Saran Boye 36-40
No. 36
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
_KAWATA INA KIKA KOYO HADADDUN CAKES DA GIRKUNA NE HAKA? KINGA ABINCIN NAN NAKI DA NAYI TAKE AWAY BABAN AMEER BAKIGA YADDA YAKE SANTIN SABA, KWANA BIYU INA GIRKI AMMAN NAKI DAI YAKE TA SANTI, YACE LALLAI KAFATA KAFARKI KI RAKANI INDA KIKA KOYO_
_TAB! LALLE MAMAN SUDEIS AN BARKI A BAYA, AI WAJEN *UMMU AYMAAN’S KITCHEN*!NA KOYO HADADDUN BIRTHDAY CAKES, SNACKS, DA ABINCIN YAN GAYU KE HARDA NA NAHIYAR KETARE.. BIKIN ADAMA KANWATA MA ITA NA BAWA ORDER TAYI MANA NA MUTANE DARI BIYAR.._
_LALLE AN BARNI A BAYA, WAI.. YANZU YA ZANYI NA KOYA DAN ALLAH?_
_SHA KURUMIN KI MATAR MIJIN TA.. UMMU AYMAANS KITCHEN TA SAKE DAWOWA DA KOYAR DA BIRTHDAYS CAKES AND DECORATIONS WANDA ZATAYI A KWANAKI 2, PRACTICAL CLASS , AMMA IDAN KINASON KOYA TA ONLINE NANMA ZATA KOYA MIKI._
_WAYYO ALLAH NA DADI..! YANZU YAUSHE ZAAI WANNAN BONANZA? KUMA NAWANE KUDIN?_
_NAIRA DUBU 6 KACAL WALLAHI, DUK ABUNDA YA SHAFI HARKAR BIRTHDAY CAKES AND DECORATIONS ZATA KOYAR_
_BA’ANAN TA TSAYA BA, AKWAI_ CAKE PARFAIT,
CUPCAKES
SAMOSAS
SPRING ROLLS
MEAT PIE DA DOUGHNUTS.
_DUKA TANAYIN NA SHAGULAN BUKUKUWA, TARON SUNA, DANA CI A GIDA DAN MOTSA BAKI, KE HARDA GIRKUNAN DA KIKESON KI KOYA NA NAHIYAR KETARE DANA NAMU GIDA NIGERIA._
_KAI NAGODE KAWATA, AWANE GARI TAKE NE?_
_FARKO DAI GA NUMBER WAYAR TA :08032964266_
_SANNAN TANA NAN KANO, UNGUWA UKU, LAYIN MAI FATA, ZARIA ROAD KANO._
_CLASSES DIN ASABAR DA LAHADI NE KAWATA WATO 5 DA 6 GA WATAN JUNE DINNAN. MAZA FADAWA SU UMMI DAKE KADUNA KICE ZATA KOYAR A ONLINE MA.._
_KAI AIKO NAGODE DA SANARWARKI KAWATA. SHIN TANA INSTAGRAM?_
_Eh SUNANTA:_
@Ummu_aymaan_kitchen.
_TANA TURA KAYANTA A KOINA A FADIN KASAR NAN, INGANCI, KYAU, RAHUSA, LAGWADA GA CIKA CIKI DON DADI SAI UMMU AYMAANS KITCHEN AND CATERING SERVICES_
No. 36
.............“Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku. Amma kuyimin afuwa idan ya kasance na shiga hurumin da ba nawa ba”.
Gaba ɗaya suka juya suna kallon bakin ƙofar har Nu'aymah data fara ganin dishi-dishi cikin idanunta.
Ba kowa bane mai maganar face ɗaya daga cikin amintattun almajiran baba malam mai suna Hamisu. Hamisu ɗan anguwar su Nu'aymah ne, hasalima maƙwaftan junane. Mahaifin su baba malam yayi zaman mutunci da girmama juna da kakansu Hamisu, dan takai harda ɗaukar nauyin karatun mahaifin Hamisun a wancan lokwcin. Sai dai ALLAH bai masa tsahon rai ba, dan ya rasu tun su Hamisu suna ƙanana sosai. Wannan dalilin ne ya saka zuri'ar gidan su Hamisu ta dawo ƙarƙashin kulawar zuri'ar ɗan Jibiya bisa wasulcin da ya barma ƴaƴansu su baba malam.
Tabbas baba malam ya cika wannan wasiyya, dan babu irin ɗawainiyar da bayayi da gidan su Hamisun, har takai Hamisu yana ɗaya daga cikin amintattun almajiransa da sukasan abubuwa masu yawan gaske da ya shafesa, kuma Hamisu har cikin gidan yakan shigo bisa yarjewarsa musamman akan aiko da wani abu cikin gidan idan babu ɗaya daga yaran gidan a tare da shi...
A fusace Yah Ab ya miƙe yana nunasa da yatsa. Har tdallaken kalma yake wajen faɗin, “Amma kasan wannan matsalace ta family da bata shafekaba ko malam. To ta yayama akai kai kasan cewar ana wannan zancen a gidan nan? da har zaka wani shigoma mutane tsulum batare da neman izini ba sai kace wasu sa'anninka. Wannan ma ai raini ne da keta haddin mutane”.
Nasir da shima baƙin ciki ya lulluɓe ya miƙe a fusacen yana cewa, “Tabbas maganarka gaskiyace Abdallah, mi zaisa ya.........”
“Kunga ya isa haka” baba malam yay saurin dakatar dasu ganin yanda Hamisu duk ya muzanta abin tausayi. Ya cigaba da cewa, “Tabbas yayi kuskuren shigowa kai tsaye, amma ina ganin mu bashi dama ƙila mu sami bakin zaren matsalar tamu. Hamisu ya akai kasan da wannan issue ɗin?”.
“ALLAH ya gafaeta malam ka gafarceni, tabbas nima a yanzu na fahimci nayi kuskuren shigowa babu izininku. Ba komai ya jawo hakanba kuma sai ɗunbin ruɗanin dana tsinci kaina a ciki. Abinda yasa kukaji zancen nan a gareni jiya da daddare na dawo daga inda ka turani kai saƙo. Duk da dare yayi sai naga ya dace nazo na kawo maka saƙon koda ban samu damar maka bayani ba. Da ƙyar ma na samu maigadi ya barni na shigo, to a lokacin dana shigone na samu duk jama'ar gidan a sashenka, na iskeku cikin tashin hankali shine na juya da saƙon gidanmu, sai da safe na dawo kawowa nakejin abinda ke faruwa bisa fahimtar da nai daga maganganun ku. Har fitarsu asibiti akan idonane, wlhy da farko naso ɓoyewa nima, sai dai tashin hankalin danaganka a ciki ne naga ya cancanci na bayyana abinda na sani kodan ka samu nutsuwar warware al'amarin yanda ya dace, ku fita daga ruɗani kuma”.
Duk da sun gamsu da jawabinsa Naser da Abdallah sai zabga masa harara sukeyi. Baba malam ya bashi izinin ƙarasowa ciki. Da ga ɗan gefe ya durƙusa, ya miƙama Abban Adawiya dake kusa da inda yake Envelope ɗin dake a hannunsa.
Amsa Abban su Adawiya yayi, batare da ya buɗe ba ya miƙama baba malam. Nuni baba malam ɗin yay masa daya buɗe kawai. Abban su Adawiya ya buɗe Envelope ɗin ya ciro hotuna dake a ciki guda uku. Ba ƙaramin razana yayi ba matuƙa, har ta kai yana dubawa hannunsa na rawa.
Hoton Nu'aymah ne da Yoohan, a ranar farko da tsautsayi ya saka shi taimaka mata lokacin da zata faɗi a ranar salla, har ta kaisa ga kissing ɗinta saboda baki data wage zata masa ihu. Sai rana ta biyu itama ranar daya musulunta. Saina ukun shima dai a ranar farko ne, ya ranƙwafa a kanta suna kallon juna.
Yanda baba malam yaga ɗan uwan nasa ya shiga wani haline ya sakashi zare hotunan daga hannunsa. A take jinsa ya ƙauracema kunnensa. Hakama ganinsa neman kuɓucema idanunsa yake neman yi. Saurin fara ambaton UBANGIJI yayi yana ƙoƙarin ajiye hotunan Abban Abdallah ya amsa. Shi kam ma na farko kawai ya iya kallo ya miƙama hajjo. Itakam ta jima tana kallon hotunan ko ƙyaftawa batayi, ta haka ne Nu'aymah da ke gani dishi-dishi ta samu damar ganin hotunan gaba ɗayansu a hannun hajjo.
Babu wanda ya lura da ita. Sai ganinta kawai sukai kwance ƙasa wanwar. A take falon ya sake rikicewa gaba ɗaya. Duk suka rufu a kanta banda Baba malam da Umm da ko motsi basuyi ba da ga inda suke. Hajjo ma da bata tashiba sai ta maida hotunan a Envelope ɗin batare da ta sake bama kowa ba. Sai ma miƙewa tai ta shiga bedroom ɗinta da su. Babu jimawa ta fito lokacin anata ƙoƙarin zubama Nu'aymah ruwa dan son aga ta farfaɗo. Sai dai kuma ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa.
Gidan ya sake cakuɗewa fiye da farko, sai da baba malam ya musu magana sannan suka ɗan nutsu. Tamkar bai damu da halin da Nu'aymah ke a ciki ba ya kalli Hamisu dake zaune tsuru-tsuru yana zare idanu. “Hamisu su waɗanan hotunan ina ka samesu ne haka?”.
Kansa a ƙasa yace, “Baba malam nine na ɗaukesu da waya gaba ɗaya”.
“Hakan na nufin komai ka gani kenan Hamisu? Ina nufin duk abinda ke a cikin hotunan nan a gaban idonka aka yisa?”.
“Eh wlhy duk na gani”.
“To miyasa baka taɓa sanar minba kuma?”.
Jimmm Hamisu yayi kafin yace, “Wlhy ina tsoron ɗaga maka hankaline, tare da gudun abinda zai iya zuwa ya dawo malam. Amma ka gafarceni nayi kuskure ”.
Nannauyan numfashin baba malam ya sauke. kafin a sanyaye yace, “Shike nan jeka abinka. na gode sosai”.
Godiya shima Hamisu yayi ya tashi ya fita.
Hajjo da duk kejin komai na neman kufce mata tace, “A kaita asibiti, koma minene sai a yisa da ga baya, ciki kuwa harda neman yaron shima. Da yawan mutane wannan suke tsoro ga taimako, shiyyasa bahaushe ke faɗin kasa mutun inuwa ya saka rana. Ko a fuska bazaka taɓa tunain yaron nan zai aikata makamancin hakanba duk da kuwa a farkon shigarsa jikinmu kafiri ne. Ashe ya lulluɓe mune kawai yazo jikinmu ya cutar damu, da alama dama yarinyar nan ya biyo bawai alkairin da muke tsammani daga garesa ba. To kansa yay mawa, ALLAH kuma ya saka mana da gaggawa indai muna da haƙƙi a kansa”.
A tare duk suka amsa mata da amin. Banda baba malam da yay wani ɗan murmushi ya ɗauke kansa kawai. Abdallah ne ya ɗauki Nu'aymah dake a sanƙame ya fita da ita bisa umarnin Hajjon.
_________________
An musu ƙarɓar gaggawa saboda halin da Nu'aymah ke a ciki. Musamman ma da suka sami mace ce Doctor ɗin dake dutyn lokacin.
A yanda suka ga likitocin na kai kawo ɗakin da aka saka Nu'aymah hankalinsu ya daɗa tashi sosai. Duk kuma sanda wani ya fito suka tambaya baya basu amsar komai yake wucewa da sauri. Tun suna ɗaukar al'amarin ƙarami har suka fahimci yanada girma sosai, dan Doctors har uku sun ƙaru bayan ta farko. Sai faman yin ƙus-ƙus kuma sukeyi a tsakaninsu.
Cikin ƙarfin hali Abba Musbahu ya dubesu yana faɗin, “Bayin ALLAH inaga idan yarinyar nan ta rasa ranta ne ya kamata ku sanar mana, dan kunata sake ɗaga mana hankali da rashin cewarku komai da kai kawon nan naku”.
Ɗaya da ga cikin likitocin ne ya sadda kansa ƙasa cikin girmamawa yace, “Ai mana afuwa malam, ba muna ɓoye muku komai baneba. Kawai muna akan aikine shiyyasa, amma insha ALLAHU zakuji komai nanda ƴan mintuna kaɗan”.
Shiru wajen yayi babu wanda yace komai, sai dai a zukatansu sam basu gamsu da zancen likitan ba.
★★★
Tunda aka fita da Nu'aymah asibiti baba malam ya koma sashensa. Zaune yake a study room ɗinsa saman wata kujera da ke ɗan lilasa idan yana kanta. Duk da rana ce ɗakin yayi duhu sosai kasancewar bai ɗaga labule ko guda ɗaya ba a ɗakin. Bai kuma kunna fitila ba sai ɗan hasken da ake gani kaɗan kasancewar na hasken rana. Kwance yake a jikin kujerar idanunsa a lumshe ya faɗa duniya mafi nisan zango a tunani.
Tun daga daren jiya har zuwa yanzun zuciyarsa a ruɗani take. Ruɗani irin wanda ƙwaƙwalwa bata iya rarrabe gaskiya da ƙarya, fari da baƙi, haggu da dama........
Motsin da yaji a kusa da shine ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar. Umm ce ya gani cikin ɗan hasken da ɗakin ke da shi. tsaye take a gefensa dafe da kanta alamar tana a cikin matsala. Zumbur ya miƙe ya riƙota ganin tana layi, ga hakki tanayi kamar wadda tayi gudu a cikin sahara.
Kujera doguwa dake a ɗakin ƙwara ɗaya kacal ya nufa da ita, ya kwantar da ita jikinsa sai tsuma ya keyi. “Jannat miya sameki?”.
Duk da halin da take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yay magana. Tasan ƙarfin hali kawai ya keyi tun jiya akan al'amarin nan, amma shima a ruɗanin yake. Hannunsa ta kamo da ɗayan hannunta, ɗayan kuma na akan ƙirjinta da ke mata azabar zafi tamkar zai buɗe.
“Sooraj inaji a jikina mutuwa zanyi, a wannan karon zuciyata bazata iya ɗaukar wannan al'amarinba. Abban Nu'aymah akwai ruɗani a cikin zancen nan, amma ni kaina na kasa banbance mai gaskiya tsakanin ƴarmu da likitocin nan. Idan da ace likita ɗaya ne ya faɗa sai muce ko haɗa baki akayi da shine, amma kaga harsu uku, ɗayan ma bamu santa ba tunda asibiti suka sameta. Sannan Sooraj a kwanakin cikin nan da aka ambata ya kasance jikin Nu'aymah ban taɓa ganin wani alama na mai ciki tattare da yarinyarta ba, babban tashin hankalina kuma shine tabbas watan da ya shige na azumi banga Nu'aymah tayi jini ba har suka wuce saudia, wancan watan kuma a farkon wata tayisa. Kasan dai ita jininta baya ɓoyuwa a gidan nan saboda lalurar da yake zuwa mata da shi. Sooraj na shiga ruɗani wlhy”.
Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba ɗaya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ɗagota yana kallon yanda take faman dafe ƙirjin nata har yanzun.
“Jannat bazaki mutuba, bana fata ki tafi ki barni cikin wannan tarnaƙin, nima zuciyar tawa ba iya ɗauka zatai ba. Ki daure dan ALLAH muyi imani da ƙaddara. Amma kamar yanda kike cikin ruɗani a wannan al'amarin wlhy nima haka nake a ciki. Na ƙiyasta duka zuwan Yoohan cikin gidan nan gaba ɗaya ban iya tunano ta yanda har ya samu keɓancewa da Nu'aymah ba. Wlhy zuciyata ta kasa yarda Nu'aymah da Yoohan zasu aikata wannan ɓarnar. Idan kuma nace ban amince sun aikata ɗinba yaya xanyi da waɗan nan hujjojin bayyanannu kuma Jannat? Ya ALLAH ka bayyanar da gaskiyar al'amarin nan koda a cikin Zukatanmu ne ya Rabbi”.
Haka sukaita hawaye har sai da baba malam ya fahimci Umm na neman rasa numfashin ta. Sake ruɗewa yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi da iya ƙarfinsa.
Hakanne ya jawo hankalin su Hajjo da ke zaune jigum-jigum suna jiran jin halin da Nu'aymah dake a a sibiti take a ciki. Har rige-rigen shiga sashen sukeyi, gashi duk mazan gidan sun wuce asibiti tare da Nu'aymah, dama baba malam ɗinne kawai ya rage.
A hankali inuwar mutum dake a jikin windown tana kallon su baba malam ta kafar labule ta janye daga wajen. Hakan yay dai-dai da fara shigowar matan gidan. Babu wanda hajijiya bata kusan kwasa ba ganin da gaske Umm bata numfashi, ga baba malam yau duk jarumtarsa da kawaici yana zirar da hawaye............
_____________★★★
A asibiti bayan sallar la'asar Doctors ɗin suka buƙaci ganin wasu a cikin su Abba. Su duka ukun suka shiga office ɗin, aka bar su Abdallah kawai a waje.
Sai da aka nuna musu wajen zama kafin likitar mace tai ɗan gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta.
Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a samu mafita. Muna da likitan da zai iya duba matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yau kwanakinsa goma sha ɗaya kacal da barin nan, sannan aikinsa yana da ƙa'ida bana waje ɗaya bane balle muce muku kai tsaye ga inda zaku iya samunsa. Amma yanzu dai in taƙaice zance matsayinku na iyaye a garemu masu daraja da kima bazamu iya ganin matsala a gareku ba mu kauda idanunmu, dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira amintaccen sa da ke a garin Lagos a yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne”.
Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “ALLAH yasa a dace” tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a cikin ransa da jin tausayin ɗiyar ɗan uwan nasu dama ɗan uwan nasu shi kansa fiye da ko yaushe a yau.
Kamar da wasa sai ga su Abbah sun shafe fin awanni bakwai amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu'oi a zukatansu har tsahon wani lokaci. Shigar lokacin sallar la'asar ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake fitowa suka sake zaman jiran tsammani.
Wata cikkakkiyar awa biyu suka sake sharewa gangariya, Abban Abdallah na ƙoƙarin miƙewa zuwa office ɗin Doctor ɗin nan mace mai suna Doctor Ai'sha yaji yaya ake ciki? sai ya hangota tana fitowa da ga office ɗin nata fuskarta washe da murmushi.
Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ƙofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo.
Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ƙarfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka iya ɗauka tsabar isa ce da izza ke ɗawainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka.
Kansa duƙe yake sakamakon file ɗin Nu'aymah da ke a hannunsa yana dubawa. Ya ɗan rame, hakan ya saka sake fiddo hasken fatarsa da ƙyawun da ALLAH yay masa. Ga wani annuri na hasken ibadar ALLAH tattare da shi, wanda ya sake ɗaukaka ƙwarjininsa da cikar haiba kai kace farin watane ɗan daren sha biyar. Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ɗin sun kasance Coffee color, sai farar shirt da ke a ciki babu necktie, dan maɓallan Shirt ɗinma kusan uku a buɗe suke.
Doctor Aysha na daga gefen damarsa duk da yaɗan zartata kaɗan a tafiyar kasancewar ya fita tsayi, da alama bayani take masa akan matsalar. Sai Solomon dake ɗauke da jikkarsa a hannu, da Doctor Sa'ad da wasu likitoci biyu da Nurse kusan huɗu na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abban Abdallah bai ga fuskarsa da ƙyau ba, dan har lokacin kan nasa a sunkuye yake ga file ɗin. A dai-dai ƙofar ɗakin da Nu'aymah ke ciki suka ja birki, su Abdallah da duk suka zuba nusu ido duk suka miƙe, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ƙofar ɗakin ya shige har lokacin hankalinsa nakan file ɗin.
Iya shi da Doctors ɗin suka shiga, yayinda Solomon da Nurses ɗin suka ja birki a bakin ƙofar.
Sai da ya ƙarasa gab da gadon da Nu'aymah ke kwance sannan ya ajiye file ɗin ya kai dubansa gareta, bai ganeta ba sam, saboda na'urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ɗan ranƙwafo kanta kaɗan ya kai hannu ya zare na'urar mai haɗe da oxygen. Ba ƙaramin tsirgawa zuciyarsa tayi ba, amma saboda son sake gaskta abinda yake tunanin sai ya zare Glasses ɗin idonsa da ya ƙara ƙawata fuskar tashi. ‘Kamar dai itace’ ya ayyana a zuciyarsa cike da kokwanto.
A fili kam sai yay saurin maida mata na'urar saboda ganin yanda ƙirjinta ke sama da ƙasa da sauri-sauri ga jikinta na vibration har gadon kansa na motsawa. Luuu ya ɗanyi da idanunsa ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi Doctor Aysha a ɗan faɗace ya ke faɗin, “Anyi matuƙar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman shiga matakin ƙarshe, ina mamakin yanda mutane suke abu tamkar basu san muhimmacin lafiya ba. Mtsoww!!. Su Iyayenta fa?”.
Dr Sa'ad ne ya bashi amsa da “Haka suke wlhy Doctor, sai kuma an mutu suce likitoci ne da sakaci bayan tun farko sune da matsalar su.........”
Cikin sauri Dr Aysha ta katse Dr Sa'ad ɗin dan bata son ya sake tunzura Dr Yoohan, “Ayi haƙuri sir, duk family nata suna waje, duk da kasancewarsu manyan mutane suna tare da ita tun ɗazun fiye da awa tara wlhy”.
Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Nu'aymahn, sai kuma yay azamar ɗauke kansa batare da nasan dalilin yin hakan ba. Juyawa yay zai fita. Doctor Aysha tai saurin ɗaukar file ɗin da ya ajiye su ka sake bin bayansa ita da su Doctor Sa'ad da ke ta faman cika yana batsewa saboda haushin kare dangin Nu'aymah da tayi.
Yanzun ma bai duba kowa ba a cikin su Abdallah yay wucewarsa. Duk da kallo suka sake binsa suma, yayinda Abban Adawiya yaso gane sa, sai dai baiyi magana ba jin suma su Abban Abdallah basu ce komai ba.
Da ga shi sai Solomon suka shiga office ɗinsa, komai ƙal yake, dan tunda Dr Aysha ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ɗin duk da dama ƙa'ida kullum sai an share an goge. Ƙaramin ɗakin hutun dake cikin office ɗin Solo ya ƙarasa. Ganin nanma komai dai-dai yake yanda yasan Yoohan ɗin na buƙata sai ya ajiye jikkar ya fito.
Tsaye ya iske sa yana ƙoƙarin zame rigar suit ɗinsa, har Solomon ɗin ya kai ƙofar fita ya tsinkayi muryarsa ya na faɗin, “Kiramin Dr Aysha”.
“Okay sir”.
Solo ya faɗa da sauri yana ficewa. Hanging ɗin rigar yayi bayan kujerarsa ta zama, sannan ya fara ƙoƙarin kunna Computer ɗin da ke a saman desk ɗin na sa. Yanda yay matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Aysha ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, dan tasan ba lallai ta samu amsa ba musamman a irin wannan lokacin da ta tabbatar hankalinsa gabaki ɗayansa nakan patient ɗin da ke jiran taimakonsa.
Batare da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin theatre yanzun, dan haka ku shiryata zuwa theatre room”. Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta ko mijinta. Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”.
Ɗan jimm Dr Aysha tayi. sai kuma komi ta tuna oho, ta gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice shi kuma ya miƙe ya nufi ɗakin da ke a cikin office ɗin.........✍
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 38
.............Duk yanda su Abdallah sukaso a tuhumi Yoohan tun a asibiti game da zancen Nu'aymah baba malam ya hana, hakama su Abba basu bada goyon baya ba.
Zuwa yanzu dai Yoohan ya fahimci alaƙar baba malam da patient ɗinsa. Ya kuma gane Nu'aymah. Sai dai taka maimai abinda bai gama fahimta ba shine hotunan da Abdallah ya kawo masa da tsantsar ɓacin ran da yake ganni tattare da samarin gidan su baba malam ɗin gaba ɗaya harsu malam ƙarami da ya fara sabo da su.
Bayan samun damar shiga ɗakin da Nu'aymah ke kwance da sukayi ɗai-ɗai suka dubata duk da bata farfaɗo ba baba malam ya tattarasu su duka suka bar asibitin. Dan Yoohan ya tabbatar musu ba'a buƙatar wani mai jiyya tattare da ita har sai ta farfaɗo.
Suna tafiya baifi da mintuna talatinba shima ya amshi key ɗin motar Dr Mubarak Solo ya jashi zuwa gidansu baba malan ɗin. Kamar yanda yay tsammani ya iske kowa a gida da alama ma zaman jiransa sukeyi. Omar ne ya fito yay masa iso har sashen Hajjo. Hajjo ce kawai a sashen sai su baba malam su duka. Omar ma yana shiga da shi fitowa yayi.
Duk da Hajjo najin haushin Yoohan sai ta danne ta amshesa da fara'a kamar ranar salla dasu Ahmad suka shigo da shi wajenta. Ta kuma kawo masa ruwa da lemo. Yaji daɗi kuwa sosai, tare da sake jin ƙaunar ƴar tsohuwar har cikin ransa.
Bai iya sakin jiki ya sha ruwan yanda ya kamata ba, ya ajiye kofin tare da sake nutsuwa yana jiran ji daga garesu.
Bayan shuɗewar shiru na wasu mintuna Abba Musbahu yay gyaran murya idonsa akan Yoohan da kansa ke a rissine. Ba bu wani kwalo-kwalo ya shiga zayyano masa duk abinda ke faruwa.
Sosai mamaki ya kusa kashe Yoohan, ya sake tsuke fuska yana girgiza kansa. Idanunsa da suka kaɗa sukai jajur ya ɗago ya duba baba malam, “Uncle ni a rayuwar turai da nayi ma ba taɓa aikata haka da wata mace da yardarta ba ma balle anan ƙasata. Nasan anyi hakane kawai don shiga tsakanin alaƙarmu, ko kuma kasancewata musulmi a yanzu. Sai dai kuma ko wanene bai samu nasara ba, dan babu wani ɓatanci da za'aimin koda yafi wannan da zai girgiza zuciyata daga barin bautama UBANGIJINA shi kaɗai. Ban musulinta domin kowa ba, ba kuma zan fita domin wani ba. Nasan zaku yarda da ni, Tunda har kuka yarda da dani alokacin da ba addininmu ɗaya ba ma, dan kuɗin nagartattun mutanene masu ƙyawawan zukata. Zan faɗa muku ainahin gaskiyar abinda ya faru”. Cikin nutsuwa da ɗacin rai ya bayyana musu tun daga haɗuwarsa da Nu'aymah ta farko har zuwa ranar da ya musulinta. Bai iya ƙarya ba tun yana kafirinsa, balle yanzun da ya ƙara sanin muhimmancin gaskiya a harshen ɗan adam. dan haka ko kissing ɗin Nu'aymah da yayi bai ɓoye musu ba ya faɗa. Ya ɗora da faɗin, “Zan koma asibiti yanzun insha ALLAH, na muku alƙawarin bincike akan cikin da akace itama ya zuba a jikinta, dan sam ni dai banga wannan matsalar tattare da itaba saboda ba akanta na fuskanci matsalarta ba. Amma zan kawo muku hujja a yanzu da yardar ALLAH”.
Gaba ɗaya sun gamsu da bayaninsa har Hajjo da Abba Musbahu ke fassarama maganar Yoohan ɗin dan da turanci yay bayaninsa.
Baba malam ya ɗanji nauyin zuciyarsa ya ragu sosai da bayanin Yoohan, a yanzu kuma hankalinsa ma yafi kwanciya da binciken Yoohan ɗin fiye da na likitocin farko. Sannan tunaninsa ya fara karkata akan wani abu da ban kuma.
Ko mintuna goma Yoohan bai ƙara a gidanba ya fice ya koma asibiti. Sam baiji zafin su baba malam ba akan wannan maganar. Sun ƙarama mutunci a idanunsa ne, haka yake son iyaye su kasance akan ƴaƴansu. Ya sake fahimtar addinin musulinci addinine abin koyi, domin yana ƙyamatar abinda wasu addinan su a wajensu ado ne, Wayewace. Hasalima zuciyarsa wani hasashe take masa daban akan wannan ƙullin da akai musu. Duk da bai tabbatar ba amma zuciyarsa na kinsa masa papa.
Tare suka koma asibiti da su Abdallah da har yanzu su dai basu wani gamsu da Yoohan ɗinba.
Shi da Doctor Aysha suka gudanar da duk wani bincike akan Nu'aymah da har yanzun tana cikin halin sumar allurar da sukai mata. Dr Aysha ta tattara komai zuwa lab ta danƙama wanda ta aminta da shi. Daga haka ta dawo ta sanarma Yoohan.
Kansa kawai ya iya ɗaga mata, dan yana lafe jikin kujerarsa ne idanunsa a lumshe. Fuskar nan tasa kuwa a tsuke take matuƙa. yana cigaba da nazarin komai dalla-dalla. Babu abinda ya iya taɓukawa a wannan yinin sai zuwa salla idan lokaci yayi da leƙa Nu'aymah da suke tsumayen farfaɗo warta a kowane irin lokaci.
Misalin ƙarfe biyar saura na yamma Dr Aysha ta kawo masa duk results ɗin bincikensu. Ko buɗewa baiyi anan ba ya miƙe da shi ya fito, su Abdallah da suka zame masa bodyguard shi da Nasir da Ahmad biye da shi.
Har zuwa yanzun su baba malam duk suna gida suna jiransu. Yanzun dai saɓanin ɗazun, duk mazan gidan ne suka taru banda ƴammatan da yaran da su Umm, dan hajjo ce kaɗai mace ma a cikinsu. A maimakon Yoohan ya buɗe yanzun ma sai ya bama Abdallah damar buɗewa dan ya tabbatar musu zai gane.
Tun a result ɗin farko Yoohan yaji saɓanin abinda yay tsammani. Hakama sauran ƴan gidan, aka tafi na biyu dana uku, Abdallah baima ƙarasa na ukun ba Yoohan ya miƙa hannu a hankali ya zare file ɗin da takardun results ɗin ke a ciki yana binsu ɗai-ɗai da kallo. Tabbas babu ƙarya dai-dai Abdallah ke faɗa. Dan kuwa duk Results ɗin sun nuna Nu'aymah tasan ɗa namiji, ta kuma ɗauki cikin sati shida da wasu kwanaki, cikin kuma tayi ɓarinsa kwana biyu kenan.
Dimmm kan Yoohan yayi na ɗan wani lokaci, sai kuma ya sake duba duka takardun sannu a hankali. Su baba malam dai babu wanda yay magana sunata binsa da kallo. Sai Abdallah ne da Naseer ke jifansa da wani mummunan kallo tamkar zasu hau kansa da duka.
A harzuƙe Abdallah yace, “Yanzu kuma wace ƙarya zakai mana dan ka kare kanka?”. Yay maganar yana riƙo rigar Yoohan.
“Abdallah!!!!” Abbansa ya daka masa tsawa yana miƙewa. Ransa a ƙololuwar ɓace yace, “Sake sa”.
Kamar Yah Ab ya kashe Yoohan haka yakeji, amma kasancewar an musu tarbiyyar jin maganar magabatansu sai ya saki Yoohan ɗin da shi sam hankalinsa ma bawai yana tare da su baneba. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta shige a wani sabon nazari ne. Ɗan hankaɗashin da Abdallah yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ɗagowar da zaiyi sai idanunsa suka sauka jikin Windown falon hajjo. Inuwar mutum ya gani, yay ma wajen kallon kusan seconds goma kafin wanda ke a tsaye ya farga ana kallonsa yay saurin barin wajen. A take kan Yoohan ya kawo masa wuta kasancewarsa mutum mai kaifin tunani da basira.
Kallon sashen da baba malam yake yayi, ya ɗanyi luuuu da idanunsa da haskensu ya ɗan sirka yana wani bahagon murmushi, kamar zai lumshe su sai kuma ya ɓuɗesu a hankali. Cikin muryarnan tasa mai kauri da amo data hadu da ɓacin rai a yanzun yace, “Uncle wannan tatsuniyar akwai marubucinta kusa da mu daf. Amma mizai hana ka bani damar yankar ticket ɗin fara game da shi? Dan ni bana wasa a saman ruwa tunda ba masinci bane. Nafi yarda da shiga ƙarƙashin ruwan kasancewata mai yawan bincike akan ma'adanai. Kasan masu iya magana kance idan ka hango biri bisa tsumagiyar reshe ba gangancine ya kaisa ba, tsabar ƙwarewa ce a iya hawan bisa. Ko zaka amince ka bani aurenta idan ta girma?”.
Kowa a falon sai da ya zaro idanu waje, harma da masu zabura. Nasir da Ya Ab kam ai dingangan suka tsaya akan ƙafafunsu tare da hassalowa lokaci guda kamar zasu haɗiye Yoohan da ko kallo basu ishesaba. Sai dai kafin su ƙarasa Abban Adawiya ya daka musu tsawa. Tilas suka ja burki badan rayukansu sunso hakanba.
A karon farko baba malam yay tattausan Murmushin da har haƙwaransa sai da suka bayyana. idanunsa ƙyam akan Yoohan. zamansa ya gyara da ƙyau yabi duk jama'ar falon da kallo, su Abban Adawiya ma duk murmushin sukeyi, hadda hajjo da malam ƙarami ke fassarama maganar yoohan ɗin.
Murmushi baba malam ya sakeyi a karo na biyu, kafin yace, “Yoohan maganar aure ba abin wasa bace a musulinci, dan haka bazan iya baka amsar bukatarka a yanzun kai tsaye ba. Amma kaje zanyi magana da ƴan uwana, duk hukuncin da muka yanke zamu sanar maka insha ALLAHU”.
Duk da Yoohan yaso samun amsar baba malam take a wajen sai kawai ya jinjina masa kai alamar ya amince da hakan. dan haka ya miƙe yay musu sallama ya fice abinsa yana jifan Naser da Abdallah da wani irin kallon na ban ƙyaleku ba kuma, kamar yanda suma suke binsa da kallon kishi da tsana.
A yanzun kam zamu iya cewa komai ya harmutse musamman a gidan su Nu'aymah. Dan tun bayan barin Yoohan gidan baba malam ya kasa zaune ya kasa tsaye da fashin baƙi akan kalaman yaron mai hikima. Kai kawo kawai yake a bedroom ɗinsa tamkar mai safa da marwa. Hakama Abdallah da Naser hankalinsu a matuƙar tashe yake, dan su dukansu suna tsananin son Nu'aymah har cikin ransu. Umm kam da hajjo bama a maganar halin da suka tsinci kansu a ciki. Umm ba maganar wa Nu'aymah ya kamata ta aura bane damuwarta. Abinda likitocin keta tabbatarwa ga ɗiyarta shine tashin hankalinta. Itace ta haifi Nu'aymah, itace tai mata tarbiyya, sannan a gabanta ta tashi har zuwa yanzu da ake akan rikicin. Tunda take da yarinyarta bata taɓa kamata da kuskuren sauka akan turbar tarbiyyar data ɗorata ba. To tayaya za'ace hakan ta faru? Kanta ya kulle gaba ɗaya, tama rasa wazata gaskta tsakanin likitoci da Nu'aymah. Dan zuciyarta taƙi aminta ƴarta zata aikata haka, to sukuma likitocin mizaisa su musu ƙarya? Ta yama zasu musu ƙarya bayan sun kasance daban-daban?.
A ɓangaren Yoohan kam yana fita yaci karo da Solomon. Bai wani zaman tunanin yanda akai ya biyisaba ko inda ya samo motar da yazo ɗaukarsa kawai ya shiga kusa da mazaunin driver.
A tsorace Solomon ya dubesa, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. saurin zagayawa yay mazaunin driver ya tada motar suka bar anguwar. Har suka isa hotel babu wanda yace uffan a tsakaninsu. Solo yay masa rakkiya har ɗakin da ya kama masa. Yana ganin ya shiga shi kuma ya koma da baya. Wayarsa ya zaro yay kiran papa. Bugu biyu kuwa Papa ya ɗaga saboda muhimmancin da Solo yake da shi a wajensa. Cikin girmamawa ya gaishe da shi, kafin suyi magana mai tsajo wadda bilyn ku bataji saboda da yare Solo ke magana. Sun kusa mintuna talatin sannan Solomon ya yanke wayar yana wani cizon lips da yin ƙwafa.
Ƙarar waya ce ta saka Yoohan dake zube saman gado idanu a lumshe ko takalmi bai cire ba buɗe idanunsa. Kasancewar ring ɗin daya sakama iyayensa da banne yasa ya fahimci papa ne. Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Ya saka a kunne batare da yayi maganaba.
Daga can Papa yace, “Yoohan kana lafiya?”. “Uhhm!” Yoohan ya amsa a taƙaice. Papa da keta ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Ni bansan lokaci daka fara zama maƙaryaci ba. Ni nasan dagajin muryarka akwai matsala ai, dan an kirani daga asibitinku an sanarmin duk abinda ke faruwa”. Kamar Yoohan zaiyi magana sai kuma yay shiru abinsa yana sake tsuke fuska. Takaici ya kuma kume papa, yace, “John kana jina kuwa?”. Yanzunma kamar bazai amsa ba, sai kuma ya nisa muryarsa a harɗe yace, “Papa inason nayi aure! Kuma ɗiyar Sheikh Sooraj Hashim jibiya zan aura, sai dai yarinyar ta cika ƙankanta”.
Wani irin bugawa ƙirjin Papa yayi a lokaci guda. Tamkar wanda aka ƙwaɗama guduma a saman kai ya miƙe zumbur da faɗin, “What?!. John! Are you Mad?!!”. Yanda papan yay maganar da tsananin tsawa ne ya saka Yoohan janye wayar daga jikin kunnensa yana matse idanu tam-tam. Sai kuma kawai ya yanke wayar yay wurgi da ita ta tarwatse ƙasa kamar wani zararre. Harya ɗan zabura zai miƙe sai kuma ya koma baya ya sake zubewa a gadon yana ambaton addu'ar da Manager Hamza Ibrahim da a yanzu suka sake zama abokai sosai ya koya masa. Ita ya shiga maimaitawa a cikin ransa. Cikin amincin UBANGIJI a hankali yaji ƙirjinsa ya fara rage nauyi, sai kuma wani irin barci ya fara fisgarsa a hankali.
Gaba ɗaya papa ya haukace a gaban abokansa da ƙanninsa. Dan suna a tare lokacin wajen wani meeting ɗinsu na manyan ƙauyensu, dan dama yaje ƙauyensu ɗinne tun jiya da daddare saboda meeting ɗin mai muhimmanci ne suka shirya yi.
Uncle Godwin ne ya kama hannunsa ya zaunar da shi yana faɗin, “Hah Friend. Please calm dawn ”.
Papa ya furzar da wani zazzafan huci jikinsa na wani irin tsuma, ya doka sandar hannunsa a ƙasa yana cizar lip ɗinsa na ƙasa da masifar ƙarfi. Da turanci yace, “Tayaya kake tunanin hankalina zai kwanta Godwin? Ko nauyin faɗamin Yoohan baijiba wai zai auri ƴar arewa, ɗiyar hausawa masu sallah?”.
Da sauri Uncle Mike yace, “Ah!Goshpower wani lokacin kana abu kamar ƙwaƙwalwarka baya aiki da kyau. kai nefa ka sanar min yaron nan ya sanar maka yana da manufa akan duk abinda ya keyi. Mizai hana ka amince masa ya aureta ɗin. Muma wata damace tazo hannunmu akan mahaifinta.....”
A fusace papa yace, “Sai kuma akace muku da ɗana kawai zamu iya samun wannan damar? Salon suje su maidashi mai salla, to ni......”
Saurin ɗaga masa hannu wani da suke kira Chief yayi da sauri. Ya juya maganarsa zuwa yarensu da ayanzuma bilynku bataji ba😪. Magana ya farayi kamar zai haɗiye harshenshi cikin maida gaba ɗaya hankalinsa ga papa. A mamakina kuwa sai naga gaba ɗaya papa ya nutsu yana saurarensa tamkar ƴan uwansa. A hankali na ga fushin papa ya fara sauka daga fuskarsa. Saima ya koma sakin wani mugun murmushi yana gyaɗa kai. Kafin ya miƙe cike da wani irin farin ciki ya rungume Chief ɗin. Suma sauran duk tsantsar farin cikinne ya bayyana a fuskokinsu. Da alama dai shawarar Chief ta zauna da ƙyau a zukatansu.
Tashi papa yay ya shiga neman Number Yoohan. Sai dai kusan kira goma bata shigaba. Canja akalar kiran yay ga Solomon.
Yoohan na kwance har yanzu a gadon Solomon yay knocking. Bai motsaba balle ya amsa masa. Shikuma Solo jin yayi har kusan sau huɗu babu amsa sai kawai ya tura ƙofar ya shigo. Ƙarasawa yay inda Yoohan ɗin ke kwance cike da tsoro da girmamawa yace, “Am sorry sir. Boss ne yace na baka waya”. Kamar Yoohan bazai tankaba ya watsar da shi. sai kuma zuwa can ya miƙa masa hannu alamar ya basa wayar. Yana bashi ya fice abinsa. Yoohan ya ɗora wayar a kunne batare da yayi magana ba.
Cikin sanyin murya papa daga can yace, “I am so sorry my son. Raina ne kawai ya ɓaci dan ina tsoron su canja min kai su cuceni. Amma kuma sai nayi tunani da sake tuna bayanin da kaimin kwanaki sai na fahimci kaima ba ƙaramin abune mai muhimmanci zai saka yin hakan ba. yanzu yaya kaso ayi to?”.
A karon farko Yoohan yayi wani munafukin murmushi ya kai hannu ya shafi sumar kansa har zuwa sajensa. Idanunsa ya buɗe a hankali ya sauke bisa frame ɗin da akai adon ɗakin hotel ɗin da shi. Magana ya farama papan nasa da yare cikin taushin murya.
To su dinɗin dinkum balkisu saina koma gehe kawai ina zare idanu dan anzo dai-dai wajen. Turancinma da yaya nake haɗosa nake masa fassara🙄😜🚶🏻.
Papa da Yoohan sun ɗauki lokaci mai tsaho suna waya. Dan har sai da na ƙosa kafin su kammala. Yanda naga Yoohan ɗin ya ɗan rage buyagin nasa ne ya sakani fahimtar maybe har sun gama tsara wani abune.
★★★★★
Kusan ƙarfe tara na dare Nu'aymah ta farfaɗo. Dr Sa'ad dake tare da ita dan duty ɗin dare ne da shi yay azamar kiran Dr Yoohan da har yanzu yana a hotel ɗin bai kuma waiwayar asibitin ba.
Cikin kuwa mintuna ƙalilan ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses da yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin hasken musilinci dake mamaye da shi. Tunda ya shigo asibitin baiyi magana da kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma'aikatan hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a ƙasa ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin. Shi dai Solomon na biye da shi kamar jela.
Ɗakin da Nu'aymah ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sa'ad da Nurses guda biyu dake a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna gaishesa. Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya miƙama Dr Sa'ad hannun sukayi musabaha shi kuma.
A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kan Nu'aymah ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne.
Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar saboda bala'in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Dr Yoohan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare glasess ɗin idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara ganesa ba.
Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta yunƙura zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, ‘Aushhh kaina!’.
Yoohan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba.
Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka Nurses ɗin nufarta da sauri tare da Dr Sa'ad. Yoohan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta ƙasan ido. Yanda duk sukaso Nu'aymah ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Yoohan ɗin ya sake dawo mata da komai cikin memory ɗinta, wanda hakan ke mata barazana cikin kanta tamjar ƙwanyarta zata tarwatse.
“Ku barta” ya faɗa a hankali tamkar ba shine yay maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika umarninsa, amma tausayin Nu'aymah fal ransu. Dr Sa'ad kam sai ƙoƙarin son riƙo hannun Nu'aymah data riƙe kanta da shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata..............✍
Ni dai nace ‘Hummm’.😶 inji mai tsoron gulma.
__________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
BARKA DA JUMA'A
No. 39
.............Ba Dr Sa'ad ba hatta Nurses ɗin da Dr Aysha dake ƙoƙarin shigowa da drip a hannu sai da suka kalli Dr Yoohan ɗin. Amma a mamakinsu ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba. Sai tura tattausan nasa hannun yay ƙarƙashin kan Nu'aymah da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman filon.
Da sauri ta sake buɗe idanunta, dan kusancin da suka samu gaba ɗayansu neman haifar da barazana yake a bugun Zucikatan su, cikin rawar jikinta daya ƙaru ta sake buɗe baki zatai magana, sai dai kuma hakan kamar da wuya a gareta. Dan saɓanin yin maganar sai hawaye sharrrr!! Suka fara bin kumatunta. Yanda damshin ruwan hawayen nata suka sauka bisa fatar hannunsa ne ya sakashi lumshe idanu yana wani jan numfashi da sassarfa. Sai kuma a hankali ya janye hannun nasa daga cikin kanta dama jikinta gaba ɗaya ya ɗan matsa baya kozaiji sauƙin yamutsawar da dukan gaɓɓan jikinsa ke masa.
Da sauri Dr Aysha tace, “Doctor akwai matsala ne?”.
Shiru mai amsa mata ba. Sai idanu da ya zubama Nu'aymah da jikinta ke vibration a hankali, har zuwa yanzun kuma riƙe take da kan nata da duka hannayenta tana ɗan mirginashi bisa filon. Kusan mintuna biyu yana kallon nata, kamar yanda su Doctor Aysha ke kallonsa a tsorace, kafin ya ɗauka file ɗin Nu'aymah yaja da baya daga gaban gadon. jikin Window ya koma tamkar halin da take ciki bai damesaba. Ya shiga buɗe shafukan takardun dake a ciki file ɗin yana bin rubutun ciki daki-daki da nazari a nutse.
Su Dr Sa'ad kam duk sun rikice, sai dai sun kasa fahimtar wane taimako ya dace su bata ne. Dawowar da yay gaban gadon riƙe da file ɗinne ya sakasu zuba masa idanu su duka. Ya ajiye file ɗin a saman drawer'n gefen gadon da take sannan yay magana a ɗan kausashe yana kallon Aymah. “Malama ki nutsu”.
Ai maganar tasa tamkar zuga Aymah ma ma tayi, dan gani kawai sukai tayi wani irin masifar zabura zata miƙe. Cikin sassarfa Dr Aysha ta ƙaraso ta tareta. Da ƙyar ta iya dannata saman gadon ta kwantar, duk da hakan kuma fisge-fisge takeyi har yanzun. Batare da Yoohan ya ƙara magana ba ya matsa jikin makunnar wutar ɗakin ya kashe. a take duhu ya mamaye ko ina. Wata razananniyar ƙara da ta amsa duka Word ɗin Nu'aymah ta ƙwalla. Duk firgita su Dr Aysha sukayi, dan haka suka shiga lalube a cikin duhu kowa na neman wajen ɓuya. Shiko yana tsaye ko gezau, duk da kuwa ƙarar tata jiyay tamkar zata tarwatse masa kayan cikin kansa. Lumshe idanu yayi ya buɗe a hankali sannan ya kunna wutar. Baiko kalli inda su Dr Sa'ad suka maƙalƙale ba ya taka zuwa ga Nu'aymah dake yashe a ƙasa alamar faɗowa tayi ƙasa.
Duƙawa yay yasa hannu biyu ya ɗauketa cak ya maida saman gadon, a kallo ɗaya zaka fahimci batama yin numfashi. Sai da yaja bargo ya lulluɓa mata sannan ya maida mata duka na'urorin da ke manne da kanta ɗazun. Juyawa yay yayima su Dr Aysha alamar su fita. Suna gaba yana biye dasu riƙe da file ɗin Nu'aymah.
★★★★★
Tun barin Yoohan gidan su Nu'aymah babu wanda ya sake samun nutsuwa. Musamman ma Naseer da Abdallah. Dan furicin Yoohan akan Aymah ba ƙaramin girgiza musu zukata yayi ba.
A yanzu hakama Naser ne zaune can bayan sashen samarin gidan. Waya ce mane a kunnesa alamar magana yake da wani. Muryarsa cike da rauni yace, “Ananah wlhy ina sonta, dan ALLAH karku bari wannan karon na rasata. A wancan karonma na haƙura ne saboda duk kun goyama Abdallah baya. Ni kuma banason abinda zai kawo rikici a cikin zuminci ta dalilina. Amma a yanzu wlhy babu abinda zai sakani na janye, dan ALLAH kizo kano, nasan Hajjo duk abinda kikace zatayi, dan kece ke sakata tayi abu koda bataso matsayinki na babbar yayarta”.
Shiru ya ɗanyi yana sauraren abinda take cewa daga can. Sai kuma naga ya saki lallausan murmushin daya sake ƙawata ƙyawun fuskarsa ta jinin katsinawa, ya kai hannu ya shafi kwantaccen sajensa da faɗin, “Na gode sosai Ananah, furucinki ya koremin dukkan damuwata da tashin hankali, wlhy ba cikiba ko ƴaƴa goma Zainab ta haifa ina sonta a hakanta, kema kuma shaida ce akan hakan Ananah”. Ya sake jim na saurare sannan yace, “To nagode sosai, sai kun iso”. Daga haka ya yanke wayar yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi. Yanaji a ransa insha ALLAHU a wannan karon ya gama mallakar farin cikin rayuwarsa Nu'aymah ya gama, musalta irin son da yakema yarinyar ɓata bakine, amma wlhy ko rantsuwa yay babu kaffara a cikinta yafi Abdallah son Nu'aymah.
(To masu karatu kun yarda😉😂?).
A can sashen su Abdallah kuwa Abdallah ne zaune a gaban Momy a karo na farko tun dawowarsa gidan, dan daya gaisheta baya ƙara ko minti ɗaya yake barin wajen. Tun tana damuwa da hakan harta zuba masa ido kawai da kaima UBANGIJI kukanta. A yau kan tun bayan watsewar kowa daga falon hajjo bai zame ko inaba sai sashen iyayen nasa. Momy na zaune a bedroom ya sameta. Ganinsa kawai tai a gabanta ya ɗora kansa bisa cinyarta yana hawaye.
Cikin tsoro da mamaki tace, “Abdallah lafiya kuwa?”. Da muryar kuka yace, “Momy wannna karonma zasu rabani da ita. Wlhy ina sonta, dan ALLAH karki bari su rabamu, itama tana sona Momy”. “Ikon ALLAH Nu'aymahr dai?”. Da sauri ya gyaɗa mata kansa, kafin ya shiga bata labarin duk abinda ya faru yanzu a falon hajjo.
Cike da al'ajabi Momy tace, “Nikam wannan lamari da ɗaure kai, har raina zuciyata ta kasa aminta da zancen likitocin nan akan Nu'aymah. To amma yanda duk bakin nasu yake zuwa ɗaya ne zai sakama kowa ruɗani, sannan shi kuma yaron yanzun yazo da batun cewa zai aureta. Kodai....? Kai ina ba haka bane, hakanma bazata taɓa faruwa ba”. Ta ƙarasa faɗa tana girgiza kanta.
Abdallah yace, “Momy wlhy koma hakan gaskiyane ni inasonta a hakanta, ƙilama fyaɗe yay mata”. Murmushi Momy tayi a karon farko, tace, “Humm Abdallah zuciyata na hasashen abubuwa da yawa a gidan nan, sai dai bazan furtaba har sai zargina da zatona sun zama gaskiya a idanun kowa”.
“Momy kamar ya?”. Abdallah ya faɗa da sauri yana kallonta. Kanta ta girgiza masa. “No, bazaka ganeba share kawai. Yanzu kai da kake batun auren Nu'aymah su Adawiya daka yima aika-aika fa? Kasan kowa a gidan nan ciki yake da kai harni wlhy. Abinda ya hana ace maka komai wannan tashin hankalinne kawai. Abdallah kodai ka fara shaye-shaye ne bamu sani ba?”.
“Momy shaye-shaye kuma? Ni ban fara shaye-shaye ba wlhy. Kawai dai na rushe katangar da sukace itace zata hanani mallakar burina ne, kema kin sani momy Nu'aymah farin ciki nace, da sonta na fara sanin kaina, tayaya lokaci ɗaya za'ace za'a ruguzashi. Itama tana sona. Batason a rabamu”.
“Nasan duk haka Abdallah, shawarar da zan baka kawai kabi komai a hankali, ka kuma saka a ranka wani ramin rijiyar yafi gaban tsallakawa saboda faɗin baki, a kuskure kaɗan zaka iya afkawa ciki ka halaka. Zan tayaka da Addu'a, insha ALLAH kai da Nu'aymah sai kunyi farin ciki. Daga ni har mahaifinka kuma sai inda ƙarfinmu ya ƙare wajen ganin ka mallaki Nu'aymah a wannan karon kodan samun farin cikinku kai da ita”.
Sosai yaji daɗin kalaman mahaifiyar tasa. Yay mata godiya sannna ya fice daga sashen cike da ƙwarin gwiwa.
________★★★________
Baba malam na zaune a falonsa hannunsa riƙe da Littafin gawurtaccen barubucin malamin addinin nan Sheikh: Salihu bn Fauzan bin Abdallahil Fauzan yana dubawa, sai dai sam hankalinsa bama ya tare da fahimtar abinda littafin ya ƙunsa. Karantawa kawai ya keyi. Kiran da akaima wayarsa ne a karo na biyu ya saka Umm dake kwance cikin kujera idanunta a rufe an cire mata drip ɗin da aka saka mata kallonsa. Ganin sam bama yajin kiran wayar ya sakata miƙewa a hankali zaune. Hannu ta miƙa ta taɓashi.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke da juyowa ya kalleta da sauri, sai kuma ya maida ga wayarsa data nuna masa da hannu. Sake sauke numfashin yayi, ya gyarama Muhammad dake kwance jikinsa yayi barci kwanciya, sannan ya ɗauka wayar dai-dai ta tsinke. Ganin wanda yay kiranne ya sakashi kiransa babu jinkiri. Sai dai kuma bai ɗaga ba harta tsinke shima, tana tsinkewa kiransa ya sake shigowa wayar baba malam ɗin. A karon farko baba malam yay ɗan murmushi, wannan ɗabi'ar Yoohan ce, baya taɓa yarda baba malam ya kirashi sai dai shi ya kira. Koda kuwa baba malam ne ya fara kiransa zai bari har sai ta katse sannan shi ya kirasa.
Kamar yanda ya saba cike da ladabi yayma baba malam cikkakkiyar sallama da harshensa da baya fita da kyau. Baba malam ya amsa masa da kulawa tamkar yanda ya saba, bazaka taɓa cewa wani abu ya faru tsakaninsu ba. Gyara zama sosai Yoohan ya sakeyi a kujerar office ɗinsa kafin ya farama baba malam ɗin bayani a nutse.
“Uncle Alhmdllh patient ɗin ta farfaɗo, sai dai kuma.......” Sai yay shiru kuma. Cike da dauriya da kawaici irin na baba malam yace, “Yahya! Sai dai me? Karkaji komai kai min bayani akan duk halin da Nu'aymah take, domin UBANGIJIN daya jarabceta a wannan yanayin ya fimu sanin dalilin hakan, ita rayuwa da ƙaddara duk suna cikin kundin jarabawa ne, mai ƙarfin imani da ƙwaɗayin rahama ne kuma kawai ke iya juriyar cinyesu komai tsanani da zafin da sukazo masa da shi. UBANGIJI ya fimu sonta ai, bai kumayi shawara damu ba sanda ya bamu, idan ya ƙarɓeta a yanzu sai dai mu gode masa da ni'imar da yay mana na samunta tsawon shekaru sha bakwai a gabanmu. Dan haka faɗamin kawai”.
Baki Yoohan ya cika da iska ya fesar, zuciyarsa da ruhinsa na ƙarajin ƙauna da son baba malam har cikin jini. A komai nasa yana fatan yin koyi da baba malam. Cikin harshen turanci yace, “Uncle tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin matsalarta bane kamar yanda nai maka bayani ɗazun kafin mu taɓata. Aikin da mukai mata zai bata taimakone kawai wajen hana ƙwaƙwalwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata raɗaɗin da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha ALLAHU zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ɗaukar kamar watanni biyar kafin ai mata aikin gaba ɗaya, dan dole sai an fita da ita waje, a ƙasarnan bamu da isassun kayan aikin matsalarta, koma muna dasu zaka samu bana zamani bane tunda shuwagabannin namu bawai hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ɗaya ne insha ALLAH, inba hakaba zata iya loosing memory ɗinta a koda yaushe”.
Ɗan rumtse idanu baba malam yay yana ambaton sunayen ALLAH, muryarsa da ƙoƙarin jarumta yace, “Shikenan Yahya, duk yanda kake ganin ya kamata akai kayi tunda aikinka ne, yanzu zamu iya zuwa mu ganta?”.
Ɗan jimm Yoohan yayi, kafin yace, “Eh to amma karkuzo da yawa dai”. “Babu damuwa”. Baba malam ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.
Batare da kowa ya saniba a gidan Umm da baba malam da Hajjo suka tafi asibiti duba Nu'aymah. Yoohan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu rakkiya har ɗakin da Nu'aymah ke kwance. Ba ƙaramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan Aymah da na'urori, Hajjo da Umm harda hawayensu. Basu wani jimaba suka fito. Office ɗin Yoohan suka sake komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka masa albarka da jera masa addu'oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Nu'aymah zata iya farkowa a kowane irin lokaci.
Zamansa babu jimawa Solomon ya shigo ɗakin ɗauke da takeaway da yayo masa acan hotel ɗin da suke sauka. Dan idan yazo kano abincin can kawai yake ci, sai ko yanzu da suka haɗu da su baba malam. Ganin yana waya ya saka Solomon komawa gefe ya tsaya yana sauraren yanda Yoohan ɗin ke wayar a nutse.
Magana suke da wani likita abokinsa dake a ƙasar Canada. Yana buƙatar a aiko masa da wasu allurai ne masu matuƙar tsada da zaima Nu'aymah amfani da su. Kuma yana buƙatar sune da gaggawa daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu. Shine suke maganar ta yanda za'a kaisu airport ɗin ƙasar a damƙawa wani abokinsa matuƙin jirgi da Yoohan ɗin yasan kayan zasu iso yanda yake fata. Sai da suka kammala maganarsu har Yoohan ɗin yayma Dr Androi transfer ɗin kuɗaɗen allurar take anan masu yawa daga asusunsa sannan ya ajiye wayar.
Solomon dake kallonsa cike da takaici da mamakin ganin kuɗin daya biya na alluran tamkar baisan ciwonsu ba yay saurin faɗin, “Good evening sir! Ga abinci na amso maka, naga bakaci komaiba tun breakfast ɗin safe”.
Ɗan luuuu da idanu Yoohan dake miƙewa yayi, kamar zai lumshesu sai kuma ya buɗe su akan Solomon ɗin. “Karka damu banajin yunwa. Haɗamin coffee kawai is ok for me”.
Ganin yanda ya tsuke fuska sosai ya saka Solo amsa masa da “To” kawai. Cikin bin umarni yayi masa yanda ya buƙata, acan rukunin kujerun office ɗin daya koma yana aiki a lap-top yaje ya kai masa coffee ɗin. A hankali yace, “Thanks”. Shiru office ɗin yayi na wasu mintuna, Yoohan nata aikinsa da shan coffee kamar ya manta da Solomon. Sai kuma ya ajiye kofin ya ɗago yana kallon solo ɗin. “Kaje ka kwanta, basai kazo nan da safe ba, inaga zuwa dare zamu wuce Abuja, sai ka mana booking ɗin jirgi”.
Cike da girmamawa yace, “Okay sir”. Daga haka yay masa sallama ya fice.
Solomon na isa hotel ɗin wayar Papa ya fara kira. Ba a ɗauki lokaciba kuwa ya ɗaga. Bayani ya shiga yimasa da yarensu wanda sam ban fahimci akan minene ba. Sunja lokaci mai tsaho suna wayar sannan ya kira madam Chioma itama. Itama ɗin dai magana sukai ta tsahon lokaci da wani yaren ba irin wanda sukai da papa ba. Batun yau ba na fahimci Solomon najin yare ba ɗaya ba. Kamar yanda na kula shima Yoohan ba yare ɗaya kawai yake jiba bayan turanci. Shiyyasa a lokuta da dama nakan gaza banbance shin su wane yarene wai?.
*_WASHE GARI_*
Washe gari da safe ƴan gidan su Nu'aymah sukaje asibitin suka duba Nu'aymah data sake farfaɗowa. Sai dai har suka gama abinda zasuyi suka taho basuga Yoohan ba. Yana office yana duba marasa lafiyar da suke da tsananin buƙatarsa duk da da da farko baiyi niyyar hakanba.
Suna dawowa gida kuma suka iske baƙin da basu san da zuwansu ba. Kakar Nasir data haifi babansa ce tazo daga katsina mai suna Hajiya Hassana. Sai dai suna kiranta Ananah, yayar Hajjo ce uwa ɗaya uba ɗaya, wadda ita kaɗai ce ta rage mata a duniya. Hajjo na tsananin girmamata dan itama tana ƙaunar hajjon, batason abinda zai taɓa hajjo da zuri'arta, ta zame mata tamkar uwa da uba. Itama ta tsufa sosai fiye ma da Hajjo, sai dai da yake ALLAH ya basu lafiya sosai ga jin daɗin rayuwa, ko ina suna zuwa, garama hajjo tana fama da ciwon ƙafa. Ananah kuma idanuntane dan sai da galashi take gani da ƙyau.
Tare take da jikokinta da yaranta biyu ƙannen mahaifin Nasir ɗin mata. Dama duk babbar salla anan take salla kano, ita kuma hajjo sai gab da azumi take zuwa mata can katsina tai kamar wata guda. Hakan na sakasu farin ciki sosai.
‘To yanzu kuma Nasir ya ɗaɗɗago Ananah akan batun Nu'aymah. Ko yaya zata kasance?. saimu bisu muga wane mai rabo ne zai ɗauki wannan allurar ta cikin ruwa😉?’.
Ba ƙaramin farin ciki hajjo dama duk jama'ar gidansu Nu'aymah sukaiba da zuwan Ananah. Dan yanda take son kowa a gidan haka kowa ke sonta da ƙaunarta har surukan Hajjo. Take gidan ya rikice da murna dan duk tunaninsu ta iso da wurine saboda bikin su Kubrah nan da kwanaki goma. Ciwon Nu'aymah ne ma yaɗan sanyaya shirye-shiryen da akeyi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya abinci gabansu kala-kala daga kowanne sashe. Da mamaki Ananah tace, “Wai ni banga ƙawalliyata ba ita?”. Kowa yasan Nu'aymah take nufi. dan suna shiri sosai-sosai da Ananah, saboda Nu'aymah nada sunan hajjo ma take cemata ƙawalliya.
Rufaidah ce tai caraf ɗin cewa “Ananah tana asibiti babu lafiya” a rikice Ananah take tambayar, “Asibiti kuma? Miya sameta ni Hassana ɗiyar malam Haruna”. Shiru kowa yayi ya gaza bada amsa. Sai hajjo ce tai ɗan murmushi da cewar, “Ciwonta ne ya motsa, amma Alhmdllh da sauki ma”.
Cikin jimami Ananah ta share ƴar ƙwallar data taru mata a ido, tace, “Kai duk wanda yay sanadin shigar wannan yarinya a bala'innan yayi asarar rayuwarsa wlhy, ALLAH ya saka mata, ko wanene kuma ALLAH ya hanashi farin cikin duniya dana lahira”.
Kusan a tare duk falon suka amsa da amin.
★★
Bayan sallar magriba Ananah sukaje asibiti suma suka duba Nu'aymah, a lokacin Yoohan yaje airport amso saƙon da aka aiko masa daga ƙasar canada. Hakan yasa har suka kammala suka wuce yanzunma basu haɗu da shi ba. Sai bayan wucewarsu da kamar awa guda ma ya dawo.
Kansa tsaye ɗakin da Nu'aymah take ya nufa. Solomon biye da shi ɗauke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya samu Nurse ɗin data gama gogema Nu'aymah dake barci jiki.
Da girmamawa ta gaida shi, Solomon kuma ya ajiye bag ɗin ya fice. Matsawa yay gaban gadon lumsassun idanunsa akan Nu'aymah da fuskarta tai wani irin fayau. Sai uban haske data ƙara tamkar mai yaron ciki. Ya kafe Laɓɓanta da sukayi wani irin jajur gwanin sha'awa, gashi taɗan tsuke bakin ya sake komawa mitsitsi.
Huci ya ɗan furzar ya janye idanunsa daga kallonta, yana faɗin ‘Bakin tsiwa’ a zuciyarsa. ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da ɗaukar bag ɗin da Solo ya ajiye ya buɗeta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya buɗesa sai ga ƙanƙara a sama tanata huci. a ƙasan ƙanƙarar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda bakwai ƴan ƙananu, yanda kwalaben suke ƴan mitsitsi sai ka ɗauka wani tarkacen banza ne. Nanko kuɗaɗene masu shegen nauyi zaune da ƙafafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu ciki ya fiddo ɗaya kawai.
Miƙama Nurse ɗin dake a ɗakin yayi, murya a daƙile yace “Kiyi mata allurar nan yanzun nan”. Amsa tayi da girmamawa. A gabansa ta buɗe syringe ta kwashe ɗan ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai cikin syringe ɗin. Shine ya nuna mata a inda zatayi. (A raina nace da idon Aymah biyu sai anyi ƙaramin yaƙin duniya na uku kafin ayi allurar na kuwa🤣).
Mintuna uku ba'a rufa dayin allurarba wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ƙofar gashi ta jikin Nu'aymah. Kafeta da kallo Yoohan dake zaune ƙafa kan ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji yayi. Yanda take wani irin mutsu-mutsu kamar macijiya mai tsohon ciki ne ya sakashi sakin wani tattausan murmushi daya ƙawata cikar haibarsa da kwarjinin bautar UBANGIJI. Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta yana jan ajiyar zuciya.............✍
‘Saura naji wani yace ɗan kaɗan ne😣😒. Da gobe saina ƙara rage mudu🚶🏻😑😚’.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
*Ga breakfast nan aci a hankali har dinner ɗin gobe idan ALLAH ya kaimu sai ku ɗumama😎😁⛹🏻♀️*.
No. 40
............Ƙarfe sha ɗaya na dare Yoohan da Solomon suka bar kano zuwa Abuja. Tafiyar da bata kulle awa guda ba jirginsu ya sauka. Sun iske guards ɗinsa tuni suna a airport ɗin ma, dan haka basu ɓata lokaciba wajen wucewa gida.
Kamar yanda yay tsammani ya iske gidan nasu shiru, alamar duk sun kwanta, madam Chioma kawai suka iske a falo zaune cikin kwalliyar riga da wando da sukai mata ƙyau sosai. Yanda ta zubamasa ido haka shima kallonta yake babu yabo babu fallasa. Cikin takun nasa ya ƙarasa gareta, itama sai ta miƙe tana mai buɗe nasa hannayenta alamar yazo gareta.
Gabanta yaje ya tsaya batare da ya shiga jikin nata yanda ta buƙata ba. Ya kamo hannunta ɗaya yana ɗan shagwaɓe fuska kaɗan. Cikin sanyin muryar da tabbatar da agajiye yake, da yarensu yace, “Mom na girma ni”.
Ɓata fuska tayi itama cikin wani yanayi, muryarta na harɗewa wajen fita tace, “Please my boy”. Karan farko ya saki lallausan murmushin da ya nema sumar da ita a wajen. Ya ɗora hannunsa na haggu saman tattausan sajensa ya shafa yana ɗan kauda idonsa daga gareta zuwa ƙafar benen dake a falon inda Miracle ke tsaye cikin kayan barci, ƙirjinta rungume da madaidaicin teddy bear ta wani kafesa da idanu tamkar zata haɗiyesa ta huta.
A hankali ya janyesu gareta yay wani luuuu da su kamar zai rufe sai kuma ya buɗesu yana sakin hannun Mom yaja baya. Hannayensa duka biyu ya ɗaga mata da faɗin “Sweet mom gudnit”. Kafin tace wani abu harya fara hayewa upstairs ɗin da ɗan sauran kuzarinsa batare da ya sake duban Miracle ba ya raɓa ta gefenta ya wuce.
Su duka da kallo suka bisa harya ɓacema ganinsu, mira ta share ƙwallar data cika mata idanu ta juya da gudu zuwa ɗakin barcinsu ita da joy. Wata malalaciyar harara Mom ta raka Mira da ita. Kafin ta taune lip ɗinta na ƙasa da ƙarfi zuciyarta na ƙuna fiye da yanda gangar jikinta ke tsuma.
Yoohan daya iske ɗakinsa kamar yanda yay fata komai fes bai wani zauna ba ya shige toilet. Bayan wasu mintuna masu ɗan tsaho ya fito jikinsa na ɗigar da raɓar ruwan wanka. Da sauri yaja ya tsaya ganin Mom zaune bisa sofa. A ɗan daburce yace, “Mom lafiya kuwa?”. Saurin ɗago idanunta dake akan wayarta tayi ta dubesa, dai-dai shi kuma yana ƙoƙarin saka farar t-shirt ɗin daya ɗauka. Miƙewa tai ta nufosa tana wani sakin tattausan murmushi, ta ɗauka ƙaramin towel ɗin daya fito da shi a hannu ta nufi sumar kansa alamar zata tsane masa gashinsa dake ɗigar da ruwa. Da ɗan hanzari yaja baya kaɗan yana tsuke fuska.
“Mom!!”
Ya faɗa aɗan tsawace. Jin a yanda yay maganar ne ya sakata tsayawa cak daga yin abinda tai niyya.
Da ɗan shagwaɓa yace, “Haba Mom! Miyasa kike son maidani baya ne kullum? Nifa ba Abraham bane ko Victoria Please”.
Ƙanƙance mayatattun idanunta tayi tana ɗan matsosa, cikin muryarta dake wani irin rawa tace, “Kaine kake ɗaukar kanka babba John! Ita uwa ɗanta kullum yaro ne a gareta. Ina sonka Yoohan fiye da yanda kake tunani, kai ɗin farin cikinane fiye da sauran ƙannenka”.
Ɗan lumshe idanu yay ya buɗe a kanta, ya ɗan sassauta muryarsa da fuskarsa dake a tsuke. Dan shi harga ALLAH bai fassara maganarta da komaiba face soyayyar ɗa da uwa. “Na sani Mom, nima ina sonku da ƙaunarku fiye da zato ke da papa da ƙannena. Amma Please ki ringa rage cewa zakimin wasu abubuwan. Bama ni ba ko Abraham ɗan shekara goma ba komai zaiso kimasa ba yanzun. Mun rigada mun girma, hidimar da kikai mana muna ƙanana ta wadatar uhmyim?”.
Yanda yay maganar cike da lallashi ne ya sake narkar da ita a wani irin yanayi mai wahalar fassara. Ta buɗe baki zatai magana aka turo ƙofar aka shigo. Gaba ɗayansu ƙofar suka kalla. Papa ne cikin kayan barci da alama ma ya fara barcin tashi yayi.
Cikin ƴar shagwaɓa Yoohan yace, “Yauwa papa Please kwashi matarka ku wuce dama ta sakani a gaba nikam”.
Papa dake bin Mom da wani irin kallo ya haɗiye yawu da yin guntun murmushi yana maida idonsa akan Yoohan ɗin da ya sake ƙwaɓe fuska. Muryarsa da alamun barci ya tashi yace, “Yaushe ka dawo?”.
Mirror Yoohan ya nufa yana faɗin, “Yanzun nan babu jimawa nazatama baka gida ai”.
Komai papa bai ceba ya kama hannun Mom suka fice yana faɗin, “Huta abinka sai da safe”. Suna fita Mom ta fisge hannunta da ga na papa tana kumbura kumatu. Baice mata komaiba yay gaba abinsa dan jin Yoohan yana sakama ƙofarsa key. Yasan ko mi zatayi bazai sake buɗe mataba kuma. A ransa kuwa mamakin yanda Matar tasa ke nuna tsananin so ga ƴaƴansu yakeyi. shi bai taɓa ganin mahaifiya mai ƙulafucin ƴaƴa irin Madam Chioma ba.
Yoohan kam koda ya kammala kimtsawa falo ya fito ya haɗa tea ya koma bedroom ɗinsa. Zaman sha yay zuciyarsa da tunaninsa duk na wajen Nu'aymah. Ji yay yana buƙatar sanin yaya take yanzun, dan haka yaja wayarsa ya nema Dr Aysha a karo na farko a rayuwarsa.
Ita kanta Dr Aysha ba ƙaramin mamaki tayi ba ganin kiran Dr Yoohan a wayarta. Abinda bai taɓa faruwa ba. Jikinta har tsuma yake wajen saurin ɗauka. Ta kara a kunne murya a narke tace “Hello! Doctor good evening”. Maimakon ya amsa mata sai cewa yay “Assalamu alaiki”. Idanu taɗan zaro waje jin sallama yayi, saɓanin da da sai dai ya ce maka hii. Itafa dama gaba ɗaya a wannan zuwan nasa abubuwa da yawa taga idan yanayi tamkar ba shiba. Shekaranjiya ma har ganinsa tai kamar ya fito massallaci......
Sallamar da ya sake maimaita matace ta katse mata tunaninta. “I'm sorry sir. wa'alaikissalam. Kunje lafiya?”.
“Humm”
ya faɗa a taƙaice yana lumshe idanu da kai kofin tea ɗin bakinsa. Sai da ya kurɓa ya haɗiye kafin yace, “Ya yarinyar nan ta farka ne?”. Ta gane Nu'aymah yake nufi, dan ita kaɗaice patient ɗin daya kwantar dai. Cikin sanyaya muryarta tace, “A'a har yanzu tana barci, amma an saka mata drip ɗin daka ce ɗin yanzun babu jimawa”. “Okay night” ya faɗa a taƙaice da yanke wayar batare da ya ƙara komai ba.
Nannauyan ajiyar zuciya Dr Aysha ta sauke tana ɓata fuska kamar zatai kuka. Akan laɓɓanta ta furta, ‘Ɗan wulaƙanci’.
Oho baimasan tanai ba, dan shi tea ɗinsa ya ƙarasa sha kafin ya miƙe ya nufi toilet. Alwala yayo. Ya saka sallayarsa sabuwa da baba malam ya bashi ya tada salla kamar yanda ya keyi yanzu a kowanne dare. Idan har ya samu dama yakan fara daga ƙarfe ɗaya ko biyu, zuwa uku sai yaɗan kwanta kafin asuba.
*_WASHE GARI_*
A gidan su Nu'aymah kuwa a safiyar yau bayan kammala breakfast ɗunguma sukai asibiti suka duba jikin ta, kamar ko yaushe basu duka aka bari suka shigaba. Baba malam ne kawai dasu Abba Musbahu. Sai hajjo da Ananah. Umm dama batajeba dan tanason zuwa gidan Gwaggo mahaifiyarta. Daga can zata biya asibitin tare da Gwaggon.
Basu jima a asibitinba suka dawo gidan, baba malam da ƙannensa uku da hajjo sai Ananah a falon hajjo suka yada zango domin tattaunawa. Sunyi zaman kusan awa guda sannan Abba Musbahu yay kiran Abdallah da Naser a waya. Ba a rufa mintuna biyarba kuwa sai gasu dan dama duk suna gida. Zama sukai inda Ananah ta nuna musu kowanne kansa na a ƙasa..
Fuskar baba malam a ɗaure ya dubi Abdallah, “Abdallah zan fara ta kanka, dan karka zata shirun da mukai maka kamar mun ƙyalekane bisa abinda ka aikata mana. Gani ga ƴan uwana ga Hajjo harma da Ananah. Inason ka faɗa mana dalilinka na aikata abinda ka aikata. Shin bamu da daraja a idanunka ne mu da muka baka auren yaranmu kokuwa raini ne dan kaga ka girma?”.
Cikin sauri Abdallah ya ɗago yana kallon baba malam ɗin da girgiza kansa. “Wlhy sam ba haka bane ba Abbah. Kuna da darajar da bayan MANZON ALLAH babu mai ita a idona a duk faɗin duniya sai ku”.
“Ban yarda ba Abdallah, inda ace munada wannan darajar da bazaka aikata abinda kayi ba. Mu aura maka yara ka sake mana su akan wani banzan dalilinka mara amfani”.
“Abba ku gafarceni, amma wlhy ina son Nu'aymah, son da zaku iya rasani idan kuka hanani mallakarta. dan ALLAH a wannan karon karkuce mani a'a”.
“Ba maganarta nai makaba ni ai, maganar yarana daka saki nake maka”.
Shiru Abdallah yay zuciyarsa na masa ƙuna da zafi mai raɗaɗi, sai faman haɗiyar zuciya yake kamar budiddigin ƙwaɗo. Ganin yaƙi cewa komai hajjo ta amshe zancen da cewa,
“In banda zancen banza taya dan kawai nayi maka magana zakaje ka aikatama yara wannan wautar, ina iliminka yake? Ina wayonka yake? Kaine fa babba a gidan nan, kuma ka tabbatar abinda ka aikata da shi na ƙasa da kai zasuyi koyi. Ta hakane zaka iya zama jagora uba garesu a randa ƙasa ta lulluɓe idanunmu mu da iyayen naka?”.
“Kiyi haƙuri hajjo”.
Ya faɗa muryarsa na zuga.
“Idanma banyi haƙuri ba dukan ka zanyi Abdullahi. Yanzu dai ka maida matanka, batun Zainabu kuma gaka ga Nasiru yanzun, sai ku sasanta kanku dan babu mai shiga a wannan karon. Duk wanda ya sameta a cikinku mu abin farinciki ne a garemu, kuma zamu saka albarka. Sai kuje ku nema yarda daga gareta, wanda duk ta zaɓa magana ta ƙare”.
Hukuncin hajjo yayma kowa dai-dai, sai dai banda Naser da Abdallah. Dan a kallo ɗaya zaka hango tsantsar tashin hankali cikin idanunsu. Lokacin da suke ficewa daga falon har tafiya suke kamar zasu kifa, musamman ma Abdallah.
*_ABUJA_*
Aɓangaren Yoohan kam yau da azumi ya tashi kasancewarta al-hamis. Azumin litinin da alhamis yana ɗaya daga cikin ibadar da tun bayan musulintarsa ta fara zame masa jiki. Bayan ya idar da sallar asubahi yay zaman yin azkar kamar yanda baba malam ya koyar da shi ta bidiyo kol da sukeyi a kullum. Sai dai kasancewar bai gama haddacesu ba sai yake karantasu a littafin. Sai da gari yay haske kamar yanda shari'a ta koyar sannan ya miƙe zuwa ɗakin motsa jikinsa.
Kamar yanda ya saba ya farayi yana haɗa uwar zufa, kasancewar kwana biyu bai samu damar yin na kirki ba a kano sai yau yaji jikinsa yay masa ɗan nauyi. Hakan ya sashi zarta lokaci kaɗan, dan har Solomon ya shigo masa da tatattun kayan itatuwa (fruit) bai kamalla ba.
“Good morning sir”
Solo ya faɗa yana ɗan risinar da kansa tire a hannunsa.
A taƙaice Yoohan dake ɗan hakki ya share zufar goshinsa da cewa “Same”. Da ga haka ya cigaba da abinda yakeyi. Shigowar Solo da kusan mintuna sha biyar sannan ya kammala, lokacin har an fara gudanar da program ɗinsa a NTA. zama yay Solo ya miƙo masa juice ɗin. Kai ya girgiza masa yana goge zufar dake tsiyaya masa da ƙaramin towel, yace, “Barsa kawai”.
Sosai Solomon yayi mamaki. dan a watan nan ya fara lura da wani abu daga ogan nasa. Duk monday and Thursday da wahala kaga yaci wani abu har yamma. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. Shima Yoohan ɗin bai sake tankawa ba, sai ma maida hankalinsa da yayi ga television ɗin gaba ɗaya. Ana kammala program ɗin ya miƙe, anan yabar Solomon na kimtsa ɗakin.
Tsaf ya tadda ko'ina Solo ya gyara, sai ƙamshi da sanyin ac dake ratsa ko ina. Toilet ya nufa yay wanka, ya ɗan jima a ciki kafin ya fito. Bashi da sha'awar fita ko'ina yau ɗin nan, dan haka body spare kawai ya saka da boxer ya haye gadonsa ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Cikin mintuna kaɗan barci kuwa yay gaba da shi.
A falo kam koda su madam Chioma suka haɗu dan yin breakfast kakarsa data haifi papa ce ta saka Destiny wai taje ta kira Yoohan ɗin. Sosai Destiny ta waro idanu waje. cikin yare tace, “Granny inajin tsoro gaskiya. Brother John baya son mutane”. Harara mama ta zuba mata, cike dajin haushi ta duba Madam Chioma. “Ai ga wadda ta watsa shi nan bai ganin kowa da gashi sai ita data haifesu. Yaro sai masifar taurin kai”. Banza Momy tai mata, sai mamanta ce ta karɓe zancen da faɗin, “Inma a bauɗen yake ai ba ita kaɗai ta bauɗar da shiba harda ɗanki. Debora ki daina sakama yarinyata baki akan rayuwarta fa, ni dama nasan masiface ta kawoki ba komaiba. dan kawai kinga nazo, yanda kikejin gidan ɗankine nima gidan inlow ɗina nen ai”.
Ai kafin kace kwabo sun hargitse da cacar baki kamar wasu kaji. Su dai jikokin duk idanu suka zuba musu kawai suna kallo da ƙannen papan dama momy ɗin kanta. Abun nasu zattakaici da dariya. Basuyi shiru ba sai da papa ya fito yay musu magana cikin damuwa.
Daga haka suka koma harar juna suna huci kamar wasu zakuna. Daga ƙarshe basuci abincin a Dining ɗinba sai dai kowa masaukinta ta koma aka kai mata nata.
Yoohan da baisan sunayi ba kam sai wajen sha biyu ya farka. Wanka ya sakeyi yay shiri cikin ƙananun kaya. Blue jeans da t-shirt fara ƙal an rubuta HERO da kalar blue a gaba. Ya gyara sumarsa da sajensa yanata zabga ƙamshi. Slippers masu taushi ya saka dan ba nisa zaiyi ba. Ya ɗauka wayoyinsa ya fito.
Da sauri Favour ta ɗauki remot ta rage kiɗan da suka saka a sifiku kamar zai tsaga falon lokacin da yake sakkowa. Fuska a matuƙar tsuke ya dubesu, baiko amsa gaisuwar da suke jera masa ba yace, “Wannan kiɗan da kuka cikama mutane kunne da shi fa?”.
Cike da tsoro Victoria tace, “Brother sai da nacema Favour karta kunna bakason ƙara da yawa, amma tace sai......”. Wani irin zabura Favour tayi ta danne bakin Victoria dan karta ƙarasa faɗa. Ba komai ta tuna ba sai marin da ya taɓa kashe fuskarta da shi ranar X-max ɗin last year da sukaje a ƙauye ya iske ta samu ciki. Cikin rawar murya tace, “Ƙarya take Uncle John, na rantse bance komai ba”.
Shi baimabi takansu ba ya fice abinsa saboda jin kakarsu data haifi papa na ƙwala masa kira da alama sunansa dasu Victoria suke ambata ta jiyo.
Da ƙafa ya fice a gidan bayan ya gaisa da ma'aikatan gidan a tsaitsaye. Can bayan layinsu ya nufa, inda yake ganin wani masallaci. Acan ya gabatar da sallar azhar, koda aka idar ya dawo gidan garden ya wuce kai tsaye. Babu kowa a ciki, sai sassanyar iskar dake kaɗawa daga ni'imar itatuwan cikin garden ɗin. Anan yay zamansa har la'asar tayi, kasancewar yanada alwalarsa massallacin ya sake komawa yayo sallar la'asar, ya cigaba da zamansa a ciki har zuwa biyar sannan ya fito.
Daya dawo ma bai shiga ciki ba, duk da kuwa Solomon ya sanar masa Momy nata zuwa nemansa tun ɗazun. Aika solo ɗin yay ya ɗakko masa key ɗin mota a ciki. Tare suka dawo da Miracle. Koda ta gaishesa sau ɗaya ya amsa ya ɗauke kansa, cikin damuwa ganin zai shiga motar tai saurin fada masa Momy tace yazo yaci abinci. Bai amsata ba sai da ya shiga motar mazaunin driver, dan ya hana kowa binsa. Kallonta yay sau ɗaya ya ɗauke kansa. “Ki sanar mata ina azumi”. Daga haka yay reverse ya fice a gidan.
Koda ta koma ta sanar ma madam Chioma sosai sukaita mamakin azumin mi Yoohan ɗin keyi? dan sunsan dai su azuminsu yanada lokutansa a addininsu. Ganin basu da mai basu amsa suka haƙura harya dawo gidan.
Yoohan kam koda ya fita wajen Hamza Ibrahim ya nufa, can suka haɗu gidan wani haɗaɗɗen abinci daya gaji da ƙawatuwa. Sun ɗan zauna kusan na mintuna talatin kafin a kira sallar magriba. Zuwa sukai sukayo salla suka sake komawa gidan abincin, anan Yoohan yay musu order ɗin abincin buɗa baki dan shima manager axumin ya keyi. Da wannan damar sukai amfani wajen sake faɗaɗa hirar tasu da duk ta kasance akan abinda ya faru a kano, wadda dama duk ya sanar masa ta waya. Hasalima shine ya bashi shawarar kawai yacema baba malam zai auri Nu'aymah ɗin koda a yanzunne. Shi kuma aranar bai wani ja zancenba ya amince da shawarar duk da a idanunsa yana ganin Aymah tayi ƙanƙanta da aure.
A fahimtar manager dai anya dama Yoohan ɗin ba ya na son Nu'aymahn bane kuwa?. Da yake baida mai bashi amsa sai ya watsar da zancen.
Duk yanda ake gudanar da bikin aure a musulinci da hidimar da hausawa keyi a al-adance manager ya sanarma Yoohan, dan haka basu rabu ba sai kusan goma na dare.
Koda Yoohan ya dawo a harabar gidan ya iske papa nashan iska. Zama yay a wajen suka tattauna abinda ya shafesu. Sai kusan ɗaya saura suka shiga cikin gida. A hakanma Yoohan ɗinne ya nuna ya gaji.
*_BAYAN KWANAKI UKU_*
A kwanaki ukun nan kullum sai Yoohan dake a birnin ikko yanzun sai ya kira Dr Aysha yaji yanayin jikin Nu'aymah da suka maida sumammiya, dan tunda ya bar kano a yanayin barci take, sai dai drip da ake ƙara mata a koda yaushe da allurai a ciki. Haka suke buƙata ta sami isashen hutu. Allurar kuma daya sa aka kawo masa daga canada tun wadda akai mata randa aka kawo ba'a sakeba. Dan ƙa'idar allurar sai bayan sati ɗaɗɗaya za'ayita, hakan yasa bai bama kowa ba ya ajiyeta a office ɗinsa a waje mafi sirri. Dan daga Lagos nan kano yake fatan dawowa ya duba Nu'aymahn. Kamar yanda ya sabarma kansa kuma kullum sai ya kira baba malam sun gaisa safe da maraice.
A gidan su Nu'aymah kuwa shirye-shiryen biki ake babu kama hannun yaro, dan yau saura kwanaki shida kacal a ɗaura auren su Hajarah. Da Abban su Adawiya yace a ɗaga har sai Nu'aymah ta samu sauƙi. Amma sai baba malam ya hana hakan. Ya ce babu abinda za'a fasa ALLAH zai bata lafiya itama.
Yayinda aketa shirin biki Abdallah da Naser ƴar tsama a tsakaninsu kullum sake faɗi da tsauri takeyi akan Nu'aymah. Gashi sun maida asibiti wajen yininsu duk da ita wadda sukeyi domintama batasan sunayi ba ma. Duk sunbi sun tashi hankulansu akanta. Yayinda Adawiya ita nata hankalin yafi nasu tashi. Dan har yanzu Abdallah yaƙi maida auren nasu. Su baba malam kuma babu wanda ya sake cewa da shi komai akan hakan.
Sosai Adawiya ta rame, kamar ba itace suka dawo ta zama lukuceciya ba. Tabi ta ɓoye kanta a gidan babu mai ganinta sai ƴan sashensu. Ita kuma Addah tayi kamar bama tasan halin da Adawiya ke a ciki ba. Dan tun lallashin datai mata na farko taki saurarenta saita watsar da ita bayan ta babbanka mata zagi da yi mata kaca-kaca.
Ƴan uwantane kawai da Umm ke tausayinta, dan Hajarah tamafi kowa damuwa da halin da Adawiya ta jefa kanta. Har kwatance take mata da yanda Yusrah tai kamar komai bai dametaba tanata harkokinta ita. Hakama Nu'aymah lokacin da aka rabasu aka bashi aurensu. Amma sam Adawiya taƙi fahimta. Sai bin hanyoyin da zatai magana da Abdallah takeyi shi kuma ya toshesu ya hanata kowacce dama. Gaba ɗaya ya maida hankalinsa ga takarar neman yardar Nu'aymah da take a rabin duniya da barzahu.
A washe garin da Yoohan ya cika kwanaki huɗu da tafiya su Papa sukazo kano shida ƙannensa da abokansa uku. Babu wanda yasan abinda ya kawosu. Shi kuma baba malam bai faɗama kowa ba sai ƴan uwansa da Hajjo da Ananah kawai.
Amma yanda Papa da gayyarsa suka koma ransu a ɓace zai baka tabbacin zaman baiyi daɗi ba. Dan shima baba malam ɗin dai ranar yini yayi babu walwala tattare da shi.
★★★★
Ana saura kwanaki huɗu ɗaurin auren su Kubrah Yoohan dake a birnin ikko har yanzu ya kira Dr Sa'ad ya sanar masa su tsagaita da yima Nu'aymah allurar barci haka nan, idan ta farfaɗo a kowanne lokaci a kirasa a sanar masa.
Haka kuwa akayi, ƙarfe kusan sha biyu na daren rar Nu'aymah ta farfaɗo............✍
_________________________
Leave a Comment