cikin motocin gidan mai girma waziri,banason ko kadan motar masarauta ta shiga wajen,don banson labari ya zowa ammi har sai na gama aiwatar da abinda na qudurta"

"Baka da damuwa man" ya amsa mishi cikin qarfafa gwiwa.



    *******   ****    ********



       Duk yadda ya dokanta da zuwan washegarin sai gashi tazo mishi a baibai,ta kuma zo mishi da sakamakon da yake gani shine mafi muni cikin kowanne sakamako da aka taba bashi a rayuwa.



         Ko cikin motar kallonshi kawai abdulrashid yakeyi,baisan da wanne harshe zai lallasheshi ba,dukkan wanda yasan azeez dakiya irin tashi,jarumta da taurin zuciya,zaiyi mamaki qwarai idan yaga yadda ya sauya lokaci daya,daga sadda jerin gwanon amsoshin suka shiga kunnuwansu

"Tabar qasar jiya ko shekaran jiya,babu kuma wanda ya sani ko yake da masaniyar inda taje ko zataje a can din". Amsoshin dashi kansa abudulrashid suka bashi mamaki,bare azeez daketa jujjuya maganganun cikin kwanyarsa.



        Ta yaya ɗa ba bawa ba za'ace ba'asan inda ya tafi ba?,shin bata da mahaifiya data damu da ita ne?,wanne irin mahaifi gareta da zai bar diyarshi tafiya zuwa wata qasa bashi da tabbacin muhallin da zata tsinci kanta?.



         Hannunsa dake dunqule tun daxun ya saka ya daki kujerar gabashi,yana jin wani zafi zugi da radadi na ratsa ilahirin jiki da zuciyarsa,amsoshin da aka bayar kamanceceniya suke da ana masa bushara da ya rabu da shukar daya dasa,shukar dake mallakinsa wani bangare na jikinsa,da ko yarsa zasu zama basusan wayeshi ba.



         Wasa wasa kafin sukai gida saiga wani irin zazzabi yana neman lullubeshi,tun abdulrashid na daukan abun wasa sai yaga da gaske ne,amma sam azeez din ya hana a shaidawa fulani,duk data aiko jin lafiyarsa saboda rashin ganin gilmawarsa wunin jiya dayau gaba daya,yace a shaida mata lafiya qalau yake,bata kawo komai a ranta ba,saita aza hakan da nauyin da maimartaba yabar musu ne na kula da qasa ya kawo hakan,ta saki murmishi tana jin dadi har cikin zuciyarta,tanajin cewa ko a yanzun babu ko tantama taci riba wajen maqiyanta.



             *_BILKISU_*



        Tun tana kuka saboda farincikin tarin dangi da gata da suke dashi ita da mahaifiyarta har hawayen suka daina zuba,sai.mamaki daya cika zuciyarta taf,ta sake yarda da cewa mahaifiyarta ta daban ce,hakanan zuciyarta mai tsarki ce,samun irinta cikin matan wannan zamanin abu ne mai matuqar wahala,ta yarda tabar dukkan wani daula jin dadi da arziqi na mahaifanta da danginta ta zauna da mahaifinta,mutumin da ko cikin ma'aikatan gidan akwai da yawa da suka fishi arziqi,amma sam bata duba wannan ba,ta martaba soyayya ta gaskiya,ta bata qima da daraja ta zauna dashi,to amma shin shidin ya biya ta?,ya saka mata da dukkan tarin alkhairinta da kara da yakanar data yi masa a rayuwa?.



         Tamkar xasu cinye bilkisu haka kowa ke haba haba da ita,ta sake yadda tabbas maimunatu ta musamman ce cikin danginta sanda taji anty zuhriyya tana qorafi

"Wato kunga makwafin maimunatu shine za'a koma 'yar gidan jiya,aci gaba da nunamin wariyar launin fata ko?,wannan karon kota ni ba'ayi,dadin abundai nidin dai nice na kawo muku ita" ta fada cikin tsokana da zolaya,wanda bilkisu ta lura tafi bada qarfin tsokanar tata ga jakakarsu,wadda ta haifi mahaifinsu,wanda ita daya tal ta rage musu,da alama kuma tare ta rayu dasu tun quruciya tasan quruciyar kowa a cikinsu

"To dama an gaya miki akwai abinda zai ture gwamnatin maimunatu ne a wajena duk da bata a duniya?,ai babushi" yanayin yadda tayi maganar xai gaya maka cewa,duk da tarin tsufanta amma hakan bai hana mutuwar maimunatu sukar zuciyarta ba,uwa uba mutuwar mahaifin maimunatun kanshi bisa dukkan alamu itama bata barta ba,duk sai jikin kowa yayi sanyi a wajen,don har abada ba zasu manta da mutuwar uba da diyarsa ba da suke ababen soyuwa a zukatanta.



       Duk yadda zata fadi kasancewarta cikin danginta a ethopia tasan baki yayi kadan ya bayyanashi,girma da tsadar lokuttan qauna kulawa da tattali ya sata ta manta duk wani qalubale data taba fuskanta,takan manta meya faru da ita a yawancin lokutta idan ba cikinta ta shafa ba,wanda yake yin wani irin girma naban mamaki,saidai hakan bai fiya damunta ba,saboda lafiya qalau take jinta,tamkar bata sha fama da azabar laulayi ba kamar bazata kai labari ba.



        Sanda suka gama satittikan da suka tsara yi sannan su wuce brasil sai sukaso riqe bilkisun,saidai anty zuhriyya tace samm qafarta qafar bilkisu,akayita ja amma taqiya,daga qarshe abbu yace su barta,don yadda ta kafe din baijin akwai abinda zai sauya ta.



        Suma din basuga laifinta can ba,tunda ita tadauko musu ita ta kawo musu,bai kyautu su gwada qarfin dantsensu suce saisun riqeta ba,tsohuwar ta dungure kanta tana cewa

"Ja'ira,har yanzu taurin kai kafiya da tsiwar tana nan,ta yaya bazanfi son maimunatu ba?"

"Eh din,nadaiji" itadai bilkisu na gefe tana murmushi,yanayin yadda suke qaunar junansu tana burgeta,waiyau ita bilkisu ce ake rububin daukarta,ana gasar nuna mata soyayya da gata.



        Lallai duniya labari ce,hakanan dukkan tsanani yana tare da sauqi,tunda ko hakane,indai ta manta dukkan wata damuwa da barazana da rayuwarta ta fuskanta a baya,babu abinda xai hana ta shimfida sabuwar rayuwa da zata baro dukkan wani miki data taba samu cikin zuciyarta,duk da tasan cewa an bar mata babban tabon da bazai taba warkewa kota manta dashi ba,saita dora hannunta ta shafi cikinta da a satittikan nan yake yawaita motsi,motsin da aduk sanda suka yishi take sake ganin girma isa da buwayar mahaliccinta daya sanya dan adam cikin dan adam,ya kuma rayashi ya maidashi mutum cikakke.



       Kwanaki uku suka qara suka tattara suka wuce brasil,yanayin rayuwar can din yayi mata dadi qwarai,ya kuma sake mantar da ita abubuwa da yawa,ta samu isashshen lokaci ta tsarawa kanta dukkan abinda takeson gabatarwa,da kuma abinda takeson zama anan gaba bayan ta rabu da cikin jikinta,kusan komai sai data tsarashi,wani cikin kwanyarta,wani kuma a rubuce,sannan ta tattara ta miqawa Allah lamuranta,ta kuma duqufa da addu'ar ya cika mata dukkan burikanta data qudurta,tare da bara da roqon kada ya sake qaddara wani abu da xai gilma ya sake ruguxa mata mafarkinta.



*_YARIMA ABDUL'AZEEZ_*




        Dukkan wata juriya da jarumta tashi ta qare,kamar yadda tunaninsa kan yadda zai nemota ya qure,zazzafar damuwa ta kwantar dashi,ciwo sosai wanda yake jinsa cikin kowanne lungu da saqo na jiki da zuciyarsa,yana jin zuciyarsa ta masa wani irin qunci,yakanji zuciyarsa tana radadi da ciwo,wanda yake saka ran nan gaba kadan komai zai iya faruwa da zuciyarsa.



         Ciwon nashi ya sake daga hankalin ammin sosai,hakan ya sanya ta saka ido sosai kan duk wani lamarinsa,sanya idanun da yayi sanadin binciko abinda ya boye,ya bayyana a gareta yaga bilkisu,ya kuma shiga fafutukar nemanta.



        Sosai hankalinta ya tashi,ta rasa inda zata sanya rayuwarta,wai meke faruwa ne?,me yake faruwa?,me yasa azeez ya kasa cire yarinyar daga rayuwarshi?,me yasa ya kasa ajeta gefe yaci gaba da rayuwarsa kamar yadda tayi hasashe ta kuma tsara?.



       Hankalinta ya sake tashi sanda ta tuna da zancan safwa,qorafin data kawo mata cikin wancan satin,duk zuwan da take duba azeez yaqi bari ta ganshi,hakanan duk wani kiran waya ko saqo da take aika masa babu feedback ko guda daya,saita alaqanta hakan da rashin lafiyarsa,ta kuma bashi uzuri tare da alqawarin dai daita komai.



       Saidai abinda basu sani ba shine,tuni ya yankema ranshi cewa,matuqar ya zauna ya rayu da wata macen cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,tamkar ya tafka wani mummunan zalunci ne ga rayuwar wata halitta da bata taba zaluntar tashi rayuwar ba,tamkar ya fasa gobensa ne.



         Wadan nan bayanan data samu ya sanyata ta gaza zama,qarfe goma na dare ta shirya daga ita sai kubra ta nufi sashen yarima azeez,ranta a matuqar bace,zuciyarta a dugunzume,tana jin cewa wannan karon zata masa mai gaba daya ne,zata masa mai dungurun gum,zatayi masa ta yanke ta gille mai gaba daya haihuwa da hanji.


47

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899

Ko

09033181070




       Dai dai lokacin da yake zaune shi daya cikin katafaren falonshi labarin isowar fulani ya riskeshi,ya daga kai ya dubi agogo sai yaga goma harda mintuna na dare,hakan ya bashi mamaki qwarai tare da tabbatar masa lallai muhimmin abu me girma ne yake tafe da ita,sai ya miqe zuwa cikin bedroom dinsa,ya sanyo wata jallabiya ruwan gold mai dogon hannu santsi da sulbi da kuma daukar idanu,sannan ya dawo zuwa cikin falon.



       Koda ya dawo tuni ya isketa tsaye tsakiyar falon,goye da hannayenta,idanunta na duban qofar dakin gadon nashi,kallo daya zaka yiwa tsakiyar idanunta kasan cewa ranta yakai qarshe wajen baci,hakanan fushi ne kwance rubuce saman fuskarta.



        A nutse yayo tattaki zuwa gabanta,ya rusuna a ladabce yace

"Barka da dare...." Bai qarasa ba ta daga mishi hannu,cikin kakkausar murya ta soma magana

"Ni na dauki cikinka cikin qunci da wahala wata ɗai ɗai ɗai har watanni tara cif,ba tare dana sauke na huta ba harsai da kakai wadan na kwanakin,na tsugunna na haifeka cikin rashin tabbacin zan rayu ko bazan rayu na,nice cinka shanka,fitsarinka,lafiyarka da lalurarka,idan kayi dariya nayi,idan kayi kuka nayi,idan kana da buqatar abu sai inda qarfina ya qare,nakan haqura da komai idan baka sonshi,hakanan nakan dauka kona rungumi duk abinda kakeso,ban daina dawainiya dakai ba da kula da dukkan lamuranka,da kuma duk wani abu da zai cutar dakai ba har kawo yau da kake da shekaru ashirin da shida a duniya......amma yau.....ni aishatu nizan maka umarni kan wasu abubuwa ka nemi bijiremin?,wai shin?,me kake nema wajen yarinyar da babu shi ga sauran mata da har xaka gagara fitar da ita daga rayuwarka kamar yadda na tsara na kuma buqata abdul'azeez!" Ta qarashe maganar cikin daga sauti dake cike da bacin rai,abinda kusan bazai iya tuna yaushe ya taba faruwa tsakaninsa da ammi ba,hakan ya sanya ya sake sadda kanshi qasa,yana jin wani rauni yana mamayarsa,zuciyarsa tana kakkaryewa gami da tsinkewa kamar zare,yayim da sautin muryarta yaci gaba da ratsa falon cikin bacin rai

"Kome zanyi nayishi ne saboda kai wanda kai din na zaka taba fahimtar hakan ba sai nan gaba!,ni na kawo yarinyar cikin rayuwarka nace kuma ta fita,na kawota a sanda baka santa ba bakuma kayi zata ba,a yanzu kuma nace bana buqatar hakan!,shin ka shirya fito na fito dani ne abdul'azeez?!" Ta saje jefa masa tambayar cikin fada sosai,wanda ya sanyashi zamewa saman gwiwoyinsa ya tsugunna anan gabanta,yana jin fadan nata har cikin jininsa,yana iya jiyo sautin bacin ranta daga zuciyarta,cikin taushin murya yace

"Ammi....maganar da sukazo miki da ita kikaqi gasgatata gaskiya ce,zancan yarinyar tana dauke da......"

"Ya isa!....ba wannan naxo ji ba,na jima da bunne batunta,na jima da bunne duk wani daya shafeta,saura ya rage naka,idan aure ne matsalarka.......ka shirya aurenka da safwa nan kurkusa,amma ka sani,dole kaje kayi karatu tuquru ka zama wani,dole matsayin da nakeson ganinka akai ka takashi,dole ka manta da an taba yin wata halitta cikin sa'o'in rayuwarka mai suna bilkisu...inhar ka shirya ci gaba da kasa cewa a sunan dan aisha diya ga sarkin mali!,idan kuma ka shirya cire jinina daga naka!,ka shirya sauya uwa to kaci gaba da dorawa daga inda ka tsaya,ni dakai aga wanda zai fasa abdul'azeez,kaci gaba nace!,amma ka shirya sauya wata uwar bani ba!" Daga haka ta juya tayi tafiyarta ba tare data tsaya taji koda kalma daya daga bakinsa ba,ba tare data waiwaya tayi masa duba na biyu ba,ta dinga takawa tana jin bacin rai sosai da tsanar bilkisu,yarinyar tana son zame mata qarfen qafa,tana son ta zame mata wata katanga daga cikar burikanta kan danta datasha wahalarsa,me yasa tun farko nata sauyawa bilkisun qasa ba ta yadda ba zasu sake haduwa da azeez din ba,banda kyau na fuska bata san kuma bataga wani abu da zaija azeez zuwa gareta ba,me yarinyar keda shi haka?,ta yiwa kanta tambayar da bata da amsarta.



        Tunda ta fita bai motsa daga inda yake tsugunne ba inda ga barshi,ji yakeyi kamar wanda ake watsawa ruwan qanqara,tun daga saman kanshi zuwa yatsun qafarshi,a rayuwa bashi da kamar ammi,hakanan babu kamar uwa cikin rayuwar kowacce halitta,kama daga mutum aljani dabba tsintsaye qwari harma da tsirrai,dukkanin wanda zai soka to bazai maka koda kwatankwacin soyayyar datayi maka bane,itace ta soka tun baka zama mutum ba,tun bata sanka da idanu ba,bata taba ganinka ba,kana boye cikin fatar cikinta amma take qaunarka,har kazo duniya baka da hankalin bambance mai kyau da mara kyau,harka zama cikakken mutum da kowa ke qaunar ka rabeshi,akwai soyayyar datafi wannan?.



       To amma abu mafi daure kai shine,ina wannan tausayin na daa da uwa?,ina wannan soyayyar?,duka ammi ta sanya qafa tayi fatali da ita?,meye abunyi a gareshi?,ya mata biyayya ya banzatar ya kuma sarayar da haqqunan rayukan da zuwa yanzu baisan guda nawa bane?,ko kuwa ya bijire mata ya shirya tunkarar dukkan wani abu da xai sameshi a rayuwa?.



         Wannan tunanin shi ya kusa daskarar da qwaqwalwarsa,har baisan adadin lokutta daya shafe durqushe a wajen ba,sai daya ji jikinsa na fidda wani irin hucin zafi dake alamta masa tempurature din jikinsa ya hau sosai,sannan ya iya dafa abinda ke gefansa ya miqe tsaye da qyar,kamar wanda ya shekara a duqe,yakai kanshi dakinsa da qyar.



        Bai damu da yanayin jikinsa ba bare yasha wani magani,tsahin daren kawai ya qarar dashi wajen yanke hukunci na qarshe a rayuwarsa,wanda wayewar garin ranar da sassafe ya isa gaban ammin,ya kuma shaida mata hukuncin daya karba cikin zabi biyun data bashi.



*_kaso na biyu cikin labarin kenan masu karatu,zamu shiga cikin kaso na uku,ku biyoni_*





    *BAYAN SHEKARA BAKWAI*



       Cikin nutsuwar 'yar madaidaiciyar motar mai azabar kyau fasali da tsari gami da daukan hankali take sako kai cikij katafaren asibitin dake zaman kanshi wanda keda mazauni cikin brasillia dake qasar brasil,bansan me ya sanya ba ban kuma san dalilin daya saka duk inda motar ta gifta saita dauki hankulan jama'a da dama dake kai kawo cikin asibitin,wasu kuma na zaune guraren da aka kebance saboda buqatuwar masu zuwa asibitin wanda a nan gida nigeria yafi kama da wajen shaqatawa ko shan iska,saboda yadda ya wadata da ababen zama masu kyau,korayen tsirrai da kuma iska mai dadi qwarai da kwantar da rai.



       Bata gushe ba motar tana ci gaba da ratsawa cikin asibitin,har sai data isa muhallin da aka tanada a dokance saboda ajiyar ababen hawa,akayi mata parking me kyau kafin a kasheta,wanda zai gaya maka drivan dake sarrafa motar ba shakka yasan abinda yakeyi.



         A qalla saida aka dauki kyawawan mintuna uku kafin qofar motar ta bude a hankali kuma cikin nutsuwa,wanda budewat motar yake dai dai da fitowar wani rantsatsen qamshi mai kwantar da zuciya da sanya nutsuwa,hadi da sanyin acn da aka kasheta a yanzu.



       Idan kakai dubanka cikin motar sai kace tirqashi!,wata halitta ce mai cikar zati haiba da kwarjini,wadda kamala da nutsuwa suka sake qawata kyanta,kwarjininta kuma yake bayyana kansa.



        Zaune take a sit din drivern da alama itace me tuqin kuma mamallakiyar motar,sanye cikin wani lallausan yadi mai azabar kyau da daukar idanu,wanda sam ba'a cika masa ado ko qawa ba,an masa dinkin riga wadda tsahonta ya kawo har gwiwa,sai kuma street skert mai matsakaiciyar tsaga wadda ba zata fidda halittar qafarta ba,tayi rolling da mayafi madaidaici wanda bata buqaci dankwali ba tunda ya rufe mata dukkan inda ake buqata,fuskarta sam babu kwalliya ko kadan idan ka dauke powder da man lebe masu taushi wanda yasa lebunan nata suka qara kyau da qyalli,sai jikinta dakw fidda wani irin sihirtaccen qamshe mai nuna tsada da ajin turaren da take amfani da shi.



    hannunta dake sanye da wani kyakkyawan zobe qwaya daya,sai agogo a tsintsiyar hannunta daketa aikinsa ta sanya ta zare muqullin motar,sannan ta waiwaya sit din gefanta ta saka hannunta tana tattara kayayyakinta dake zube a wajen,wanda takardu ne cikin wasu folders,qaramar hand bag nata wayoyinta sai labcoat dinta dake rataye a fuskar kujerar.



       Sai data gama tattare kayan tana shirin dorasu saman cinyarta don ta samu damar fita sai idanunta suka sauka kan wani qaramin lunch box da aka dan turashi qasan kujera da alama ana boyewa wani ne kada ya ganshi.



       Idanu ta zubawa lunch box din kafin ta miqa hannu a hankali ta daukoshi,sannan ta dorashi saman cinyarta ta bude.



        Komai da komai da ta zuba yana ciki,babu abinda aka taba ciki sai drinks din data zuba aka kwashe,choculets da biscuit.



        Wani murmushi ne ya subuce mata bata shirya ba,ta dora yatsanta guda biyu saman labbanta tana girgiza kai

"Amatullah....amatullah,Allah ya shirya min ke" harta maida lunch box din sai kuma ta fasa ta hada da dukka kayayyakin nata ta zuro santala santalan qafafunta dake cikin hillshoes mai igoyiyi ta fito zuwa waje.



         Nan take Dr Bilkees Bilyamin ta bayyana,kamanninta da suka dan sauya kadan sakamakon gishirin rayuwa wato ilimi daya ratsata,wayewa hutu jin dadi uwa uba nutsuwa da kwanciyar hankali data samu cikin wadan nan shekaru bakwai din.



        Tana gama kulle motar ta soma takawa zuwa wata hanya da zata sadata kai tsaye da office dinta,tana mai sauya yanayin fuskarta,ta ragewa fuskarta fara'ar dake samanta a daxun,tadan daureta tana sake maida hankalinta ga inda take sanya qafafunta.



        Daga yanayin yadda ma'aikatan asibitin ke gaidata cikin girmamawa kawai ya isa ya gaya maka ita din wata ce,ta dinga amsa musu bakin gwargwado cikin kulawa,har takai jerin inda office dinsu yake.



        Office na kusa da qarshe ta saka card dinta wanda bayan ya gama duba bayanan jiki qofar ta bude mata,ta sanya kai cikin sauri ta shige.



        Tana qoqarin maida qofar idanunta ya sauka kan wani office da yake opposition da nata office din,allon dake dauke da suna da matsayin me office din na mamallakin asibitin ya bayyana,tayi hanzari maida qofar ganin tana yunqurin budewa,bakinta cike fal da addu'ar Allah yasa ba zuwanta yaji ba ya fito,taja qaramin tsaki tana rage kayayyakin dake hannuntanta hanyar ajiyesu,donta hana kowa ya amsar mata kayan,matsayin da suke bata da girman da suke bata ita bata sonshi sam,batasan me yasa Dr adam yayi mata haka ba,ya fiya naci kafiya da kuma rashin zuciya,ta tabbata idan da wani ne da tuni ya tattara lamuranta ya watsar,amma shi ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,duk abinda takeyi din nunawa yake kamar ma bai fahimceta ba,sai sake shige mata ma da yakeyi.



         Sai data gama duk abinda zatayin sannan ta soma amfani da kayan wutar dake gabanta,kama daga cellphone zuwa kwamfuta,ta soma da neman wanda ke kula da office dinta,taji ayyukanta na yau.



        Akwai yaran data yiwa aiki jiya wanda dole yau zata shiga ta duba yadda suka kwana,sa'annan akwai wasu yaran da zata gani a yau din,duk da cewa sai yanzu ake gaya mata,don a qa'ida ba lallai ita zata gansun ba,amma iyayensu sun dage kan cewa ita din sukeso ta dubasu.



        Tana cikin hada kayan da zata buqata idan ya fita round din,tana kuma jiran isowar nurses din da suke qarqashin kulawarta wadanda tare zasuyi round din qofar office din nata ya bude,wanda tun bata daga kanta ta kalla bakin qofar ba tasan ko waye.



         Dr adam ne,shi kadai qofar ke budewa ba tare data bada izini ba,don haka bata daga kai ta kalli bakin qofar ba taci gaba da sabgarta.



        Dogon matashi ne,ma'abocin tsaho da kuma fari,irin farin nan qal wanda kana kallonshi xaka san cewa ruwa biyu ne,a shekaru duka duka bai wuce shekara talatin da biyu ba,amma tsahonshi ya sanya akan bashi shekaru sama da haka,daga kallon farko xaka fahimci cewa shi din ruwa biyu ne kamar yadda na fada a baya,haka yake,mahaifiyarsa haifaffiyar qasar brasil din ce,yayin da mahaifinsa ya kasance dan asalin nigeria,bafulatanin jigawa,saidai dukka rayuwarsa yayita ne yana kuma yinta a qasar ta brasil,zai iya cewa tunda yake zuwanshi nigeria dangin mahaifinsa sau daya ne.



        Cikakken likita wanda haihuwar mahaifiyarsa a qasar da haihuwarshi shima da akayi a qasar yasa ya samu damammaki masu tarin yawa,ya kuma zama shima halastaccen dan qasar,wanda hakan ya bashi damar mallakar fili da gina asibiti nashi na qashin kansa,babban asibiti na kudi wanda yayi shuhura cikin garin,yake kuma da kyakkyawan tarihi na qwarewa da iya kula da marasa lafiya,musamman mata da qananan yara,wanda a halin yanzu bilkisu take aiki a qarqashinsa,cikin asibiti bangaren cututtukan da suka shafi yara.



        Ya fada soyayyar bilkisu tun bata gama karatunta ba,bayan ta gama kuma yasan yadda yayi ba tare da masaniyarta ba ya bata aiki a asibitinsa,wada farawarta aikin babu jimawa ya bayyana mata qudurinsa,saidai ko kadan ita bata dauki kalmar soyayya a bakin komai ba,face kalma mara ma'ana mara amfani a rayuwar mutum,kalmar da bata bata sha'awa kota burgeta,hasalima tana mata kallon azzalumar kalma mai cutar da duk wanda ya raɓa kanshi da ita.



       Duk wani halin ko in kula da hannunka mai sanda bilkisu ta nunawa dr adam saboda ya shafa mata lafiya,ya barta ta rayu qalau cikin salama amma yayi funfurus,da fari ya dauka sonshi ne batayi,amma data gaya mishi ita bata taba soyayya bama saiya dauki tutsun da take masa ba'a bakin komai ba,yaci gaba da qoqarin kafa gwamnatinsa a wajenta,duk da yaji shakkun cewa da tayi bata taba soyayya ba,amma tunda daga bakinta yaji hakan,bashi da ikon musantawa,ya kauda kanshi daga duk wani zille zille nata,ya kafa dukka kayan aikinsa ,yaci alwashin saiya mallaketa a matsayin matar aurensa.



        Tunda yake duniya bai taba ganin macen datayi masifar tafiya dashi ba,ta kuma kwanta mishi a rai irin bilkisun ba,ta hada dukkan wani abu da yake zata ga diya mace,harma ga wanda hankalinsa bai taba bashi mace kamar bilkisun zata mallaka ba,wata irin soyayya yake mata har cikin jininsa,hatta da mahaifiyarsa tasan da zaman soyayyar da yakewa bilkisu,yaci alwashin bazai sassauta ba har sai yaga abunda ya turewa buzu nadinsa.



       Nannauyar ajiyar zuciya ya saki gami da murmushi kana ya sake hannayensa dake harde a qirjinsa tun daxun yana qare mata kallo,yayin da take zaune saman kujerarta tana ci gaba da duba wasu takaddu tana hadasu waje guda ba tare data dubeshi ba tunda ya shigo,ita ala dole bata ga shigowarsa ba,yasan kuma sarai ta gani,saidai shima yadda ta basar din yayi masa,tunda ko banza ya kalleta son ranshi,sai ya soma takowa zuwa bakin table din nata,yaja kujera ya zauna yana cewa cikin yaren nasara

"Kome kikayi kyau yake miki,kome kuma kikayi kin isa kiyishi"

"Assalamu alaikum warahmatullah" ta fada ba tare data dubeshi ba,saiya dan dafe bakinsa yana cewa

"Afwa,na sha'afa ne,kyakkyawar fuskarki ta shagaltar dani.....assalamu alaikum warahmtullah" a fakaice ta tabe baki kana ta amsa mishi ciki ciki,banu kaifi adam.din yana da dabi'u na gari,saidai hausawa sunce society da mutum ya rayu a ciki yana da matuqar tasiri cikin dabi'unsa da halayensa,dabi'unsa mafi yawa na turawa ne,wanda wasu abubuwan wajen cikakken bahaushe musulmi dan arewa abun kubya da qyamata ne,amma zaka samu su a wajensu ba komai bane,sabida tasirantuwa da sukayi da dabi'unsu,bare shi da aka haifeshi cikinsu,ya rayu dasu har yau kuma yake rayuwa a cikinsu,abubuwa da yawa na halyayyarsa tana cin gyaranshi akai,yana kuma gyarawar tare da qoqarin kiyayewa,don da wuya ya maimaita kuskure idan ta gyara mishi saboda zallar soyayyar da yakeyi mata,bata bashi dama ya sake cewa wani abu ba ta miqe tana riqe da wani file guda daya ta dubeshi

"Idan ka gama idan babu damuwa.....ka rufe min office din,zan fita round" fuskarshi babu alamun damuwa yace

"Me zanyi da office din da babu ke a ciki,wajenki nazo,ya kamata ko minti biyar a bani" saita gyara riqon takardun hannunta ta sake cewa

"Mubar aikin mu xauna hira kenan ko kuwa?"

"Da zakiyi hakan da nafi kowa murna" idanu ta dan fiddo,wanda hakan ya qara mata kyau a idanunsa

"Kafi kowa sanin cewa ba wannan nazo ba....sannan duk wani ganganci ko kuskure dazai faru a asibitinka,qasarka ba zata qyaleka ba zata hukuntaka ne,sannan waima.....shin ku turawa ba 'ance kunfi kowa kiyaye doka da qa'ida ba?" Dariya sosai yayi harta tsaya kallonshi,kana ya tsagaita ya bata amsa

"Baki fada dai dai ba,kin manta ni bahaushe ne dan nigeria?,kusan kullum saina gyara miki fa?" Kusan tunda ya soma sonta ya maida kanshi dan nigeria sosai,saboda yadda ya lura tana kishin qasarta,tana kuma yawan maganarta dason komawa can nan kusa,sabanin daa dabai damu ba,ka kirashi dan nigeria ko dan brasil duk daya ne a wajensa

"Banga alamu ba,tunda nidai a dan brasil na sanka...." Tana kaiwa nan qofar ta shaida mata akwai mutane dake tsaye a wajen,hakan ya nuna mata nurses din sun qaraso,don haka sai kawai tayi gaba abunta,batason ya sake tsaidata.


48


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899

Ko

09033181070






         Tsayin wani lokaci tana round din tana duba dukan yaran da suke qarqashin kulawarta,cikin nishadi take komai gami da cikakkiyar qwarewa tare da kulawa ta musamman,lokaci daya Allah ya sanya mata son aikin nata duk da cewa a fari ba shine zabinta ba,amma a yanzun sai ya zama aiki mafi girma data fi so da qauna albarkacin yaran da take ceto rayuwarsu,hakanan Allah ya bata tarin farinjini wajen yaran,duk yaron data zama likitarsa saiya qaunaceta,babu banbancin yare kalar fata qasa ko addini,hakanan Allah yake sanya sabo da qauna tsakaninsu,don da yawa ma ko bayan sun bar asibitin sukanci gaba da hulda da ita da kuma zumunci.



        Bayan ta gama dubasun ta soma ganin patient din nata suma cikin qwarewa da karsashi,ta samu sakewa don ba kasafai dr adam gake shigowa ba idan tana ganin marasa lafiya.



        Ta dan dauki lokaci mai tsaho kafin ta gama dubasun,duk da cewa can din ba kamar qasarmu bane,babu cinkoson marasa lafiya da ake tilawa likitoci tarin aikin da yafi qarfinsu,saidai ita din qwarewarta ya sanya koda yaushe bata rabo da ganin marasa lafiya.



        Ajiyar zuciya ta sauke tana duba agogon hannunta,lokacin dauko yara daga makaranta ya kusa,mintuna kadan suka rage,duk da cewa motar makaranta tana daukosu tun daga cikin makarantar har zuwa qofar gidajensu,amma yau ta musu alqawarin cewa zata zo da kanta ta daukesu,don lokacin tashinta yayi dai dai da lokacin tashinsu suma.



       A nutse ta miqe ta soma warware rolling din kanta,idanunta nakan calender dake maqale a jikin bangon office din,tana lissafin kwanakin wata da kuma kwanakin da suka rage musu tafiya seminer din da aka turasu zuwa qasar dubai,ba kasafai ta fiya son irin wadan nan tafiye tafiyen ba saboda kare mutuncinta da kuma rage zargi a zukatan mutane,saidai duk sanda wani abu na samun qwarewa ya taso daga asibitin dr adam baya yin qasa a gwiwa wajen sanya sunanta a sahun farko farko,hakan na daya daga cikin mabudin nasararta,da kuma silar zamantowarta qwararriya kuma gogaggiya akan aikinta.



       Gefe guda kuma tana samun dukkan wani qwarin gwiwa daga wajen anty zuhriyya da kuma abbaa,wanda batasan da wadanne kalmomi a kullum zata gode musu ba,hakanan batasan dame zata saka musu ba,sun bata dukkan wani taimako qwarin gwiwa da kuma goyon baya,har ta kawo matsayin da take kai a yanzun.



        A nutse ta gama warware rolling din nata,kyakkyawan gashinta daya wadatu da gyara ya bayyana,yanata sheqi da fidda qamshi,ta nadeshi da band fari qal,ta zare agogon hannunta sannan ta shige bandaki ta daura alwala,wanda kusan sabonta ne,bayan ta fito ta ciro wani tattausan handkherchief wanda ke fidda wani qamshi mai sanyi ta goge ruwan jikinta,kana ta maida dukka nadinta da agogonta tsaf.



       Lunch box din amatullah kawai ta dauka sai handbag dinta ta fita a office din,da saur i sauri ta wuce office din dr adam don kada ma ya fuskanci fitarta bare ya biyota,don tsaf zai iya shige maya mota yace sai sunje tare,abu na qarshe da tafi tsana kenan,don bata son yaranta su dinga ganinta da wani mutum na daban baquwar fuska,wanda hakan zai iya illawa tarbiyyarsu,hakanan batasan amsar da zata basu ba kan waye ne nasu,inda ma abun yazo mata da sauqi,duk da tarin wayo kaifin basira da fikira da Alla ya basu,Alla bai taba budar bakinsu sun tambayeta waye mahaifinsu ba,inda take godewa Allah kenan.



         Sai data tada motar ta soma barin harabar asibitin sannan ta hangi dr adam ta madubin gaban motar,tsaye yake harde da hannayensa yana bin motar da kallo,hakan yayi mata dadi sosai,da alama yaso cimmata,saidai hakan bata samu ba,duk yadda akayi kuma aiki ya tsareshi ya manta actual lokacin tashinta ne sai daga baya ya farga,data tabbatar saiya mata katsalandan din daya saba mata.



         Tun batayi nisa ba taji alamun shigowar saqo wayarta,bata raba dayan biyun shine,don haka ta share ba tare data duba ba taci gaba da tuqinta hankali kwance.



       Minti ashirin da biyar kyawawa ta isa makarantar tasu,daga inda ake aje motoci tayi parking tana kallon yara nata ficewa zuwa motocin dake daukarsu zuwa gidanjensu,kusan dukkanin yaran yaran turawane masu jajayen fata,wasunsu 'yar qasar wasu kuma baqin haure kamar dai su.



       Idanunta kan hanya har zuwa sanda ta hangi yaran suna nufota,kyawawan 'yan biyu masu masifar daukar hankali,duk da cewa ba jinsinsu daya ba wato mace ne da namiji amma kuma kamanninsu daya,kai daga gani basai an gaya maka ba kasan cewa 'yan biyu ne irin identical din nan,wadanda da ace jinsu guda n zaiyi wuya adinga banbance hassan da usaini ko hassana da usaina,sai Allah ya taqaita ya yosu jinsin daban daban.



         Kallonsu take sosai kamar bata sansu ba,kallonsu take tana jin wata qaunar yaran nata tana ratsata,tanajin wata soyayya ta musamman dake tsakanin uwa da 'ya'yanta.



       Murmushi ya subuce mata ita daya sanda taga sun tsaya sun danyi magana tsakaninsu,abdulrahman dake a mazaunin hassan ya hade rai yayo gaba abinsa,sau tari takan zauna ta jima ta kuma bata lokaci tana lalube tare da binciken dawa suke kama?,kaf danginta uwa da uba basu dauki kamar kowa ba,hakanan halaye da dabi'un abdur rahman sau tari suna bata mamaki,wata dabi'a ta daban kai kace babban mutum ne,dukkan tunani da hasashenta kan yanke ya kuma qare da bacin rai idan zuciyarta ta gaya mata

"Wala'alla dangin mahaifinsa ya dauko a kama,haka halayya da dabi'un ma" takan miqe cikin bacin rai kamar da wani take maganar,a sarari kuma ba'a boye ba ta furta

"Allah ya tsare,ya kiyashi 'ya'ya na"



      Abdur rahman ne ya soma isowa,ta dubeshi fuskarta har yanzu dauke da murmushi

"Sarkin miskilanci sarkin fushi,me kuma akayi?" Ta fadi sanda yake shigowa sit din kusa da ita

"Abokina ne yace wai bamu da daddy...tunda bai taba ganin daddynmu ba,shi kuwa nashi daddyn ne yake kawoshi makaranta kullum,shine yace zai bamu daddynsu,amatu tace eh muna so" wani abu mai nauyi ne ya sauka a qirjinta,wanda har yayi tasiri wajen hanata cewa komai,a haka har amatu ta qaraso ta bude gidan baya ta shiga ta rufe,saita gaza cewa da yaron komai har zuwa sanda ta tashi motar,tana jin lokacin da amatu tayi hugging dinta tana murnar xuwa daukarsu da tayi,amma ta gaza waiwayawa ta dubeta ko tace wani abu,haka taci gaba da yin shuru,tana jin yaran na sabgarsu sama sama.



       Wato komai nisan jifa qasa zai fado,sannu sannu ranar da take murnar bata zo ba takeson riskarta,wacce amsa ce zata dace da tarin tambayoyinsu da zasu ci gaba da zuwa mata dasu anan gaba kadan?,tunda koda yaushe wayo suke dada yi.



      A hankali ta waiwaya tana duban sashen da abdurrahman yake xaune da litattafansa saman cinyarsa,saita lura da wata babbar takarda daya wareta yana kallo,ta sake duba karo na biyu,hoton wannan business tycoon din ne,wanda yayi wani irin shuhura da shahara a fadin duniya,qasashe iri daban daban,zata iya cewa a shekara gudan nan taga hotunanshi taji labarinsa babu adadi,saidai a duk sanda idanunta zasuga hotonshi saita hadu da wata mummunar faduwar gaba da fargaba da batasan dalili ba,wala'alla hakan baya rasa nasana da sunan da yake amfani dashi daya danganci sarauta,wadda batasan ta wacce qasa yanki ko nahiya bace *A M YARIMA*.



      Tun abinda ya faru a wancan qarnin ta tsani duk wani abu da xai danganci sarauta,ko zai fito shafi sarauta,kama daga suna sutura da sauransu,hakan ya sanya take zaton dalilin faduwar gabanta kenan,harma ta soma tsanar ganin hotunan,wanda koda bata gansu a poster ba,takan ci karo dasu lokaci zuwa lokaci matuqar zata kalli labaran duniya a kowacce tasha,kuma zasu sako labaran kasuwanci,to abune mawuyaci suyi su qare basu sako shi ba

"Ina ka samu wannan hoton?" Ta tambayi abdul tana maida kanta ga tuqin da takeyi

"Uncle ne ya bani....mami...inason xama irin wannan mutumin idan na girma,uncle ya gayamin jajirtacce ne,inason na zama jajirtacce kamarsa" murmushi kawai tayi ganin yadda yake bayanin bilhaqqi daga zuciyarsa kamar wani babban mutum,ba tare data dubeshi ba ta sanya hannunta saman kanshi,ta shafi sumarsa sannan tace

"Allan yayi maka albarka,ina fatan ka fishi komai da komai,bakasan wayeshi ba,kullum kace kanason ka fishi ne ta hanyoyin alkhairinsa kaji?" Kai y gyada mata yana ci gaba da duban hoton daya bude din,da alama yana ji da takardar.



          Sanda suka isa gida yaran sun rigata fita,kasancewar ta tsaya tattara duk abinda suka bari nasu a motar,ta gama ta fito tana shirin kulle motar ta hangi amatu datayi gaba kanta sanye da crown a kanta irin na yara.



       Hakanan gabanta yayi mummunar faduwa,da hanzari ta gama rufe motar ta rufa mata baya,cikin taku qalilan ta cimmata sanda take dab da shiga falon gidan,ta jawota tana cire abun daga kanta,cikin fada ta soma magana

"Wannan abun fa daga ina?,ina kika samoshi?" A narke take duban ummin nata ganin yadda take fada tace

"Qawata ce ta bani" hakanan taji ranta yana baci ganinta da abun,ta zazzaro idanu tana dubanta

"Ashe baki da hankali amatu?,roqo kika koyo?,meye hadinki da wannan abun da zata baki shi?" Saita maqale kafada idanunta na cikowa da qwalla

"Ina sonshi mommy,yana bani sha'awa,shine tace tana dasu da yawa na birthday dinta,saita bani daya" wurgi bilkisu tayi da abun yana tuna mata wani abu,tana jin kamar masarautar kaisa ce a jikin abun,kamar ta bishi ta tattakeshi,ta maida dubanta ga amatu data fara qwalla,tana bin abun da idanu tana jin kamar taje ta dauko abunta

"Gargadi na qarshe zan miki,karki sake na sake ganinki dashi,bama shi ba,karna kuma ganin kin karbi wani abu daga hannun wani,idan ba haka ba saina yanka hannuwanki,kina jina?" Ta fada a tsawace tana dan murda kunneta,da sauri ta daga kai tana dafe kunnun nata da hannunta,hawaye yana sauko mata,sai kuma taji tausayinta ya ratsata,ta sakar mata kunnen tana cewa

"Oya...ku wuce ciki" dukka suka shige din da hanzari,ta maida dubanta inda tayi wurgi da abin na wasu sakanni sannna ta dauke kanta da zummar bin bayansu zuwa ciki itama,sai a sannan ta lura anty zuhriyya tana tsaye ashe tana kallon duk abinda ke faruwa,da suka hada ido saita dauke kai kawai ta matsa mata ta shige zuwa ciki.




          A dakinta ta taddasu zaune babu wanda ya cire unifoarm dinsa bare yayi wanka koya sauya wasu kayan,tana shiga dukkansu suka taso suka rungumeta,amatu na kuka sai abdulrahman ne yace

"Kiyi haquri ummi,ba zata sake ba" wani irin tausayi da qaunarsu ta sake ratsata,wani irin so yaran suke mata,basason ganin bacin ranta ko yaya yake,yanzun zasu kasa sukuni gaba daya su addabi kansu,saita duqa saitinsu ya hadesu gaba daya cikin jikinta tana shafar kan amatu tana cewa

"Shikenan ya isa,kiyi shuru" cikin lokaci qanqani suka ware,ta sake musu wanka ta sauya musu kaya,sannan sukaci abinci suka fita falo,don yau gidan babu kowa,ateeq da najwa already suna makaranta,sai weekend suke zuwa hutu,abeed sun fita tare da babanshi,sai khadija dake barci abinta saboda ta rigasu dawowa daga makaranta,ba makaranta daya suke ba,nurain kuma yana bayan anty zuhriyya din.



         Sai da suka fita sannan tayi nata wankan,ta zauna gaban madubi tana shafe lallausar fatarta da mayukanta da take amfani dasu,masu azabar taushi qamshi da tsada,tana duba saqon dr adam

"Na gode qwarai da kika gudu kika barni,amma dai duk da haka na godewa Allah daya bani ikon ganinki a yau,ina dokin zuwan gobe don na sanyaki a idanu na,ina kuma addu'ar ranar da zaki aminta na kawo miki ziyara koda sau daya ne a tarihin rayuwata" baki ta tabe,cikin ranta tana mita,tana kuma ganin iska na wahal dame kayan kara ne kawai.



        Tana gama sanya rigarta tana shirin fita anty zuhriyya ta iskota

"Sannu da aiki bilkisu" tace da ita,koda batace komai ba tasan tana mata magana ne kan amatu,yaran na gaban goshinta ne fiye da kowa,ba'a tabasu a kwan lafiya,wani irin so take musu,kamar yadda hakanan suke da tarin farinjini wajen kowa dake baiwa bilkisu mamaki.



      Bata amsata ba harta zauna gefan gadonta sannan tace

"Yanzu har amatu ta isa wannan fadan a wajenki?,yarinyar da batasan komai ba,batasan wacece ita ba?,nasha gaya miki dole kiyi haquri da wasu abubuwan da zaki dinga gani,ko munqi ko munso jinin sarauta ne su,akwai wannan jinin dake yawo a jikinsu kullu yaumin,zamu iya ganin halayya da dabi'u na izza da sarauta tattare dasu,wanda mu bamu isa mu cire musu ba tunda ahalin abunne,haka Allah S W T yaga dama ya haliccesu......so pls ki daina zafafawa da yawa haka,basusan komai ba su din,kada gudun gara ki fada zago,kici gaba dayin abubuwan da zasu sanya su saka ayar tambaya akan kansu"



       Hakane kalaman anty zuhriyya,to amma itama bayin kanta bane,wani abun batasan tana wuce gona da.iri ba akansa har sai ta gaya mata,ita din kamar uwa take mahaifiya a wajenta,cikin sanyin jiki tace

"Zan gayara mami in sha Allah"

"Allah ya yarda,bari na qarasa naga kema kaman fitowa zakiyi"

"Eh mami yanzun nan,zan baki labarin wani yaro dana duba yau,ciwonshi akwai ban mamaki da daure kai" murmushi anty zuhriyyan ta saki

"Banga abinda a yanzu kikeso sama da aikinki din nan ba,kullum akwai sabon labari,kamar ba'a nan muka dinga dambarwa muna qoqarin tanqwaraki nida abbaa ban kan ki zabi bangaren" dariya sosai bilkisu tayi har herarrun fararen haqoranta suka bayyana kana tace

"Mami banda tuna baya fa"

"Oho dai" ta fada tana dariya gami da ficewa,itama saita juya gaban mudubin nata tana murmushi,ta jawo wani turare me kama da cream.ta lakata ta soma shafe hannayenta fatar cikinta zuwa wuyanta dashi,wani qamshi mai taushi ya soma tashi cikin mintuna qalilan,ta maidashi inda ta dauko kana ta dauki wayarta ta fito.


49



*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899

Ko

09033181070




       A falon ta samu anty zuhriyan itama tana shirin cin abincin rana,saboda haka ta zauna suka ci tare,suna ci tana bata labarin yaron da aka kawo mata din.



       Suna gab da kammalawa anty zuhriyya tace

"Kinsan tunanin da nakeyi?" Kai ta girgiza tana dubanta

"Da qyar qarshen shekarar nan idan ba nigeria zamu bafa,wannan karon munfi ko yaushe dadewa bamuje ba,ga abbaa yana son muje kazaure,mun jima sosai rabonmu dasu" 

"Allah ya nuna mana" ta fada a taqaice kawai,don hakanan bata son zuwansu amatu qasar,gaba daya kamar an cire mata qasar daga kanta,banda qannenta babu wanda take jin ta aje a qasar bare ta dameta.



       Anty zuhriyya ta fahimceta,saita saki murmushi kawai sannan tace

"Daughter....bakison zuwansu abdulrahman ko?" Murmushin yaqe tayi kawai ta kada kai

"Hakane mana....karki damu,babu wani abu da zai faru,ayau koda masarautar kaisa ce tayi iqirarin yaransu ne banga uban daya isa ya tabbatar da hakan ba bare yace zai amshesu a hannunmu,yara nakine halak malak,kamar yadda suka mallaka mana su tun suna ciki" lomar data rage mata a baki taji ta tsaya mata,ta hadiyeta da qyar tana tsame hannunta daga abincin,sai taji sauran gurbin daya rage a cikinta ya cike taf,ta qoshi.



       A rayuwa ko kadan batasan abinda zaya tuna mata da wadan nan azzaluman,ta tattara su da dukkan matsalarsu da damuwarsu ta watsata a bayan rayuwarta.



        Ranar hakanan ta qarasa wuninta sukuku jikinta kamar bata jin dadinsa sosai,don haka saita fidda wayarta bayan sallar magariba tayi kiran hannatu,wadda zuwa yanzu ta zama 'yammata,tana aji daya a jami'a,don ta dage karatu takeso haiqan,itama shine burinta,hakan ya sanya dukka sauran qannen nasu suma burinsu ya zamana iri daya.



      Bayan sun gaisa ta hadata dasu amatu sun gama shiriritarsu sannan ta amshi wayar suka ci gaba da magana

"Na kikkira lambar wayar baba bata shiga,yaya jikin nasa?"

"Da sauqi dai za'a ce yaaya"

"Kamar yaya?,ina asibitin da mukayi magana tun wancan satin za'a kaishi?" Ajiyar zuciya hannatu ta saki

"An kaishin yaaya,amma abun mamaki ya rasa me taqamaiman ciwon dake damunshi,suma kuma da suka duba din sun kasa banbamce komai,amma dai sun bashi magunguna,sunce ya soma amfani dasu,duk yadda yaji a jikinsa ya sanar musu" ajiyar zuciya itama ta sauke,ciwon malam bilyan ya zama wani abu na daban,yau yace ciwon qafa,gobe ciwon baya,gata ciwon gabobi,gaba daya ya tattara ya zama wani iri,kullum da kalar ciwon da yake damunsa,asibiti ba wanda ba'a zagaya dashi ba,ko yasha magunguna dai saidai kawai ace da sauqi.



       "Akwai wani asibti dake abuja,Inajin xan sa a kaishi,kai mishi wayar taki muyi magana" da to ta amsa mishi.



        Cikin laushin murya suke gaisawa da bilkisun,tayi masa sannu da jiki ya amsa

"Yauwa mai gado,kinga yadda Allah yayi dani,yau lafiya gobe babu,an rasa taqamaiman matsalar....ban sani ba ko Allah ne yake hukuntani ba da tarin laifukana,ko kuma ajalina ne yake kusantowa Allah masani" hakanan taji tausayinsa ya kamata,cikin mutuwar jiki tace

"Cuta ai ba mutuwa bace baba,zaka samu lafiya in sha Allahu,akwai asibitin da xansa akaika,zaka warware da.izinin ubangiji" kalamai tayi masa masu kwantar da hankali,daga qarshe da zasuyi sallama sai taji muryarsa kamar tana rawa,kamar me kuka,hakan ya sake sanyayar mata da jiki sosai.



  ********    *****    ********



        Da hanzari take hada dukkan tarkacenta daga bajesu saman table din don ta wuce gida,saboda ta kammala duba patient din da take da appointment dasu.



        Tana yi tana duba agogon hannunta,saboda alqawarin da sukayi dasu amatu yau zata fita dasu gari,sakamakon qoqarin da kowannensu yayi a jarabawarsu da suka kammala qarshen satin daya wuce,abdulrahman ya dauki 1st position,amatu ta mara masa baya da 2nd position.



       Tana saqala jakarta a kafadarta aka nemi izinin shigowa office din nata,kamar ta hana sai kuma ta bada izinin,daya daga cikin manyan ma'aikatan dake kula da sashen kasuwanci,qorafe qorafe da hulda tsakanin marasa lafiya da likitoci.



      Cikin girmamawa ya soma mata magana da harshen turanci,saboda yaren qasar ba wani zama mata yayi kan harshe ba,sai abinda ba'a rasa ba

"Ranki ya dade....akwai mara lafiya daya data rage zaki gani,an dan samu matsala ne jirginsu ya yada zango,amma yanzu haka suna kan hanya" dubanshi tayi

"Idan sunzo a basu daki idan abun yayi tsanani,idan baiyi ba suna iya tafiya,gobe mu hadu"

"Ranki ya dade manyan mutane ne,kuma daga wata masarauta suke,zuwan nasu mai muhimmanci ne,kuma kusan ke kadai ce kike da qwarewa kan ciwon dake damun yarinyar" ya qarashe maganar yana miqa mata takardar.



       Kaman ba zata amsa ba jin ya ambaci masarauta,amma saita fasa,ta miqa hannu ta karba kana ta soma duba takardar,wadda tana qunshe ne da dukkan bayanan ciwon yarinyar,da kuma muhallin da aka musu transfer zuwa nan.



       Ta fahimci bayanan da ciwon sosai tun kafin taji daga bakinsu,saidai sam sai taji bata da sha'awa kan case din,hakanan tambarin masarautar data gani jikin takardar yasa kula da case din ya fita a kanta,don ta tsani duk wata sabga data shafi masarauta.



      Takardar ta maida masa tana cewa

"Bazan iya zaman jiransu ba,idan sun matsun ayi yadda nace kawai" 

"Ranki ya dade,zuwan daya daga cikin familyn asibitin nan neman lafiya tamkar wata babbar nasara ce ga asibitin,kuma qarin daukaka ne a garemu da qarin samun suna a duniya,ke kanki ma ranki ya dade wani matakin nasara ce,kuma abun alfahari a garemu gaba daya" dubanshi sosai take,tana mamakin wadanne irin mutanene su har haka,sudin da zai zama kamar alfarma awajensu likitan ya duba su ya basu magani amma su da zasuyi aikin sune zai zame musu alfarma?,kodon suna da wata sarauta ne?,shi yasa har a kullum take qara tsanar sarauta,babu komai cikinta face tsabar girman kai da jin izza da dagawa

"Koma meye indai suna da buqatar aikina saidai ayi yadda nace,don yanzun haka ina da abunyi" daga haka ta soma takawa zata fice,dole yabi bayanta shima,ta wuce inda ta aje motar tana sake duba lokaci.



       A harabar gidan ta samesu suna wasa,amatu khadija abeed da nurain,gogan abdulrahman na zaune daga gefe abinsa yana binsu da kallo,da alamu 'yan miskilancin nasa ne a kusa.



       Murmushi kawai ta saki tana mamakin miskilanci irin na yaron,fitowarta daga motar yaja hankalinsu,dukkansu sukayo kanta suna mata oyoyo,ta hadasu dukka ta rungume,yayin da abdulrahman ya tsaya daga baya,sai data dago mishi hannu sa'annan ya qaraso,jakar hannunta ya soma amsa yana mata sannu da zuwa,ta amsa suka rankaya ciki gaba dayansu.



        Cikin mintuna qalilan dukkansu suka shirya,ta debesu suka fita,basu tsaya a ko ina ba sai wajen sannin yara,sun dan jima awajen sosai,kowa cikinsu ya sake yadda sukeso,ci wannan ci wancan,ta kashe musu kudi sosai,duk inda yaran sukayi idanuwanta akansu,tana jin qaunarsu da alfahari dasu,a baya idan akace mata zata so yaran har haka tana iya qaryatawa,sai gashi yanzun tana yiwa yaran soyayyar da bata zaci zata musun ba.



        Saida suka tashi tafiya aka nemi amatu sama ko qasa aka rasa,sosai hankalinta ya tashi,ta bazama nemanta cikin wajen,daga baya ta hangeta tsaye kusa da wani,yana riqe da hannunta,baqar fata ne kuma tafi kyautata zaton dan nigeria ne,duk da cewa bata ga fuskarshi ba,ta qara hanzari donta cimmasu,tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta isa garesu.



        "Ke amatu?,me kikeyi anan?" Ta fada da kaushin murya sanda ta isa bayansu,ko hakan zai taimaka su farga da isowarta,don sanda ta qaraso din ta fuskanshi surutu amatun keta yiwa mutumin shi kuma yana biye mata harda dariyarshi,bisa dukkan alamu me son yara ne.



        Tare suka waiwayo ita da mutumin,gabanshi yadan fadi ganin fuskar da bai taba zata ba,ya kafeta da idanu yana kallonta tare da son tabbatar da abinda idanuwansa suka gane masa,saidai ita din bata ma lura da kallon da yakeyi mata din ba,don tafi karkata hankalinta ga amatun

"Bilkisu" taji an ambaci sunanta,saita daga kai tana dubanshi itama kamar yadda yake dubanta,tayi mamakin jin ya ambaci sunanta,duk da cewa a zahiri batasanshi ba.



       Yanayin yadda take kallon nashi ya tabbatar masa da cewa bata ganeshi ba,sai ya saki murmushi saman kyakkyawar fuskarshi

"Banyi mamaki ba,don a zahiri dukkan alamu sun nuna rayuwa ta sauya daga bigiren data doramu akai zuwa wani daban,amma bari na miki bayani,Allah yasa zaki iya tunawa,kin tuna wani tsohon masoyinki abubakar saddiq?,wanda kukayi bankwana ranar da baba ya shaida min cewa ya bada ke?,aurenki xaiyi?" Tun kafin ya qarasa ta tuna dashi,sai yanzun kuma kamanninsa ke dawo mata,baikai ga kammala bayaninsa ba murmushi ya wadaci fuskarta,ta tunashi,mutum na biyu baya ga qannenta da taga damuwa saman fuskarsa sanda yaji batun auren,mutumin da ya taba nuna damuwarsa da kulawarsa akan rayuwarta,shi alkhairi komai qanqantarsa bai iya yiwuwa dan halas ya manta dashi,hakan yasa itama lamarin bai bacewa kwanyarta ba duk da cewa kamanninsa sun gushe cikin qwaqwalwar tata

"Yes....na tuna,kaine?" Ta fada cikin mamakin ganinsa,kusan shi ya fita mamaki,to amma baiso su tsaya wata doguwar magana,tunda zuwa yanzun dai indai anyi auren da mahaifinta ya fada din,to babu shakka ita din matar wani ce,don haka a taqaice yace

"Nine,ya bayan rabuwa?,da alamu sai alkhairi ko?,hala wanan babynki ce?,naga kamanni kadan" ya fada yana duban fuskar amatu,murmushi ta saki tana duban fuskar amatun itama,kusan bata taba jin wanda yace suna kamanni da amatu ba saishi,kowa mamakin da wanda suke kama yakeyi,saidai kuma jini ba wasa bane,wala'alla ta wasu guraren a iya tsinkayar kamanceceniyar tsakaninsu koda bata fuska kawai ba.



       Bai jira ta amsa mishi tambayarsa ta farko ba yace

"Yi haquri kada na tsaidaki,hala da daddynsu kuke tare ko?" Batasan ya akayi ta girgixa mishi kai ba,saida tayi hakan kuma taji me yasa?,murmushi yadan saki yanajin dadi cikin zuciyarsa,yana kuma fatan Allah yasa hasashensa ya zama gaskiya,ba shakka daya zama cikakken mai sa'a

"Ok,na gane.....single kike yanzun kenan?" Murmushi tadan saki tana kama hannun amatu

"Nidai bance ba" saiya sake sakin wani faffadan murmushi wanda yafi na baya qayatarwa

"To yaya ne?" Sai taja baya kadan tana da niyyar tafiya.



       Akaran kanshi shi ya sani cewa bilkisun ba irin tada bace,ko ada dinma ba gama garin mace bace kamar sauran mata,bare da ayanzun da komai nata ke nuna mai tsada ce ita,yasan cewa ba qaramin abu bane yasha kanta ta amince da qudurinsa,yasan zaiyi yaqine sosai kafin ya mallaketa,amma ko meye ya yiwa kansa alqawari cikin yan sakannin na gudu babu ja da baya,hakanan bazai tsaya kallon ruwa kwado ya masa qafa ba kamar wancan karon,saboda haka cikin hanzari ya rufa mata baya,ya kuma cimmata

"Saiki tafi ko sallama ba zaki tsaya kiyimin ba kuma?,bayan nidin baqo ne,ba wanda na sani a qasar,hasalima jiya na shigo" dan dubanshi tayi ta dauke kai fuskarta a sake ba'a daure ba

"Afwa,nabar yara ne,hankalina yana kansu,na gode sosai abbakar,sai wani lokacin ko?" Ranshi ya bata,ya kuma sha gabanta yana dubanta

"Yanzu irin wannan rabuwar ya kamata muyi kamar bamusan juna ba tsakani da Allah?,aiko guga baiyi tsiran komai ba yayi na igiya ko?,kya tsaya na tambayeki su hannatu da sauran jama'a" batayi mamakin yadda ya san su hannatu ba,don a lokacin sun soma saninshi kamar yadda shima ya soma saninsu,to amma batason tsaiwar tasu tare tayi tsaho,kowanne lokaci takanyi takatsantsan tsantseni da saka kula saboda idanun yaranta,wadanda Allah ya zubawa shegen wayo kaifin basira da ganewa.



       Gyara tsaiwarta tayi tana sake duba agogonta

"Nace nabar yara ne,kada su sake yin wani wajen su hadani da nemansu" kai ya gyada

"Gaskiya ne,shikenan to idan babu damuwa abani adress da phone num,kinga a matsayina na baqo na samu wajen zuwa hira ko 'yan uwana 'yan qasata,don da alama ku ba zuwan yau ko jiya bane irina,naji amatu ta iya wasu daga cikin yarensu" dukkan abinda ya nema wajen bamai sauqi bane,ba zata iya gaya mishi muhallinta ba,hakanan ita bamai jurar amsa kiran waya bace indai ba kiran 'yan uwanta ba,amma idan ta hada dukka ta hanashi xaiga rashin kyautawar ne,duk da tarin kirkin data fuskanci yana dashi,don haka ta langabar dakai kawai tace

"Ga phone num ina sauri later na baka adress din"

"Hakan ma na gode" ya fadi yana ciro wayarshi da hanzari daga aljihun trouser dinsa,ta jera masa numbers din ya saka sannan ya kirata,cikin sakanni qalilan kiran ya shigo wayarta dake cikin mitsitsiyar handbag din dake hannunta

"Ranki ya dade...sai a taimaka ayi serving tawa,kada na kira a rasa ganeni cikin dubunnan masu kiran" dariya ma ya bata,don dole sai data murmusa kawai.tana gyada kai,sa'an nan tayi masa sallama ta wuce,ya bisu da kallo har suka bacewa ganinsa

"Alhmdlh" ya fada yana jin wani dadi yana ratsashi,wala'alla alkhairi da rabon haduwarshi da bilkisun ya kawo tsaiko wajen maganar aurensa da rabi'ah,ya bude idanunsa yana sakin murmushi sannan ya juya a hankali shima don barin gurin.



        Ganin assadiq da tayi yau yasa ta dinga dan tuna wasu abubuwa da suka shude cikin rayuwarta,gwagwarmayar data sha fadi tashi da sauran wahalhalu na rayuwa,sa'ilin da takai qarshe saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,tana tuna Allah ne kadai yasan adadin yaran dake cikin wahala irin wadda ta taba fuskanta a yau,wasu sun fita kamar ita,wasu suna ciki har yanzu.



*****    *****    ******



     Motar qirar aston martin lagonda 2021 ita taci gaba da daukar hankulan mutane,tun daga wajen masarautar zuwa cikin masarautar,kowa na zuba idanu suga waye a cikin motar?,duk da cewa suna da masaniyar mutum daya tak shike da tarin iren iren wadan nan motocin na alfarma da kere sa'a kaf fadin masarautar,saidai kuma babu labarin cewa zayaso qasar kamar yadda aka saba a shekarun baya na samun labarin isowarshi duk lokacin daya tashi zuwa kwanaki qalilan kafin zuwan nashi.



      Bata tsaya ko ina ba sai data zo babban katafaren gini da yake mallakin macen alfarma,mai tarin izza da gado na sarauta gaba da baya wato fulani aisha,motar ta tsaya na wasu mintuna kafin qofa daya ta mazaunin dake baya ya bude na wasu sakanni,sa'an nan ya ziro qafafunsa daga bisani gangar jikinsa ta biyo baya.



       Yarima abdul'azeez abdallah mu'az kaisa ne ya bayyana,cikin wata irin siffa ta kamala,tarin kwarjini daya ninka na baya,kyau cikar haba zati da kuma izza,wanda kana masa duba qwaya daya tal xaka san cewa lallai Allah shike da zamani,hakanan lokaci kan wuce da wasu abubuwan masu tarin yawa,ciki harda quruciyarmu izuwa mataki na girma da kuma qaruwar shekaru,wanda shekarun ka qarawa wasunmu da yawa girma kwarjini hankali da nutsuwa,musamman idan akayi katari suka riski mutumin daya tashi tun daga zamani na quruciya bisa kyakkyawan bigire da turbar da zata kaishi zuwa ga wadan nan siffofi.



       To kusan hakan take ga yarima abdul'azeez,shekarun sunzo masa da tarin abubuwan da bai tsammacesu ba cikin shekaru bakwai kacal,ya canza ya zama wani irin cikakken matashi wanda ke kan ganiyar kyau quruciya ilimi suna tarin dukiya da sarauta,ya zama wani na musamman,hakanan ta fannin dabi'u akwai sauye sauye masu tarin yawa tattare dashi,wanda duk wani wanda ya sanshi a shekarun baya dana yanzu yasan da zaman wadan nan canje canjen.



        Kamar yadda mahaifiyarsa fulani aisha dake tsaye cikin varender dinta ta alfarma take kallonshi cikin alfahari,farinciki da tarin walwala da jin dadi na cikar burikanta,yaron nata ya zama irin mutumin datake masa mafarkin ya zama din,ba shakka abdul'azeez da guda ne amma tamkar da miliyan,irin yaran da samun kamarsu sai an tona,shi yasa albarka take bibiyarsa,hakanan ba zata gaza ko ta qasa wajen yi masa addu'ar samun dukkan wani abu daya saka a gabansa a rayuwa,hakanan bakinta bazai tana daina furta kalmomin samun dacewa a gareshi ba ranar gobe,saidai abu guda dakan rage walwala da farincikinta duk sanda ta dubi fuskarsa shine.



        Ya sake zama wani ZAKI mai saurin fushi,fada da kuma fusata,murmushi yayi qaranci da tsada mai yawa akan fuskarsa,kana iya jera zama na watanni dashi ba tare da kaga wannan abun da ake kira da murmushi saman fuskarsa ba,duk da cewa ta alaqanta faruwar hakan da al'amarin daya faru dashi abaya,kuma zarginta kusan yafi qarfi kan tabbas hakanne,amma tana ganin tunda yakai matakin da take da buri,to lallai watan watarana shima wannan batun zai wuce daga ranshi,ya goge ya zamana tarihi,ya kuma zama kamar bai taba faruwa ba.



       Kusan kowanne lokaci ta zauna tana mamakin me yasa ya kasa mantawa?


No comments

Powered by Blogger.