Saran Boye 41-45

 

41

        Cikin sati guda rak wani irin laulayi mai azabatarwa ya rafeketa ba tare da ita kanta tasan laulayin take ba,don sam anty zuhriyya ta kasa gaya mata,gani take abun saiyayi mata yawa,babu abinda take iya ci ya zauna cikinta qalau,koda ruwa ne sai anci babbar sa'a bare akai ha abinci,hakan ya sanya koda yaushe cikin qarin ruwa take,ta zabge ta sake yin wani fari bau,gefe daya ga wata rama ta musamman datayi,dukka kayanta basa zaunar mata a jiki sun mata yawa,don wani lokaci rigunan najwa zuhriyya ke kawo mata ta saka,saboda tana da dan jiki,hakanan batanson hayaniya ko hasken rana mai yawa,wani irin azababben laulayi daya sanya anty zuhriyyan ta dinga mata kuka a boye,idan ka ganta saika zaci ba zatayi raiba saboda yadda take azabtuwa,itakam.har fatan cikin ya zube anty zuhriyya takeyi cikin ranta

"Wannan baqar qaddara taki Allah ya yanke miki ita bilkisu" haka take yawaita fada,saboda ganin irin yadda takeshan wahala da cikin da batasan ma yana maqale a jikinta ba.       Wata guda cur da satittika wajen uku sukayi a asibitin,sannan aka dan fara samun sauqi,har zuwa sannan batasan da wani ciki ba,saboda bata cikin nutsuwarta bare hankalinta da har zata lura da wani sauyi ko wata alama.       Da wani yammaci ta farka a bacci da wani irin fitsari daya matsota,a lokacin anty zuhriyya tana sallah,idan tana wajen duk sanda zata bandaki saita rakata,qaunar ummin na sake qaruwa cikin zuciyarta dakuma tausayinta,yadda take mata ko najwa ce iyaka abinda zatayi mata kenan a matsayinta na uwa,ta aje dukkan wasu harkokinta ta tattara a wajenta,hatta da gida saidai taje lokaci bayan lokaci ta dawo asibitin,duk hankalinta da kulawarta tana kanta.        Ganin yau jikin nata da qwari qwari ya sanya ta zuro qafafunta qasa a hankali,ta saka takalmanta ta miqe zuwa bandakin,don yau itama ta tabuka ta ragewa ummin aiki.        Tana zuwa fitsari sai taga jini,batayi wani mamaki ba,ta kawo a ranta period dinta ce tazo

"Dama naga kamar tayi jinkiri wannan karon bata zo akan kari ba,ko saboda ciwon nan ne" ta fada tana yin tsarki sannan ta miqe,amma sai taji mararta ta riqe,tadan cije bakinta,ikon Allah,tasan bata ciwon mara idan tana al'ada,amma yaya akayi yau mararta ke mata ciwo?,ta tambayi kanta tana fitowa daga bandakin a daddafe.        Sanda ta fito ummi zuhriyya ta gama sallar carbi take ja,ta zuba mata ido ganin yadda ta fito a duqe,da sauri ta tambayeta

"Lafiya daughter" saidata zauna gefan gadon sannan tace

"Marata ce take ciwo ummi,kamar period ne inaga"

"Periode?" Ta tambaya cikin fargana da faduwar gaba,saita gyada kanta

"Eh"

"Jini kika gani!" Ta fada tana miqewa a hanzarce har bilkisu na mamakin dalilin rudewarta haka,saita sake gyada mata kai

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ta furta sannan ta durfafi qofa da hanzari,binta kawai tayi da kallo cike da mamaki,toko bai kamata ace tana period bane?,tayiwa kanta guntulalliyar tambayar da bata da amsa.      Sanda likita ya iso ya dubata saiya tabbatarwa da anty zuhriyya wahalar data sha ne bakin mahaifar ke niyyar budewa,saboda haka dole su bata bedrest again kona wata daya ne su gani.      Lokacin da suke bayanin kawai kallonsu take,kanta a daure tamau,ta kasa fahimtar komai,mahaifar waye zata bude?,waye keda ciki?,kuma wa za'a bawa bedrest?,duk da tambayoyin dake cin kanta bata iya furta ko guda daya ba,taci gaba da binsu da kallo ne harya gama abinda zaiyi ya fice,dakin ya rage daga ita sai anty zuhriyyan.       Ta lura da dimuwar da bilkisun ta shiga,da yadda take dan kallonta,da alamu tambaya ce fal kanta,tasan dama dole hakan zata kasance,tunda taji wasu magangun da bata gane kansu ba daga bakin likitan,don haka saita janho kujera zuwa bakin gadon da take kwance,ta zauna idanunta kan bilkisun,tana wassafa tare da tsara yadda zata mata bayanin da zai kwantar da hankalinta,duba da yanayin da take ciki,saboda rufewar ba zata amfana komai ba,face sanyata cikin tunani da kuma wani rudanin na daban.      "Daughter....nasan a rayuwa,daga sanda nake tare dake zuwa sanda bama tare,kin fuskanci abubuwa da dama arayuwarki,kin kuma rasa abubuwa da dama,kuma dukka kin juresu,rayuwa mataki mataki ce,kowanne mataki na jarrabawa idan yazo.maka kayi haquri kana iya cinyeshi yakuma wuce kamar ba'ayi ba,komai yayi farko tabbas yana da qarshe,kiyi haquri bilkisu....kina da juna biyu,wanda shine kusan silar ciwonki" wani irin abu taji yazo ya cake mata a maqoshi,ba don babu wasa tsakaninta da anty zuhiriyya ba da sai tace wasa antyn take mata,amma tasan babu wannan tsakaninsu,wani irin abu takeji yana mata yawo saman ka,kalaman antyn suna bangazar juna kamar xasu wargaza maya qwaqwalwa,saita rintse idanunta tana furta

"La haula wala quwwata illa billa" daga haka bata sake furta komai ba,bata sake cewa komai ba,saidai wani abu daya tsaya mata a wuya bata samu ya sauka ba har sai ranar da aka sallameta daga asibiti,sanda ta isa dakinta ta kwanta saman gadonta ita kadai,tana lissafin abinda yake cikinta,cikakken dan halas ne ko kuwa akasin haka?,ina ubansa?,tananda tutiya ko zarrar da xata nuna ubanshi harta furta shine yayi mata cikin da take dauke dashi a yanzu?.     Kuka ne mai wani irin nauyi a qirji da zuciya ya kubce mata,ashe haka matan dake yin cikin shege suke ji?,ashe haka suke tsintar kansu?,wanne irin bayani zata yiwa 'ya ko dan cikinta a duk sanda ya girma ya nemi mahaifinsa,shin ta yiwa rayuwasa ko rayuwarta adalci?,ta hanyar data cancanci a samar dashi kenan?.       Wadanne irin mutanene wadan nan da babu halin girma ko dattako cikin jininsu?,wadanne irin azzalumai ne su da suka zabi rayuwarta cikin miliyoyi suka tarwatsa ta,meta musu ne haka suka hanata cimma dukkan wani buri na rayuwarta,matsalarsu dai a kullum ita ke dakatar da ita daga samun duk wani ci gaba,a duk lokacin data yunqura don ci gaban rayuwarta saisun daqileta,wancan karom sune silar karatunta,wannan karonma dukkan alamu sun nuna sune zasu zame mata tarnaqi.        Tayi kuka mai yawan gaske,irin kukan data kwana biyu bata yishi ba,har zuwa wayewar gari,yadda idanunta suka tasa ya sanya anty zuhriyya ta fahimci irin kukan data yi,fada sosai ta dinga yi tana bala'i,saboda har yanzun ranta a bace yake itama,wani da bilkisu take kan me yasa zata zauna tana kuka,yayin da mafi yawa kuma dukka kan masarautar kaisa ne,wanda basusan halin da ake ciki ba.      Sai data gama son ranta sannan ta sauko,taci gaba da lallashin bilkisun tare da kwatanta mata illar bacin rai da damuwarta ga lafiyarta.       Ba qaramin jajircewa anty zuhriyya tayi ba wajen ganin ta daidaita lamari da yanayin bilkisun,wanda sai bayan kwanaki data tabbatar ta sake warwarewa ta nemi abbaa ya bata izini zataje tayi magana da malam bilya,daga nan su sanar da masarauta,don ta inda aka hau ta nan ake sauka,bai musa ba mata ba ya amince mata,don haka ta sanya lokaci yammaci liqis sanda tasan za'a iya samunsa a gida ta sanya bilkisu ta shirya suka nufi gidan.          Cikin doguwar riga take purple,saqar qasar dubai,ta yafa mayafin doguwar rigar kawai saman kanta ba tare data nannadashi ba,mai kawai da turare ta sanyawa jikinta,amma idan ka kalleta sai kaga ta qara wani kyau na musamman,kai kace an mata amfani ne da wasu kayayyakin gyaran fata na musamman,saidai tana nan babu qiba ko kadan tattare da ita,plate din takalmi kawai ta zira,ko wayarta da anty zuhriyya ta sauya mata zuwanta gidan bata dauka ba ta fito suka wuce,daga ita sai antyn sai hisham wanda bilkisu ke riqe dashi saman cinyarta,antyn tana tuqi.        Sanda suka isa gidan ana kiraye kirayen sallar magariba,wasu da yawa sunata daura alwala suna tafiya zuwa masallaci don samun jam'i.      Suna shiga gidan bayan sun faka motarsu qofar gidan malam bilya yana fitowa daga cikin gidan,cikin hanzari jikinsa jiqe da ruwan alwala,yana ganin zuhriyyan gabanshinya fadi

"Jarababbiya masifaffiya,ko dame kuma tazo" ya fadi,amma gefan ranshi yana jin dadin yadda bikisun ta warware sarai fiye da sanda ya ganta a asibiti.       Itace ta soma magana

"Munzo ganinka,gashi kuma kana shirin fita" tayi maganar fuskarta a daure tamau,wannan furucin ya sake sanyawa gabanshi ya fadi

"Da wata aqasa kenan" ya fada a ranshi

"Ku shiga ku jirani,zanje nayi sallah na dawo" bata amsa mishi ba ta juya tayi ciki,tabar bilkisu na gaidashi kafin itama ta biyo bayanta.        Umaima da aminatu ne a falon da alama salla suma zasuyi,,suna ganinta kowacce tasoma rige rigen isa wajenta,suka rungumeta cikim jin dadi,itama rungumesun tayi tana jin dadi,don tayi kewarsu sosai,tunda tabar gidan anty zuhriyya bata sake barinta tazo gidan ba,saidai tayi musu dukkan abinda tace zata yi musun,kuma taga alamun sauyi da canji tattare dasu,bata taba kawowa cewa qaddara zata sake rabasu ba,ba zata sake barinsu su zauna tare ba.       Murnarsu ta fiddo da hannatu dake cikin bandakinsu tana musu wankin unifoarm,itama murna ce ta cikata,suka baibaye bilkisun kowa yana son bata labarai gami da tambayoyi,anty zuhriyya na zaune saman kujera tausayinta na ratsasu,ta wani fannin kuma suna bata matuqar sha'awa na yadda suke qaunar junansu da kuma yadda suka saba,bata ankara ba taga tuni sun janyeta zuwa dakinsu,saita saki murmushi kawai tana kada kai.      Murmushin nata ya katse sanda anty ta shigo falon,sai anty zuhriyyan ta hade ranta tsam,don ta gama karanatar kowaccensu,itama antyn bataga wajen wargi ba,don haka ta gama abinda ya shigo da ita kawai ta fita.         Babu jimawa umma katti ta shigo,saita soma washe baki ganin zuhriyya,ita kuwa babu abinda ya sauya dangane da yanayin fuskarta

"A'ah,zuhriyya ce a gidan namu?"

"Nice" ta bata amsa a taqaice

"Maraba lale,kyazo ki zauna shuru ke kadai,aiko bamu zauna da maimunatu ba kya nemeni" wani kallo tayi mata tana tabe baki,rainin hankalinta ma yaso zarta na kowa,saidai duka zataji dasu,sa'arsu daya ma yanzu bata tasu take ba,da kowacce saita kwashi kashinta a hannu,don tanajin ciwon riqon da sukewa diyoyin mijin nasu,riqo na zallar jahilci qauyanci da kuma son kai.      Banza ta baiwa ajiyarta harta gama sunadin surutunta,wanda yafi kama da tabarmar kunya tabata waje sanda malam.bilya yake shigowa ya umarci a bashi ruwa yasoma sha tukunna,mama ladi dake da girki ta nufi kitchen don kawo masa.        Tana daga zaune anan ta qwalawa bilkisu kira,ta kuma jiyota,sai gata ta fito,ta qaraso a hankali ta samu gefan anty zuhriyya ta zauna,kanta a qasa,batasan yaya baban nata zai amshi lamarin ba,kuma ta yaya za'a samu warwarar qullin.       Duban gefanta tayi ganin mama ladi xaune dafa'an,bisa dukkan alamu tana nufin gabanta za'ayi zancan kenan,don haka ta dubi malam bilya

"Kaman baka shirya zaman ba,don naga wadanda ba ahalin maganar ba zaune a wajen" ya gane sarai dawa take,don haka ya dubi ladi

"Ladi...bamu waje" haushi ne ya cikata,haushin zuhriyya take ji,don ta fuskanci bata daukar raini,hakanan bata daukesu a bakin komai ba

"Kome meye muna zaune zamuji" ta fada tana shirin fita

"Daga baya kenan,wai anyi sadaka da karuwa" anty zuhriyya ta bata amsa.       Sai data fice sannan ta dawo da dubanta kanshi,takaici yana cin ranta tace

"Malam bilya,shukar da kayine nazo shaida maka lokacin girbinta yayi,wala'alla babu wannan cikin tsari hasashe ko shirinka ko?" Dubanta yake cikin rashin fahimta,sai kuma ya hade rai wai karta kawo masa wargi ko raini

"Kamar yaya,me kike nufi?,kefa baki rabo da jarfa,idan zakimin bayani kiyimin" gyara zamanta tayi yana amsa mishi

"Shi zan maka yanzu" sai taga baima kamata aci gaba dayin maganar a gaban bilkisun ba,saboda haka tace tatashi ta koma,cikin matuqar mutuwa da sanyin jiki ta miqe ta fice daga falon.       "Diyarka kuma diyar maimunatu da ka bada hayarta...don haya shine sunan da yafi dacewa da aurenta,taje ta kuma dawo maka da tsarabar jika,in sauqaqe maka dogon nazari,yanzu haka juna biyu gareta" wani irin gumi ne me dumi ya karyo masa,idanunsa dukka a waje yace

"Kamar yaya zuriyya,me kike fada ne?"

"Abinda kunnuwanka suka jiye maka" ta maida masa cikin gatse da matuqar jin haushinsa. Baisan sanda ya zame hular kanaa ba yahau firfita gami da ambaton

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"._afwan,kuyi manage yau yayi guntu🙏🏽🙏🏽_


_ale bilya na gaisuwa,yace ku tayashi da addu'a🤲🏽😝_


42

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899

Ko

09033181070

      Tsayin lokaci yana firfitar gamida mai maitaba innalillahi,ita kuma tana zaune tana kallonshi tare da mamakin rudewar tasa,shi duka baiyi wannan lissafin ba,ko tsabar rainin hankali ne kawai.          A hankali ya aje hularshi gefe sannan yace

"Yanzu meye abunyi?" Baki ta tabe

"Bansan muku ba,tunda badani aka qulla ba,abinda na sani kawai shine,ta inda aka hau tanan ake sauka,kasan dukka hanyar da zakabi ka sanarwa da uban cikin ajiyarsu dake jikin 'yata,bama buqatar wani abu face su kwana da sanin akwai jininsu a jikinta" daga haka ta yunqura ta miqe,sai yayi saurin dakatar da ita

"Ya zaki tafi kuma?" Kallon banza tayi masa

"To ce maka akayi dama zama nazo yi?,saqo nazo isar maka,kuma tunda ya isa shikenan" daga haka ta juya tayi ficewarta daga falon,ta tsaya ta kirayi bilkisu suka wuce.      Tashin hankalin da bai tana zaton zaijishi ba shi yakeji,gumi ne kawai ke yanko masa ta kowanne sashe da loko na jikinsa,bai taba hasashe ko tsammanin faruwar hakan ba,bai taba kawo hakan zai iya faruwa ba,ko kallon mama ladi dake faman tambayarsa abinda yake faruwa cikin salon bugun ciki baiyi ba.      Zumbur ya miqe yana maida hularsa dake ajiye dafa'an a gefe saboda hasashen da qwaqwalwarsa ta bashi

"Ina zaka haka kuma malam?,wai wanne irin jarababben albishir wannan masifaffiyar matar tayi maka daya daga maka hankali haka,bayan nasan babu kalar abinda baka gani ba"

"Rayuwar 'yata....." Kawai ya fada yana yin gaba.       Yana tafe shi daya yana zancan zuci da qananun sumbatu,tabbas ta inda aka hau tanan ake sauka kamar yadda zuhriyya tace mishi,dole susan da zaman cikin,saidai bashi da wani yaqini ko tabbacin xasu amshi maganar,tunda sun riga tunda fari sunzo da dukkan sharudda nasu,shi kuma ya karba hannu bibbiyu ya amince musu,a lokacin da idanunsa suke a rufe,matsera yake nema kawai da hanyar da zai kubuta daka dukan da talaucin yake masa tako ina,bai tsaya wani dogon nazari ko tunani ba,sai gashi yau wannan al'amarin ya sameshi bagata tan.      Baiyi burki ko ina ba sai qofar gidan umma luba,wanda idan ka ganshi a yanzu ba zakace shi bane,saboda rushe mata shi akayi gaba daya aka sake mata sabon gini me bene,aka qawatashi da qaramin gate da fenti mai kyau harda shukoki,bayan umarar da sukaje tare da malam bilya din,da kuma kudade da aka danqa mata wanda suka isheta jari,bayan matsayi da fulani ta sake qara mata a masarautar kaisan.        Bakinsa cike fal da addu'ar Allah yasa tana nan ya sake gyara tsaiwarshi ga qofar gidan,ya kirayi wani yaro dake shirin giftawa,ba musu yaron ya qaraso da hanzari

"Shiga gidan nan maza  kace ana sallama da luba" ya amsa mishi sannan ya tura gate din gidan ya shige,babu jimawa ya fito ya gaya masa tana zuwa.      Shudewar mintuna biyu aka taba qofar sannan aka budeta,umma luba ta bayyana,ganin malam bilya saita saki murmushi,har haqorin makkan data maqala yana bayyana

"A'ah,dama kaine.....aida ka shigo daga ciki ko?"

"Shigowar nan kuwa zata yiwu?,don gsky a gaggauce nake" cikin mamaki take dubanshi

"Koma meye ai shirin zaune yafi na tsaye ko?" Bai sake tankawa ba yabita a baya,basu tsaya ba har zuwa madaidaicin falon gidan,da aka qawata da kayan zamani.       Suna zama ta kira mai aikinta ta kawo masa lemo,don yanzun me aiki gareta,wadda take kula mata da gidan idan ya tafi gidan maimartaba

"Bar lemon nan luba.....babban tashin hankali ne ta tunkaroni ko ince ya tunkaromu" qirji ta dafe cikin razana ta fidda idanu

"Mun shiga uku!,wani abune ya faru?" Sai daya sanya gefan babban rigarsa ya sharce gumin fuskarsa,duk da sanyin acn dake falon wanda umma luba ta qure tana morewa jin dadin duniyarta,takan ce sai tayi qara'i yadda ya kamata,tunda hutun baizo mata a quruciya ba,yanzunma da yazo mata duk daya wai mamaci ya karye.       "Bilkisu 'yar wajena,mai gado,juna biyu gareta....juna biyun yarima"

"Tashin hankali!" Umma luba ta furta tana zama sosai saman kujera gamida fidda idanunta waje sosai,kamar wadda bata gani,zallar tashin hankalin data furta a bakinta yana bayyana qarara saman fuskarta

"Wannan wanne irin bahagon lamari ne,ya akayi haka ta faru?,me yasa dukkanmu bamuyi tunanin yuwuwar afkuwar hakan ba?" Ta qarashe maganar tana kallon malam bilya,karon farko a bigiren farko da yaji kishin jininsa,don haka saiya hade rai tsam,shima yaso yadan motsa qwanjinsa wannan karon ko yaya ne,kamar yadda yaga zuhiryyar tayi

"Oho,wannan kuma bani zaki tambaya ba,abu daya ne,kawai ki shaida musu abinda ke faruwa,so ake su sani kawai,bawai wani abu ake bida daga wajensu ba" shuru tayi tana juya maganarsa cikin ranta,kowanne daya cikin biyun zai iya yiwuwa,imma dai idan tayi shuru nan gaba har aka haife abinda aka samu ta shiga sahun masu laifi wajen fulani,wanda hakan zai jawo mata matsala,inma kuma taje ta shaida mata hakan ya zama tashin hankali ko kuma ya ballo da wani ruwan,to kowanne tayi ciki tana zato da kokwanton babu mafita,amma kuma da ace shurun tayi wani abun ya bullo bayan watanni suyi kuka da ita,gwara ta shaida musu tun yanzun sunsan da maganar.       Shaidai malam bilya miqewa yayi ya kade babbar rigarsa ya qara gaba,saidai koda ya isa gida kasa shiga yayi,yayi zaune anan qofar gida lamarin na masa kai kawo,yana jujjuyashi cikin ransa tare da hasashen meke iya faruwa nan gaba,wala'alla hakan ya qara masa daukaka da girma na hada jini da masarauta,wala'alla kuma ya sake fadawa wata daban.       Dukkaninsu shi da umma luban a wannan daren basuyi wani isashen barci mai dadi ba,kowa da zancan ya kwana a ranshi yana juyashi tare da taraddadin meye zai biyo baya?.       Washegari sam bata da agender na shiga masarauta,a yadda ta tsara sai jibi,amma zuwan ya zame mata tilas don isar da wannan saqo zuwa kunnuwan fulani,don haka tun goma na safe ta gama shirinta ta doshi masarautar kaisa.       Sanda taje akwai baqin da fulanin ke ganawa dasu,tadai shaidawa jakadiya zuwanta,ita kuma ta shaidawa fulani,sai kuma tayi zaman jiran ayi mata iso.      Lokacin da aka bata izinin shiga ita kadai tasan yadda ta dinga ji,gumi ya dinga karyo mata,qafafunta babu qwari ta dinga kutsa kai falon,cike da taraddadin sakamakon da maganar zata bayar.      Sanda ta shiga tana zaune saman daya daga cikun kujerun alfarma dake wajen,fuskarta a sake take duban luba harta qaraso,ta zube cikin girmamawa a gabanta

"Allah ya taimakeki....ya baki yawan rai...Allah ya iya miki yakuma dafa miki,ya danqwafar da maqiyanki,ya qasqantasu a gabanki.....barka da warhaka ranki ya dade" murmushi tayi har cikin ranta tana jin dadin addu'ar da luba tayi mata

"Yauwa sannu luba,barkanmu....ya iyali"

"Kowa lafiya Allah ya baki yawan rai"

"To madalla,haka mukeso" shuru umma luba tayi tana jujjuya maganar,harsai da fulani ta fuskanci akwai magana bakinta,ta dago tana gyara zamanta sosai sannan tace

"Lafiya dai ko?" Kanta zuwa gefan fuskarta ta shafa,tana jin wani irin rashin sukuni

"Lafiya amma ba lau ba"

"Uhmm,gaggauta sanar dani,meye yake faruwa?" Zama tayi sosai dirshan,don a jikinta tana jin cewa maganar ba qarama bace

"Wato Allah ya baki yawan rai,jiya da daddare bayan sallar isha'i,mahaifin yarinyar nan da aka yiwa auren shekara daya da yarima Allah ya qara masa lafiya.....yazo ya taddani har cikin gida..." Saikuma tayi shuru,cikin sakanni da basu wuce biyu ba yanayin fuskar fulani ya sauya,ta zuba luba idanu tana kallonta

"Uhmmm,ina jinki,ina fatan jin badai wani abunne zai biyo baya ba,tunda mun riga da mun gama tsarawa da kuma qulla dukkan wata yarjejeniya dasu ko?"

"Allah ya taimakeki,tuba nake,amma kusan kamar baya ce ta haihu"

"Ki hanzarin fayyacemin komai,baya ce ta haihu kamar yaya?" Ta sake tambayar luba kamar mai shirin miqewa tsaye

"Yarinya dai juna biyu gareta" ta fada a hankali kamar batason fadar.
        Wani irin rugugin aradu ne ya gifta saman kan fulani aisha,zuciyarta ta wani damqe waje guda na sakanni

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un?,garin yaya haka ta faru?,ya akayi haka?,ya akayi wannan kafar ce kawai.suka bari basu tosheta ba?,saboda tayi tunanin yariman zai kauce mata da.kanshi,tayi tunanin ko bata toshe ta ba shi xai toshe da kansa,tunda yasan irin auren da nau'insa,amma ya akayi basira ta bace mata bata jaddadawa sodangi ba?,me yasa basira ta bace mata bata gayawa ita kanta luba din ba?,ya akayi basira da wannan tunanin aka daukeshi cak daga kwanyarta?,me yake shirin faruwa?,tonuwar asirinsu?.      Batasan ta miqe tsaye har tana safa da marwa ba saida kalaman umma luba suka dawo da ita hayyacinta

"Allah ya huci zuciyarki,ki dade ki qarko,babu abinda zai faru fiye da abinda kike son ya farun"

"Kije zan nemeki" shine amsar kawai data iya baiwa umma luba,saboda ba al'amari bane da zata yanke hukunci da hanzari ba,akwai buqatar tayi zuzzurfan tunani akai,tunanin da ita daya take buqatar yinsa,ta kuma yanke shawarar abinda zai fishsheta,don wannan karon bata da buqatar kowa yaji ko yasan me ya kuma afkuwa.       Da hanzari umma luba ta miqe tana godiya,sallamar data mata a lokacin tayi mata dadi,don dama Allah Allah take ta matsa daga wajen,saboda kwarjinin fulanin dake sake sanyata cikin firgici da dimuwa.      Wunin ranar kaf cikin wani mawuyacin hali tayishi,maganar taketa maimaitawa tana dorata bisa mizani iri daban daban,duk hukuncin data bata sai taga batayi mata ba,tabbatuwar cikin da wanzuwarsa tamkar barazana ce ga duk wani sirri nata da kuma rayuwar azeez,zubewar mutuntakarta taba qima sa darajarta data ahalinta gaba daya.       Ranar kaf bata sake bari kowa ya ganta ba,har zuwa dare sanda take zaune gefan gadonta sanye da kayan bacci,hannunta dauke da cup tana kurbar tea wanda ta tilastawa kanta sha don kada ta kwanta da yunwa,maganar ce dai a ranta take sake juyata gami da yi mata fashin baqi.      Dire cup din tayi da sauri,saboda wata magana da tayi amsa kuwwa cikin kanta

"Karki zama shashasha mana.....daga sun fadi magana ki dauketa gaske..." Maganar ta shigeta sosai,sai tayi tsam da hankalinta tana dora maganar kan ma'auni

"Tabbas talakawa ne wadanda basu da komai,mahaifinta ma'abocin son abun duniya ne,babu wanda yake irin yanayin da suke ciki,wanda xai shiga daula irin haka kuma lokaci daya ayi handing over dashi ya yarda ya karba,ya kuma fita salin alin ba tare daya qirqira wasu abubuwa da zasu biyo baya ba,kudi qalilan sukan ruda irinsu,su kuma sauya musu hali da alqibla,ba shakka zasu iya komai saboda komai yaci gaba da tabbata tsakaninsu,waya sani ma ko sun qirqiro maganar ne don suyi blackmail dinsu.      Murmushi ya kubce mata,sanda ta tattara dukkan bayanan da kwanyarta ta bata na cewa qarya suke,babu wani ciki,sunaso ne kawai suyi amfani da wannan hanyar su dinga tatsar dukiya daga garesu

"Da sun sani bata haka suka biyo ba,tabbas basu san wace aisha ba,da sun fadi abinda sukeso kawai cikin girma da an basu,albarkacin igiyar auren data taba gittawa tsakanin d'ana da d'iyarsu" ta furta a sarari,tana miqewa,sai a sannan taji duk wani nauyi da kanta yayi,da cushewa da cikinta yayi ya warware,har taji wata yunwa,sannan taji tana buqatar abinci,don haka tamiqe ta fito don bada umarnin a gabatar mata da abinci.


   ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶


      Hakanan cikin daren bacci suka qauracewa idanuwansa,ya takurawa kanshi da tuhuma da tambayar me yake damunshi ne haka a kanta,sau nawa ya ganta da zata zauna haka cikin zuciya ruhi da kuma gangar jikinsa,har yake jin kamar yabar wani abu nashi tattare da ita?,kodon itace mace ta farko daya soma sharing ainihin abinda ake kira da rayuwa da ita?.      A hankali ya dauko wayarshi dake dake aje a gefe,hakanan saiya samu kanshi da bude tsohon saqo,tsohon saqon da bai sake bi ta kansa ba tunda aka turo mishi,tsohon saqon da bai taba tunanin xai waiwayeshi ba,sai gashi yau ya samu kanshi da budewa,saqon da ammi ta tura masa na hotonta tun lokacin da ake zancan hada aurensu,yana tunanin idan ya gan hoton zai samu relief.       Saidai tunaninsa ya saba,wani irin abu yaji yana ratsa zuciyarsa,wani irin feeling mai kama da kayi kewa da abinda kayi matuqar sabawa dashi,hankalinsa ya sake tashi fiye da dazun,don haka ya aje wayar ba tare daya fita daga gun hoton ba ya miqe.     Bandaki ya fada kai tsaye,ya sakarwa kansa ruwa,wanka yayi cikin mintina ashirin,sannan ya fito ya soma shiryawa.      Cikin lokaci qanqani ya gama shirinsa cikin wani kyakkyawan yadi da yaji aikin sarauta,yayi masifar dacewa dashi hakanan ya fidda ainihin shi din waye,sai da yagama feshe jikinsa da turarukansa sa'annan ya duba agogo,ya tabbatar yanzun ammi batayi bacci ba,idan ma ba abincin dare take ci ba,to bata jima da gama ci din ba,mai yiwuwa suna falonta ita dasu afnan,kamar yadda takan zauna dasu a yawancin lokuta.43

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899

Ko

09033181070
       Kamar yadda ya zata din kuwa,sanda ya isa sashen ammin tana saman katafaren dining din da aka cika da nau'in girke girke tana cin abincin dare,afnan kuwa na saman kujera zaune riqe da handout tana dubawa,daya daga cikin bayin dake aiki a sassan tana duqe gabanta tana gyara mata qafarta,sai sumaira dake kwance saman kujera tana charting,sanyin ac ne gaba daya ke ratsa falon,sai tv dake aikinta ita kadai ba tare da kowa ya damu da ita ba a cikinsu,don kowa da akwai abinda ya sanya a gabanshi.       Sallamarshi kadai ta saka kowa cikin taitayinsa,baiwar ta zube ba tare data iya kallonshi ba ta soma gaidashi,hannu ya daga mata,kana ta miqe cikin sauri da hanzari ta soma tattare kayan amfaninta,don dama ta gama yiwa afnan din

"Barka da warhaka yaya" duka suka hada baki wajen fada tsakanin afanan da sumaira,cikin qasaita muryarsa can qasa ya amsa musu,afnan ta kare fuskarta da littafi kana murguda baki tana hararar sashen da ya nufa wato wajen ammi fulani,cikin ranta tana mita

"Wannan duk randa ya zama sarkin ma ai mun kade,kullum fuska kamar kashin shanu,amma duk da haka ya sake dado wani daurewar fuskar saboda mugunta". Sumaira kam tuni ta sauko ya kwashe headphone dinta da charger dinta ta wuce daga falon da nufin sauya falon,sai afnan din kawai ta bari,wanda dama yawancin lokaci ita kadai ce ke iya zama waje idan yazo wajen ammin tasu.      "Barka da warhaka ammi" ya fada bayan ya zauna kan kujerar dake fuskantarta

"Ka yini lpy" ta jefa masa tambayar tana sake mamakin yadda gaba daya cikin lokutan take ganin sabbi da baqin al'adu tattare dashi,duk da ta sani cewa shi din miskili ne,wanda bayason yawan magana,mai qarancin fara'a,amma dukka wadan nan halayen nasa sun sake qaruwa tare da daukan sabon salo

"Lafiya alhmdlh" ya amsa mata,saita aje cokalin hannunta,tana hade hannayenta waje daya

"Kullum nakan qaryata lafiyarka da kwanciyar hankalinka,don yanayinka da fuskarka basu nuna hakan" sai daya dan kalleta,kana ya kauda kai

"Babu komai fa" shuru tayi kamar mai tantama akan maganar,sannan tayi ajiyar zuciya,ta dauki cokali ta soma ci gaba da cin abincinta ta sake cewa

"Amma....meya hanaka har yanzu ka zabi makarantar da zaka ci gaba da karatunka?"

"Ina nazari ne har yanzu" tsaida taunar da takeyi ta dubeshi

"Nazari kamar yaya?....kaga....na baka nan da jibi,lallai lallai kazomin da sunan makarantar daka zaba,kuma ba'a qasar nan ko maqociyarta ba"

"To" kawai yace mata,don ya kauda yanayin saiya miqa hannun ya dauki tataccen ruwan inibi dake cup,wanda ammin ta zuba da niyyar sha ya soma kurba.       Rabin kofin yasha sannan yadan kira sunan afnan,ta amsa tana aje handout dinta ta taso,da hannu ya mata nuni ta zuba masa abinci,ta tsani wannan miskilancin nasa,dom haka saita nuna kamar bata fahimta ba,maimakon ya bata amsa saiya dauki wayarshi ma ya soma latse latse ya barta nan a tsaye,saida ammi tace

"Ki zuba mishi mana kin tsaya saman kan mutane" qafa tadan buga sannan ta zumbura baki ta soma zuba mishin,ta gama ta saka mishi cokali ta sauka ta dauki handout dinta itama ta fice kamar yadda taga sumaira tayi dazun.      Jan plate din yayi gabansa yasoma ci,akwai tambayar da yakeson mata amma baisan yadda zata amshi kota kalli tambayar ba,haka ya dinga cin abincin yana gwada ta yadda zai tambayetan,kafin daga bisani ya tattara dukkan gwanintarsa yace

"Sun aiko sun fadi adadin abinda suke buqata kuwa?" Ya jefa mata tambayar,saboda ya tabbatar kudi ne suka rudesu har suka yarda suka aikata abinda suka aikata din,don haka zasu biyo ba'asi daga baya na kudin da akace su fadi nawa sukeso,qila ta wannan hanyar zaiji wani abu,ko yaya daga garesu.        Mutum ne shi da bayason mutum mai kwadayi ko son abun duniya,amma baisan me yasa ita bai ganinta da wannan abun ba,baisan me yasa ya kasa mantawa da ita ba.       Cikin rashin fahimta ammi ta dago tana dubanshi

"Wa kenan kake nufi?" Rasa yadda zai mata bayani yayi,sai daya hade lomar bakinsa sannan yace

"Yarinyar da aka turan mexico" wani irin hade rai da bai taba gani saman fuskarta ba ammin tayi,ta wani gefen gabanta yadan fadi,ta kafeshi da ido,yaji a jikinsa kallonsa take,amma saiya basar yaci gaba da cin abincinsa kamar bai gani ba.       Dama ta kusa qoshi da abincin,maganarsa tasa sauran wajen da zata zuba abincin ya cike,saita ja kujerarta baya tana ci gaba da tsareshi da ido,a hankali cikin muryar dake bayyanar da bacin rai tace

"Meye hadinka dasu?,meye damuwarka da sun aiko ko basu aiko ba?,abdul'azeez,ina fata baka manta da maganarmu ta qarshe ba kafin in turo maka ita,ka sakata a idanunka banda zuciyarka,karka yadda ko gefen zuciyarka taje,idan taje din akwai matsala,saboda ita din ba kininka bace,sannan ita din ta wucin gadi ce a wajenka,abdul'azeez...koda wasa banason na sake jin wata magaba makamanciyar wannan daga bakinka....har abada"

"Afuwan" ya fada cikin girmamawa,daga haka shuru ya biyo baya,saita miqe tana sauka daga wajen,da alamu ranta ya baci ne.      Shima bai wani ci gaba da cin abincin ba,cokali biyu ya qara ya miqe ya sauko daga wajen,ya mata sallama ya fito.       Kan hanya ya dinga jin kansa yana wani daukan zafi,ranshi yana baci,baisan ainihin dalilin ba,amma yakan tuna bai samu jin komai daga wajen ammin ba,yana jin wani feeling mai qarfi nason karya zuciyarsa,irin feelings din da baisan menene ba.      Maimakon ya zauna a sashensa kamar yadda ya tsara,sai yaji ya kasa zaman,ya dauki wayoyinshi kawai ya fito,ya soma takawa cikin gidan sarautar yana nufar sassan da xasu fiddashi daga gidan,ya dinga wuce qofa qofa gate gate,akwai tazara mai dan yawa tsakanin ainihin sassansu zuwa babbar qofar da zata fitar dakai daga gidan sarautar gaba daya,amma haka yaci gana da takawa,yanajin tafiyar kamar zata debe masa kewa ne,yana tsaka da wannan tattakin wayarshi ta dauki tsuwwa,sunan safwa ya bayyana,sai yayi rejecting kiran sannan ya kashe wayar gaba daya ya jefata a aljihun wandonsa.******    ***"""*****   *******     Kasa zama tayi lokacin da fulani aisha ta yi kiranta,tana son taji wacce amsa ce zata fito daga bakinta?,idan har ta amshi cikin ne tasan cewa lallai ita din tazo duniya a sa'a,ta soma aiki a masarautar kaisa da qafar dama,hakanan kakarta ta kuma sake yanqe saqa kenan,zata samu arziqi da alherin daya ninka na baya,idan kuma akasin hakan ta faru to dole kowannensu ya amshi hukuncin,don basu da qarfi ko qwanjin da zasuce zasu ja da hukuncin.        Yau din cikin matuqar daurewar fuska ta fito,wanda hakan ya sabbaba faduwar gaba wajen umma luba,tun fulanin ma batace komai ba.       Sai data gama dukka tattakinta sannan ta tsaya gabanta,ta dubeta da kyau cikin kaushin murya

"Ki gaya musu cewa wannan maganar cikin labarin qanzon kurege ce,qirqirarren labari ne da aka samar dashi saboda ayi wasa da hankalin masarauta,ki gaya musu,basusan wacece fulani ba,ki shaida musu sunyi kuskure,da sun sani kansu tsaye sun fadi adadin kudaden da suke da buqata...komai yawansu fulani tafi qarfinsu,amma bawai su biyo ta wannan hanyar ba,ki sake shaida musu cewa....ban tura ta mexico na hadata da yarona don tayi ciki ba,ban tura bilkisu mexico don ta dace dashi ba,na turata ne tamkar ma'aikaciya ta wucin gadi,saboda sanin kansu ne ce cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,saboda haka ki jadda musu,hawainiyarsu ta kiyayi ramata,kudi kuwa ko nawa suka yanke suna da buqata su shaida miki,gari bazai waye ba zai tabbata a gabansu,kudin da zai zamo abu na qarshe da zai shiga tsakaninmu kamar yadda muka tsara bisa yarjejeniya....kije ki shaida musu...ruwansu su haqura da batun ciki....ruwansu suci gaba dayi....".       Kamar daga sama ya dinga jin tashin maganganun ummin sanda yake hanyar shigowa wajen ummin,da alama cikin bacin rai take maganar,sunan data kira kawai yaji tamkar an jefeshi da wani abu,kalaman da suka biyo baya kuma suka so birkita masa kwanya da kuma tunaninsa gaba daya,har ya kasa tantance ainihin furucin dake shigowa kunnuwansa yake ji ko kuwa,don haka ya kutsa kanshi kai tsaye cikin falon,burinsa kawai ya isa yaji abinda kunnuwansa suke jiyo masa hakanne?.        Dubanshi tayi sanda ya shigo,saita dauke kai ta maida ga luba

"Kije ki shaida musu dukkan abinda na gaya miki,hakanan ki dawomin da dukkanin amsar da suka bada"

"Da izinin Allah kuwa ranki ya dade....Allah ya huci zuciyarki....a tashi lafiya" daga haka ta miqe ta fice daga falon.       "Ummi....ciki?,waye yake da ciki?" Ya samu bakinsa da furta mata kalaman ba tare daya shirya ba,dukkan kallonta ta maida kanshi,cikin matuqar hade rai tace

"Sun shirya qara tare da tsara cewa tana da ciki,saboda idanuwansu sun rufe,suna tunanin shashashai ne mu,suna so yi amfani da wannan damar don suyita tara dukiya damu,bayan sun amince da dukkan yarjejeniyar da mukayi dasu" Hakanan yaji batun cikin ya samu kyakkyawan matsugunni cikin zuciyarsa,ya kuma zauna daram bisa kansa,hakanan yaji baida sha'awar ci gaba da zama,don haka ya qaraso tsakiyar falon,ya samu kujera daya ya zauna

"Amma ammi....bincakawa ya kamata ki soma yi,ki tabbatar da ainihin sahihancin maganar ko kuma akasinta" karon farko ya samu kanshi da musawa hukuncinta,karon farko daya soma fadin ra'ayi da views dinsa kan wani hukunci data zartas.       Sosai take dubanshi itama,kafin daga bisani ta motsa bakinta

"Wacce jami'a ka zaba?" Ta jefa masa tambayar ba tare data bi takan qorafinsa ba.      "B U K kano" ya fada yana motsa labbansa,kamar wanda aka yiwa dole wajen furta lafazin,wani kallo ta watsa masa

"Kana da hankali kuwa?,ka manta wacce jami'a ka gama?,ko kuwa ka manta gargadin da nayi maka na cewa banda duk wata jami'a dake cikin qasar nan?" Baki ya bude zai mata magana,cikin fusata ta daga mishi hannu gami da cewa

"Ya isheni....tashi ka bani waje tun bai gama fusata ba" tsam ya miqe ba tare daya furta abinda yayi niyya din ba,yana jin ranshi a jagule,bacin rai na mamaye zuciyarsa.      Har ya kusa fita ta kirayi sunanshi

"Abdul'azeez" ya tsaya kana ya waiwayo,ta baiwa qofa baya don haka bai ganin fuskarta

"Idan wani abun ke damunka,ka gayamin tunda wuri mu maganceshi,idan kuma wani abu kake saqawa cikin ranka,ina mai baka shawarar kayi gaggawar cireshi....saboda bazai taba haifar maka da d'a mai ido ba".......


********    ******    ********


     Tunda umma luba ta shaidawa malam bilya saqon fulani aisha yaji ranshi yana baci,a karon farko kenan,bai taba kawowa ko tsammanin zasu ture ko su qaryata maganar cikin ba,shi kadai zancan ya dinga damu yana masa kai kawo cikin zuciyarsa,yana son shaida zuhriyya saidai baisan gidanta ba,bai kuma san inda zai sameta ba,yasan cewa koda zatayi fada masifa da tashin hankali a qalla ya samu sassauci ya gayawa kowa,haka maganar ta dinga damunsa taba sanyashi bacin rai da baqinciki.


*****************       Misalin bakwai da rabi ne na safiyar ranar,anty zuhriyyan ta shirya don takai najwa da ateeq tahfiz da suka sanyasu dan iyakacin lokacin zamansu a kaisa kafin su tattara su koma inda suka fito,saboda gudun kada karatunsu ya samu tasgaro kafin su koma.      Yawancin lokutta abba ne yake kaisu,amma yau anty ce zata kaisu sakamakon fita da yayi tun sassafe.       Da kanta ta iske bilkisu a daki,ta sanyata ta shirya zata rakata takai yaran makaranta,sabanin daa da ita da haule suke bari a gidan,amma yau tace tare zasu,saboda har yanzun walwalar bilkisun bata dawo ba,duk da cewa tadan samu sauqi,amma laulayi kam har yanzu bai barta ba,don wani lokaci idan ya waiwayeta haka take wuni akwance,ba tare data kai komai bakinta ba,wala ruwa ko abinci,wani lokaci kuma ka ganta da 'yar lafiyarta.       Yawan tunane tunane da anty zuhriyyan ta fuskanci tana yawan zama tayi shike damunta,don haka ta sake zage damtse wajen janta a jiki,hanata zaman kadaici,da qirqiro mata abubuwa da tasan zasu janye mata hankalinta.       Da fari tayi shawara da abbaa kan zata sama mata skyline universty,yace aah,yanaga yanzu abu mafi kyau shine suyi tattalin lafiyarta tukunna,tunda har yanzu ba wani cikakkiyar lafiya ne da ita ba,sannan shi yafison idan sun koma brasil tayi karatunta a can,inda babu wani wanda ya santa bare ta samu takura ko wani abu makamancin haka,ta yarda da shawararsa don haka ta jingine wannan batun,saita sauya mata waya da laptop,hakanan lokaci lokaci takansa ana dauko mata qannenta su wuni wajenta,hakan saiya sake rage mata damuwar da take ciki sosai,duk da cewa zuciyarta har yanzu a quntace take,ta cika da tsana da zargin ahalin kaisa,hakanan ta boye wani quduri cikin zuciyarta.      Da yake duk sanda ta tashi sallar asuba sai tayi wanka saboda ta samj temprature din jikinta ya mata dadi,yanzun ma da wankanta,kaya kawai ta sauya zuwa doguwar riga,saboda yanxun tafi ta'ammali dasu,sakamakon cikinta daya daga ya soma fitowa,don ya shiga wata na biyar,ta samesu tuni suna cikin mota.     A hanya surutu ateeq da qawarta najwa suketa mata tana biye musu,motar bata zauna shuru ba har sai da ummin ta saukesu suka juyo iya su biyu kawai,suka daukon hanyar komawa,saidai wannan karon a hankali ummi take tuqin.      Basuyi wani nisa ba ummi zuhriyya tace

"Inaga ya kamata mu leqa gidanku ko?,muji meye feedback na mutanen can kan batun cikinki" boyayyar ajiyar zuciya kawai bilkisun ta sauke ba tare data ce komai ba,don ita gaba daya bata qaunar tunasu ma bare maganarsu,ta ajesu can wani sashe daban na rayuwarta mai nisa,wanda take fatan watan watarana ta mance da babinsu,saidai ko hakan zai yiwu?,tunda ga wata igiya mai qarfi ta ratsa tsakaninsu?.      Har suka je gidan bilkisun bata tanka ba,sukaci sa'a baban yagama shirin fita kasuwa kenan yana tsaye a falo yana baiwa umma katti kudin cefane,wanda cikin satin ya sake gyara lamarinsa,tare da gyara abubuwa masu yawa cikin gidan,harda wadanda ma baya yi.       Daga yanayin yadda ya karbesu bilkisu taga wani irin sanyi da laushi mai yawa tattare dashi,ba ita ba,hatta da anty zuhriyya abokiyar burminsa ta lura da hakan,saidai yace musu su xauna minti goma yanzun zai dawo,tabe baki kawai antyn tayi batace masa komai ba har ya fice.      Qofar gida ya tsaya yana neman yaron da zai aika gidan umma luba,saboda nashi yaran duka basa nan sun wuce makaranta,bayajin zai iya gaya musu wannan saqon da bakinsa,yana jin zuwa yanzu ya kamata ya sauya daga asalin bilya zuwa bilyaminu,ya kamata ya dainda dabawa diyarsa wuqa haka a zuciyarta,ya tabbatar dole amsar da zata biyo baya ta taba zuciyar kowacce mace,ki dauki ciki kina wahala dashi,sa'annan wadanda keda alhakin hakan suce basu yarda da batunsa ba?,ba qaramin mummunan xance bane ga kunnuwan kowacce diya mace.      Da qyar ya samu yaro ya aika,saiya tsaya nan qofar gidan yana jiran dawowarsa,Allah ya taimakeshi sai gata da yaron,cikin mamaki take tambayarsa lafiya?

"Maigado ce da mariqiyarta,wadda take da alhakin jin komai sukesu suji amsar da masarauta ta basu" ita kanta wannan karon abun saiya mata nauyi,amma ba yadda ta iya dole ta isar da saqon,don tana da buqatar amsar da zata kaiwa fulanin,don haka ta cije suka shige tare.       Sau daya bilkisu ta daga kai ta kallesu ta dauke kanta,mutum biyun da kullum idan ta gansu sai taga kamar taga wadanda suka sanya gatari suka rinqa sassaqar rayuwarta har zuwa qarar da ita.       A sanyaye umma luba ta gaida anty zuhriyya datayi mata kwarjini,ta amsa mata ba yabo ba fallasa,don batasan wacece ba

"Sannu maigado" ta sake yiwa bilkisu sannu,bata iya dubanta bama bare ta amsa,saita gyara zama cikin dan da wurwura,ta gaya musu dukkan abinda fulanin ta fadi.       Ƙololuwar fushi anty zuhriyya ta shigeshi,yayin da bilkisu ta shiga wani irin yanayi wanda batasan wanne iri bane,abu daya kawai taji jiki da zuciyarta na gaya mata,basason zamansu a wajen,basason ci gaba da sauraren bayanan umma luba,duk da alamu sun nuna ta gama fadin abinda zata fada din,saita miqe tsam.idanuwansu dukka suka rakata,kowa yana jin wani yanayi game da ita a zuciyarsa.       Haka ta dinga sanya qafarta kawai duk inda ta fuskanta,bata tsaya ba sai data isa jikin motarsu,ta sanya hannu ta bude ta shiga ta zauna,gamida curewa waje daya,taso cusa fuskarta tsakanin qafafunta ko zataji salama,amma babu damar haka,saboda cikin dake jikinta,don haka sai taja mayafin rigarta ta lullube fuskar tata,sannan ta dora ta saman tafin hannunta,tana sakin ajiyar zuciya a jejjere kamar zuciyar tata zata fito.        Tamkar zatayi aman wuta daga qirjinta haka takeji,batason ta yanke hukunci babu yawun abbaa,amma tanajin dole ta aikawa da fulanin saqo,saqon da zai isa jikinta da zuciyarta yadda ya kamata


44


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899

Ko

09033181070
       "Inason nima ki shaida mata,ni zuhriyya qanwa ga mahaifiyar bilkisu,kuma uwa a yanzu a gareta....auren danta da bilkisu qaddara ce....wata qaddara wadda ta sanyani nayi nesa da 'yata,wata qaddara wadda a yanzun bata isa ta zama sanadin maimaituwarta ba,ki gaya mata....bilkisu ta yiwa danta nisa,tayi masa tazara kwatankwacin yadda sama ta yiwa qasa nisa,ki shaida mata ashe shi arziqi bawai kudi bane kawai....arxiqi yana a zuciya ne ba'a hannu ba,ki shaida mata,munfi qarfin dukkan wata dukiya tata da take tunanin ta mallaka,komai yawanta,ciki kuwa dan duma ne,yado yakeyi,da kansa zai fasa kansa,wala'alla kuma sanda zai fasa kan nashi,yafi dukkan qarfinta da tunaninta,ya mata nisa ya mata zarra,ki sake shaida mata dai,ta rubuta ta ajjiye,akwai ranar nadama,akwai kuma ranar qin dillanci....ki jadda da mata,ta sanyawa ranta bata taba alaqa da wata mai suna bilkisu ba,bare tayi zaton ta taba hada dangantaka da wani d'a nata,wannan shine saqona" daga wannan bata qara cewa komai ba,hakanan bata sake waiwaya ta dubi daya daga cikinsu ba ta fice,don hankalinta gaba daya yana kan bilkisu tunda ta fice.        "Kukan me kikeyi?,bai kamata kiyi kuka ba daughter kina da uwa kamata,share hawayenki" ta fada tana daga bilkisu,saidai yanayin da ta ganta ya kadata gamida daga hankalinta,duk yadda taso shawo kan abun ya gagara,dole sai data danganata da asibiti,wanda sai data kwana biyu sannan tasamu shawo kanta,wannan dalili ya sanya ita da abbaa suka yanke shawarar fara shirye shiryensu su koma inda suka fito,amma da farko zasu fara yada zango a ethopia don kaita taga tarin dangi da 'yanuwa wadanda bata sansu ba,suma basu santa ba.       Cikin qanqanin lokaci komai ya kammala na bilkisu,su dama ticket kawai zasu siya,don suna da visas dinsu kuma basu qare ba.*********   """"""""" *********
         "Shaida min abinda suka sake aikoki dashi" fulani dake tsaye ta fada tana duban wani guri daban,kamar yadda ta umarceta haka ta gaya mata komai dalla dalla,bata boye komai ba.      Ga mamakinta murmushi fulani tayi tana jijjiga kai,sannan tayi tattaki mai dan dama kafin ta dakata,tana mamakin yadda saqon ya samu muhalli me kyau a cikin zuciyarta,amma duk da haka ta bari son rai yayi mata jagoranci,ta bude baki tace

"Wannan kadai ya isa ya zamemin shaida kan cewa qarya suke,idan har da gaske suke...zasu tsaya iyakacin tsayawarsu suga sun tabbatar da gaskiyarsu,mu rubuta duka mu ajiye,maga wanda zaiyi dana sanin....tashi kije luba" ta fada tana takawa tabi wata siririyar hanya.       **********      ***********      Tsit falon yake wanda sai kayi tsammanin babu wata halitta a cikinsa,qarar ac ne kawai ke tashi sai na sauran na'urori dake da alaqa da dakin.      Mutum biyu ne zaune saman lausasan kujerun da aka yiwa falon qawanya dasu,azeez ne da abdulrashid,wanda shurun ya afku ne sanadiyyar maganar da suka gama yi yanzu tsakaninsu.      Gauruwar ajiyar zuciya abdulrashid yasaki sa'an nan yace

"Babu wanda ya zaci al'amarin zaizo a haka,yanzun maganar ta canza,ana maganar jininka ne wani sashe na jikinka,abdul'azeez's photocopy,tamkar wani copy naka ne ajiye a wani waje,wanda bai cancanci koda kowa ya wofantar dashi ba kaika aikata hakan" wata iriyar ajiyar zuciya dake nuna gazawarsa da gajiyawarsa ya saki yana duban abdulrashid,da wani irin amo a muryarsa ya sake bude baki karo na biyu

"Wannan shine the same tunani na abdul.....indai har da gaske ne,yanzu ana magana ne ta jini,ana magana ta zuri'a....ban damu da amincewarta ta yadda da shirin da duk akaje mata dashi saboda kawai dukiya ba,ina duba da jinina ne,jini na ne a jikinta...but...fulani ta kasa fahimtar hakan,taqi yarda nayi mata bayani,taqi tsayawa ta saurareni,infact tama qaryata maganar,if maganar gaskiya ne me zai faru a gaba?".       Duban azeez din sosai abdulrashid yake,yana karantar wasu emotions dake saman fuskarsa,yana maganar ne deep inside him,akwai kuma wani babban lamari mai girma tattare dashi,bai taba ganin azeez din tunda suka taso daga quruciya zuwa yanzu ba ya damu da lamarin wata mace ba,bai taba ganinsa yana maimaita batu kan wata diya mace ba sai yanzu,koda ya take dashi kuwa idan ka dauke mahaifiyarsa,sai yanzu gashi wasu emotions na tashi daga saman fuska da kuma muryarshi,lallai wani abu na shirin faruwa.      Ajiyar zuciya abdul ya saki sannan yace

"Ni ina ganin kawai ka shaidawa mai martaba...." Idanu azeez ya zuba masa,sannan a hankali yace

"If idan qarya ne fa,maganar ba gaskiya bace?" Shuru yasake yi na wasu sakanni sannan yace

"Akwai fahimtar juna da qauna mai yawa tsakanin fulani da mai.martaba,idan har na shaida masa ni nasan girman abinda zai biyo baya,bazai yiwa kowa dadi ba,kuma ya zamana maganar ba haka take ba...yaya kenan?,na watsawa fulani qasa a idanu,na tozartata gaban maqiyanta,na bata tsakaninta da mijinta,akwai abubuwa masu tarin yawa da zasu iya biyo baya" kai abdul ya kada,tabbas shima ya hango cakwakiya mai tarin yawa cikin aikata hakan,shuru yayi yana lalubar wata mafitar,wanda kafin yakai qarshen nazarin nasa maganar azeez din ta katse masa hanzari

"Akwai hanya guda daya da nake tunanin zata bullemin"

"Waccece?"

"Zan binciki sahihancin maganar ta hanyar matar data kawowa ammi saqon"

"Good...amma a ina zaka samu matar?"

"Ma'aikaciyar masarautarmu ce,zanyi magana da sunusi,yasan kusan fiye da rabin barori da ma'aikatan gidan,zan dorashi ya bincika min komai..." Ya qarashe maganar yana miqewa tsaye,yana jin tamkar an warwareshi daga wani sasari da aka sanya masa,kai tsaye dakin abdulrashid din ya shige,yanason ya samu bacci don ya sake samun nutsuwa na aiwatar da komai.       Sanda abdul ya shiga dakin ya tadda shi tuni yayi nisa a kwanciyarsa,daga shi sai dogon wandon rigarsa,da fara qal din singlet,ya ware ac da fanka gaba daya,murmushi mai hade da dariya ya saki

"Problem solved"

"In sha Allah" ya amsa mishi yana lumshe kyawawan idanunsa da sai yanzu yaji bacci nason rinjayarsu.        *******   *****   *****   *****     Hannayenta goye a baya take kai kawo,tabbas babu wanda zai sanya sunusi binciken inda luba take sai azeez,tunda shine shugaba kuma babba a masu kula da sassansa,akan yana nufin kenan ya take maganarta,gaba daya lamarin me yake nufi?,binciken luba yana da alaqa da yarinyar nan,ko kuwa wani issue ne na daban.      Sosai hankalinta ke a dage,karon farko data soma cin karo da wani abu da yayi kama da saba umarni daga azeez din,ba shakka zata nuna masa qarfin qwanji,da qarfin kasancewarta uwa,bata so kuma bata fata abinda zuciyarta ke qissima mata ya tabbata,ko a mafarki bata buri ko tunanin haka.       Cikin gaggawa tasa a nemo mata azeez din tana nemansa duk inda yake,saidai kuma aiken nata bai sameshi da wuri ba,sakamakon yana wurin mai martaba suna tattaunawa,yana son xaiyi tafiya marocco,kuma a qalla zai dauki kusan sati guda a can,duk da cewa yakanyi tafiye tafiye,amma bai fiya zama ko ya dade ba saboda mutanensa.       Lokacin daya fito daga wajensa,saqonta shine abu na farko da aka gaya masa,duk da yadda yakeso ya watsa ruwa a jikinsa amma haka ya yanke dukkan wani uzurinsa ya nufi sassanta.       Yanayin daya taddata yasa hankalinsa ya daga,ta jefa masa wani kallo da zai iya cewa bai taba ganinsa irinsa cikin idanunta ba,sannan cikin kakkausar murya ba tare data amsa gaisuwar da yake miqo mata ba,murya mai cike da gargadi tace dashi tun bai ida zama ba

"Wannan shine karo na qarshe da zan maka magana kan wani batu daya shafesu indai nina haifeka....ka dakatar da duk wani lalube da bincike da ka sanya ake maka kan luba,don ko ka samu luba ba zaka sake samun komai ba daga gareta,abdul'azeez!....karka sake ka tsallake gonata,karka sake mu sanya qafar wando daya dakai,a karo na biyu ina sake gaya maka....ka ajjiye duk wani abu daya dangancesu daga kwanyarka,tun baka shigo gonata ba,ka fuskanci abinda yake gabanka!,wannan shine umarni na" bata bashi damar cewa komai ba tayi gaba tabarshi a nan,shi dinma baijin koda ta bashi dama zai iya cewa wani abun,saboda yadda kwanyarsa gaba daya ta dinke,ya juya cikin wani irin yanayi yana takawa shima ya fice daga farfajiyar.       Wani irin juyawa yaji kansa yana yi,yanajin gangar jikinsa kamar ba tashi ba,karon farko da yaji har cikin zuciya da gangar jikinsa umarnin ammi bai samu masauki ba a qwaqwalwarsa,yakejin kamar bazai iya biyayya wa umarninta ba,ya miqe a hankali kamar me ciwon laka ya soma takawa,gaba daya zuciya da qwaqwalwarsa tayi nisan zango a tunani.      Kwananshi biyu ko ammin bata ga idanunsa ba,yana cikin wani irin yanayi da iya tsahon rayuwarsa bai taba shiga ba,ya qure tunaninsa gaba daya kan hanyar da zaibi ya kawowa kanshi mafita,yafi kowa sanin ammin nashi kaifi daya ce,gaba daya 'yan hamayya da abokan adawa sun gurbata tunaninta,tabbas duk wanda ya santana shekarun baya ba haka ammin take ba,to amma kusan shi a kansa komai yakeso ya qare,shin wannan soyayya ce?,kuma gata ne?,zai iya cewa eh,amma bisa hasashe da tunanin mahaifiyarsa,saidai akwai tarin kusakurai masu yawan gaske cikin dukkan hukuncinta da take yankewa,wanda takan dora komai ne bisa mizanin ramuwa da ganin ta cimma gaci,ta cusa baqinciki da bacin rai cikin zuciyar maqiyanta,amma hakan gashi yanason shafar rayuwa da walwalarshi.


*********   *****    *********      Kamar kowanne lokaci yau cikon kwana na uku,yana kwance shi daya a falonshi sanye da singlet da dogon wando,idanunshi saman tafkekiyar tv dake girke tana aikinta,rabin hankalinsa na kanta,yayin da wani rabin hankalin nashin ya tafi wani tunani na daban.       Shuru sashen nashi yake babu motsin kowa,don tun kwanaki ukun da suka gabata ya sanya sunusi ya sallami dukkan hadimai da barorinshi,saboda baya buqatar kowa bare a dameshi,dukka ammin tasan da wannan amma tayi biris dashi,labarin abinda ya aikata din yazo mata,abu daya take tsoro gami da fargaba,sannan kuma bata da amsar hakan,me azeez yake nufi?,meye nufinsa na damuwa da yarinyar?,me yasa take ganin wasu alamu da take take nason soma kaucewa umarninta?,tambayoyin da takan kwashe lokutta tana yiwa kanta,saidai bata da amsar ko guda daya,tabbas matuqar ya zamanto cewa ra'ayin azeez ya soma sauyawa babu shakka akwai gagarumar matsala da take hasashen zata iya afkuwa,bata fata da ko burin abinda aka shiryashi na wani taqaitaccen zamani ya zama tarnaqi ga rayuwarta,ko ya lalata dukkan wani shiri data dauki tsahon lokaci tana yiwa rayuwarsu.      Gyara kwanciyarsa yayi,ya soma gajiya da kwanciyar,ya lumshe idanunsa yana sake matsawa qwaqwalwarsa zuwa ga tunanin mafita.       Kamar wanda aka tsikara ya bude dukkan idanunsa da sauri,sannan ya miqe a sukwane ya zauna sosai saman kujerar,a sarari cikin daga murya yace

"Yes!" Saiya soma lalubar wayarshi wadda tun kwana uku take a kashe ya kunnata,babu jimawa ta daidaita,saqonnin safwa ne suka fara shigo masa iri daban daban,saina abdulrashid jabir da sauran makusantanshi.       Duka baibi ta kansu ba,ya soma lalubar lambar sunusi,bugu daya tak ya daga,cikin girmamawa ya soma miqa masa gaisuwa,bai amsa ba ya gaya mishi saqon da ya sanya yayi kiranshi

"Kana ta ina?"

"Ranka ya dade,ina can bakin sassa kamar yadda ka umarta"

"Ka qaraso ciki,inason ganinka" daga haka ya katse kiran,sa'annan ya miqe ya soma barin wajen.       Bedroom dinshi ya tura ya shiga,ya qawataccen toilet dinsa,ruwan wanka ya hada mai dumi sosai yayi wanka,kana ya fito ya shirya kansa cikin wasu qawatattun kaya dake nuna ainihin wayeshi,sun matuqar karbarshi da kuma dacewa dashi,ya gyara sumarshi da kyau ya sanya hula data sake qawata adon nashi,sannan ya feshe jikinsa da turare baya ga na jiki daya sanya kamar yadda ya saba,ya zura takalmansa da suke mahadi da kayan,sannan ya duba agogo,zuwa yanzun yasan sunusi ya jima yana jiransa,don haka ya fito.kai tsaye zuwa falon da sukan zauna su jirayeshi a duk lokacin daya buqaci ganinsu.      Kamar yadda ya zata din kuwa ya sameshi xaune saman kilishi yana jiransa,yana daga tsaye yayi magana dashi

"Ka nemo min sodangin,ka shaida mata ina buqatar yin magana da ita cikin sirri,sannan kuma a gaggauce"

"An gama ranka ya dade" ya fada yana ficewa da hanzari,kamar yadda ya fuskanci buqatar ganawar tasu ta musamman ce,hakanan ya samu kanshi da kasa zama,burinsa kawai sodangi ta iso,ya tabbata komai zaizo cikin sauqi,yana da yaqinin a yau zata kaishi gidansu,zaije ya ganta,sannan ya tabbatar da gaskiyar wanzuwar jininsa tattare da ita ko akasin hakan.          Tana daga tsaye a katafaren kitchen na alfarma da ake amfani dashi wajen samar da abincin sassan fulani aisha,dukkan wani abinci da fulanin xata ci kusan yana qarqashin kulawar sodangi ne,daya daga cikin manyan amintattun ta ,wadanda takanyi amfani da shawarwarinsu,musamman idan suka dace kuma sukayi dai dai da ra'ayinta.      Dudduba yadda ake gudanar da girkin take cikin nutsuwar nan tata da kamalarta,daidai lokacin data gama duba tattasan da aka gama markadawa,kubra ta qaraso bayanta,cikin girmamawa murya qasa qasa

"Shugaba yarima yayi aike,ya aiko sunusi,yana da buqatar ganawa dake yanzu" shuru ta danyi tana tunani,don kusan tun dawowarsu daga mexico fulani ta karbi fiye da rabin aikinta a sashensa ta dora wasu,batasan me yasa ba,amma tana tunanin hakan bai rasa nasaba da tarayyarsu da bilkisu,tanason sai tafiya ta sake nisa komai ya daidaita kafin lamuranta gaba daya su koma can,don kada ya zamana suna yawan ambarta ta kasa bacewa daga bakunansu,tana hasashe dukka dalilinta baya wuce wannan.      Ba tare da dogon nazari ba tace

"Muje" saboda jikinta ya gama bata cewa tabbas akwai abinda ke faruwa,cikin kwanakin taga yariman ya kusa sau uku,kallon farko tasan akwai abunda yake damunshi,a matsayinta na wadda ta sanshi tun daga yarinta zuwa girma.       Kamar yadda ta xata kuwa daga fallon farko ta fuskanci matsala da damuwa kwance saman fuskarshi,falon ya dauki shuru bayan fitar kowa,ya zamana daga ita saishi,cikin nuna kulawa da tausasawa tace

"Allah ya taimaki yarima,ko meye yake faruwa zanso najishi daga bakinka,dom ns tabbatar akwai alamun matsala da damuwa tattare dakai".        Dukkan abinda bata sani ba ya gaya mata,bai boye mata komai ba,da buqatarsa nayin tattaki da kansa zuwa gidansu bilkisun don tabbatar da gaskiyar lamarin.        Idanunta na kallon qasan carfet din,saidai sun cika fal da hawaye,tausayin bilkisu matsananci yana ratsata,inama ace tasan gidansu bilkisu,inama ace tasan inda zata ganta,lallai ba shakka koda zuwanta ko kai yarima zai zama sanadin qarshen zamanta a masarautar kaisa da sai taje,tana hasashe da tunanin yadda rayuwa zata kayawa yarinyar,rayuwar da zatayi dauke da cikin da bata da iko isa ko qwarin gwiwar nuna ubanshi,zata raini ciki cikin al'ummar da basusan da zama ko labarin ta taba aure ba,me zasu kalli cikin,shege kenan fa?,tanaji a jikinta zancan cikin gaskiya ne,tunda ita din kusa shaida ce na dukka abinda ya faru,meya sanya fulani ya ta sauya haka?meya qeqasar da zuciyarta ta zama wata iri bayan ba haka dukka suka santa ba?.       Yatsunsa tasa ta dauke hawayen da suka gaza boyuwa sannan tace

"Iyakar zamana na jima banga yarinya kamar bilkisu ba,yarinyar dake da dattako da kyawawan halaye da sukafi shekarunta yawa,shekara sha shida amma zaka tsammaci ta mallaki shekaru ɗai ɗai har gda arba'in ne,quruciyarta me kyau ce da burgewa duk da rashin gata da wanda zai damu da ratuwarta,inaji a jikina zancan cikinta gaskiya ne,ba shakka tana da ciki,saidai.....ina neman afuwarka....ina kuma mejin dadin shaida maka cewa....bansan koda hanyar gidansu ba,mun rabu tun a airphort da ita,bansan ya akayi ta isa gida ba,ladingo da luba su sukasan ainihin gidansu,saidai suma na jima da daina ganin gilmawarsu cikin masarautar nan".       Idanunsa kawai ya rufe tsahon wasu mintuna ya gaza budesu,haka nan itama shuru tayi tana taya bilkisu jin ciwo,saboda tasan cewa Allah ne kadai yasan ciwon da a yanzun yarinyar takeji a ranta.      Izini aka nema na shigowa,bai iya bada amsa ba sai sodangi ce ta bada,saboda ta fuskanci dan aiken daga sassan me martaba yake

"Mai martaba yana son ganinka,yayo aike daga sassansa" sodangi ta shaidawa azeez,sai a sannan ya bude idanunsa da suka sauya kala,haka kawai yaji aiken ya sanya gabanshi faduwa,abinda ba kasafai hakan ke faruwa gareshi ba,ya motsa labbansa da qyar yana amsawa,sannan ya miqe yana sallamar sodangi yasake shige ciki.       Ya jima zaune yana qoqarin controlling kansa don ya samu zuwa kiran me martaba,baya son yaje masa a wani yanayi na daban wanda zaibar ayar tambaya a zuciyar maimartabar.        Tsahon wani lokaci sannan ya samu rage kaso hamsin na mode din da yake ciki sannan ya fito,ya samu wasu daga cikin barorinsa acan qofar waje,sunso masa rakiya kamar yadda aka saba amma ga dakatar dasu,shi kadai ya durfafi sassan mai martaban.


45

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899

Ko

09033181070

__________________________

*_kina da burin koyon sana'a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*


*_kin jima kina sha'awar yadda yake hada BIRTHDAY CAKE DA DECORATION amma kin rasa wajen da zaki koya?,ko FARASHIN YA MIKI TSADA?_*


*TOFA MATA!*


*_Ga dama ta samu_*


*_UMMU AYMAAN KITCHEN ta shirya tsaf don koya muku yadda ake hada gangariyar BIRTHDAY CAKE wanda ya gama hada dukkan gamayyar kayan dadi masu sanya harshe su motsa,gefe guda kuma ta koya miki yadda zaki qawata waje da walwali da kuma walainiyar KAYAN ADO DA QAWA na wajen gudanar da SHAGALIN BIKI SUNA TARON BIRTHDAY WEDDING ANNIVERSARY da sauransu_*


*_ba'a nan UMMU AYMAAN KITCHEN YA TSAYA BA,tana da ajujuwa na musamman don koyar da mata nau'in girke girke MAIDA TSOHUWA YARINYA,hakanan tana karbar kwangilar abincin taro kowanne iri_*


*_ta fannin kayan maqulashe na fulawa ta samar da abubuwa kamar haka_*

Cake perfait

Cup cake

Samosa

Springrolls

Meatpie

Doughtnout


*SIYAN DAYA KO SARI*


*_za'a koyar dake BAKING AND DECORATION QIRI DA MUZU ta sigar zancan nan da hausawa kance GANI YA KORI JI,gani ga malama_*

*_sa'an nan kuma akwai tanadi na musamman ga masu sha'awar koya ta hanyar yanar gizo wato ONLINE,duka kan farashi mai rangwame_*


*_ZA'A IYA SAMUNTA A UNGUWA UKU,LAYIN MAI FATA ZARIA ROAD*


KO A TUNTUBETA A WANNAN LAMBAR WAYAR

08032964266


*_ZA'A GUDANAR DA KOYARWA NE ON 5&6,GARZAYA MAZA KI REGISTER*🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️


        Sashe ne da kusan yafi kowanne sashe dake cikin gidan tsaro kyau tsaruwa da kuma yawan ma'aikata,hakan ya sanya tun kafin ya tunkari qofa barori dake kai kawo kowanne ke qoqarin aika gaisuwarshi cikin kirari da nuna qauna da kuma girmamawa,saidai a duk sanda sukayi kirarin sai ya dinga jinsa cikin kwanyarsa,tamkar suna gaya masa cewa sarauta zata zama kota zama sanadiyyar rushewa duk wani tsari na karan kanshi da rushewar rayuwarshi,don haka ya soma daga musu hannu yana dakatar dasu,da haka har ya isa ga me martaba.       Kayan jikinsa kawai zasu nuna maka bai jima da barin xaman fada ba,kaya ne nashan iska,saidai fuskarshi da wani sassan na jikinsa akwai sauran damshin ruwa dake nuna wanka yayi bayan shigowarsa,fulani suratu na zaune daga gabanshi tana bare mishi ayaba,bayan kofi data miqa masa wanda ta cika mishi shi da sassanyar lemo.       A fakaice ta yiwa azeez din wani kallo kana ta dauke.kanta tana ci gaba da yin abinda take,ta tsani ya dinga kiran yaron haka a lokacin kebewa irin wannan,lokacin da take gani su kadai ya cancanta su kasance tare dashi.       A qasan shima ya zauna,kansa a qasa cikin girmamawa ya gaida mai.martaba,ya amsa mishi cikin kulawa,fuskarsa dauke da fara'a,ya waiwaya ya dubi fulani saratu

"Barka da warhaka mama" ya gaidata itama,murya can ciki,cikin dakiya da kuma shariya ta amsa

"Barka kadai" duka mai martaba yana ankare,saiya murmusa kawai cikin ranshi,shi yana mamakin kishin qarfin hali irin na mata,a iya saninsa da abdul'azeez bai taba wani abu da zai nuna raini garesu ba,kowacce yana bata girmanta bakin gwargwado,shidai kawai barshi da miskilancinsa,qarancin fara'a da rashin son yawan magana.       "Ranki ya dade....ki aramin wasu lokuta daga lokutanki mana" mai.martaba ya fada cikin fara'a,ta watsa mishi idanunta,duk da taso yin qorafi amma yanayin yadda yayi maganar dole ta sallama,saita aje abinda takeyi din kawai ta miqe ta basu waje.    Bayan ta fita ya tashi ya zauna sosai daga kashingidar da yayi,yasa hannunsa ya shafi fuskarsa yana aje numfashi sannan ya kira sunan abdul'azeez,kiran daya sanya gabanshi faduwa ya amsa mishi yana sake nuna tsantsar ladabi

"Wato bansan mutane me suka dauki zalunci ba a wannan zamanin....kusan kowa ya zama azzalumi ba tare da ya sani ba,kowa burinsa ya samu wata dama komai qanqantarta ya zalunci dan uwansa,bansan wanne gardi ko dadi yakewa al'umma cikin ruhinsu ba,nayi tsammanin kowanne muminin qwarai zaiyi qoqarin gudun fanfalaqi wa zalunci iyakacin numfashinsa,komai qanqatar wannan zaluncin kuwa,koda na mummunar magana ce bare na aiki a aikace,a rayuwa zalunci na daya daga cikin manya manyan laifuka,saboda girman laifin Allah daya halicci komai da kowa yace ya haramtawa kansa da kansa shi,ya tauna tsakuwa don aya taji tsoro,ya nunawa bayi shi da yake da ciakken iko da izza ya haramtawa kansa,hakan yana nuni da cewa matuqar wani cikin bayi ya aikata wa wani dan uwanshi wannan zaluncin...bazai barshi ba saiya fidda masa haqqinsa....abdul'azeez,wallahi wallahi wallahi dukkan bawan daya zalunci dan uwansa koda da bawon rake ne bazai shiga aljanna ba sai Allah ya fiddawa wannan wanda ka zalunta haqqinsa,koda kuwa arne ne ba musulmi ba baka ci bagas ba"      "A yau na yanke wani hukunci da naso ace kana wajen na zartar dashi,wanda har cikin zuciyata inajin cewa shine dai dai....bazan daga qafa ga duk wanda na kama da laifin xalunci ba!,ko waye shi!". Sosai kalaman maimartaba suka dakeshi qwarai,bawai kalamanshi na qarshe ba,tunda ya soma magana suke shigarsa,saiya soma hada maganarshi data sodangi,indai har da gaske ne rashin gata ne!,indai har da gaske abinda zuciyarsa ke ayyana amasa haka ne,hakan na nufin an zalunceta?,hakan yana nufin ammin tayi zalunci?,shima zai iya fadawa ciki?,to amma zaluncin cikin sani ne ko cikin rashin sani,idan har ya tabbata zalunci ne ta yaya zai kubutar da ita a matsayinta na mahaifiyarsa da yake burun ganin tsiranta,ci gaba da yi mata biyayya irin wannan tamkar bata qofa ne naci gaba dayin abubuwan da basu dace ba?.

 


      "Zanyi tafiya ethopia gobe,akwai taro da zamuyi a kamfanin dana sanya hannun jarina,naso ace muje tare dakai ko,kafin nan da shekara hudu da nake saka ran ka cika shekara talatin ka soma wakilatata,nima na soma ragewa kaina wasu al'amuran,to amma hakan bazai yiwu ba don lokaci ya qure,naso magana dakai kwanaki uku baya amma ka bace sam ba'a ganinka,don haka gobe zaka rakani airphort...zan bar riqon masarauta hannun waziri,saidai daga wannan karon inason ka soma sanin wasu abubuwa kaima,zaku riqe qasar tare,zaka zama tamkar mataimakinsa,har zuwa sanda Allah yayi na dawo".      Baya jin xai iya cewa wani abu illa

"In sha Allah ranka ya dade,Allah ya saka da alkhairi" baya son yawan qorafi,don yasan cewa saratu na qididdige da lokacin da aka shigar mata,don haka basu dora kowacce hira ba ya sallameshi,ya kuma gaya masa lokacin da zasu fita din zuwa airphort.      *******    *****   *********       Akwatuna ne a gabanta a bubbude wasu da kaya da ajere a ciki wasu kuma yanxun ta soma jerawa,bisa dukkan alamu aiki takeyi ta katse ta zauna kallon takardun hannunta guda biyu.     Wani murmushi take fitarwa dake nuna farincikin da zuciyarta take ciki,duk da tayi katatu tuquru amma bata taba tsammanin kyawun sakamakon nata zaikai har haka ba,ko kusa ko alama,dukkan jarabawarta guda biyun sakamakon sun fito mata a ba zata.       "Kai bilkisu,basan wanne irin qauna haka kikewa karatu ba" sai data sauke ajiyar zuciya sannan ta daga kai tana duban ummi anty zuhriyya,ta sake sakin murmushi

"Inason karatu sosai ummi,inason naga ina karatu a rayuwata" murmushi ummi tayi

"Karki damu daghter,zakiyi karatu in sha Allah,har sai kinji a karan kanki kin qoshi dashi" murmushin itama tayi mata tana kada kai

"Na gode ummi sosai,na gode" yatsanta ta dora saman lips dinta

"Shshsh,Allah xaki godewa,amma nikam na sha gaya miki karki sake godemin ko?" Saita rufe fuskarta da hannunta,ummi ta bita da kallo daga fuskarta zuwa cikinta daya fito cikin tausayi,wani irin mahaukacin girma yake,wata shidda amma saika tsammaci yayi watanni tara ko goma,abun har mamaki yake basu,hakan ya sanya likitan dake ganinta yace idan ta cika wata bakwai zai sake mata ultrasound scan a sake ganin lafiyar baby,duk da cewa tace bata jin komai,hakan shima yana alamta komai lafiya yake,don badon hakan ba da zata ga wata alama ko sauyi a jikinta.       Kusan ummi zuhriyya ce ta tayata qarasa hada kayan nata,tunda su nasu dama ba wani abu zasu dauka ba,tunda komai nasu yana can,banda ma zasu soma sauka ethopia din da babu abinda zasu dauka

"Duk abinda fa kikasan kina da buqata ki dauka abinki,don idan muka tafi din babu lallai mu dawo nan kusa,har sai sanda abbaa ya kammala abinda ya kaishi"

"Toh ummi" ta miqe tana sake laluba kayanta dakyau,dai dai sanda hisham ya callara qara,da alamu ya tashi a baccin da yake ne,ya samu babu kowa kusa dashi,da sauri ummi ta miqe

"Ga dam gidanki can ya tashi,bari na duba shi" murmushi tayi

"A shafamin kanshi,yanzu zan fito na wanke shi tas ko yaji dadin wasa da kyau" harara ummi ta jefa mata

"A haka da wannan turtsi billin naki" tayi daroya tana ficewa,ita kuwa murmushi ta saki,a hankali kuma murmushin nata saiya yanke sanda ta dora hannun nata saman cikinta,ta soma shafashi daga sama zuwa qasa,har yanzu bata ji qauna ko shaquwar da akan fada ba wai tun yaro yana ciki,bata sani ba ko tata qaddarar kenan?,ko kuma sai yazo duniya?,ko abinda mahaifi da ahalinsa suka mata ne ya danne wannan feeling din?,duka bata da wannan amsar.      Ƙoƙari tayi ta watsa wannan tunanin gefe,kamar yadda ta yiwa kanta alqawarin mantawa da komai,ta kuma fuskanci rayuwarta ta gaba,don haka ta miqe,taci gaba da lalubar sauran abinda yake da muhimmanci a wajenta tana hadasu waje guda gami da ci gaba da shiryasu a kwatin nata.       Washegari ana ya gobe zasu tafi wunin gida tayi tare da qannenta,sabanin daa a yanzu damuwarta kadan ce,ba kamar lokuttan baya da takanyi tafiya ba,saboda ta gamsu a yanzu da yanayin da suke rayuwa,yanayi mai kyau,wanda anty zuhriyya ta tsaya musu da gasken gaske,hakanan ko cikin gida ga mahaifinta taga wasu sauye sauye da bata zata ko tsammata ba,duk da tayi mamaki amma ta barwa Allah lamarinsa.       Bayan la'asar ne,ta idar tana saman abun sallar hannatu ta qaraso gabanta da baqar leda ta ajiye maya,bin ledar tayi da kallo tana duban hannatun,don bata gane ba,sai daya zauna sannan tace

"Kudadenki ne da aka baki ranar da kika dawo din nan?" Sai a sannan ta tuna da batun,ta miqa hannu a hankali ta daukesu gamida yaye ledar tana kallonsu,kudaden da suka zama tamkar fansa ga mutuncinta fansa kuma ga duk halin da zata tsinci kanta a gaba,badan Allah yaji qanta ba ya aiko mata ds uwa a gareta.      Maidasu tayi tamkar yadda suke sannan ta miqawa hannatu,tsayawa tayi tana dubanta,da alamu tana neman qarin bayani

"Kuyi amfani dasu keda sauran qannanki,ki kula da kanku" yawan kudin yasa hannatun ta dinga ji kamar ba zata iya dasu ba,sai suka zauna ita da bilkisun tana kwatanta mata yadda zasuyi amfani da kudin,da doguwar takards me cike da list,wanda hakan ya daukesu lokaci mai tsaho kafin su gama.       Suna gamawa din hannatu ta dubi bilkisu da idanunta wadanda suka cika taf da ƙwalla

"Ba shakka yaya me gado kin zama uwa kuma uba a garemu,jigon rayuwarmu,ba don ke ba bansan ya rayuwarmu zata kasance ba" saita qarasa fashewa da kuka,sanyata bilkisu tayi a jikinta tana rarrashinta,itama tana qoqarin boye tata qwallar

"Kowanne bawa yana qarqashun kulawar ubangijinsa ne,babu wanda yake rayuwa saboda wani na raye,ko babu ni zaku rayu,hannatu,a yanzun kin soma bin sahun 'yammata,tunda kinkai shekara ta sha biyar,ina horonki daki kame mutuncin kanki,ki kula da kanki da kyau,kada ki yarda rashin mahaifiyarki gaban idanunki yasa ki aikata abinda yake kinsan ba dai dai bane,gwargwadon iko nasan cewa na doraku bisa turba mai kyau,wanda kunsan dai dai kunsan kuma kasin haka,koda bani kusa daku in sha Allahu ba zaku rayu cikin tsanani ba yadda kuka rayuwancan karon,ki kula dakanki da qannenki,idan hauwa'u bata dawo ba har zuwa sanda zan dawo qasar nan,nayi alqawarin in sha Allahu zan nemo mana ita a duk inda take" sallama sukayi mai karya zukata,bata bar gidan ba sai bayan sallar isha'i driver yazo ya dauketa,tabar gidan cike da kewarsu.
********    ******    **********      Jeri gwanon motocin masarautar kaisa masu kyau tsari da daukan hankali ne suka ci gaba ratsawa manyan titunan garin kaisan,wanda zai sadasu da filin sauka da tashin jiragen sama dake garin.       Duk wani titi da motocin suka gilma sai an samu jama'a da zasu daga musu hannu gami da kyakkyawan fatan alkhairi ga adalin sarkin nasu,daya tamkar da dubu,basu damu da cewar yana ganinsu ko baya ganinsu ba,burinsu addu'o'insu da fatan alkhairinsu ya riskeshi a duk inda zashi.       A dai dai lokacin da yake xaune cikin motar data ɗarawa duka sauran motocin kyau da tsada,gefanshi kuma azeez ne zaune cikin shigar sarauta shima,yayi kyau har ya gaji da haduwa,duk da cewa baya cikin wannan mode din,amma duka yayi hakanne don ya faranta ran mahaifinsa,ya kuma kautar da idanunsa daga gano damuwa tattare dashi.       "Abdul'azeez" mai martaba ya  ambaci sunanshi cikin kulawa,cikin girmamawa ya amsa mishi

"Inason idan Allah ya bamu aron rai,na dawo daga tafiyar nan,zamu zauna da iyayen yarinyar nan 'yar wajen alh ibarahim,a tsaida magana me kyau kan aurenku,ya kamata zuwa yanzu a san inda aka nufa kan aurenka,bai kamata magajin sarki ya zaman bashi da future me kyau kan tara iyali ba..." Ya qarashe maganar cikin raha,wanda sam bai lura da yanayin da fuskar azeez ta fada ba,ya dora da cewa

"Sannan idan karatun ya isheka hakanan,inaga ya kamata kayi magana,kawai sai nayi reforming kan dukiyoyina da kadarorina kaci gaba da gudanar dasu,na samu na huta hakanan nima na tattara hankalina kan abu guda,duk da ita kanta sarautar ta soma gundurata,amma munyi magana da mahaifiyarka kan haka...saidai nata ra'ayin ya nuna,kana da tarin kadara wadda ta mallaka maka ita da mahaifinta,da kuma nawa wanda nake saka ran miqa maka su,tafi sha'awar ka gudanar da taka,ta yadda zaka ci gaba da tashi cikin hazaqa kishin kai neman na kai da sanin ciwon nema,duk da hasashenta na a bigire me kyau,amma dole ya kamata a duba wasu abubuwan,wanda duka ba damuwa bane,idan na zauna duk xamu tattauna kan hakan a samu matsaya" duka baice komai ba har sai da maimartaba ya kammala sannan yace

"Alla ya taimakeka,na gode bisa wannan zabi da aka yimin da kuma karramawa,ina da maganganu biyu masu alaqa da juna,zancan zuwa gidansu safwa....ina roqon alfarmar a dakata a yanxun sai zuwa nan gaba,maganar kula da harkokinka kuma Allah ya taimakeka idan Allah ya dawo dakai lafiya,saikayi tunani a nutse,ka zartars da dukkan abinda kaga ya dace"

"Allah ya bamu aron ran,amma meye dalilinka na tsaida maganar aurenka?,baka da labarin dukka 'yan uwanka nasa sun fidda miji?,inason wai da na hada aurenku dasu lokaci guda....amma...bansan naka tunanin ba,na baka lokaci,saidai kada ka bari ya tsawaita baka zomin da gamsashshen bayani ba"

"In sha Allah" ya fada yana lumshe idanu,a wannan qadamin da yake ciki baison ya sake qarawa kanshi matsala,baiyi solving ko daya daga cikin matsalolinsa ba tukunna.        Dai dai lokacin da anty zuhriyya da nata ahalin suka isa cikin filin sauka da tashin jiragen saman,duba daya zaka musu kasan cewa happy family ne,hatta da bilkisun yau fuskarta a sake take cike da walwala,idan ta tuna inda zasu,tana fata walwalarta ta dore,tana fatan tabar dukkan wata damuwa da matsala tata a kaisa,kowa janye da akwatinsa suka shige ciki,bayan driver ya ajjiyesu ya juya da motar zuwa gida.       Basu sake wata doguwar tafiya ba motocin nasu suka isa airphort din,suka samu wuri na musamman suka ajjiye motocin nasu,sanda maimartaba yake shirin fitowa sukayi kacibus da waalin kaisa,shi yadan kawo tsaiko saboda tsayawa gaisawa da sukayi,har aka soma screening na matafiya,ganin lokaci na shirin qwacewa yasa abdul'azeez matsawa bayan maimartaba cikin girmamawa ya sanar dashi,don haka basu sake jimawa ba sukayi sallama,maimartaba ya wuce ciki,abdul'azeez na take masa baya,bayan sun baro dukka dogaran a waje,don shi kadai zaiyi tafiyar,sai mutum daya da zai masa rakiya cikin amintattunsa.


No comments

Powered by Blogger.